Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tawada.
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki. Lallai wannar masoyiyarsa ce ta haƙiƙa.
Jaruma Riya tayi gaggawar lulluɓe jikin Jaanu da farin mayafi, sannan ta ƙaraso gaban Aymanul Faris ta tsaya.
"Mene ne?" ta tambaye shi.
Aymanul Faris ya yi gyaran murya ya ce, "Idan kika kammala, ki zo mu tafi daular Shaha domin aiwatar da wani aiki, fatan dai jikin Arya yana samun sauƙi."
Jaruma Riya tayi murmushi ta ce, "Jikinta ya samu sauƙi. Saura ta gama warwarewa kawai. Ina zuwa."
Tana gama faɗin haka ta koma ta ci gaba da yiwa Jaanu wanka.
Aymanul Faris ya ƙarasa wajen da Hajriya ke zaune suka ci fara tattaunawa.
"Mama! Mun kusa komawa ainihin birnin mu!" inji Aymanul Faris.
Hajriya tayi murmushi ta ce, "Naga alamun hakan. Tabbas mun kasance masu tsananin sa'a da zamu sake komawa cikin birnin da babu wanda ya kaishi daɗi a duniya."
A daidai lokacin jaruma Riya ta ƙaraso wannan waje.
Aymanul Faris ya baiwa Hajriya labarin aikin da zasu je su gudanar.
"Ubangiji ya baku sa'a," inji Hajriya.
Nan take suka yi sallama da Aymanul Faris.
Aymanul Faris yaje kan wannan gado da gimbiya Jaanu take kwance akansa, ya sumbaci hannunta sannan ya dawo suka gama kimtsawa shi da Riya.
Ba tare da ɓata lokaci ba, suka shiga cikin ƙaramin jirgin ruwa suka bar wannan tsibiri suka tunkari gabjejen teku.
Wannan ƙaramin jirgin ruwa yana da tsananin gudu fiye da tunanin jaruma Riya.
Amma dukda ƙarfin gudun wannan jirgin ruwa, saida suka shafe kwanaki goma sha-uku cir suna tafiya sannan suka hango katangar birnin Shaha.
Jirgin ruwa yana zuwa bakin gaɓa ya tsaya, Aymanul Faris da jaruma Riya suka fito daga cikinsa.
Akan ƙafafuwansu suka ƙarasa har bakin ƙofar shiga daular Shaha.
Ƙofar tana nan kamar yadda suka taɓa ganinta.
Ƙofar shiga birnin Shaha kaɗai abar dubawa ce, domin kuwa mutum ba zai na hango ƙarshenta ba face ya ɗaga kansa can sama.
Gaba ɗaya garin a kewaye yake da wata irin katanga wadda aka gina da wani irin tubali mai ban mamaki, yana da haske kamar na jar zinari amma yana da laushi kamar yashi. Katangar ma kaɗai, tana da tsananin tsaho kamar husumiya.
A bakin ƙofar shiga wannan gari akwai ƙwarangol da yawa na mutane a zuzzube, wasu sun gama ruɓurɓushewa sun zamo ƙasa, wasu kuma da saura.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka ƙarasa kusa da wannan ƙofa, yasa hannunsa guda ya murɗa wata kuba dake jikin ƙofar.
Nan take wannan ƙofa tayi ƙara sannan ta fara buɗewa a hankali.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama wangamewa gaba ɗaya.
Aymanul Faris da Riya suka kunna kai izuwa cikin wannan birni.
Shigowarsu cikin birnin keda wuya, idanuwan Aymanul Faris suka soma nuna masa waɗansu ramuka da sarki Samudul Ansari ya binne kafi a ciki.
Nan take Aymanul Faris ya ƙarasa kusa da guda ɗaya yasa Saif-Al-Barzaƙ ya tono abinda ke cikin ramin, sannan ya fasa shi.
Daga wannan lokaci ya yi ta bin wadannan ramuka ɗaya bayan ɗaya yana fasa abinda aka binne a cikinsu.
Sai da suka kwana huɗu suna fidda waɗannan kafi sannan suka kammala, suna kammalawa suka tunkari babban gidan sarautar garin.
Bayan ɗan lokaci suka iso cikin gidan sarautar, Aymanul Faris ya hau saman wani mumbari, yazo kusa da wannan ƙaton gunki wanda aka gina da zallar zinari a tsakiyar wannan fada.
Aymanul Faris yasa hannunsa guda yaja wannan baƙin mayafi da ya rufewa gunkin fuska, take mayafin ya yaye fuskar gunkin ta bayyana.
Abin mamaki a zamani mai tsaho aka gina wannan gunki amma surar Aymanul Faris ce dashi.
Siffar wannan gunki tana gama bayyana, gaba ɗaya daular Shaha tayi girgiza.
Duk wajajen da suka yi ƙura ko kuma jini da ƙwarangwal ya ɓata suka ɓace ɓat!
Cikin daƙiƙa biyar daular Shaha ta dawo kamar yadda take a da, zamanin babban sarki Samudul Ansari.
Abinda kawai ta rasa a wannan lokaci shi ne, cukowar jama'a da kuma amfanin gona.
Aymanul Faris ya sauƙo daga kan wannan dogon mumbari, yazo inda Riya take suka rungume juna cikin tsananin farin ciki.
Nan take suka fara kewaye cikin wannan birni suna ganin albarkatu da ni'imomin dake cikinsa.
Iya rayuwar Aymanul Faris da jaruma Ria basu taɓa zuwa waje mani'imci kamar Shaha ba.
Hatta iska da ruwan sha na wannan daula dabam ne.
Nara ya bayyana a gaban Aymanul Faris ya risina yayi gaisuwa.
"Ina jinka?" inji Aymanul Faris.
Nara ya ce, "Nazo ne domin na sanar da kai, wannan saƙo wanda zaka sanar da mutanenka domin ku sake haɗewa a daular Shaha."
Aymanul Faris ya gyaɗa kai alamar yana ji.
Nara ya saka hannu a cikin rigarsa ya fiddo wata takarda mai kaurin gaske ya baiwa Aymanul Faris.
Aymanul Faris ya karɓi takardar ya haɗe fuska ya budeta.
Abin mamaki rubutu layi ɗaya ne kawai akanta, amma daga can ƙasa akwai sa-hannu da hatimin babban sarki Samudul Ansari.
"ISRABIL ya kusa bayyana ku dawo daular Shaha, ko kuma ya ƙarar daku ɗaya-bayan-ɗaya!" shi ne abinda aka rubuta akan wannan takarda.
"Sarki Samudul Ansari ya bani wannan takarda ya ce, a duk lokacin da ISRABIL ya bayyana ko kuma ka mallaki wannan ruhi nasa, na baka takardar.
"Idan ka nunawa Jerawa da Hajarr wannan takarda, zasu shiga taitayinsu sannan su dawo daular Shaha saboda sun san cewa, lokacin zama a waje ya ƙare. Lokaci ne na komawa gida!"
Aymanul Faris da Riya suka yi sallama da Nara sannan suka kama hanyar zuwa ƙasashen Jerawa da Hajarr.
A wannan karo ma saida suka shafe sati biyu suna tafiya sannan suka iso waɗannan wajajen.
Ƙasashen Jerawa babban yanki ne a arewacin duniya, wanda mutane ƙalilan ne kawai suka san da zamansa.
Saboda mutanen yankin basa hulɗa da kowa a duniya, abinda kawai suka mayar da hankalinsa akansa shi ne noma da kiwo wanda kuma ya karɓe su.
Aymanul Faris da jaruma Riya suna fuskanto wannan yanki suka ji an busa ƙaho daga saman wani tsauni, take dakaru gabza-gabza suka fara fitowa ɗauke da makaman yaƙi suna kewaye su.
Dukkanin dakarun sun shafe fuskokinsu da shuni, babu yadda za'ayi mutum ya iya shaida su.
"Su wane ne ku!" wata murya ta dakawa su Aymanul Faris tsawa.
Yadda muryar ta furta waɗannan kalmomi ya tabbatar musu da cewa, lallai ɗan asalin Shaha saboda harshen akwai kamanceceniya.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi shuru suka ƙura musu idanu, kamar suna so su tabbatar da abinda suke kallo.
Mayaƙan na ganin haka suka kwarara uban ihu, zasu afkawa su Aymanul Faris.
"Ku dakata!" wata murya ta daka musu tsawa daga baya.
Suna jin wannan murya suka ja baya, sannan suka buɗa hanya wanda yayi musu tsawar ya ƙaraso.
Wani mutum dogo kuma fari fat wanda ke sanye da shuɗin sulken yaƙi, ya ratso ta tsakiyarsu yazo gaban Aymanul Faris ya tsaya.
Mutumin ya ɗan risina a gaban Aymanul Faris ya ce, "Suna na SHARBIL ni ne shugaban jama'ar dake rayuwa a wannan yanki na Jerawa.
"A yadda aka bayyana siffofi da bayanai na magajin Samudul Ansari a littatafan tarihi sun nuna mana cewa, kana matuƙar kama dashi.
"Shin zamu iya sanin wane ne kai?"
Aymanul Faris yana jin wannan batu ya ƙarasa gaban sadauki Sharbil ya ce, "Suna na AYMANUL FARIS ɗan HASANUL JALWAR ɗan KUSUFUL JALWAR ɗan SAMUDUL ANSARI!"
Sadauki Sharbil da mutanensa suna jin nasabar Aymanul Faris suka zube ƙasa suka yi mubaya'a.
"Ka karɓi mubaya'armu ya kai magajin babban sarki. Lallai muna daga cikin jama'a masu sa'a da muka kasance daga cikin masu komawa daular Shaha, gidan aminci." inji sadauki Sharbil.
Aymanul Faris ya kamo kafaɗun Sharbil ya miƙar dashi tsaye sannan ya fiddo wannan takarda wadda Nara ya bashi ya nunawa Sharbil.
Sadauki Sharbil yana ganin wannan umarni ya ja da baya a tsorace, ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Nan da cikar kwanaki goma zamu koma cikin birnin Shaha saboda umarnin babban sarki ya bayyana!"
Nan take sadauki Sharbil yasa aka kai Aymanul Faris da Riya masauƙi mai kyau, shi kuma ya baiwa jama'arsa umarnin fara shirye-shiryen ƙaura saboda umarnin babban sarki ya iso.
Aymanul Faris da matarsa suka kwana a cikin wannan masauƙi da aka sauƙe su, da safe suka ga sadauki Sharbil da kansa ya shigo musu da abincin safe.
Ya ajiye abincin ya juya zai fita amma sai Aymanul Faris ya kira shi ya ce yazo su ci abincin tare.
Saida Sharbil ya ɗan yi gardama amma daga ƙarshe yazo ya zauna suka fara cin abincin.
"Tsahon wanne lokaci kuka shafe kuna zaune a wannan yanki," Aymanul Faris ya tambaye shi.
Sadauki Sharbil ya ce, "Daga lokacin da aka gwabza yaƙi tsakanin Meher da Deher sa'adda wannan kafi ya fara aiki akanmu."
Aymanul Faris ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Shin a cikin jama'ar dake wannan yanki, akwai mayaƙa kuwa?"
Sadauki ya ɗago kansa ya dube shi ya ce, "Babu abinda ake koyawa 'yan ƙabilar Kuyuru ƙarƙashin jagorancina, idan ba horon yaƙi ba. Kusan kaso sittin na samarin dake rayuwa a wannan yanki mayaƙa ne."
Aymanul Faris ya dube shi cikin jinjinawa ya ce, "Tabbas kayi aiki mai kyau, ya kai Sharbil. Lokacin komawa gida yayi, mu koma gida domin kare jama'armu da dukiyarmu daga babban abokin gabarmu."
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi sallama da sadauki Sharbil suka wuce izuwa ƙasashen Hajarr.
Shugabansu ya taryi su Aymanul Faris, nan take Aymanul Faris ya nuna masa saƙon babban sarki.
