Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zasu iya yin komai akan cikar burinsu."
Gimbiya Jaanu ta goge hawayen da ya zubo daga idanunta ta ce, "Idan mahaifina da sarki Kuffuru sun gudu daga sharrin Marganu, nasan cewa kai ba zaka gudu ba. Bani labarin abinda ya faru mana har ka sami wadannan raunika?"
Aymanul Faris yana jin haka, ya kwashe labarin yadda wannan gumurzu nasu ya kasance tun daga farko har ƙarshe ya zayyane mata.
Gimbiya Jaanu ta cika da tsananin mamaki ta kwanta akan ƙirjin Aymanul Faris ta ce, "Gaskiya na jinjina maka, sannan na sallamawa jarumtakarka. Saboda inda ƙananun jarumai ne suka sami kalan wannan rauni da ƙarshensu yazo, amma kai gashi har har yaƙi kake da raunin.
"Ina sonka, jarumina..."
Aymanul Faris yayi murmushi ya fara shafa gashin kan Jaanu, suka ci gaba da hira irinta masoya har gari ya gama wayewa.
Gimbiya Jaanu da kanta ta miƙe ta shiga cikin gidan ta shaidawa Hajriya da jaruma Riya Aymanul Faris ya farfaɗo.
Dukkansu suka shigo cikin ɗakin suka gaisa dashi, gimbiya Jaanu ta dawo ɗauke da abinci bisa faranti.
Da kanta ta ciyar da Aymanul Faris wannan abinci sannan ta baiwa su Hajriya labarin duk gumurzun da Aymanul Faris yayi da ISRABIL.
Dukkansu sai da suka cika da tsananin mamaki sannan suka sake sallamawa Aymanul Faris.
Nan dai suka shiga hira akan ci gaban da aka samu a daular Shaha wanda hatta zamanin babban sarki, ba'a samu irinsa ba.
Lokacin da rana tayi tsakiya Hodon da Ranganu suka sauƙo cikin wannan birni, suka zo suka gaishe da Aymanul Faris sannan suka yi masa jinjina gami da ƙarfafa masa gwiwa bisa bajintar da ya nuna.
Da yamma Ranganu da Hodon suka keɓe da Aymanul Faris.
"To, mu kam zamu tafi gudanar da aiki na takwas," inji Ranganu. "Aiki na takwas aiki ne mai wahalar gaske sannan zai ɗauke mu lokaci wanda hatta ni kaina bansan adadi ba.
"Sai dai wannan aiki na takwas zaiyi mana gagarumin amfani amma acan gaba... Fatan nasara akan abubuwan da ka saka a gabanka..."
Aymanul Faris yayi murmushi ya ce, "Nima ina muku fatan nasara. Tabbas ba ƙaramin dacewa nayi ba, da na haɗu daku..."
"Kada ka damu," inji Hodon.
Nan take suka yi sallama da juna akan cewa su Hodon zasu tafi gudanar da aiki na takwas wanda shi kansa Aymanul Faris baisan me zasu ɗauko da inda zasuje ba.
Bayan tafiyarsu da rabin sa'a, Hajriya da jaruma Ria suka shigo cikin wannan ɗaki.
Jaruma Riya tana sanye da doguwar riga daga sama har ƙasa duk jikinta a lulluɓe yake.
Hajriya tayi murmushi ta dubi Aymanul Faris ta ce, "Na kusa na samu jika!!!"
Aymanul Faris ya zaro idanu cikin tsananin farin ciki, "Me kike nufi, mama?"
Maimakon Hajriya ta bashi amsar wannan tambaya, kawai sai ta ɗan yaye doguwar rigar dake jikin Riya.
Nan take Aymanul Faris yayi arba da tsohon ciki wanda za'a iya haihuwa a kowanne lokaci.
Aymanul Faris ya cika da tsananin farin ciki, ya lumshe idanu cikin tsananin farin ciki.
Wai shima ya kusa ya zamo baba?
A daidai wannan lokaci, likita Laziyya ta bayyana a cikin wannan ɗaki domin baiwa Aymanul Faris magungunansa.
Bayan ta bashi magungunan yasha, sai ya dube ta ya tambayeta nan da wanne lokaci zai warke daga wannan lalura.
Laziyya ta ce, "Mafi yawancin wadanda aka yiwa irin wannan rauni naka, suna shafe watanni biyu suna jiyya.
"Amma kai jikinka yana da kyau sosai, ba zaka wuce wata guda ba tare da ka warke ba. Kaga kenan an kusa..."
*****
Yau *01/07/2023*
Babi na gaba zaizo *03/06/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 147: *Dabarar Yaƙi: Samfurin K*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
~Daular Nehiya.
*
Dukda cewa sarki Kuffuru yasha maganin wannan dafi da Marganu ya saka masa, saida ya kwana biyu yana jiyya sannan ya warke.
A cikin waɗannan kwanaki guda biyu, babu yadda mahukuntan wannan daula basu yi da su sarki Ayubu ba akan su faɗa musu abinda suke buƙata a maimakon ladan wannan magani amma sun ƙi faɗa.
A ranar da sarki Kuffuru ya farfaɗo ne, yana zaune akan karagar mulkinsa ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba.
Ɗaya daga cikin wadannan mutane guda goma, ya baiwa sarki Kuffuru labarin wadannan mutane guda biyu da suka kawo masa maganin da yasha ya warke.
Sarki Kuffuru ya riƙe baki ya ce, "Mutane kamar waɗannan masu daraja, za ku jinkirta bani labarin su. A je a gaggauta tahowa dasu domin na karrama su a wannan fada."
Nan take waɗannan mahukunta guda goma, suka baiwa wasu hadimai umarnin zuwa masauƙin su sarki Ayubu sannan su taho dasu.
Hadiman suka fita bayan ɗan lokaci suka shigo da su sarki Ayubu cikin wannan fada.
Tun daga nesa sarki Kuffuru ya ƙura musu idanu cikin tsananin mamaki.
Abinda yake mamaki na farko shi ne, halittar Ron ta Kentauron.
Abinda yake mamaki na biyu kuwa shi ne, mene ne dalilin da zaisa Ayubu ceton rayuwarsa?
Ana ƙarasowa da su Ayubu wannan waje sarki Kuffuru ya nuna musu wajen zama, ya ce su zauna.
Nan take dukkansu suka zazzauna, sarki Kuffuru yasa aka kawo musu abinci da abinsha na alfarma.
Ba tare da gardamar komai ba, Ayubu da Ron suka ci wannan abinci suka ƙoshi, koda suka sami nutsuwa sai sarki Kuffuru ya bayar da umarnin a kaisu ɗakin-gani kafun yazo.
Waɗannan hadimai suka shiga gaba, suka yiwa Ayubu da Ron jagora izuwa wani ƙasaitaccen ɗaki dake gefen wannan fada.
Sarki Kuffuru ya zauna aka ci gaba da tafiyar da harkokin mulki a wannan fada, har la'asar sannan ya tashi daga fadar ya shiga ɗakin-gani inda manyan baƙinsa suke.
Yana shigowa cikin ɗakin yayi arba da sarki Ayubu da Ron suna zaune bisa kujeru suna shan shayi suna hira.
Sarki Kuffuru yaje gefensu bisa wata karaga ya zauna.
Bayan sun gama gaisawa da sarki Ayubu, Kuffuru ya dube shi ya ce, "Shin ko zan iya sanin dalilin da yasa ka ceci rayuwata, saboda ance wajajen da kaje ka samo waɗannan magunguna wajaje ne masu mugun haɗari?"
Sarki Ayubu yana jin wannan batu ya zuba shayi a cikin kofin dake hannunsa ya kurɓa sannan ya ɗago kansa ya dubi Kuffuru ya ce, "Yardar dake tsakanin mu ita ce tasa na ceci rayuwarka.
"Ka yarda dani ne yasa ka bani aikin tarwatsa ƙabilar Kuyuru dake rayuwa a tsibirin Gazwar a shekaru masu yawa da suka shuɗe.
"Ka yarda dani ne yasa ka yarda aka ɗauki fursuna mai daraja daga kurkukunka, aka kai ta dajin Marsas domin a karɓo 'yata.
"Marigayi sarki Ratanam ya juya min baya, akan ɗan rashin fahimtar da muka samu amma kai baka juya min baya ba.
"Ka yarda dani ne yasa kaje da kanka birnina, lokacin da Marganu yake ƙoƙarin ci wa 'yata mutunci.
"Wannan shi ne dalilin da yasa na ceci rayuwarka..."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu jikinsa yayi sanyi.
Sarki Ayubu ya kasance mutum mai daɗaɗan kalamai, idan kana jin kalamansa ba zaka taɓa cewa ya kasance mutum mai muguwar ɗabi'a ba.
Don haka waɗannan kalamai da ya furtawa sarki Kuffuru sai suka kashe masa jiki, ya kore duk wata tantama dake ransa.
Sarki Ayubu ya ci gaba da bayani, "Ya shugabana! Mene ne dalilin da yasa ka yaƙeni a lokacin da na taho wajenka domin na shiga tawagarku ta son kamo Barban?"
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu ya dubi sarki Ayubu cikin tsananin mamaki ya ce, "Kana nufin a wancan lokaci, kaima tawagarmu kazo shiga, ba yaƙa ta ba?"
Ayubu ya gyaɗa kai ya ce, "Kwarai kuwa, amma nasan ba haka boka Hubbazu suka sanar da kai ba. Saboda shi boka Hubbazu munafuki ne, yana da wani shiri na musamman a ransa wanda yake ɓoyewa.
"Tabbas nasan cewa kaga zahiri, lokacin da ya yaudare ku ya kawo muku Marganu na bogi."
Sarki Kuffuru ya dubi Ayubu cikin rashin yarda ya ce, "Kaima zaka iya sanar da ni dalilin da yasa kake son shiga tawagar mu ta kamo Barban?"
"Haba, ya shugabana." inji sarki Ayubu. "Shin ka manta cewa, Barban ya taɓa sace min 'yata ce. Fansar wannan abu nake so na ɗauka."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu yayi shuru yana tunani, tsahon ɗan lokaci kafun ya dubi Ayubu.
"Yanzu faɗa min mene ne abinda ke tafe da kai?"
Sarki Ayubu ya sake kurɓar wannan shayi dake hannunsa sannan ya ce, "Ina so na ɗauki fansa akan Marganu saboda fyaɗen da ya yiwa 'yata, sannan ina so karɓo 'yata daga hannun Aymanul Faris.
"Haka kuma ina so na ɗauki fansa akan birnina da suka ruguje.
"Zan cimma waɗannan abubuwa ne kawai, idan na haɗa hannu da kai. Wannan yasa na taso da kaina, na sameka."
Sarki Kuffuru yana jin haka, ya gyaɗa kai cikin fahimta. Su biyun ababen harinsu ɗaya ne: Marganu da Aymanul Faris.
Kuffuru ya dubi Ron ya ce, "Baka yi min bayanin wannan halitta da kuke tare ba, wane ne shi?"
Sarki Ayubu yayi gyaran murya ya ce, "Sunansa Ron, ɗan ƙabilar Kentauron. Waɗannan halittu da suka haɗa kai da sarki Farhama na birnin Kufa a shekarun baya.
"Waɗannan halittu zasu taimaka mana sosai a yaƙi da Marganu da kuma Aymanul Faris."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu ya sake gyaɗa kai ya ce, "Tabbas kun kama hanyar da ta dace. Saboda da ni da ku dukkanmu abokan gabarmu ɗaya ne.
"Marganu ya ci min mutunci wanda ba zan iya yafewa ba. Yanzu haka ya auri 'yata, ko kuma nace tsinanniyar 'yata saboda tuni na rubuta sunanta a cikin waɗanda zan kashe.
"Waye zamu farmaka, tsakanin Marganu da Aymanul Faris?"
Lokaci na farko Ron ya saka baki a cikin maganar tasu, "Duk wanda ka zaɓa shi zamu fara tunkara, ya shugabana. Babu wanda muke shakka..."
Sarki Kuffuru yana jin haka yayi shuru yana tunani.
Abinda ya fara faɗo masa a rai shi ne, irin baƙaƙen maganganu da kuma cin mutuncin da Marganu yake yi masa.
Nan take ya ƙudurce a ransa, Marganu zasu fara farmaka.
"Yarima Marganu na daular Gorgon zamu fara farmaka," inji sarki Kuffuru.
Sarki Ayubu da Ron suna jin amsar da ya bayar suka dubi juna cikin mamaki. Dama sun san amsar da zai bayar kenan saboda yadda Marganu ya wulaƙanta shi a kwanakin baya.
"Shi kenan," inji sarki Ayubu. "Yau da dare zamu tsara yadda zamu yi yaƙi da Marganu, kai kuma gobe ka taho mana da sarkin-yaƙin daular ka."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu yayi sallama da su Ayubu ya fice daga cikin wannan ɗaki.
Hadimai suka mayar dasu masauƙi.
A cikin wannan dare sarki Ayubu da Ron basu yi barci ba, raba dare suka yi suna ta shawarwari akan dabarun yaƙi iri daban-daban.
Washe gari da safe bayan sun gama karyawa, sarki Kuffuru tare da sadauki Zaili-Zaila suka shigo cikin masauƙin nasu ɗauke da wani ƙaramin teburi mai ɗauke da duwatsu kamar mayaƙa.
Mafi yawancin lokuta ana amfani da irin wannan teburi wajen gabatar da salo da dabarun yaƙi.
Dukkansu suka zauna a cikin wannan ɗaki, suka saka wannan ƙaramin teburi a tsakiya.
Sarki Ayubu ya dubi Kuffuru ya ce, "Jiya da dare ni da Ron bamu rintsa ba, mun zauna mun tsara dabarun yaƙi akan yadda zamu ɓullowa daular Gorgon.
"Ron yana da cikakken bayani akan daular Gorgon da kuma ƙarfin sojojin yaƙinsu, wanda hakan zai taimaka mana ƙwarai da gaske a wannan yaƙi.
"Idan ya kammala bamu bayani akan ƙarfin daular, zamu gabatar muku da dabarar yaƙin da muka zo da ita."
Sarki Ayubu yana zuwa nan a zancensa, ya dubi Ron ya gyaɗa masa kai.
"Babbar illar ƙabilar Gorgon a tunani da nazari na ƙabilata ba zai wuce abubuwa guda uku ba;
"Abu na farko shi ne, idanuwan Renin-Yilan.
"Renin-Yelin: Waɗansu irin idanuwa ne masu mugun haɗari a duniya. Masana na ƙabilata sun ce waɗannan idanuwa suna iya fitar da farin hayaƙi mai ɗauke sinadarin Aiys.
"Sinadarin Aiys na iya juyar da jiki mai jini da tsoka izuwa gunki saboda tsananin sanyin da sinadarin yake da.
"Ma'abota Bankai suna da irin waɗannan idanuwa, amma ba kowanne daga cikinsu ne yake da irin idanuwan ba.
"Babban masani na ƙabilata ya ce, duk wanda muka kalla da takobin Bankai mai mataki na arba'in yayi sama, yana iya sarrafa irin waɗannan idanu.
"Wannan shi ne babbar illar ma'abota Gorgon ta farko. Wato juyar da jiki izuwa dutse.
"Abu na biyu shi ne, wannan dafi da suke sakawa a cikin ruwan sha wanda yake watsa muggan cututtuka a cikin al'umma.
"Wannan shi ne babbar illar ma'abota Gorgon ta biyu; gurɓata ruwan sha.
"Abu na uku shi ne, TAKOBIN-BANKAI.
"Kamar yadda muka samu bayanai, waɗannan shaiɗanu sun yi imani matuƙa da waɗannan takubba nasu masu mugun haɗari.
"Bankai mataki-mataki ne. Akwai mataki na ɗaya zuwa na huɗu, akwai biyar zuwa goma, akwai sha-ɗaya zuwa talatin da tara.
"Akwai arba'in zuwa casa'in da tara.
"Akwai ɗari zuwa dubu.
"Mataki na ɗaya zuwa na huɗu, yana sakawa abokin gaba *dafi* a cikin jininsa idan aka sare shi da takobin.
"Mataki na biyar zuwa goma yana fitar *fai-fai* mai ɗauke da sinadarai guda biyu yayin aka kaiwa abokin gaba sara.
"Mataki na sha-ɗaya zuwa talatin da tara, yana iya samar da *manya-manyan macizai* su afkawa abokan gaba.
"Mataki na arba'in zuwa casa'in da tara, yana baiwa mutum dama yayi amfani da abinda yafi ƙwarewa akai. Wasu walƙiya, wasu hadari, wasu ƙanƙara da dai makamantansu.
"Mataki na ɗari zuwa dubu, yana baiwa mutum dama ya kai abokin gabarsa cikin duniyar-Bankai sannan yayi amfani da ikon duniyar ya gama dashi.
"Wannan shi ne cikakken bayani akan takobin Bankai.
"Ya shugabana, wannan shi ne cikakken bayani akan ƙarfin dakarun daular Gorgon..."
Sarki Kuffuru yana gama jin wannan bayani ya dubi Ron ya ce, "Ya batun BES banji kace komai akan su ba?"
Ron yayi guntun murmushi ya dubi Kuffuru ya ce, "Abinda duniya bata fuskanta dangane da BES ba shi ne, su fa an riga an kashe su.
"Ruhinsu ake haɗawa da ruhin da yafi kowanne ƙarfi a daular.
"A zamanin da mun ga yadda BES suka mutu, sa'adda sarauniya Yilan ta mutu.
"Yanzu ma kamar haka ne, BES ba zasu taɓa mutuwa ba face an tarwatsa ruhin Marganu.
"A cikin bayanin dabarun wannan yaƙi zamu tattauna akan su."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu ya gyaɗa kai cikin fahimta. Ko shi kansa ya samu nasarar kashe ɗaya daga cikin BES amma ta sake dawowa.
Sarki Ayubu ya matso gaban wannan ƙaramin teburi sannan yayi gyaran murya domin kama hankalin sarki Kuffuru da sadauki Zaili-Zaila dake zaune a gefensa.
"Zamu iya kiran wannan salon yaƙi da Samfurin K," inji sarki Ayubu. "Ku matso domin ganin salon yaƙin ku fahimci abinda nake nufi..."
Sarki Ayubu ya ɗauko waɗansu duwatsu da aka sassaƙa a matsayin dakarun Gorgon, ya ajiye su a tsakiyar wannan fili.
"Marganu zai iya fitowa wannan yaƙi da dakaru dubu ɗari shida, kasancewar gaba ɗaya dakarun daular tasa ba zasu wuce miliyan ɗaya da rabi ba.
"Akwai waɗanda ba zasu iya fitowa wannan yaƙi ba, sannan akwai waɗanda za'a bari a gida suyi gadi. Saboda haka mu ɗauka kawai da dakaru dubu ɗari shida kawai zai fito wannan yaƙi."
Sarki Ayubu ya sake ɗauko wasu duwatsu guda talatin ya ajiye a gaban waɗannan mayaƙa, duwatsun sun fi mayaƙan girma sosai.
"A hasashe da hange irin na tsofaffin mayaƙa, Marganu zai iya fitowa wannan yaƙi da sarakunansa guda talatin. Kamar yadda kuke gani yanzu."
Sarki Ayubu yana zuwa nan a zancensa ya ɗauko wasu duwatsu guda biyar da suka fi na sarakunan girma ya ajiye a gaban sarakunan.
"Mu ɗauka wadannan su ne BES: Dakaru guda biyar masu amfani da ruhin Marganu."
Ya sake ɗauko guda ɗaya wanda yafi BES girma ya ajiye a gabansu.
"Wannan shi ne babban mai gidan nasu, wato Marganu ko kuma ISRABIL.
"Ina so ku ƙarewa tsayuwar waɗannan duwatsu kallo sosai, saboda a hasashenmu wannan shi ne irin tsayuwar da zasu yi."
Sarki Kuffuru, Ron da sadauki Zaili-Zaila suka ƙurawa yadda Ayubu ya ajiye waɗannan duwatsu, tsahon dan lokaci sannan suka kammala nazarinsu.
Sarki Ayubu ya dawo ɗaya ɓangaren ya fara ajiye duwatsu masu siffar UMKAS.
"Zamu fita wannan yaƙi da dakaru guda miliyan ɗaya."
Yana faɗin haka ya sake ɗauko wasu duwatsu guda talatin ya ajiye a gaban dakarun UMKAS.
"A cikin sarakuna guda tamanin da uku dake wannan daula, muna so ka zaɓo mana gawurtattun jarumai guda talatin."
Ayubu ya ɗauko duwatsu guda goma ya ajiye a gaban waɗannan sarakuna guda talatin.
"Waɗannan su ne Ron da dakarunsa guda goma..."
Ya ɗauko wasu manya guda biyu ya ajiye a gaban Ron da Kentaurons ya ce, "Waɗannan guda biyu su ne: Ni da sarki Kuffuru."
Sarki Ayubu na zuwa nan a zancensa ya ɗago kansa ya dubi sarki Kuffuru da sadauki Zaili-Zaila ya ce.
"Ya ya wannan yaƙi zai kasance? Ku sake nazarin tsayuwar mayaƙan mu da kyau."
Sarki Kuffuru da sadauki Zaili-Zaila suka ƙurawa mayaƙan idanu da kyau, har tsahon ɗan lokaci sarki Ayubu ya tabbatar da cewa sun haddace tsayuwar mayaƙan.
"Yadda wannan yaƙi zai kasance shi ne," sarki Ayubu ya ci gaba da bayani.
"Ni da sarki Kuffuru zamu tari yarima Marganu.
"Ron da dakarunsa zasu tari BES.
"Waɗannan sarakuna guda talatin namu, zasu tari sarakunan Marganu guda talatin.
"Sadauki Zaili-Zaila da mayaƙan UMKAS guda miliyan ɗaya zasu tari ma'abota Bankai guda dubu ɗari shida.
"Abinda yasa zamu tari Marganu shi ne, sarki Kuffuru yana da gawurtattun takubba guda biyu - LESIM da Siwod-del-bulod.
"Ni kuma ina da takobi wadda nake kira da suna Anjan, takobin da nayi amfani da ita wajen kashe shugaba Hasanul Jalwar a farmakin da na kaiwa tsibirin.
"Takobin LESIM tana samar da taurari masu mugun ƙarfin gaske, waɗanda suke jifa da duk wani abinda suka doka.
"Siwod-del-bulod tana samar da Infirons sadaukan da babu kamar su..."
Kafun sarki Ayubu ya rufe bakinsa Kuffuru ya dakatar da shi da hannu.
"Ba tattaunawa zaka yi akan ƙarfin mu ba, kamata yayi ka kawo batun ƙarfin abokin gabar mu da makamin da yake sarrafawa.
"Na gwabza yaƙi dashi, dukda takobinsa ta haske ba tai min komai ba amma yana da wata hatsabibiyar takobi wadda take juya muhalli.
"Da wannan takobi yaso yaga bayana na kuɓuta da kyar."
Sarki Ayubu ya dubi Kuffuru yayi guntun murmushi ya ce, "Ya shugabana! Wannan yaƙi da zamu fita babban yaƙi ne. Akwai buƙatar kowanne daga cikinmu yasan ƙarfin abokinsa, saboda hakan zai taimaka sosai.
"Wannan takobi da Marganu ya yaƙe ka da ita? Ita ake kira takobin-taswira wadda aljani Barzas ubangidan Rauziyya yake sarrafawa.
"Marganu ya mallaki wannan takobi, sai dai abinda bai sani ba shi ne, mun san da zaman wannan takobi tunda daɗewa kuma har mun yi maganinta.
"Takobina ta Anjan zata magance mana matsalar takobin-taswira.
"Wannan takobi tawa tana iya sauƙar da iko na musamman a waje, wanda zai sa na gudanar da aiki ba tare ansan na gudanar dashi ba.
"Nayi amfani da wannan takobi a lokacin yaƙina da Hasanul Jalwar kuma na gama dashi, ba tare mutum ɗaya a wannan waje yaga abinda ya faru ba.
"Sarki Kuffuru zai iya amfani da takobin Siwod-del-bulod ya danne mana ikon Marganu, hakan zai bani dama nayi amfani da ikona na sare kansa.
"Idan muka sare kansa, BES zasu mutu a take a wajen.
"Cikin ƙanƙanin lokaci zamu ci nasara a wannan yaƙi..."
Sarki Kuffuru da sadauki Zaili-Zaila suna jin wannan batu na sarki Ayubu suka cika da tsananin mamaki, daga bisani suka fara yi masa jinjina.
"Mun amince ɗari bisa ɗari da wannan dabarar yaƙi," inji sarki Kuffuru.
Nan take ya dubi sadauki Zaili-Zaila ya ce, "Kuje ku fara shirye-shiryen wannan yaƙi, sannan a rubuta wasiƙar yaƙi a kaiwa Marganu."
******
Yau *03/07/2023*
Babi na gaba zaizo *06/07/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi 148: *Uku masu daɗi, uku marasa daɗis*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U~M~S
*
~Daular Shaha.
*
Kamar yadda Laziyya ta faɗa haka al'amarin a kasance, wato saida Aymanul Faris ya shafe wata guda cir yana jiyyar wannan ƙaton rauni dake kan cikinsa sannan ya warke.
A wannan rana ya miƙe zaune, sannan ya sauƙo daga kan wannan gado ya tunkari ƙofar fita daga wannan ɗaki.
Yana fitowa daga cikin ɗakin yayi kiciɓus da gimbiya Jaanu, cikin tsananin farin ciki tayi tsalle ta rungume shi.
"Wannan rana nake jira, ranar da zan ga ka warke daga wannan ciwo mai ban tsoro." inji Jaanu.
Aymanul Faris ya ce, "To ai gashi ranar tazo, ko? Yau ina so na fita fada saboda haka kije ki shirya tare zamu fita..."
Gimbiya Jaanu ta cika da tsananin farin ciki ta sumbaci Aymanul Faris sannan ta wuce izuwa yankinta.
Aymanul Faris ya ƙarasa babban falon wannan gida inda Hajriya da jaruma Riya suke zaune, koda suka ganshi sai suka cika da tsananin farin ciki.
Ya ƙarasa gaban Hajriya ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya koma gefen Riya ya zauna.
Ya saka hannunsa akan cikinta ya ce, "Ya kike, ya ɗana?"
Jaruma Riya tayi guntun murmushi ta ce, "Ƴar mu tana nan lafiya, ina ji a jikina mace zan haifa..."
"Ah haba, magana ce..." inji Aymanul Faris. "Babban sarki ma namiji ya fara haihuwa, saboda haka nima namiji nake tunanin zan fara haihuwa..."
"Mu jira lokaci yayi, wannan na Ubangiji ne..." inji jaruma Riya.
Aymanul Faris ya gyaɗa kai ya ce, "Haka ne..."
Ya sake dubansu cikin nutsuwa ya ce, "Yau nake so na fita fada domin ganin yadda al'amura suke tafiya."
"Wannan yana da kyau," inji Hajriya. "Kaje ka shirya saboda lokaci yana tafiya."
Aymanul Faris yayi murmushi sannan yayi sallama da su ya fice.
Aymanul Faris da gimbiya Jaanu suka caɓa ado na gaban kwatance, suka saka kaya kala ɗaya.
Idan ka hango su daga nesa zaka ɗauka 'ya'yan manyan sarakunan aljanu ne saboda tsananin kyawunsu.
Dakaru da hadimai suka yi ta zubewa a gabansu suna ɗiban gaisuwa.


Please Login or Register in order to submit comment