Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

“ ke dube ni nan bana son shirme To shi ma tausayin
ki yi gaggawar cire shi a ranki, domin daga tausayin
ne ake samun soyayya, auranki da shi kuma ya kusa zuwa karshe saura kiris
Don rayuwarki dama ba ta dace da ta
Sa ba,dukiyarsa da son cikar burina su ne musabbabin
auranku, kamar yadda cikar burina, zai
Zama musabbabin rabuwarku”.
Hannatu ta numfasa, ta dade tana ganin mata
marasa imani, ciki har da mahaifiyarta, amma ba ta
taba ganin mara imani irin Hajiya Kilishi ba, a duk
lokacin da ta yanko wani sharrin ta kan yi zaton ko shaiden ne ya fito a suffarta.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️

Page 126
Mama Hauwa ta mika hannu saman firij
ta dauko wata bakar leda, ta fice ita da Na'ima. Afrah
ta mike da nufin rakasu, amma ga
mamakinta suna fitowa, sai ta ga Mama Hauwa ta durkusa ta kwashe
tarkacen kayan mayen da ta tara,
ta zuba su a cikin ledar. A nan ne Afrah ta dubeta ta ce "Mama me za ki yi da su?” ta karasa magana tana kokarin gyara tsaiwarta.

Ta balla mata harara ta ce “zan kaima
mahai finki tsarabar da na samo daga gidanki ne, ina ganin zai fi gamsuwa da halin da kike ciki idan ya gani”.
Gaban Afrah ya yi mummunan faduwa,
da sauri ta karasa gabanta ta ce cikin magiya da nuna tsananin damuwarta
"Don Allah,
Mama kada ki yi min haka, kada ki tayar
ma da Baba hankali, meye amfanin yin hakan?"
Ta kara sakar mata harara ta ce “Tashin
hankalin me zai yi, bayan duk wanda ya sai rariya,
ya san za ta zubar da ruwa, ke mu tafi da Allah" ta fada cikin rashin nuna damuwa. tasa hannu ta jawo
hannun Na'ima suka fice ba tare da ta damu da
magiyar da Afrah take yi mata ba.
Haka Afrah ta kasance a cikin bakinciki,
Bayan tafiyarsu Mama Hauwa da kyar
ta gama wankin, amma ta kasa yin guga, haka ta ninke ta
ajiye, hatta abincin da ta yi, ta kasa ci,
saboda damuwa, ga Musaddik tun safe daya fita, har yanzu bai dawo ba.

Ta bangaren Mama Hauwa kuwa, haka ta kasance cikin wani irin nishadi da farinciki,tun bayan komawarta gida.
ta kosa kwarai Mallam Mahmud ya dawo ta zazzage tanadin rashin mutuncin da ta tanadar masa. Har sai da Malam Mahmud ya
dawo, bayan sallar Issha'i, ya zauna kan tabarma, a kofar dakinsa inda ya saba zama .

Page 127
Mama Hauwa ta kawo masa tuwo, zai fara ci kenan, saboda
wulakanci da rashin mutunci, kawai sai
ta koma ta zauna kan kujera 'yar tsugunno tana murmushi tace
“Ba ka tambayeni ya na baro Afrah ba,
bayan ka san na ce maka zan je gidanta yau?" Ya dan muskuta ya na dan murmushi yace
"'Na san lafiya lau take ai, shi ya sa
ban tambayeki ba, kuma ko kadan,
kada ki bari jama'a su san cewa sai yau ki ka je gidan Afrah,
domin abin kunya ki ka yi. Ace tsawon
wannan lokacin ba ki je kin ga dakinta ba, sai yau."
Ta tabe baki ta ce "Idan jama'ar suka ji,
me za su yi min? Dole ne na je akan lokaci? Ba sai na
sami lokaci ba, sannan zan je."
Ya juya kan tuwonsa zai fara ci, ba tare
daya Kara magana ba. Amma sai ta Kara katse shi, tamkar
tana yi masa bakin-ciki da cin tuwon
tace “Na je na tadda ita tana ta akin yima mijinta
wanki, gama tsarabar dana taho maka da ita daga
cikin wadanda yake ragewa a aljihun wandonsa”,
Malam -Mahmud ya juya yana kallon
kayan mayen da take zazzage masa a gaba, a fusace ya zaro idanunsa alokacin da ya gama fahimtar ko me take juye masa a kasa, rai a bace yace

