Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiyar
da matarka dadin da kowace mace ke
mafarkin samu, domin zan tsaya tsayin daka wajen ganin na inganta rayuwar ku duka kai da matar ta ka”.
Alhaji Yusuf Sanda ya muskuta yace
“Ka ga ka huta da zaman banza, kuma wannan wata hanya ce ta ci-gabanka,
don haka me ka gani? Ina fatan ba za ka ki karbar wannan garabasar ba”. Shuru Alh yusuf sanda ya yi ya kara zuba masa ido tamkar yana addu’a a cikin ransa na cewar Allah yasa ya amshi aikin.
Musaddik ya muskuta ya gyara zamansa, ransa da zuciyarsa cike da dimbin tunanin wannan aikin, da hakanan yake jin tamkar hatsari ne a gare shi.

Ya nisa yace “Na ji bayananku, sai dai bazan iya baku amsa kai tsaye ba ina
bukatar dan lokacin da zan yi tunani

Page 174
idan na yanke shawara zan neme ki na sanar da ke”, fara’ar fuskar yusuf sanda ta dauke ya dube shi da sauri yace “ Har wane tunani zaka yi akan wannan maganar cigabanka ne fa, bana jin akwai mutum irinka da za’ayi masa irin wannan tayin ya bada irin wannan amsar da ka ba da”, Haj Hudah tayi saurin dakatar da shi tace “A’a bar shi yaje ya yi tunaninsa ai babu komai”, ta dawo da kallonta gare shi tace “ kada ka damu kaje kayi tunaninka, na baka dukkan lokacin da kake so”,
Musaddik yace “Nagode Hajiyan Allah”, Alh yusuf sanda ya girgiza kai yace “ shikenan amma ina fatan duk tunanin da zaka yi, karshe ya zama eh ce amsarka”, ido kawai musaddik shi ma ya sama Alh yusuf sanda yana tunanin tamkar dalilin da ya fada da yake son ya yi aiki a karkashin matarsa ba shi kadaine dalilinsa ba, domin yadda yaga tsantsar damuwa a cikin idanunsa don kawai bai amshi tayinsu farat daya ba.
Ko da ya tashi zai tafi, baisan wane tunanin Alh yusuf sanda ya yi ba ya karkace ya fito da kudi masu yawa ya mikama musaddik, ya amsa yayi godiya sannan ya yi musu sallama. Har ya fice daga falon Haj Hudah shi take yi ma wani irin sassanyan kallo, shi kuma Alh yusuf sanda ita yake kallo, daga bisani ya jinjina kai gami da lumshe idanunsa.


A ranar da wuri Musaddik ya koma gida,
bai bari ya yi daren da ya saba ba, sannan bai sha wani abu mai karfi ba wanda zai gusar masa da hankali saboda yana so ya yi
magana da Afrah, musamman akan
shawarar da ya ce ta yi. Yau ita ce rana ta biyu. Afrah na zaune
akan kujera, zuciyarta cike da tunane-
tunane Musaddik ya yi sallama ya shigo, cike da mamakin
dawowarsa da wuri, ta amsa sallamar,
Ya shigo ya zauna daf da ita,
Bayan ta yi masa sannu da zuwa ne, ta
ta shi domin ta dauko masa abinci, ya dubeta cikin yanayi na kulawa yace
"Ina za ki je” ta dakata tana kallonsa tace “zan je na dakko maka abinci ne, nasan tunda ka dawo da wuri kila kana jin yunwa”, ya mika hannu ya hanyo hannunta ya zaunar da ita kusa da shi sosai yana kallonta yace “ zo kiyi zamanki, ba na Jindadin cikina da daddaren nan, babu abinda zan iya ci, kila ko sai dan ruwan lipton din nan naki me dadi”, tayi murmushi tace “ to bari naje na dora”, ya girgiza kai yace “ Aa ki bari sai anjima , idan mun gama magana” , ta bude ido sosai tace “ wace magana kuma zamu yi?”, ya kara matse hannanta a cikin nasa yace “ kin manta maganar mu ta shekaranjiya”, nan da nan ta canja fuska, ta shiga kokarin zame hannunta a cikin nasa, shi kuma ya kara matse hannun yana cigaba da shafawa.

