Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma cikin farinciki yace “Nagode, sunyi rankiyadade Allah ya kara girma”, sosai yake nanata yawan kudin a cikin zuciyarsa, Afrah kawai yake hangowa da tunanin yadda zai dinga faranta mata da wannan kudin na halak domin burinsa kenan ya ciyar da matarsa da halak .jin kudin yake kamar bai taba rike irinsu ba, bayan in banda canjin rayuwa meye dubu dari a wajen musaddik kudin da bai wuce ya ba da kyautarsu ba kullum.
Daga bisani Alh yusuf sanda ya mike yana dukan iska, sai dai fuskarsa dauke take da murmushin da shi kadai yasan dalili, ya shige cikin gidan.
Daga karshe su ma suka yi mata sallama bayan ta sanar da shi daga gobe zai fara zuwa aiki. Ta ba Alh Hamza dubu ashirin tace yasa mai a mota, duk kuma inda musaddik zai je ya tafi yaje ya sauke shi.
Ya jidadin kudin domin baima yi tsammanin zata bashi ko sisi ba, a ransa dai yace ya ci albarkacin musaddik ne.
Kai tsaye gida ya aje musaddik kamar yadda ya bukata.
Karfe takwas da rabi ne na dare, ko kadan babu wanda ya tsammaci dawowarsa a wannan lokacin, hakan yasa muryarsa da Haj kilishi ta ji yana magana da Baba maigadi yasa ta yi saurin dage labulen leken gulmarta, don ta tabbatar da shi ne, fuskarta ta canja bakinciki da takaici ya lullubeta, jin zuciyarta take tana bugawa. A fusace ta saki labulen, wai me ke faruwa ne? Kwana nawa kenan musaddik bai dawo gida a buge ba, yanayinsa ya fara canjawa ba taga kazanta a tare da shi ba, fes yake, yauma har wani wasa da dariya ta ga yana yi shi da maigadi, ta tsani ganin murmushi a fuskarsa ta tsani ganin natsuwa a tare da shi, shin ko dai asirin ya karye ne?.
Ta tambayi kanta lokaci daya kuma ta girgiza kai tana karfafama kanta guiwar cewa asirin bai karye ba, don tasan babu wanda ya tono tukunyar nan, gabanta ya fadi ta mike ta shiga shawagi tana tunanin idan kuma wani yaje ya tone ne fa ko da da kuskure.
Da sauri ta dakko wayarta

Page 185

Ta danna number Haj Rakiya bugu biyu a cikin na uku ta dauka, tana kokarin tsame hannunta a cikin tuwon shinkafar da take ci, “Da girman kujerarki”, cikin sautin muryarta me cike da damuwa tace “Haj bana cikin nutsuwata”, tayi tsam da ranta tace “ me ya faru Haj”, Haj kilishi ta saki ajiyar zuciya tace “Abubuwa ne na ke ta ganin canjinsu ko kinsan musaddik yanzu kwana biyun nan ya daina dawowa gida a buge, kuma ina ganinsa tsaf cikin tsaftarsa kamar yadda yake da, yadda yake zama duku duku yanzu babu datti a kayansa, yadda kuma yake shigowa ya gaishe ni ina shan kamshi shi ma duk ya daina shigowa, itama kinibabbiyar matarsa ta daina shigowa,”
Ta ja numfashi ta cigaba da magana ba tare da Haj Rakiya ta katseta ba,
“Ni daman batun yau ba nasan auren wannan fitinanniyar yarinyar da Musaddik fitina ne kawai a gare bi, shi yasa ban so akayi ba don dai banda yadda zanyi ne kawai,” Haj Rakiya tace “ ki kwantar da hankalin ki Haj, ke yanzu meye tunaninki”, a daburce tace “ ina tunanin ko wani yaje ya tone asirin nan ne”, da sauri tace “ wa haba Haj ki daina wannan tunanin, yadda na ke kula da kaina haka nake kula da wannan ajiyar, ta yaya zan dauke kaina a kai bayan irin alherin da kike yi min, duk don na kula da wajen”.
Haj kilishi tace “ Na sani Haj amma yanzu ki je ki duba wajen ki gani ko na samu sukuni”. Ta yunkura ta tashi tace “ tunda kin damu bari naje yanzu”, ta kashe wayar, ta wuce ta wanke hannunta, ta zari gyale ta fice da sauri. Ta je ta samu bakin kukar lafiya lau babu inda aka tone, tun a bakin kukar ta kira Haj kilishi ta sanar da ita komai lafiya lau ta kwantar da hankalinta, canjin da ta gani ba wata bace sila illa Afrah amma batun shaye shaye babu abinda zai hana shi yi. Karo da dama kenan da Haj kilishi taji tsanar Afrah ta kara baibayeta, tana ganin lokaci ya yi da zata kai maganarta wajen boka mai rakwacam.

Ita kam Afrah a dai dai wannan lokacin suna can cikin farinciki ita da Musaddik, domin Afrah tafi kowa jindadin samun aikin nasa, ga albashi mai tsoka, gashi an kwashe masa mafiyawan lokacin da yake da shi, don haka dole ayyukan da yake aikatawa masu muni su ragu.

Har ya sayyadi Habib washegari da taje islamiyya sai da ta gayama. Sosai shi ma ya jidadi, domin yadda yaga farinciki a fuskar Afrah ya fi masa komai dadi ya yi addu’ar Allah kara kawo sanadiyyar shiryuwar musaddik ko don Afrah ta cigaba da samun farinciki.

daga Islamiyya kuwa bayan an tashi kai tsaye Afrah gidansu ta wuce,
domin ta sanar da mahaifinta kyakkyawan labari. Sai dai kamar kullum Babu wata kyakkyawar tarba da
ta samu da ga gun Mama Hauwa, sai ma harare-harare gami da
kumbure-kumbure da take yi. Ita kuwa
Na’ima dama ba ta nan, ta tafi Suleja bikin kawarta.
Haka Afrah ta ci-gaba da zama a
darare tana zaman jiran mahaifinta, yana ko dawowa, ta gaya
masa maganar samun aikin Musaddik
har da iya adadin albashin da zai dinga kwasa duk wata,
Mama Hauwa na gefe tana ji, bakin-ciki ya cika mata ciki, hatta numfashi wahalar fita yake mata saboda tsananin hassada, nan da nan idanunta suka rine
su ka yi jawur,Yaushe Musaddik har ya yi hankalin da zai yi
tunanin neman aiki, kuma aikin ma me
tsoka haka, kuma ma ko ba komai yana tare da manyan mutane Hajiya Hudah
yar Majalisa guda, ai alheri kala-kala ya dinga samunsa kenan daga gareta, kilama har daga abokan arzikinta.
Zahiri ba ta ji dadin wannan al'amari ba.

A yayin da Malam Mahmud farin-ciki ya
cika zuciyarsa ya ji dad sosai, ya kuma yi masu addu'a
ta-gari, tabbas tun bayan auransu da
Afrah Sai yanzu ya dan fara samun natsuwa, domin tabbas sun fara ganin cigaba, a yau kuma ya kara jin karfin guiwar cewa in sha Allah Afrah zata zama silar maida musaddik nagari cikin taimakon ubangiji.Ya so
kwarai ta tsaya ta ci abincin dare, tunda
an kusa gamawa, amma Afrah ta ki, saboda yadda ta ga Mama Hauwa take kaiwa da komowa cikin tsananin fusata .