"Meye haka Hauwa?"cikin nuna halin ko’in kula mama Hauwa tace

" meye kuwa da ya wuce Kayan mayen
Musaddik, na taho maka da su domin ka gani".
Ya yi mata wani mummunan kallo ya ce.
"Amma Hauwa ba ki da mutunci, to
yanzu da ki ka kwaso min, idan na gani, me zan yi, meye
kuma amfanin kawo min?"

Page 128
Ta tabe baki ta na sa hannu tana kara
tona kayan,tace “Haka ne fa kuma,
babu amfanin na kawo maka, tunda ka riga ka sani, ka
san komai, amma ka dauki 'yarka ka ba
shi,Hakika ni ma na fara tunanin akwai abinda ka
ke hange a gun Musaddik, da ya sa ka ba shi auran
'yarka, don idan ba hangen wani abu ba, na dukiya ban ga
dalilin da za ka kashe ma 'yarka rayuwa da auran Musaddik ba, don banga amfanin da hakan zaiyi maka ba daga kai har Halimar me mara maka baya”
Malam Mahmud ya buga tsaki ya ce "Dukiya,
dukiyar banza, me Musaddik din ya aje? Kin sani,
na sani. Musaddik komai nasa ya Kare, tabbas ina
da manufar hada su aure.
Amma ba irin manufar da ku, ku ke tunani ba,
don haka Afrah 'ya ta ce, ni na ga damar yin hakan
da ita. Kuma ina gargadinki da ki fita harkata da ta
'yata, tunda ba 'yarki bace balle ki ce ban isa na yi iko da ita ba, ita taki yar ai na bar miki kayanki ko, to babu ruwanki tsakanina da yata, kuma ko dar banji ba don naga wannan abin, illa kaimi da ki ka kara min na kara jajircewa da yi ma yayana addu’a”.
Mama Hauwa ta mike "Eh ai dama
bance yata bace, ba kuma na fata ta zama yar tawa, ni ma karambanina ya jawo min, ina ruwana kuwa,idan musaddik ya na iyawa ma ya zama dan kashin kasuwa karewar iskanci”
Ya kara watsa mata wata uwar harara yace "Na ji, ki tafi ki ba ni waje, kuma kada ki kara
takawa gidan Afrah balle har ki je ki sa idon daukar
magana, babu ruwanki da ita, balle
mijinta yadda ba mu kasa da ke ba don Allah kada ki dauka”,Ta yi shewa ta ce
"To sai me? Sai ka ce wani
mijin kirki, gidan Afrah kuma ba zan kara zuwa ba,
tunda ba aljanna ake rabawa a can ba,
ga kayen mayen nan, idan ka gama gani, sai ka san inda za ka
aje". Ta saki tsaki ta shige daki ta rufe kofarta

Page 129
Malam Mahmud ya kurawa kayan
mayen ido,idanunsa cike da hawaye, zuciyarsa tana tafasa matukar tafasa damuwa ta kara mamaye shi. Hakika ba haka ya so
rayuwar 'yarsa ta kasance ba, amma babu yadda ya
iya, haka Allah ya kaddara musu duka.
Tausayin Afrah ya kara kama shi, a hankali ya
janyo kayan, ya kwashe ya maida su cikin ledar,
cikin matsanancin tashin hankali, ya ture kwanon
tuwon gefe, ya tashi ya nufi bandaki, ya jefasu
cikin masai. Sannan ya shige dakinsa ya
kulle kofarsa ba tare daya ci tuwon ba. Duk da yunwar da yake ji, ya kasa runtsawa domin yadda ya ga rana haka ya ga dare, sai dai ya yi kokarin raya daren ta hanyar yin nafilfilu wanda duk addu’ar kan Afrah da Musaddik ta kare

