Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi
da wata mace da yake so, asalima shi bai taba
tsayawa ya yi soyayya da ko wace mace ba.
Ko da ya je gidan Inna Halima ya gaya mata
abinda mahaifinsa ya umarce shi da yi, shawara
kawai ta ba shi akan ya tsaya ya nemo ma 'yayansa
uwa ta-gari, don haka ya yi taka-tsantsan!
wajen nemo matar aure.

Page 100

Domin zai iya yiwuwa macen ta so shi domin
abinda ya mallaka ko don gidan daya fito ko don
kyau da cikar kamalarsa. Tabbas! Maganar Inna
Halima gaskiya ce. Ya zamar masa dole ya tsaya
ya nemi abokiyar rayuwa ta-gari.

A yayin da gefe daya Mama Hauwa ta fara yi
ma kawun musaddik Malam Mahmud maganar
mai zai hana Musaddik ya zo ya nemi 'yarsu Sakina, ayi tuwona maina.tunda tana ganin ya isa da Musaddik din yana cewa ya ba shi sakina shikenan, domin tana kwadayin yarta ta samu gidan hutu gidan arziki irin gidan Alh mansur.

Nan da nan Malam Mahmud ya gargadeta
akan kada ta fito da maitarta a fili, idan
Musaddik yana son Sakina, da kansa zai furta. Tunda ai gidan
ba bakonsa bane, yana zuwa yana kuma.
ganinta, Don haka idan yana sonta, ba sai an yi
masa magana ba, da kansa zai furta, hakan
yasa dole Mama Hauwa ta yi shiru da maganar.
sai dai ta dora Sakina a hanyar ta dinga nuna ma Musaddik
so da kulawa a duk sanda ya zo gidan, har ya
'Fahimci inda ta dosa, Amma abinda Mama Hauwa ba ta sani ba, shi
ne tuni Hajiya Kilishi ta gama shirinta tsaf akan
kokarinta na farko na ganin ta tarwatsa
rayuwar Musaddik.Domin zuwa wannan lokacin gaba daya ta gama tsara yadda zata kawo karshen kyakkyawar rayuwar da Musaddik yake shimfidawa.Don haka
Ta yi tunanin hada auran Musaddik da 'yar
kanwarta Hannatu da suke zama a birnin
tarayya Abuja, ta bukaci ta dawo nan Minna
gunta da zama tunda ta; gama makaranta zaman banza kawai take yi.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 101

Amma kafin Hannatun ta dawo , sai da
Haj kilishi tayi magana da Kanwarta Hajiya Kubra, wacce kusan
halinsu daya, don haka koda ta gaya
mata kudurinta na hada Musaddik da Hannatu aure da dalilinta, ba
ta ji darr! Ba, ta amince, domin tana
ganin duk Karuwarsu ce. Hannatu za ta zama musabbabin
kusanta su da arziki, ta umarci Hannatu da ta tafi minna,don haka Hannatu ta tarkata kayanta ta yi minna.

Gargadì na farko da Hajiya Kilishi ta fara yi
mata, shine kada ta sake ta dora ma
Kanta son Musaddik, domin ta sa a ranta aure ne za su yi na
wucin gadi, na dan lokaci, sai ga shi
Kuma anyi sa'a Musaddik din burge Hannatu kawai yake yi,
amma babu sonsa ko kwayar zarra a zuciyarta.
Sai dai ta ci-gaba da shishige masa tare
da nuna masa kauna da kuma kokarin nuna masa ita
yarinya ce ta-gari, kamar yadda Haj kilishi ta nuna mata, sai dai ko kadan Musaddik bai
taba sa ma ransa wai zai so Hannatu
ba Ko kurna tana yin abinda take yi masa, don ya
so ta ne. Tsawon lokaci Hannatu ta share a gidan,
amma Musaddik baya ko bi ta kanta, hidimarsa kawai yake yi.
Hakan kuwa ya fara tayar ma da Hajiya
Kilishi hankali, ta rasa mafita, don haka
ta nemi aminiyarta Hajiya Rakiya, domin neman shawarar
yadda za'a bullo ma lamarin, ba tare da wani dogon tunani ba.


