Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daula komai girmanta. Kafun mu dawo daga wannan yaƙi, nake so ki kammala..."
Zainila ta zube a gabansa ta ce, "Zan yi kamar yadda kace, ya shugabana. Amma baka buƙatar dafi a yayin wannan yaƙi?"
Marganu ya dafa kafaɗarta ya ce, "Amfanin abinda za ki haɗa yafi abinda za kiyi a wannan filin yaƙi. Shi yaƙi ɗan zamba ne. Baya ga haka akwai Ileisha, Narima da Laila masu sarrafa macizai sama da dubu, zasu maye gurbinki a wannan yaƙi. Ke dai ki gudanar da wannan aiki yadda ya dace."
"Kamar yadda ka umarta, ya shugabana..." inji Zainila.
Marganu yayi murmushi ya ƙarasa gabansu dukkansu ya tsaya, ya dubi BES guda huɗu ya ce, "Abin harinku a wannan yaƙi dakarun da zasu taho dasu ne. Ina so ku haɗa ƙarfi-da-ƙarfe ku gama da dakarun nasu a cikin ƙanƙanin lokaci."
Yelila, Shedima, Kubwana da Ishana suka zube a gabansa suka ce, "Zamuyi kamar yadda ka ce, ISRABIL!"
Marganu ya sallame su sannan ya basu umarnin ci gaba da horo har zuwa ranar da za'a fita wannan yaƙi, sannan yasa aka kai Zainila cikin wani ɓoyayyen ɗaki inda zata gudanar da aikin da ya saka ta.
Marganu ya dubi Laila, Ileisha da Narima ya ce, "Ku kuma ina so ku jagoranci dakarun mu a wannan yaƙi. Ku kashe duk wani mai ƙarfi wanda ke tsaye a bayan Kuffuru da Ayubu..."
Nan take suka shaida masa zasuyi hakan. Marganu ya sallame su daga wannan filin horo.
Bayan tafiyarsu da kaɗan ya zaro maɗaukakan takubbansa guda huɗu.
Takobin-haske. Takobin Bankai. Takobin-taswira. Takobin tarwatsa komai.
Marganu ya ƙarewa takubban kallo ɗaya bayan ɗaya sannan ya haɗe su a waje guda.
Ƙarafunan takubban suna haɗuwa a waje guda, takobinsa ta haske ta fara haske tana zuƙe su izuwa cikinta.
Jim kadan, takubbansa guda huɗu suka haɗe a waje guda. Ya ɗaga takobin sama wadda zai iya kira da kowacce daga cikin takubbansa.
Takobin tana bayar da haske sannan akwai zanen taswira akan ƙarfenta, akwai inuwar Bankai a cikinta, ga kuma ƙarar aradu dake fita lokaci-lokaci daga cikinta.
Marganu ya ɗaga takobin sama ya juyata a cikin iska.
Gagarumin iko ya sauƙa a wannan waje, filin gaba ɗaya yayi girgiza, aradu ta zubo, filin ya juya sakamakon juya takobin.
"Hmm," Marganu yayi murmushi. "Lokaci nake jira, domin bayyanar da babban iko..."
Yana faɗin haka ya rarraba takobin izuwa kaso uku, sannan ya mayar da kowacce mazauninta.
A daidai wannan lokaci Firziyya ta ƙaraso wannan waje riƙe da zabga-zabgan takubbanta guda biyu.
Marganu yayi murmushi ya dubeta ya ce, "Na gama shiryawa wannan yaƙi, abinda nake jira kawai shi ne ranar ashirin ga watan Yuni..."
Firziyya ta yi murmushi ta ce, "Da gaske? Gani na dawo da takubban nawa, me zamu yi?"
Marganu ya ce, "Ina so na baki horon yaƙi kamar wanda jaruma Riya take da. Kin san cewa, jaruma Riya ta taɓa tarar mahaifinki sun gwabza yaƙi na ɗan lokaci amma bai yi mata komai ba.
"Tabbas idan kika samu irin wannan horon yaƙi, za ki iya tarar sarki Ayubu a wannan yaƙi..."
Marganu yana faɗin haka ya zaro takobinsa ta taswira, ya dubi Firziyya ya ce, "Ki afka min da yaƙi..."
Gimbiya Firziyya tayi murmushi domin ta gane me yake nufi, ta rugo kansa ta afka masa da azababben yaƙi. Kai kace wani babban abokin gabarta ta tunkara.
Marganu ya tareta suka fara gumurzu mai ban tsoro. Ta wanzu tana kawo masa sara da suka da takubbanta shi kuma yana karewa cikin tsananin zafin nama.
Saida suka shafe sa'a ɗaya da rabi suna gumurzu sannan ya fara mayar mata da martani.
Yana fara hakan yaƙin ya sauya, domin cikin ƙanƙanin lokaci ta daina kawo masa hari sai dai ƙoƙarin kare kanta kawai.
Kafun a jima Marganu ya gajiyar da ita, har ya samu nasaran buge takubban dake hannayenta.
Ta durƙusa a gabansa tana ta haki. Marganu yayi murmushi ya miƙa mata hannunsa guda, ta riƙo shi ta miƙe tsaye.
"An kammala horon safe, saura na yamma." inji Marganu.
Daga wannan lokaci Marganu ya ci gaba da baiwa Firziyya mugun horo na yaƙi wanda bata taɓa samu ba. Kafun cikar kwanaki goma tuni ta gama kwarewa yadda Marganu yake so.
A wannan lokaci daular Gorgon ta gama shiryawa wannan yaƙi. Abinda ya rage kawai shi ne fita filin yaƙin Shizis dake garin Nayet.
****
Yau *10/07/2023*
Babi na gaba zaizo *13/07/2023* da yaddar ALLAH.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment