Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗakin ya bayyana a fili.
Marganu yayi arba da Firziyya zaune tana ta kuka. Tunda aka fara wannan gumurzu bata taɓa kawo Marganu ne yazo cetonta ba. Saboda ita a tunaninta Marganu ya daɗe da mutuwa.
Ƙamshin jikin Marganu yana dukan hancinta ta ɗago kanta a gaggauce.
Ai kuwa sai tayi arba da abinda ko a mafarki bata taɓa tunanin zai sake dawowa gareta ba.
Marganu yayi tsayuwa irinta manyan jarumai, idanuwansa tsaye cak akan Firziyya, yana mai tsananin tausayinta bisa wannan hali da ta shiga saboda shi.
Marganu ya buɗe hannuwansa ya ce, "Taho gare ni, ya masoyiyata!"
Firziyya tana jin haka ta ruga da gudu kan Marganu tamkar babu abinda ke damunta. Buƙatarta kawai ita ce ta tabbatar da abinda take gani.
Shin gizo Marganu yake yi mata ko kuma mafarki.
Bisa mamaki jikinta yana haɗuwa da nasa, taji ɗumin jikinsa wanda ya tabbatar mata da cewa, wannan abu dake faruwa gaskiya ne ba mafarki ba.
Firziyya ta yiwa Ubangiji godiya da ya dawo mata da masoyinta a lokacin da take tsananin buƙatarsa.
Marganu yayi amfani da takobinsa ta haske ya ruguje wannan gidan kurkuku gaba ɗayanta. Iya wannan ɗaki da aka kulle Firziyya kawai ya bari, ya zamo tamkar kabarin mahaifinsa.
Marganu ya kama hannun Firziyya suka sauƙo daga saman wannan tsauni, sannan ya bata dokinsa ta hau suka juya suka tafi. Shi yana tafe bisa ƙafafunsa.
*****
Yau *01/05/20023*
Babi na gaba zaizo *03/05/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 119: *Dama ta biyu*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U-M-S
*
~Dajin Lardik, birnin Faizara.
*
Mutanen guda uku a tafe suke cikin sassarfa sun tunkari wani ƙaton tsauni da suke hangowa a can cikin ƙungurmin daji.
Wanda ke tsaye a gefen dama, murjejen ƙato ne baƙin-fata wanda yayi askin ƙwal-kobo. Wanda ke tsaye a ɓangaren hagu kuwa, wani dattijon mutum ne mai yawan gemu da dogon gashi.
Wani mutum ne dogo mai manya-manyan gaɓɓai da murɗaɗɗen jiki, tsaye a tsakiyar waɗannan mutane.
Lokaci-lokaci ƙamshin sarauta da sadaukantaka yana tashi a jikin wannan mutumi wanda ke tsaye a tsakiya.
To, amma idan muka sami dama kaɗan muka ƙarewa fuskar wannan mutumi kallo zamu gano cewa, ba wani bane illa Sarki Kuffuru.
Mutum zai cika da tsananin mamaki idan ya kalli sarki Kuffuru a wannan waje. Saboda idan aka yi duba duk cikin SADAUKAI-UKU 'yan baiwa, babu wanda ya kai sarki Kuffuru burin kamo Barban.
Saboda wanne dalili zai rabu dasu sarauniya Rauziyya da sarki Darwazu ya taho wannan waje?
Idan ka duba wannan sadauki baƙar-fata dake tsaye a hannun daman sarki Kuffuru, babu abinda zai fara faɗo maka a rai kamar kurkukun-mutuwa wadda aka taɓa ganawa Marganu azabobi a cikinta.
Wannan kurkuku wadda sarauniya Rauziyya da sarki Kuffuru suka gwabza yaƙi a cikinta a shekarun baya, har sarauniya Rauziyya ta fusata ta ruguje ta.
Mun ji cewa ta ruguza wannan kurkuku amma bamu ji halin da sauran dakarun kurkukun suka shiga ba.
Wannan sadauki wanda ke tsaye a gefen sarki Kuffuru, ba wani bane illa SADAUKI ZAYYADU ƊAN GUNDAS - Shugaban dakaru masu tsaron kurkukun mutuwa.
