Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matukar wari,
tana idarwa, ko addu' a ba ta gama yi ba, ta
tashi ta shiga aikin goge aman, tana kuka me dauke da sautin ban tausayi.
Bayan ta gama gyara wajen ne,ta taimaka
masa ta janye shi daga falon zuwa uwardaka. Ya
bata wandonsa da fitsari, ya bata rigarsa da
amai duk da tana cike da jin nauyinsa, haka ta
taumaka masa wajen cire kayansa, ta sa masa
wasu , sannan ya koma kan gado da kansa, ya kwanta, cikin rashin cikin rashin dawowa hayyacinsa .
Bayan ya kwanta ne. Afrah ta fice ta koma
falonta, ta zauna ta dasa wani sabon kukan,
gaba daya har jikinta ya yi dumi, shin wace irin
mummunar rayuwa ta shigo a daranta na farko a
gidan mijinta?
Ba ta fara da komai ba, sai da aikin kwasar
aman dan giya da aikin gyara wajen fitsarinsa,
shin haka rayuwarta za ta kasance tare da Musaddik?
Idan ko har haka ne rayuwarta ta riga ta kare
babu sauran wani abu na farin-ciki ko na jin dadì
da ya rage à gareta. Kaiconta, kaicon wannan
mummunan rayuwar, hakika ta yi sadaukarwa
me girma, a yanzu ne kuma ta fahimci ba karamin aiki bane a gabanta, duk yadda take tunanin abin ya wuce nan,lalle dole ta karfafama kanta guiwa,

Karfe takwas Afrah ta yi wanka, ta gyara
kanta, sai dai kallo daya za ka yi mata ka san
tana cikin tashin hankali da matsananciyar damuwa,
domin kuwa har ta rame idanunta sun zurma ciki,
fuskarta ta yi fauu! Idanunta ma'abota girma da

Page 84

haske, duk sun kankance, a sakamakon kukan
da ta yi, har zuwa lokacin Musaddik barci yake yi ko motsi ba ya yi, ta leka shi yafi a kirga amma kwance yake tamkar matacce.

A dalilin hakan Afrah ta janyo hijabinta ta sa
ta fito zuwa cikin gidan, domin ta gaida Hajiya
Kilishi. A katon falonta ta tadda ita zaune da me
aikinta Amimi, tana ta kaiwa da komowa wajen
shirya abincin karyawa akan tebur, cikin sallama
Afrah ta shiga falon Hajiya Kilishi. Ta dago ta
kalleta gami da amsa sallamar can cikinta.
Har kasa Afrah ta zube tana gaida ta cike da
girmamawa da mutuntawa. Hajiya Kilishi ta
amsa ba yabo, ba fallasa, rai a bace kamar wacce aka yi
ma wani laifi, hakan ko ya ba Afrah mamaki,
Domin sanda aka kawota gidan a jiya, ba
haka ta karbeta ba, ta karbeta cikin kyautatawa
da kauna, to mènene yanzu? Me ya yi zafi? Za ta
ga irin wannan canji nan da nan, ko daman Hajiya Kilishi tana da
dalilinta na yin duk abinda ta yi a baya ne? "Ya
kwanan amarci?"
Tambayar Hajiya Kilishi ta katse Afrah daga
tunanin da take yi, ta dan kalleta kadan, ba tare
da ta ba ta amsa ba.
Hajiya Kilishi ta ci-gaba da cewa "Na san kin
yi kwanan amarci me dadì, domin ina da
tabbacin angon naki ya ba ki kyakkyawar kulawa
da dawowa akan lokaci dai-dai sallar asubah, na
san kuma ya zo maki da kyakkyawan sakamakon kaiwa asubah a waje, kinsan abinda yasa yakai wannan kokacin a waje , nasan kuma kin fahimci cewa mace bata gaban musaddik, abinda ke gabansa kenan wanda idanunki suka ganar miki”.

