Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan murmushi gami da kallon
Malam Mahmud, wanda ya yi tagumi hannu biyu,
sannan ta dawo da kallonta ga Inna Halima ta ce
"Me ya sa za ki fadì haka Inna? Ya za ki ce miji
irin yaya Musaddik bai dace da ni ba, bayan jininmu daya.
Dan-uwana ne, käda fa ki manta a da, ba haka
rayuwarsa take ba, ina ganin kuma kuna son ya
yi aure ne, saboda ya samu natsuwa.
To ai ina ganin wannan jahadi ne gaba dayan
mu lada za mu samu, kuma akan maganar yi ma
mahaifina biyayya, ina miki rantsuwa ko wuta ya
hura ya ce na fada, zan fada;, domin da 'shi kadai na
samu nasara yin rayuwa, bayan Allah ya amshi
ran mahaifiyata, don haka ina so ki sa a ranki, auran

Page 33
Yaya Musaddik shine biyayya mafi kankanta da
na ke ganin zan iya yi ma, mahaifina.
Hawaye ya digo a idanun Inna Halima, so da
Kaunar Afrah ya kara kamata, ta dubi Malam
Mahmud wanda shi ma maganganun Afrah sun
taba masa zuciya, ido kawai ya dora mata, yana
yi ma Allah godiya a zuciyarsa daya ba shi "ya irin Afrah.Inna Halima tace
'"Gaskiya ne yaya. Allah ya
ba ka 'ya daya tamkar da dubu, yau Afrah ta sa
ni alfahari da ita, ta Kara dasa min soyayyarta,
zahirii mun yi dace da samun ya irin Afrah.
Me cike da tausayi, jinkai da uwa uba ilimin
addini daya gama ratsa zuciya da jikinta, hakika
Musaddik mun yi masa dukkan gata, na ba shi
mata irin Afrah, ina kuma da tabbacin Afrah ita
ce sanadiyyar maido da shi irin hanyar da yake akai a da, ba ni da haufin itace zata taimaki rayuwar Musaddik” tasa hannu ta kara jawo Afrah cikin jikinta ta rungumeta sosai tana fadin
"Allah ya yi miki albarka ,
Allah ya hadaki da dukkan farin-ciki a gidan
Musaddik da rayuwarki duka, ke ma Allah ya ba ki ya ya irin ki masu biyayya”

Malam Mahmud ya amsa da "Amin Halima,
ai Afrah ta zama sanyin idaniyata, ta, zama
farin ciki na, darajarta da kima sun kara fadada
a zuciyata, ba ni da kamarta a duk 'ya yan da na
haifa. Matsayinta daban yake"

Page 34

Inna Halima ta ce “Tabbas hakane yaya”
Kalaman Malam Mahmud sun sanyaya zuciyar
Afrah daga kunci, natsuwa ta fara zuwa mata, ta
kuma kara dammarar amincewa tare da yarda
da umarnin mahaifinta. Malam Mahmud ya ce.
"Halima ki nemi Musaddik gobe ki yi masa
bayanin canjin alherin da aka samu, ya zo su yi
magana da Afrah, domin auransu ba na so ya wuce nan da wata daya”
Gaban Afrah ya fadì, ta runtse
idanunta ta bude. Wata daya!
Da sauri ta tashi daga jikin Inna Halima ta
fice. Inna Halima ta bi ta da kallo tana murmushi tace “ kunya ki ke ji Afrah?”, ta gyara zama
Ta dawo da kallonta ga yayanta tace
"Eh, to ai daukar lokaci baida wani amfani,
tunda dama Islamiyya ce kawai take zuwa, aure
kuma ba zai hanata zuwa da kuma koyar da
dalibanta ba, saboda hakan goben nan zan kira
shi na san kuma duk inda yake zai amsa kirana da gaggawa, don ko a wane hali yake baya iya kin amsa kirana, ko da zai shigo min acikin yanayin da zan uni zubar da hawaye”. Yace

"To shi kenan. Allah ya kai mu. Ita
kuma Hauwa sai ta jika Na'imarta ta sha". Inna
Halima ta ce "Lallai kam! Shi ya sa ai aka ce gida
biyu, maganin gobara, yau da Na'ima ce kadai
'yarka da bakin-ciki ya kashemu, taje ta zaba mata wanda ya fi kowa natsuwa a duniya, to wai yaya idan ana kyamatar irin su musaddik ta yaya zasu shiryu”, ya jinjina kai yace “kwarai Halima irin su janyosu ake ajiki a nuna musu souayya da tausayi sai kiga idan da rabo wata rana mutum ya daina ya shiryu, yanzu idan Hauwa ce ta haife shi zata kyamace shi ne irinsu ma iyayensu mata sun fi son su, Allah dai ya shiryi Hauwa domin in da zata daure data da gyara da yawa da yakamata ta zauna ta gyara”, inna Halima tace “ Allah dai ya shiryeta”, Mallam Mahmud ya kalli agogonsa dake manne a jikin bangon dakin, sannan ya dawo da kallonsa gareta yace
“Dare ya yi Halima ki tashi ki tafi gida kada Mai-gidan ya ga dadewarki".ta tattaro hijabinta tace
"To Allah ya tabbatar mana da alheri"
Ta tashi ta

Page 35
gyara zaman hijabinta, sannan ta yi masa
Sallama ta fita zuwa dakin Afrah, amma sai ta ta tadda ta tana
shafa'"i da wutri, don haka ta wuce zuwa gida
zuciyarta fes! Da farin-ciki Afrah ta share masu
hawaye

Washegari tun safe Inna Halima ta kira Musaddik
a waya, don haka gab! Da azahar ya shigo
gidan idanunsa jajir! Kayan jikinsa kuwa kaca-kaca duk
sun dafe da datti, kai da gani ka san sun dade a
jikinsa, sai da Inna Halima ta samu natsuwarsa,
sannan ta gaya masa duk halin da ake ciki a yanzu.
Musaddik ya yi shiru, jikinsa ya yi matukar
sanyi a hankali ya ce "Afrah Inna?"ta gyada kai
tace "Ita fa". Ya girgiza kansa ya ce
"A gaskiya Inna
ba"a yi ma Afrah adalci ba.
Matukar aka aura mata ni, domin ta kowace
fuska ba mu dace ba, tana da hankali, tana da
natsuwa tana da kunya, uwa uba tana da
matukar riko da addini, ya kike ganin mai irin wannan halin ta dace da ni, da banda aiki sai zubar da mutunci” Inna Halima ta kafe shi da ido
tana ganin yadda duk ya birkice da ga jin maganar , ta aje numfashi tace
"Kada ka damu ko kadan dama wadannan
halayen na ta da ka fada sune dakilin hada auran naku, domin za mu hada ka aure da ita ne
domin muna da tabbacin da wadannan halayen da ka lissafa zatayi amfani da su za ta janyo hankalinka,
ka natsu ka zama mutumin kirki kamar da, don
haka wannan babbar dama ce a gareka, damar da nake da tabbacin ba zaka kara samun ita ba”

Page 36

Musaddik ya dago ya dubeta ya ce idanunta sun kara rinewa yace “ Amma Inna, takurawa Afrah kawai ku kayi ta aure ni, ba don wai tana sona ba, idan kuma hakane gaskiya inna ba dai dai bane”
Inna Halima ta girgiza kai ta ce.
"Kada ka sa ma kanka dole sai ka gano tana
sonka ko ba ta sonka, abu dai mafi dadi, shi ne
da kanta tà amince za ta aureka, don haka duk
ka aje wannan kwakule-kwakulen ka yi ma Allah
godiya daya ni'imtaka da samun Afrah. Kawunka
kuma ya umarce ka da ka je ku tattauna da ita"
Ya Kara kallonta ba tare da ya yi magana ba,
ta ci-gaba da cewa "Eh, saboda auran ba zai wuce nan da wata daya ba”
"Wata daya?" Ya tambaya a gaggauce tace

"Eh, wata daya. Ko akwai wani abin ne?" Ya
girgiza kansa ya ce
"Babu komai Inna, zan yi kokari naje, nagode Allah ya saka maku da alheri, ya kuma baku ladan zumunci, domin babu abinda zance da ku ina ganin halaccin dangin uwa” tayi murmushi
Tace “Amin, sai dai kada ka je mata a haka,
ko yaya ne ka samu kaya masu tsafta kasa idan za ka je, kuma ka tabbatar kana cikin nutsuwarka don Allah musaddik kada ka sha komai “ musaddik ya yi kasa da idonsa
Ya dubi kayan jikinsa, shi kansa ya san ya yi
datti, ya yi dan murmushi sannan ya ce "To Inna nagode zan kiyaye”.
Daga nan ya tashi ya tafi, haka nan ya ji ya
sami kansa da jin wani farin-ciki, hakika samun
Afrah a gare shi ba karamin al'amari bane, duk
da babu son aure a zuciyarsa.
To fa, sai ya ji ya samu kansa da jin dokin son
auran Afrah wacce ko a mafarki bai taba lissafota

Page 37

a cikin matan da zai aura ba, duk da rayuwarta
ta dade tana burge shi, tana daya daga cikin mutanen
da yake jin nauyin aikata mummunan abu a
gabansu, shi kansa bai san dalili ba. Amma ya
san dai yana matukar jin nauyinta duk da kananan shekarunta.

Yau kwata-kwata a makaranta Afrah ta kasa
samun natsuwar da za ta koyar da dalibanta,
tana cikin matukar damuwa wacce iya yadda ta
so ta boye, sai da Sayyadi Habib ya fahimci tana
cikin damuwa, saboda haka bayan an tashi, suna kan hanyarsu na zuwa gida ya dan dubeta cikin nazarin yanayinta yace “Afrah me ke faruwa ne?”, ta dan dube shi tace “ me ka gani?”, ya yi murmushi yace “kin tabbata cikakkiyar yar nigeria me amsa tambaya da tambaya”, ta kara murmusawa tace “ai ban fahimceka bane shi yasa na tambaya” yace “Ni kuma na fahimci damuwar dabkike ciki shi yasa na tambayeki “
Ta girgiza kai ta ce “Ba ni da wata damuwa “

Ta fada a gajarce, ya girgiza kai Ya ce "Ki na da ita, sai dai idan ki na kokarin
Boye min, wanda ina ganin bai kamata ba, duk
da ban san damuwar ba, na san idan ki ka gaya
min zan amfaneki koda da shawara ne ko nasiha, amma
idan ki na ganin sanina bai zama dole ba, to ki
bar shi ba sai kin gaya min ba, na dinga taya ki
da addu'ar Allah ya kawo miki mafita.”


Page 38

Nan da nan idanunta suka cika da kwalla , ta yi
kokarin maidawa sannan ta ce "'Hakika idan
akwai wanda ya cancanci ya san damuwata a yanzu, to kai
ne, domin damuwar ba tawa bace ni kadai, ta
mu ce mu duka Ya kalleta, nan da nan ya ji damuwa ta cika ransa domin ganin yanayin davta koma .
Yace “To idan har haka ne, me ya sa ba za ki
gaya min ba, ko don mu hadu mu shawo kan
matsalar gaba daya" ta aje ajiyar zuciya tace
"Hanyar da zan bi na gaya maka ita ce
na rasa, domin ban san yadda za ka dauki lamarin ba” ya girgiza kai yace
"Zan dauke shi a duk
yadda ya zo min, domin Allah ya fi ni sanin dalilin
yin komai"
Ta numfasa dai-dai lokacin da suka iso kofar
gidansu, suka tsaya sannan ta ce "to shi kenan
kayi hakuri zuwa gobe, za mu yi magana, zan
sanar da kai komai, sai dai, ina addu'a tare da fatan Allah ya ka fahimce ni”
Ya yi dan murmushi ya ce “ Bazan tursasa
miki ki gaya min yanzu ba, zan jira har zuwa
goben, sannan ina tabbatar miki da cewa zan
fahimceki, domin na san halinki gaba da baya"
Ta gyada kai ta ce "To na gode: Ya Sayyadi,
Sai goben” ya gyada kai yace “Allah ya kai mu, ki gaida mutan gidan” tace “ zasu ji n sha Allah “
Daga nan ya tafi, zuciyarsa cike
da sake-sake akan damuwar Afrah, wacce ya ji