Wannan dattijon mutumi kuwa, kallon farko zaka yi masa ka gane cewa hatsabibin boka ne.
Zaka ga furfura ta lulluɓe ko'ina da ina na gashin kansa, kai hatta gashin bakinsa da gemunsa wannan furfura bata bari ba.
A waje ɗaya ne kawai muka taɓa arba da wannan boka. Lokacin da ya kira sarki Darwazu wajensa, sa'adda Barban da Aymanul Faris suka shiga birnin Askandariyya suka saci farin lu'u-lu'u.
Wannan boka shi ne, boka Balwaz babban bokan da sarki Darwazu ya yarda dashi.
To, mene ne dalilin da zai sa sarki Kuffuru ya baro ɓangaren su Rauziyya yazo ya haɗa kai da waɗannan mutane guda biyu?
Sannan wannan tafiya da suke a cikin daji, ina zasu je?
Sarki Kuffuru ya dubi boka Balwaz ya ce, "Amma akwai tabbacin cewa, sarki Fairaz ɗan ƙabuilar Adbenchan ne?"
Boka Balwaz ya girgiza kai ya ce, "Babu tabbas! Dole sai mun je na gudanar da bincike akansa kuwa."
Sarki Kuffuru ya gyaɗa kai suka ci gaba da tafiya.
Bayan dogon lokaci suka kewayo ta bayan wannan dogon tsauni da suke hangowa daga nesa. Abin mamaki sai ga ganuwar wani ƙaton birni ta bayyana a nesa dasu kaɗan.
Cikin gaggawa suka ƙara sauri suka iso ƙofar shiga wannan birni.
Gaba ɗaya wannan yanki babu wani birni ko ƙaramin gari kusa da wannan birni wanda suka zo ƙofar shigarsa. Shi daya ne tal a cikin baƙin daji.
Saboda haka wannan birni baya samun baƙi sosai, don sai a shekara babu baƙon da yazo.
Don haka masu tsaron ƙofar shiga wannan birni, basu da wani tsauri sosai.
Dakaru ne guda sha-biyu kacal! dukkansu suna zazzaune a gindin bishiya suna hutawa.
Kasancewar babu aiki sosai, yasa waɗannan dakaru suke shiga daji wataran su yiwo farauta.
A wannan lokaci ma, ga dukkan alamu daga farauta suka dawo saboda ga barewa an tsire tana gasuwa a gabansu.
Koda dakarun suka hango su sarki Kuffuru, sai suka zaro makaman yaƙinsu, cikin gaggawa suka rugo suka kewaye su sarki Kuffuru.
Sarki Kuffuru ya daka musu tsawa, dukkansu suka ja baya, ya nuna ɗaya daga cikinsu ya ce, "Kaje wajen sarkinku, ka ce masa sarki Kuffuru yazo ƙofar shiga birninsa yana jiransa!"
Cikin badakaren na karkarwa ya kama dokinsa ya hau, sannan ya shige cikin birnin.
Sarki Kuffuru da su Zayyadu suka koma gindin wannan bishiya suka zauna. Sarki Kuffuru yasa wuƙarsa ya yanko naman wannan barewa ya fara ci.
Zayyadu yayi koyi dashi. Dama sun daɗe basu ci nama ba, kasancewar tafiyar da suke ta gaggawa ce yasa basa tsayawa a daji suyi farauta. Iya abinda suke ci abincin guzurinsu ne.
Jim kaɗan suka jiwo ƙarar busa algaitu, suna ɗaga kawunansu suka hango kekunan doki masu kyawun gaske guda biyu.
Sarki Fairaz suka ga ya fito daga cikin ɗaya daga cikin kekunan dokin ya ruga gaban sarki Kuffuru ya kwashi gaisuwa.
Tunda sarki Fairaz ya fito daga cikin keken dokin, sarki Kuffuru ya ƙura masa idanu yana nazarinsa.
Bayan sarki Fairaz ya gama gaisuwa a gaban sarki Kuffuru saiya miƙe tsaye ya yiwa su sarki Kuffuru umarnin shiga cikin wadannan kekunan doki.