Page 102

Hajiya Rakiya ta bada shawarar a hada
Lamarin da Malamai, domin a hada
soyayyar Musaddik da Hannatu ta karfi da yaji, wannan
shawara ta yi dai-dai da tunanin Hajiya
Kilishi don haka ta bukaci rakiyar Hajiya Rakiya zuwa wajen amintaccen bokanta
Wato Mai Rakwacam, suna isa tun kafin
su fadi abinda ya kawosu. Mai Rakwacam ya gaya
masu dalilin zuwansu, ya kuma tabbatar masu da
cewa auran Musaddik da Hannatu tamkar an yi, an
gama ne. Ya yi ta surkullen ayyukansa, daga bisani
ya ba ta kwallin da Hannatu za ta sanya a idanunta,wanda suna hada ido do
Musaddik Shi kenan, sai turare da za ta shafa a jikinta,wanda so ake kawai
ya ji kamshin,
sai kuma wani garin magani da za ta
zuba masa a cikin abincinsa da zaran
ya ci abincin shikenan bukata ta gama biya. Bayan dawowarsu daga
wajen Mai Rakwacam ne. Hajiya Kilishi
ta ba Hannatu duk abubuwan da za ta yi amfani da su.
Na sawa a abinci kuwa da kanta take sanya
masa, kuma sai ta tabbatar ya ci, sannan take barin
wajen, kwanaki uku kacal! Tsakani. Musaddik ya
haukace akan soyayyar Hannatu. Bai sami sukuni
ba, sai da ya gaya mata, ta kuma amince.
Da kansa ya sami Alhaji Mansur ya gaya
masa ya sami matar aure, wato Hannatu. Alhaji Mansur
ya karbi maganar babu yabo, ba fallasa, don dai a
so samunsa ne, ya sami wata wacce ba ta da alaka

Page 103
da Hajiya Kilishi. Domin baisan dalilin da yasa ya ji kwata kwata bai samu wata natsuwa ba da jin zabin musaddik duk da baida wani buri da ya wuce na musaddik din ya fito da matar aure ya yi masa .Amma tunda abinda dansa yake
so, shi yake so, ya sa ya amshi zabin na
sa hannu biyu ba tare daya bari ya gane zabin na sa bai yi masa ba.

Ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa, ta sami
jindadi, farin-ciki da kuma natsuwa,
domin hakanta ya kusa cimma ruwa, nan da nan aka shiga shirye-shiryen biki
kasancewar Hannatu marainiya ce
mahaifinta ya rasu, kuma zuwa wannan lokacin ba su da komai sai gidan da suke ciki a Abuja shine kadai rufin asirinsu bayan haka basu da wani abin da zasu yi tunkaho da shi. Hakan ne ya sa Alhaji Mansur ya dauki nauyin komai na dakinta da abinda za’ayi mata. Haj kilishi kuwa marairaicewa ta yi ta na yi masa godiya, tana kuma nuna masa tamkar bata damu da auren ba tamkar bata so, don ta nuna don dai kawai musaddik din ya matsa ya na sonta ne ba don haka ba ai Musaddik ya fi karfin Hannatu. Sabida tsabar makirci.

A ranar da Musaddik ya je ya gaya ma
Inna Halima, Hannatu ya zaba a matsayin matarsa ta yi
masa fatan alheri tare da sanya ma lamarin albarka.duk da acan kasan zuciyarta itama tana jin tamkar danta musaddik bai dace da Hannatu ba, amma alokacin da ya kawo mata ita har gida ta gaisheta sai ta ji ta yaba da hankalinta da nutsuwarta saboda nuna mata tayi duk duniya babu wanda ya kaita ladabi da biyayya da kuma son Musaddik din. Hakan yasa inna Halima ta watsar da wancan tunanin nata, ta yarda da Hannatu.

Daga bisani musaddik ya je gidan kawunsa Malam Mahmud domin
shi ma ya sanar da shi maganar auren nasa da Hannatu., a ranar ya tarar da Afrah tana wanke-wanke
cike da mutuntawa ta gaishe shi. Ya
amsa cikin nuna yabawa da lamuranta.
Domin dai duk cikin *ya yan Kawunsa,
babu yarinyar da haka nan yake ganin girmanta tare da kaunar
dabi ‘unta irin Afrah, yarinyar gaba daya
rayuwarta daban ce, ba ta da hayaniya.
Bayan ya gaisa da Kawunsa da Mama
Hauwa yake sanar da Malam Mahmud maganar Hannatu
Malam Mahmud ya yi murna, ya kuma
sa albarka sabanin Mama Hauwa da ta
hade girar sama da ta kasa, idan ranta ya yi dubu, to ya baci, ta dubi Musaddik
tace “Amma Musaddik ca na ke
soyayya ka ke da Sakina?”

Page 104
Ji
Musaddik ya yi saurin kallonta ya ce
Cike da mamaki yace”Soyayya, kamar
yaya?" Ta ce "Irin yadda na ga taku ta zo daya, sai
na ke zaton ko soyayya ku ke yi, ka ga
shikenan tuwona, maina, sai ayi hadin zumunta kawai"
Musaddik ya girgiza kai ya ce
“Mama Hauwa kin fahimta a bai-bai, domin gaskiya ba
soyayya muke yi ba. Asalima ni ban taba dasa ma
kaina tunanin zan so-ta ba, daya wuce ina sonta amma soyayya ta
'yan-uwantaka. Hannatu dai ita ce na ke son na aura, ita nake kwadayin ta zama abokiyar rayuwata”.
Mama Hauwa ta yi turus! Tana kallonsa
Cike da takaici, a yayin da Mallam Mahmud ya ce "Kyaleta
ka ji, neman zance ne da ita kawai. Musaddik Allah
ya sanya alheri, ya sa Hannatu abokiyar arzikinka ce, ya kawo zaman lafiya a tsakaninku”

Cike da girmamawa Ya amsa da "Amin"
Daga nan ya zaro kudi
ya aje masa, Mallam Mahmud ya yi godiya, kamar yadda ya saba.sannan ya tashi zai tafi,
dai-dai inda Afrah take, ya tsaya ya
dakko kudi masu yawa ya ba ta, ganin irin kallon wulakancin
da Mama Hauwa ke yi masa, ya sa ya fice ba tare da ya bata ko sisi ba.
Kamar mama Hauwa na jiran musaddik ya fita kawai ta kafama mallam mahmud
gwanjon bala'i, wai yana da damar da
zai sa Musaddik ya auri Sakina, amma ya ki sa baki, illa
ma goya masa bayan auran Hannatu da
yake yi. Daya gaji da sababi da bala'inta
ne ya kakkabe rigarsa ya tattara ya bar gidan.

Page 105

Bayan auran Hannatu da Musaddik, a
Katafaren gidan da Alhaji Mansur ya ba shi ya tare, babu
Wanda baya sha'awar rayuwar Musaddik. Allah ya
rufa masa asiri, amma baya wulakanci.
Baya kyamatar talaka, ga taimako da
son shiga duk abinda zai daukaki addini, ba Alhaji
Mansur kadai yake yaba da halayen dansa ba, har
sauran jama"a suna matukar ganinsa
da kima da daraja, domin dai Allah ya tabbatar da natsuwa a
cikin rayuwarsa. Musaddik Mansur musaddik kenan. Wadannan halayen nasa da jefa shi a cikin sahun mutanen kirki da kowa yake yi, da kuma alfahari da mahaifinsa yake yi da shi, ya na matukar bakanta ran Haj kilishi ji take kamar ana fisgar ranta.

Duniya ba matabbata ba. Watanni biyu
kacal Da auran Musaddik. Allah ya dauki ran jigo kuma
gatan Musaddik, wato Alh. Mansur, ya yi
rasuwar farat daya a dalilin hadarin mota a hanyarsa ta zuwa
Kano daga Abuja, domin halartar wani taron yan kasuwa da suka gayyace shi.
Sai gawarsa ce ta dawo Minna, inda a
nan ne aka yi masa suttura aka rufe shi.
Fadin tashin hankali da kuncin da Musaddik ya shiga, bata lokaci ne.
Nan da nan ya rame, ya fige, ya fita
hayyacinsa. Rasuwar mahaifinsa ta yi
Mummunan taba shi, hatta abinci baya iya ci. Duk wani me
imani, dole ya tausaya masa, domin ya fada mawuyacin hali.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 106


Haka Inna Halima da Malam Mahmud
su ka yi ta Kokarin dawo da shi musaddik hayyacinsa tare da yi masa
addu'ar samun dangana.
Ita kam Hajiya Kilishi duk da rasuwar
mijin nata ya taba mata zuciya, to fa maganar abinda ya
mutu ya bari, ya fi damunta, bakin-cikinta daya ne
na kaso mafi tsoka da Musaddik zai samu, domin
dai ta san kason 'ya' yanta mata biyu. MusaddiR zai ci shi kadai.

Idan da akawi abinda za ta fi shi da shi,
bai wuce tumunin takabarta ba da kason 'yarta daya, ta
san kuma babu abu daya da 'ya'yanta
zasu bari a hannunta, tunda sun riga sun mallaki hankalinsu.
Suna kuma tare da mazajensu, don haka ta san da
kasonta kadai za ta tashi, shin ya za ta yi? Ta san
dai ba ta da damar hana Musaddik gadonsa, domin ya san yancinsa. Yasan abinda musulunci ya tanadar masa.

Abinda ko take gudun ne ya faru, domin
bayan fitarta takaba, aka yi rabon gado,
ba gidan Musaddik ba motarsa ba kuma kamfaninsa na siminti a cikin rabon
Domin Alhaji Mansur ya rubuta a rubuce
cewar duk wadannan abubuwan ya ba
shi su kyauta ne. Hakan ko ya tada hankalin Hajiya Kilishi, domin zahiri wannan karon Alh mansur ya yi son rai don kamata ya yi yadda ya ba musaddik wannan tarin dukiyar ace su ma su Hassana ya basu domin su ma yayansa ne, amma soyayyar musaddik ya makantar da shi daga ganin illar wannan bambancin da yake nunawa a tsakanin yayansa, wanda kusan shine dalilin da ya jefa rayuwar gudan jininsa cikin gararin rayuwa bayan rasuwar tasa, domin dai Haj kilishi ta kara haukacewa da tsanar musaddik fiye da kullum, domin duk akasafin rayuwarta babu abinda take hangowa sai gado, duk da babu wanda yasan gawar fari,

To ga dai abu a rubuce, balle ta ce karya
ne ta kuma danne , babu wannan damar Sannan da aka yi rabon gadon
Musaddik ya tashi da kaddarori da
Kudade makudai amma duk ba su a gabansa, ba su kuma burge shi ba, ya fi

Page 107
bukatar mahaifinsa fiye da komai a
duniya, ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa gaba daya tunaninta
ya tafi ne akan dukiyar Musaddik da
tunanin yadda dukiyar za ta zama nata, watau ta mallake ita daya.

Abu na farko da Hajiya Kilishi ta fara yi,
shi ne kokarin mallake Musaddik, da taimakon Bokanta
Mai Rakwacam, ta kashe makudan kudi
Kafin bukatarta ta biya, domin kuwa ta sami mallake
Musaddik, komai zai aikata ko zai zartar
akan duk abinda ya shafi rayuwarsa sai da saninta, sai da kuma amuncewarta
Yana matukar jin tsoronta tare da tsoron bata
mata rai, sai daya zamana duk duniya
Musaddik gani yake baida kowa sai Hajiya Kilishi, hatta
dangantakarsa da su Inna Halima duk ta ja baya,
domin ko kafin ya je gidanta ma aiki ne. Kwata kwata ya dauke kafarsa basa ganinsa wanda hakan ba karamin ta da hankalin su ya yi ba.A yayin da
Hannatu take tsiro da halayen wulakanci da musgunawa ga musaddik
sam ba ta ganin mutunci ko darajarsa
mutuncin ko darajarsa.abu kadan tun bayan rasuwar Alh mansur zata hau cin mutuncinsa. Gaba daya duk ta canja.

yayin da shi kuma musaddik din ya dora
ma kansa tsoronta da shakkarta, gaba daya lamuran Musaddik
suka dagule, rayuwarsa ta shiga cikin gigita da dimauta. Wannan shine tushen fara lalacewar rayuwar musaddik.

Domin dai baida tunani nasa na kansa,
sai wanda Hajiya Kilishi da Hannatu suka tusa masa,
haka zalika baida ta cewa, sai cewarsu,

Page 108

A hankali Hajiya Kilishi da Hannatu suka
fara karar da dukiyar Musaddik,ya zama wanda da sun ce,ya yi kaza
bai samun sukuni, sai ya aikata masu, Haka Hajiya
Kilishi ta yi ta sa Musaddik yana sa hannu akan
Kadarorinsa me tabbatar da cewa ya mallaka mata,
wasu kuma ya mallaka ma Hannatu.
Daga Inna Halima har Malam Mahmud
babu wanda ya san wainar da ake toyawa, balle su
taimaka masa su yi ma tufkar hanci tun
nesa sa kofa .Hatta kamfanin ya daina zuwa kullum yana
gida, hakan ko ya fi komai yi ma Hajiya
Kilishi dadì, inda ta fara tura Hannatu kamfanin tana shiga
ofis dinsa hakan ko ya janyo cece ku ce a kamfanin
a tsakanin ma'aikatan, daga bisani Hajiya Kilishi
tasa Musaddik ya yi ma ma'aikatansa bayanin cewa Hannatu ce
za ta ci-gaba da daukar nauyin
kamfanin, domin shi ayyuka sun yi
masa yawa Sannu a hankali cikin dabara da kauce hanyar Allah ta bin
Bokaye da Hajiya Kilishi ta saba ta sami
nasarar kwace kamfanin daga hannun Musaddik, inda ya sa hannu
aka kuma kafa shaidu akan cewa ya bar
ma natarsa kamfanin halas-malak.
Wanna lamari ya daga hankalin abokin
Masaddik kuma (Cashier) na kamfanin
Murtala domin zuwa wannan lokacin ya fara zargin tamkar Musaddik baya cikin
hankalinsa, domin abubuwan da suke faruwa abubuwa ne masu matukar daure kai matuka. Akwai alamar tambaya domin hatta mu’amalar Musaddik da mutane duk ta canja. Yana yin abubuwa tamkar bai san abinda yake yi ba.

Page 109

Da kansa ya sami Musaddik ya tunantar
da shi muhimmancin kamfanin a gare shi, ya kuma
tambaye shi meye dalilinsa na barin ma matar da
bai taba koda haihuwa da ita ba irin
wannan dukiya? Anya kuwa yana cikin hayyacinsa.
Musaddik ya numfasa yana kallon Murtala, sannan yace cikin wata irin
fuska “Ni fa babu abinda ke gabana, ko
Yake min dadì gaba daya rayuwar ma ni ta fita kaina, don
haka duk wata dukiya, ni ba ta gabana.
Kuma Hannatu matata ce, ko ta haihu ko ba ta haihu da ni
ba, zan iya yi mata kyauta, saboda haka don Allah
ka tsaya a matsayinka na aboki na, ka daina kokarin
shiga abinda bai dameka ba,”
Haka Murtala ya bar Musaddik cike da
mamakin irin maganganun daya gaya masa, domin
dai ya san ba haka Musaddik yake ba a
da don haka bai ji haushi ba.
Ya yi alkawarin zai ci-gaba da fahimtar da shi
illar abinda yake aikatawa, har ya fahimta, ko ya
nemi wani shakikin Dan-uwansa ya sanar da shi
abinda ke faruwa ko za su iya taimakawa.

Sai daya zamana Hajiya Kilishi ta gama
zare komai, domin hatta gidan da yake ciki, ya mallaka
shi ga Hannatu, sannan har zuwa wannan lokacin babu abinda bangaren dangin Musaddik na wajen uwa suka sani.a lokacin ne Hajiya Kilishi ta ga ya
kamata ta dauki mataki na karshe na karasa lalata rayuwar Musaddik.

Page 110

Domin ba ta kaunar duk wani sanadi da
Zai sa Musaddik ya farga ya dawo hayyacinsa, ya fahimci
irin mummunar barnar da ta yi ma rayuwarsa, ko
kuma hankulan mutane da na dangin mahaifiyarsa
su ankara da halin da ta jefa Musaddik.
Don haka ta fara neman shawarar aminiyarta
Hajiya Rakiya yadda za su yi da Musaddik. Hajiya
Rakiya ta yi shiru tana nazarin lamarin, a nan ne
Hajiya Kilishi ta dubeta ta ce
"Ni fa Hajiya
Zuciyata a bushe take akan Musaddik ko kadan ba
na kaunar yaron nan, musamman idan na tuna ni fa
ba ni da da namiji, sannan ga irin fifikon da ya samu sama da nawa yayan, sannan wannan daraja da natsuwa da yake da shi da kowa ke sha’awar sa ya na matukar bata min rai,sai na ji tamkar
na raba Musaddik da doron Kasa"
Ta dan hadiye yawu gami da kallon
Haj Rakiya da take sauraron ta, sannan ta ci-gaba da cewa cikin wata muguwar
Fuska, da gaba daya ta canja yanayin ta, ta koma tamkar ba ita ba.
"Kamar yadda a yanzu na gama tunanin
lokaci ya yi da zan raba Musaddik da duniya gaba
daya, domin duk wani amfani da zai yi min, ya riga
ya gama yi min, kuma ina ganin mutuwarsa ita ce
kadai hanyar da asirina zai rufu akan dukiyarsa,
domin babu wanda zai tuhumeni..”
Hajiya Rakiya ta yi gaggawar dakatar
da ita tana yi mata kallon ko kin haukace ne? Ta ce "Haba
Hajiya. Shin rashin imaninki har ya kai ki
fara tunanin daukar rai, bayan duk irin ta'asar da ki ka
yi masa na raba shi da arzikinsa mallakarsa, da raba shi da yancin zama miji me cikakken iko a gidansa.duk
wannan bai isa ba, sai kin kashe shi?

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

page 111


abin ya yi yawa gaskiya, kuma ni ban goyi bayan wannan shawarar ta ki ba na a kashe shi, saboda babu komai a cikin shawarar taki sai gagarumin hatsari
Shin ba kya ma tunanin ko Musaddik ya
rasu yan-uwan mahaifiyarsa za su iya bin kadin dukiyar musaddik din
daya mallaka miki, ba gara kin bar shi
araye, shi ya gaya ma duniya da kowa ma cewa shi
ne ya mallaka maku dukiyar ba.
Idan ko mai kaya ya ce ya bayar, to
waye ya isa ya ce bai bayar ba? Idan kuma ki na tunanin shi zai iya
yi miki bore wata rana ne, ai akwai wata
hanyar da ta fi wacce ki ke son bi saukin bi."Haj kilishi cike da gamsuwa da
maganganun Hajiya Rakiya ta ce
"Wace. hanyar
ce?" Hajiya Rakiya ta ce "Ba sai a lalata rayuwarsa
ba, a raba shi da kyakkyawan tunani, a
hana shi shiga cikin mutanen kirki, balle har shawarwarinsu
su yi tasiri wata ran a rayuwarsa.
Me zai hana a kwace kwarjini da kamalar da
jama"a suke ganinsa da ita, ina nufin a hada shi da
shaye-shaye, domin shaye-shaye shine tushen
lalacewar rayuwar, duk wani matashi. Shine kuma
zai zama abin kyama a wajen mutanen
kirki “ Ta gyara zama tana kallon aminiyarta cike da jindadin maganarta da jin shawarar ta ta itace abar dauka ta ce “ ina jinki Haj”

Hajiya Rakiya ta ci-gaba da cewa, "Kin
ga kuma mutane ba za su taba zarginki ba, za su
dauka don dukiyar da aka bar masa ne
ya sa ya canja halinsa da kuma bakin-cikin rashin mahaifinsa,

Page 112

wasu ma cewa za su yi ya sayar da kaddarorinsa ne,ya yi iskancinsa, babu wanda zaiyi zargin kece kika kwashe dukiyarsa,”
Hajiya Kilishi ta yi dariya sosai ta ce
“Amma haj ban taba tunanin ki na da kaifin basira haka ba, idan
ka kashe makiyin ka ma, ai ka taimaka
masa ne, gara ka'aje shi ka yi ta kallon sa yana wahala a
rayuwarsa, don haka shawararki ta yi,
na kuma dauketa, ki na kuma da tukuici na musamman'
Hajiya Rakiya ta ce "To godiya na ke babbar giwa, musaddik din me da zai dinga tayar miki da hankali”

Hajiya Kilishi ta dubeta ta ce "Amma ina
fatan za ki ci-gaba da rike min sirrina kamar yadda ki ka saba, kada wanda ya ji ko ya gani, mu haka mu binne, kamar yadda muka saba”

Haj Rakiya ta yi dan murmushi ta ce "Haba, haba, ai ba ki da wata matsala
in dai nice, ki sha kuruminki, babu me ji ai tsakanin mu ya wuce haka” Haj kilishi ta sauke ajiyar zuciya ta na jin tamkar ta gama mallakar komai na daga cikar burinta a duniya.

daga nan suka ci-gaba da tattaunawa akan yadda komai zaibtafi yadda suke so ba tare da wata matsala ba.

Page 113

Washegari kuwa da taimakon rakiyar
haj Rakiya suka tafi rugar Mai Rakwacam dauke da
bukatunsu, da fatan samun dacewa. Mai Rakwacam
ya dauk tsawon lokaci yana bincikensa, kafin ya
dubi Hajiya Kilishi ya ce,
'"Aiki zai yiwu, bukata
kuma za ta biya, ki aje Naira dubu dari biyu da
hamsin, za' a sayi kayan aiki."
Nan da nan Hajiya Kilishi ta Balle jakarta ta
aje masa kudin, ya kara kallonta ya ce "To ku tashi
ku tafi, jibi goshin magariba ki dawo”

