Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan hukunci da sarki ya yanke?
"Idan kuwa hakane, mun sallame ku dukkan ku. Kuyi mana fatan nasara da samun abinda zamu tafi nema..."
Sarki Samudul Ansari na jin abinda Zarifa ta ce yayi murmushi ya dubi yan-majalisa ya ce, "Ku baiwa sarauniya Arya haɗin kai yadda ya dace, domin taji daɗin tafiyar da harkokin mulkinta kamar yadda ta saba.
"Duk wanda a cikin ku, ya saɓawa umarninta ko kuma yayi wani abu wanda zai taɓa kimar wannan daula, a duk inda nake a faɗin duniya zan gani sannan zan dawo na yanke masa hukunci..."
Yana gama faɗin haka, ya miƙe tsaye ya fidda hular sarautar dake kansa sannan ya ɗaurata akan sarauniya Arya.
Dukkan waɗannan yan-majalisa dake wannan wuri suka zube a gabanta suka yi mubaya'a.
Ba tare da ɓata lokaci ba, sarki Samudul Ansari ya sallame su, sannan ya basu umarnin su sanar da duk wani mahaluƙi dake wannan daula.
Ƴan-majalisar suka zube a gabansa, suka tabbatar masa da cewa zasu cika wannan umarni. Daga bisani duk suka miƙe suka fice daga fadar.
Sarki Samudul Ansari, sarauniya Arya da Zarifa suka yi hawa suka fice daga wannan fada, suka tunkari dajin Ƙaiz inda boka Ƙaizadu yake domin su yi bankwana dashi.
Bayan shafe tafiya ta kwanaki uku, suka shigo cikin wannan daji.
Ƙaizadu da kansa ya bayyana ya tarye su sannan ya kaisu cikin fadar sa.
Ba su ɓata wani lokaci ba, Ƙaizadu ya fiddo taswirar da zata kaisu har cikin birnin Irashnur ya baiwa Samudul Ansari.
Ƙaizadu ya samar da irin waɗannan dawakai nasa, masu kofaton haske da idanuwan haske guda biyu, sarki Samudul Ansari ya hau kan guda, Zarifa ta hau kanta.
Sarauniya Arya ta riƙe hannun sarki Samudul Ansari idanuwanta a cikin nasa ta ce, "Zan riƙe amanar wannan daula, zan tafiyar da komai kamar yadda ka saba. Fatana shi ne ku sami nasara akan abinda zaku tafi nema..."
Sarki Samudul Ansari ya ce, "Ya ke matata! Nayi miki alƙawari tsahon lokacin da zan shafe a wannan tafiya, ba zan taɓa mantawa dake ba. Za ki kasance a cikin zuciyata. Wannan alƙawari ne."
Bayan gajeren lokaci suka yi sallama da juna, Samudul Ansari da Zarifa suka tunkari hanyar da ta nufi yamma domin nan ne wannan taswira ta nuna.
Tun su Ƙaizadu suna hango su, har sai da suka ƙule a cikin ƙungurmin daji.
"Ina taya ki, farin ciki..." Ƙaizadu ya faɗawa sarauniya Arya.
Cikin rashin fahimta sarauniya Arya ta dube shi ta ce, "Farin ciki? Na me kenan?"
Ƙaizadu ya ce, "Ba zan iya sanar dake a yanzu ba, amma nan gaba kaɗan za ki fuskanci hakan..."
Arya ta haɗe fuska ta ce, "Idan ka san baza ka faɗa min ba, mene ne dalilin da zai sa ka faɗa min?"
Ƙaizadu ya ce, "To ai ni umarni na bi... Kada ki damu sarauniya gagarumin abin farin ciki ne... Za mu ci gaba da saka idanu a daular nan, domin taimaka miki..."
Ƙaizadu na faɗin haka, ya shige cikin wannan kogon dutse nasa.
Sarauniya Arya tayi shuru tsahon daƙiƙu masu yawa tana tsaya tana tunani, kafun ta juya ta nufi hanyar komawa gida.
