Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Haj Rakiya suka dauki hanyar rugar boka mai rakwacam, wanda har suka
Ka rugar, la'antar Musaddik take tare da
la’antar rayuwarsa, kamar ko yaushe idan suka je gaban me Rakwacam Haj kilishi tana cikin kaskantar da kai a gabansa, wannan karon ma tana zaune a gabansa cikin nutsuwa tamkar me daukar karatu, ta gama sanar da shi duk abinda ke damunta, ta kara da cewa “Bana son alakar auren da ke tsakaninsu, shi yasa nake son araba su rabuwa ta har abada, shi kuma musaddik a raba shi da duk wani mutum da zai zama alheri a tare da shi,sannan ina son shaye shayen da yake ya fi na da”.

Boka me Rakwacam ya gyada kai ya dakko kayan surkullensa ya buga katon faifan dake gabansa, ga mamakinsu kawai saiga fuskar Afrah ta bayyana, cikin shiga ta kamala tana zaune kan sallaya rike da casbi a hannunta.
Boka me Rakwacam ya ja baya hannunsa na rawa lokaci daya fuskar Afrah ta dauke, Haj kilishi da haj Rakiya suka shiga kallon kallo,
Boka me Rakwacam ya dago hannunsa daker da ya sage ya dubi Haj kilishi ido cikin ido sannan yace “Haj babu nasara, ki kiyayi wannan yarinyar kawai, domin kamar yadda na gaya miki babu me hana aurenta da musaddik to hakanan zan kara gaya miki yau domin tsakanina da ke babu cin amana, musaddik da Afrah ba zasu taba rabuwa ba sai dai wani iko na Allah sannan wannan yarinyar tana da tsananin addu’a ta na ambaton Allah ko yaushe, matukar kuma tana cikin wannan halin babu abinda zan iya yi mata na cutarwa da zai sameta ko yanzu wannan bayyanar da tayi sai da na sami rauni a hannuna, saboda haka ina baki shawarar ki kiyayeta”.
Gaban Haj kilishi ya cigaba da faduwa ta ji komai ya tsaya mata, ta dube shi murya shake tace “yanzu kana nufin babu abinda zaka iya taimaka min dashi”, ya girgiza kai yace “Babu, domin idan ki kayi wasa wannan yarinyar itace silar tunuwar duk asiranki”.
Tikisa nan ma haj kilishi dafe kai tayi wata irin damuwa tana kara cika zuciyarta. Lalle Afrah ta zamar mata masifa, ta kara duban shi tace “To shi musaddik din fa?” Ya gyara zama yace “Duk aikin da mu kayi a kansa yana nan sai dai tsananin addu’ar da matarsa take masa yana ta raunata mana aikin, saboda haka abinda kikace ayi masa yanzu zanyi masa, wannan kada ki damu tunda shi bai damu da yin addu’a ba komai zai iya kama shi”,
Ananne ta dan ji sanyi kadan a ranta tace “ To a kara yin aiki a kansa, ko bamu sami nasara akanta ba idan muka samu akansa ai an gama da ita tunda koma meye dole zai tabata”.
Daganan Boka me Rakwacam ya fadi kudin aikinsa ta kuma cake masa kudin a gabansa harda kari, wata bakar laya ya bata yace tasan yadda zatayi tasa a bakin kofar da tasan dole zai tsallaka to fa da zaran ya tsallaka to zai yi mugun bakin jini awajen duk wanda yake mu’amalar arziki da shi, shaye shaye kuwa da lalacewa tunda tukunyar da suka binne a bakin kuka tana nan a binne to babu abinda zai canja zai cigaba a haka har abada. Ta karbi layar gami da godiya sannan suka bar rugar cikin tashin hankali Afrah ta na neman ta zamar mata dan hakin da ka raina.

Page 192

A daren ranar, musaddik ya gama cin abinci, Afrah ta shigo ta zauna kusa da shi sosai tana rike da kofi da ruwan da ta gama tofe Ayatul sihir a ciki ta mika masa tace “yaya ka sha wannan addu’ar da bisimilla”. Ya dubeta cikin murmushi yasa hannu ya karba yace “duk abinda ki kace haka za’a yi zan sha ko da addu’ar mallakeni ne”, tayi dariya sosai tace “Bama akai ga haka ba yaya”, ya sa kofin a bakinsa sai da ya shanye tas sannan ta amshi kofin, zata yi magana kenan wayar musaddik ta dauki kara yasa hannu ya dauka ganin Haj kilishi ce yasa ya yi saurin dauka, “ kazo ka same ni yanzu”, cewar haj kilishi cikin fusata kafin yayi magana harta aje wayar.

