Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa yafi Me Rakwacam iyawa ya fi shi kuma hatsabibanci.
Tun a motar Haj kilishi ta dubi Haj Rakiya tace, “yanzu ina zamu samu kogi da ruwa ke gudana”,Haj Rakiya ta yi murmushi tace “lalle Haj abubuwa sun yi ma kanki yawa, in banda haka ace har kin manta da kogin can yamma da gari kogin da muka jefa abubuwan da ba su da adadi, ko akan marigayi Alhajinki abu nawa muka je mu ka jefa”.

Page 198

Haj kilishi ta yi dariya sosai ta miko hannunta daya suka tafa, tace “Allah ya bar min aminiyata na rantse sai yanzu na tuna, lalle abubuwan da ke kan nan nawa suna da yawa musaddik da Afrah suna neman su haukata ni”. Haj Rakiya tayi dariya tace “Kada ki damu Haj ai kin dade kina wahala don haka lokacin hutunki ya zo da ikon Allah”, ta yi murmushi tace “Nagode da gudunmawarki bazan taba mantawa da ke ba a tarihin rayuwata”, Haj Rakiya tayi dariya tace “Haba Haj ai amana daya take, ke din aiba kashin yarwa bace meye baki min ba”, tace “Duk abinda na miki tabbas kin cancanta ne”.

Haka suka cigaba da tattaunawa, daga bisani kai tsaye Haj kilishi ta wuce inda kogin yake, bayan sun isa bakin ruwan babu kowa da kanta Haj kilishi ta jefa layar cike da farinciki tana jin aranta Afrah ta gama yawo. Ita kuma Haj Rakiya babu abinda take acikin zuciyarta sai dariya tare da daukar Haj kilishi wahalalliya wacce batasan inda rayuwa ta dosa ba. Daga nan kai tsaye gidan Haj kilishi suka wuce.
Ta yi ta hon, sai da aka dauki lokaci sannan Baba maigadi ya bude get din da sauri, cike da fusata ta shiga tana tsaida motar ta balle kofar motar ta fito rai a bace tana yi ma Baba maigadi wani irin kallo na wulakanci sannan tace “wane irin wulakanci ne wannan ina ta hon amma saida kaga dama sannan ka bude saboda baka dauke ni da muhimmanci ba”, Baba maigadi ya yi kasa da kansa yana neman afuwa yana gaya mata dalilin jinkirin da ya yi wanda baya wuce yana bandaki yana kama ruwa, amma duk da haka, haka ta cigaba da fada dai dai lokacin Afrah ta fito daga bangarenta rike da wata cooler abinci me kyau daya hannun rike da lemon roba.

Dif Haj kilishi tayi gaba daya daga ita har Haj Rakiya kallo suka bi Afrah da shi ita kam bata damu da kallon ba illama yi da tayi kamar bata gansu a tsayen ba.
Cike da fara’a ta mikama Baba maigadi cooler abincin da lemon tace “Baba ga abincinka”, cikin farinciki ya mika hannu ya karba yace “sannu da kokari Afrah Allah ya yi miki albarka Allah ya tsare ki daga dukkan sharri”, cikin jindadin addu’ar ta amsa da amin, lokaci daya ta juya zata koma, sannan ta dan dubi gefen da su Haj kilishi suke tsaye a ciki tace “sannunku Haj”.
Bata damu da rashin amsawar su ba ta shige bangarenta.

Haj kilishi ta watsama Baba maigadi harara a fusace ba tare da tace uffan ba ta wuce cikin gida Haj Rakiya na binta a baya.
Cikin bakinciki ta fada kan kujera ta na maida numfashi tamkar wacce ta shiga gasar gudu, Haj Rakiya ta zauna tana kallon ta tace “Eh lalle Haj kya kara shiga damuwa, yanzu alfarmar musaddik har ta kai su dinga kyautar abunci harda lemo, bayan da abinda zasu ci ma ba su da hanyarsa”, Haj kilishi ta yunkuro ta zauna sosai tace “Gara da ki ka gani da idonki, me yasa na kara shiga tashin hankali, duk a rayuwata cigaban musaddik nake adawa da shi, gashi kuma a idona ina ganin cigaban nasa, wannan samun aiki da wannan auren nasa masifa ne a tare da ni, na rantse bazan hakura ba sai nayi fito na fito da su duka”.
Haj Rakiya ta numfasa tace “Gaskiya sai kin kara tashi tsaye kada wankin hula ya kaiki dare, amma ni nasan Tsiduhu zaiyi miki duk abinda ki ke so”.
Haj kilishi ta mike ta shiga daki tana fadin “Ni ma naji ajikina za’a dace da aikin nasa”, tana shiga daki Haj Rakiya ta yi mata gwalo gami da murmushi.
Bata dade ba ta fito da kudi ta mika mata tace “Ga cikon kudin Tsiduhu gobe ki yi kokari ki je ki kai masa”, ta amsa sannan ta kara mika mata wani kudin tace “ga dubu talatin nan sai kiyi shatar mota ki je nagode sosai Allah yabar zumunci”.
Ta amsa gami da godiya, nan ta zauna suka cigaba da yi ma juna hudubar shaidan, nan ta ci abinci ta huta, daga bisani tayi gida cike da farinciki, duk duniya ba taga busness din da zata yi ta dinga samun irin wadannan manyan kudaden irin wannan busness din da ta fara, shin me yasa tuntuni bata yi tunanin yin wannan harkar ba da tuni Allah kadai yasan irin dukiyar da ta tara, domin irin kudaden da Haj kilishi ta ba bokaye sun isa mutum ya zama me kudin kansa.
Haj Rakiya ta kira Tsiduhu a waya tace ya rike dubu darin ita kuma zata rike dubu dari da ashirin din, godiya ya yi mata sosai, tare da fatan samun wasu kudin nan kusa.

Page 199

Afrah dai ta dage wajen inganta rayuwar mijinta, bata barin kayansa da datti ita ke wankewa ta kuma goge, wani abin sha’awa sai gashi da kansa zai hada kayan wankin nasa ya kuma hada da na Afran ya je ya kai wanki da guga.
Da ya sami kudi kuma zai je ya kai ya dakko, zuciyar Afrah tana cika da farinciki idan taga haka, dama kuma abinda yake so kenan wato farincikin Afrah.Duk asubar duniya sai ta tashi musaddik sunyi sallah sannan sunyi azkar tare bata taba yarda ya fita gida ba tare da ya yi azkar ba, ta kuma sa shi ya yi mata alkawarin yin sallah a duk inda yake in dai lokacin sallah ya yi to ya tsaya ya yi sallah, domin tana da yakinin matukar ya rike sallah to zai nisanta da duk wani sabon Allah.
A kullum Afrah tana cikin yi ma Allah godiya domin tana ganin cigaba, domin dai soyayyarta da ta cika zuciyar musaddik dole yasa yake kiyayar duk wani abu da yasan zai iya sosa zuciyarta, domin dai sosai yake jin damuwar da tafi ta ta zafi a duk lokacin da ya bata mata, ya wayi gari da soyayyar Afrah me tsanani wanda har ji yake kamar ba shi ba, duk inda yake cikin tunaninta yake,
Ya kuma daukar ma kansa iya lokacin da zai dauka bai dawo gida ba bazai taba shigowa hannu biyu ba sai ya sayo mata wani abu da zata ci ko zata sha don kawai ya faranta ranta.
Ba wai musaddik ya daina shaye shaye bane a’a yana yi amma ba kamar da ba komai ya yi baya, domin rabonsa da yasha wani abu ya bugu ya fita hayyacinsa shi kansa ya daina kirga kwanakin, yana sha amma ya rage sosai, sannan kuma baida wani lokacin zama wajen abokan banzansa domin bai zuwa har sai ya tashi aiki karfe shida idan yaje ya kan kai takwas a wajen daganan zai tashi ya taho gida, bayan sun gama shaye shayensu sai dai su kansu abokan nasa suna mamakin wannan canjin nasa, sanin a da yafi su shan komai amma yanzu sun fi shi don sau tari wani zubin ma sai dai yadan zuki daya biyu ya tashi.
Wani kuma abin burgewa a duk lokacin da ya sami lokaci ya kan je ya gaida mallam Mahmud da Inna Halima, yadda yakan je gidan inna Halima a hargitse yanzu fes zaka gan shi, hakan yasa Inna Halima bata ko gajiya da kallonsa ta sa ma Afrah albarka bata san iyaka ba.
Gidan mallam Mahmud kuwa in dai yaje haka Mama Hauwa ke tsare shi da kallo zuciyarta cike da mamakin irin canjawar da ya ke ta yi, tunda ya sami aikin nan komai ya ke masa kyau, abin dake kara girgiza zuciyarta shine yadda wani lokacin da har kudi yake ba mallam mahmud, shi kuma a ranar duk abinda ya fita ya sayo na amfanin gidan ya dinga cewa “ Da kudin da musaddik ya bani na sayo”, wannan kalmar kamar ta fasa zuciyar Mama Hauwa take ji.
Damuwa ta fara cika zuciyar Mama Hauwa, ko kadan bata son rayuwarsa ta baya ta dawo ba don komai ba sai don tafi son Afrah ta dauwama cikin matsala, bata son ta jidadin zaman aure ko kadan, domin tasan duk duniya babu wata masifa sama da ace mace ba tayi dacen gidan miji ba.
Ga abinda ke kara dugunzuma zuciyarta shine yadda har yanzu Na’ima bata samu miji ba, babu wanda ke zuwa wajen ta da sunan soyayya, duk da kullum ta na yawon bikin kawaye, amma ita har yanzu bata dace ba,duk da itace gaba da Afrah amma ga Afrah can a dakin miji ita kuwa ko mashinshini babu har yanzu sai kace wacce akayi ma kauri da jaba.

Page 200

A ranar kuwa da Musaddik ya fara daukar albashi. Tun rana ya tashi aiki bayan ya dauki izini wajen Haj Hudah tunda babu inda za su ranar, zaune yake kawai Haj Hudah na aikin kallonsa, sai kace tsohuwar mayya, bayan yabar gidan Hai Hudah kai tsaye wajen abokinsa Murtala ya wuce, ya sanar da shi ya sami albashi shine yake son ya taimaka ya raka shi ya yi sayayyar kayan abinci.Wani irin kallo me cike da jindadi da kauna Murtala ya tsare musaddik da shi lokaci daya kuma yana yima Allah godiya, lalle musaddik ya samu,addu'ar da yake masa a kullum na dawowa hanya madaidaiciya ta fara tasiri,tunaninsa mai kyau ya fara dawowa, yau ga makudan kuɗi a hannunsa da zai je ya yi sharholiyarsa da su amma baiyi ba maimakon hakama tunanin ya sayi kayan abinci ya kai gidansa ya yi, me yafi wannan farinciki.Sosai Murtala ya nuna masa jindadin sa, duk da kuma motarsa ta lalace haka su ka dunguma suka tafi shago tare. Da taimakon Murtala musaddik ya sayi duk abinda ya dace nau'in kayan abinci da sauran tsarkake. Sannan ya sayi atamfofi guda uku.Domin dai Haj Hudah tayi masa gata ta hanyar ƙara masa wasu kuɗin bayan albashinsa, da ta nuna masa jindadin yadda yake tafiyar da aikinsa yasa ta kara masa kuɗin acewarta babu wani dalilin yi masa ƙarin bayan wannan.koma dai Meye musaddik dai ya jidadi domin duk saye sayen da ya yi sai da ya sami rarar wasu kuɗin, a ciki ne kuma ya yi ya yi Murtala ya karbi wani abu amma yace bazai karbi ko sisi ba, a hakan ma ji yake kamar ya fi kowa farinciki. Bayan sun kammala duk saye sayen ne sannan musaddik ya yi shatar a daidaita sahu ya taho gida, shi ma Murtala ya tare mashin ya haye ya koma wajen aikinsa cike da annashuwa.

Musaddik ya turo get ya shigo bayan ya sallami me adaidata sahun da ya kawo shi, Baba maigadi cike da farinciki ya dubi musaddik sannan ya dubi kayan abincin dake zube a gabansa yace “sannu da kokari musaddik Allah ya kara shiga lamarinka”, ya yi murmushi yace “Amin nagode”, muryar musaddik da Haj kilishi ta jiyo yasa ta yaye labulen windo tana kallon komai, Baba maigadi yace “Bari na tayaka kwasar kayan”, akan idon Haj kilishi Baba maigadi ya dinga diban kayan abincin yana shiga da shi Haj kilishi na kirga kayan harda katan katan din lemu,don ƙarin takaici ma harda su cakulet sai kace wasu kananan yara.
Jin zuciyarta ta yi kamar zata fashe ta saki labulen gami da zuba tagumi ji kawai ta yi hawaye yana sauka a saman kuncinta, zafi take ji a ko’ina a cikin jikinta, wai meke faruwa ne?, ta tambayi kanta, kuka sosai take yi don me musaddik zai dinga cigaba bayan irin kudin da take kashewa don a datse duk wata hanyar cigaban nasa.
Ta janyo wayarta cikin hawaye ta kira Haj Rakiya amma bata dauka ba ta zauna ta zubama wayar ido ta kuma kasa tsaida hawayen da ke fita mata, domin tana jin wannan itace kadai hanyar da zata sami saukin masifar dake yawo a cikin zuciyarta.
Cikin kurewar hakuri ta kara danna sunan Haj Rakiya ta kira, wannan karon ta yi sa’a bugu daya Haj Rakiyar ta dauki wayar……………

Yanzu aka fara babu inda aka je, akwai badakala ta kin karawa sai mun hadu a littafi na biyu .


Yar gidan imam ✍️


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment