Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ce, "Me zai hana mu karkashe waɗannan yaran, sannan mu fara ƙone wannan daula? Na san cewa sarauniya zata yi farin ciki idan taga mun yi hakan..."
BES suka amince da wannan shawara ta Gauhan sannan suka zaro takubbansu, suka tunkari inda su Jalwar ke tsaye, suna tafe a hankali takubbansu a tsaye suna kallon sama.
Jalwar na ganin haka ya baiwa su Husufa umarnin zaro takubbansu, sannan ya basu umarnin afkawa abokan gaba.
Jalwar ya nunawa Husufa BES guda biyu, sannan ya nunawa Kusuf BES guda biyu shima.
Shi kuma ya tunkari Gauhan.
Takobin Gauhan mai zane-zanen taurari tana tsaye a cikin iska, hasken rana na haskata.
Suna haɗuwa a tsakiya suka ruguntsume da azababben yaƙi mai tsananin razanarwa.
Jalwar da Gauhan suka ware a gefe, suka fara gwabzawa. Haka ɓangaren su Husufa da BES.
Gauhan ya wanzu yana kaiwa Jalwar sara da suka cikin baƙin zafin nama da kuma ƙwarewa.
Shi kuma Jalwar ya wanzu yana karewa cikin zafin nama.
A cikin daƙiƙa guda Gauhan yana iya kaiwa Jalwar sara kamar sau bakwai ko ma fiye.
Ba don Jalwar ya kasance mai tsananin zafin nama ba da tuni Gauhan yayi kaca-kaca da namansa.
Tsahon daƙiƙu masu yawan gaske suna ta gwabzawa amma babu wani sauyin da ya afku.
Ko sau ɗaya Jalwar bai mayarwa Gauhan sara ba, ƙoƙarin kare kansa ma kawai yake.
Tun da yake gumurzu a duniya, bai taɓa haɗuwa da jarumi mai baƙin zafin nama da iya yaƙi kamar Gauhan ba.
Ana cikin wannan gumurzu Gauhan ya shammace shi, ya damƙo ƙasa a hannu ya watsa masa a fuska.
Nan take ƙasa ta shiga idon Jalwar ya daina ganin komai, ya shiga ƙoƙarin mutsitstsike idanunsa.
Hakan ne ya baiwa Gauhan dama yayi tsalle ya kawo masa sara a wuya, zai datse masa kai.
Dukda cewa Jalwar baya kallo saida yayi ƙoƙarin kaucewa wannan sara na Gauhan.
Ya samu nasarar kaucewa saran amma dukda haka saida takobin Gauhan ta sare shi a kafaɗa.
Take waɗansu abubuwa guda biyu suka fice daga cikin Gauhan suka shige cikin jikin Jalwar.
A daidai lokacin ne Jalwar ya samu nasarar mutsitstike idanunsa sosai, har ya ɗan buɗe su.
Cikin tsananin fusata Jalwar ya dunƙule hannunsa ya gabzawa Gauhan naushi a gefen ƙirji.
Saboda ƙarfin naushin Jalwar saida Gauhan yayi tsalle ya faɗo acan nesa, bakinsa da hancinsa suka fashe jini ya fara yoyo.
Gauhan bai taɓa jin naushi mai ƙarfi irin wanda Gauhan yayi masa yanzu ba.
Saida ya ɗan jima a kwance sannan ya miƙe zaune, ya tofar da yawun jini.
Jalwar ya fiddo salkarsa ya wanke fuskarsa dukkan ƙasar dake kan fuskar ya fita.
Yana ganin Gauhan ya miƙe ya sake rugawa kansa da gudu, yana kwarara uban ihu.
Gauhan na ganin haka shima ya sake rugowa kan Jalwar, suka sake haɗuwa a tsakiya suka ruguntsume da sabon gumurzu wanda yafi na farkon tashin hankali.
A wannan lokaci kowa daga cikinsu kaiwa ɗan-uwansa hari yake. Saboda haka banda ƙaran ƙarafkiyar ƙarafa babu abinda ke tashi a wajen.
Duk tsananin zafin nama irin na Gauhan a wannan lokaci saida Jalwar ya bashi mamaki, domin mayar masa da martani yake tamkar ba da shi yake yaƙi ɗazu ba.