Afrah ta dube shi tace “kai da waye na ga yanayin ka ya canja”, ya dan numfasa yana kokarin tashi, yace “Haj ce tace na je yanzu tana son ganina”, ta dan tsare shi da ido tace “To canjin yanayin na menene?”, ya ce “Na ji ta cikin fusata ne a fadace take shi yasa na ji damuwa a raina ina tunanin ko nayi mata laifi ne”.
Afrah ta gyada kai tace “Ko ma meye idan laifi kayi mata sai ka bata hakuri” ya juya ya fara tafiya sai kuma ya tsaya ya waigo ya zubama Afrah ido, ta dan daga girarta sama tace “yaya dai?”, ya girgiza kai yace “Naji faduwar gaba ne da tsoro ya cika zuciyata hakanan”.
Jikin Afrah ya yi sanyi kalau, ta ja hannunsa gaba daya suka zauna kan kujera tana rike da hannunsa tace a hankali, “zan karanta wata addu’a duk abinda na fada ina son ka maimaita har mu kai karshe”, babu wani musu ya gyada kai. Tace “Bismillahillazi la yadurru ma’asmihi shai’un fil’ardi wala missama’i wahussami’ul aleem”.haka shi ma musaddik ya maimaita, daganan ta dube shi tace “ ka taka duk inda ka so, babu abinda zai sameka kana cikin tsarewar ubangiji”.
Ji ya yi ya sami wani irin kwarin guiwa ya mika bakinsa kan hannunta ya sumbaceta yace “madallah da samun mata irinki”.
Ya saki hannunta ya tashi ya fice da sauri Afrah ta bishi da addu’a domin dai sosai haj kilishi tuni ta fara bata tsoro.

A kasan kafet din kofar falonta Haj kilishi ta daga ta sa layar da boka me Rakwacam ya bata, wanda tasan babu yadda za’ayi musaddik ya shigo cikin falonta ba tare da ya tsallaka layar ba, dama burinta kenan.

Cikin sallama ya shigo falon idon haj kilishi na kansa har ya tsallako ya shigo sai zuwa lokacin ta ji wata nutsuwa ta shigeta tana ganin asiri ya riga ya kama shi, sai dai abinda bata sani ba Allah ya riga ya tsare shi domin kafarsa kawai da ya tsallake layar tuni ta kora yin bakinkirin fiye da yadda ta karbota a wajen boka.
Kan kujera ya zauna yana kokarin gaisheta ita kuma tana karewa natsuwarsa kallo domin yau cikin natsuwa yake , yadda yake shigowa a firgice cikin rashin natsuwa yau sabanin haka ta gani, shi yasa ta ji ranta ya kara sosuwa, “ Haj kin ce kina son ganina” Ta daga ido ta watso masa harara tace “To ai naga ka zama hukuma ne sai lallashi yanzu ka manta matsayina a wajenka har zaka iya yin kwanaki ba tare da ka shigo ka gaishe ni ba, har kuma zaka sami aiki amma ka ki shigowa ka gaya min sai dai matarka ta zo ta gaya min saboda kai kafi karfin ka gaya min ko?”
Musaddik ya girgiza kai yace “Duk ba haka bane Haj, abubuwa ne kawai suka zo a bazata amma ta yaya zanfi karfin zuwa na gaya miki na sami aiki”.

Page 193

Haj Kilishi ta kara zuba masa harara tace “Babu abinda zaka gaya min, domin batun yau na kula da yadda tunda ka yi aure kake kokarin wofintar da ni, yanzu baka ganin kowa sai matarka”, ya kara girgiza kai yace “ki daina wannan maganar Haj, ki kuma yi hakuri don Allah”, ta saki numfahi tace “shikenan, aikin me ita yar majalisar ta baka?”, ya dan yi murmushi yace “Ba wani aiki bane aikin kula da lafiyarta ta ba ni”, ta sakar masa wani irin sakaran kallo tace “kai kaji wata maganar banza aikin kula da lafiyarta, yanzu kai don lalacewa aikin bautar kula da lafiyar mace zaka zauna kana yi to
kwata wannan aikin bai dace da kai ba,
wannan ai Wulakanta kai ne. Ka tuna fa
Ka yi karatu har Masters gareka, amma za ka kare da yin aikin
wanda bai yi karatun komai ba”.

Musaddik ya nisa sannan ya ce,
“Maganarki gaskiya ne Hajiya. Amma kada ki damu wannan
aikin na dan wani lokaci ne, zan sami
wani aikin yanzu haka ma na riga na mika takarduna wajen
neman aikin daya dace da karatuna"
Gaban Hajiya Kilishi ya yi mummunan
faduwa, lalle ta yi sakaci Musaddik yana
neman ya dawo Musaddik dinsa na da, lalle auran Afrah da
Musaddik babban kalubale ne a gareta
ta ya ya ba zata tsani Afrah ba ji tayi kirjinta har wani bugawa yake da karfi, bakincikinta ya kasa boyuwa,yanzu Musaddik har yana da kyakyawan
tunanin da zai tsara ma kansa rayuwa ta-gari?har yana da tunanin neman aiki a wajen da ya dace da shi.
Ta muskuta daker tace “To ashe har aiki kake nema”, ya yi murmushi yace “sosai kuwa haj sai ki tayani addu’a Allah yasa na samu aikin da yafi wannan”. Bata ce komai ba sai da ta yi kasa da kanta tayi ta kokarin daidaita hankalinta, tana son boyr mugun halin da ta shiga, sannan ta dago tace “Amma dai wannan neman aikin da ka ke yi da kuma wanda ka karba yanzu ka fara, duk tunanin matarka ne ko ba tunaninka ba?”

Ya yi murmushi gami da gyada kai yace,
"Eh, tunaninta ne, ai a gaskiya Hajiya na
yi sa’ar mata, Afrah tana da hankali ga hangen nesa tunaninta yayi nesa da shekarunta,ina jindadin zama da ita domin a kullum burinta ta maida ni hanya ta-gari,ta maidani mutumin kirki
Ita ke tunatar da ni abubuwa da yawa da na manta, mace ce ta-gari".
Hajiya Kilishi ta yi murmushin Karfin hali tace “Hmmm lalle kayi sa’a, shi yasa ni baka fahimtar ina cikin damuwa akan halayenta a gare ni, kai tana mutuntaka ni kuma tana kuntata min, sam bata ganin kima ko girma na……….
Da sauri ya dakatar da ita yace “Anya Afrah kuwa ina dai ganin kila kin sami kuskuren fahimta ne, domin Afrah ko karami bata raina ba balle babba”. Ta watsa masa harara tace “Ai nasan ba zaka yarda da laifinta ba tunda idonka ya riga ya rufe a kanta, kayi hakuri ba zaka kara jin laifinta a bakina ba”.
Ya girgiza kai yace “Don Allah kiyi hakuri ba na nufin hakan kawai dai gaskiya ce na fada” ta daga masa hannu tace “ya isa, tashi ka tafi Allah ya tashemu lafiya.
Shi ma tuni zaman dama ya gundure shi hakan yasa ya yi gaggawar tashi ya yi mata sai da safe, duk da bata amsa ba bai damu ba ya fice a binsa.
Yana fita haj kilishi ta tashi da sauri ta dage kafet din ta fito da layar, yadda ta ga ta kara yin baki kamar an konata yasa taji ta aminta a ranta asirin ya riga ya gama kama musaddik.

Page 194

Tayi wani murmushi ta wuce cikin daki ta adana layar, sannan ta shiga kai gauro da mari a tsakiyar dakin har
Yanzu zuciyarta a zafafe take,yadda musaddik ke yabon Afrah kadai ya isa yau ya hana mata samun bacci, ta tsaneta fiye da yadda ake tsammani, shin ta yaya zata yi maganinta, bayan boka me Rakwacam ya nuna shi ma ta fi karfinsa, lalle wannan yarinyar ta zamar mata karfen kafa.