Washegari kuwa shi ma din cike da
damuwa Mallam Mahmud ya je gidan Inna Halima, ya gaya mata
komai gami da yi mata umarnin ta je ta kara karfafama
Afrah guiwa tare da ba ta hakuri. Inna Halima
ba ta yi kasa a guiwa ba, ta nemi izinin mijinta, ta
tafi gidan Afrah. Wanda Afrah ta ji dadin ganinta,
amma tana fara yi mata maganar Musaddik. Ta san
Mama Hauwa ta je ta yi abinda take zaton za ta yi.
Ta dubi Inna Halima ta ce
"'Inna me zai sa ku
tashi hankalinku, don kawai Mama Hauwa ta je ta
gaya maku abinda ku ka riga ku ka sani? Kun san
Yaya Musaddik ba mutumin kwarai bane, akan
wannan dalili ne ma na aure shi, to me zai sa ku
damu? Bayan addu'a kawai ya kamata ku bi mu da shi ba damuwa ba”
Inna Halima ta jinjina kai , sha’awar Afrah da halayenta suka kara kamata
tace “Maganar ki haka take Afrah, don haka Allah ya yi maku
albarka, ya taimake ki akan duk abinda ki kasa a gaba, mun gode da hadin kanki, Allah yasa wata rana farinciki ya wanzu acikin rayuwarki”.

Page 130

Afrah ta sauke numfashi a hankali Tace "Amin Inna". Inna Halima Ta dan dubeta
tana kokarin gano wani abu, tace
"Amma Afrah yaya zamanku, ki na jin
jindadin zama da shi, kuma ki na ganin akwai alamun yana
rage mugayen dabi'unsa, ma'ana ana samun canji ko yaya ne kuwa?”
Afrah ta dan yi murmushi me kama da
yake sannan tace "Inna ai Yaya Musaddik yana da dadin zama
Kwarai, kuma ana samun canji da abubuwa da dama
akan halayensa, sai dai mu ci-gaba da addu'a kawai domin babu abinda ya gagari Ubangiji “
Fuskar Inna Halima ta cika da fara'a da jindadin maganar Afrah, ta shiga fadin
"'Alhamdulillahi. Allah ya kara
taimakon mu akan wannan kyakkyawar niyyar ta mu. Allah ya saka miki da
alheri Afrah”,Duk wasu tambayoyi da Inna Halima ta yima
Afrah, tana kokarin ba ta amsar da za su sata farinciki
ta kuma yi sa’a har ta bar gidan, ba ta
fahimci karya ko daya a cikin maganganun Afrah ba.

Daga taskar

Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 131

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, yau fari gobe baki, tuni Afrah ta aje maganar wai dole saita sami kulawa ko nunin soyayya daga Musaddik domin tasan babu wannan a gabansa, A hankali har garar da Malam Mahmud ya yima Afrah
ta Kare, har ta kai abincin da Afrah
zata ci ya fara yi mata wahala, tunda Musaddik baida ko halin da zai iya
ciyar da ita, idan ma ya samu abinda zai ciyar da itan abin takaici duk sai dai ,
su Kare a wajen sbaye-shayensa da kuma bawa sauran mutane domin duk abinda ya samu shaye shaye kan ci rabi jamaa kan ci rabi,don akwai fa kyauta da ka tambaye shi in dai yana da shi zai dakko ya baka, ko da zai zauna baida ko sisi. Har kuma yanzu ya kasa jin aransa shi ma magidanci ne.
Ta Bangaren Hajjya Kilishi kuma ko
farantin daya na abinci ba ta iya ba ta balle harta sa ran zata iya taimaka mata da wanda zata dafa. Ko cikin gidan ta shiga takan yi kokarin maidata baiwa ne ta hanyar sanyata yin aikin gidan duk da ga masu yi mata aiki nan, sannan ga cin zarafi da wukakanci na ba gaira ba dalili, wanda Afrah take ganin ba zata iya dauka ba, domin dai a tsaye take bata jurar duk wani wulakanci daga Haj kilishi shi yasa ta ja kanta ko cikin gidan ta rage shiga, babu kuma yadda za’ayi komai wuyar da take ciki ta bude baki ta roki haj kilishi wani abu domin tasan tozarta ne a gareta da mijinta, ya kuma dole ta boyewa Haj kilishi gaskiyar halin da take ciki saboda bata son ta yi farinciki ko kadan akan yanayin zamansu da musaddik,
Amma ko da ta daina shiga bangaren Haj kilishi, hakanan za ta turo masu aikinta su kirata. Idan taje kuma ta sata aiki , Afrah takan dage ta boye jin zafinta ta yi mata aikin, amma a gabanta zaa gama abinci, Haj kilishi tayi mirsisi ta hanata a zuba mata, haka zata dawo bangarenta da yunwa,ta rasa me yasa take mata wannan mugun horon, sai a wata rana ta gane dalilin da yasa take mata haka.
Zata shiga bangaren Haj kilishi kenan ta ji tana waya da yarta Hassana, tana gaya mata yadda ta maida Afrah me aikinta da hanata abinci da take yi ko ta yi mata aikin, Afrah na tsammanin Hassana ta tambayeta dalilin da yasa bata bata abinci ne yasa Haj kilishi tace “Ai yarinya ce me shegen zurfin cikin tsiya, duk yadda na so naji kanta da Musaddik ta ki kullum nunawa take komai lafiya, na kuma san ko abinci baya bata shi yasa nake mata haka ina son ta bude baki da kanta ta roke ni na basu abinda zasu ci amma ta ki”.