PAGE 85

Cike da mamakin maganganunta. Afrah ta
dubeta idanunta sun kada sun yi jajir!
Hajiya Kilishi ta gyara zamanta gami da yi
mata wani sakaran kallo, sannan ta ce
“Afrah na yi mamakin da ki ka amince da auranki da Musaddik a
matsayinki na yarinya mai natsuwa, mai kuma
ilimi, na yi zaton za ki yi kokarin girmama kanki,
ki samu rayuwa ta-gari, wacce za ta amfaneki ta kuma amfani yayanki, wadanda zasu so samun uba nagari, sai ga shi kin buge da watsa ma
kanki rayuwa da kanki. Meye riba ko amfanin
auranki da mutumin da bai san inda rayuwarsa tasa gaba ba, me zaki tsinta?”

Ta kara kura mata ido ta ci-gaba da cewa.
"Shi mahaifin naki daya hada auran ku, ya san
cewa Musaddik bai dace da ke ba, idan kuma
don abin duniya ya aura miki shi.
Ya san cewa Musaddik baida ragowar komai
na gadonsa, asalima inda ku ke zaune yanzu, a
matsayin alfarma ce, taimaka maku na yi,
alfarma nai maku, na ba shi aron wajen da ya aje ki. Idan na
so sai na ce ya je ya nemi wajen zama, amma na
taimaka masa, domin Allah."
Anan ne Afrah ta dago da idanunta, da tuni
suka fara zubar da hawaye ta ce
"Mahaifina bai
taba tunanin ya aura ma Yaya Musaddik ni
sabida tunanin fanshewa daga wani abin duniya daga gare shi ba…………..

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan Imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM


Page 86

ya aura ma sa ni ne, saboda Allah ya riga ya
rubutani a cikin matan da Yaya Musaddik zai
aura Ita kuma Kaddarar Ubangiji babu wanda ya
isa ya kauce mata, don haka a shirye na ke da
na karbi Kaddarar, zan kuma rike Yaya
Musaddik da daraja fiye da tunanin me tunani, zan zamar masa majingina “
Hajiya Kilishi ta saki tsaki ta ce "A hakan har
wace daraja Musaddik yake da ita? Ke kam! Ki
na da babban aiki a gabanki, na zama da dan
iska, dan giya a matsayin miji"
Afrah ta yi dan murmushi ta ce "Ba komai.
Allah ya ba ni ikon ci-gaba da zama da shi a
hakan domin ta nan zan sami aljannata”.
Tana gama fadin hakan, ta mike, ta ce "Dama
na zo na gaisheki ne, bari na koma, kada ya
tashi barci ba na nan”
Tana gama fadin haka ba ta saurari komai ba,
ta fice, a yayin da Hajiya Kilishi ta bi ta da wani
mugun kallo, zuciyarta a zafafe, lallai yarinyar
nan zuciyarta a dake take, yanzu duk abinda
musaddik ya yi mata a jiya ba ta gani ba?
Mai-gadi ya tabbatar mata da cewa sai asubah
ya dawo gida, kuma ya dawo a buge da giya,
ace ango ya yi ma amaryarsa haka a daren
farkonsu ai ya isa dalilin da za ta nemi kashe auran ma, amma
kalleta ko a jikinta. Hmm! Rashin sani, ya fi dare
duhu, domin Hajiya Kilishi ba ta san dalilin auran

Page 87

Afrah da Musaddik ba kenan, don ya sami me
taimaka masa, tare da tallafa masa da kuma
Kokarin maido da shi hanya madaidaiciya, don
haka duk halayensa ba baki bane agun Afrah, ta
sani, asalima halayen nasa su ne suka sa ta aure
shi . Afrah na shiga daki, ta tadda Musaddik
zaune a bakin gado, ya yi tagumi hannu biyu,
tana ganinsa a haka, ta yi saurin korar damuwar da ke fuskarta cike da fara' a, ta karasa inda yake, ta ce “ ka tashi kenan”, ya dago fuska cike da damuwa mara misaltuwa, ya kalleta a hankali cikin matsananciyar kunya, ya
dauke kallonsa daga gareta, sannan ya ce.
"Afrah don Allah ki yi hakuri, ki yi min afuwa “
- Ta dan yi murmushi ta ce "'Me ka yi da ka
ke ncman afuwata?"
Ya numfasa ya ce "Kin fi kowa sanin abinda
na yi, domin ko ni da na yi, sai dai na kintaci
abinda na yi, na tuna, dan abinda zan iya tunawa amma sanin
komai, sai ke da na yi a gabanki, don haka ki yi
hakuri, koma me na yi a daran jiya, ina neman
yafiyarki, don Allah"ta jinjina kai tace
"Ya wuce, babu komai, amma kasan wani abu?”
Ya so ya kalli cikin kwayar idonta amma sai yaji bazai iya hada ido da ita ba, ya girgiza kai yace “A’a” Afrah ta
dan gyara tsayuwarta tace "Ina yi maka
kallon me ilimi wanda ya san abinda Allah ya
fada akan giya da kuma me shanta, ban taba tunanin zan

Page 88

tadda kai a cikin shaukin shan giya ba, bayan ka
san giya ita ce uwar kaba’irai
Komai za ka iya aikatawa, idan ka sha giya,
to me zai sa ka sha, me zai sa ba za ta zama
abar tsana a gunka ba, sai dai abar kauna,
sannan ka rasa lokacin da za ka sha, sai a daren
auranka yaya Musaddik? Me ya sa za ka yi min haka?, ko ya ya ne ba zaka iya hakuri ba ko da a wannan daren ne, da nake bakuwa a gareka”.
Musaddik ya runtse idanunsa, ya bude, sannan
ya ce "Ba za ki taba ganewa ba Afrah, ba za ki gane ba, wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa na ke tsoron aurenki, ba zaki gane komai ba a yanzu, ni nasan yadda nake ji”

Yana gama fadin haka, ya mike yana kokarin
shiga bandaki. Ya na kauda kansa a dalilin baya son taga hawayen da yake kokarin boye mata.
Afrah ta yi kokarin maida hawayenta, jikinta ya yi sanyi tayi saurin cewa “yakamata ka fara yin wanka ne kafin kayi sallah, bari na kaima ruwan wankan”
A hankali musaddik ya dawo da baya, ya
koma ya zauna a bakin gadon, ya sadda kansa kasa,a yayin da Afrah ta
yi gaggawar fita, ta hada rishonta, ta dura
Kananzir wanda harda shi a cikin kayan da aka kawota da su.ta kunna ta dora masa ruwan wanka, cikin kankanin
lokaci ruwan ya yi zafi, ta juye ta kai masa. Ya yi
wankan, ya yi kuma alwala , bayan ya fito ne ya
kintsa ya yi sallar asubah. Dai-dai Karfe tara da
rabi zuwa lokacin ta gama abin karyawa.
Domin Malam Mahmud ya yi kokarin hado
Afrah da garar abinci, hatta garin tuwo,
sai da ya hadota da shi. Musaddik yana gama karyawa bai saurari komai ba ya fice duk da abincin ma kadan ya ci.

Ko kadan babu dokin auran a ransa, balle har
ya yi tunanin ya zauna a gida na dan lokaci tare
da matarsa. Haka ya tafi ya bar ta cikin matsananciyar

Page 89

damuwa. Domin duk yadda ta dauki abinda
sauki Ta ga ba haka bane, hakika akwai katon aiki a gabanta, ta ko wane bangare.

WAIWAYE, ADON TAFIYA.......