Zahiri ta kara shiga damuwa domin ko da ta kwanta ta kasa bacci sai juye juye kawai take yi, babu wani abu daya da ke yi mata dadi a cikin rayuwarta, da kudi tana neman yadda zata sami farinciki amma ta rasa.
Bata jin kuma zata hakura kamar yadda boka me Rakwacam ya bata shawara.
Wasgegari Haj kilishi ta kira abokiyar sharrinta haj Rakiya, ta sanar da ita musaddik ya tsallaka laya don haka tana da yakinin aiki ya ci, sai dai kuma maganar Afarah matukar zata cigaba da sa mata ido to zata bata mata duk wani shiri da ta dauki shekaru tana yi, haj Rakiya ta yi kasa da murya tace “To kece ai haj kullum kina ganin idan ba wajen me Rakwacam ba babu inda zaki samu biyan bukata bayan akwai manyan bokaye da ni na sani da zasu iya yin abinda me Rakwacam bazai yi ba, su da suke tsafi”, Haj kilishi ta jinjina kai tace “yanzu kina ganin mu cigaba da bin wasu bokayen kina ganin babu asarar kudi irin na wancan lokacin”, cikin karfafa guiwa Haj Rakiya tace “za’a dace saboda inda zan kai ki shi ma fa ya iya aiki, ayyuka nawa ya yi min na samu nasara na kai wasu ma suma sun dace, kawai ki manta da wani Afrah ta fi karfin me Rakwacam don idan tafi karfinsa bata fi karfin wasu ba, don gaba da gabanta”. Nan da nan Haj kilishi ta ji ta aminta da ta je wajen wani bokan bayan me Rakwacam duk da dai da ta ce ta daina asarar kudinta a wajen kowa bayan me Rakwacam, sun kuma tsaida magana akan haj Rakiya zata rakata wani kauye dake can bayan gari wajen wani hatsabibin bokan.
Kai duniya anya kuwa akwai wahalalle irin me bin bokaye, duk rayuwar mutum ta kare a asarar lokaci da imani da kuma rasa kwanciyar hankali da sukunin rayuwa, yanzu meye amfanin rayuwar Haj kilishi da duk daular da take ciki da bokayen da take bi bacci ba zata iya yi me dadi ba, to ina sauran dadin rayuwa.
Aiki ya sami me yi domin dai a ranar karfe daya da kwata na rana, Haj kilishi da Haj Rakiya suka dauki hanyar wani kauye da ke nesa da minna, Haj kilishin ce ke tuka mota, kamar yadda ta saba tukawa a duk sanda zasu je wajen bokayensu, bata daukar direba saboda sirri.sai da su kayi tafiya me nisa karshe ma aje motar su kayi a bakin hanya suka karasa a kafa saboda mota ba zata shiga wajen ba.
Tsiduhu ya karbesu hannu bibbiyu, Haj kilishi kuwa bata sami nutsuwa ba da jin ta zo inda yakamata saida Tsiduhu ya fara gaya mata abinda ya kawota wajensa, yadda yake bayanin komai kai ka rantse da Allah a gabansa akayi komai, zuciyar Haj kilishi ta kara yin sanyi a lokacin da Tsihudu ya tabbatar mata zai iya raba musaddik da Afrah zai kuma iya sabauta rayuwarta ma gaba daya, sai dai akwai tsada aikin.
Haj kilishi tace “in dai za’a sami biyan bukata ko nawa ne zata iya biya”, haj Rakiya ta dubeta da sauri tace “Haba Haj yanzu har wani shakku zaki sa a ranki a wannan aikin, kina ganin yadda da zuwan mu ya fadi duk damuwarki ai ki cire shakku kawai”, tace “Ai na cire Haj lalle kin kawo ni inda ya dace”.
Tsiduhu yace “zaki bada nera dubu dari hudu kudin sayen kayan aiki”, babu musu ba neman ragi tace “Babu damuwa”, katuwar jakarta ta dakko ta bude ta kirgo bandir hudu na yan dubu dubu ta aje a gabansa, baiko dubi kudin ba yace “ ku tashi ku tafi ku dauka komai ya yi dai dai ku dawo nan da kwana shida zan baki mahadin aikin”