Abinda ya kwantarwa Gauhan hankali shi ne, ya san cewa ya sari Jalwar da wannan takobi ta hannunsa.
Gauhan ya kawowa Jalwar sara, Jalwar yasa takobinsa ya kare saran, Gauhan ya danna takobin Jalwar da ƙarfi domin ya durƙusar dashi ya samu nasarar saran sa.
Jalwar ya yiwa Gauhan dabara ya goce cikin zafin nama, sannan ya sake gabza masa naushi a ƙirji.
Gauhan ya yi tsalle ya faɗo acan baya, bayansa ya gwaru da wata bishiyar dabino ya faɗo ƙasa yana aman jini.
Kafun ya sake miƙewa tsaye tuni Jalwar ya daka wawan tsalle ya dira a gabansa, Jalwar yasa ƙafarsa guda ya doki bakin Gauhan. Kan Gauhan ya kalli sama, jini yayi tsartuwa daga bakinsa.
Jalwar ya sa hannayensa biyu ya kamo kwalar Gauhan ya ɗaga shi sama, saida ya miƙe dashi sama ya nunawa Allah sannan ya doka shi da ƙasa.
Jalwar ya haye kan ruwan cikinsa, ya tallafo kansa da hannu guda ya fara gabza masa naushi da ɗayan.
Bakin Gauhan ya fashe, hancinsa ma ya fashe, idanuwansa suka yi ɓulu-ɓulu.
A ɓangaren su Husufa da Kusufa tuni gumurzu ya gama ɗaukar zafi, har a wannan lokaci babu wanda ya sami nasara ta azo a gani.
Amma BES sun addabe su, sun hana su sakat.
Masifu da bala'in dake sauƙowa cikin wannan filin yaƙi, ba'a magana. Gajimarai kala daban-daban sun bayyana a sararin samaniya.
Wani lokacin manyan macizai su yi ta sauƙowa ƙasa, suna tunkarar Husufa da Kusuf.
Da ƙyar da siɗin goshi suke samun nasarar kashe macizan.
Suka ci gaba da gumurzu har tsahon lokaci, BES suna aikowa Husufa da Kusuf bala'i kala daba-daban suna ƙwacewa da ƙyar.
Jalwar na zaune akan ruwan cikin Gauhan yana dukan fuskarsa, ya ga waɗansu abubuwa sun fara kumburowa akan damatsan hannayensa.
Kafun ya gama ƙarewa abubuwan kallo tuni sun riƙe ƙasusuwan hannayensa. Sannu-a-hankali abubuwan suka juye izuwa siffar taurari.
Jalwar ya gagara motsa hannayensa saboda sun riga sun riƙe tamkar an ɗaure da igiyar tsafi.
Gauhan yayi dariyar mugunta, ya hamɓare Jalwar dake zaune a kansa.
Jalwar yayi tsalle ya faɗi a can nesa.
Gauhan ya miƙe tsaye yana dariya, jini na zuba daga bakinsa da hancinsa har a wannan lokaci.
Jalwar ya miƙe tsaye da sandararrun hannaye waɗanda basa motsi tamkar sun daskare.
Gauhan ya nuna shi da takobinsa ya ce, "Kana tunanin don na ƙyaleka, kana ta gabza min naushi, na rasa yadda zan yi ne?
"Kai yaro ne, yau na nuna maka cewa, ba ka san komai a duniya ba. Kana tunanin shirin da muka yi na tsahon shekaru ɗari a banza ne?
"Ƙyaleka da nayi kana ta dukana, wani shiri naje na aiwatar ma... Yanzu ɗalasimin TAKOBIN LESIM sun shiga jikinka, duk wani ɓangare na jikinka da waɗannan taurari suka ratsa ta cikinsa, zai daina aiki.
"A yanzu hannayenka sun daina aiki, saura sawayenka da wuyanka..."
Gauhan yana gama faɗin haka, Jalwar yaji sawayensa sun soma kumbura, kafun ya duba tuni irin wadannan taurari sun sake bayyana sun riƙe sawayen.
Bisa dole ya durƙushe kan gwiwowinsa saboda ƙafafuwan basa aiki.
Gauhan yayi dariya, ya daka tsalle ya dira a gefen Jalwar.
Ga Jalwar durƙushe akan gwiwowinsa, sawayensa da hannayensa basa aiki. Ga Gauhan riƙe da takobi tsirara zai sare shi.
***
Sarauniya Yilan tayi ihu mai razanarwa dukkan halittun dake cikin wannan duniya suka amsa mata.
Maimakon ta sake rugowa da gudu kan Samudul Ansari kawai sai ta kaiwa iska sara da takobin dake hannunta.
Takobin Bankai mai mataki na casa'in da biyar zuwa sama, bata buƙatar fitar da fai-fai idan mutum yayi amfani da saran takobi-mai-tafiya da ita.
Dai-dai inda saran zai dira ne, irin waɗannan alamu koraye zasu bayyana kamar yadda tuni suka bayyana akan ƙirjin Samudul Ansari da gefen wuyansa.
Cikin daƙiƙa guda sara guda biyu suka dira akan Samudul Ansari. Ɗaya akan ƙirjinsa, ɗaya kuma a gefen wuyansa.
Jini mai yawa ya fara tsartuwa daga jikin Samudul Ansari.
Irin waɗannan korayen sinadarai suka fara bayyana akan raunikan.
Sarauniya Yilan ta mayar da takubbanta cikin kufe, ta sarrafa wani dutse izuwa kujera sannan ta zauna akai.
Ta ƙurawa Samudul Ansari idanu tana jiran mutuwarsa.
Waɗannan korayen sinadarai suka fara zuƙan jinin Samudul Ansari, suna ƙara girma.
Wani mugun jiri, zogi da azaba ya soma shiga jikin Samudul Ansari yaji tamkar ɓare fatar jikinsa saboda tsananin azaba.
Idanuwansa suka soma ganin abubuwan dake wannan waje hazo-hazo.
Gwiwowinsa suka yi sanyi, fatar jikinsa ta soma komawa fara saboda rashin jini, raunikan jikinsa suka ci gaba da ƙara girma.
Jikinsa ya tafi ƙasa a hankali zai durƙusa kan gwiwowinsa, amma cikin zafin nama yaji cewa, ba zai taɓa durƙusawa daular Gorgon ba.
Cikin tsananin jarumtaka ya caka takobinsa a ƙasa, ya tallafi kansa ya ƙi yarda ya durƙusa kan gwiwowinsa.
Idanuwan Samudul Ansari suka soma kaɗawa baƙin cikinsu yana faman ɓacewa, take ya fara numfarfashi, alamar ransa ya kusa fita.
Sarauniya Yilan ta ci gaba da kallon mutuwar wanda ya kashe mata mahaifi cikin tsananin farin ciki.
Sarauniya Yilan tana da tabbaci a ranta, ɗari bisa ɗari sai Samudul Ansari ya mutu.
Ƙarya ne a sari mutum da takobin Bankai mataki na ɗari, sannan ya tsira da rayuwarsa.
Kowane ne sai yayi mutuwa mai muni.
Jinin Samudul Ansari na ci gaba da ƙarewa ya fuskanci cewa, akwai wani koren-dafi wanda yake maye gurbin jinin nasa.
Sannu-a-hankali wannan ruwan dafi ya gama cika ko'ina da ina na jikin Samudul Ansari.
Jikinsa ya sandare, idanuwansa suka kafe, gaɓoɓin jikinsa gaba ɗaya suka yi sanyi.
Wani irin aminci ya cika ran sarauniya Yilan, ta taso daga wannan kujera tazo gaban Samudul Ansari wanda ke durƙushe.
Tana isowa gabansa, jikinta ya juye izuwa wata mummunar siffa wadda bamu taɓa kallonta dashi ba.
Ta sa hannunta ta ɗago kan Samudul Ansari wanda ke sunkuye, ta buɗe idanunsa da zara-zaran yatsunta.
Sarauniya Yilan tayi duba izuwa cikin idanunsa, nan take ta hango har cikin ruhinsa.
Zuciyar Samudul Ansari ta daina bugawa, ruhinsa ya daina aiki, ya tarwatse.
Waɗannan dalilai ne suka tabbatar mata da cewa, Samudul Ansari ya mutu.
Sarauniya Yilan tayi dariya mai nuna tsananin farin ciki, ta zaro takubbanta guda biyu ta sumbace su.
Ta aikawa waɗansu manyan tsaunika sara-mai-tafiya domin nuna farin cikinta.
Dukda haka cikin shammata ta sake haɗe wadannan takubba a waje guda, ta cakawa Samudul Ansari a ƙirji daidai inda zuciyarsa take.
Takubban suka faso ta bayansa, dunƙulen naman zuciyarsa ya faɗo.
Har ta yunƙura zata sare masa kai, sai idanuwanta suka kai kan takobin Saif-Al-Barzaƙ.
Cikin gaggawa ta miƙa hannu zata ɗakko takobin, bazato taga wani baƙin hayaƙi ya bayyana ya lulluɓe takobin.
Daga bisani ta ɓace ɓat!
Sarauniya Yilan ta zaro idanu cikin tsananin tsoro. Bata taɓa tsammanin wannan baƙin hayaƙi zai bayyana a wannan duniya da take ba.
Ta sake dudduba Samudul Ansari ta sake tabbatar da cewa, ya mutu.
Wani farin ciki ya sake lullubeta, ta dafa kan Samudul Ansari da hannunta guda.
Take wannan waje da suke ya fara komawa hazo-hazo, kafun daga bisani ya ɓace ɓat!
Filin yaƙin Ajalin-Abokan-Gaba ya maye gurbinsa.
Saura ƙiris Gauhan ya sare kan Jalwar dake durƙushe a gabansa, sarauniya Yilan ta daka masa tsawa, ya dakata.
A ɓangaren BES da su Husufa da Kusuf kuwa, tuni BES sun kama Husufa da Kusuf suna faman ɗaure su.
Husufa da Kusuf suna ta ƙoƙarin kwacewa amma sun gagara, su kuma BES sun gagara ɗaure su.
Koda suka ga gawar Samudul Ansari durƙushe a gaban sarauniya Yilan sai jikinsu yayi sanyi.
BES suka kama su, suka ɗaɗɗaure da irin igiyar aka yi amfani aka ɗaure Jalwar.
Sarauniya Yilan ta baiwa Gauhan umarnin ɗaukar gawar Samudul Ansari ya saɓata a kafaɗarsa domin su yi amfani da ita, su karya ƙarfin wadannan dakaru, su ci daular gaba ɗaya da yaƙi.
****
A can wani waje kuwa, tau'rin ne tare da ɓoyayyen hadimi ke zaune suna tattaunawa.
A wajen babu turbaya, babu sararin samaniya, babu taurari, babu gajimare.
Zaka iya cewa wajen a cike yake da tarin hayaƙi, saboda idan ka duba sama ko ƙasa babu abinda zaka gani idan ba jan hayaƙi ba.
Tau'rin da ɓoyayyen hadimi suna zaune bisa waɗansu baƙaƙen karagu na mulki waɗanda ke tsaye akan iska.
"Shin ka san fita da nayi daga jikinsa, yasa ya rasa shekaru goma na rayuwarsa?" inji tau'rin.
Ɓoyayyen hadimi ya ce, "Babu komai koda shekaru ɗari zai rasa, saboda idan ba hakan muka yi ba, ba zamu taɓa samun nasara a wannan yaƙi ba,"
Tau'rin ya jinjina kai ya ce, "Idan bana tare da Samudul Ansari yayin da yake fafatawa da sarauniya Yilan akwai yiwuwar taga bayansa fa."
Ɓoyayyen hadimi ya gyaɗa kai ya ce, "Dole ne sai Samudul Ansari ya rasa rayuwarsa, idan har muna so ya karya ƙarfin sarauniya Yilan. Saboda ruhin dake jikinsa a yanzu baida ƙarfin da zai iya ja da ita.
"Idan wannan ruhi yana tare dashi, baya baka damar da zaka samu yin aiki a jikin Samudul Ansari yadda ya dace. Saboda haka dole ne wannan ruhi ya bar jikinsa."
Tau'rin yayi shuru shima yana tunani kafun ya gyaɗa kai daga bisani ya ce, "Na fahimce ka! Tsahon wanne lokaci zan ɗauka kafun na sake komawa cikin jikinsa?"
Ɓoyayyen hadimi ya ce, "Lokacin da sarauniya Yilan da dakarunta suke daf da fara cin daular Shaha da yaƙi!"
Tau'rin ya gyada kai cikin fahimta ya ce, "Amma idan na maye gurbin asalin ruhin dake jikinsa, za mu samu nasara akan sarauniya Yilan cikin sauƙi?"
"Ɗari bisa ɗari ma kuwa," inji ɓoyayyen hadimi.
*****
Babi na gaba mai suna: *ƘARFIN BABBAN RUHI* yana nan tafe ranar *20/04/2023* da yaddar ALLAH.
*
*Sanarwa ta musamman:- Chapter 113-133 are available on WhatsApp, ga duk mai buƙata ya ɗau wannan numban +2348136093283. Akan farashi mai rahusa - N400 kacal. Ask before payment pls.*RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 113: * Ƙarfin Babban Ruhi*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U-M-S
*
Tun daga kan ƙauyukan dake kan hanyar zuwa babban birnin Shaha, su sarauniya Yilan suka fara cin karensu babu babbaka.
Sara guda na takobin Bankai mai mataki na ɗari dake hannun sarauniya Yilan, yana iya ƙone ƙaramin gari da duk mutanen dake cikinsa.
Kafun a jima bala'i da masifu sun fara sauƙowa cikin daular Shaha.
Cikin sa'a guda kacal! sarauniya Yilan da mutanenta suka ƙone garuruwa goma sha huɗu, suka tasarwa babban birnin Shaha wanda tazarar tafiyar dake tsakaninsu daga wannan waje tafiya ce ta wuni biyu cir.
Sarauniya Yilan, Gauhan da BES basu da imani ko kaɗan, duk waɗannan garuruwa guda sha huɗu da suka ƙone, basu ƙyale kowa ba. Babu batun tsoho ko yaro balle batun mace ko na namiji.
Hatta dabbobin garuruwan basa bari da rai.
Tun da suka fara wannan tafiya, babu wanda ya sake kula su Jalwar balle ma a basu abinci.
Dukkansu suna ɗaɗɗaure a cikin sarƙoƙi hannu da ƙafa. Kai kace bayi ne aka kamo daga wata ƙasa ake wulaƙantawa.
Idan ka dubi Gauhan zaka iya cewa, a duk cikin wannan runduna tasu babu wanda ya kaishi farin ciki. A wannan lokaci idan ba murmushi ba, babu abinda yake.
Amma a duk sa'adda ya tuno cewa, Zarifa bata raye sai zuciyarsa ta sosu ainun. Wani irin takaici da azababben baƙin ciki ya rufe shi.
Take sai yaji kamar ya zare takobinsa ya afkawa Yilan da yaƙi, ya ɗauki fansar kashe masa masoyiya da Jiz'Ban yayi.
Amma da yake akwai wannan koren-sinadari wanda jikinsa ya zuƙa sa'adda ake tsuma su, sai yaji ba zai iya cin amanar daular Gorgon ba.
Suka ci gaba da tafiya har tsahon sa'a bakwai, sannan suka tasarwa ganuwar birnin Shaha.
Ya zamana cewa, suna ganin ganuwar birnin ƙarara a gabansu, hakan ne ya tabbatar musu da cewa, sun kusa isa can.
Bayan gajeruwar tafiya suka iso ƙofar shiga birnin Shaha, ƙofa mai girma da tsahon gaske.
A bakin ƙofar ne suka yi arba da dakaru ɗari uku da sittin suna gadi. Dukkansu suna sanye da baƙaƙen tufafi, sannan suna rataye da takubban da Samudul Ansari ya rarraba musu.
Koda masu tsaron ƙofa suka yi arba da gawar Samudul Ansari bisa kafaɗar Gauhan, sannan suka kalli 'ya'yansa ɗaɗɗaure a cikin ankoki tamkar bayi, sai jikinsu yayi sanyi.
Sarauniya Yilan ta daka musu tsawa, ta basu umarnin zubar da makaman yaƙin su.
Dukda haka suka ƙi bin wannan umarni nata, suka zare takubbansu suka kewaye sarauniya Yilan, Gauhan da BES a tsakiya.
Babban cikinsu ya basu umarnin afka musu da yaƙi, ba tare da ya tsaya kace-nace da sarauniya Yilan ba.
Sarauniya Yilan ta nunawa Gauhan wani ƙaramin dutse ta ce, "Mu zauna akan wancan dutsen, mu ga yadda BES zasu gama da waɗannan shashashun,"
Tana gama faɗin haka, ta nufi kan wannan dutse ta zauna, Gauhan yazo ya zauna a gefenta, suka fara kallon wannan gumurzu suna tattaunawa.
BES suka zaro Bankai ɗin dake ɗaure a gadon bayansu, suka haɗu a waje guda suka fuskanci dakarun dake tsaron Shaha.
Shugaban waɗannan dakaru ya basu umarnin rabuwa kaso huɗu. Kowanne kaso guda su tunkari BES guda ɗaya.
Nan take suka cika wannan umarni.
Kafun kace kobo tuni gagarumin yaƙi mai mugun haɗari ya tashi a wannan waje.
Kowanne BES guda ɗaya ya fuskanci dakarun Shaha guda casa'in-casa'in.
Duk tsananin ƙarfin BES da ƙarfin makaman dake hannunsu, sai da suka gane sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi.
BES suka fara sauƙewa dakarun Shaha ruwan masifu da bala'in.
Dunƙulen ƙanƙara mai girman gaske ya soma sauƙowa cikin filin yaƙin, yana shiga tsakiyar dakarun Shaha, yana mayar da su ƙanƙara.
Duk da wannan masifa da bala'in dake faruwa saida suka shafe sa'a biyu da rabi suna gwabzawa.
BES suka ƙarar da waɗannan dakaru gaba ɗayansu, amma kafun wadannan dakaru su mutu, saida suka kashe BES guda ɗaya.
Ganin wannan al'amari ya fusata sarauniya Yilan, yasa ta zaro takobin ta Bankai mai mataki ɗari ta kaiwa ƙofar birnin Shaha sara da ita.
Wani irin fai-fai na iska ya fice daga tsinin takobin nata, ya tunkari ƙatuwar ƙofar zai ɓallata.
Tun kafun faifan ya isa kan ƙofar, ta fara karkarwa da girgiji tamkar zata tumɓuko. Kai kace tsoron haɗuwa da wannan fai-fai take.
Sarauniya Yilan tana da tabbaci ɗari bisa ɗari a ranta, wannan fai-fai zai tarwatsa wannan ƙofa sannan ya shiga cikin birnin Shaha yayi mummunan ɓarna.
Cikin daƙiƙa biyu kacal! wannan fai-fai ya dira akan wannan ƙatuwar ƙofa. Gagarumar ƙara wadda duk wanda ke rayuwa a cikin birnin Shaha ya jiwota ta cika daular gaba ɗaya.
Ƙura mai kauri ta turnuƙe sararin samaniya.
Sarauniya Yilan ta dubi BES da Gauhan ta ce, "A kashe kowa a wannan daula, sannan a ƙone komai da komai. A ruguje gidaje. Yau zamu mayar da wannan daula tarihi..."
Sai dai kafun ta rufe bakinta wannan ƙura ta lafa, nan take wani abin al'ajabi ya faru.
Ƙofar birnin Shaha suka gani ta bayyana, sabuwa dal tamkar babu abinda ya sameta.
Sarauniya Yilan ta zaro idanu cikin tsananin mamaki. Wannan ƙofa ita ce abu na farko a duniya, da Bankais 100 ta gagara yiwa kwarzane.
Mun ga yadda hatta shi kansa Samudul Ansari wannan takobi tayi ajalinsa.
To, amma abin da ya baiwa sarauniya Yilan mamaki shi ne, bayan wannan ƙofa da take sake bayyana sabuwa, akwai wani baƙin hayaƙi dake kaɗawa a wajen tamkar hazo.
Da farko ita kaɗai ce take kallon baƙin hayaƙin, amma sannu-a-hankali ya soma ƙara yawa da kauri yana taruwa, har Gauhan da BES guda uku, suka fara kallonsa.
Gawar Samudul Ansari na shimfiɗe a gefen Gauhan, tana kallon sama.