Alhaji Mansur Musaddik Mai Fata shahararre ne,
kuma hamshakin dan kasuwa, wanda ya mallaki
manya- manyan kamfanoni na sarrafa fatu,
sannan bayan hakan yana safarar fatun zuwa kasashe makwaftan Nigeria.
Hakan ya sa kasuwancinsa ya kara fadada, ya
kuma sami karbuwa sosai, mutum ne me saukin
kai, me addini tare da son kyauta ma 'yan’uwansa,
duk da ya taso cikin matsananciyar tsana ta
Yan uba a dalilin maraicin uwa da uba da ya yi gaba daya, amma duk da haka bai hana shi taimaka musu ba, bayan da Allah ya zabe shi a cikinsu ya azurta shi. Haj kilishi itace matarsa
ta farko,auren saurayi da budurwa. Haj kilishi
macece me ji da kanta, fadin rai da daukar kanta wani abu, tana da karfin izza,
gata da matsanancin kishi, wanda hakan yasa
take ganin Alhaji Mansur ba zai iya yi mata
kishiya ba, musamman idan ta yi la'akari da irin
son da yake mata, da kuma bai taba nuna mata yana da sha’awar wata ya mace ba bayan ita, ko sha’awar ya kara aure ba, shi yasa ta mike kafa take shimfida iko da mulki.ta haifa masa 'ya' ya har uku duk mata
Hassana da Hussaina, sai Amina. Bakincikinta
daya a rayuwarta, shine yadda bata da da
namiji, ga haihuwar ta tsaya mata, ta tashi hankalinta wajen ganin likita da son ta cigaba da haihuwa amma likita ya tabbatar mata lafiyarta kalau haihuwar ce dai kawai Allah bai kawo ba. Wannan al’amari ya kara tada hankalin haj kilishi domin tana da

Page 90

gamshahshen sanin cewa babu abinda mijinta
yake so yake kuma nema ido rufe irin magaji da namiji, saboda yana kwadayin ya samu mataimaki a lokacin da karfinsa ya kare, jikin Haj kilishi ya fara sanyi, damuwa ta fara mata yawa, tunaninta na mijinta va zai iya mata kishiya ba ya fara canjawa.don haka
kullum addu'oi 'nta. Allah ya ba ta haihuwar da
namiji, amma ba ciki ba dalilinsa,
Hakan ya sa a lokacin da Alhaji Mansur ya
furta mata maganar Karin auransa da Harirah
hankalinta ya yi masifar tashi, hauka ne kawai ba
tayi ba, haka zalika ta yi Kokarin lalata auran ta
hanyoyi da dama.
Domin ta yi ta asarar kudinta a wajen
Malamai da Bokaye, don dakatar da auran.
amma da yake Kaddararran al'amari ne. Allah ya
riga ya Kaddara Harirah sai ta kasance uwar dan
Alh Mansur, sai da Allah ya tabbatar da auransu.
Sai dai Harirah ta zauna cikin kunsar bakin-
cikin Hajiya Kilishi, domin kuwa ta kankane komai
a gidan. Harirah ba ta da wani karfi a matsayinta
na matar gida, komai sai Hajiya Kilishi ta amince,
ta kuma sa baki sannan yake yiwuwa.
Koda ta bangaren Mai-gidan ne, domin Hajiya
Kilishi ta riga ta gama mallake shi ta hanyoyin
sihirinta. Hakan ya sa Harirah ta ci-gaba da
zama a wulakance a kaskance a gidan mijinta.
Har zuwa lokacin da Allah ya yanke mata
wahala, ya dubi hakurin da ta yi a dalilin cikin
da ya bata, tunda ta sami cikin, kadarin Hajiya
Kilishi ya Karye, domin yadda Alhaji Mansur ya dauki son duniya ya dora akan cikin, tamkar ba’a taba yin ciki a gidansa ba sai akan Harirah.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam
MUSABBABI
BISMILLAHIR RAHMA NIRRAHIM

Page 91
ga kuma kyakkyawar kulawa da take samu daga gare shi,
wannan lamari ya fi komai tayar ma da Hajiya
Kilishi hankali.
Musammam da ta fuskanci da gaske Harirah
ciki, gareta don haka ta ci-gaba da asarar
Kudinta a wajen Malamai, domin a lalata cikin
Harirah Amma ina. Alkawarin Allah baya tashi.
Komai tayi a banza, cikin Harirah ya ci-gaba da
girma da kuma samun kulawa. Haj kilishi ta cigaba da zama cikin dar dar da fargabar kada Harirah ta haifi da namiji.
Har zuwa lokacin da cikin ya isa haihuwa. Da
yake Allah ya riga ya rubuta Harirah ba za ta
rayu da danta ba, ya sa tana haihuwar dan,
Allah yana daukar ranta, ga koshi, ga kwanan yunwa kenan!
Alhaji Mansur na murnar samun abinda ya dade
yana addu'ar samu, ga tashin hankalin rashin
matarsa, uwar dansa daya tilo daya fara samu.
Wacce yake sa ran za ta kula masa da dansa har zuwa girmansa. Ya shiga tsananin tashin hankali, irin rashin kyautatawar da ya ke yi ma Harirah a da ya yi ta dawo masa yana ta da masa hankali, ya so Harirah ta rayu ko don ya jiyar da ita dadin da bai jiyar da ita ba a baya.

Ta Bangaren Hajiya Kilishi kuwa, ba Harirah
ta so ta rasu ba, dan da ta haifa ta so ya rasu, domin tana ganin duk duniya ba ta da wani
bala'i sama da shi.don haka don Harirah ta rasu,
ai ta barta da masifa tamkar an
kashe maciji ne , ba a sare kan ba
Rasuwarta ba wata fa'ida a gareta, gaba daya
tsanar dan da Harirah ta haifa ya gama ratsa
Jinin jikin Hajiya Kilishi, ko kadan ba ta kaunarsa.
Hankalin yan’uwan Harirah yafi na kowa tashi adalilin rashin yar’uwa da su kayi da kuma tunanin yadda dan Harirah zai rayu ba tare da mahaifiyarsa ba.

Page 92
Tunaninsu kuma ya kara karkata akan waye zai dauki Musaddik ya rike shi, ya raine shi kamar yadda uwa zata raini danta.Inna
Halima wacce ita ke bin Harirah a haihuwa, da
yake kuma shekarunsu ba wani tazara bane
sosai, ya sa tare aka yi masu aure.
'Inna Halima kuma ta rigata haihuwa da
makwanni hudu, danta ita ma namiji ne, mai
suna Abdullahi, don haka ta roki Alhaji Mansur
da ya bata Musaddik ta hada da Abdullahi ta shayar da su.
Alhaji Mansur ya yi farin-ciki matuka, ya
kuma sami dimbim natsuwa ya kuma kalli Inna
Halima a matsayin maganin matsalarsa, kuma
mai taimaka masa akan gudan jininsa Musaddik
dan da yake jin kamar ba shi da kowa duk
duniya Sai shi. Dan da yake jinsa har cikin jinin
jikinsa, wannan shine dalilin da ya sa Inna
Halima ta dauki Musaddik ta hada shi da danta da ta haifa.
Wanda ba haka Hajiya Kilishi ta so ba, ta so
Musaddik a bar shi ya tagayyara ne,
da rashin nonon uwa, har' shi ma ya bi uwar ta
sa, amma sai ga shi ya sami wata uwar wacce take da tabbacin zata bashi kulawa kamar yadda mahaifiyarsa zata ba shi ko ma fiye da haka, domin yan’uwan Harirah suna daya daga cikin yan’uwan da bata taba ganin zurfin zumunci irin na su ba, ga shi dai basu da yawa sai shegiyar zuciya da hadin kai kamar kashin awaki.

