Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iso gwiwowin ƙafafuwansa yasa suka yi sanyi ainun.
Aymanul Faris ya tafi ƙasa zai faɗi akan gwiwowinsa amma sai ya dake. Ba wai yin kansa bane, wata ƙatuwar murya ce ta daka masa tsawa.
"KAI SARKI NE! SARKI BAYA TAƁA DURƘUSAWA!!!"
Wannan shi ne karo na farko da Aymanul Faris yaji muryar wannan ruhi tayi masa magana.
Nan take Aymanul Faris ya girgije ya miƙe tsaye dukda cewa kuwa layi yake kamar zai faɗi.
Koda waɗannan mutane guda uku hatsabibai suka ga haka, sai suka haɗu a waje guda sannan suka haɗe takubbansu.
Takobin Bankai mai mataki na ɗari da talatin da shida ta bayyana.
Wannan shi ne lokaci na farko da aka taɓa bayyanar da takobin Bankai mai mataki sama da na ɗari.
BES ta kaiwa iska sara da wannan takobi.
Babu faifai babu alamun fitar hari, amma sai sassa da dama na jikin Aymanul Faris suka yi alamun kore-kore.
Kafun ya ankara yayi wani yunƙuri tuni sassan jikinsa suka fara guntulewa suna zubewa ƙasa.
Hannayensa suka zube ƙasa, ƙafafuwansa ma haka.
Ransa na daf da fita kenan, baƙin hayaƙi ya cika wannan waje.
BES da wadannan ma'abota Bankai suna ganin haka, suka juya da baya suka falfala da azababben gudu.
Kafun su isa ƙarshen wannan tsauni, Aymanul Faris ya miƙe tsaye cikin ƙoshin lafiya.
Tau'rin ya miƙa hannunsa guda ya damƙi ƙarfen Saif-Al-Barzaƙ. Baƙin hayaƙi ya fito daga hannunsa ya shiga ƙarfen takobin.
Aymanul Faris ya aika musu mugun saran takobi-mai-tafiya.
Ƙatoton faifai baƙi ƙirim ya fice daga takobin yayi kansu da gudu.
Waɗannan ma'abota Bankai guda biyu su ne a bayan BES, saboda su Saif-Al-Barzaƙ ta fara kashewa.
Saura ƙiris ya fille kan BES ta faɗa ƙasan wannan tsauni.
Aymanul Faris yayi murmushi ya mayar da takobinsa cikin kufe, ya tunkari cikin wannan gidan bauta.
Yana shigowa gidan bautar yayi arba da tukwanen sinadarai kala daban-daban.
A jikin kowacce tukunya akwai rubutu wanda ke nuna abinda ta ƙunsa.
Anyi rubutun ne da yaren wannan daula wanda Aymanul Faris bai taɓa gani ba.
Nan take ya fara tunanin ta ya ya zai gane tukunyar dake ɗauke da sinadarin Yirlish?
Yana cikin dube-dube idanuwansa suka kai kan tukunyar farko. Wani aminci yazo ransa.
Irin amincin da yaji sa'adda ya kalli waɗannan furanni da suka tsinko a lambun Gotohn waɗanda suka bayyanar da asalin kyawun Arya.
Aymanul Faris yasa hannunsa guda ya dauki wannan tukunya sannan ya juya zai fita daga.
Nan take yayi arba da yarima Marganu a ƙofar shigowa wannan gida yana yi masa murmushin mugunta.
Aymanul Faris ya zaro takobin Saif-Al-Barzaƙ zai afkawa Marganu amma sai wannan hatimi dake bayan wuyansa ƙasan gashin kansa ya fara ɗaukar zafi sosai.
Kafun ya sake wani motsi tuni jikinsa ya juye izuwa na aljanin-wuta.
Idanun Aymanul Faris suka fara ci da wuta, gashin kansa ya soma fitar da jan hayaƙi. Kayan jikinsa suka koma baƙaƙe ƙirim suna bayar da launin wuta.
Kafun Marganu yayi wani motsi, Nara ya bayyana a gaban Aymanul Faris ya caka manya-manyan hannayensa cikin wannan tsauni.
Take wawakeken rami ya bayyana, ya busa wuta cikin wannan rami, sannan shi da Ayamnul Faris suka faɗa cikin ramin.
Gangunan jikinsu suna haɗuwa da wutar ramin, suka ɓace ɓat!
Marganu ya kwarara uban ihu ya ce, "SAI NI DODON MAZA, MAI SA ƘANANU SU GUDU."
****
Yau *05/06/2023*
Babi na gaba zaizo *08/06/2023* da izinin ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 135: *Cuta da magani*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S.
*
Har a wannan lokaci gimbiya Jaanu tana kwance akan wannan gado lulluɓe a cikin wannan bargo.
Dukda cewa ƙwararriyar likita Laziyya tayi mata aiki mai kyau amma har a wannan lokaci barci take.
Tun da Aymanul Faris yayi wannan tafiya kullum jaruma Riya tana kusa da Jaanu tana kula da ita.
Duk wata buƙata ta gimbiya Jaanu jaruma Riya ce ke yi mata.
Hakan ne ya yi matuƙar burge Hajriya tayi ta godewa Ubangiji da ya basu Riya.
Dukda cewa ta san nan gaba sai Aymanul Faris ya auri Jaanu amma hakan bai dameta ba.
Saboda ta san cewa wannan hali da gimbiya Jaanu ta tsinci kanta a ciki, tana buƙatar kulawa ta musamman.
A wannan rana jaruma Riya tana zaune a gefen Jaanu tana kallonta, bisa mamaki taga Jaanu ta buɗe idanunta.
Cikin tsananin farin ciki Riya ta ƙarasa kusa da Jaanu ta dafa hannunta guda, wai ko zata buɗe idanunta tayi magana.
A daidai wannan lokaci da jaruma Riya take mamaki bisa farfaɗowar Jaanu, acan falon wannan gida kuwa, sarki Ranganu tare da Barban suke tattaunawa.
Ranganu yana zaune kusa da Barban yana nuna masa hoton wata hular sarauta mai sheƙi da walwali.
"Wannan hular sarauta ita ce wadda zamu sakawa Aymanul Faris a ranar da zamu rantsar dashi a matsayin sabon sarkin daular Shaha.
"Inda aka yi rashin sa'a shi ne, wannan hula tana can daular Nehiya ƙarƙashin mugun tsaro irin wanda bamu taɓa ganin irinsa ba.
"Wannan hular sarauta ita ce, abinda zamu sato na bakwai daga cikin jerin wajibabbu.
"Yanzu haka Aymanul Faris ya samo maganin wannan dafi wanda ke yawo a cikin jikin gimbiya Arya. Nan da ɗan ƙanƙanin lokaci zai ƙaraso.
"Idan aka yiwa gimbiya Jaanu wanka da wannan magani, zata warke. Idan ta warke, bai wuce ta ƙara wata guda tana jinya ba, zata wartsake.
"A cikin wannan wata guda Aymanul Faris tare da jaruma Riya zasu je birnin Shaha su karya wadannan kafi waɗanda Samudul Ansari ya bibbinne.
"Idan suka kakkarya waɗannan kafi, zasu je yankin ƙasashen Jerawa da ƙasashen Hajarr su tabbatar musu da cewa, daular Shaha a shirye take domin sake ɗaukar su.
"Kayi sani cewa, idan ba ɗauke hankalin daular Nehiya muka yi ba, babu yadda za'ayi mu samu nasarar ɗauko wannan hular sarauta cikin sauƙi.
"A yanzu a imanin daular Nehiya da duk wani mahaluƙi dake rayuwa a cikin duniya shi ne, an kama Barban.
"Hakan zai sa su rinƙa fiddo wannan hular sarauta fili kowa ya ganta."
Barban yana jin wannan batu ya ce, "Wannan batu haka yake, ya shugabana. Tun sa'adda muka haɗu bani da buri wanda yafi ace na ɗauko wannan hular sarauta mai tsadar gaske.
"Babban abinda yafi ɓata min rai shi ne, yadda daular Nehiya suke baiwa wannan hula tsaro. Kai kace tun fil-azal tasu ce."
Ranganu yayi murmushi ya ce, "Wannan aiki shi ne babban aikin da zamu gudanar a cikin gaba ɗaya ayyukanmu. Wannan aiki har dani kaina zamuje domin gudanar dashi. Babban dalilin da yasa na ƙyale sarki Kuffuru, sa'adda ya yaudari su Hubbazu shi ne, hawa kan wannan karaga.
"Saboda idan ba sarki Kuffuru ne ya hau kan karagar ba, babu yadda za'ayi suna fiddo wannan hula ta daraja."
Barban ya ce, "Haka ne. Amma yaushe zamu je ɗauko wannan hula sannan ya ya tsare-tsaren ayyukan zasu kasance?"
Ranganu yana jin wannan batu ya nuna wannan takarda dake gabansu da hannunsa na hagu.
Nan take abinda ke kan takardar ya juye izuwa hoton wani kyakkyawan gini a tsakiyar wani tangamemen gidan sarauta.
Ginin yana da siffa da fasali kamar husumiya.
Ranganu yayi ta rage girman ginin da yatsunsa guda biyu.
Barban ya yi ta arba da rukuni-rukuni na dakaru wajen rukuni guda arba'in dake tsaron wannan dogon gini.
Gaba ɗaya waɗannan rukunai babu jinsin bil'Adama ko guda.
Dukkansu UMKAS ne, suna riƙe da mahaukatan makaman yaƙi irin wanda Barban bai taɓa kallo ba.
"Wannan dogon gini shi ne inda ake ajiye wannan hular sarauta, wadannan dakaru kuma, su ne masu tsaron hular.
"Duk faɗin daular Nehiya, babu zaƙwaƙuran dakaru, masu baƙin naci da iya yaƙi kamar waɗannan dakaru dake tsaron wannan hular sarauta.
"Hatta ni kaina ba zan sami nasara akan waɗannan dakaru ba, idan nace zamu yi fito-na-fito.
"Saboda haka nayi zama na musamman na tsara yadda wannan aiki zai kasance.
"A duk ƙarshen shekara irin wannan lokaci, daular Nehiya tana tura manyan hadimanta izuwa kasuwannin bayi na duniya domin su sayo musu bayi masu hikima da basira.
"Saboda kada abokan gaba su gano yadda ake gina wannan husumiya yasa daular Nehiya take samo samun ƙwararrun bayi ta basu horon gini na musamman.
"Idan aka gama basu wannan horo, sai a kaisu wajen da za'a gina wannan husumiya.
"Idan suka gama gina wannan husumiya sai a kashe su don kada su bawa wani labarin yadda aka gina husumiyar.
"A ƙarfin sihirin tsafina zan iya juyar da jikinmu izuwa irin na magina, yadda zamu ja hankalin wadannan hadimai na daular Nehiya.
"Waɗannan hadimai zasu saye mu, sannan zasu kaimu wajen da za'a bamu horo. Idan aka bamu horo, washe garin ranar da za'a kaimu wajen wannan gini ne. Ni da kai zamu saci jiki mu shiga cikin wannan husumiya, mu ɗauki wannan hular sarauta.
"Dukda cewa zamu iya sace wannan hular sarauta amma bamu isa mu bar wajen da take babu komai ba, dole zamu ajiye hotonta wanda zai sa dakarun wajen ba za su ankara ba.
"Zan ɓoye wannan hular sarauta a jikina, mu je mu sake gina musu wata sabuwar husumiyar.
"Da zarar aka gama kammala gina wannan husumiya, za'a wuce damu wajen da za'a kashe mu.
"Yadda wani aljani ɗan daular Nehiya ya bani labari shi ne, a bakin wani ƙaton tafki ake kashe waɗannan ma'aikata da suka gina sabuwar husumiya.
"A wannan waje ne, ni da kai zamu daka tsalle mu faɗa cikin wannan tafki.
"Dakarun dake wajen zasu yi tunanin biyo bayanmu.
"Kasancewar ba dukkansu ne suka iya ruwa ba, sannan wannan tafki wanka a cike yake da jini da ƙwarangwal ɗin mutane. Duk wanda a cikinsu ya biyo bayanmu zan iya kashe shi.
"Idan muka yi nutso mai zurfin gaske a ƙarƙashin wannan tafki zan iya juyar da jikina izuwa na jibgegen kifi na tseratar damu.
"Bayan sa'a guda da guduwar mu zasu ankara da an sace wannan hular sarauta, hakan zai sa dukkan wani mahaluƙi dake daular Nehiya hankalinsa yayi mummunan tashi.
"Wannan hula ita ce abar dogaronsu, saboda tana da wani babban sirri na musamman.
"A duk inda wannan hula take, akwai ƙarfin mulki a wajen, sannan babu batun tashin hankali ko kuma hatsaniya.
"Wannan na daga cikin dalilan da suka sa, har gobe ba'a ci daular Nehiya da yaƙi ba.
"Babban dalilin da zai sa mu sato wannan hula shi ne, saboda Aymanul Faris yaji daɗin samun nasara akan Kuffuru a yayin da zasu gwabza yaƙi."
Barban yana jin wannan batu yayi murmushi ya ce, "Lallai idan muka yi wannan shiri da kace, sai mun sami nasara. Wannan yasa nake jin daɗin haɗa kai da kai saboda tsananin lissafinka da ƙarfin ƙwaƙwalwarka."
Ranganu yayi murmushi ya ce, "Waɗannan ayyuka guda huɗu da suka rage, sun fi wahala sannan suna buƙatar nutsuwa da lissafi. Bari naje na taho da Aymanul Faris..."
Nan take suka yi sallama da Barban.
Ranganu ya miƙe tsaye yayi girgiza ya ɓace ɓat daga wannan waje.
*****
Marganu yana gama kwarara wannan uban ihu nasa, ya daka tsalle ya faɗa cikin wannan rami wanda Aymanul Faris da Nara suka nutse a cikinsa.
Tun kafun Marganu ya iso wannan wuta dake ci a cikin ramin, ya nunata da takobinsa.
Sirrin haske mai haɗe da ƙanƙara ya fice daga takobin, ya kashe wannan wuta sannan ya daskarar da ita.
Marganu yana dira akan wannan ƙanƙara ya fara fasata da takobinsa yana yin ƙasa yana laluɓen Aymanul Faris.
Tun daga saman wannan wuta har zuwa ƙasanta duk ya daskare, saboda haka indai Aymanul Faris yana cikin wannan wuta sai ya kama shi.
Saida Marganu ya shafe sa'a uku cir yana fasa wannan ƙanƙara sannan yazo ƙarshenta, amma ko alamun su Aymanul Faris bai gani ba.
Yana fasa ɓangare na ƙarshe na wannan ƙanƙara, jikinsa ya zame ya faɗa cikin wani ƙaton teku.
Kafun Marganu ya ankara tuni ya nutse izuwa can ƙarƙashin wannan teku.
Nan take ya ƙaddamar da idanuwansa na haske sannan ya fara iyo a cikin wannan teku yana tasowa sama.
Kamar daga sama ya hango alamun mutum-mutum.
Cikin gaggawa ya tunkari abun, sannan ya ƙare masa kallo da wadannan idanuwa nasa.
Abinda ya fuskanta wannan abu da yake hangowa, mutum ne.
Kafun Marganu ya ƙarasa inda abin yake, yaga wani irin murgujejen kifi ya bayyana ya haɗiye mutumin.
Marganu da wannan kifi suka yi ido huɗu.
Kifin ya juya da baya ya fara tsala azababben gudu. Marganu ya take masa baya, yana so ya fasa cikin kifin ya ɗauko mutumin yaga wane ne.
Sai dai basu daɗe suna wannan tsere ba, kifin ya nuna cewa, KOWA A GIDANSA SARKI NE.
Kafun Marganu ya ankara tuni wannan kifi ya bashi tazara mai yawan gaske. Kan a jima kifin ya ɓace masa da gani.
Babu irin laluɓen da baiyi a ƙarƙashin wannan teku ba domin ya gano wannan kifi, amma ko alamunsa bai gani ba.
Bisa dole Marganu ya haƙura ya fice daga wannan teku.
Shi kuwa wannan kifi, cikin ƙanƙanin lokaci yayi gudu mai nisan gaske ya bar nahiyar wannan teku gaba ɗaya ya shiga wani tekun dabam.
Ya ci gaba da zabga azababben gudu har tsahon sa'a goma sha ɗaya sannan ya iso wani ƙaton tsibiri.
Kifin ya fito saman wannan tsibiri ya amayar da mutumin dake cikin cikinsa, sanna ya yi girgiza ya juye izuwa Ranganu.
Ranganu ya dafa Aymanul Faris da hannunsa guda, take Aymanul Faris ya buɗe idanuwansa.
Abinda ya fara laluɓa a jikinsa shi ne wannan tukunya, ai kuwa sai yaji tana nan.
Cikin tsananin farin ciki suka ƙarasa cikin birnin Darul Barban, sannan suka ƙarasa wannan gidan su Hajriya.
A guje Aymanul Faris ya ƙarasa cikin wannan ɗaki wanda aka kwantar da Jaanu.
Yana shigowa cikin wannan ɗaki yayi arba da jaruma Riya tana lulluɓawa Jaanu bargo.
Lamarin da yayi matuƙar burge shi kenan. Jaruma Riya ta rugo suka rungume juna, cikin tsananin farin ciki.
Aymanul Faris ya tambayeta ya ya jikin Jaanu.
"Da sauƙi," inji jaruma Riya.
Lokacin Ranganu da Barban suka ƙaraso cikin wannan ɗaki, sannan Hajriya ta biyo bayansu.
Aymanul Faris ya sake rungume Hajriya, tana mai tsananin farin ciki bisa ganinsa a raye.
Ranganu ya karɓi wannan kwalba ya ce, "Barkan mu da samun maganin wannan lalura da Arya ta tsinci kanta a ciki. Yanzu za'a yi mata wannan magani sannan mu jira zuwa kwanaki arba'in domin tabbatar da cewa, ciki bai shiga ba."
Aymanul Faris yana jin an kawo batun ciki, gabansa ya faɗi. Baya so koda wasa ciki ya shiga.
Ranganu yana gama wannan batu ya miƙawa likita Laziyya wannan tukunya sannan ya kira Aymanul Faris da Barban suka fice daga cikin ɗakin gaba ɗaya.
Laziyya ta tunkari wannan gado da Jaanu ke kwance akansa da wannan magani.
Tana zuwa ta yaye wannan bargo da ya lulluɓe Jaanu.
Ta saka jaruma Riya fidda duk wata sutura dake jikin Jaanu.
Nan take jaruma Riya tayi hakan.
Gimbiya Jaanu ta bayyana tsirara babu wani hijabi da ya rufe ko'ina a jikinta.
Jaruma Riya sai da ta cika da tsananin mamaki da tayi arba da surar gimbiya Jaanu, saboda ta ko'ina tayi.
Ga kyawun fuska, ga cikakken ƙirji, ga mazaunai masu tudu, ga manya-manyan cinyoyi da fararen sawaye.
Abinda kawai ya bata tausayi shi ne, ƙasan gimbiya Jaanu.
Dukda cewa wajen ya fara warkewa amma har a wannan lokaci jajawur yake, lallai ba ƙaramin shigan ƙarfi aka yi mata ba.
Laziyya ta buɗe wannan tukunya, wani irin tiriri ya taso daga cikinta.
Ta tunkari wannan gado gadan-gadan.
Tana zuwa kan wannan gado ta fara kwararawa Jaanu wannan ruwa jikinta.
Jaruma Riya da Hajriya suka cika da tsananin mamaki. Babu yadda za'ayi su yarda wannan ruwa ba zai ƙona jikin gimbiya Jaanu ba saida ruwan ya taɓa jikinta.
Nan take ruwan ya soma shigewa ta cikin ƙofofin gashin jikinta yana shigewa cikin jikinta.
Koda Laziyya ta juye kamar rabin wannan ruwa akan Jaanu sai ta baiwa jaruma Riya umarnin juya ta.
Jaruma Riya ta matso kusa sannan ta gyara kwanciyar Jaanu ta kwantar da ita a rigingine, wato ta kwantar da ita akan cikinta ta basu baya.
Jaruma Riya tayi arba da rubutun sunan Aymanul Faris a gadon gimbiya Jaanu.
Anyi rubutun da baƙar tawada kamar haka:
"AYMAN AL FARIS"
Jaruma Riya ta gyaɗa kai, lallai soyayyar gaskiya Jaanu take yiwa Aymanul Faris.
Duk tsananin tsaro na mahaifinta da yadda ya tsani ƙabilar su Aymanul Faris hakan baisa ta ƙi bayyanar da soyayyarta ga Aymanul Faris ba.
Laziyya ta ci gaba da zuba masa wannan ruwa har ya ƙare.
Ruwan yana gama shigewa cikin jikin Jaanu. Wani irin baƙin abu ya soma zubowa daga jikinta daga ta kowanne ƙofar gashi.
Gagarumin farin ciki yazo kan fuskar jaruma Riya da Hajriya.
A wannan lokaci an sake tsarkake jinin Arya, babu wani gauraye, jininta ya dawo kamar da.
Abinda zasu jira kawai shi ne, lokacin da zata warke domin a ɗaura mata aure da Aymanul Faris ya farkar da babban sirrin dake cikin jininsa.
*****
Yau *07/06/2023*
Babi na gaba zaizo *10/06/2023* da izinin ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 136: *Lokacin Komawa Gida Yayi*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
Kai tsaye Ranganu ya kai su Aymanul Faris cikin wannan ƙaton falo suka zazzauna suka fuskanci juna.
Ranganu ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Kwantar da hankalinka, Ayman. Nan da cikar wata guda gimbiya Jaanu zata warke, kuma akwai alamun cewa wannan ciki ba zai shiga ba. Amma dukda haka muna buƙatar tabbatarwa."
Aymanul Faris ya gyaɗa kai ya ce, "Nagode." sannan ya dubi Barban ya ce, "Aka ce mana, sarki Kuffuru ya samu nasarar kama ka?"
Barban yayi murmushi ya ce, "Haka ne. Sarki Kuffuru ya samu nasarar kama ni,"
Aymanul Faris ya dakatar dashi ya ce, "Ban gane me kake nufi ba, idan ya kama ka, me kake a wannan wuri alhali ance babu wanda zai iya fasa wannan kurkuku?"
Barban yayi murmushi ya dafa kafaɗar Aymanul Faris ya ce, "Wannan shi ne amsar da kake yawan tambayata, sa'adda nake ce maka ZAN GIRGIZA DUNIYA!
"Akwai ayyuka guda huɗu da suka rage bamu kammala ba.
"Waɗannan ayyuka guda huɗu ba za su taɓa kammala ba face mun yaudari su sarki Kuffuru.
"Aiki na farko daga cikin wadannan guda huɗu shi ne, ɗauko hular sarautar babban sarki Samudul Ansari daga daular Nehiya."
Barban ya yiwa Aymanul Faris bayanin daular Nehiya inda sarki Kuffuru ya koma: Ƙarfin daular da kuma yawan sojojin yaƙinta.
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamakin ganin ƙarfin wannan daula.
"Ta ya ya kake tunanin zamu shiga wannan waje mu ɗauko wannan hula wadda kowa dake rayuwa a cikin wannan daula zai iya bayar da rayuwarsa saboda ita?"
Aymanul Faris ya girgiza kai, "Wannan ba zai yiwu ba dole saida cikakken shiri."
Barban yayi murmushi sannan ya ci gaba.
"Wannan shi ne aiki na farko da maigirma Ranganu da kansa zai shiga domin a gudanar dashi.
"Ni da maigirma Ranganu mun gama tsare-tsaren yadda wannan aiki zai kasance, sannan mu biyu kawai zamuje gudanar da aikin..."
Aymanul Faris yana jin haka ya cika da tsananin mamaki ya ce, "Idan ku biyu zakuje gudanar da wannan aiki, ni kuma mene ne amfani na?"
Ranganu ya tari numfashin Barban ya ce, "Zaka je daular Shaha, ka karya kafin da sarki Samudul Ansari ya bibbinne, sannan kaje daular Jerawa da ta Hajarr ka sanar da su saƙon babban sarki."
Aymanul Faris yana jin wannan batu ya sake cika da tsananin mamaki ya dubi Ranganu ya ce, "Idan naje daular Shaha tayaya zan gane wajajen da aka bibbinne waɗannan kafi, sannan wanne saƙo ne zan sanar da Jerawa da kuma Hajarr?"
Ranganu ya dube shi ya ce, "Idan ka shiga daular Shaha, idanuwan tau'rin zasu motsa, su nuna maka wajajen da aka bibbinne kafin.
"Saƙon da zaka sanar da Jerawa da Hajarr? Aljanin-wuta Nara-ya zai sanar da kai saƙon saboda shi kaɗai Samudul Ansari ya faɗawa."
Aymanul Faris yana gama jin wannan jawabi ya yiwa Ranganu godiya sannan ya sake juyawa wajen Barban ya tambaye shi.
"Idan kai kana nan, wane ne wanda ke tsare a hannun su sarki Kuffuru?"
Barban yayi dariya ya ce, "Mutum-mutumina! A tunanin sarki Kuffuru shi ne kaɗai yake iya samar da mutum-mutumi, bai san tun kafun ya fara samarwa ba ma, munyi nisa sosai.
"Ina so ka sani cewa, sau dama da mutum-mutumina kake tattaunawa baka sani ba.
"Suna kiransa da suna 'Barban' ni kuma ana ce min 'Hodon'."
Aymanul Faris yana jin wannan batu ya cika da tsananin mamaki. Lallai al'amarin Hodon babban al'amari ne.
"Daga yau zaka iya daina kirana da Barban, ka dawo ce min Hodon, saboda shi ne ainihin sunana wanda aka yanka min rago.
"Barban sunan ƙaramin yankin mu ne, sannan sunan mutum-mutumin dake hannun su sarki Kuffuru ne."
Aymanul Faris yana jin wannan batu ya dubi sarki Ranganu cikin tsananin al'ajabi ya ce, "Tabbas su sarki Kuffuru zasu girgiza, idan suka gano cewa, mutum-mutumi suka tsare.
"Amma mene ne dalilin da yasa dukkan jama'ar daular Nehiya suka damu da wannan hula dukda kasancewarta ba ainihin tasu ba?"
Ranganu ya sake taran numfashin Hodon ya baiwa Aymanul Faris amsa, "Wannan hular sarauta ta musamman ce, ita ce hular da sarauniya Arya ta sakawa sarki Samudul Ansari a ranar da ta mallaka masa wannan daula.
"Hatta ni kaina bansan daga ina sarauniya Arya ta samo wannan hula ba, amma hular tana da sirri na musamman.
"A duk inda wannan hular sarauta take, akwai ƙarfin mulki a wajen.
"Duk basaraken dake sanye da wannan hula, zai kasance mai tsananin kwarjini da cika-ido."
Aymanul Faris ya gyaɗa kai cikin fahimta.
"Babban jarumi! Akwai buƙatar kuyi tafiya izuwa daular Shaha da wuri, saboda a kowanne lokaci daga yanzu Marganu zai iya kawo hari dukda cewa har yanzu bai san da akwai zaman wannan birni ba." inji Ranganu.
Aymanul Faris ya ce, "Idan na karya waɗannan kafi, ina zan koma, birnin Shaha ko kuma nan?"
Ranganu ya ce, "Idan ka karya waɗannan kafi sannan kaje ka sanar da Jerawa da Hajarr saƙon babban sarki, wannan garin zaka dawo, ka auri Arya.
"Idan ka farkar da babban sirrin dake cikin jininka, zamu koma birnin Shaha."
Aymanul Faris yana jin wannan batu yayi godiya.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, suka yi sallama da su Hodon.
Aymanul Faris ya tashi ya fice daga cikin wannan falo, ya koma cikin wannan ɗaki wanda aka kwantar da gimbiya Jaanu.
Yana shigowa cikin ɗakin yayi arba da jaruma Riya tana yiwa Jaanu wanka, tana wanke mata wannan dafi da ya zubo daga cikin jikinta.
Abinda idanuwan Aymanul Faris suka fara gano masa shi ne, gadon bayan Jaanu inda aka rubuta sunansa da baƙar

Please Login or Register in order to submit comment