Haj Kilishi ta yi godiya, suka tafi
Kwanaki biyu tsakani goshin magariba kamar yadda me Rakwacam ya
bukata. Hajiya Kilishi da Hajiya Rakiya suka isa
rugar, sun tadda Mai Rakwacam ya kammala duk mugun aikin da zaiyi akan bukatar su.don haka
Ya dauko wata bakar laya da ta ji surkulle, ya dubeta yace
ta sami kasan jijiyar bishiyar kuka ta binne hade
da wani dan karamin kasko daya ji daure-dauren
bakin zare, duk jikinta an zaneta da
Sunan Musaddik, ya ce ta hada da layar ta binne, da zarar
ta binne aiki ya kammala.
Babu wanda zai raba Musaddik da
Shaye-shaye da lalacewa, sai ranar da aka tono wannan
layar da kaskon. Don haka ta san yadda za ta binne
da kuma inda za ta binne.domin ana son dadaddiyar kuka da ta dade.
Ya kara da cewa, ba zai karbi ko sisi ba,
sai aiki ya ci. Daga nan za ta dawo ta cake masa Naira
dubu dari uku cif! Hajiya Kilishi ta karbi komai ta

Page 114

yi godiya tare da alkawarin dawowa ta
ba shi hakkinsa da zarar bukata ta biya, daga nan suka dauki hanyar gida

Suna cikin tafiya ne. Hajiya Kilishi ta
dubi Hajiya Rakiya ta dan rage gudu fuska cike da farinciki ta ce
"Yanzu ina za mu samu
bishiyar kuka, inda za'mu binne wannan asirin?"
Hajiya Rakiya ta yi murmushi ta ce.
"Dadina da ke mantuwa, ai ni tunda ya
ambaci bishiyar kuka, na ji na sami kwanciyar hankali , kin manta rikakkiyar bishiyar kukan da ke
bayan gida na, abubuwa nawa muka binne a kasanta, tun marigayi megidanki na raye,”

Hajiya Kilishi ta fashe da dariya ta ce "Godiya
“ Anyi haka, godiya na ke da samun aminiya, mai share hawayen kuka
na, yanzu kawai mu wuce gidan naki mu aiwatar da aikin kafin na wuce gida” Haj Rakiya ta yi dariya tace “Angama kawata”.

Sun isa dare ya yi, gari kuma ya yi duhu,
Hajiya Rakiya ita' ce me haska ma
Haj kilishi bakin bishiyar da hasken wayarta. Hajiya Kilishi
kuma na aikin haka, sai da ta haka rami me zurfi.
Sannan ta binne kaskon da layar. Babu
Wanda ya gan su har suka gama, suka tafi.hankali kwance kamar wadanda su ka aikata abinda ya dace, Allah kasa mu fi karfin zuciyar mu, yasa duk runtsi mu tsira da imanin mu.

Kwanaki biyu tsakani, sai ga Hannatu
hajaran majaran tana gaya ma Hajiya Kilishi ba za ta koma.
gidan Musaddi& ba, domin jiya kwana ya yi yana
shaye-shaye, ta ce dama ya iya shayc-shaye ne?
Mutumin da ko taba ba ta taba ganin ya sha ba,

Page 115

amma rana
amma abin tsoro da mamaki sai gashi rana tsaka ta gan shi cikin wannan
mummunan halin.
Hajiya Kilishi ta fashe da dariya, ta mike
tayi rawa, ta yi juyi, ta daga hannu tana yi ma Allah
godiya tare da yi ma kanta kirari na sharri. Hannatu
ta yi galala tana kallonta cike da mamaki Hannatu tace

“ Ya na ga ki na murna Inna, wannan fa magana ce ta canja sabon babi magana
ce ta lalacewar rayuwar Musaddik da ni kaina”
Hajiya Kilishi ta koma ta zauna, tana
Fadin “ waye yace miki haka Lalacewar rayuwarsa dai, ina ruwan ki, ko kin
manta tun farko na gaya miki wannan aure ne na
dan lokaci; aure ne kuma na samun arziki, ko kin yi
kuskuren fara sonsa ne?"
Hannatu ta girgiza kai ta ce
"Ban fara sonsa ba gaskiya amna a
zahiri na fara tausayinsa, saboda in dai rayuwar da ya fara a yanzu akanta zai cigaba da tafiya to babu abu daya na alheri da zai zo gabansa a duniya “
.Haj kilishi ta saki tsaki tace

Please Login or Register in order to submit comment