****
Sarki Samudul Ansari da Zarifa suka yi ta gabza azababben gudu a cikin daji, suka yi ta ratsawa ta cikin dazuzzuka kala daba-daban.
Saboda tsananin kwarjinin sarki Samudul Ansari babu wanda ke kawo musu hari.
Komai yawan yan-fashi da hatsabibanci irin na aljanu da zarar sun jiwo ƙamshin Samudul Ansari suke guduwa.
Zarifa ta cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda waɗannan dawakai nasu suke zabga azababben gudu.
Gifta wajaje suke tamkar kibiyar da aka harba.
Wani abin da ya bata mamaki shi ne, duk ƙarfin gudun waɗannan dawakai, ko kaɗan iska bata damunsu, hakan ne zai basu damar tattaunawa cikin nutsuwa.
Abinda ya sake bata mamaki shi ne, duk ƙarfin wadannan dawakai ace sai sun shekara goma kafun su je inda birnin Irashnur yake?
To wai shin wannan birni wanne irin nisa ne da shi?
Zarifa ta dubi Samudul Ansari ta ce, "Ammafa sarauniya Arya ta bani mamaki, ban taɓa tunanin zata amince ta barmu muyi wannan tafiya tare ba,"
Samudul Ansari yayi murmushi ya ce, "Wannan ai ba wani abu ne a wajenta ba, shin kin manta nace miki ita ce ta kula da babana sa'adda muke gudanar da bincike ni da Abu-Sharjas..."
Zarifa ta gyaɗa kai ta ce, "Lallai sarauniya Arya mace ce mai cikakken adalci..."
Samudul Ansari ya ja linzamin dokinsa ya tsaya a lokacin da suka zo bakin wani ƙaramin tafki, cikin tsananin mamaki itama Zarifa ta tsayar da dokinta sannan ta dube shi tace.
"Mene ne dalilin da yasa ka tsaya, alhalin na tabbatar da cewa, waɗannan dawakan namu zasu tsallake wannan tafkin?"
Samudul Ansari ya zaro wannan taswira wadda Ƙaizadu ya bashi ya warwareta.
"Wata shawara na yanke a zuciyata yanzu. Ba mu san inda muke dosa ba, meye zai hana mu duba wannan taswira domin ganin ko akwai wani babban birni a gaba?"
Zarifa ta ce, "Wannan shawara ce mai kyau." ta ƙarasa kusa da Samudul Ansari ta tsaya.
Ita da sarki Samudul Ansari suka fara duba wannan taswira.
Daga wannan waje da suke tsaye, akwai wani babban kogi acan gabansu wanda bai wuce tafiyar wuni guda daga wajen ba.
Kogi ne ƙatoton gaske wanda zasu iya kwanaki uku, kafun su fita daga cikinsa.
"Kin ga duba wannan taswira yayi amfani ko? Yanzu sai mu sari itace a cikin wannan daji mu sassaƙa jirgin ruwa..." inji Samudul Ansari.
Zarifa ta gyaɗa masa kai.
Samudul Ansari ya zaro Saif-Al-Barzaƙ ya sari wata ƙatuwar bishiya dake can gefensu.
Bishiyar tana da kauri sosai tamkar bishiyar kuka, amma saran Saif-Al-Barzaƙ guda ɗaya ya rabata daga ƙasa ta faɗi a gefe guda rikica.
Samudul Ansari ya dubi Zarifa ya ce, "Na umarce ki, ki je bakin wannan kogi ki jira ni, zan taho. Ina so na sassaƙa wannan kwale-kwale..."
Zarifa ta gyaɗa kai sannan ta sukwani dokinta da gudu ta nufi hanyar wannan kogi.
Tafiyarta keda wuya, wani gagarumin baƙin hayaƙi ya lulluɓe wannan waje gaba ɗaya.
Abin mamaki, wannan baƙin hayaƙi daga cikin idanun sarki Samudul Ansari yake fitowa.
Baƙin hayaƙi na gama gauraye ko'ina siffar tau'rin ta bayyana.
Tau'rin ya zube a gaban Samudul Ansari ya kwashi gaisuwa.