Boka Balwaz da sadauki Zayyadu suka shiga cikin keken doki guda, shi kuwa sarki Kuffuru da sarki Fairaz suka shiga cikin guda.
Nan take masu tuƙa kekunan dawakan suka juya su, suka tunkari cikin gari.
Bayan sarki Kuffuru da sarki Fairaz sun sake gaisawa, sarki Kuffuru ya dubi sarki Fairaz ya ce, "Ya ya waɗannan sarakuna guda tamanin da uku suke?"
Sarki Fairaz ya ce, "Suna nan lafiya, wata guda da ta shuɗe ne muka sake zama dasu, na tabbatar musu da cewa, ka karɓi wannan aiki na kamo Barban...
"Dukkansu sun yi farin ciki, kuma sun tabbatar min da cewa, har yanzu suna kan bakarsu - indai ka kamo Barban zasu yi maka mubaya'a.
"Kwanan nan ne, nake tunanin zuwa wajenka domin na tambaye ka halin da ake ciki?"
Sarki Kuffuru yayi murmushi ya dafa kafaɗar Fairaz ya ce, "Wannan aiki da ka kawo min, baya buƙatar gaggawa. Saboda mutumin da zamu tunkara yafi kowa haɗari a duniya.
"Dole akwai buƙatar mutum yayi gagarumin shiri wanda yafi na wannan ɓarawo."
Sarki Kuffuru na zuwa nan a zancensa ya fiddo waɗansu takardu guda biyu daga cikin aljihunsa masu tsananin kauri.
Sarki Kuffuru ya warware ɗaya daga cikinsu ya nunawa sarki Fairaz ginin wata kurkuku guda ɗaya wadda aka gina a tsakiyar wani ƙaton daji.
"Wannan ita ce kurkukun da muka gina domin kulle sarkin-ɓarayin duniya Barban a ciki. Ya ɗauke mu lokaci mai tsaho kafun mu gano inda zamu samu tubalin da zamu gina wannan kurkuku.
"Kuma anyi asarar rayuka masu yawan gaske, a ƙoƙarin samo wannan tubali."
Sarki Fairaz yana jin haka ya risina a gaban Kuffuru ya ce, "Aikinka yana kyau, ya shugabana. Shin mene ne sirrin wannan kurkuku?"
Kuffuru ya sake yin murmushi ya ce, "Duk duniya babu kurkukun da za'a kulle sarkin ɓarayin duniya a zauna lafiya, idan ba wannan kurkuku da muka gina ba.
"Saboda babu abinda zaiyi tasiri wannan kurkuku. Komai ƙarfin mutum da hatsabibancinsa sai dai yayi haƙuri."
Sarki Fairaz ya ce, "Ya shugabana, ko zan iya sanin dalilin da yasa kazo ƙasata, alhalin a duk inda kake, indai ka umarce ni da zuwa zanzo?"
Sarki Kuffuru ya sake yin murmushi a karo na uku ya ce, "Bayani ne mai tsaho. Sai mun zauna tukunna."
A daidai lokacin ne aka tsayar da waɗannan kekunan dawakai, sarki Fairaz dasu sarki Kuffuru suka fito daga cikinsu.
Sarki Fairaz yasa aka kaisu masauƙi mai kyau, aka basu komai da suke buƙata.
Daga wannan lokaci bai sake nemansu ba, sai bayan kwanaki biyu.
Tunda safe sarki Fairaz da kansa ya tunkari wannan gida wanda aka sauƙe su sarki Kuffuru a cikinsa.
Yana shigowa cikin gidan, ya fuskanci cewa, a wannan lokaci ne suka gama cin abincin safe.
Sarki Fairaz yazo ya zauna akan wata kujera gefen waɗanda suke zaune akai, suka fuskanci juna.
Bayan sun gama yiwa juna barka da kwana, sarki Fairaz ya sake tambayar sarki Kuffuru dalilin zuwansu ƙasarsa?
Sarki Kuffuru yana jin haka ya dubi Balwaz ya gyaɗa masa kai.