Jin hakan yasa Afrah ta juya ta koma bangaren ta tare da shan alwashin har abada ita da ta nemi taimakon wani abu daga Haj kilishi. Ta kuma kara dauke kafa a sasan ko ta aiko a kirata takan kirki bata da lafiya. Ta fita harkarta gaba daya,wanda hakan ya kara tunzura Haj kilishi sosai.

Lokuta da dama idan Afrah taje islamiyya ya sayyadi Habib ya kan yi mata kyautar kudi ba don ta roka ba sai don kawai yana ganin cancantar hakan a matsayinsa na yayanta a yanzu. Sai dai ko shi daker take amsa sai ta ga bata da wata mafita sannan take amsa.
Wani lokacio ne ma idan ta je Islamiyya.
don kudin daya ba ta gudunmawa ma da ta yi niyyar tayi sana’a da su tuni
suma suka Kare, saboda zararsu da
take yi tana yin hidimar gidan. Da kuma
Musaddik ya fahimci akwai dan wani abu a hannunta, gaba daya sai ya amshe sauran kudin ya yi sha’aninsa da su. Gaba daya Afrah ta dorawa kanta hakuri da juriya gami da dangana.
Ta maida hankalin ta wajen cigaba da yi masa addu’a tare da kauda kanta daga sa ma kanta muguwar damuwar da zata yi mata illa, komai a matsayin kaddararta take dauka a matsayin ta na musulma kuma tasan yarda da kaddara yana daga cikin cikar imanin musulmi.

Page 132
Tuntuni jarabawar Afrah ta fito ta kuma fita da sakamako mafi kyau, domin duk ta cinye ko pass daya bata da shi. Sai dai mafarkin ta na cigaba da karatu tana ganin kamar bazai tabbata ba, domin tana ganin abubuwa da dama sun canja dole wani abun sai tayi hakuri da shi. Yanzu abu biyu ta fi maida hankali a kai shine yi ma musaddik addu’a da kuma yi masa nasiha, gami da kokarin dawo da shi irin hanyar da ya baro a baya, domin cikama mahaifinta burinsa. Domin dai a kullum sai tayi tsayuwar dare, tana nema ma musaddik shiriya. Domin idan ka dauke wannan halin nasa bashi da wata makusa ko matsala,
sai dai abu daya ke daure mata kai
Shine a duk lokacin da take masa
nasiha, ya kan nuna mata shi ma ba haka ya so ba.
Duk abinda yake yi, ba a son ransa yake
yin sa ba, To amma don me ya kasa yaki
da zuciyarsa ya daina ya natsu? Wannan ita ce tambayar da kullum
take neman amsarta.Ta bangaren Mallam Mahmud kuwa kullum ya
samu haduwa da Afrah yana kara karfafa mata
guiwa tare da yi mata addu"a. Hakan
shi ne kadai ke sanyaya ran Afrah tare da karfata mata guiwar cigaba
da zama da Musaddik cikin aminci.