Page 93

Bayan "yan watanni, lamarin ya fara kwanta ma
Hajiya Kilishi, musamman da yake ba ganin
Musaddik take ba, ta kuma mallaki hankalin
Mijinta waje daya, domin baya sha'awar ya kara
wani auran. Amma abu daya ya ci-gaba da nukurkusar
zuciyar Hajiya Kilishi tare da hanata samun,
sukuni shine ganin irin yadda Alhaji Mansur yake
matukar kulawa da Musaddik.
Domin hatta gadon da zai kwanta, sai da ya
saya masa, kaya kuwa na sawa na alafarma
yake saya masa, duk wani abu da ake ma da dan gata, to
fa shi yake ma Musaddik, kuma kullum kwanan
duniya, in dai yana kasar , to duk aikin da ke
gabansa, sai ya ture ya je ya ga Musaddik sau
uku safe rana da daddare, hakan ya sanya
shakuwa tsakaninsa da dansa.
Su kansu su Inna Halima rikon Musaddik ya
amfanesu sosai, tunda mijinta ba shi da wani,
Karfi don haka Alhaji Mansur ya dauke shi ya ba
shi aiki a daya daga cikin kamfanoninsa, wanda
ake yin takalma, sannan kuma shine ya rushe gidansa, ya
Kara gina masa sabo dai-dai da rayuwar dansa.
Wannan lamari ya tayar ma da Hajiya Kilishi
hankali, dalilin da ya sa kuma kenan ta tsani Inna
Halima, domin ta sha nikar gari ta je har gidan ta
ci mata mutunci ta kuma kirata da makwadaiciya , tun
tana shanyewa har ta gaji, ta gaya ma Alhaji
Mansur.

Page 94

Wanda hakan ya yi sanadiyyar da suka sami
sabani da Hajiya Kilishi. Ya yi mata kaca-kaca,
ya kuma gargadeta da kada ta kara taka gidan
Inna Halima da sunan cin mutunci, idan kuma ta
Kara to ta shaida a bakin auranta.
Hakan ya sa dole Hajiya Kilishi ta hakura da
zuwa gidan Inna Halima, ba don ta so ba, ko don
ta daina jin zafinta ba, sai don tana son igiyar auranta da take tunkaho da ita, sai dai ta cigaba da bin bokaye da malamai domin a raba soyayyar da ke tsakanin Musaddik da mahaifinsa, ta kashe kudi ba iyaka, amma bata dace ba, ko ya yi kamar ya kama sai kuma ya karye. Ta rasa yadda zata bulloma al’amarin.

Shekarun Musaddik biyar , ya fara makaranta
wacce ta masa sunanta, a lokacin ne kuma
Haj Kilishi ta fara sa kahon zuka tare da tusa ma
Alh Mansur son ya amshi Musaddik ya dawo
hannunsu Amma Alhaji Mansur ya ki daukar hudubarta,
domin ya fi kowa sanin halinta, yana da tabbacin
Musaddik ba zai taba jin dadin zama da ita ba.
A haka a daddafe har Musaddik ya kammala
firamare, cikin kyakkyawan yabo da sakamako,
ga kyakyawar tarbiyyar daya samu daga uwar
rikonsa ,halinsa na hakuri da son mutane ya kara
taimaka masa wajen cikar kamalar rayuwarsa.
Musaddik tun yana yaronsa, kyakyawa ne sosai
me cikar kamala, kwarjini ga farin-jini.

Burin Hajiya Kilishi bai cika ba na raba Inna
Halima da Musaddik har sai da Musaddik ya kai
aji hudu na sakandire, sannan Alhaji Mansur da
kansa ya zauna da Inna Halima da mijinta Malam
Saminu da kuma Malam Mahmud mahaifin Afrah, ya

Page 95
bukaci zai maida rikon dansa hannunsa, ya
Kuma yi masu godiya a bisa rikon da suka yi ma
marayan dansa.
À ranar Inna Halima ta yi kuka har hawayenta
suka Kare , domin ta shaku da Musaddlik tana kuma
Kuma Kaunarsa fiye da ya' yanta da ta haifa,
babu wanda bai tausaya mata ba a cikin wadanda aka yi zaman da su.
Alhaji Mansur ya ba Inna Halima da mijinta
da Malam Mahmud kyautar kujerun makka, tare
da kudi masu tsoka, domin ya yi ikirarin ba shi da
wanda suka fi masa 'yan-uwan Harirah,
Domin su ne suka taimake shi akan dansa a
lokacin da yake bukatar taimako, kuma ba zai
taba mantawa da 'Yar-uwarsu Harirah ba, wacce ta ba
shi abinda zuciyarsa ke shaukin samu, ta kuma
rasa ranta a dalilin hakan.
Wannan karamci da Alhaji Mansur ya yi
masu, ya ba su sha'awa sun kuma yi masa
godiya sosai, sai dai kamar yadda Inna Halima
ta shiga damuwa akan rabuwa da Musaddik,
haka shi ma Musaddik din ya shiga matsananciyar damuwar
rabo da Mamansa, ya yi kewarta, ya yi kuka mai
tsanani, amma ba shi da yadda zai yi, domin
haka Allah ya Kaddara ma rayuwarsa.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 96



Komawa da rayuwarsa gidan mahaifinsa ya
fuskanci bambanci matuka na kulawar uwa
abinda ya saba Inna Halima na yi masa, na nuna
Kauna tausayi da soyayya, sam ba haka ya riska a gidan mahaifinsa ba.
Daga matar ubansa, domin babu abinda yake
fuskanta sai tsana da tsangwama daga Hajiya
Kilishi. Amma a bayan idon mahafinsa, domin a
gaban idonsa, duk duniya babu me kima da mutuncin musaddik a gun Haj kilishi.domin takan nuna duk duniya babu wani abin da take so sama da shi.
Hakan ya sa Alhaji Mansur ya sami natsuwa,
domin a tunaninsa Hajiya Kilishi ta canja halinta,
tana zaune da dansa domin Allah akan mutuntawa.
Shi kam Musaddik masifar tsoron Hajiya Kilishi
yake yi, don haka ko a cikin tunaninsa.
Bai taba tunanin ya gaya ma mahaifinsa halin
da yake ciki da Hajiya Kilishi ba, sai dai idan abin
ya dame shi, ya kwaso jiki zuwa gidan Inna Halima da kukansa ya na gaya mata.
Amma ko ta yi kokarin ta je ta gaya ma
Alhaji Mansur, sai Musaddik ya hanata, a
Cewarsa baya bukatar duk wani abu da zai tayar
da hankalin mahaifinsa, don haka idan tana son farin-cikinsa, to
kada ta gaya masa komai, har kullum Inna
Halima tana sha' awar halin Musaddik na
damuwa da farincikin wasu fiye da farin-cikinsa. bata da yadda zatayi tunda tana bukatar kwanciyar hankalin musaddik, sannan kuma bata son ta shiga lamarin gidan Alh mansur, a kokarin ta na tsira da mutuncinta a wajen Alh mansur din.

Haka lamarin ya ci-gaba har zuwa lokacin da
Musaddik ya kammala makarantar sakandire,

Page 9

inda Alhaji Mansur ya yanke shawarar kai
Musaddik kasar waje, domin ya samu Digree
dinsa a can,Tashin hankali!
Hajiya Kilishi ta samu matukar damuwa akan
hakan, shin wace irin kulawa ce Musaddik yake
samu fiye da "ya 'yanta, wadanda tuni suna ma'aura, ko wacce na gidan mijinta.
ita shi kenan ba ta da wani abu da za'a kyautata
masu, kamar yadda Alhaji Mansur yake kyautata
ma musaddik Me ya sa ya fi son Musaddik akan
kowa? Ko don shine Magajinsa? Ita shi kenan haka za ta tashi
a tutar babu? A gaskiya Musaddik ya zamar
mata fitina, yanzu har kasar waje zai je ya yi
karatu domin idonsa ya Kara budewa.yasan
"yancinsa, ya gagareta ya kuma
buwayi rayuwarta. Duk hanyar da za ta bi, don ta
kawo cikas akan kai Musaddik kasar waje, ta bi,
amma ba ta sami nasara ba.don tuni Alh mansur ya samo masa gurbin karatu a oxford university dake london.Haka zalika ba a dauki wani
dogon lokaci ba, aka gama komai. Alhaji Mansur
da kansa ya dauki Musaddik zuwa London, bai
dawo ba sai da komai ya yi dai-dai.
Watau ya tabbatar da Musaddik ya fara shiga
aji,sannan ta dawo Nigeria kan kasuwancinsa
a yanzu ji yake ya mallaki komai na
duniya, tunda yana da babban da namiji kamar

Page 98

Musaddik,wanda zai iya daukar nauyin kasuwancinsa, zai iya kula masa da dukiyarsa,
shi ya sa yake kokarin ba shi ingantaccen ilimi da
zai amfane shi. Ya kuma amfani rayuwarsa.
baida fargabar komai a yanzu, koda mutuwa ya yi.

A yayin da Hajiya Kilishi kullum take kwana
take tashi da tunanin, yadda za ta yi da,
Musaddik domin ta dauke shi a matsayin shine matsalar rayuwarta.
Musaddik ya dage wajen mutunta rayuwarsa a
London, ya rike mutuncinsa, duk wata harka,
idan ba ta arziki bace, ba za ka taba ganinsa a
ciki ba, ya rike addini da al'adarsa, abinda ya kai shi, shi yake
yi, ya maida hankalinsa sosai wajen karatunsa domin ya riga
ya fuskanci abinda mahaifinsa ya fi bukata
kenan a duniya Don haka ba zai taba ba shi kunya ba, zai tsaya ya yi
abinda ya kamata. Dalilin hakan
Musaddik sai da ya zama (Best Student), saboda tsananin hazakarsa .cikin haka
har ya kammala Digree dinsa, ya kuma dora
Masters dinsa, sau uku kawai ya taba dawowa
Najeriya.
Sai dai Alhaji Mansur da yake kokarin
ziyartarsa akai-akai, har ya kammala Masters
dinsa ya tattaro ya dawo gida Najeriya, ya zama
nagartaccen matashi me kwarjini da cikar kamala, ga kyakkyawan hali abin koyi ga kowa.


Page 99

Dawowar Musaddik Najeriya bayan kammala
karatunsa. Alhaji Mansur ya sami cikar burinsa,
gaba daya ya ji ya gama mallakar duk wata
ni’ima ta duniya, mako uku da dawowarsa.
Aka yi gagarumin bikin ba shi kamfanin yin
siminti na Alhaji Mansur daya mallaka masa, ya
kuma mallaka masa katafaren gida, da mota.
amma wannan. karon sai da Hajiya Kilishi ta yi
bore akan ba za ta taba yarda da wannan hukuncin ba.
Domin ita ma 'ya' yanta da ta haifa ai 'ya' ya
ne, ganin yadda ta tada hankalinta, ya sa akan
dole ya sai ma 'ya'yanta motocin hawa, duk da
suna gidan mazajensu, sannan ya mallaka musu makudan kudade domin su tsaya da kafafunsa.hakan ne kawai ya sassauta mata
damuwar da take ciki.
Sai dai tana ganin lokaci ya yi da za ta dauki
Kwakkwaran mataki akan Musaddik. A lokacin ne
kuma Alhaji Mansur ya bukaci Musaddik ya fito
da mata, ya yi masa aure.
Domin cikar kammalarsa, domin duk a
rayuwarsa abinda ya rage ya yi masa kenan, ya
cikasa rayuwar dansa, shi kam! Musaddik ba

Please Login or Register in order to submit comment