Boka Balwaz ya dubi Fairaz da Zayyadu sannan ya fara yi musu bayani.
"Ina so ku sani cewa, damar da muke da ta kamo Barban ko Hodon guda biyu ne kacal!
"Dama ta farko tana buƙatar abubuwa guda uku, idan ana so a kammala ta.
"Abu na farko shi ne SADAUKAI-UKU 'yan baiwa. Abu na biyu gina wannan gidan kurkuku wadda Kuffuru ya nuna muku. Abu na uku shi ne hallaka aljani Ranganu, aljanin dake taimakawa Barban.
"Kowa ya san haɗa SADAUKAI-UKU 'yan baiwa da gina wannan kurkuku, ba wani abu ne mai wahala ba. Amma hallaka aljani Ranganu yafi komai tashin hankali.
"Ina so ku sani cewa, duk duniya babu mahaluƙin da yafi Ranganu ƙarfin sihirin tsafi.
"Ance shi tsafi gadon gidansu, ba wai koya yayi kamar kowa ba. Sannan baban Ranganu yana daga cikin aljanun farko da suka ƙirƙiro ɗalasimai.
"Saboda wannan dalili, duk wani motsin da ake yi na kamo Barban. Tun daga farko har ƙarshe aljani Ranganu yana gani, kuma ya sani.
"Ta ya ya kuke tunanin hatsabibin aljani kamar Ranganu zai san cewa, ana shirye-shiryen kashe shi sannan yayi shuru?
"Wannan yasa sa'adda naga su sarki Kuffuru sun gama gina wannan kurkuku, naje na same shi da kaina muka tattauna. Na nuna masa illolin dama ta farko da kuma abubuwan da zasu faru har ta kaimu ga rashin nasara.
"Sarki Kuffuru ya fahimci bayanaina sosai, sannan ya amince da abinda nazo masa da shi.
"Kuffuru bai nuna ya rabu dasu Rauziyya ba, mutum-mutumi mai tsananin kama dashi ya bar musu.
"A halin yanzu in banda ɓatan basira da rashin hankali irin nasu, birnin Jai'zin suke tunkara fa wai zasu yaƙi aljani Ranganu acan.
"Ya ya kuke tunanin zasuje gidan matsafin da yafi kowa tsafi a duniya, sannan su hallaka shi?"
Zayyadu da Fairaz suka ce, wannan abu ba zai taɓa yiwuwa ba!
Balwaz yayi murmushi ya ce, "Wannan shiyasa nace muyi amfani da 'DAMA TA BIYU' amma kafun nan, ina so kowanne daga cikinku yayi min bayanin kansa, ƙabilarsa da abinda yafi ƙwarewa akai."
Zayyadu ya yi caraf ya ce, "Suna na Zayyadu ɗan Gundas. Ban san ainihin ƙabilata ba, kasancewar a hannun ƙabilar Edwan na girma nayi wayo, saboda a da can ni bawansu ne. Wani attajiri ne ya sayo ni, ya kawo ni ƙasar Kufa sarki Kuffuru ya saye ni, yayi min muƙamin shugaban kurkukunsa.
"Abubuwan da na ƙware akansu abu biyu ne: Abu na farko shi ne ina da ilimi akan taswira sosai kasancewar a hannun sarauniya Rauziyya na girma. Abu na biyu ina da baiwar ƙarfin damtse fiye da tunanin mutum."
Boka Balwaz da sarki Kuffuru suna jin batun Zayyadu, suka dubi juna cikin tsananin al'ajabi.
Boka Balwaz yana mai tsananin mamakin irin shirin sarki Kuffuru da yayi tanadin mutum haka.
Sarki Fairaz yayi shuru kamar yana tsoro yayi magana akan asalinsa da kuma baiwarsa. Daga can ya dubi boka Balwaz ya ce.
"Shin ina da wani amfani a cikin wannan aiki da zaku je na kamo Barban ne? Ai babu buƙatar nayi bayanin kaina, tunda ba da ni za'aje ba..."
Boka Balwaz ya dube shi ya ce, "Ba haka bane. A halin yanzu zaka iya cewa, tawagar SADAUKAI-UKU ta daɗe da rugujewa. Saboda wannan mutum-mutumi dake wajen su sarki Darwazu hoto ne kawai. Baida baiwa da hikimomi irin na asalin sarki Kuffuru.
"Zayyadu zai iya maye mana gurbin sarauniya Rauziyya saboda yana da irin baiwarta ta sanin taswira. Amma bamu san wanda zai maye mana gurbin sarki Darwazu ba.
"Duba da yanayin gashin kanka da kuma kalar ƙwayar idanunka, shin kana da nasaba da 'yan ƙabilar Adbenchan ne?"
Sarki Fairaz yana jin wannan tambaya jikinsa yayi sanyi. Fairaz baida burin da yafi ya sake komawa matarsa a matsayin mijinta, saboda tun sa'adda Barban ya sace masa sarƙoƙin-zinarinta bai sake kusantarta ba.
Ya ziyarci bokaye har ya gaji bai sami abun kamawa ba, bisa dole ya haƙura. Boka Balwaz ne kawai ya bashi buri mai kyau akan matarsa. Saboda haka zai iya baiwa boka Balwaz yaddarsa.
Idan aka kamo Barban tamkar ya sake mallakar matarsa ne.
Sarki Fairaz ya tashi daga inda yake zaune, yaje rurrufe ƙofofi wannan waje da suke ciki da tagoginsa, yadda babu mai iya jin abinda zasu tattauna.
Ya juyawa su sarki Kuffuru baya ya ce.
"Ni da sarki Darwazu uwa-ɗaya-uba-ɗaya muke. Ni ne yayansa, sa'adda mahaifinmu ya mutu. Rikici ya tashi a birninmu akan wanda za'a ɗaura sarki.
"A matsayina na yayansa na janye na bashi mulki, amma 'yan majalisa suka ce sam ni suke so.
"Aka naɗa ni sarki. Bayan lokaci mai tsaho bansan meyasa ba, amma kwata-kwata garinmu ya fita a kaina.
"Rana guda kawai na yanki daji na bar garin, tun daga wannan lokaci ban sake komawa birninmu ba. Ina da mata da 'ya'ya amma ko tunaninsu ban sake ba.
"Ina tafiya a cikin daji ne, na haɗu da wata budurwa jaruma. Jarumtakata da kyawuna suka burgeta ta ɗakko ni ta kaini wajen mahaifinta wani sarki ya aura min ita.
"Tun da na bar birninmu ban sake bayyanawa wani sunan ƙabilata da asalina ba. Duk wanda ya tambayeni labarina sai nace masa ƙasarmu aka ci da yaƙi na gudu cikin daji.
"Bayan wannan sarki ya mutu, matata ta bani mulkin ƙasar da yake mulki. A taƙaice wannan gari shi ne nake magana akai. NI ƊAN ƘABILAR ADBENCHAN NE, kai har nafi Darwazu ƙwarewa akan komai na ƙabilar..."
Sarki Kuffuru, boka Balwaz da sadauki Zayyadu suna jin wannan batu na sarki Fairaz gagarumin farin ciki ya lulluɓe su.
Farkon haɗuwarsu har sun fara jin tsoro akan kada su yi kuskuren raba kan SADAUKAI-UKU 'yan baiwa, sannan basu sami damar sake haɗa su ba.
A halin yanzu wannan abu ya wuce. Sabbin SADAUKAI-UKU 'yan baiwa sun sake haɗuwa.
Sarki Fairaz ya sake dawowa ya zauna ya fuskanci boka Balwaz.
"Yauwa," inji boka Balwaz. "Bari nayi muku bayani DAMA TA BIYU...
"Kamar yadda dama ta farko take buƙatar abubuwa guda uku. Haka DAMA TA BIYU take buƙatar abubuwa guda huɗu.
"Abu na farko SADAUKAI-UKU 'yan baiwa. Abu na biyu asalin taswirar Barban. Abu na uku LESIM. Abu na huɗu tsafi mai mataki na tara.
"Bari nayi muku bayanin komai dalla-dalla yadda zaku gane.