Page 175

A hankali cikin faduwar gaba yace “Afrah ina son na ji shawarar da ki ka yanke akan maganar da muka yi, ina son kuma ki sani na baki wannan zabin ne saboda banda wani zabi”ya
fadì maganar ne cikin faduwar gaba, domin bai san
dalilin da ya sa ya sami kansa da addu'ar Allah ya
sa ba ta zabi rabuwa da shi ba, domin yana jin tamkar bazai iya jure rabuwa da ita ba, yana jin wani abu a game da ita me wuyar fassara. Afrah ta gyara zamanta, har yanzu hannayensu na manne da na juna.
Ta dube shi sosai, sannan ta ce
"Kasan musabbin aurena da kai?”, kai ya girgiza alamar bai sani ba, yace, "Ban sani ba, amma dai nasan duk wani musabbabi ba zai wuce biyayyar iyaye ba”, ta gyada kai tace “Bazan ce babu ba, tabbas akwai biyayyar a ciki, amma ina son ka sani na aure ka ne
akan kyakkyawar niyyar mu na kokarin
saka hanya ta-gari, ba kamun kanka na aura ba, balle nace saboda ba ka da kamun kai zan rabu da kai, babu halinka daya da ban sani ba kuma na aureka, to don me zaka kawo kalmar rabuwa a tsananin mu, bance na gaji ba, don me ka ke son ka gajiyar da ni


Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 176

to wai ma me yasa kake son mu rabu akan dalilin da yasa muka hadu, ba ni da burin rabuwa da kai ko da na kiftawar ido ne”, idonsa na cikin nata musaddik ji yake kamar ana zuba masa ruwan sanyi a cikin kirjinsa.

Afrah ta numfasa ta cigaba da cewa
“Duk irin abinda ka ke hange akan rayuwata a dalilin auranka,
ni ma na hangi irinsa kafin na aureka,
amma kai ne mijin da Allah ya kaddara min, kuma kai ne wanda
na ke fatan na gama rayuwata da shi a matsayin mijina”

Haka nan wani dadì ya dinga bakuntar
zuciyar Musaddik, wani irin so da kaunar Afrah me tsanani
ya dinga kutsowa yana Kara samun wajen zama a cikin zuciyarsa,duk yadda ya so ya ki yarda da cewa yana son Afrah hakan ya faskara, domin a wannan daren ya tabbatar ma da kansa cewa yana son Afrah so na hakika.
darajarta da kimarta suka kara fadada
a cikin ransa, ta zuba idanunta a cikin nasa, sannan ta ci-gaba da magana
"Eh, na yarda a lokacin da na aureka,
biyayya ce da son cika buri da umarnin mahaifina, Amma
babu soyayyarka a zuciyata, amma a
yanzu ina tabbatar maka da cewa zuciyata cike take da
soyayyarka, ina sonka da zuciya daya,
ba kuma na fatan rabuwa da kai, don halayenka munana, domin a Yadda
na sanka da , ina sa ran wata rana za ka koma haka,
Na kuma amshi komai a matsayin
Kaddarar rayuwata, don haka ni ba zan rabu da kai ba, zan
zauna tare da kai da dadi ba dadì, zan ci-gaba da yi
maka addu'a tare da zama mata ta-gari a gareka,”