Page 195

Cikin godiya suka tashi suka tafi, har suka kai bakin motar Haj Rakiya kara yabon aikin Tsiduhu take yi, tana karfafa aikin nasa. Hakan yasa Haj kilishi ta kara jin ta aminta da aikin nasa Afrah kam sai dai wata ba ita ba zata gane ta shigo gonarta, za kuma tasan tayi kuskuren auren musaddik domin babu komai a cikin auren nasa face masifa.
Har ta aje Haj Rakiya a kofar gidanta tana mata godiya, domin dai ita din aminiya ce ta rufin asiri.
Motar Haj kilishi na bacema ganin Haj Rakiya, ta juya ta shiga cikin gida tana murmushi, fuska cike da jindadi, dama ba wani damuwa ta yi da yin sallah ba ko zatayi ta fi yinta ba’a kan lokaci ba, hakan yasa dan abinda zata ci kawai ta sarrafa me sauki ta ci ta koshi ta dan huta, tasan megidanta sai dare zai dawo gida don haka ta tashi ta canja gyale ta fito ta kara kulle gidanta ta nufi bakin titi.
Shatar taxi tayi zuwa kauyen da suka baro dazu,cikin kankanin lokaci suka iso inda dole zai tsaya, ta fito ta sanar da shi ya jirata yanzu zata dawo.
Sannu a hankali tayi ta tafiya har ta kawo inda Tsiduhu yake, ta tura kofar galangalan din a hankali tana kiran sunan sa, Tsiduhu ya juyo suka hada ido gaba daya suka fashe da dariya harda kyakyatawa, “zauna”, cewar Tsiduhu cikin dariya, ta lalubi gefen tabarmar ta zauna tana cigaba da dariya tace “Amma fa kayi kokari, duk abinda ka fada ya zauna a zuciyarta sosai”, ya nisa yace “kai mata na zuba rashin imani akan yan’uwansu mata, yanzu ita wannan Afrah irin wannan mugun abun da take son ayi mata ina zata kai girman hakkinta idan anyi”.
Haj Rakiya ta tabe baki tace “Ina ganin mata marasa imani ciki kuwa har da ni amma ban taba ganin irin haj kilishi ba, yaron nan duk abinda take son a maida rayuwarsa an maida ya zama abin tausayi amma ta kasa hakura, Afrah kuwa bokanta da kansa ya gaya mata ta kiyayeta, a gaban mu shi ma sai da ya wahala alokacin da ya yi kokarin cutar da ita, amma duk bata samu ta yi tunanin lokaci ya fara kure mata ba, shi yasa nayi amfani da wannan damar mu yagi rabonmu kafin ta gama samun matsala”.
Tsiduhu ya yi dariya yace “Ai kin gama min komai rabon da naga dubu daya tawa har na manta lalle kin kawo min babbar harka, zamu cigaba da tazarta idan kura na maganin zawo tayi ma kanta mana duk bokan da yake mata aikin ai sabida kudi yake yi mata to me yasa shi bazai azurta kansa ba kawai ya huta da sai yayi aiki an biya shi”.
Gaba daya suka fashe da dariya, Haj Rakiya tace “Dakko kudi mu yi kasafi na tafi nabar me mota yana jirana”. Da sauri ya janyo ledar da ya zuba kudin ya mika mata, ta amsa ta dauki dubu dari biyu da hamsin ta mika masa dubu dari da hamsin ya amsa cike da murna ji yake kamar yafi kowa kudi a duniya, lalle Haj Rakiya saninta alheri ne. Daganan su kayi sallama akan sai nan da kwana shida zasu dawo kamar yadda yace.
Kai tsaye daga nan wajen me taxi dinta ta wuce zuciyarta fes da farinciki gobe kaji zata bararraka ta ci abinta ta kuma biya yan basussukan da ake binta, cin kudin Haj kilishi yanzu ta fara tunda ta fahimci babu burbushin imani a tare da ita, dama kuma irin wannan rayuwar da haduwa ta bariki ai babu amana a ciki……….


Yar gidan imam ✍️
Musabbabi

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 196

Alh yusuf sanda dai ya tattara ya tafi paris, domin shigo da wasu kaya.Haj Hudah kuwa tun bayan rantsar da ita har yanzu ta ki komawa gidanta da aka mallaka mata a Abuja sai dai duk bayan wasu yan kwanaki tana shiga Abujar, kuma ba kasafai take kwana ba a duk lokacin da ta je din, domin hakanan take jin rashin jindadi a duk ranar da zata kwana a Abuja kasancewar in dai kwana zata yi musaddik ba ya biyota sai dai idan ta dawo ya zo.
Dalilin da yasa kenan bata son kwana a Abuja sai ya zama dole,Tana jin kamar ta yi matukar wauta da ta sabama idanunta ganin musaddik kullum, domin hakan na nema ya zamar mata wata illa bata san abinda zuciyarta ke nufi ba da sanya musaddik a cikin tunaninta, musamman idan ta zo kwanciya, ta kan ji bacci ya kauracewa idanunta, abin mamaki kuma bata yin tunanin kowa sai musaddik, abin takaici kuma sai zuciyarta ta yi ta bijiro mata da tunanin yana can tare da matarsa yana jindadi hakanan sai ta ji wani irin abu me kama da kishi ya tokare kahon zuciyarta, tana jin kishin matar musaddik sosai shin meye dalili?, ita kanta kai tsaye ba zata iya cewa ga dalili ba, amma wannan abin yana matukar damun zuciyarta ta kuma rasa inda zata bulloma lamarin.

Ta bangaren Haj kilishi kuwa ta kafa ta tsare ta ji Haj Hudah ta kori musaddik daga aiki amma shuru, domin dai kullum tana jin fitarsa zuwa wajen aiki da dawowarsa, ta dan ba da lokaci ta gani domin a ranta tabbas tana jin aikin boka me Rakwacam ya ci sai dai jiran lokaci kawai.
Haka zalika kwanaki shidan da Tsiduhu ya dibar musu ya yi, don haka suka koma kamar yadda ya bukata, wanda kafin komawar tasu tuni Haj Rakiya ta kira shi ta bashi labarin duk abinda ke faruwa, hakan yasa da suka koma ya shiga gayama Haj kilishi tana cikin damuwa,akan aikin da ta kaima wani bokanta tana jiran taga aiki ya ci amma har yanzu ta ji shuru.

Page 197

Cikin dimbin mamaki ta dube shi tace “Tabbas hakane, kuma bai saba min aiki na dauki wani lokaci banga ya ci ba sai wannan”, Tsiduhu yayi dariya yace “Ai saboda bai ci ba ne aikin shi yasa ki ka ga sabanin tunaninki”, Haj Rakiya ta gyara zama a cikin zuciyarta ta na yaba yadda Tsiduhu ke tafiyar da komai.
Haj kilishi ta bata fuska tace “Ko da ba ji kace aikin bai ci ba”, ya gyada kai yace “kwaraibkuwa, ko da yake wannan ba damuwa ta bace, ungo nan”, ya mika mata wani kullin magani da wata laya da aka daureta tsaf da allurai.
Da sauri ta amsa tana juyawa alamar neman karin bayani,
Ya kara kallonta sosai yace “wannan kullin maganin duk yadda zaayi ki yi kisa mata a cikin abinda zata ci, kadan zaki barbada mata idan kika cika zata iya mutuwa, ita kuma wannan layar ki sami ruwan teku me gudana ki jefa a ciki , in dai kin bi yadda nace to shikenan rabuwar Afrah da musaddik ta tabbata, za kuma ta cigaba da rayuwar kunci.

Tayi murmushi tace “Nagode”, Haj Rakiya ta matso sosai kusa da kunnanta tace “Tunda yace wancan asirin da me Rakwacam ya yi bai ci ba, basai ki sa shi ya kara yi miki wani ba, tunda naga aikin nasa akwai nasara a ciki”, nan da nan ko Haj kilishi ta gyara zamanta ta kwantar da kai kamar wacce za’a ba kyautar duniya tace “Sai maganar wancan aikin da kace bai ci ba, wane taimako zan sanu ta bangarenka”.

Yace yana wani zazzaro ido kamar tsohon maye, “Duk abinda ki ke so zaki samu, ba so ki ke a raba shi da duk wanda za suyi huldar arziki ba, asa bakin jini a gare shi, sannan ya dauwama a shaye shaye”, sakwake tayi gaskiya Tsiduhu yana daya daga cikin bokayen da ta sani wanda suke da abin al’ajabi da yawa, ka duba yadda yake fadin abinda ke cikin zuciyarta kamar yana karantawa, duk abinda akayi a bayan idonsa ya sani zai kuma iya fada
Ta aje numfashi a gaggauce tace “Abinda nake bukata kenan”, yace “To kin samu Haj ki kwantar da hankalinki kawai ki biya nayi miki aiki”,
Ta gyara zama tace “Nawa ne?”
Yace “wannan aikin ai mai sauki ne don haka bazai ci kudi kamar wannan ba, nera dubu dari biyu kawai da ashirin zaki bada ni ma kuma bayarwa zanyi aje a samo kayan aiki, domin babu abinda zan baki ni da kaina zanyi aikin ke kuma za kiga biyan bukata”.
Ta yi murmushi tace “To babu damuwa, yanzu ban taho da kudi ba ga dai wanban”, ta bude jaka ta mika masa dubu dari tace “sauran dari da ashirin din kuma zan ba Haj Rakiya zata dawo ko zuwa gobe ne ta kawo maka”. Ya gyada kai kamar tsohon kadangare yace “Babu damuwa”.
Daganan su ka yi masa sallama suka dauki hanya, Haj kilishi na cigaba da kakabin yadda Tsiduhu yasan komai har tana ma ji a ranta

Please Login or Register in order to submit comment