"Babu buƙatar na sake sanar da ku, amfanin SADAUKAI-UKU da kuma taswirar Barban. Amma bari nayi bayani akan SADAUKAI-UKU koda sama-sama ne.
"Amfanin sarki Kuffuru shi ne kare waɗannan sadaukai guda biyu.
"Amfani Zayyadu karantar taswirar Barban.
"Amfanin Fairaz karya duk wani sihiri na tsari wanda Barban ya kafa.
"To, amma idan muka kawo magana akan LESIM. Shin akwai wanda yasan wani abu koda kaɗan ne akan LESIM?"
Boka Balwaz ya tambaye su gaba ɗaya.
Sarki Kuffuru yayi shuru ya faɗa kogin tunani, kamar ya taɓa jin wannan kalma amma ya gagara tuno a ina ne.
Bayan lokaci mai tsaho Balwaz ya fuskanci baza su iya bayar da amsar wannan tambaya ba. Don haka yayi gyaran murya ya ci gaba.
"LESIM: Sunan wani tauraro ne a duniyar sama mai jan launi. A ƙarni na goma an ƙirƙiri wata takobi wadda take iya fitar da taurari shiyasa aka saka mata wannan suna [LESIM]
"Wannan takobi mallakin wani gawurtaccen jarumi ne wanda yayi zamani da sarki Samudul Ansari waishi Gauhan..."
Sarki Kuffuru yayi gaggawar dakatar da boka Balwaz da hannu guda ya ce, "Za mu iya tattaunawa akan komai, amma kada a sake kawo maganar magabata na!"
Boka Balwaz ya haɗe fuska ya ce, "To, idan bada taimakon magabatan naka ba, sai ka faɗa min yadda za'ayi burinka ya cika?"
Sarki Kuffuru yana jin haka jikinsa yayi sanyi.
Balwaz ya ci gaba da bayani, "Takobin LESIM tana ajiye a cikin wata ƙatuwar kwalba wadda ya ajiye a ƙarƙashin ƙasa.
"Amfanin wannan takobi shi ne, a wajen da Hodon yake a halin yanzu, akwai masifu da bala'i kala-kala a wajen.
"Waɗannan masifu hatta ɗan ƙabilar Adbenchan ba zai janye mana su ba face LESIM.
"Saboda haka dole ne mu ɗauko wannan takobi..."
Sarki Kuffuru na jin haka ya ce, "Ta ya ya haka zata yiwu. Ai wannan takobi wadda take cikin kwalbar Gauhan babu yadda za'ayi a ɗaukota face an fasa wannan kwalba. Ni kuma ba zan iya fasa kwalbar ba saboda akwai abubuwa da dama da zanyi da ita anan gaba."
Boka Balwaz ya yi murmushi ya dubi Kuffuru ya ce, "Ai cewa aka yi, zaka yi amfani da wannan takobi a lokacin da kake kan hanyar zuwa kogon Madarul Ansari. Shin don kayi amfani da ita, wata damuwa ce?"
Jikin sarki Kuffuru ya sake yin sanyi. Buƙatar ita ce ana so yayi amfani da wannan takobi, sannan don ya ɗaukota daga yanzu ai ba wani abun damuwa bane.
Boka Balwaz yana ganin jikin Kuffuru yayi sanyi ya ci gaba da bayani.
"Tsafi mai mataki na tara, zai na nuna mana hanya... Duk wani bincike ko kuma abinda ya shige mana duhu zamu iya amfani da tsafi mai mataki na tara mu gani.
"Ban daɗe da shiga mataki na tara a harkar tsafi ba, kun ga kenan nima zanyi amfani a wannan tafiya taku."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu yayi shuru, tsahon ɗan lokaci kafun ya ɗago kansa ya dubi Balwaz ya ce.
"Mene ne motsin mu na gaba?"
******
Yau *04/05/2023*
Babi na gaba zaizo *06/05/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 120: *Manufar sana'ar Barban (1)*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U-M-S
*
~Birnin Darul Barban.
*
A tsakiyar birnin Darul Barban Aymanul Faris, Barban da Riya suka bayyana. Ba tare ɓata wani lokaci ba, suka tunkari unguwar Barbanul Kuyr inda gidan Hajriya yake.
Duk inda suka wuce sai dai kaga jama'a nata risinawa a gabansu suna ɗiban gaisuwa.
Ba su yi wata doguwar tafiya ba, suka iso ƙofar shiga wannan gida.
A ƙofar shiga gidan suka ga aljani Ranganu ya sauƙo ƙasa da fararen tufafi. Nan take ya shaida musu cewa, shima har da shi za'a shiga cikin gidan.
Tun da aljani Ranganu ya bayyana Aymanul Faris ya ƙura masa idanu, yana so ya gano wani abu.
Masu gadin ƙofar shiga wannan gida, suka buɗe musu ƙofa take suka shiga.
A tsakiyar wannan falo suka hango Hajriya tana zaune tare da kuyangi.
Tana hango su jaruma Riya ta miƙe cikin gaggawa ta taho gare su. Bayan sun gama gaisawa da juna, Barban ya nuna musu waɗansu kujeru guda shida dake gefe yace su zauna akai.
Babu musu suka zazzauna akan kujerun. Aymanul Faris, Riya da Hajriya suna zaune a hannun dama. Barban da Ranganu suna zaune a hannun hagu.
Hajriya ta tambayi Aymanul Faris halin da suka shiga bayan rabuwarsu.
Aymanul Faris ya kwashe labarin komai ya zayyane mata, tun daga sa'adda suka farmaki sarki Raja suka ɗauki makullin taskar Samudul Ansari da yadda suka ziyarci Samazan ya basu cikakkiyar hikayar Samudul Ansari.
Hajriya ta cika da tsananin mamaki domin a wannan lokaci ta soma fuskantar abubuwa da yawa akan su Barban.
Ranganu ya ɗaura hannayensa akan teburin dake tsakanin su ya dubi Aymanul Faris da Hajriya cikin nutsuwa ya ce.
"Ya ku waɗannan sarakuna guda biyu, idan ba za ku manta ba, sa'adda Barban yazo ɗaukar Aymanul Faris a wannan birni lokacin da zasu tafi gudanar da aiki na uku a cikin wajibabbu. Ya sanar da ku cewa, duk wani aiki da muke tare da Aymanul Faris yana da manufa, amma ba zai bayyana wannan manufa daga wannan lokaci ba.
"Ya ce sai ranar da suka kammala waɗannan ayyuka guda goma zai sanar da ku, hakane?"
Aymanul Faris da Hajriya suna jin abinda Ranganu ya ce suka yi shuru suna tunani. Tsahon ɗan lokaci kafun su ɗago su dube shi su ce, haka ne.
Ranganu ya ci gaba da jawabi, "A yanzu lokaci yayi da ya kamata mu sanar da ku, manufofin waɗannan ayyuka. Saboda haka ku bamu aron kunnuwanku da kuma nutsuwar ku."
Ranganu yana zuwa nan a zancensa ya yi shuru, Aymanul Faris, Riya da Hajriya suka gyara zama.
Ranganu ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Na san ka saurari cikakkiyar hikayar Samudul Ansari, ka ji yadda ya karya zalunci a duniya ya kafa adalci.
"Iya abokan gabansa da aka bayyana a wancan lokaci sun kai guda uku, waɗanda duk duniya babu waɗanda suka isa suyi gogayya dasu.
"To, ku sani cewa yana da abokan gaba aƙalla zasu kai dubu ashirin waɗanda ƙarfinsa da jarumtakarsa ya hana su bayyana.
"Ranar da aka ce Samudul Ansari yayi ƙaura sai waɗannan abokan gaba nasa, suka sakawa kayayyakin da ya bari idanu.
"Na san cewa, an sanar da ku iya Saif-Al-Barzaƙ kaɗai ya ajiye a cikin wannan kogon dutse.
"Duk inda aka samu babban sarki kuma jarumi mayaƙi, yana da makaman yaƙi fiye da tunanin mutum.
"Iya abubuwan da na san ya bari guda goma ne, waɗanda bayan yayi ƙaura aka neme su

Please Login or Register in order to submit comment