Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sani. Wannan dodo yana da jibgegen sungumi mai tsananin nauyi.
"Wannan dodo da kuma sungumin dake hannunsa duk an ƙirƙire su daga sirrin tau'rin wato baƙin hayaƙi.
"Tsafi ko sihiri ba zai yi tasiri akan sa ba. Abu guda da zai ƙwaci mutum daga sharrinsa shi ne tsantsar jarumtaka.
"Wannan shi ne abinda bokayen duniya da jaruman duniya basu gane ba kenan, suka yi ta asarar rayukansu a hannun wannan dodo a banza.
"Babban abinda zai ƙwace ku a hannun dodo shi ne, tsagwaron jarumtaka da juriya.
"Shi kuma daji na biyu kamar yadda kuka sani, mutum-mutumin tau'rin ne suke gadinsa. Sarki Samudul Ansari bai sanar dani sirrin wannan daji ba, amma a hasashena babban abinda zai ƙwace ku daga sharrin mutum-mutumin shi ne jarumtaka da tsananin juriya.
"Daji na uku kuwa, babu wanda yasan abinda ke cikinsa idan ba Samudul Ansari ba. Saboda haka babu wani abu da zamu sanar da ku dangane da wannan daji sai abinda kuka tarar kawai.
"Daji na huɗu dajin wuta ne, babu abinda ke rayuwa a cikin wannan daji face azababbiyar wuta wadda take ci kullum babu dare babu rana.
"Idan mutum ya kai mataki na takwas a sarrafa aljanin-wuta, zai iya juyar da jikinsa izuwa wuta da kuma makusancinsa. Idan zaka tuna, aljani Nara ya taɓa juyar da jikinka da nasa izuwa wuta.
"Shin kana da tambaya ko kuma neman ƙarin bayani, kafun mu yi sallama ku tafi?"
Aymanul Faris da matarsa Riya suna gama jin abinda Ranganu ya ce, suka yi shuru suna tunani.
Daga can Aymanul Faris ya dube shi ya ce, "Dangane da waɗannan dazuzzuka guda huɗu, bani da wata tambaya. Amma tambayata ita ce, ta ya ya zan saka wannan ruhi a cikin jikina, alhalin ko shi kansa Samudul Ansari ruhin ne ya shiga jikinsa ba wai shi ya saka shi ba?"
Sarki Ranganu yana jin wannan tambaya ya ce, "Idan kuka je cikin kogon Madarul Ansari, kayi gaba-da-gaba da wannan ruhi, hannunka guda zaka dafa akan kwalbar sannan ka rufe idanuwanka.
"Hakan zai sa wannan ruhi ya fito daga cikin wannan kwalba sannan ya shiga jikinka.
"Amma ba zai zauna a cikin jikinka din-din-din ba, dole sai ka samu jinin ARYA sannan zai zauna a jikinka kamar yadda ya zauna a cikin jikin Samudul Ansari."
Aymanul Faris ya gyaɗa kai alamun fahimta ya ce, "Na gane bayananka, yanzu sai muyi sallama da juna."
Ranganu yayi murmushi ya samar da waɗansu irin dawakai manya-manya na haske ya baiwa su Aymanul Faris yace, "Fatan nasara!"
Aymanul Faris da matarsa Riya suka risina a gaban Ranganu suka yi godiya, sannan suka ɓace ɓat daga cikin fadar.
A tsakiyar wani gabjejen daji suka bayyana dukkansu zazzaune akan waɗannan dawakai na haske. Wata igiyar ruwa ta wani teku ta ratso ta cikin wannan daji.
Kallon farko Aymanul Faris ya yiwa dajin ya gane ina ne. Wannan daji wani yanki daga cikin dazuzzukan birnin sarki Dujalu.
Aymanul Faris da Riya suka sukwani waɗannan dawakai suka zabure su da gudu, suka tasarwa dajin Djinn wanda daga wannan waje da suke zuwa dajin tafiya ce ta wuni uku kacal.
A wannan lokaci suka fuskanci irin waɗannan dawakai da aka basu labari a cikin tarihin Samudul Ansari wato masu tsananin gudu fiye da tunanin mutum.
Duk tsananin ƙarfin gudun dawakan, ko kaɗan iska da ƙura basa damun su Aymanul Faris.
Ba su yi wani dogon tafiya ba, suka iso cikin wannan daji na Djinn.
Dajin Djinn ƙaton daji ne mai yawan dogayen itatuwa da manƴan kwazazzabai, bishiyu da duwatsun dajin siffofin aljanu ne dasu.
Sai dai kaga inuwar aljani a cikin kwazazzabo tana ta iyo, ko kuma kaga inuwan aljanu nata shawaƙi amma ba zaka aljanun ba.
Haƙiƙa wannan daji ya ci sunansa Djinn, domin duk wanda ya tsinci kansa a cikin dajin dole ne ya firgita saboda ruri da kururuwar aljanu.
Aymanul Faris ya sauƙo daga kan dokinsa sannan ya baiwa Riya ma umarnin sauƙa daga kan nata.
Tana sauƙa daga kan dawakan, Aymanul Faris ya dafa su take suka ɓace ɓat.
Aymanul Faris ya dubi Riya ya ce, "Ya ke matata! Ina so kiyi taka tsan-tsan da waɗannan dazuzzuka guda huɗu. Kada ki aikata komai idan ba ni ne na umarce ki ba."
"Zan yi yadda ka ce, ya mijina." inji Riya.
Aymanul Faris ya gyaɗa kai sannan ya wuce cikin dajin Djinn, jaruma Riya ta take masa baya.
Bayan sun shafe ɗan lokaci suna tafiya sai suka iso wannan mararrabar hanya guda biyu, ɗaya ta nufi, ɗaya ta nufi kudu.
Don gudun kada a sami matsala Aymanul Faris suka je gaban allon-arewa suka karanta abinda aka rubuta a jikin allon.
“Ya kai baƙon wannan daji, kayi sani cewa rayuwarka tana cikin masifa da bala'i wanda bashi da iyaka, idan ka bi wannar hanya zata sada ka da farkon dajin Shiwazu, bayan ka gwabza yaƙi da masu tsaron hanya ahalin aljani Sharuza.
"Muna yi maka fatan samun nasara akan abinda ya kawo ka.”
Suna gama karantawa suka je jikin allon-kudu suka karanta abinda aka rubuta a jikin allon.
"Idan baka kasance tau'rin ba, kada ku kuskura ka wuce wannan waje." shi ne kawai abinda aka rubuta a jikin allon.
Aymanul Faris ya dubi Riya "Wannan ita ce hanyar da zamu bi."
Jaruma Riya ta gyaɗa masa kai. Nan take suka kama wannan hanya ta kudu suka yi ta tafiya.
Bayan doguwar tafiya suka hango wani tafkeken daji a can gabansu, mai yawan bishiyoyi manya-manya da ƙananu.
Aymanul Faris ya dubi Riya ya ce, "Wancan dajin da muke hangowa shi ne dajin Husum inda wannan ƙaton dodo mai sungumi yake rayuwa. Abinda nake so dake shi ne kada ki manta umarnin da na baki."
Suka ci gaba da tafiya har suka iso wannan daji na Husum.
Suna shigowa cikin dajin yanayi ya sauya.
Wani irin sanyi mai kama da na hunturu ya fara kaɗawa, sararin samaniya ta soma cika da wani irin baƙin hayaƙi wanda tunda suke a rayuwarsu basu taɓa ganin irinsa ba.
Haka kuma suka fara arba da ƙwarangwal ɗin mutane, wasu sun fara zamowa ƙasa, wasu kuma suna riƙe da makaman yaƙi amma duk sun gama zamowa ƙwarangwal.
Aymanul Faris da Riya suka ci gaba da nausawa cikin wannan daji, har suka iso bakin wani ƙatoton kogo wanda ke gindin wani dogon tsauni.
Isowarsu wannan waje keda wuya, waɗansu irin takun sawaye masu girma da nauyin gaske suka soma fitowa daga cikin wannan kogo.
Lamarin da yasa wannan waje gaba ɗaya ya soma girgiza kenan, ganyayen bishiyoyi suka soma zubowa ƙasa.
Aymanul Faris ya zaro wannan zabgegiyar adda wadda Ranganu ya bashi ya riƙeta da kyau, ita kuwa Riya sai ta zaro takubbanta guda biyu ta riƙe da kyau itama.
Jim kaɗan wani irin zabgegen dodo ya fito daga cikin wannan kogon dutse. Tsahonsa ya kusan rabin wannan tsauni. Akwai wani ƙaho guda ɗaya dogo a tsakiyar goshinsa.
Yana riƙe da wani zabgegen sungumi wanda lokaci-lokaci baƙin hayaƙi yake feshi daga cikinsa.
Idon dodon guda ɗaya ne tal! a ƙasan wannan dogon ƙaho dake goshinsa.
Nan take ya sunkuyo da kansa ƙasa yana ƙarewa su Aymanul Faris kallo, su kuma sai suka ɗaga kawunansu sama suna kallonsa.
Bayan sun gama kallon-kallo wannan dodo ya ɗaga wannan zabgegen sungumi dake hannunsa ya kawo musu duka da ƙarfi.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi tsalle gefe guda, wannan sungumi ya dira akan turba.
Take wannan daji gaba ɗaya yayi girgiza, wani wawakeken rami ya bayyana.
Kafun su sake wani yunƙuri ya sake kawo musu duka da sungumin, suka sake daka tsalle gefe ya sami ƙasa.
Kan kace me wannan, ya kai musu hari wajen sau goma saboda tsananin zafin namarsa.
Aymanul Faris ya dubi Riya ya ce, "Idan ba mun yiwa wannan dodon dabara ba, duk hallaka mu zaiyi. Saboda duka na wannan sungumi nasa sai yayi daga-daga da naman mu!"
Jaruma Riya ta dube shi ta ce, "Wacce irin dabara kenan zamuyi?"
Aymanul Faris ya ce, "Ina so ki ci gaba da kaucewa hare-haren wannan dodon, nikuma zan yi amfani da wannan dama na haye izuwa kansa. Tabbas idan na fasa wancan idon nasa tamkar mun sami nasara akansa ne."
Jaruma Riya tana jin wannan batu tayi shuru tana tunani. Kafun ta gama yanke shawara wannan dodo ya sake kawo musu duka da sunguminsa.
A wannan lokaci saura ƙiris sungumin ya dira akansu, Aymanul Faris ya tureta gefe sannan shima yayi tsalle. Dukda haka saida wannan sungumi ya kuskure shi a kafaɗa.
Wani irin azababben nauyi ya danne Aymanul Faris ƙashin kafaɗarsa yayi ƙara zai ɓalle.
Cikin gaggawa yayi tsalle gefe guda. Wannan dodo yasa ƙafarsa yayi tamaula dashi, take ya tashi sama ya gwaru da wannan tsauni dake bayansu.
Aymanul Faris yayi lamo kamar wanda ya suma, lamarin da yasa wannan dodo ya ƙyale shi kenan ya juya wajen Riya ya fara kai mata duka.
Jaruma Riya ta wanzu tana mai kaucewa dukan wannan dodo cikin zafin nama, fiye da farko.
Ta san cewa, duk kuskuren da yasa ta bari wannan dodo ya kasheta, to Aymanul Faris tasa ta ƙare.
To, amma sai dai basu daɗe suna wannan gumurzu ba, wannan dodo ya soma jiwo wata halitta tana gudu akan jikinsa.
Cikin gaggawa ya waiga nan take yayi arba da Aymanul Faris riƙe da adda yana gudu akan jikinsa tamkar wanda ke hawa bango.
Dodon na ganin haka, ya ƙyale jaruma Riya sannan ya fara kawowa Aymanul Faris duka da wannan sungumi dake hannunsa.
Saura ƙiris sungumin ya dira akan Aymanul Faris sai yayi tsalle izuwa gefe guda.
Wannan dodo ya samu jikinsa, kafun a jima ya fara yiwa kansa da kansa raunika.
Waɗansu irin alamun duka suka fara kumburowa a jikinsa.
Lamarin da yasa ya fara kwarara uban ihu kenan.
Jaruma Riya ta koma gindin wannan tsauni ta tsaya tana kallon abinda ke faruwa.
Kafun a jima tuni Aymanul Faris ya isa kan kafaɗar wannan dodo.
Dodon ya taƙarƙare ya kawowa Aymanul Faris duka mai kyau akan kafaɗa.
Aymanul Faris ya daka tsalle daga kan kafaɗar wannan dodo ya tunkari idonsa da adda tsirara zai fasa shi.
Sungumin wannan dodo ya dira akan kafaɗarsa, saboda ƙarfin dukan da kuma mugun-nufin dodon saida ƙashin ya ɓalle.
Dodon ya kwarara uban ihu saboda tsananin zogin da ya ratsa shi.
Kafun ya rufe bakinsa tuni Aymanul Faris ya fasa ido guda.
Idon yayi wata ƙara sannan ruwa da jini ya soma kwararowa ta cikinsa.
Dodon ya durƙushe akan gwiwowinsa saboda zogin dake ratsa shi. Ga shi ƙashin kafaɗarsa ya karye, ga kuma idonsa da aka fasa ya zamo makaho.
Aymanul Faris ya zaro addarsa sannan ya diro ƙasa daga kan wannan dodo, sannan ya koma wajen Riya ya tsaya suka ƙurawa dodon idanu.
Nan take wannan dodo ya fara ɓallo jikin wannan tsauni dake bayansa yana jifa dashi a cikin wannan daji, ba tare da sanin inda yake jefawa ba.
Kafun kace me wannan, ɓangarori dabam na duwatsu sun soma dira a cikin wannan daji.
Aymanul Faris da Riya suka yi ta kauce musu cikin zafin nama, amma dukda haka sai da wannan dodo ya ɓallo wani ɓangare mai girma na dutse.
Ya shaƙi ƙamshin su Aymanul Faris sannan ya jefe su da shi.
Saboda girman wannan dutse da saurin da aka yi amfani dashi wajen jefo shi, yafi ƙarfin su kauce masa.
Aymanul Faris ya yi jifa da Riya gefe guda, sannan ya turje ya tsaya a inda yake.
Ɓangaren dutsen na ƙarasowa, Aymanul Faris yasa hannayensa ya tokare shi.
Dutsen ya danna Aymanul Faris baya yana ƙoƙarin haɗa shi da wannan tsauni ya matse. Aymanul Faris ya turje.
Jijiyoyin jikinsa da damatsan hannunsa suka kumburo.
Da ƙyar da siɗin goshi ya iya ajiye wannan dutse ƙasa.
Jaruma Riya ta rugo wajen Aymanul Faris ta rungume shi ta baya, sannan ta ce, "Ya kai mijina, idan fa ba kashe wancan dodo muka yi ba, ba zamu taɓa tsira daga sharrinsa ba.
"A yanzu haka, zai iya shafe kwanaki bai ƙarasa mutuwa ba."
Aymanul Faris yana jin haka ya gyaɗa kai, tabbas wannan magana ta ta haka take.
To, amma ta ya ya zai iya kashe wannan dodo.
Kaifi da tsini basa tasiri akansa, waje guda da kaifi zaiyi tasiri a jikinsa shi ne ido. Ga shi idon nasa a fashe amma ya ƙi mutuwa.
Aymanul Faris ya yi gajeren tunani, kawai sai ya tunkari inda sungumin wannan dodo ke jefe.
Riya ta dube shi cikin tsananin mamaki, kamar ta hana shi aikata abinda yake niyya amma sai ta fasa.
Ta ya ya zai iya ɗaga wannan sungumi mai shegen nauyi?
Aymanul Faris yana zuwa inda wannan sungumi yake, yasa hannayensa biyu ya fara ƙoƙarin ɗaga sungumin amma sai ya kasa.
Ya daɗa jarrabawa, jijiyoyin jikinsa suka sake cika, damatsan hannunsa suka kumburo.
Ya samu nasarar raba sungumin da ƙasa amma dukda haka bai iya ɗaga shi ba.
A daidai lokacin ne, wannan dodo ya juyo inda Aymanul Faris ya wulwula wani dutse sannan ya jefo masa.
Aymanul Faris ya fusata ya sake taƙarƙarewa ya saka ƙarfinsa gaba ɗaya akan hannayensa ya fara ɗago wannan sungumi.
Saboda nauyin wannan sungumi da kuma wahalar da Aymanul Faris yake sha, sai da rigar Aymanul Faris ta yage sannan jini ya zubo daga cikin bakinsa.
A haka ya samu ya ɗaga wannan sungumi da ƙyar sannan ya doki wannan dutse da dodon ya aiko masa.
Dutsen ya tarwatse tamkar wanda aka niƙa.
Aymanul Faris ya tunkari inda wannan dodo ke durƙuse yana jan wannan sungumi a ƙasa.
A wannan rana Aymanul Faris ya girgiza jaruma Riya saboda bata taɓa tsammanin zai iya ɗaga wannan sungumi ba.
Sungumin dutse da ƙarfe aka narka aka samar dashi, a tarihin sungumin babu wani da aka taɓa duka dashi bai tarwatse ba.
Aymanul Faris yana ƙarasowa gaban wannan dodo, ya sake taƙarƙarewa ya ɗaga shi sama, ya dokawa dodon a tsakiyar ka.
Nan take kan dodon ya tarwatse, ya sulale ƙasa matacce.
Aymanul Faris ya koma wajen Riya ya zauna yana hutawa saboda tsananin galabaita.
Jim kaɗan da mutuwar wannan dodo, jikinsa ya tarwatse izuwa baƙin hayaƙi ya ɓace ɓat!
Aymanul Faris da Riya suka cika da tsananin mamaki.
Bayan sun huta sosai sai suka miƙe suka ci gaba da tafiya.
Aymanul Faris ya fiddo musu wadannan dawakai na haske suka haye kansu suka tunkari daji na biyu.
Bayan shafe wata doguwar tafiya suka iso cikin wani daji.
Babu komai a cikin daji face waɗansu manya-manyan duwatsu guda biyar.
Aymanul Faris ya dubi Riya ya ce, "Ya ke matata! A cikin wannan daji amfaninki a wannan tafiya zai fara, saboda haka ki shirya."
Yana gama faɗin haka suka jiwo takun sawaye a saman waɗannan tsaunika guda biyar.
Nan take suka ɗaga kawunansu sama, suka hango waɗansu sadaukai guda biyar tsaitsaye a saman tsaunikan.
Akan kowanne tsauni akwai sadauki guda ɗaya.
Dukkansu suna sanye da baƙaƙen tufafi, suna riƙe da baƙaƙen takubba.
Wani irin hayaƙi mai kaurin gaske na tashi daga jikinsu.
Babu abinda su Aymanul Faris suke iya shaidawa a jikin waɗannan mayaƙa. Komai da komai baƙin hayaƙi ya lulluɓe.
*****
Yau *20/05/2023*
Babi na gaba zaizo *22/05/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 127: *SIWOD DANS*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U-M-S
*
Waɗannan sadaukai guda biyar suna ganin baƙin mutane a cikin wannan daji da suke, suka sauƙo daga saman wadannan tsaunika suka saka su a tsakiya.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka zaro takubbansu, suka ƙurawa halittun idanu, suna jira su ga ta ina za'a fara kawo musu hari?
Jim kaɗan waɗannan sadaukai suka afkawa su Aymanul Faris da azababben yaƙi da maɗaukakan takubban dake hannunsu masu zubar da baƙin hayaƙi.
Aymanul Faris da Riya suka shiga ƙoƙarin kare kansu gami da mayar da martani.
Waɗannan mayaƙa guda biyar sun kasance masu tsananin zafin nama da iya-yaƙi fiye da tunanin su Aymanul Faris.
A cikin daƙiƙa guda suna iya kaiwa su Aymanul Faris sara sau biyar ko sau shida.
Da ƙyar da siɗin goshi suke iya karewa.
Kafun a jima sun fara haɗawa Aymanul Faris da jaruma Riya gajiya.
Ana cikin haka ɗaya daga cikin waɗannan mayaƙa ya sari gadon bayan jaruma Riya da takobinsa.
Takobin tana dira kan sulken yaƙin jaruma Riya wata ƙara ta cika wannan waje.
Ko ƙwarzane takobin ba ta yiwa sulken yaƙin jaruma Riya ba.
Waɗannan mayaƙa dukkansu suka daka tsalle gefe guda cikin tsananin mamaki.
Ba wai su ba, hatta shi kansa Aymanul Faris sai da ya cika da tsananin mamaki bisa ganin wannan takobi ba ta yiwa sulken komai ba.
Waɗannan sadaukai suka ware kansu izuwa kaso biyu - nan biyu, nan uku.
Sadaukai guda uku suka rugo kan Aymanul Faris, guda biyu kuma, suka ruga kan jaruma Riya.
Nan take suka sake buɗe sabon gumurzun yaƙi mai ban tsoro.
Ƙarar karafkiyar takubban su ta cika wannan waje.
A wannan rana Aymanul Faris da jaruma Riya suka fara nuna asalin jarumtakar da aka haife su da ita.
Ga shi dai waɗannan sadaukai sun fisu yawa da komai amma sun gagara yi musu koda rauni guda ɗaya.
Jaruma Riya ta soma nunawa waɗannan sadaukai guda biyu baiwarta ta sarrafa takobi, domin dukda cewa a tare suke kawo mata hari tana iya karewa a lokaci guda sannan ta mayar da martani.
Aka ci gaba da gumurzu har zuwa ɗan tsahon lokaci sannan labari ya soma sauyawa.
Jaruma Riya ta soma gajiya saboda yadda take iya bakin ƙoƙarinta wajen kare hare-haren waɗannan sadaukai guda biyu.
Babban abinda ya ƙwace ta shi ne, albarkacin wannan sulke dake jikinta koda sun sareta basa yi mata rauni.
A ɓangaren Aymanul Faris kuwa, yadda waɗannan sadaukai basu gaji ba shima ko kaɗan bai fara nuna alamun gajiya ba.
Koda ya jiwo jaruma Riya ta fara haki sai ransa ya fara ɓaci.
Yadda suke gumurzu da waɗannan sadaukai koda zasu shekara arba'in babu wanda zai sami nasara.
Aymanul Faris ya sunkuya sannan ya taso cikin fusata da zafin nama ya sare kan sadauki ɗaya.
Kan sadaukin ya tashi sama, maimakon jini ya yi fallatsi kawai baƙin hayaƙi Aymanul Faris ya gani yayi feshi.
A daidai lokacin ɗaya daga cikin sadaukan ya sari Aymanul Faris a gadon baya.
Wani lafcecen sara ya bayyana a gadon bayansa.
Aymanul Faris ya kwarara uban ihu ya durƙushe kan gwiwowinsa.
Jaruma Riya tana ganin haka ta fusata, ta manta da gajiyar dake jikinta tayi wani irin juyi a tsakiyar waɗannan dakaru.
Take kawunansu gaba ɗaya suka cizge daga wuyansu, baƙin hayaƙi ya cika wajen.
Wannan juyi da takobi da jaruma Riya tayi shi ake kira "SIWOD-DANS" duk faɗin ƙabilar Kuyuru babu wanda ya kaita iyawa.
Aymanul Faris na ganin matarsa ta sami nasara shima ya miƙe tsaye zumbur, ya sare kawunan waɗannan mayaƙa gaba ɗayansu.
Sai dai yana kashe su ya sake faɗuwa ƙasa, idanuwansa suna lumshewa da buɗewa.
Jaruma Riya tayi gaggawar rugawa izuwa kansa, ta fara duba shi.
Wannan lafcecen rauni da aka yi masa a gadon baya shine ya motsa.
Takubban dake hannun waɗannan sadaukai guda biyar da suka kashe suna ɗan kama da Saif-Al-Barzaƙ.
Abu guda da yake kama tsakanin Saif-Al-Barzaƙ da Bankai shi ne, dukda tsananin hatsabibancinsu suna yiwa ma'abota su illa.
Kai, harma sun fi yiwa ma'abota su illa.
A halin yanzu babu wanda duniya ta sani a matsayin magajin Samudul Ansari kamar Aymanul Faris.
Saboda haka zaka iya cewa, hankalin tau'rin ya gama karkatowa izuwa kansa.
Jaruma Riya ta fiddo magani daga cikin jakar Aymanul Faris ta bashi yasha, sannan ta kafa musu tanti a wannan waje.
Wani barci mai nauyi yayi gaba da Aymanul Faris.
Saida suka shafe kwanaki uku cir! a wannan waje sannan Aymanul Faris ya warke.
Washe gari da sassafe kuwa, suka ci gaba da tafiya suka tunkari daji na uku.
To, shi wannan daji na uku babu wanda yasan abinda ke rayuwa a cikinsa.
Yadda yazo a tarihi ma shi ne, daga sararin samaniya Samudul Ansari ya jefo ɗalasimansa izuwa cikin dajin.
Hatta masana da masu bincike basu san abinda ke rayuwa a cikin wannan daji ba.
Bayan Aymanul Faris da matarsa Riya sun shafe wata da watanni suna tafiya sai suka iso farkon wannan daji.
Abinda ya fara yi musu sallama shi ne, wani zabgegen kogi mai yawan gudun ruwa.
A bakin kogin akwai wata 'yar ƙaramar kwale-kwale ɗaure a jikin turke.
"Me kike fahimta dangane da wannan daji?" Aymanul Faris ya tambayi jaruma Riya.
Jaruma Riya tayi shuru ta ƙarewa wannan kogi kallo sannan ta ce, "Ga dukkan alamu akwai muggan halittun ruwa a cikin wannan kogi, kuma ina tunanin har mu fice daga cikin wannan daji a cikin kogin zamuyi ta tafiya."
Aymanul Faris ya gyaɗa mata kai, "Tabbas, hakane. Amma bari mu shiga mu ga abinda ke rayuwa a cikin kogin."
Yana gama faɗin haka ya ƙarasa bakin wannan kogi, ya shiga cikin kwale-kwalen sannan ya baiwa Riya umarnin zama a gefensa.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, Aymanul Faris ya fara tuƙa wannan kwale-kwale ya nausa cikin wannan kogi.
Suna fara tafiya ya dubi Riya ya ce, "Matata! Shin kin san dalilin da yasa Ranganu ya haɗa mu da wadannan dawakai masu tsananin sauri?"
Riya ta ce, "Ina fa sai ka faɗa,"
Aymanul Faris ya ci gaba, "Saboda idan ba muyi sauri ba, ISRABIL zai isa daular Gorgon. Idan kuwa ISRABIL ya isa daular Gorgon komai zai iya faruwa.
"Wataƙila zai iya yin abinda Gauhan yaso ya yiwa maigirma Samudul Ansari wato hana ni tarawa da Arya.
"Wannan yasa ake so muyi gaggawa mu mallaki tau'rin, muna mallakar tau'rin abinda zamuyi na gaba shi ne, zuwa birnin Damashkar domin aurena da Arya"
Jaruma Riya tana jin wannan batu wani kishi ya sake rufeta amma sai ta kawar da batun, don kada Aymanul Faris ya gane.
"Haka ne. Amma meyasa

Please Login or Register in order to submit comment