Kafun a jima tuni wannan baƙin hayaƙi ya gama cika wannan waje, ya zamana cewa babu abinda mutum zai na kallo idan ba shi ba.
Sarauniya Yilan ta zaro dukkan takubbanta guda biyu, sannan ta baiwa Gauhan da BES umarnin zaro nasu su ma.
Wani irin iko wanda tunda sarauniya Yilan take a duniya, bata taɓa jin mai kama dashi ba, ya cika wannan waje.
Gauhan da BES duk suka ƙame a inda suke tsaye, saboda baza su iya yin komai a gaban wannan iko ba.
Sarauniya Yilan ce kaɗai wannan iko baya yiwa komai, amma dukda haka saida ƙirjinta ya soma dukan uku-uku.
Take ta kirawo manyan ɗalasimanta ta ƙaddamar da idanuwar Renin-Yilan, asalin Bankai da baƙin dafi a cikin bakinta.
Jalwar, Husufa da Kusuf suna jin wannan iko da yake busowa, gagarumin farin ciki ya lulluɓe su.
Sirrin sabuwar ƙabila dake cikin jininsu ya tabbatar musu da cewa, lallai babban sarki ya dawo.
Gawar Samudul Ansari dake kwance a gefen Gauhan ta miƙe tsaye ta fara wata irin tafiya, mai nuna iko, kamala, ƙarfin shiri da tsantsar buwaya.
Sarauniya Yilan tana duba izuwa ƙofar shiga birnin Shaha tayi arba da wani mutum mai baƙaƙen tufafi, wanda saboda baƙin hayaƙin dake kaɗawa a wannan waje bata iya shaida siffarsa.
Sarauniya Yilan taga gawar Samudul Ansari ta tunkari wannan baƙin mutumi mai baƙaƙen tufafi zata shiga jikinsa.
Tana ganin haka jikinta ya fara karkawar razana, ta tabbatar cewa, lallai idan Samudul Ansari ya riski wannan ruhi akwai matsala.
Cikin gaggawa ta daka tsalle ta dira a gaban gawar Samudul Ansari wadda ke tafiya, sarauniya Yilan ta kai mata sara da takubbanta biyu domin tayi kaca-kaca da ita.
Takubban sarauniya Yilan suka ratsa ta cikin gawar tamkar haske suka ratsa. Lokaci na farko sarauniya Yilan taga ikon da ya danne na Bankai.
Sarauniya Yilan ta zarewa wannan gawa idanuwanta na Renin-Yilan domin ta mayar da ita gunki amma duk a banza.
Tana ganin haka ta tabbatar da cewa, bata isa ta hana Samudul Ansari shiga cikin wannan ruhi ba.
Sarauniya Yilan ta ɓace ɓat! ta bayyana a gaban BES ta cakawa ɗaya daga cikinsu takobi.
Takobin ta ƙara tsaho ta fice daga jikin na farkon, ta shiga jikin na biyun sannan ta shige cikin jikin na uku.
Faruwar hakan keda wuya, BES gaba ɗaya suka ɓace ɓat.
Ƙarfin sarauniya Yilan ya fara ƙaruwa yana tashi sama. Kafun a jima ƙarfin sarauniya Yilan ya ninka na da sau arba'in.
Cikin taƙama da ƙarfi ta sake ɓacewa ta bayyana a gaban Samudul Ansari ta sake saran sa.
Dukda haka kwarzane bata yi masa ba. A wannan lokaci saura ƙiris ya shiga cikin wannan ruhi.
Idanuwan sarauniya Yilan suka kai kan Jalwar, Husufa da Kusuf dake ɗaɗɗaure a gefe.
Cikin tsananin baƙin ciki da takaici sarauniya Yilan tayi ƙwafa sannan ta ɓace daga wannan waje da take ta bayyana a gabansu.
Cikin rashin imani sarauniya Yilan ta cakawa Husufa Bankai a kwiɓin cikinsa na dama.
Husufa ya kwarara uban ihu, jikinsa ya fara ɗaukar launin kore, hawaye baƙaƙe suka fara zubowa daga idanunsa.
Sarauniya Yilan ta sake kai takobin

Please Login or Register in order to submit comment