A hasale Samudul Ansari ya dube shi ya ce, "Meyasa zaka bayyana alhalin ban baka umarnin bayyana ba?"
Tau'rin ya ce, "Ka gafarce ni, ya shugabana! Na bayyana ne domin na samar maka da jirgin ruwan da za ku ratsa wannan kogi a cikinsa, sannan na baka labarin ƁOYAYYEN HADIMI,"
"Jirgin ruwa kuma?" inji Samudul Ansari. "Nima zan iya ƙerawa ai,"
Tau'rin ya ce, "Ya shugabana! Shin kana tunanin wannan kogin ƙarami ne? Ai na faɗa ma, sai kun shafe wata bakwai ku na tafiya a cikinsa sannan za ku iso gaɓa.
"Duk kwale-kwalen da zaka ƙera daga irin bishiyoyin wannan daji, ba zasu yi ƙwarin da zai kai wata bakwai suna tafiya a ruwa ba, ba tare da sun lalace ba.
"Kwale-kwalen da na taho ma da ita, da ƙarafu aka ƙera ta..."
Samudul Ansari ya yi gajeren tunani ya ce, "To, na ji. Wane ne ƁOYAYYEN HADIMIn da kace zaka bani labari a kansa?"
Tau'rin ya ce, "Sarkin birnin Jai'zin - aljani ɗan ƙabilar Zas."
Samudul Ansari ya haɗe fuska ya ce, "Shi bai yi da suna ne? Ta ya ya aka yi ka gane zai haɗu dani, alhalin muna tare?"
Tau'rin ya ce, "Duk duniya, ni ne kaɗai nafi shi ƙarfin sihirin tsafi. Jiya-jiyan ya turo min cewa, yana so ya gana da kai, domin ya zamo hadiminka wanda zaiyi maka aiki amma a sirrance."
Samudul Ansari ya ce, "Aiki a sirrance, kamar ya ya kenan?"
Tau'rin ya ce, "Idan ka haɗu dashi zaiyi maka bayanin komai, amma ya tabbatar min da cewa kafun ka fita daga cikin wannan kogi, zai bayyana..."
Tau'rin na gama faɗin haka, jikinsa ya saje a cikin wannan baƙin hayaƙi da ya kewaye wannan waje.
Sannu-a-hankali wannan baƙin hayaƙi ya soma shigewa cikin idanun Samudul Ansari, har sai da ya gama shigewa gaba ɗaya.
Komai na lafawa yayi arba da wata kwale-kwale wadda aka ƙera da farin tagulla a nesa kaɗan da inda yake tsaye.
Jirgin ruwan baida girma sosai domin ba zai wuce mutum huɗu kacal! zai iya ɗauka ba.
Samudul Ansari ya dafa jirgin ruwan, wannan baƙin hayaƙi ya lulluɓe shi sannan ya ɓace ɓat!
Cikin gaggawa ya haye kan wannan doki sannan ya zabure shi da gudu ya nufi bayan Zarifa.
Bayan doguwar tafiya, ya hango Zarifa zaune a gaɓar kogi ta ƙurawa ruwan cikinsa idanu.
Samudul Ansari na ƙarasowa inda take ta dube shi, taga babu wani kwale-kwale sai ta cika da tsananin mamaki.
Kafun ta buɗi baki ta tambaye shi, Samudul Ansari ya buɗe hannayensa biyu, wannan baƙin hayaƙi ya sake bayyana.
Baƙin hayaƙin yana ɓacewa wannan jirgin ruwa ya bayyana.
Ya ɗauki jirgin ruwa ya saka a cikin kogin, sannan ya saka dawakansu ma.
Ya baiwa Zarifa umarnin shigowa cikin jirgin, shima ya shiga.
Nan take wannan jirgin ruwa ya soma tsala azababben gudu a cikin kogin.
Zarifa tana so ta tambaye shi amma ganin cewa, yayi shuru baice da ita komai ba, sai tayi shuru kawai.
Suka ci gaba da tafiya a cikin wannan kogi, kwana da kwanaki, amma ko alamun gaɓa basa hangowa.
Abin mamaki, akwai wani akwatin abinci guda ɗaya a cikin wannan jirgi, wanda suke samun duk abinda suke buƙata.
Saboda haka basu da matsalar abinci.
"Za mu yi tafiya mai tsaho akan wannan kogi," inji Samudul Ansari.
Zarifa ta dube shi cikin mamaki ta ce, "Tsahon kwanaki nawa kenan?"
"Watanni dai," inji Samudul Ansari.
Cikin mamaki Zarifa ta ce, "Wanne irin kogi ne wannan?"
Samudul Ansari ya ce, "Waye ya sani, amma ga dukkan alamu, da wuya a samu wanda zai kaishi girma a duniya..."
Haka dai Samudul Ansari da matarsa Zarifa suka yi ta tafiya a cikin wannan kogi suna tattaunawa, lokaci-lokaci suna yada zango a ƙananun tsibirurruka har tsahon watanni shida.
A ranar da suka cika wata na shidan ne, da tsakiyar rana, wani gagarumin abin al'ajabi ya soma afkuwa cikin wannan kogi.
Rana ta disashe a cikin wani gajimare, sanyi mai ratsa ƙashi ya soma busowa wanda yayi sanadiyar sumewar Zarifa.
Wannan sanyi ya wuce misali, cikin ƙanƙanin lokaci dusar ƙanƙara ta soma zubowa wadda tasa ruwan wannan kogi daskarewa.
Abin mamaki duk tsananin wannan sanyi, bai yiwa Samudul Ansari komai ba, kai kace ba a wajen yake ba.
Sannu-a-hankali wannan dusar ƙanƙara ta soma juyewa izuwa fara ƙal, ta cika wajen, ya zamana babu abinda mutum zai kalla idan ba farin ta ba.
Jim kaɗan, wani sadaukin aljani ya bayyana wanda ya rufe fuskarsa ta farin rawani mai kama da irin kayan da suke jikinsa.
Akwai wani irin iko na musamman dake tashi a jikin wannan aljani, wanda ba don Samudul Ansari ya gawurta ba, da ba zai iya tsayawa a gabansa ba.
Kasancewar ya rufe fuskarsa da farin rawani, Samudul Ansari bai gane wane ne shi ba.
Aljanin ya tako da sawayensa yazo har gaban Samudul Ansari sannan ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa.
"Ya shugaban sarakunan duniya! Ni dan ƙabilar Zas ina so nayi maka aiki, amma a sirrance, ina so aikin ya kasance tsakanina da kai kawai."
Samudul Ansari na jin haka ya ce, "Ance zaka yi min bayanin yadda ayyukan da zaka na yi min zasu kasance, faɗa min ina jin ka..."
Wannan aljani na jin haka ya zayyanewa Samudul Ansari yanayin yadda ayyukansu zai kasance. Idan ba shi da Samudul Ansari babu wanda yasan abinda suka tattaunawa.
Samudul Ansari na gama jin bayanan aljanin, ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Lallai zan yi alfahari da kasancewa tare da kai,"
"Godiya a gareka bisa fahimta ta da kayi..."
Wannan aljani na gama faɗin haka ya ɓace ɓat!
Wannan farin ƙanƙara da ya bayyana ya soma narkewa a cikin wannan ruwan kogi, sannu-a-hankali har ya gama narkewa.
Wannan baƙon sanyi da ya bayyana, ya yaye a hankali.
Samudul Ansari ya watsawa Zarifa ruwa a fuska ta farfaɗo, cikin tsananin mamaki ta dube shi ta ce, "Mene ne abinda ya faru a wannan waje?"
"ƁOYAYYEN HADIMI ya bayyana, kada ki tambaye ni waye shi, domin ba zan bayyana shi daga yanzu ba,"
Yana gama faɗin haka ya mayar da hankali akan tuƙin wannan jirgi, ba tare da tsaya sauraron wani abinda zata ce ba.
*****
Yau *25/03/2023*
Babi na gaba zaizo *27/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 103: *Sarki Buƙalshiyyu Djinn*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra, da fatan kun sha ruwa lafiya.
*
UMS
*
Bayan gajeriyar tafiyar jirgin ruwan Samudul Ansari ya isa bakin gaɓar wannan kogi, cikin gaggawa shi da Zarifa suka fito daga cikin kogin, sannan suka fiddo dawakansu.
Samudul Ansari yayi amfani da wannan baƙin hayaƙi ya ɓatar da wannan jirgin ruwa sannan ya hau kan dokinsa ya baiwa Zarifa ma umarnin hawa.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, suka shige cikin ƙaton dajin dake gabansu cikin azababben gudu.
Kamar yadda suka saba ratsa dazuzzuka haka suka ɗinga ratsa dazuzzukan dake gabansu.
Ƴan-fashi da hatsabiban aljanu ko kyakkyawan kallo basa yi musu suke giftawa ta gefensu.
Suka ci gaba da tafiya har tsahon shekara uku, sannan suka iso wani waje mai yawan farar ƙasa.
Iya ganin mutum wannan waje, farar ƙasa ce iya hangenka.
Samudul Ansari yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak! a farkon wannan farar ƙasa, cikin sauri Zarifa tayi koyi da shi.
Samudul Ansari ya zaro wannan taswira dake cikin aljihunsa ya warwareta sannan ya fara duba daidai inda suke.
A jikin wannan taswira an zana wannan farar ƙasa sannan tana da tsananin yawan gaske, mutum zai iya cewa harma tafi wannan kogi da suka shafe watanni bakwai suna tafiya a cikin sa girma.
Samudul Ansari ya haɗe fuska sannan ya warware wannan taswira gaba ɗaya.
Abinda ya bashi mamaki shi ne, daga wannan waje da suke tsaye har zuwa inda wannan taswira ta ƙare, wannan farar ƙasa ce ta mamaye ko'ina.
Samudul Ansari ya sa hannunsa guda ya damƙo farar ƙasar sannan ya shinshina ta a hancinsa.
Cikin tsananin mamaki ya dubi Zarifa ya ce, "Wannar ƙasar ba sahara ba ce, sannan ba yashi bane. Tabbas akwai yiwuwar cewa duk duniya, idan ba wannan wajen ba, babu inda mutum zai sami irin wannan ƙasa..."
Zarifa ta ce, "Hakan yana nufin mun shigo wani yanki dabam kenan?"
Samudul Ansari ya gyaɗa mata kai.
"To amma ina ne?" ta sake tambayar sa.
Samudul Ansari ya sake duba wannan taswira dake hannunsa.
"Akwai yiwuwar daga wannan farar ƙasa zamu soma shigowa cikin daular Irashnur..."
Yana faɗin haka ya sake hawa kan dokinsa, sannan ya sukwane shi ya shiga cikin wannan farar ƙasa.
Saida yayi tafiya ta taku talatin sannan ya baiwa Zarifa umarnin biyo bayansa.
Cikin gaggawa ta take masa baya, suka jera sannan suka yi ta tafiya.
Iya rayuwar Samudul Ansari da Zarifa basu taɓa shigowa irin wannan waje ba, sai fa yau.
Farar ƙasar tana da ban al'ajabi. Ba ta sakawa waɗanda ke cikinta ƙishirwa kamar sahara.
Saɓanin cikin sahara akwai iska mai sanyi dake kaɗawa a cikinta wadda take baiwa wadanda suke kanta ni'ima.
Abu ɗaya ne kawai yasa take kama da sahara. Kamar yadda mutum zaiyi arba da sahara a shimfiɗe iya-hange, itama haka take.
Samudul Ansari da Zarifa suka ci gaba da zabga azababben gudu a cikin wannan farar ƙasa.
Saida suka shafe wata uku cir! suna tafiya a cikin wannan farar ƙasa, sannan suka fara hango waɗansu irin manyan tsaunika a can nesa.
Cikin mamaki Zarifa ta dubi Samudul Ansari ta ce, "Kaga waɗansu irin tsaunika can? Iya rayuwata ban taɓa ganin masu girma da tsaho kamar su ba."
Samudul Ansari ya ɗaga idanunsa na tau'rin ya hanga izuwa tsaunikan suke.
"Wa ya faɗa miki wadancan abubuwan tsaunika ne?" ya faɗawa Zarifa.
Zarifa tana jin haka, jikinta ya fara tsuma.
Ta fara ayyanawa a ranta cewa, kada dai ace waɗancan abubuwan da take hangowa su ne aljanu dangin duwatsu.
Samudul Ansari ya sake dubanta ya ce, "Ga dukkan alamu, wannan farar ƙasa yanki ne daga cikin yankunan daular Irashnur.
"Waɗancan tsaunikan da kike hangowa, ba duwatsu bane kamar yadda kika yi tsammani. Gangunan jikin waɗannan halittu ne."
Ai kuwa Zarifa tana jin abinda yace, jikinta ya soma karkarwa razana.
Komai ƙarfinka da ƙarfin shirinka, baka isa kayi yaƙi da duwatsu ba. Saboda sara da suka baya tasiri akansu, sannan basu da jini wanda zai sa su gaji a yayin gwabza yaƙi.
Waɗannan halittu da Zarifa take hangowa basu da bambanci da duwatsu.
Ko ta ya ya zasu yi yaƙi dasu?
Samudul Ansari ya bata umarnin ci gaba da tafiya domin ƙarasawa inda waɗannan tsaunika suke.
Cikin sanyin jiki Zarifa ta sakarwa dokinta linzami ta bi bayansa.
Ba tare da tsoro ko shakkun komai ba, Samudul Ansari ya tunkari inda waɗannan halittu suke tsaitsaye cikin azababben gudu.
Zarifa ta take masa baya amma a wannan lokaci, bata yarda sun jera ba.
Bayan doguwar tafiya ta kimanin taku ɗari biyu da ɗoriya, Samudul Ansari da Zarifa suka iso gaban waɗannan halittu da suke hangowa a nesa.
Kamar yadda Samudul Ansari ya faɗawa Zarifa haka halittun suke, wato gaba ɗaya jikinsu da duwatsu aka halicce su.
Halittun dogwaye ne sosai sannan suna da tsananin faɗi. Idanuwansu jajazur tamkar wuta ke ruri a cikinsu.
Samudul Ansari na isowa gabansu, yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak!
Aljanun dake tsaye a wannan waje guda goma ne kawai. Dukkansu suka ƙurawa Samudul Ansari da Zarifa idanu kawai ba tare da sun ce dasu komai ba.
Koda suka ga Samudul Ansari da Zarifa sun ja linzaman dawakansu sun tsaya, sai suka matso kusa da su.
"Su wane ne ku!" inji wata murya mai tsananin kaushi tamkar aradu.
Wannan yare da suka yi magana dashi, Samudul Ansari da Zarifa basu taɓa jin mai kama da shi, amma kalmomin suna shiga kunnuwan tau'rin ya fassarawa Samudul Ansari abinda suka ce.
"Daga wannan waje da muke, tafiyar kwana nawa ce ta rage mana mu isa birnin Irashnur, babban birnin ku?" inji Samudul Ansari.
Abin mamaki da asalin harshensa yayi maganar amma tana fita daga bakinsa ta juye izuwa irin harshen waɗannan halittu.
Halittun suna jin abinda ya ce, suka fizgo waɗansu manya-manyan duwatsu dake kewaye dasu.
Nan take duwatsun suka juye izuwa zabga-zangan takubba masu tsaho da nauyin gaske.
A fusace halittun suka kewaye Samudul Ansari da Zarifa.
"Shigowa cikin wannan farar ƙasar kawai laifi ne, balle kuyi ikirarin zuwa babban birnin Irashnur inda sarki Buƙal yake mulki..." inji ɗaya daga cikin halittun.
Samudul Ansari yayi murmushi sannan ya zaro takobinsa ta Saif-Al-Barzaƙ.
Bayyanar Saif-Al-Barzaƙ a wannan waje yasa ƙasa gaba ɗaya tayi girgiza, gagarumar ƙura ta turnuƙe ko'ina.
Waɗannan halittu suna ganin haka suka kwarara uban ihu, suka ruga da gudu kan Samudul Ansari.
Takun sawun ƙafarsu guda bisa wannan farar ƙasa na haifar da gagarumar ƙura wadda ta ninka ta Samudul Ansari sannan ƙasar wajen gaba ɗaya ta fara girgiza kamar zata rufta ciki.
Cikin gaggawa Samudul Ansari ya kamo Zarifa sannan ya goyata a gadon bayansa saboda wannan gumurzu yafi ƙarfinta.
Halittun suna isowa inda Samudul Ansari ke tsaye suka fara kawo masa mahaukatan sara da suka da waɗannan takubba nasu.
Samudul Ansari ya shiga kaucewa cikin zafin nama wanda yafi gaban misali.
A duk lokacin da suka kawo masa sara ko suka ya kauce, idan suka sami wannan farar ƙasa sai dai mutum yaga wawakeken rami ya bayyana.
Kafun a jima wannan waje da suke ya soma cika da ramuka masu girma da faɗi.
Suna tsakiyar fafatawa tau'rin ya dakawa Samudul Ansari tsawa.
"KAIFA SARKI NE, AKAN WANNE DALILI ZAKA TSAYA ƁATA LOKACI AKAN WAƊANNAN ƘANANUN HALITTUN? HARINKA GUDA KAWAI ZAI GAMA DA DUKKANSU!"
Tau'rin yana gama faɗin haka ya dafa takobin Saif-Al-Barzaƙ dake hannun Samudul Ansari.
Wannan baƙin hayaƙi wanda ke tashi daga jikinsa ya shiga cikin ƙarfen takobin.
Samudul Ansari na ganin haka ya juya ya kaiwa waɗannan halittu guda huɗu dake tsaye a ɓangaren dama sara.
Waɗansu irin ƙananun takubba masu shegen tsini suka fice daga tsinin takobin nasa, suka cake waɗannan halittu guda hudu.
Nan take jikin halittun ya soma tsatstsagewa yana kumbura, basu san sa'adda suka fara kwarara wani irin uban ihu ba.
Jikin nasu na gama tsatstsagewa suka soma tarwatsewa suna bin iska.
Sauran guda shidan na ganin yan-uwansu sun mutu, suka rugo kan Samudul Ansari.
Sai dai kafun su iso tuni ya aikata musu abinda ya aikatawa yan-uwansu.
Gaba ɗaya gangunan jikin waɗannan aljanu yana gama rushewa, Samudul Ansari ya mayar da takobinsa cikin kufe.
Yana mayar da takobin cikin kufe, ya sauƙar da Zarifa ƙasa daga gadon bayansa wadda a wannan lokaci ta daɗe da sumewa.
Samudul Ansari ya watsa mata ruwa ta farfaɗo.
Cikin tsananin mamaki ta ɗaga kanta sama, ko zata ga waɗannan halittu amma babu su.
"Ta shiga mu ci gaba da tafiya, mun shigo daular Irashnur!" inji Samudul Ansari.
Zarifa ta dube shi cikin mamaki ta ce, "Wai kana nufin ka hallaka waɗannan halittu gaba ɗaya..."
Samudul Ansari yayi murmushi ya miƙa mata hannunsa guda ya ta riƙe ta taso tsaye, ya hau kan dokinsa sannan itama ya ce ta hau.
"Wannan tambaya ta ki bata buƙatar amsa. Mun shigo daularsu, inda za ki gaji da kallon mutuwar su..." inji Samudul Ansari lokacin da ya kaɗa linzamin dokinsa ya nufi cikin wannan farar ƙasa dake gabansu.
Cikin gaggawa Zarifa ta take masa baya.
****
A can wani wuri kuwa, kimanin tafiyar zango huɗu daga wannan waje dasu Samudul Ansari suke, wani zabgegen aljani ne zaune akan wani gajeren tsauni.
Gaba ɗaya jikin aljanin da duwatsu aka halicce shi.
Sai dai duwatsun suna da ban al'ajabi. Suna bayar da launin ƙanƙara, sannan gagarumin tiriri

Please Login or Register in order to submit comment