Page 177

Ta dago tana kallon rikitattun idanunsa tace “Ka ji shawarar da na yanke."
ta kara gyara zamanta ta ci-gaba da cewa “ Ya rage ruwanka, ka
kyautata min tare da sauke hakkin da ke
kanka nawa, Ko yin akasin haka, ni dai ina nan tare da kai”.
Tana gama fadin haka, ta yi gaggawar
zare hannunsa a cikin nasa ta mike zata shiga uwardaka, Musaddik baisan lokacin da yasa hannu a gaggauce ya riko hannunta gami da janyota gaba
daya ta fado jikinsa, a zafafe ya sa hannayensa biyu duka
ya rungumeta tsam! A kirjinsa tamkar
Zai tsaga jikinsa, ya sanyata a ciki. Haka nan ya sami kansa
da kuka sosai, hawayensa na sauka a gadon bayanta, cikin kuka yake magana
"Afrah zuciyata ta yi nauyi, tabbas na so
na ba ki farin-cikin da ki ke bukata, na so na natsu, na koma mutum nagari
saboda soyayyarki, ke ta dabance
Afrah, ina sonki fiye da tunanin ki”,
Afrah ta runtse idanunta itama hawaye ya na fita mata gabanta na faduwa saboda ta ji kalmar da take fatan ji daga bakinsa, cikin sanyin murya tace “kana sona”, ya kara matseta a kirjinsa yace “ina sonki Afrah so na hakika”. Ta saki ajiyar zuciya tace “Ni ma na ina sonka yaya Musaddik , kuma zan iya zama
da kai a cikin kowane hali da yanayi."
Musaddik ya ce, "Kaunarki ita ce ta sa
na ke miki hangen kyakkyawar rayuwa a wani wajen, don
na san ba za ki yi farin-ciki tare da ni ba"
Ta girgiza kai tace “Ka yi kuskure, domin da kai kadai zan iya zama na
sami farin-ciki”.
Musaddik ya dagota yana kallon
fuskarta gami da goge hawayen da ke zuba mata yace
"Ba zan yi miki alkawarin zan daina duk
abinda na ke ba, amma zan yi Kokari na dainan ba

Page 178

tare da na yi miki alkawari ba”, ta lumshe idanunta gami da yin ajiyar
zuciya ta ce
"Allah ya tabbatar da hakan, Allah yasa zan kuma cigaba da yi maka addu’a “
Ya maida kanta ya kwantar a saman kirjinsa , yana cewa “Nagode Afrah Allah ya kara ba ki hakuri da juriyar zama da ni”
Ta kara dagowa ta zuba masa ido gami da gyara zamanta, sannan tace
'"Amma ina da shawara daya” ya saki
hannunta yana cigaba da kallonta yace
"Shawarar menene?”,
Ta dan dube shi fuska sake, sannan
tace “Me zai hana ka nemi aikin yi, ka na
da takardunka, tun daga Primary har
Masters, A yanzu ne za su yi maka amfani, sannan samun
aikinka zai rage abubuwa da dama, kuma hanya ce
ta samun natsuwarka, wannan zaman babu aiki, shi
ne musabbabin kara lalacewarka"
Ya kamo hannunta ya rike yana kallonta cikin wani murmushi wanda ya kara masa kyau, sannan yace “Wannan yana daya daga cikin maganar da na
ke son na yi da ke, bayan wannan maganar da mu kayi,saboda ina son na nemi shawararki, don
yanzu ba abinda zan yi ba tare da shawararki ba,
don na fahimci ban da kowa duniya, bayan ke da kawu mahnud da inna Halimata, domin sune silar samun ki a cikin rayuwata”.
Ta ji dadin maganarsa, ta yi murmushi
tace “To ya aka yi?" Ya gyara zamansa ya kwashe duk
yadda suka yi da Hajiya Hudah ya gaya
mata,ya cigaba da cewa “shi kansa mijin nata na fahimci yana matukar son
na karbi aikin, sai dai ina ganin kamar aikin yana da hatsari,
kuma ba zan sami lokacin kaina ba"
Afrah ta runtse idanunta cike da fara'a ta gyara zama, tabbas wannan Haj Hudah tana son ta taimaki musaddik sannan kuma irin wannan aikin irinsa yakamaci mutum irin Musaddik aikin da sam bazai sami lokacin kansa ba, balle ya samu lokacin da zai je ya aikata abinda bai dace ba. Don haka wannan aikin dole ta bashi karfin guiwar amsar aikin nan. Ta kara kallonsa tace
"Yaya Musaddik irin aikin nan shi ne ya dace da kai, domin in dai har da gaske kana son daina abinda kake yi, to ka karbi aikin nan domin rashin samun lokacin naka, shi zai sa ka nisanci
abokanka na banza, ya kuma nisantaka
da aikata halayen banza, tunda cikin jama'ar kirki za ka dinga