Page 133

Zabe ya Gabato , hakan ya sa gaba
daya Musaddik ko kwanan gida bai cika yi ba, sai ya kwana daya
kwana biyu baya gida. Ran Afrah da
hankalinta yana matukar tashi akan wannan bangar siyasar.bata so sam
domin ta san hatsarn da ke ciki.
tayi nasihar har ta gaji, amma Musaddik
ya riga ya ya rufe kunnansa , sai dai a duk sanda ya kwana
baya gida, idan ya dawo, ya kan dawo
da kudi Domin har dubu biyar yana ba
ta , ta rike ta ci abinci, a wannan tsakanin abinci baya yi mata
wahala, duk abinda take so, shi take ci,
da yake tana da hankali, ta kuma san samun na dan lokaci ne, ba
me dorewa ba, shi ya sa idan ya bata
takan kasa uku ta aje kashi biyu, ta ci abinci da kashi daya, da
dan sauran hidimominta na yau da kullum, amma
duk da haka Afrah babu farin-ciki a
rayuwarta,kullum ji take yi kamar bangar siyasar nan zai iya kara jefa rayuwar cikin garari.

Alhaji Hamza Sarkin yakin kamfen din
Haj. Hudah ne, wacce take neman
takarar zama yar Majalisar Wakilai, ta
Kasa.Yana zaune a katon falonta a gidanta na ganawa da manyan baki
Gefe daya Musaddik ne a zaune yana
karema falon kallo, yana nazarin yadda aka kawata falon da kayan alatu masu kyau da tsada.cikin kaguwa ya dubi Alhaji Hamza yace cikin yanayin maganarsa,

"Alhajin Allah, ni fa duk a rayuwata
babu abinda na tsana irin jira, ina mutunta lokaci, shi ya
sa ba na Kara lokaci akan wanda aka ba
ni” Alhaj Hamza ya yi dan murmushi
Yace “Mazaje ayi hakuri, na san hakan, batun yau ba

Page 134
itama Haj na tabbata akwai abinda ya tsayar da ita, amma na san
tana hanya, bari na Kara kiranta”
Ya tura hanmu a aljihunsa ya ciro waya,
ya danna kenan, ya jiyo hon din motar Hajiya Hudah,
ya yi murmushi gami da kallon Musaddik, a yayin
da yake maida wayar cikin aljihunsa
Yana cewa “Ga yar halak din nan ta
iso”,Musaddik ya gyada kansa ya co "Ya dai kamala'
Yana rufe
dai kamata, amma ina dalili kayi ta zaman jiran mutum”, yana rufe bakinsa. Hajiya Hudah ta danno kanta cikin
falon kyakyawar bafullatar mace ce, fara ce, amma ba
inn farin nan me daukar ido ba, tana da
kyawun fuska dai dai gwargwado hade
da kyawun diri.Tana sanye da kaya na alfarma, kallo daya za
ka yi mata, ka San goggaggiyar mace ce, wacce ta mallaki masu gidan rana, kuma wayayyiya wacce tasan abinda duniya take ciki.
“Alh Hamza kuyi hakuri, na zaunar da ku ko? Kun san abubuwan da
yawa ne, babu zama”
'Ta fada tana kokarin zaunawa. Alhaji Hamza muskuta ya gyara zamansa
gami da yin dabi arsa ta murmushi ya ce

“Da girman kujerarki, barka da isowa
Kada ki damu da hakan, ai dole ayi miki uziri” Ta amsa "Yauwa Alhaji", Ta fada
'tana kallon Musaddik, wanda yake zaune baida ko alamar
gaisheta. Musaddik ya yi matukar yi
mata kwarjini,haka nan kuma ta ji ya burgeta, yadda bai yi wani rawar jiki don ya ganta ba, da nuna baima damu da shigowar ta ta ba. Ta dawo da kallonta
ga Alhaji Hamza wanda tun shigowarta ya kara samun nutsuwa ta ce.
"Shine wannan wanda kace yana yi
mana Kokarin nan?"
Alhaja Hamza ya dube shi ya ce
“Eh shine Haj Musaddik kenan, ku gaisa mana mazaje” ya fada yana sauke kallonsa a kan fuskar musaddik.


Page 135
Musaddik bai amsa ba, illa kallonta da ya ci-gaba da yi.sai daga bisani ya daga hannayensa biyu ya kai tsakiyar fuskarsa yace “Barka dai hajjaju”, tayi murmushi sosai tana kara kallonsa tace “ Barka dai, ina ta godiya dai”,ya girgiza kai yace “Ah kada ki damu, ai kin cancanci ayi miki komai saboda mu ma kina aikowa a sauke mana”. Dariya kawai tayi tana jin zuciyar ta na son ta dinga yabon musaddik da kuma jin komai ya yi yana burgeta.
Alhaji Hamza ya fara magana. "Hajiya.
Kamar yadda ki ka sani da wanda ba ki sani ba, amma na yi kokarin
gaya miki Musaddik shine wanda yake
mana kokan a wajen matasa, to kamar yadda na fara gaya
miki a waya, ki ka kuma bukaci na taho da shi domin ku ga juna ku gaisa,
Yan’uwan aikin nasa suna da bukatar
Kudin kayan aiki, tunda zaben nan jibi ne, don haka suna
bukatar kayan maye da makamai, wadanda za su
sha a yayin tashin hankulan mutane a lokacin zabe,
sai kuma kudade wadanda za su sa a cikin aljihunsu,
domin jin karfin gudanar da aikin.
Don haka a matsayinsa na ogansu
wanda kuma da shi nake mu'amala, ba da su ba kuma duk jama'ar
nan shine ya nemosu, shi ya sa suka wakilta shi akan komai.”

Hajiya Hudah ta gyara zamanta, gami
da kara kallon Musaddik, wanda duk
Kallon da za ta yi masa, ta kan sami zuciyarta da bugawa, yana kuma
matukar kara yi mata Kwarjini tace
*Musaddik ba dai matsala a can
Bangaren naku ko?"
Ya kara dubanta yana gyara zama yace
*Matsalar kenan ta kudì da kayan maye,
in dai da su, to za ku ga biyan bukata, ta bangaran mu, kuma
jama"ar tawa korafi suke yi min suna ganin kamar ana yi min wata katuwar sauka ne ta tamaye amma bana aje musu nasu kason”.

Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️


Page 136

Musaddik ya kara gyara zamansa ya cigaba da cewa “to a yadda na fahimce su, tunda ba mutunci gare su ba,suna
Iya yi min bore a ranar zaben,su ki yi mana abinda ya kamata don haka sai ku san yadda za ku yi da mu idan kuna son komai ya tafi yadda ya kamata”.

Alhaji Hamza ya muskuta yana kallon
Musaddik yace "Ba ku da sauran
matsala, ga ka ga Hajiya Hudah nan, gani kuma a tsakiya,babu komai
duk abinda ku ka nema, za ku samu”
Hajiya Hudah ta dora kafa daya kan daya tana dan murmushi, yadda musaddik yake magana da kwanjinsa yana kara mata matukar kwarjini. Ta maida idonta kansa sosai tace
“Babu damuwa, babu abinda zai gagara shi yasa kuma nace sarkin yaki ya taho min da kai,saboda duk abinda zai kawo mana cikas a cikin wannan tafiyar bama bukatar sa,muna son komai ya tafi yadda zukatanmu ke bukata”.
Ta dauko katuwar jakarta da ke yashe a gefenta wanda da ita take yawo saboda jakar tana daukar makudan kudad,sannu a hankali ta bude jakar ta
dakko naira dubu dari biyar ta mika ma
Musaddik, yasa hannu ya amsa, ta maida bayanta ta kwantar a jikin kujerar sannan tace “wannan ka je ka raba masu, su sa a aljihunsu, domin su jidadin yi mana aiki”, Alhaji
Hamza ya wage baki, yana mamaki.
yana ganin duk mako gami da matsolancin Hajiya Hudah da tsoron
fitar da kudinta, ta ba Musaddik duba dari biyar ba tare
da ta ga jama'arsa ba. Wanda yasan ba ta taba yin hakan ga
wani ba, tsarinta ne dole sai ta ga zahiri. In dai kudi za ta bayar, sai taga yawan jama’arka.
Lalle Musaddik yau ya taki sa'a.
Musaddik tunda ya karbi kudin yake juyasu ba tare da yace uffan ba, wanda ji Alh Hamza yake kamarya matse bakin Musaddik yasa shi ya dinga yi mata godiya akan komai, baya son wannan shurun da yake yi. Wanda hakan sam bai dami haj Hudah ba illama burgeta da yake yi. Domin kara janyo jakar ta yi ta fito da naira dubu dari hudu ta kara mika masa tace “wannan naka ne kai kadai”.

Cikin karin wani mamakin Alh Hamza ya zaro ido, zuwa lokacin zuciyarsa ta fara
tunanin wane irin matsayi musaddik ya samu a wajen uwar dakinsa.A yayin da Musaddik ya karba,lokaci daya a kuma
Karo na farko Ya yi mata godiya, Ta yi murmushi tace “Wannan dubu dari
biyar din kamar yadda na gaya maka, ka rarraba ma mutanen naka , na san a ciki zasu sami wanda zasu sayi kayan shaye-shayensu harma da wani biyan
bukatar tasu,ni kawai burina a ranar duk akwatin da ku ka ga alamar ba
zamu kai labari ba, to ku far masa, ko ku dauke shi ko ku

Page 137
Lalata shi. Idan kuma duk babu dama,
to kawai ku tada fitina a wajen. Taimakon da na ke nema kenan a
gare ku”.Musaddik ya ce "Kada ki damu,
duk abinda ki ka lissafa za mu yi, sai dai wani hanzari ba gudu ba kuma”
Ta ce "Ina jin ka". Ya ce "An dade ana
amfani da mu a wannan harka, amma daga baya mu kan
tura mota ne ta tashi, ta bulbulemu da
hayaki,Ma'ana, da zarar kun sami biyan
bukatar ku sai ku manta da mu, ku kyamace mu, a lokacin ne
za ku san mu ba mutanen kirki bane, sai ku kulle yin duk wata alaka da mu,
Wannan babban kuskure ne ku ke yi,
domin muna yi maku abinda ko 'ya yanku bà su iya maku,
don haka bai kamata ku dinga mantawa
da mu ba bayan kun kafa gwannatin ku dare kan madafun iko”.
Hajiya Hudah ta dubi Alhaji Hamza da
har yanzu yake yi mata kallon mamaki, sannan ta yi murmushi tace,

"'Ka kwantar da hankalinka, za ka
ga bambanci a wannan karon, domin in
dai na haye wannan kujerar to da kai za'a tafi gwamnatin, kada ka Kara sa
wannan matsalar a matsayin damuwarka, domin zan
yi maganinta, da zarar na haye"
Tun zamansa, sai yanzu ya saki jiki sosai domin ko banza ya jidadin maganarta yana kuma fatan ta cika alkawarin ta, yace "To godiya na ke ranki ya dade, Allah ya bamu nasara”
daganan ya mike, yana kallon Alhaji
Hamza yace “Alhajin Allah taso ka aje ni inda ka dauko ni"

Page 138
Yana magana yana dauko leda a aljihunsa, ya zuba duka kudin,
ya daure. Alhaji Hamza ya ce "yanzu
Kuwa zan maida kai”, Ya mike yana kallon Hajiya Hudah ya ce.
"Gari fa ya yi zafi, ga abubuwa sun mika, jibi za'a fita
fagen fama , ko zan sami na fetur?" Ta
Yi masa wani irin kallo, gami da hade rai wanda tuni ganin hakan yasa ya cire ran zai samu wani abu a hannunta,amma Alhaji Hamza bai san irin tunanin
da ta yi ba, bayan ta dubi Musaddik, sai
ta janyo jakarta ta Kirga dubu talatin, ta mika masa.
Ba yabo, ba

Please Login or Register in order to submit comment