Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

“Baka da sabulun wanka da wankin ne”, ya gyada kai alamar eh ba tare da ya yi magana ba tace “Amma ba ni nace ka dinga zuwa kana yin wanki ba,har cewa nayi ka dinga dakko wankin kana kawowa gidana ni zan dinga yi maka, irinku ba a wofintar da ku ajiiki ya kamata a dinga janku , na gaya maka duk damuwarka ka dinga zuwa kana gaya min” idanunsa cike da hawaye ya mike tsaye ya juya baya saboda baya son ta ga hawayensa ,
Yace cikin muryar kuka yana magana yana tafiya, “zan zo nayi wankin gobe inna”daga
nan ya yi sallama da ita ya fice daga gidan.

Page 16

Zuciyarsa cike da tunanin maganganun da suka
gama tattaunawa da Innarsa.washegari da yamma dawowar Afrah kenan daga
makarantar Islamiyya, tare suka jero da
Sayyadi Habibu, hira suke cike da annashuwa da
kaunar juna har zuwa kofar gidansu.
Anan suka tsaya, domin su yi sallama, dai-dai
lokacin Musaddik ya tsaya shi da dan acaba,
daga shi har wanda ya goyo shi, babu mai kyan
gani idanu jajir! "Ka jira ni yanzu zan fito"
Musaddik ya gaya ma abokin tafiyar ta sa,
sannan kai tsaye ya nufi cikin gidan, murya a
sanyaye Afrah ta gaida shi, ya amsa yana kallonta
"Afrah ya gidan?"
Ta ce "lafiya lau".
Mallam Habibu ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya shige cikin gidan, a yayinda Mallam
Habib ya dawo da
kallonsa ga Afrah, wacce duk fuskarta ta canja
ta shiga wani irin yanayi na damuwa, ya ce
"Afrah me ya faru ki ka canja fuska haka?”
Ta yi dan yake ta ce "Ba komai Ya Sayyadi."
ya gurgiza kai cike da kulawa yace “Hmmm! Da komai mana,
Afrah duk abinda ki ka ga ya faru da bawa, to
rubutacce ne akan allon kaddararsa, ko kadan
Kada ki sa damuwa akan lamarin Dan-uwanki,
bai kamata ba, domin addu' a kawai ita ce magani, ita ce kuma zata taimake shi

Page 17

Domin duk wanda Allah ya Batar, babu
wanda ya isa ya shiryar da shi, haka zalika duk
wanda ya shiryar, babu wanda ya isa ya batar
da shi. Idan ki na tuna haka, ba za ki taba samun
damuwa ba. Da ai ba haka yake ba, don haka a
yanzu ma wata kaddarar ce ta hau kansa, wacce sai an dage kwarai da addu’a”.
Afrah ta gyada kai cike da jindadin nasihar
malaminta, wanda hakan yana daya
daga cikin
dalilan da ya sa take matukar sonsa, ta ce,
“Naji ya Sayyadi, nagode kwarai da nasiharka,
na kuma yarda da duk abinda ka fada, sai dai ina rokon kai
ma ka dinga sa Dan-uwana cikin addu"arka da
bakinka me cike da ambaton Allah”
Ya yi murmushi ya ce "Zan sa shi a cikin
dukkan addu'oi ta Afrah. Allah ya shiryemu gaba
daya." Ta amsa "Amin, nagode",

Hayaniyar da Afrah ta jiyo tana tashi daga
cikin gidan, ya tilasta mata yin sallama da
Mallam Habib, domin ba ta son ya fahimci akwai
matsala a cikin gidan, bayan sun yi sallama. Da
sauri Afrah ta shige cikin gidan hankalinta
a tashe , muryar Mallam Mahmud cike da fusata yake cewa, “Na gaya miki ki yi shiru ko, Na’ima
dai ya ta ce, ina da damar da zan aura mata duk wanda na
ga dama ko da dan kashin kasuwa ne, karewar
lalacewa, ke wace ce da za ki dakatar da ni?"
Cewar Malam Mahmud da yake tsaye ransa a
matukar bace. Musaddik na tsugunne a gabansa.

Page 18

Mama Hauwa na dogare a jikin katanga, ta yi
zufa ta yi kasharban saboda tsabar masifa.
Afrah na shigowa ta jingina da jikin kofar dakinta,
idanunta sun cika da hawaye.
Don ta tsani damuwar da take gani a idanun
mahaifinta, kamar yadda ta tsani muzantar da ta
ga Musaddik ya yi a tsugunne. Mama Hauwa ta
ta ja tsaki tace “Duk abinda za ka fada, sai dai
Ka fada amma ba zan taba nade hannu na zauna nasa maku
ido kuna kokarin nakasa rayuwar 'yata ba, don
haka Musaddik ka tattara ka tafi.
Duk abinda Kawunka ya fada, ka watsar da
shi, don ba mai yiwuwa bane, zan kuma yi
mummunan saba maka matukar ka matsa sai ka
auri "yata, babu ruwan biri da gada, don haka
ina mai gargadin ka da ka dauki maganar da na ke gaya
maka, don ita ce hanya me bullewa a gareka.
Ka koma can gun tsohuwar matarka da ta
talautaka ta kuma gudu ta bar ka, bayan ka
zama abinda ka zama. Wacce ta sa ka zabeta, ka bar
Sakina, iya rashin kunya yau ina ganinta, to ba
dai Na'ima ba, ka kara gaba”.
Idanun Musaddik jawur! Ya dago ya dubi
Malam Mahmud ya ce
"Kawu na gode kwarai da niyyar da kayi
na kuma kara tabbatar da cewa ba ni da wanda ya fi ku kai da Inna Halima, domin wannan abinda kake son yi babu me yi min shi sai wanda ya ke matukar kaunata, don duk macen da zata iya aurena yanzu da kuma mahaifin da zai iya ba ni yarsa na aura to sai nasu karfin imani”

Ya maida bakincikin da yake yunkuro masa ya cigaba da cewa “ Duk abinda mama Hauwa ta fada gaskiya ne ban cancanci Na’ma ta aure ni ba , haka kuma ba ni da wata cancantar
daya kamata ace na sami mata me cikar kamala,

Page 19

bayan ni ba ni da wannan cikar kamalar, gaskiya
ne ko wace uwa tana bufatar farin-cikin 'yarta,
don haka Mama Hauwa ba ta da laifi don ta hangi rashin
farin-ciki ga "yarta bayan ta aureni".
Ya Kara kallonsa, bayan ya ajiye numfashi.
sannan ya ci-gaba da cewa,
"Saboda haka abar
wannan maganar, ni aure ma baya gaba na, kuma bazan boye maka ba bani da wani
sha'awar yin aure a yanzu, domin
babu yarinyar da na ke bukatar na cutar da rayuwarta
Zamana ba wani a karkashina ya fi min
kwanciyar hankali, don haka Kawu abar maganar nan kawai don Allah “
Kalamansa sun yi matukar ba Afrah tausayi,
nan da na hawayen da take kokarin mayarwa suka
suka balle a kumatun ta. Mama Hauwa ta dubi
Mallam Mahmud daya sandare a tsaye, komai ya tsaya masa
cak! Don bakin-ciki da damuwa. Mama Hauwa
Ta watso ma musaddik harara sannan ta dawo da kallonta ga Mallam Mahmud tace “To ka ji yaro, ashe akwai sauran tunani a
kansa, abin mamaki ma sai na ga yana neman
Yafi Kawun nasa zurfin tunani, domin duk abinda
ya fada gaskiya ne.
Don haka ya rage naka, kai ma ka'aje
makaman yakin naka, kai da kanwar taka da take zuga ka”.
Tana gama fadan hakan,
daga nan ta juya a fusace ta shige dakinta dai-
dai an fara kiran sallar magariba.

Page 20

Mallam Mahmud ya a saki ajiyar zuciya sannan shi ma ya durkusa
a gaban Musaddik yana kallonsa, ya dagoshi
gaba daya suka tashi tsaye, yana kallonsa ido cikin ido.
Musaddik ya ce "Kada ka sa ma kanka damuwa
Kawu, ka bar maganan nan, komai lalacewata,
ina da tabbacin ba zan rasa wacce za ta iya sona domin Allah ba”
Malam Mahmud ya girgiza kai ya ce.
Cikin matukar fusata, “Ina nan fa akan bakata, na riga na yi alkawarin sai na
aura maka ya ta ,a cikin wannan halin da ka ke
ciki kana bukatar kulawa ba daga bare ba, daga
Yar’uwa, don haka kada ka yi tunanin zan tashi
akan maganata, yanzu ka wuce ka yi alwala, mu
tafi masallaci mu yi sallar magariba, sannan ka
tafi gida, zan nemeka da kaina idan na gama
daidaita komai”
Da sauri Afrah ta goge hawayenta ta wuce da
sauri ta dauko buta guda biyu ta cikosu da ruwa
tazo ta aje, daya a gaban mahaifinta, daya a
gaban yayanta. Malam Mahmud ya dago ya zuba mata ido
a hankali ya ce "Sannu Afrah. Shi ma Musaddik
din kallonta kawai yake ba tare da ya ce mata
komai ba, ya ja butar ya fara alawala.duk da yasan akwai bashin salloli a kansa ba, amma baya son kawunsa ya fahimci hakan.’

Ita ma Afrah ta wuce a hankali zuwa dakinta,
kasancewar tana fashin sallah, hankalinta a
tashe yake tana matukar jin tsoron rayuwar,
duniya musamman idan ta tuna yadda Musaddik yake ada da yadda ya koma a yanzu.

Ku dakace ni

Yar gidan imam

Rashin yin comments tabbas zai iya sawa na bar yin wannan posting din.
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️


https://youtu.be/UxoBM6ImosM?si=SA_azT97toNTQa7P

Page 21

da yadda kuma mata ke kokuwar kawo kansu gare shi, amma yau saboda canjin yanayi
, mace daya da za ta so shi ta
zauna da shi, ya rasa.
Shi kansa Musaddik bai taba Bata lokaci ya
tsaya ya yi tunanin rayuwarsa da makomarta ba.
irin daran wannan rana, ya dade yana nemar ma
kansa amsar dalilin canjawar rayuwarsa, amma har
yanzu ya rasa amsa, da ba haka yake ba.
Babu kuma dalilin da zai sa ya koma haka a
yanzu, shin wace irin rubutacciyar kaddara ce
Allah ya rubuta masa? Sai dai duk da haka yana
addu’ar Allah ya ba shi ikon cinye wannan jarabawa.

Washegari tun hantsi Mama Hauwa ta kwashi jiki
zuwa gidan Inna Halima da kashedin ta fita
harkar ta da ita da 'yarta, anan ma Inna Halima
da Mama Hauwa sun kwashi 'yan kallo, don babu wanda ya
raga ma wani a tsakaninsu, kaca-kaca su ka yi
cikin diban albarka.
Mama Hauwa ta bar gidan Inna Halima, tana
komawa gida ta shirya Na'ima ta ba ta kudin mota
ta ce ta tafi can garinsu, wato Suleja, gidan
kakanninta ta zauna can, sai ta gama da lamarin
Malam Mahmud.
Sai ta tabbatar ya sauko daga maganganunsa,
sannan ta dawo, ai ko nan da nan Na'ima ta shirya
ta tafi abin ta, ba tare da Malam Mahmu* ya sani
ba.

Page 22

Har sai bayan ya dawo daga sallar Issha'i
Inna Halima ta zo ta gaya masa duk wulakanci
da diban albarkar da Mama Hauwa ta je ta yi mata har
gida. Kwarai da gaske ran Malam Mahmud idan
ya yi dubu ya baci, a fusace ya kira Mama
Hauwa ta fito, tana yamutse-yamutse ta dogare a tsaye ta ce
"Ga-ni menene?"
Malam Mahmud ya dubeta rai bace ya ce
"Wai ke Hauwa me ki ke nufi da ni ne, meye
matsalarki, shin Na'ima "yar ki ce ke kadai, don
me za ki tayar mana da hankali, kin hanamu sakat! dan kawai nayi nufin kulla alheri”
Ta yi karaf, ta katse shi ta ce
"Ka yi niyyar
Kulla sharri dai, kuma ba dai da
'Yata ba, banda
mugunta, ai ba Na'ima bace kadai 'yarka da ba ta yi aure ba
Don me ba za ka canja ba, sai ita, don ba ka
Kaunarta."
Ya jinjina kai ya ce
"Na ji, to meye ya
kai ki gidan Halima ki ka yi mata wulakanci?
Wannan abin ai tsakanina da ke ne, don me za ki
sa yar-uwata a ciki?" Ta ce cike da fusata
"Saboda na san duk kulle -kullenta ne wannan
saboda ba ta kaunata, shi ya sa take bakin-
ciki da kwanciyar hankali na, don haka ka
gargadeta ta fita harkata da 'ya'yana". Inna
Halima ta dubeta tace.
"'Kin ci sa'a a gaban yaya muke, duk abinda
za ki fada, ba zan iya maida miki a gabansa ba,

Page 23

don yana da daraja da kima a guna."
Ta tabe bak;
"Wannan ke ki ka sani kuma”
Malam Mahmud ya daka mata tsawa ya ce
"Ke Hauwa ba ruwanki da Halima kuma idan ki
Ka Kara taka gidanta, ki ka yi mata abinda bai kamata
ba, sai kin yi mamaki na, don ki sani, ba tsoranki
nake ji ba, kin kusa kai ni bango, ki fita a cikin
lamarina, kafin na yi miki abinda zakiyi mamaki”
shiru ta yi ta na cigaba da kumbure kumbure, Ya bude baki ya kwala ma Na'ima kira.
Mama Hauwa ta dube shi ta ce "Wace Na'imar?
na riga na turata inda ya kamata, ba kuma za ta
dawo ba har sai ka janye wannan mummunar maganar, daka tsiro da ita ana zaune lafiya”
'Malam Mahmud ya fiddo da idanu waje ya ce
"Ina ki ka turata ba tare da sanina ko izinina ba?"
Ta ce
' ta kara tamke fuska tace “Ba dole bane ka sani, izininka kuwa dama
ban nema ba, don na san ba zan samu ba, shi ya
sa nayi gaban kaina”, Mallam Mahmud cike da fushi yace “To shikenan ina son ki sani na ba ki daga wannan daran zuwa gobe, ki tabbatar
Na'ima ta dawo gidan nan, ko kuma ki tattara ki bi ta , domin bana bukatar ganinki a gidana matukar zansa doka ki ki bi banga amfanin kasancewarki mata ta ba”. Inna Halima tace
"A’a yaya kada ayi haka, ka
fita harkar Hauwa, don na lura tana jin dadin
ci ma mutane mutunci, ka bar ta, duniya ma ai makaranta ce, idan har wani abu zai samu dan wani na assha baki tausaya ba a matsayinki na uwa ba to ba na zaton akwai imani a tare da ke, musaddik kuma da ki ke kyamata ki sani shi ma ba shi ya tsarawa rayuwarsa haka ba, kin kuma fi kiwa sanin cewa da ba haka yake ba, idan baki tausaya masa ba bai kamata ki dinga nuna masa irin wannan tsanar ba”
Mama Hauwa ta ce "Kada ma ya bar ni, ba
kuma za ta dawo ba, ni ma ba inda zan je, zama
daram! Idan kuma neman kwanciyar hankali ku
Ke yi to ku janye batun auren nan, shine kawai maslaha, kuma naganar kyamata na kyamace shin meye abin so a gun sa”

Page 24

Daga nan ta juya fuuu! Ta shige dakinta
gami da rufe kofa.
Inna Halima ta juyo tana kallonsa ta ce "Yaya
ina ganin maganar Na'ima a bar ta, saboda
abinda muke kwadayi, ba za mu samu ba, hakuri
da juriyar zama da Musaddik ba za ta iya ba, ko
mun tursasa an yi, to ba za mu samu hadin kanta ba balle
ta ba mu gudunmuwar dawo da rayuwarsa kan
hanya, tunda ba ta so, mahaifiyarta ma ba ta so.
Domin tashin hankalin Hauwa ma kadai, ya
isa ya hana su zaman .lafiya da kwanciyar hankali,
koda ita ma Na'imar tana so.
Balle bisa dukkan alamu ya nuna tana tare da
mahaifiyarta, tunda har suka iya shirya ta gudu.
Allah ya ga tunanin mu, ya kuma ga niyyar mu.
Allah ya ba mu ladan niyya, shi kuma Musaddik
Allah ya kawo sanadiyyar shiryuwarsa, ko da ba
ta dalilin auren ba, domin ko anyi auren sai dai ya kara jefa musaddik cikin wani kangin”.
Malam Mahmud ya saki ajiyar zuciya ya ce
"Kai babu wata jarabta ga da namiji irin rashin
sa'ar mata ta-gari, shi ya sa ba zan taba mantawa da
marigayiya ba, wacce ta so-ni, ta yi min biyayya
har me rabawa ta rabamu, na yi kwadayin ace ita ce
ta cika min gida na da 'ya*ya kafin rasuwarta,
amma duk da haka na san tà bar min daya
tamkar da dubu wato Afrah"
Inna Halima ta gyada kai ta ce "Haka ne,
Allah dai ya jikanta, yasa ta huta, tabbas kayi rashin mata” ta karasa magana fuskarta cike da jimami, tana tuna irin zaman arzikin da sukayi da mahaifiyar Afrah.
.Mallam Mahmud Ya ture hularsa keya ya ce

Page 25

"Amin, kuma ina nan akan bakana na hada
Musaddik da 'yata aure” Inna Halima ta dube
shi sosai tace “Amma ta yaya, ina za mu iya da tashin hankalin Hauwa, bayan faruwar komai ba ni gaba daya al’amarin ya fita kaina, domin na hango fitina acikin auren nan har garama kada ayi “Mallam Mahmud ya jinjina kai yace “ Na fahimci duk abinda kike nufi na kuma gamsu amma babu komai, akwai wata
mafitar da na fara hangowa, bayan maganganun da Hauwa tayi yanzu na hango wata mafitar, ki tashi ki tafi gida
dare ya yi sosai, zuwa jibi idan na gama tunani zan neme ki”
Ta jinjina kai, ta ce "To Allah ya kai mu, ya
kuma kara maka hakuri da juriya akan zama da
Hauwa". Ya ce "Amin Halima”
Daga nan ta tashi
ta yi masa sallama ta leka dakin Afrah wacce
duk abinda ke faruwa tana zaune akan katifarta
tana jinsu, nan ma sallama ta yi da Afrah.
Sannan ta wuce zuwa gida, zuciyarta cike da
tsanar Mama Hauwa da jin haushinta.

Page 26

Yau alhamis ba makarantar Islamiyya, tun safe
Afrah ta kwashe wankin mahaifinta ta wankesu
tsaf? Ta shanya; sannan ta shiga dakinsa ta
gyara Kamar yadda ta saba duk ranar alhamis,
haka zalika duk wani aikin gida, babu wanda
Mama Hauwa ba ta, ba ta ba, duk kuma ta yi ta
gama har zuwa yanzu da ta hada wutar guga ta
goge kayan mahaifinta Ta kammala kenan, ta kwasa za ta kai masa
daki, ya dawo, ya shigo yana kallonta dauke da
kaya ya ce "Afrah, yanzu bayan wanki har guga
Ki ka sami damar yi min, bayan aikin da na fita
na bar ki da shi a gaba?" Ta yi murmushi ta ce
"Eh Baba,
ai har ma na gama, sannu da zuwa" cike da kauna yace “ Yauwa Allah miki albarka, Allah yasa ki gama da duniya lafiya, Allah ya baki kema masu jin kan ki, masu taimakon ki yadda ki ke taimako na”. Cike da jindadin addu’ar tace “Amun Baba”
Daga can nesa inda Mama Hauwa ke zaune
ta saki tsaki ta ce “ Ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta”, wani irin mugun kallo ya sakar mata sannan ya wuce dakinsa ba tare da ya tanka mata ba, don maganar gaskiya haushi take ba shi ba ta ko son kallonta.
"Ayi dai mu gani."
Ya yi mata wani irin
Ita ma Afrah ta bi bayansa dauke da kayan
a hannunta.
Tana shiga dakin ta tarar da Malam Mahmud
zaune akan kujerar da ita kadai ce a dakin, ya yi
tagumi hannu biyu fuskarsa dauke da
matsananciyar damuwa, bayan ta aje kayan ne,inda ta saba ajewa ta shiryasu, sannan ta

Page 27

juyo ta dora masa ido, zuciyarta ta dagule ta
shiga damuwa, domin gain mahaifinta cikin damuwa.
Tana matukar so ta zauna su tattauna
damuwarsa, amma ba ta da yadda za ta yi,
domin bai nemi hakan daga gareta ba, ta juya a
hankali zata fita, har ta kai kofar dakin, zuciyarta cike da addu’ar Allah yasa ya kirata domin su tattauna damuwarsa, ta ji muryar mahaifinta ta
dakatar da ita daga fita, ta hanyar kiran sunanta, ta
amsa da sauri, lokaci daya ta dawo ta durkusa a
gabansa ta ce "Ga-ni Baba”
Malam Mahmud ya dawo da kallonsa gareta,
ya fara magana. "Afrah ina cikin wani hali na
tsaka mai wuya, na daukar ma kaina alkawarin da na ke
neman na gaza a kansa, na shiga wani hali da
banda wani zabi da ya wuce na roke ki a matsayinki na
wacce na ke tunanin tana da maganin matsalata."
Ya dan numfasa, sannan ya ci-gaba da cewa
"Musaddik Dan-uwanki ne, idan rayuwarsa ta
gyaru, na yi imanin za ki zama daya daga cikin
masu jin dadì, ko kadan ba ni da nufin kara ma
rayuwarki damuwa, saboda maraicin ki da kuma
irin hannun rikon da ki ka taso.
Hakan ya sa na ke miki kwadayin samun miji
na-gari wanda zai taimakeki, wanda zai rikeki da
mutunci, wanda kuma za ki sami dukkan gata daga gare shi
Shi ya sa ban yi tunanin hadaki aure da
Musaddik ba, don na san duk abinda na lissafa,

Page 28
ba za ki taba samu daga Musaddik ba, shi ya sa
na yi tunanin hada shi da "Yar-uwarki Na'ima.”
Ya numfasa gami da gyara zamansa, ya
kurama fuskar Afrah ido
wacce take tsugunne, banda
faduwar gaba ba abinda take yi, ya ci-gaba da
cewa “Ba sai na gaya miki matsalar da na ke
fuskanta daga Hauwa ba
Tunda na furta maganar hada auran nasu,
domin na san kin ji, kin kuma ga irin cin mutuncin
da Hauwa ke min, karshe ma ta dauke Na'ima ta
boyeta, ban san inda ta kai ta ba.
Don haka Afrah ina rokonki da hannaye na
biyu, ki taimakeni ki share min hawaye, ki sadaukar
da farin-cikinki saboda farin-ciki na, ki yi min
biyayya kamar yadda ki ka saba, ki amince ki
auri Musaddik don Allah...
Da sauri Afrah ta dakatar da shi "Don Allah
Baba ka daina rokona, wace ce ni da har sai ka
rokeni, don na yi maka biyayya, duk irin so da
kauna da ka nuna min ace sai ka rokeni don
kawai za ka aura min Dan-uwana.
Har kullum ina fatan Allah ya kawo ranar da
za ka nemi wani abu daga gareni, domin ba ni da
abinda zan saka maka ko na biyaka daga irin rikon da ka yi min “
Ta yi kokarin maida hawayen daya cika mata
ido, sannan ta ci-gaba da cewa "Saboda
haka zan sadaukar da farin-ciki na, kamar yadda ka

Page 29
bukata, zan auri Yaya Musaddik, zan kula da shi
tare da kokarin sanya shi a hanya madaidaiciya
Allah kuma ya shirya shi."
Son Afrah tare da tausayinta ya kara kama
Malam Mahmud, a yayin da farin-ciki ya cika
zuciyarsa, amma daya kalli cikin idanun Afrah,
sai ya ji wani bakin-ciki ya kama shi, domin duk
yadda Afrah ta so ta Boye damuwarta, to ba za
6oye ma Malam Mahmud ba, hakika bai hango
son Musaddik ko son auransa a kwayar idanunta ba.
Abinda ya hango daya ne, shi ne tsantsar
biyayya da kaunar faranta ransa, ya nisa gami
jinjina kansa sannan ya ce.
"Ki yi hakuri Afrah, ba haka na so rayuwar
ta tafi ba. Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki
'ya"ya masu jinkanki, Allah kuma ya albarkaci
abinda zai shigo rayuwarki. Allah ya juya wannan
al'amari ya kasance alheri a gareki, da mu ba ki
daya, domin Allah ya ga kyakkyawar niyyar mu
akan wannan auran, na gode, na gode"
Afrah ta dan yi murmushi ta ce “ Baba kana
sa ni jin nauyi, idan ka na min godiya, don Allah
Ka daina min godiya". Ya gyada kai cike da kauna yace “Allah ya yi miki albarka Afrah
tashi ki tafi.”.
' A hankali ta mike ta fita, gabanta na cigaba da
matsanancin faduwa.
Tana shiga dakinta ta fada kan katifarta,kuka
take riris Komai ya kwance mata, meke shirin
faruwa da ita? Ko a mafarki ba ta taba kwatanta

Page 30

Musaddik a matsayin mijin aurenta ba, shin me
kaddara ta tanadar mata? Zama da mutum irin
Musaddik wanda bai ma san inda rayuwarsa tasa gaba ba.
Wanda bai san yadda zai tarbiyantar da ita ba sai dai ita ta tarbiyyar da shi, ko
kadan ba irin Musaddik bane mijin da take
kwadayin zama a karkashinsa. Ya Sayyadi Habib
shine wanda ta horar ma da zuciyarta kaunarsa,
take kuma kwadaita ma kanta auransa.
Domin tana da tabbacin shine wanda zai yi
mata jagora har gidan aljanna, sai dai kash! Ba
ta so yadda labarin ya tsaya ba, ba ta so karshen labarin ya zama haka ba.
Domin kuwa ko ta ki ko ta so soyayyarta da
Ya Sayyadi ta zama tarihi daga lokacin da
mahaifinta ya umarceta da auran Musaddik, tabbas!
Za ta yi ma mahaifinta biyayya, koda hakan zai
zama sanadiyyar fadawarta mummunar rayuwa,
domin duk duniya ba ta da kamar mahaifinta.
Ba ta tunanin akwai abinda zai bukata ta yi
masa, matukar tana da halin yi masa ta kasa yi,
don haka za ta iya sadaukar da komai nata, domin
samun farin-cikin mahaifinta, tunda Allah ya
taimaketa ta samu ta yi rayuwa da shi, dole ta
lallaba ta samu albarkansa, tunda Allah bai kaddari
za ta yi rayuwa da mahaifiyarta ba.
Ta sa hannu ta goge hawayen da ke malala a
saman kumatunta, ko kadan babu soyayyar Yaya Musaddik a cikin zuciyarta.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam ✍️

Kuyi comments da ra’ayiyun ku rashin yin comments zai iya sa wa na daina posting
MUSABBI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 31

sai dai acan karkashin zuciyarta akwai tsantsar tausayinsa, gefe daya kuma
tana tausayin kanta da Ya Sayyadinta na yadda
za su rabu da junansu, domin Allah bai rubuta
shi ne mijinta ba a allon kaddarar su, ta kara goge hawayenta.
Sannan ta yunkura ta tashi ta tura kofar
dakinta, domin ta ji dadin yin kukanta, sannan ta
dawo ta kure karshen katifa ta ci-gaba da rasgar
kuka,; domin tana ganin hakan ne kawai zai
sassauta mata radadin da take ji a cikin zuciyarta.
Haka Afrah ta kasance cikin rashin sukuni a
wannan ranar, har zuwa idar da sallar Issha'i, tun
bayan idar da sallar, tana zaune akan sallaya da
casbaha a hannu tana lazimi, lokaci daya ta kan
yi kokarin goge hawayen da ke fita mata da daya
hannun.
Tana jin dawowar mahaifinta daga masallaci,
bai dade da shigowa ba, kuma ta ji sallamar Inna
Halima,
haka nan Afrah ta tsinci kanta cikin
matsananciyar faduwar gaba.
An dau tsawon lokaci kafin ta ji muryar
Malam Mahmud, ya kwala mata kira. A daburce
ta amsa da sauri, ta tashi ta aje carbin, sannan
ta fice kai tsaye dakin mahaifinta ta nufa.
•Mama Hauwa da ke zaune a kofar dakinta ta
rakata da kallo har ta shige dakin, sannan ta saki
tsaki ta tashi ta dauki kujerarta 'yar tsugunne ta

Page 32
shige daki tana fadin "Halima uwar kinibibi, sai
dai ya Kare a kanku ba dai 'yata ba”, a fili take fadan maganar cike da zafin rai.
Cikin sallama Afrah ta shiga dakin, ta yi
Kokarin boye dukkan damuwarta, ta nufi inda
Inna Halima ke zaune, ta zauna kusa da ita. "Inna sannu da zuwa”
Ta amsa tana yi mata wani kallo me cike da
Kauna da tausayi, ta fara magana "Afrah ban
Yarda da hukuncin da mahaifinki ya yanke ba a
Kan aurar dake ga Musaddik. Afrah ke marainiya
ce ina matukar tausayin rayuwarki, miji irin Musaddik bai
kamace ki ba, gara kawai an hakura mu ci-gaba
da yi masa addu'a."
Afrah ta yi

Please Login or Register in order to submit comment