Page 179

shiga, dole ka dinga jin nauyin aikata abubuwan da suka sha bamban da nasu halayen”, ido kawai ya dora mata har ta cigaba da cewa “Duk da dai ba irin wannan aikin bane ya dace da kai, a matsayin ka na me masters, sai dai babu komai da babu gwara ba dadi, wannan din ma Allah yasa masa albarka”, ya kara murmusawa yace “Na fahimce ki, sai dai kuma ni banji natsuwa akan wannan aikin ba, amma tunda kin kawo wannan shawarar zan amshi aikin nata”, tayi murmushi sosai tace “Alhamdulillah “, ya matso kusa da ita sosai yace “sai dai duk da haka zan fara neman aiki da takarduna, zan nemi abokina murtala zan bashi takarduna ya cigaba da nemar min aiki, a duk kuma lokacin da na samu wani aikin zan aje ma Haj Hudah nata aikin “.
Afrah ta saki murmushi tace “Hakan ma ya yi yaya musaddik, Allah yasa
alheri “,

Ya sa hannayensa ya kara janyota ya rungumeta, yana jin soyayyarta har cikin bargonsa. A wannan daren dai zuciyoyinsu sun aminta da soyayyar juna, wanda wannan shine mataki na farko na samun cikar burin Afrah da Mallam Mahmud da inna Halima.
domin tabbas idan akwai soyayya komai zai zo da sauki.

Page 180

Washegari karfe biyu na rana Musaddik
yana gaban ofishin da Murtala ya koma,
tun bayan barinsa kamfanin Musaddik. Murtala Ya ji dadì ya kuma yi
murna da ganin ya cika da farincikin yadda Musaddik har ya yi tunanin
neman aikin yi. A zahiri sai yanzu ya fara sa ran shiryuwar
Musaddik, a dalilin auransa, abinda ya dade yana addu’ar tabbatarsa, domin tun barinsa aiki a kamfanin Musaddik ko haduwa ya daina yarda su yi, idan kuma ya gano shi daker, da zaran ya fara masa nasiha zasu rabu baram baram, daga bisani ma wata rana da yaje nemansa gida da kanta Haj kilishi ta fito ta yi masa gargadin kada ya kara zuwa neman Musaddik ya fita harkarsa. Tun daga lokacin ya ja baya da shi. Yau kuma sai gashi ya zo har inda yake. Cikin tsananin farinciki ya dubi Musaddik ya ce,
"'Na ji dadì kwarai, da tunanin ka ya
fara dawo maka. domin kullum addu’a ta kenan, saboda haka in sha Allahu zan yi iya kokarina wajen
nemar maka aiki, domin ba zan taba
mantawa da irin taimakon da ka yi min ba a lokacin da na ke
aiki a kamfaninka, ba ka daukeni ma'aikacinka ba,
ka daukeni aboki, kuma amini, kuma
kaddara da karayar arziki babu wanda ya gagara Allah ya jarabce shi “.
Musaddik ya jinjina kai, karo da dama
Kenan daya tuna irin daula da arziki da dimbin dukiyar
daya mallaka a baya, wanda babu takamaiman
takamaiman abinda zai iya fadì, na dalilin faruwar abinda ya farun .
Musaddik ya jinjina kai yace “Haka ne Murtala na gode kwarai da
gaske. Allah ya taimaka." Murtala ya ce,
yana kallonsa “Allah ya shirya mana kai ka dawo da irin rayuwarka ta asali”.
A hankali yace “Amin Murtala, na gode"

Dai-dai lokacin wayarsa ta dauki ruri da sauri ya tura hannu a aljihu ya dakko wayar, ya dubi number sosai ba shi da ita a cikin wayar, don haka ya dauka lokaci daya ya kara a kunnansa gami da yin sallama.

Daga can daya bangaren, cikin wata murya me cike da izza Alh yusuf sanda ya amsa sallamar lokaci daya ya kara da cewa, “Alh yusuf sanda ne ke magana”…….


Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 181

Musaddik ya yi saurin gyara zamansa ya ce, “Alhajin Allah,barka da rana”, cikin isa Alh yusuf sanda ya ja numfashi sannan yace “yauwa kana lafiya”, ya jinjina kai yace “lafiya lau,ina fatan dai lafiya domin ban yi zaton jin kiranka ba a wannan lokacin”, Alh yusuf sanda ya wani tamke fuska tamkar yana ganin musaddik, sannan ya maida bayansa ya kwantar a kujerar da yake kai,sannan
Yace “Na sami lambarka a wayar Hudah
ne,sannan na kiraka ne, domin na ji shawarar da ka yanke
akan aikin da Hudah ta ba ka, saboda ni
Jibi na ke sa ran komawa Paris, ba kuma na son na bar kasar ba tare da na Ji abinda ka yanke akai ba”, ya yi shuru kamar me jiran tsammani.

Musaddik cike da mamakin yadda ya ga
Alhaji Yusuf ya damu da lamarin aikin,
wanda shi a ganinsa bai ga dalili ba, ya dan waiwaya ya dubi murtala wanda shi ma shi yake kallo, sannan a hankali ya dauke kallonsa a kansa, gami sa muskutawa, wanda zuwa lokacin Alh yusuf sanda har hakurinsa ya gaza yace “kayi shuru, wannan fa dama ce a gareka wanda ba kowa yake samun irin damar ba”, Musaddik ya kara muskutawa, bai bari tunanin da yake yi ya sa shi canja shawara ba, yace
"Ba damuwa, na ji, na kuma amince zan yi aikin”.

Alhaji Yusuf sanda ya yi murmushi sosai tamkar wanda ya gama cika dukkan burinsa na duniya, ya lumshe ido ya bude ya kara baza babbar rigarsa a kan kujerar da yake zaune, lokaci daya yasa hannunsa daya yana shafa gemun da ya cika masa fuska.gami da
gyada kai sannan ya ce,
"To shi kenan, ina tayaka murna ,sai ka samu ka bullo zuwa
yamma, domin ka ji yadda tsarin akin yake" hakanan musaddik ya ji gaba daya guiwoyinsa sunyi sanyi, a sanyaye yace “To nagode in sha Allah zanyi kokarin zuwa anjiman”, Alh yusuf sanda ya riga shi aje wayar, cike da murmushi ya mike ya shiga shawagi a tsakiyar katon falon.

A yayin da Murtala ya dubi Musaddik sosai yace “Musaddik kai da waye a waya”, ya saki ajiyar zuciya yace
"Alhaji Yusuf Sanda ne Mai-gidan
Hajiya Hudah, ya kira ni ne akan aikin da na yi maka bayani dazu, dalilin da yasa ya kirani kenan, shi yasa na gaya masa na amince."
Murtala ya numfasa yana yi ma musaddik wani irin kallo me kama da kayi hankali,sannan ya ce
"A gaskiya ka yi taka-tsantsan! Kuma ni
na ma kasa gane wane irin miji ne Alhaji Yusuf Sanda,
wanda baya kishin matarsa, da har neman me kare
lafiyar matarsa yake a bayan idonsa, shi zaman me yake da bazai zama me kare lafiyarta din ba, musaddik bana jin nutsuwa akan aikin nan”.

Page 182

Musaddik ya dubi murtala ya ce,
"Ni kaina abin yana daure
min kai, ya damu kwarai da maganar aikin nan fiye da yadda Haj Hudah ta damu” murtala yace
"Koma dai menene, ka sani dole sai
ka natsu ka san abinda ka ke yi, saboda wanan aikin yana da hatsari “Ya ce,
“Hakane Murtala, na kuma gode da shawararka, zan kuma kula sosai”
Murtala ya ce "Ba don wannan wata babbar dama ce a gareka ba
na yin aiki a karkashin mace kamar
Haj Hudah Yar Majalisa, da nace ka yi hakuri ka jira asamu wani aikin , amma matsalar bansan iya wane lokaci za’a dauka ba’a sami aikin ba, kuma shi wannan aikin ko da ban san nawa ne
albashin da za ta yanka maka ba, na san za ka sami
damar wadata iyalinka, aikin kuma zai
sa ma maka daraja da kima”.

Musaddik yace “Tunanin da daga ni har Afrah mu kayi kenan yasa muka yanke shawarar karbar aikin , saboda ni a yanzu banda wani buri da ya wuce faranta ran matata “. Murtala ya gyada kai ya yi dariya sosai yace “Angon Afrah,Allah yasa haka shi yafi zama alheri abokina ka kula don Allah “, ya yi murmushi yace “ kada ka damu murtala zan kula”.

Daga nan su ka cigaba da tattaunawa har zuwa lokacin da Murtala ya
tashi aiki, daga nan suka dunguma tare suka fita, kowa ya yi na shi wajen domin tafiyar su ba zata zamo daya ba

Musaddik yana zaune a dabar shaye shayen su, yau dai ya dage kadan ya sha ya ki shan komai da yawa duk da har wani zafi zuciyarsa take masa don rashin shan komai yadda ya saba. Kallon abokan shashancin nasa yake yi can kasan zuciyarsa yana jin tsana da kyamatar halayensu, sau tari yakan zauna yana tunanin yadda wadannan mutanen su ka zama sune abokansa yanzun ma tunanin da yake yi kenan, wayar Alh Hamza ta shigo wayarsa, bai bata lokaci ba wajen daukar wayar, shi ma kuma bai wani ja magana ba ya sanar da shi ya shirya duk inda yake karfe biyar zai zo ya dakko shi bisa umarnin Alh yusuf sanda,
Toh kawai musaddik yace masa tare da gaya masa inda zai gan shi.sannan su kayi sallama, lokaci daya musaddik na cigaba da mamakin irin wannan kaguwa da Alh yusuf sanda yayi akan aikin da yasan bazai amfane shi da komai ba, shi ne kadai zai amfana da shi amma yadda yake nunawa tamkar shi ne zai amfana fiye da shi.

Wajen karfe biyar da rabi Alhaji Hamza
ya iso inda zasu hadu da musaddik ya dauke shi zuwa gidan
Hajiya Hudah. Gidan cike yake da jama’a masu neman taimako , su kam cikin alfarmarsu suka shiga cikin gidan har cikin katon falon da nanne Haj Hudah take zama da duk wani mutum me muhimmanci da ya zo wajenta. Yanzu ma tana zaune Ta sha kwalliya sai walkiya take yi,kyanta ya fito sosai
gafenta Alhaji Yusuf Sanda ne, shi ma ya ci shadda me tsada tamkar me shirin zuwa liyafa.
Hajiya Hudah ta rasa dalilin da ya sa
take rasa dukkan natsuwarta, a duk lokacin da Musaddik ke gabanta
Kuma ko mutane sun kai dubu, ta kan ga
Musaddik din ya bambanta da kowa, musamman wajen kwarjini, da cikar kyawu, shi din komai nasa na dabanne, hakan yasa take jin takaici idan Alh Hamza ya na nuna mata Musaddik wani wulakantacce ne, wanda baida wata kyakkyawar makoma.

Sun tattauna sosai akan aikin, Alh yusuf sanda yafi kowa zakewa shi ne kuma me fadin yadda aikin zai kasance , ido kawai musaddik yasa masa har ya gama fadan abinda yake so, a tunaninsa musaddik bazai kawo wata magana ba, ga mamakinsa sai ya ga Musaddik ya gyara zama ya fara kafa na shi sharudan.

Page 183

Cike da nuna shi ma yasan yancinsa yace “Da farko kun san dai ni magidanci ne ,matata na bukatata ako wane lokaci don haka babu wani aiki da zaisa na wafintar da iyalina, don haka maganar da kayi megida na awa goma sha takwas na awannin ranata zanyi su ne wajen kula da Haj bazai yuwu ba, awa goma sha daya kawai zan iya sadaukarwa daga karfe bakwai na safe zuwa karfe shida na yamma, daganan zan tashi na je na ga iyalina”.
Ya kara kallon Alh yusuf sanda da shi ma ya zuba masa ido, tunaninsa na musaddik sakaraine ya fara barin zuciyarsa.
Lokaci daya ya kara sauke idonsa kan matarsa, wacce ta dazu tamkar ta manta a inda take, domin yadda ta zubama musaddik ido bata ko kiftawa. Murmushi kawai ya yi gami da dauke kansa yana cigaba da girgiza kansa.
Musaddik ya cigaba da cewa “ sannan komai runtsi bazan dinga kwana a cikin gidanta ba,kuma duk wata tafiya idan ta kwana ce baza ni ba” ya dakata yana kallonsu yace “wannan sune sharudana idan kun amince shikenan ko gobe zan iya fara aiki,idan kuma baku amince ba sai a hakura”.

Da gangan Alh yusuf sanda ya yi shuru yana cigaba da nazarin yanayin Haj Hudah, so yake yasan abinda ta yanke a karan kanta,ita ko Zahiri Hajiya Hudah har cikin ranta tana matukar son
ganin Musaddik kusa da ita, domin ta rasa dalilin da yasa take jin wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali a duk lokacin da Musaddik ya kasance kusa da ita, ko wannan aikin ma ta dai
bukaci ya yi ne kawai, amma tana da
jami’an tsaronta masu bin ta duk inda zata je, bayan masu yin gadin gidanta.
don haka wannan sharadin na Musaddik, bai dameta ba, ba kuma zai hanata daukarsa aikin ba, Don
haka ba tare da wani dogon nazari ba ta yi saurin amincewa, wanda dama abinda Alh yusuf sanda yake tsammanin ji kenan daga gareta.

Zama kawai ya kara gyarawa yana cigaba da girgiza kafafunsa, sannan yace “Badamuwa musaddik duk sharudan da ka aje na yarda kamar yadda Hudah ta amince “.
Alh Hamza ya yi murmushi yace “Alhamdulillah musaddik ina tayaka murna, lalle ka shigo tafiyar nan da kafar dama”.
Haj Hudah ta dan waiwayi inda Alh yusuf sanda ke zaune, idonsa na kafe a kanta, ta dauke idonta ta dawo da shi kan musaddik tace
"Dama saboda na tabbatar da na yi
tafiya da kai a cikin siyasata, bayan na ci zabe, ya sa na ba ka
wannan aikin, saboda ka sami abinda
zaka dinga ciyar da iyalinka, ba tare da wahala ba, uwa uba ina son na tabbatar maka da cewa tafiyata tafiyace ta amana “, Musaddik ya jinjina kai yace “Hakane, nagode Allah ya kara girma”


Page 184

Alh yusuf sanda yace “ Sai ki gaya masa albashin sa”, Haj Hudah tayi murmushi ta kara kallon musaddik tace “Duk wata zan dinga biyanka naira dubu dari, ina fatan sun yi?”, Alh Hamza ya bude ido ya na mamaki, lalle musaddik ya haye, shi da yake wahala da ita tun da dadewa bai amfana da komai ba a duk wata, sai musaddik da ya shigo tafiyar jiya jiya, sai dinga tashi da dubu dari duk wata sannan ga wata irin daraja da yaga ya samu, ji ya yi wani abu me kama da hassada yana tsikarar zuciyarsa.
Musaddik shi

Please Login or Register in order to submit comment