Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi wata guda a kulle, na shiga na tambaye shi inda ya ɓoye sarƙoƙin zinarin matata."
Sarki Kuffuru ya ce, "Wannan ba wani abun damuwa bane, ka cika wannan umarni da na baka..."
Sarki Fairaz ya sake risinawa sannan ya tashi sama ya bar wannan waje da wata irin darduma.
Kuffuru ya sake kewaye wannan kurkuku yayi murmushi, gagarumin farin ciki ya cika ransa.
Nan take tunanin 'yarsa Firziyya ya faɗo ransa, zuciyarsa ta fara tafarfasa ya tuno yadda ta fara haɗa kai da Marganu domin su ga bayansa.
Sarki Kuffuru ya ce a ransa wannan lokaci shi ne yafi dacewa da ta karɓi hukunci.
Yana ayyana hakan ya kirawo aljaninsa, ya hau bayan aljanin sannan ya bashi umarnin zuwa Kurkukun Azaba-Uku.
Cikin ƙanƙanin lokaci sarki Kuffuru ya isa wannan kurkuku, tun daga sararin samaniya yayi arba da kurkukun a ruguje.
Zuciyarsa ta ci gaba da tafarfasa, ya sauƙo daga kan wannan aljani ya ƙarasa cikin rusasshen ginin kurkukun yana nazari.
Gaba ɗaya kurkukun ta gama rugujewa, ɗaki guda kawai aka rage.
Sarki Kuffuru yazo ƙofar wannan ɗaki ya tsaya, a wannan ɗaki aka kulle Marganu idan zai tuna.
Hakan yana nufin Marganu ne ya dawo wannan kurkuku ya rugujeta kenan?
Wannan ba zai yiwu ba, saboda a gaban idanunsa aka yiwa Marganu yankan rago.
Babban matsalar babu wanda zai tambaya a wannan waje, babu kowa.
Sarki Kuffuru ya fara duba sassan jikin Duksum waɗanda suka tarwatse.
Ba da takobi aka yi amfani wajen tarwatsa shi ba, hasalima ko ɗison jini babu a jikin Duksum.
Jim kaɗan sarki Kuffuru ya fiddo madubin tsafinsa ya fara bincike akan abinda ya faru.
"SIRRIN ISRABIL!" shi ne kawai abinda sarki Kuffuru ya jiwo a cikin wannan madubin tsafi.
Nan take ya jefar da madubin tsafin sannan ya kwarara uban ihu.
"Kenan Marganu shi ne ISRABIL?!" inji Kuffuru cikin ɗaga murya.
Cikin gaggawa sarki Kuffuru ya haye bayan wannan aljani, suka bar wannan waje.
*****
Yau *25/05/2023*
Babi na gaba zaizo *27/05/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 129: *Hular Babban Sarki*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
Sarki Fairaz yana barin wannan kurkuku da aka kulle Barban a cikinta, ya hau wani irin ingarman doki mai ƙarfin gudu ya tasarwa daular Nehiya.
Wannan doki nasa yana da ƙarfin gudu tamkar aljani a sararin samaniya.
Da sassafe ya fara wannan tafiya amma kafun azahar tayi ya fara hango wata ƙatuwar ganuwa acan gabansa.
Bayan gajeren lokaci ya iso gindin wannan ganuwa inda aka gina wata ƙatuwar ƙofa mai girma da faɗi. A saman wannan ƙofa an kafa tuta mai ɗauke da tambarin bishiya.
Akwai dakaru masu tsananin yawan gaske tsaye a wannan waje cirko-cirko suna gadi.
Koda suka ga sarki Fairaz ne sai suka yi gaggawa suka buɗe masa ƙofa.
Sarki Fairaz ya kunna kai cikin wannan daular cikin azababben gudu bisa wannan doki nasa.
Dukda tsananin ƙarfin gudu irin na dokin Fairaz saida ya kai magariba yana tafiya a cikin wanan daula sannan ya isa babban birnin tarayya na wannan daula.
Duk inda yazo wucewa da zarar an ga shi ne, sai a buɗe masa ƙofa ya wuce.
Yana shigowa cikin wannan birni wanda babu kamar sa a wannan daula ya rage gudun dokinsa.
Wasu gabza-gabzan dakaru guda goma suka bayyana a gabansa a cikin wannan siffa ta UKSUM.
Nan take suka shige gaba suka yi masa jagora har zuwa babbar fadar daular Nehiya wadda aka yiwa sarki Kuffuru tanadinta.
Sarki Fairaz ya rasa ta ya ya zai fara wassafa wannan fada saboda tsananin kyawunta, saboda tafi ƙarfin wassafawa sai dai abinda idanu suka gani kawai.
Wasu sarakuna guda goma ya gani zazzaune akan waɗansu ƙananun karagu na mulki gefen wata garƙaƙemiyar karaga wadda babu kowa akanta.
Sarakunan guda goma dukkansu suna sanye da jajayen tufafi, suna ganin Fairaz ya shigo cikin wannan fada suka miƙe tsaye cikin tsananin farin ciki suka tarye shi.
Saboda lallai abinda suka gani shimfiɗe akan fuskarsa alheri ne.
Bayan sun gama gaisawa, sannan sun kawo masa abinci ya ci ya ƙoshi.
Sai Fairaz ya fiddo wannan hoto da sarki Kuffuru ya bashi ya nuna musu.
Koda suka yi arba da Barban kulle a kurkuku sai gagarumin farin ciki ya lulluɓe su.
Dukkansu suka fara yiwa Fairaz jinjina tamkar shi ne ya kamo Barban ba Kuffuru ba.
Suka tambaye shi yaushe sarki Kuffuru zaizo?
"Gobe da sassafe," inji Fairaz.
Gagarumin farin ciki ya sake lulluɓe sarakunan, suka ci gaba da hira a wannan waje har dare ya soma rabawa sannan suka watse.
Kafun gari ya waye sun bayar da sanarwa a duk faɗin wannan daula cewa, babban sarkin da suka shafe zamani suna jira ya bayyana kuma a wannan rana zaizo wannan daula domin karɓan matsayinsa.
Mutanen wannan daula suka yi ta farin ciki.
Gaba ɗaya jama'ar wannan daula da na farkonsu da na ƙarshen su, duk suna gadin wata hular sarauta ce da aka ajiye a cikin gidan sarautar daular.
Tsaron da aka baiwa wannan hular babu wanda aka baiwa a duk faɗin wannan daula.
Babban dalili da yasa suka ɗaga hankali kuma suke so Barban ya shiga hannu shine, kada Barban yayi tunanin satar wannan hular sarauta.
Barban ya tsorata duk wani mahaluƙi dake wannan daula domin sai da yayi sata sau tamanin da uku a jere a wajaje mabambanta amma ko fuskarsa ba'a iya ganowa ba.
Wannan yasa mahukunta na wannan daula suka yi alƙawari duk wanda ya samu nasarar kamo Barban, zasu bashi mulkin daular gaba ɗaya.
To, wai ita wannan hular sarauta ta wane ne?
Mene ne dalilin da zai sa ba zasu zaɓi wani a cikinsu ya mulki wannan daula ba?
Ita dai wannan hular sarauta asalinta ta babban sarki Samudul Ansari ne, sa'adda yayi ƙaura wasu daga cikinsu suka yi shiri suka je suka sato ta.
Mutum ɗari daga cikinsu ne suka hallaka a ƙoƙarin saka wannan hula akansu, saboda ƙarfin jininsu bai kai su saka wannan hula ba.
Jinin Samudul Ansari ne kaɗai zai iya saka wannan hula ya zauna lafiya, saboda ɓoyayyen hadimi ne ya bashi ita.
Sarki Kuffuru baida jinin Samudul Ansari a cikin jininsa amma yana da nasaba tun ta iyaye tsakaninsa da Samudul Ansari.