Yar gidan imam ✍️
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 186

hakan yasa tasan tsayawarta cin abincin ba karamin damuwa zai haifar ba,shi ma Mallam Mahmud din bai matsa mata ba, domin ya san tana da
dalilin kin tsayawa ta ci abincin , domin har kullum yasan baiyi sa’ar matar farko ba, halin Mama Hauwa na son rai da son kai, da rashin kallon dan wani a matsayin da, da yana da iko da tuni ya rabata da wannan halin, shi yasa bazai taba daina kewar mahaifiyar Afrah ba, mace me kirki da sanin yakamata wacce ta bashi gatan da bazai taba mantawa ba. Afrah ta yi masa
sallama, Ita ko Mama Hauwa
ko da ta yi mata sallamar a ciki ta amsa saboda bakin-ciki, ita ma Afran ba ta saurareta ba, ta yi tafiyarta,
mahaifinta na sa mata albarka kamar yadda ya saba a kullum.

Afrah na fita kai tsaye gidan
Inna Halima ta wuce. Ita ma ta gaya mata batun samun aikin musaddik Inna
Halima cike da farin-ciki ta sanar da ita dazun nan Musaddik din ya zo
ya gaya mata da kansa. Inna Halima ta yi addu’a sosai, ta kuma yi ma Afrah godiya abisa wannan canjin da ake samu. Anan gidan ta ci tuwon masara miyar kubewa danya wacce ta ji bushasshen kifi da man shanu, ta ci ta koshi, harda yi ma musaddik guzuri sanin yana son miyar kubewa tun daga danya har bushasshiya. Daga bisani ta kama hanyar gida zuciyarta cike da farinciki.
Domin wannan samun aikin nasa, ya kawo farinciki a rayuwarsu duka.

Washegari kuwa Afrah da kanta ta shirya mijinta, dama tun dare ta hana idonta bacci har sai da aka kawo wuta ta goge masa kayan da zaisa gobe. Karfe bakwai saura kwata hatta abin karyawa musaddik ya gama ci, Afrah ta ta gama masa komai, sai da zai tafi ne ta dube shi tana murmushi tace “ yaya kaga yadda kayi kyau kuwa kyau ace daganan sai wani katon office”, shi ma ya yi dariya yace “Wannan duk me sauki ne idan Allah ya sa mana hannu”, ta kara kallonsa ya na kokarin fita tace “ka gayama Haj kuwa ka samu aiki?”, ya girgiza kai yace “Ban gaya mata ba ai ni rabona da shiga cikin gidan ma na so na manta”, ta girgiza kai tace “Baka kyauta ba, ai yakamata ta sani, saboda haka kafin ka wuce ka shiga ka gaya mata".

Ya wuce ya na tafiya yana fadin “ kai Afrah ki yi hakuri, idan nace zanyi hakan zan makara,ayi min addu’a “, ya karasa ficewa da sauri, Afrah ta bi shi da kallo cike da sha’awar sa, mijinta fa tamkar da dubu ne, dubi yadda ya fito ya yi kyau cikin shiga ta kamala kai idan ba an gaya maka ba babu yadda za’ayi ka dauka yana da wata nakasa ta dabi’ar rayuwa.

Page 187

Afrah ta yi addu’ar Allah yasa wannan aikin hanyar shiriyarsa ce, Allah kuma ya kauda duk wata fitinar da ke cikin aikin ya hadasu da alherin da ke ciki. Bayan tafiyarsa, Afrah ta dan koma bacci , wajen karfe goma ta tashi ta yi wanka ta yi kwalliyarta cikin doguwar riga me ruwan kasa, kai tsaye cikin gidan ta shiga wanda rabonta da shiga tun ranar da Haj kilishi da Haj Rakiya su ka yi mata wulakanci.har falo Afrah ta
sami Haj Kilishi tana zaune tana zuba mulki tana shakar kamshi, tamkar mutuwa da rayuwa a hannunta
suke, bata damu ba ta nemi waje ta zauna, gaisuwar ma daker take amsawa nan ma ko a jikin Afrah, illa gyara zama da ta yi ta sanar da ita dalilin zuwanta, wanda bai wuce yar majalisa Haj Hudah yunus ta ba musaddik aiki tare da albashi me kauri ba.

Afrah ba ta yi mamakin yadda
ta ga tashin hankali ya bayyana a tare da Haj kilishi ba, domin dai da a kishingide Hajiya Kilishi take, amma tana
jin wannan maganar, ta yi zumbur ta tashi ta zauna sosai,
tana kallonta fuskarta cike da bacin rai hade
da mamakin jin maganar, cikin wata irin murya tace “Ya sami aiki?" Afrah , ta gyada kai , sosai take Jindadin ganin damuwa a fuskar Haj kilishi, domin tuni ta gama fahimtar ba ta kaunar musaddik don haka tasan duk wani abin alheri da zai same shi ba zata taba farinciki ba.

Tace “Eh, ya sami aiki, shi ne na
ga ya Kamata na zo na gaya miki, kafin shi ma ya zo ya gaya miki, don nasan zai zo”,
Haj kilishi ta watsa mata harara tace “ ya zo ya gaya min ta yaya? Bayan yanzu kece komai dinsa, don haka tunda kin zo kin gaya min ai bazai zo ba” Afrah bata ce uffan ba illa kara gyara zama da ta yi akan kujerar da ada bata da ko ikon zama saboda hada ran da zata gani a gun Haj kilishi kadai ya isa ta kasa zama a kujerar, amma yau ta riga ta dake babu tsoron Haj kilishi a zuciyarta ko da kwayar zarra ne.
Ta kara jifanta da wata hararar tace “yaushe rabonsa da shigowa ya gaishe ni, saboda yana cikin daula yan siyasa suna ba shi gata shi yasa ashe yake kokarin wofintar da ni, to shikenan Allah ya sanya alheri”.
Haj kilishi Ta na kawo wannan gabar Afrah ta mike tace “Dama abinda nake jira kenan na ji kin fada, amin”. Bata saurari komai ba ta fice, yayinda Haj kilishi ta bi ta da wani irin kallon mamaki, Afrah ta canja fa, wai me ke faruwa ne, da sauri ta janyo watarta ta
danna lambar Hajiya Rakiya ta
Kira bugu daya kamar ta na jira Hajiya Rakiya ta dauka. Hajiya Kilishi ba ta
damu da amsa gaisuwar da Hajiya Rakiya take mata ba , ta fara magana
cikin damuwa da bacin rai,gami da tashin hankali, “Na gaya miki akwai matsala, ni fa banda wani kwanciyar hankali, ko kinsan yar majalisa Haj Hudah yunus ta ba wannan fitinannen yaron musaddik aikin yi”. Haj Rakiya itama nan da nan ta daburce tace “Assha, ta bashi aikin yi , har yaushe ya samu nutsuwar da zai yi aiki, kuma ina ma yasan Haj Hudah da har zata bashi aiki, lalle akwai matsala “. Haj kilishi ta numfasa tace “Abinda nake kokarin fahimtar da ke kenan jiya akwai matsala sosai, komai fa ya canja, ina zai santa fa da ya wuce wajen bangar siyasarsa da nake murnar karshen lalacewa ce ta same shi, sai gashi a dalilin hakan zai samu azurta”

Page 188

Haj Rakiya tace “Gaskiya Haj akwai damuwa “ Haj kilishi tace “Damuwa kuwa sosai, saboda ni ko ya ya ne bana bukatar ya samu ko wace irin dama na fi son ya cigaba da lalacewa har karshen rayuwarsa , don haka nake tsoron kada aikin nan ya lalace”, Haj Rakiya ta jinjina kai tace “ Amma ke kina ganin wannan tunaninsa ne kuwa?”, Haj kilishi ta kara feso da numfashin damuwa tace
“Ni kaina ban yarda wannan tunaninsa bane, don ina
wani tunani ga me shaye-shaye,
na dai fi Yarda da cewan wannan tunanin makirar matarsa ne Afrah, don baki ga yadda ta shigo min falo ba yanzu da gadara da isa, anya ma kuwa yarinyar nan bata gano wani abu a game da ni ba”, haj Rakiya tace “ me ki ka gani ya saki wannan tunanin”, ta nisa tana kara nazarin yadda ta ga Afrah yau, tace “ Yadda take tsorona da shakkata yau babu komai a cikin idanunta face tana min wani irin kallo da har yanzu ban fahimci ma’anarsa ba”.

Haj Rakiya tace “Idan ko wannan ne tunaninki to ya zama dole mu san matakin da zamu dauka a kanta” Haj kilishi ta mike tsaye ta shiga shawagi a tsakiyar falon, ta yi sa’a babu kowa a gidan masu aikinta biyu ta aike su, don haka ta sake sosai su ka cigaba da tattauna yadda za’a bulloma lamarin.
Tace “kin fahimci cewa wannan samun aikin nasa zai iya rushe duk abinda muka kulla a kansa, kinga idan yana aiki yaushe zai sami damar cigaba da yawo da abokansa na banza, yaushe zai sami damar yin shaye shaye yadda yakamata?,haka zalika yin aikin nasa zai iya sawa wasu su ga darajarsa wanda kinsan abinda na tsana kenan duk duniya,sannan idan ya fara aiki zai dinga mu’amala da mutanen kirki, maimakon mutanen banza, tunda ga
Shi da mata ga aikin yi, kuma Hajiya me ya rage a cikin cikar
natsuwarsa?" Haj Rakiya ta girgiza kai
tace “Babu, gaskiya wannan
abu bai yi dadì ba, dole kuma a dauki mataki." Haj kilishi tace
"'Mataki ya wuce na raba shi da
wannan matar ta sa, domin duk
ita ce silar komai Don haka dole mu je wajen boka Mai Rakwacam, don na sanar da shi halin da nake ciki, ni fa kin ganni nan rabon da nayi bacci me dadi harna manta a rayuwata kullum cikin fargabar kada a sami matsala nake”. Haj Rakiya
tace “ Hakan shine dai dai sai mu je saboda kada ki tsaya garin kallon ruwa, don dai dawowar musaddik
hayyacinsa matsala ce gagaruma, don
Zai iya waiwayar dukiyarsa, duk da ya riga ya bayar, zai iya kalubalantar ki, kuma mafarkinki na musaddik ya kare rayuwarsa a wulakance bazai taba tabbata ba”, Haj kilishi tace “shine damuwata, bari zan gyara musu zama daga shi har matar tasa, ki shirya gobe zamu tafi ruga”, tace “Allah ya kaimu”, daganan su ka yi sallama, lokaci daya su ka aje wayoyin.

Page 189

Lalle wanda Allah dai ya batar
ya batar domin dai duk wanda ya rike wanin
Allah Tabbas! Ya tabe.Haj Kilishi
tana cikin hallaka, tunda ta maida boka
Mai Rakwacam me biyan bukatunta, ta manta duk wanda ya je gidan boka,
Ya gaya masa bai yarda ba, bai
Kuma yi amfani da abinda ya fadan ba, to Allah
ba zai taba karbar sallarsa ba ta tsawon kwanaki arba' in, kuma
yana fushi da mutum. Idan kuma bokan ya gaya masa ya ji ya yarda ya kuma yi amfani da abinda ya fadan ya
amince, to mutum ya kafirce da ga abinda Allah ya aiko manzonsa, ka yi shirka, ka fita musulunci, duk
wani aikin kwarai da ka taba yi, ya goge
amma duk zunuban mutum suna nan,
Hmm! Jama 'a wannan wace irin masifa ce ? Saboda
son duniya ka rabu da Allah da Manzonsa.
Bayan ka san cewa Allah me tsananin
Kishi ne, yana yafe kowane irin zunubi matukar tsakaninka da shi ne amma banda shirka,
matukar mutum ya mutu yana
shirka babu in da zai je, sai wuta, da shiga azaba dauwamammiya, me zai
sa ka zabi duniya abinda ba dauwamamme ba, akan lahirarka wanda ya ke dauwamamme?.
Me ya sa ba za mu hanu da abinda Allah
ya hanemu ba? Meye duniyar
balle abinda ke cikinta,Mu da mutuwa take gabannu,da kwanciyar kabari meye namu na son duniya har ya ja mu kaucewa hanyar Allah. Amma lalle irinsu Haj kilishi sun riga sunyi nisa babu Allah a zuciyarsu, idonsu rufe yake da son duniya, zuciyarta kuma cike take taf da tsanar dan kishiya wanda da ta kwantar da hankalinta sai tafi amfana da shi fiye da kowa, da ta rike shi a matsayin da, da bata kara kukan rashin da namiji da bata haifa ba, yadda ya taso baisan mahaifiyarsa ba hakika da itace zata maye gurbinta a gurinsa, amma zuciyarta ta kekashe ta manta da komai sai yadda zata sabauta rayuwarsa.

Page 190

Ko yanzu kwata kwata bata samu sukuni ba duk ta fita hayyacinta, haka ta uni a cikin gidan tamkar mara lafiya ko ya ya ta ji an taba get sai ta leko, ta kosa kwarai gobe ta yi ta tafi ruga domin ba zata yarda Aftah ta cigaba da dagula mata lissafi ba.

Ita kam Aftah yau duk addu’ar ta akan musaddik ta kare, Hakan yasa a ranarsa ta farko a wajen aiki bai fuskanci wata matsala ba, banda matsalar kallon da Alh yisuf sanda yake masa wanda ya ji a ransa tamkar dabi’ar sa ce ta yin irin kallon, amma me yasa ba ya irin kallon akan kowa sai akansa.
Musamman da Haj Hudah ta fito cikin tsararriyar kwalliyarta cikin wani babban leshi da ya ji duwatsu doguwar riga ce irin dinkin manyan mata ne tunda tana da jiki, sai dai dan gyalen da ta makala a kafadarta sam bai dace da ita ba a matsayinta na matar aure. Musaddik ya yi mamakin yadda Alh yusuf bai damu da ya tsawata ma matarsa kan irin wannan shigar ba maimakon hakama yafi maida hankalin sa akan kafesu da wannan tsinannen kallon da ya saba, yana tsaye yana kallonsu har suka shiga mota ɗaya da Musaddik sai direba, ɗaya motar kuma Jami’an tsaronta ne suka wuce suka tafi, Lamarin ya daure kan musaddik har suka kai inda zasu cike yake da mamakin waye Alh yusuf sanda ne?.

Gidan gaisuwa su ka je Haj Hudah tayi gaisuwa gami da bada kudin da zasu cigaba da ciyar da kansu zuwa wani lokaci, siyasa riya ce domin komai ta yi yan jarida na gefe su na dauka domin su yaɗata, Musaddik dai yadan sami damar kewayawa yadan bushi sigarinsa ya fito da dan karamin turare bayan ya gama ya goga a hannunsa da jikinsa sannan ya dawo cikin mota, hakanan ya ji baya son halinsa na shaye shaye ya fito a wajen Haj Hudah hakanan ya ji yana son rike mutuncin da ya fahimci Haj Hudah ta na ganinsa da shi.
Bayan ta gama abinda ya kawo su ne suka bar gidan. Wajen cin abinci suka wuce sun ci abincinsu mai rai da lafiya tebur daya suka zauna da Musaddik duk da baiso hakan ba amma ta dage akan babu komai.
Suna cikin cin abincin ne musaddik yaga wannan wata damace agare shi da zai gaya mata gaskiya, ya dago ya dan dubeta fuskarta cike da nishadi ya maida kansa kan abincinsa yace “Ranki ya dade ina son na danyi wata magana da ke dafatan ba zata bata miki rai ba”, ta aje wukar hannunta tana kallonsa wani irin shauki yana kamata tace “ babu damuwa Musaddik menene?”
Ya dan gyara zamansa yace "Ranki ya dade a matsayin ki na matar aure wacce akwai abubuwa da dama da yin su haramun ne a gare ki,ina ganin yakamata ki dinga suturce kanki a duk lokacin da zaki fita, sanya irin wannan mayafin bai kamata ba wannan caba kwalliyar itama sam bata kamata ba, kiyi hakuri fa tunatarwa ce kawai nayi miki”, wani irin dadi taji har cikin ranta ta zuba masa ido yau itace rana ta farko da aka gaya mata wannan maganar me tsada ko mijinta bai taba kishin fitarta a haka ba shi ne ma wata rana yake nuna mata dan gyalen da zata yafa ta fita, lalle Musaddik komai nasa da ban ne.

Shurun da ta yi ne ya dauka ko taji zafin maganarsa ne hakan yasa ya yi saurin cewa “ kiyi hakuri, na saba ganin matata bata fita saita suturce kanta tun daga sama har kasa hatta fuskarta da bata cikin al’aurar mace saita rufeta shi yasa a duk lokacin da naga wasu matan musamman na aure suna banzantar da kansu nake cika da mamaki da damuwa, don Allah kada ki ji haushi”.
Tayi murmushi sosai tace "waye ya gaya maka na ji haushi, burge ni kawai kayi yadda banyi maka kwarjini ba baka ji tsoron matsayina ba ka gaya min gaskiya nagode nagode domin kayi min abinda ya kara daga darajarka a guna in sha Allah kuma zan gyara”.
Ya yi murmushi yace “ To masha Allah ubangiji Allah ya bada ikon gyarawa”.
Kamar daga sama haj hudah ta watso masa tambayar "Amma dai kana son matar nan ta ka da yawa”.
Ya aje cokalin gami da ture farantin abincin gabansa, ya yi wani murmushi da ya ƙara narkar da zuciyar Haj Hudah sannan yace “Ina sonta Haj fiye da yadda nake son kaina, ina jinta a cikin jinin jikina ba a zuciyata ba, yanzu haka wannan abincin da nake ci baya min daɗi saboda nasan ba irinsa zata samu ta ci ba yau, ina sonta tamkar yadda nake so koma fiye da yadda nake son numfashin da ke bugawa a kirjina”.

Dauke wuta Haj Hudah ta yi ta kara zuba masa ido tana jin jikinta yana tsuma, tana jin wani irin damuwa a cikin zuciyarta da bata san dalili ba, nan da nan idanunta suka canja………

Yar gidan imam ✍️
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM


page 191

Musaddik bai fahimci komai ba hakan yasa ya cigaba da yabon matarsa, har sai da zuciyar Haj Hudah ta ji ba zata iya dauka ba, don haka tayi saurin mikewa ba tare da tace uffan ba, ta dube shi cikin rawar murya tace “Tashi mu tafi”, bata saurari komai ba ta wuce ayayinda musaddik ya bita da kallo, canjin yanayin da ya gani a tattare da ita sam bai sa ma kansa komai ba. Ya tashi ya bi bayanta.Har suka kai gida zuciyar Haj Hudah tafasa take, shin me yasa take jin zafi don musaddik ya gaya mata yana son matarsa?,me yasa take jin damuwa don musaddik ya yabi matarsa?. Ko da suka isa gida bata saurari komai ba ta shige cikin gida, musaddik kuwa zamansa ya yi a waje cikin mutanen da ya samu a harabar gidan. Da alama Alh yusuf sanda baya gidan, karfe shida dai dai na yamma musaddik ya kama hanyar gida ba tare da ya damu da ya yi sallama da Haj Hudah ba kamar yadda itama bata bukaci ganinsa ba, ikon Allah.

Washegari kuwa tun safe Haj kilishi

Please Login or Register in order to submit comment