Take hankalinsa yayi mummunan tashi ya tara dukkan jama'ar dake rayuwa a wajen, ya basu umarnin fara shirye-shiryen barin wannan yanki.
Da wannan Aymanul Faris da jaruma Riya suka isar da saƙon LOKACIN KOMAWA GIDA YAYI!
Bayan sun tabbatar da saƙon ya gama isa, sai suka shirya suka kama hanyar komawa birnin Darul Barban.
*****
Yau *10/06/2023*
Babi na gaba zaizo *12/06/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 137: *Aiki na bakwai*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U~M~S
*
~Wani waje a yankin ƙasashen arewa.
*
Ƙasaitaccen keken doki ne ke tafiya a cikin wani ƙaramin gari a wannan yanki. Kallon farko zaka yiwa wannan keken doki ka gane cewa, na gawurtattun attajirai ne.
Bawan dake tuƙa wannan keken doki ya ƙara masa sauri, suka ci gaba da tafiya har tsahon ɗan lokaci sannan suka iso tsakiyar wannan gari.
Abin mamaki a wata ƙatuwar kasuwa ta bayi suka tsinci kansu, babu komai a kasuwar face bayi kala daban-daban.
Kowanne irin bawa mutum yake so, idan yazo wannan kasuwa zai samu.
Matuƙin wannan keken doki ya tsayar da keken dokin, sannan ya sauƙo ya shaidawa masu gidansa cewa sun iso.
Nan take aka bude ƙofar keken dokin, waɗansu manyan attajirai guda uku sanye cikin manyan kaya suka fito daga cikin wannan keken dokin.
Wannan matuƙi na keken doki, ya ɗauko wata jaka dake cikin keken dokin suka kunna kai izuwa cikin kasuwar.
Attajiran guda uku suna shiga cikin wannan kasuwa, suka fara duba bayin da ya kamata su saya.
Ɓangaren farko na waɗannan bayi basu sami irin waɗanda suke buƙata ba, hakama ɓangare na biyu da na uku.
Har sun haƙura zasu bar kasuwar garin kenan, suka hango waɗansu bayi guda biyu a tsaitsaye.
Kallon farko kawai suka yiwa bayin, suka ji sun yi musu kamar yadda suke buƙata.
Nan take suka je wajen mutumin dake da mallakin bayin suka yi ciniki, aka sayar musu da bayin a tsadance.
Hakan ko kaɗan bai dame su ba, saboda bayin sun yi musu.
Attajiran suka baiwa wannan matuƙi umarnin sayo keken doki wanda za'a saka waɗannan bayi a ciki.
Matuƙin ya ruga izuwa cikin kasuwa, jim kaɗan ya dawo ɗauke da sabon keken doki.
Nan take aka saka wadannan bayi guda biyu a ciki, sannan aka haɗa keken dokin da ainihin nasu, suka bar kasuwar wannan gari.
Suka sake shiga wani gari suka sake sayo wasu bayin, sannan suka wuce wani suka sake saya.
Saida suka sayi bayi guda goma sha-uku sannan suka kama hanyar komawa birninsu.
Bayan shafe kwanaki tara suka iso daular Nehiya inda sarki Kuffuru yake mulki.
Wadannan bayi suna ganin inda aka shigo dasu suka fara kuka, saboda sun tabbatar da cewa lallai ƙarshen su yazo.
Babban abinda ya baiwa bayi da yawa daga cikin wadannan mamaki shi ne, akwai wasu bayi guda biyu da basa kuka ko kuma baƙin ciki bisa ganin wannan waje da aka kawo su.
Dukda cewa ba'a wannan daula suke rayuwa ba, amma suna samun labarin abinda ake yiwa bayi idan aka kawo su wannan daula.
Idan mutum ya samu dama ya ƙarewa waɗannan bayi guda biyu kallo, zai ga ɗayan yana ɗan kama da Hodon, ɗayan kuma yana kama da aljani Ranganu.
Bayan doguwar tafiya aka iso babban gidan sarauta ta wannan daula da waɗannan bayi.
Waɗannan kekunan dawakai suka ja tunga suka tsaya.
Wasu dakaru suka zo suka fiddo bayin da aka sayo, aka kaisu wani waje aka tsayar dasu.
Wasu dakaru na musamman suka zo, suka yiwa bayin kallo mai kyau sannan suka caje su.
Aka tabbatar da babu wanda ke ɗauke da makami sannan aka shigar dasu cikin gidan sarautar.
Sarki Kuffuru da kansa yazo ya yiwa bayin kallon nutsuwa, sannan yayi amfani da ƙarfin sihirin tsafinsa yaga tarihin kowanne daga cikinsu.
Dukkan abinda tarihinsu ya nuna masa asalinsu ma bayi ne, wadanda babu abinda suka sani a rayuwarsu idan ba bauta ba.
Sarki Kuffuru yasa aka kaisu wani waje na musamman acan cikin gidan sarautar.
Aka kawo tubalan gini kala daban-daban aka fara koya musu yadda zasu gina sabuwar husumiya.
*
Sarki Kuffuru yana barin wannan waje ya koma cikin turakarsa ya zauna akan wata kujera, ya zuba ruwa a cikin wani ƙasaitaccen kofi ya kurɓa.
Yana gama shan abinda ke cikin wannan kofi, ya kirawo Hasamul-Sawaz.
Hasamul-Sawaz ya bayyana a gabansa ya risina yayi gaisuwa.
Kuffuru ya ce, "Kamar yadda muka alƙawarta bayan dawowata daga birnin Damashkar, kace sai na warke daga raunikan da Marganu yayi min sannan zaka bani amsar tambayar da nayi ma."
Hasamul-Sawaz yayi gyaran murya ya ce, "Ya shugabana! Ina so ka sani cewa, wannan Marganun da ya sami nasara akanka, ba fa asalin Marganu bane.
"A halin yanzu Marganu yana cikin tukunya a daular Gorgon, gangar jikinsa tana zuƙan sinadaran da zaiyi amfani dasu ya farkar da babban sirrinsa na haske.
"Yana daga cikin wannan tukunya amma yake iya aiko wani kaso daga cikin ikonsa.
"A hasashen da ake kaso talatin kawai ya aiko na ikonsa, wanda ya kusa yayi nasara akanka da kuma Aymanul Faris."
Sarki Kuffuru ya dubi Hasamul-Sawaz cikin tsananin mamaki ya ce, "Kaso talatin kacal? In dai kuwa hakane, akwai gagarumar matsala."
Hasamul-Sawaz ya gyaɗa kai ya ce, "Tabbas idan Marganu ya gama farkar da jininsa, kawar dashi zai zamo gagarumin bala'i. Saboda ba zai yiwu ba."
Sarki Kuffuru yayi murmushin ƙarfin hali ya ce, "Babu abinda ba zai yiwu a wannan duniya ba. Tabbas zamu kawo ƙarshen sa. Matuƙar aka ce wannan daula tana ƙarƙashin ikon mu."
Hasamul-Sawaz ya dubi ya ce, "Abin da kamar wuya. Duk wani abu da muke taƙama dashi Marganu yafi mu.
"Abinda kawai muka fishi dashi shi ne, yawan sojojin yaƙi. Amma batun ƙarfi da sharri nasa sun fi namu."
Sarki Kuffuru ya dubi Hasamul-Sawaz a hasale ya ce, "Ya kake magana kamar ka sare akan Marganu?
"Kada ka manta a gabanmu ya girma yayi wayo. Mahaifinsa ma bawa ne a wajen mu.
"Don haka babu abinda zai mallaka ya bamu tsoro, saboda kafun ya mallaka mun riga shi.
"Idan yana taƙama da ma'abota Bankai ne, ni ina da UMKAS.
"Idan yana taƙama da takobin haske, ina da Siwod-del-bulod wadda har yanzu ban gama bayyanar da asalin ƙarfinta a duniya ba.
"Idan yana taƙama da BES, ni kuma ina da INFIRONS.
"Saboda haka shakkar me zamuyi akansa?
"Ko yaƙin da na gwabza dashi, dama kawai na bashi domin naga ainihin ƙarfinsa.
"Idan baka manta ba, da LESIM kawai na yaƙe shi ban fiddo Siwod-del-bulod ba."
Hasamul-Sawaz yana jin wannan batu jikinsa yayi sanyi, ya tabbatar da lallai abinda sarki Kuffuru yake fada gaskiya ne.
"Tun da ya taɓo ni, nima kwanan nan zan yi shiri na kaiwa daular Gorgon hari, domin na nuna musu ƙarfina da kuma hatsabibanci na." inji Kuffuru.
Hasamul-Sawaz ya ce, "Tabbas na gamsu da jawabanka kuma lallai akwai buƙatar mu nunawa Marganu ƙarfinmu saboda naga kamar girman kai ya soma shiga kan yaron!"
Sarki Kuffuru yayi murmushi ya ce, "Ka bar batun Marganu a gefe. Ni yanzu babbar damuwata ita ce, ta ya ya zan hana Aymanul Faris tarawa da gimbiya Jaanu?
"Sannan fyaɗen da Marganu yayi mata ba zai haifar da wata matsala ba?"
Hasamul-Sawaz ya risina a gaban Kuffuru ya ce, "Batun hana Aymanul Faris tarawa da gimbiya Jaanu, ba zai yiwu ba. Saboda bakin alƙalami ya riga ya bushe. Sa'adda ya ɗauketa ya gudu da ita izuwa wani ɓoyayyen birni dake bisa wani tsibiri wanda duk duniya babu wanda yasan ina ne.
"Kaga kenan, kafun ma mu gano wannan birni mu hana shi aiwatar da abinda yayi niyya, har komai ya taɓarɓare.
"Wannan fyaɗe da Marganu yayi mata kuwa, zai haifar mata da matsala.
"A halin yanzu Marganu da ma'abota Bankai basu da wani bambanci don haka duk abinda yayi mu'amala da Marganu zai iya fuskantar barazana daga mugun dafin maciji.
"Ina da tabbaci ɗari bisa ɗari, dafi ya shiga jikin gimbiya Jaanu, sannan a waje ɗaya kawai za'a samu maganin dafin.
"Wannan waje hatta shi kansa Samudul Ansari da yaje wajen, bai share ba. Saboda haka zamu iya cewa, gimbiya Jaanu ta mutu ko kuma tana cikin mugun mawuyacin hali."
Sarki Kuffuru yayi dariya farin ciki ya ce, "Idan kuwa haka ne, Aymanul Faris baida wani ƙarfi kenan wanda zai razanar damu.
"Abinda zamu mayar da hankali akansa kawai shi ne, kaiwa Marganu hari."
Hasamul-Sawaz ya ce, "Haka ne. Ta ya ya zaka farmaki daular Gorgon sannan kayi nasara?"
Sarki Kuffuru ya ce, "Ni da kaina zan kai wannan farmaki tare da dakarun UMKAS guda dubu ɗaya. A wannan farmaki ne zan fara nunawa duniya, me ake kira Siwod-del-bulod sannan na nunawa Marganu yaro fa yaro ne.
"Bisa aljanu zamu kai wannan farmaki, da zarar sun kaimu tsakiyar wannan daula ta sararin samaniya zamu daka tsalle zamu sauƙo cikin daular sannan mu kashe na kashewa, mu tsoratar da Marganu."
Hasamul-Sawaz ya gyaɗa kai ya ce, "Lallai kuwa wannan shiri ne mai kyau. Abinda ya kamata muyi kenan a wannan lokaci, sannan na yarda da ƙarfin wadannan dakaru, UMKAS."
Haka dai sarki Kuffuru da Hasamul-Sawaz suka yi ta tattaunawa akan abubuwa daban-daban, har tsahon ɗan lokaci, sannan suka yi sallama ya kwanta ya fara barci.
*
Saida aka shafe kwanaki uku ana baiwa waɗannan bayi guda sha-uku horo sannan aka kammala.
A cikin wadannan kwanaki uku an gana musu azaba da duka kala daban-daban dole saida suka koyi wannan aiki.
A wannan rana da safe aka tafi izuwa inda za'a gina wannan sabuwar husumiya.
Aka yi ta kutsawa ta cikin dakaru rukuni daban-daban ana wucewa.
Saida suka ratsa ta cikin rukuni arba'in sannan suka iso inda za'a yi wannan aiki.
Wani ƙaramin fili ne kusa da inda aka gina wannan husumiya wanda aka ajiye hular sarautar a cikinta.
Hodon da Ranganu suka ƙarewa wannan husumiya kallo, daga sama har ƙasa.
Ranganu ya dubi Hodon yayi masa inkiya da idanu.
Dakaru suka matso da bayin kusa da tubalin gini sannan suka basu umarnin fara aiki.
Nan take bayi suka cika wannan umarni. Wasu suna gini, wasu suna ɗebo tubali, wasu suna ɗebo ruwa. Kai har da masu ɗebo duwatsu akwai.
Kafun kace wani abu, tuni gini ya fara yin tsaho.
Tsahon kwanaki biyu suka shafe suna gina wannan doguwar husumiya sannan suka kammala.
A ranar da suka kammala ginin ne, waɗannan dakaru suka tasa ƙeyarsu a gaba suka nufi wata siririyar hanya.
Bayin guda goma sha-uku suna tafe a gaba, dakaru ashirin na kewaye dasu.
Koda suka zo giftawa ta gefen wannar tsohuwar husumiya wadda hular babban sarki take ciki, sai aka ga bayin dake kan gaba sun ruga sun tunkareta.
Koda waɗannan dakaru guda ashirin suka ga haka, sai suka ruga suka take musu baya.
Waɗannan bayi guda biyu suna zuwa gindin wannan husumiya, suka kewayeta da gudu, sannan suka tunkari inda sauran bayin suke zasu koma.
Waɗannan dakaru guda ashirin na ganin haka, suka cika da tsananin mamaki. Me waɗannan bayi guda biyu suke nufi, kawai ɗan kewaye wannan husumiya shi ne damuwarsu?
A fusace dakarun suka tunkari waɗannan bayi guda biyu zasu kama su.
Idan kayi duba izuwa cikin wannan husumiya kuwa, zaka yi arba da Hodon da kuma Ranganu a gaban wata hular sarauta wadda aka ajiye bisa wani tudu.
"Daƙiƙa talatin kawai muke da, saboda mutum-mutumin da muka bari a waje, ba zasu wuce hakan ba." inji Ranganu.
Yana gama faɗin haka ya ɗauki wannan hula ya sakata a cikin rigarsa, sannan ya shuka wani ɗalasimi akan wannan tudu.
Ɗalasimi ya tsiro sannan ya juye izuwa irin wannan hula. Kai kace ita ce a wajen.
Ranganu da Hodon suka yi girgiza suka ɓace ɓat! daga cikin wannan husumiya.
Waɗannan dakaru guda ashirin suna iso bayi guda biyun suka rufe su da gudu da waɗansu kulake na ƙarfe.
Kan a jima sun yi musu jina-jina. Ko miƙewa tsaye basa yi.
Shugaban dakarun ya bayar da umarnin ƙarasawa dasu bakin wannan tafki wanda za'a kashe su acan.
Dakarunsa suka kora sauran bayin sannan suka ja wadannan bayi guda biyu a ƙasa.
Ɗan gajeren lokaci suka ƙaraso bakin wannan tafki wanda ruwan cikinsa ya rine izuwa jini, sannan lokaci-lokaci ƙasusuwa da tsokokin naman bil'Adama suna tasowa daga cikinsa.
Sauran bayi suka zube ƙasa suka fara amai da kakarin mutuwa saboda wari da ɗoyin dake tashi a wajen.
Shugaban waɗannan dakaru yasa aka fara kawo masa bayin ɗaya-bayan-ɗaya, yana amfani da wata zabgegiyar adda dake hannunsa yana gunduwa-gunduwa da namansu sannan yana

Please Login or Register in order to submit comment