Washe gari da sassafe wannan zabgegiyar fada ta cika ta batse da tarin mutane. Ance aƙalla mutanen dake wannan waje zasu kai miliyan goma da ɗoriya.
Waɗannan mahukunta na wannan daula guda goma suna zazzaune akan karagarsu ta mulki gefen ta babban sarkin da zaizo.
A wannan rana an ɗauko wannan hular sarauta an ajiyeta akan wannan ƙatuwar karaga.
Hula ce wadda aka ƙera da zunzurutun zinari mai tsadar gaske, irin wanda ko a tsibirin Gazwar ba'a samun irinsa.
Dukda cewa babu hasken rana akanta amma ta cika wannan waje da haske da sheƙi.
Masana da masu hasashe na wancan zamani suna ganin cewa, babu abu mai tsadar wannan hular sarauta duk faɗin duniya.
Jim kaɗan kowa yana zaune yayi zugum yana jira, aka jiwo ƙarar kaɗawar fuka-fukin shirgegen aljani a sararin samaniya.
Lamarin da yasa kowa dake wannan waje ɗaga kansa kenan, sarki Kuffuru suka gani zaune a gadon wannan aljani nasa ya saka baƙaƙen tufafi.
Kwarjinin sarki Kuffuru ya doki dukkan wanda ke wannan waje, take kowa ya shiga taitayinsa.
Wannan aljani ya sauƙo da sarki Kuffuru tsakiyar wannan fada.
Sarki Fairaz da mahukuntan wannan daula suka je gaban sarki Kuffuru suka zube suka kwashi gaisuwa.
Sannan suka yiwa sarki Kuffuru jagoranci izuwa gaban wannan babbar karagar mulki suka tsaya.
Ɗaya daga cikin mahukuntan wannan daula ya dubi dukkan jama'ar dake wannan waje ya ce.
"Ya ku al'umar Nehiya, muna farin cikin sanar daku cewa, mun sami nasarar kama Hodon, gagarumin ɓarawon da yayi mana mummunar sata a shekarun baya.
"Kamar yadda muka yi alƙawari, duk wanda ya samu nasarar kamo Hodon shi zamu yiwa muƙamin wannan daula.
"Yau muna gabatar muku da SARKI KUFFURU ƊAN MEHER a matsayin sarki na wannan daula gaba ɗaya.
"Wannan hular sarautar da ta gagari kan kowa, domin sarki Kuffuru aka yi ta..."
Mutumin yana zuwa nan a zancensa ya ɗauko wannan hular sarauta ya sakawa sarki Kuffuru akansa.
Hular sarautar ta zauna akan sarki Kuffuru daram tamkar saida aka gwada kansa aka yi ta.
Sarki Fairaz da waɗannan mahukunta guda goma suka zube a gaban sarki Kuffuru suka yi mubaya'a.
Sa'annan waɗannan sarakuna guda ɗari bakwai da tamanin su ma suka zo suka yi mubaya'a.
Daga nan kowa dake wannan waje ya zube yayi mubaya'a.
Sarki Kuffuru yayi murmushi ya zauna akan wannan karaga ta mulki, ya dubi jama'a yayi bayanin godiya sannan ya sallami kowa da kowa.
Bayan fada ta watse sarki Kuffuru ya dubi waɗannan mahukunta guda goma ya ce, "Ina so ku kaini babban sansanin mayaƙa na wannan daula sannan ku kaini manyan biranen wannan daula."
Wannan mutumi yana jin haka ya ce, "Ni sunana Rauzil, wannan daula tamu tafi ƙarfin sansani guda ɗaya sai dai muna da guda bakwai.
"A wannan gari namu akwai babban sansani guda ɗaya wanda ke ɗauke da sojojin yaƙi mutum miliyan huɗu. Sunan wannan gari shi ne Yolin.
"Sauran garuruwan dake ɗauke da sansanin mayaƙanmu su ne, Rauzum, Auzur, Taliba, Lahri, Baskar, Lailiy da Jalim.
"Sansanin dake cikin garin Yolin shi ne ƙarami a cikinsu. Saboda mayaƙa miliyan huɗu kacal yake da.
"Ya shugabana! Sauran waɗannan garuruwa guda shida musamman an samar dasu ne domin baiwa wannan daula tamu tsaro.
"Babu komai a cikinsu face tarin mayaƙan mu da kuma iyalansu.
"Uku daga cikin waɗannan biranai dakarun mutane ne, huɗu kuma dakarun UMKAS ne."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu yayi shuru yana tunani. Sojojin yaƙi miliyan ɗari tara.
"Ina son naje dukkanin waɗannan sansani ɗaya bayan ɗaya domin ganin ƙarfin sojojin mu." inji sarki Kuffuru.
Su Rauzil suna jin wannan batu suka zube a gaban Kuffuru suka ce, za'a yi kamar yadda kake so babban sarki.
Daga wannan lokaci sarki Kuffuru yasa wani hadimi yayi ta nuna masa wannan gidan sarauta, hadimin ya cika umarni.
Tun da safe suka fara yawo a cikin gidan sarautar amma har rana ta faɗi basu je wajaje da dama ba.
Hadimin ya yiwa sarki Kuffuru jagoranci izuwa turakarsa.
Wata ƙasaitacciyar turaka ce wadda ta ninka asalin tasa sau bakwai. Sarki Kuffuru ya ƙarasa gaban wani ƙaramin teburi yaci abinci sannan ya kwanta akan wani fankacecen gado.
Jikinsa yana nutsewa a cikin laushin wannan gado sha'awarsa ta motsa, yaji a wannan lokaci babu abinda yake buƙata kamar mace a kusa dashi.
Sarki Kuffuru ya daɗe bai kusanci mace ba, tun sa'adda ya salwantar da rayuwar matarsa sarauniya Anisa bai sake kusantar wata mace ba.
Hakan ne yasa abin ya taso masa lokaci daya.
A yadda sarki Kuffuru yake kallon kansa yafi ƙarfin tsayawa ɓata lokaci akan kuyangi da kuma barori. Dole yana buƙatar matar aure.
To, amma wacce ce tafi dacewa dashi?
Babban dalilin da ya hana sarki Kuffuru ƙara aure shi ne, 'yarsa Firziyya.
A halin yanzu ya riga da ya goge Firziyya a matsayin 'yarsa inda ace ya sameta a kurkukun da ya kasheta.
A daidai wannan lokaci tunanin aljani Hasamul-Sawaz ya faɗowa Kuffuru cikin gaggawa ya ƙwalawa aljanin kira sau uku.
Nan take ƙasa ta tsage Hasamul-Sawaz ya ratso ta cikinta ya fito.
Sarki Kuffuru ya miƙe ya zauna akan wannan gado ya dubi Hasamul-Sawaz ya ce, "Lokaci mai tsaho mun daɗe bamu haɗu ba, ina ka shiga?"
Hasamul-Sawaz ya ce, "Ya shugabana! Shin ka manta a da can sarki Buƙalshiyyu shi ne hadiminka? Babu yadda za'a yi ina yawan bayyana a gareka alhalin ban kasance hadiminka ba, hakan zai sa Buƙalshiyyu ya kai ƙarata wajen sarkin aljanu."
Sarki Kuffuru ya gyaɗa kai ya ce, "Na kiraka ne domin ka bani shawara akan abubuwa guda biyu da nake so na gudanar..." yayi gyaran murya.
Hasamul-Sawaz ya sake kasa kunnuwa da kyau yana sauraro.
"Ina son nayi aure sannan ina buƙatar RUHIN JARUMTAKA duk a lokaci guda!"
Hasamul-Sawaz yana jin wannan batu ya yi shuru yana tunani, daga bisani ya fiddo wani allon tsafi yayi gajeren tsatsuba sannan ya ɗago kansa ya dubi Kuffuru ya ce.
"Jarumin da RUHIN JARUMTAKA ya zaɓa a matsayin magajinsa, yana daf da mallakar wannan ruhi.
"Sannan batun matar auren da kake so, wacece?"
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu ya zaro idanu cikin tsananin razana da tsorata ya ce, "Yaushe Aymanul Faris ya fara wannan tafiya kuma ya ya aka yi ban sani ba, a matsayina na magajin Gauhan?"
Hasamul-Sawaz ya dubi sarki Kuffuru ya ce, "Ya shugabana! Kayi sani cewa zamu ƙwace wannan ruhi a hannunsa koda ya samu nasarar ɗauko shi."
"Ta ya ya kenan?" Kuffuru ya tambaye shi.
Hasamul-Sawaz ya gyara zama ya ce, "Ya shugabana! Tsahon lokacin da na shafe ban bayyana a gareka ba, naje na gudanar da bincike akan abokan gabarka ne...
"Na kaiwa wasu aljanu ziyara waɗanda suke daga cikin kaɗan da suka saurari hikayar Samudul Ansari. Aljanun sun tabbatar min da cewa, wannan ruhi ba zai taɓa zama a jikin ma'abocinsa ba face yana jin jinin ƙabilar ARYA yana yawo a jikinsa.
"Sun shaida min cewa, shi kansa Samudul Ansari a wancan zamani saida ya haɗa da wannan jini sannan ruhin ya zauna a jikinsa yadda yake so.
"Kaga kenan, idan kuwa haka ne, zamu iya hana Aymanul Faris mallakar wannan jini. Idan babu wannan jini a tare dashi cikin sauƙi za'a cire ruhin daga jikinsa."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu ya ce, "Ƙabilar ARYA tuni ta riga ta shuɗe. Bana tunanin za'a sake samun ire-irensu a ban ƙasa yanzu!"
Hasamul-Sawaz yana jin abinda Kuffuru yace ya matso gabansa ya nuna masa hoton wata kyakkyawar budurwa ya ce.
"Wannan ita ce kaɗai 'yar ƙabilar ARYA da tayi saura a duniya, shin ka san ta?" ya tambayi sarki Kuffuru.
Sarki Kuffuru yana arba da tsantsar kyawun wannan budurwa, kyawunta ya ruɗe shi, saboda bai taɓa ganin mai rabinta a kyawu ba.
Saida ya shafe daƙiƙu sha biyar yana wassafa tsantsar kyawunta a zuciyarsa sannan ya dubi Hasamul-Sawaz ya ce, "Wannan kyakkyawar wace ce?"
Hasamul-Sawaz yana jin wannan batu, hankalinsa ya soma ɗugunzuma saboda ya tabbatar da cewa ya tafka babban kuskure, bai kamata ya nunawa Kuffuru ainihin surar GIMBIYA JAANU ba.
Hatta 'yan uwansa aljanu a wannan lokaci suna tattaunawa akan tsantsar kyawun Jaanu.
Babu cikakken namijin da zaiyi arba da gimbiya Jaanu a siffar da take a yanzu bai kamu da tsananin ƙaunarta ba.
Shin hakan yana nufin sarki Kuffuru ma ya kamu da ƙaunar gimbiya Jaanu kenan? Wannan ita ce tambayar da Hasamul-Sawaz ya yiwa kansa.
"Ko kaɗan ban santa ba, amma wace ce?" inji sarki Kuffuru.
Hasamul-Sawaz yana jin abinda sarki Kuffuru ya ce sai yayi farin ciki, wataƙila idan ya sanar da sarki Kuffuru ainihin wace ce zai iya haƙura da sonta.
"GIMBIYA JAANU ce!!!" inji Hasamul-Sawaz.
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu ya yi shuru. Gimbiya Jaanu 'yar sarki Ayubul-Zairiy?
"Ta ya ya aka yi Jaanu ta kasance 'yar ƙabilar ARYA?" Sarki Kuffuru ya tambayi Hasamul-Sawaz.
"Ta ɓangaren mahaifiyarta," inji Hasamul-Sawaz.
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu gagarumin farin ciki ya lulluɓe shi, ya ce, "Indai Jaanu ce anyi mai sauƙi. Zan iya zuwa har cikin birnin Damashkar na kamota!"
Hasamul-Sawaz ya ce, "Gaskiya ya kamata, muyi gaggawar hakan, kafun Aymanul Faris ya samo wannan ruhi?"
Sarki Kuffuru ya ce, "Wannan duk mai sauƙi ne. Yanzu ya ya batun Marganu da 'yata Firziyya. Wanne waje suke a halin yanzu?"
Hasamul-Sawaz yana jin wannan batu ya dubi sarki Kuffuru ya ce, "Ya shugabana! Ya kamata daga wannan lokaci kana saka Marganu a cikin manyan abokan gabarka!"
Sarki Kuffuru ya dube shi cikin mamaki ya ce, "Meyasa ka ce haka?"
Hasamul-Sawaz ya amsa, "Saboda Marganu shi ne ISRABIL; mutumin da daular Gorgon ta shafe zamani masu tsahon gaske tana jiran bayyanarsa.
"Yanzu haka yana kan hanyar zuwa daular Gorgon domin taka matsayinsa na ISRABIL. Idan Marganu ya taka matsayin ISRABIL zai mulki daular Gorgon.
"Kaga kenan yaƙi dashi sai cikakken shiryayye."
Sarki Kuffuru yayi murmushi ya ce, "Gobe zan je dukkan manyan biranen dake wannan daula domin ganin ƙarfin sojojin yaƙina. Tabbas jikina yana bani babu wanda zanyi shakka."
Hasamul-Sawaz ya yi murmushi ya ce, "Sai dai a ji tsoronmu ba wai muji tsoron wani ba. Babbar sa'ar da Samudul Ansari ya taka ita ce, a zamaninsa wannan daula ta Nehiya bata samu ba, da na tabbata sai mun ga ƙarshensa."
Sarki Kuffuru yana jin wannan batu yayi murmushi ya sallami Hasamul-Sawaz akan cewa, bayan ya gama kewaye wannan daula zai kira shi domin motsinsu na gaba.
*****
Yau *29/05/2023*
Babi na gaba zaizo *29/05/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 130: *Abinda aka daɗe ana jira*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
~Ɓangaren Yarima Marganu.
*
Isika da Firziyya suna jin abinda Marganu ya ce gagarumin farin ciki ya lulluɓe su.
Marganu ya fiddo wannan mudubi wanda su Ileisha suka bashi, ya duba mudubin da idanuwansa.
Take mudubin yayi haske. Fuskar Ileisha, Laila da Narima ta bayyana akan mudubin.
"Barka da wannan lokaci, ISRABIL!" inji dukkansu.
"Sannun ku!" inji Marganu.
Dukkansu suka yi murmushi suka ce, "Wani abun ne?"
"LOKACIN TAFIYA YAYI!" inji Marganu.
Wani gagarumin farin ciki yazo kan fuskarsu duk su ukun.
"Muna cikin wannan lambu kazo ka same mu kawai," inji Ileisha.
Marganu yana jin haka ya mayar da mudubin cikin jakarsa, sannan ya dubi Isika ya ce, "Kaimu lambun Gorgon."
Isika yayi murmushi ya dafa Marganu da Firziyya take jikinsu ya saje izuwa hasken wannan waje suka ɓace ɓat!
Kafun su Marganu su iso cikin wannan lambu, tuni su Ileisha sun gama shirya musu abinci da ababen sha.
Dukkansu suna zaune a cikin wannan ƙaramin ɗaki sun sunkuyar da kawunansu ƙasa suna jiran zuwan ISRABIL.
Jim kaɗan farin haske ya bayyana a cikin wannan ɗaki, suna ganin haka suka fara ɗiban gaisuwa.
Siffar Marganu da ta Firziyya ta bayyana a cikin wannan farin haske.
Marganu ya kama hannun Firziyya suka zauna akan wani katafaren gado dake cikin wannan ɗaki.
Ileisha, Narima da Laila suka zo gabansu suka jeru.
Marganu ya dube su ya ce, "Ina gabatar muku da matar da zan aura - FIRZIYYA. Ku girmama ta tamkar yadda za ku girmama ni.
"Na yanke shawarar tafiya izuwa daular ku. Idan na taka babban matsayina daga baya zan dawo na kawar da dukkan maƙiyana."
Koda su Ileisha Gorgon suka ji abinda Marganu ya ce sai gagarumin farin ciki ya sake lulluɓe su.
"Daular Gorgon zata bi dukkanin wani umarninka, ISRABIL!" inji Narima.
Marganu yayi murmushi ya ɗauko farantin abinci guda, ya fara baiwa Firziyya da hannunsa har saida ta ƙoshi sannan shima ta ciyar dashi.
Bayan sun ƙoshi sun sami nutsuwa, Marganu ya dubi su Ileisha ya ce, "Me muke jira?"
Suna jin haka suka jikkunansu a waje guda su ukun, take suka juye izuwa wannan jibgegiyar macijiya.
Macijiyar ta kwantar da kanta ƙasa sannan ta wangame ƙatoton bakinta.
Marganu da Firziyya suka shige cikin bakin nata, suna ƙulewa ta rufe.
Macijiyar taje ta faɗa cikin wani ƙaton tafki dake cikin wannan lambu, jikinta yana nutsewa a cikin tafkin, ta fara iyo tana wani irin gudu na gaban tunani.
*
~Daular Gorgon.
*
Daular Gorgon gaba ɗaya ta sauya saɓanin da zaka ga fuskar kowa ɗauke da firgici da tsorata.
A yanzu farin ciki ne da ƙarfin gwiwa shimfiɗe akan fuskar kowa.
Babban abinda yake basu tsoro a da shine, kada tau'rin ya sake bayyana ba tare da sun samo ISRABIL ba.
Abinda ya saka musu farin ciki da ƙwarin gwiwa kuwa, har sun samo ISRABIL amma tau'rin bai sake bayyana ba.
Wajaje da dama na cikin wannan daula an rubuta, "BARKA DA ZUWA, ISRABIL."
A wannan rana su Ileisha suka turo saƙon cewa, suna tafe tare da ISRABIL.
Farin ciki a wannan rana ba'a cewa komai. Amma kowa ka gani a daular Gorgon gagarumin farin ciki a cikin ransa.
A halin yanzu babu Ziyazilu, babu Yilan, babu BES amma akwai waɗannan sarakuna guda ɗari waɗanda mutum sha-biyu daga cikinsu sun rasa rayukansu a yaƙi da Samudul Ansari.
Dukkansu su tamanin da takwas suna zaune a cikin wannan ƙaton ɗaki wanda suka saba gudanar da taro a cikinsa.
Akwai karaga ta mulki guda ɗari a cikin wannan ƙaton ɗaki. Hamsin a hannun dama, hamsin a hannun hagu.
Acan saman wani tudu kuwa, wata ƙatuwar karaga ce ta mulki wadda aka gina da zinari mai tsadar gaske sannan aka yi mata koren fenti mai sheƙi.
Babu kowa akan wannan karaga, dama sarauniya Yilan ce ta saba zama akanta amma yanzu bata nan.
Waɗannan sarakuna guda tamanin da takwas duk sun sunkuyar da kawunansu ƙasa, suna jiran zuwan babban sarki.
Bayan gajeren lokaci, wani ƙasaitaccen keken doki ya shigo cikin wannan daula ta Gorgon.
Shigowar wannan keken doki keda wuya, wata tauraruwa mai tsananin haske ta gilma ta cikin daular Gorgon.
Tun daga kan gari na farko na daular, har zuwa gari na ƙarshe saida wannar tauraruwa ta gilma ta samansu.
Babu wani mahaluƙi dake rayuwa a cikin wannan daula da baiyi arba da wannan tauraruwa ba.
Nan take komai dake daular ya fara sauyawa.
Fararen gajimare na haske suka fara bayyana, tsirrai suka fara fitar da farin

Please Login or Register in order to submit comment