Page 39
tun kafin ya san damuwarta ta shi ma damuwar ta kama shi .Afrah na shiga gdan ta yi turus a sakamakon ganin Musaddik tare da mahaifinta a zaune akan tabarma . Tayi saurin kallon kofar dakin mama Hauwa ta ganta a kulle alamar bata nan , don haka ta karasa shigawa gidan tana kokarin kauda duk wata damuwa da ke tare da da ita. “ Afrah an dawo?”
Cewar mahaifinta, ta gyada kai fuska sake
tamkar ba ta cikin damuwa ta ce “ Na dawo Baba, sannu”, musaddik ya dago
Ya dubeta zai yi magana kenan, ta riga shi
"Sannu da zuwa yaya"
Ya kara dagowa sosai yana cigaba da kallonta sosai, duk da hakanan take masa kwarjini sai ya ji duk ya na neman ya rikice. a sanyaye yace

“ yauwa sannu ya makarantar?"ta kara yin murmushi tace “ lafiya kalau”
Cike da farin-ciki Malam Mahmud ya ce "Tun
dazu ya zo gunki, bai san ki na koyar da dalibai
ba a irin wadannan ranakun, ganin kin kusa dawowa, ya sa
na tsayar da shi akan ya jiraki". Ta gyada kai tace “ To baba bari na shiga daki na aje littafaina” mallam mahmud ya dubi musaddik
' Ya ce "Ba damuwa zai sameki a dakin”

Ta wuce da sauri zuwa daki, ta kintsa kayanta
da ta bari kan katifa, ba•ta cire hijabin ba, nikaf
kawai ta cire ta nemi bakin katifar ta zauna ta
takure gu daya, lokacin daya kuma tana karanta
"Inna-Lillahi' wa-Inna Ilaihir-Raji'un! Domin ta
samu natsuwar zuciyarta, domin ko kadan ba ta son

Page 40
Musaddik, yav fahimci tana cikin damuwa akan.
auransa Cikin sallama Musaddik ya shigo dakin,
ta amsa masa lokaci daya ya sami kan tabarmar
dake shimfide a tsakar dakin ya zauna yana
Kallonta a hankali ta gaishe shi, ya amsa, sun
dau tsawon lokaci ba tar da ya iya yin magana
ba daga bisani ya numfasa ya ce.
"Afrah ki na gain maganar auran mu babu
cutarwa a bangaren ki?" Yayi tambayar ne cikin wata murya ne cike da gazawa, Ta daidaita muryarta ta ce
"Cutarwa? Wane irin cutarwa?" Ya muskuta yace
"Ni ina ganin kamar babu dacewa a tsakanin mu
Afrah, halina ba Boyayye bane, rana tsaka na sami mugun canjin rayuwa
Irin rayuwar da na ke yi a yanzu na fi kowa
tsanar irinta a da, amma ban san kaddarar da
Allah ya Kaddara min ba, na sami kaina a rayuwar da na
tsana, ki na ganin za ki iya zaman aure da
mutum irina me shaye-shaye da gurbatacciyar rayuwa, domin kinsan komai ba kuma na son boye miki komai, sannan bansan dalilin da yasa na ji ba na son ji dunga samun damuwa ta dalilina , ina jin kamar bazan iya jurewa ba”
Afrah ta runtse idonta ta bude, zuciyarta ta
Kara cika da tashin hankali gami da tausayin musaddik ta ce "Zan iya auranka
mana, zan iya zama da kai koda halin da ka ke
ciki ya fi haka munana, domin ina da tabbacin
wata rana zaka daina, za ka shiryu don na san
wannan ba rayuwarka bace a da”.
Sha'awar halayenta da natsuwarta suka kara
kama musaddik ya kara zuba mata ido .

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan umam

Kuyi commitments domin gujewa rashin cigaban zuwan sauran posting.
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

page 41

Yace “ Amma kin zauna kinyi nazari akan rayuwata da makomar aurena” ta muskuta gami da yin wani dan takaitaccen murmushi sannan tace,”idan aka zo maganar biyayyar mahaifina bana tunanin komai sai alheri saboda haka alheri kawai na zauna na hangoma kaina agame da aurenka,kuma na amince zan aureka”.
Wanna kalamai sun fi komai dadi a zuciyar
Musaddik, ya aje numfashi gami da kallonta
Sannan yace “Wanda na ganku tare ranar da na
zo wajen Na’ima meye matsayinsa a gunki?"
Tsigar jikinta ta tashi, damuwa ta kara cika
zuciyarta, kallon da ya tsareta da shine, ya sa
jikinta ya yi matukar sanyi, ta ji kuma ba za ta iya
gaya masa gaskiya akan Ya Sayyadinta ba,
domin ba ta ga amfanin hakan ba, tunda ta riga
ta zabe shi a matsayin mijinta.
Ta kwakulo murmushi gami da gyara zamanta
sannan ta ce "Matsayi kuma? Ba komai
tsakanina da shi daya wuce Malami na, ni dalibarsa ce".
ya lumshe idanunsa ya rasa dalilin da yasa ya ji matukar dadi da jin amsarta
ya ce. "Ki na nufin ba ki da wani da ki ke soyayya
da shi, kada na zama sanadin datse soyayyar?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba ni da kowa, ina son
kuma mu bar maganar nan"cikin murmushi yace
"An gama ranki ya dade”
Ta dan yi murmushi ta ce
“Na ji Baba na maganar ba za'afi wata daya ba za’a daura auren ko?” Musaddik ya gyara zamansa yace
"Eh, haka ya yi min bayani dazu,
domin har ya ba ni damar ma na je na gaya ma
Hajiya cewar ya ba ni ke, ya sa kuma ramar biki
wata daya me zuwa, wato uku ga watan da zai
kama kenan”.

Page 42

'Nan da nan Afrah ta ji ta kara gigicewa, bakinta ya shiga karanta “Allahumma ajirni fi musibati wa akalifni khairan minha” amma a cikin zuciyarta a fili kuwa ajiyar zuciya ta saki tace “To Allah nuna mana” ya datseta da ido yace “ko akwai wani abu ne Afrah, don Allah duk abinda ke ranki ki fito ki gaya min kada ki damu ina tare da ke”
Ta girgiza kai tace “ Haba yaya musaddik babu wani abu fa,kawai dama ina son na rokeka ne ko bayan munyi aure zan cigaba da zuwa islaniyya, zan kuma cigaba da koyar da dalibaina”
Ya yi murmushi ya ce “ kada ki damu zaki cigaba da zuwa islamiyya, meye ribata idan na hanaki zuwa makaranta, duk abinda kike so ni ma ina Ta yi dan murmushi tace “ To nagode” ya girgiza kai yace “ Ni ne da godiya Afrah ba kuma zan taba mantawa da wannan halaccin ba”.

Daga nan suka ci-gaba
da tattaunawa, kai ka rantse da Allah Afrah tana
son Musaddik, kuma tana son auran.
Shi kuwa haka nan ya ji matukar natsuwa a
dalilin hira da ya yi da ita, har zuwa lokacin da
aka kira sallar magariba, sannan ya yi sallama da ita, ya
fita tare suka yi alwala. da Malam Mahmud.
gwanin ban sha’awa kamar ya dore a haka sannan Suka tafi masallaci, duk da ko azahar bai
yi ba balle la'asar, amma ya zai yi, tunda Malam
Mahmud ya sa shi a gaba zuwa masallacin.

Page 43

Washogari kuwa cike da fargaba Afrah taje
makaranta, haka zalika har aka tashi makaranta
Islamiyyar Afrah ta kasa hada ido da Ya
Sayyadi Habib, haka zalika damuwarta ta fi ta ko
yaushe fitowa. Saboda tasan ya zama dole dai yau ta sanar da shi komai . A cikin ajin makarantar suka kasance, baya
an tashi kowa kuma ya watse, a natse Ya
Sayyadi ya dubi Afrah ya ce.
"Fateema, damuwa ba ta maganin damuwa
haka zalika duk abinda ya shigo rayuwar bawa,
hakuri ya kamata ya runguma gami da addu'a
saboda haka ina son ki natsu ki yi min bayanin
abinda ke faruwa, ko akwai ta inda zan iya
taimakawa kamar yadda na fada miki”
Afrah ta numfasa gami da gyara zaman nikaf
dinta a fuska, sannan ta fara magana a hankali
“Ya Sayyadi, da farko dai ina son ka sani, ka
Kuma sa a ranka kai ne da namiji na farko da zuciyata ta fara so
Ta kuma yarda da ta zama abokiyar
rayuwarka, domin ina da tabbacin kai ne wanda
Zaka yi min jagora zuwa gidan aljanna da
Kyakkyawan halayenka da kuma iliminka me
guda na Ba na hangen komai ko kwadayin.
komai daya wuce na san za ka sanyani a hanyar
bin dokokin Ubangiji wanda shine burina”
Ta dan numfasa tana kallonsa.
ganin bai da alamar yin magana ya sa ta cigaba
da cewa.

Page 44

"Sai dai kash! Komai Allah ya riga ya gama
tsarawa, ba mu da yadda za mu yi, sai yadda ya
yi da mu, kaddara ba ta rubutaka a matsayin mijin aurena ba” a gaggauce ya dago ya dora mata furgitattun idanunsa da suka rikide
nan da nan suka yi jajir!
"Kamar yaya?" Ya Sayyadi ya yi gaggawar
tambaya, ta jinjina kai sannu a hankali ta kwashe
labarin komai ta sanar da shi.
Ta kara da cewa "Allah shine shaida, ko
kadan ba na son Yaya Musaddik, ban taba
son sa ba , bai taba burgeni ba, haka zalika ban
taba yi ma kaina sha'awar auransa ba, don na
san babu wani alheri da zan samu a cikin.
auransa Amma abu daya na daukar ma kaina,
shi ne yi ma mahaifina biyayya a cikin duk wani abu da bai
saba ma umarnin Ubangiji ba, zan yi ma
mahaifina biyayya koda yin hakan zai kuntata ma rayuwata,
zai kuma kori farin-ciki na matukar mahaifina zai
yi farinciki To a shirye na ke da na yi komai, saboda haka
ina mai ba ka hakuri, kai na ke so, amma
Yaya Musaddik zan aura, domin cika umarnin mahaifina, ka yi
hakuri Ya Sayyadi, ka yi min afuwa."
Ga tsananin mamakin, Afrah, sai, ta ga Ya
Sayyadi ya yi wani bushashshén murmushi,
Sannan ya numfasa ya dauki wani dogon lokaci
Yana kallonta ba tare da ya yi magana ba, har ta gaji ta

Page 45

domin ta kosa kwarai ya ce wani abu, sannan daga bisani ya
fara magana cikin sayin jiki da sanyin murya.
'"A yau na kara yin alfahari da ke, hakika ke
yarinya ce me tsananin hangen nesa, tunaninki
Ya yi nisa da shekarunki, komai na rayuwarki
abin burgewa ne, ki na daya daga cikin 'ya 'yan da iyaye
suke alfahari da su."
Kalamansa sun sa Afrah ta fara samun
natsuwar zuciyarta, ya ci-gaba da magana,
“Ban ji haushin biyayyar da za ki ma mahaifinki
ba, hakan ma ya Kara sa min sonki da sha'awar halayenki ne,
ya kuma Kara miki wani matsayi na musamman
a zuciyata, kin kuma zama abar kwatanta
halayenta a wajen duk wani mai hankali.
Sai dai ina taya kaina jimami da alhinin
rabuwa da mace irinki, domin ke ce irin uwar da
Manzon rahama ya umarcemu da mu zaba ma
Yayan mu , na yi mafarkin kasancewa da ke a
matsayin matata uwar 'ya 'yana, wacce za ta yi
ma ya'yana tarbiyya, amma Allah bai nufa ba, b
bazan ji haushi akan kaddararsa ba.
Domin yarda da kaddara mummuna da
kyakyawa, cikar imani ne, na kuma yarda da
kaddara a matsayina na masulmi, sannan babsan irin tanadin sa Allah zai yi min ba akan hakurin da na yi”.

Ya nisa ya ci-gaba da cewa "Ba zan so kaina
na ce kada ki yi ma mahaifinki biyayya ba, haka
zalika Musaddik ya fi bukatar ki fiye da ni, domin

Page 46

shi yake bukatar nasiha tare da dora shi a hanya
Kuma dole na so masa abinda na ke so ma
kaina, domin imanin dayanmu baya cika, har sai
mun soma Dan-uwanmu abinda muke so; ma
kanmu. Saboda haka ki ciré damuwa a zuciyarki,
zan goya miki baya dari bisa dari har sai kin cimma burinki , nasan ahankali damuwa zata sake ni”.
Murmushi ya subuce a fuskar Afrah, ta kura
ma Ya Sayyadi ido, hakika kallo daya za ka yi
masa, ka san yana cikin matsananciyar
damuwa amma baya son bayyanawa. Hakika Ya
Sayyadinta ya cika gwarzon maza, ya cika jarumi.
Jarumi , ta nisa tace “Hakika Ya Sayyadi ban taba ganin namiji
me zuciyar imani da tausayi da kuma fahimta
Irinka ba, tabbas ina taya kaina jaje da bakin-cikin rashin
masoyi irin ka, sai dai tarihin rayuwata na san ba
zai taba kammala ba, ba tare da ka shigo ciki
ba bazan taba mantawa da kai ba har na koma ga mahaliccina”.

Ya jinjina kai yana kokarin maida hawayen
da ya taru masa a ido, ya ce "Babu komai,
Fateema haka Allah ya tsara mana, ba kuma za
mu taba yin fushi da yinsa ba, domin ya yi mana ni’imomi da yawa , don ya hanamu abu daya bai
Kamata mu sa damuwa ba, bayan ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya yi hakan”.

Page 47

Ita ma ta sa hannu kasan nikaf dinta ta goge
hawayen da ke fito mata, sannan tace
“Ina neman alfarma daya daga gareka Ya Sayyadi." Ya dago ya
dubeta ya ce "Wace irin alfarma ce?
Tace "Ina neman alfarmar ka zama yayana.
wanda zan nufo shi a duk lokacin da na ke
bukatar taimako, ina son ka ci-gaba
da kasancewa
malamina wanda zai dinga yi min nasiha a duk
lokacin da zan kauce hanya, ina son ka kasance
Me karfafa min guiwa mashawarcina a cikin
Wannan sabuwar rayuwar da zan shiga, wacce ban san daga inda zan farata ba”,
Ya Sayyadi Habib ya goge hawayen da suka
ziraro masa, ya yi saurin juya bayansa, domin ko
kadan baya son ta fahimci damuwarsa ta, tsananta, baisan ya karyar mata da guiwa yace
"Kada ki damu, duk a yadda ki ke son na
kasance miki zan kasance, na yi alkawarin zama
yayanki kuma malaminki, har karshen rayuwata,
duk abinda yaya yake ma kanwarsa, na yi
alkawarin zan yi miki, ke ma kuma ina rokon
alkawari daya daga gareki"
Afrah ta ce "Me ka ke so Ya Sayyadi?" Ya ce
ba tare da ya juyo ba
"Ina son ki yi min alkawarn
ba za ki daina neman ilimi ba, ba kuma za ki
daina koyar da dalibanki ba, za kuma ki kasance
mai hakuri da juriya a cikin wannan auran naki."

Page 48

Afrah ta kara goge hawayenta ta ce “ Nayi
maka alkawari Ya Sayyadi, na yi maka in sha Allah”, daganan ya juya ya dubeta yace “Ta shi ki tafi gida”, tayi masa wani irin kallo me cike da tausayawa, tace “Na yi zaton tare zamu tafi kamar yadda muka saba”, ya girgiza kai yace “kada ki manta yanzu a matsayin yayanki nake ba me neman aurenki ba, saboda haka ki tafi zan taho daga baya”. Ta gyada kai ta so su cigaba da magana amma kiran sallar magriba ya sa tayi saurin yi masa sallama ta fice a sanyaye.

Ayayin da ya sayyadi ya koma kan kujerar ajin ya
zauna yayi tagumi hannu bibiyu, komai ya tsaya
Masa cak bai taba zaton haka lamarin zai tsaya
ba Allah ya sani ya yi, bakin-ciki na rabuwa da
Afrah, domin da ita ya yi mafarkin gina rayuwarsa,
zuciyarsa ta yi kuna, ya rasa inda zai tsoma
ransa yaji dadi, yana son Afrah matuka, amma
dole ya goya mata baya, domin zama cikakken masoyinta.

Page 49

Bayan sallar Issha'"i. Mansur da Kabir suka shigo gidan domin
amsa kiran mahaifinsu, duk suna zaune akan
tabarma a kofar

Please Login or Register in order to submit comment