Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sake kaiwa Marganu hari da taurari guda huɗu, a wannan karon Marganu ba kaucewa yayi ba, shima hari ya kaiwa Kuffuru.
Harin nasu na haɗuwa a tsakiya suka tarwatse, birnin Damashkar gaba ɗaya yayi girgiza.
Duk wani mahaluƙi dake rayuwa a cikin wannan birni saida ya faɗi ƙasa.
Sarki Kuffuru ya dubi Marganu ya ce, "Tun da ƙarfin mu yazo ɗaya, meye zai hana mu yaƙi juna da zallar jarumtaka?"
Marganu yayi dariya ya ce, "Ƙarfin mu yazo ɗaya? Ko kuma na ɗaga maka ƙafa dai,"
Sarki Kuffuru ya yi dariya ya ce, "Ƙarya kake, nafi ƙarfin wani ya ɗaga min ƙafa..."
Marganu yayi murmushin mugunta ya dafa ƙirjinsa da hannunsa wanda ke ɗauke da hatimin haske.
Wannan abu dake gefen zuciyarsa ya motsa yayi haske, Marganu ya turo sirrin haske izuwa cikin jijiyoyin dake hannunsa wanda ke riƙe da takobi.
Sirrin hasken dake gefen ƙirjinsa ya haɗu da takobin dake hannunsa.
Marganu ya kaiwa Kuffuru sara da ita, wani ƙatoton fai-fai ya fice daga tsinin takobin.
Cikin rabin daƙiƙa kacal! hasken yaje ya doki sarki Kuffuru a ƙirji.
Saboda ƙarfin dukan saida sarki Kuffuru yayi tsalle ya faɗo acan baya.
Kafun yayi wani yunƙuri tuni gangar jikinsa ta fada cikin wani ƙaton rami dake can baya.
Kuffuru ya faɗo kan rusashshen ginin dake cikin wannan rami.
Marganu yayi murmushi ya juya wajen da gimbiya Jaanu ke tsaye.
Marganu yayi arba da ita kwance a cikin wani ɗan ƙaramin rami, wani ƙatoton gini yana ƙoƙarin ruftawa kanta.
Indai wannan gini ya rufta kanta sai dai wata ba ita ba.
Marganu ya ruga da gudu wannan waje saboda saura kaɗan wannan gini ya ƙarasa ruftawa.
Marganu yasa hannayensa biyu ya jawota, lokacin da wannan gini ya ƙarasa ruftawa wajen.
Marganu ya kirawo BES da zai basu ita su tafi da ita, izuwa daular su amma sai ya fasa, ya sallami BES suka tafi.
Shi kuma ya tunkari wani ƙaramin ɗaki ɗauke Jaanu akan kafaɗarsa.
Marganu ya shiga cikin wannan ƙaramin ɗaki da ita.
Bayan kamar sa'a guda ya fito daga cikin wannan ƙaramin ɗaki yana ɗaure wandonsa.
Yana fitowa yayi arba da jarumai guda biyu sun ƙaraso wannan waje a guje.
Kallon farko yayi musu ya gane Aymanul Faris da jaruma Riya ce.
Aymanul Faris ya dakawa Marganu tsawa, "INA ARYA!!!"
Marganu yayi dariyar mugunta ya ce, "Yanzun nan na gama wani ɗan ƙaramin kasuwanci da ita!"
"AYMANUL FARIS!!!" inji Marganu. "Karo na biyu da na haɗu da kai, bayan nasha baƙar wahala wajen mayar maka da mahaifiyarka... A yau zan ɗauki alƙawarin da na ɗauka, yau zan hukunta ka.
"Saboda kaine babban dalilin da ya hana Jaanu ƙaunata, wanda hakan yayi sanadiyar tarwatsewar dukkan wani farin ciki na rayuwata!"
Marganu yana gama faɗin haka ya kaiwa Aymanul Faris sara irin wanda ya kaiwa Kuffuru.
Cikin rabin daƙiƙa kacal! aka yiwa Aymanul Faris wawan duka a ƙirji, shima yayi tsalle ya haɗu da wani gini mai kauri bayansa ya gwaru da ƙarfi, ya faɗo ƙasa a galabaice.
Ba ƙaramar sa'a ya taka ba, saboda duk wanda aka yiwa irin wannan duka indai suka haɗu da gini ƙasusuwan bayansu kakkaryewa suke.
"SIRRIN ISRABIL sai ta mulki duniya," inji wannan abu dake gefen ƙirjin Marganu.
Marganu ya juya da baya zai koma cikin wannan ɗaki wanda ya gama yiwa Jaanu abinda yayi mata domin ya ƙarasa.
Waɗansu taurari guda biyu suka dira a gadon bayansa.
Lamarin da yasa shima yayi tsalle ya faɗo acan gaba kenan.
Marganu ya miƙe tsaye cikin tsananin mamaki, nan take yayi arba da sarki Kuffuru.
"Bari na gama da kai, na hallaka Aymanul Faris na ɗauki taurin," inji sarki Kuffuru.
Marganu ya rugo kansa suka ruguntsume da azababben yaƙi fiye da na farko.
Sai da suka shafe sa'a biyar suna gwabza wannan yaƙi amma babu wanda ya sake samun wata nasara.
Tunda birnin Damashkar ya kafu ba'a taɓa gwabza mummunan yaƙi irin wannan a cikinsa ba.
Gidan sarautar birnin da kuma kaso saba'in na birnin saida ya ruguje.
Kuffuru da Marganu suna tsakiyar gumurzu Aymanul Faris ya farfaɗo.
Cikin gaggawa shi da jaruma Riya suka ƙarasa cikin wannan ɗaki wanda Marganu ya kwantar da Jaanu.
Nan take suka yi arba da gimbiya Jaanu kwance a ƙasa, jini yana ta zuba daga ƙasanta har ya ɓata mata kaya.
Ga dukkan alamu dai, Marganu fyaɗe mai ƙarfi yayi mata.
Aymanul Faris ya kwarara uban ihu, wani mugun jiri ya ɗebe shi ya sulale ƙasa sumamme.
Jaruma Riya tana ganin haka tausayin Aymanul Faris da gimbiya Jaanu ya kamata.
Cikin gaggawa ta ruga wajen da gimbiya Jaanu ke kwance tayi mata magani daidai saninta, jinin ya daina zubowa.
Kafun ta dawo inda Aymanul Faris ke kwance, Kuffuru da Marganu suka rugo cikin wannan ɗaki.
Sarki Kuffuru ya rugo da gudu kan jaruma Riya ya afka mata da azababben yaƙi.
Ta zaro takubbanta ta tare shi, shi kuma Marganu saiya tunkari inda Aymanul Faris da gimbiya Jaanu ke kwance zai ƙarasa su.
Sarki Kuffuru ya cika da tsananin mamaki saboda ganin ƙwarewa da iya yaƙi a wajen jaruma Riya.
Saboda tun da ya fara kai mata sara da suka ko sau ɗaya bai same ta ba.
Abinda ya sake ɓata masa rai shi ne, ba wai iya kare kanta take ba, a'a, har mayar masa da martani take.
Marganu yana ƙarasowa gaban Aymanul Faris ya ɗaga takobinsa ta haske sama zai caka masa a ƙirji.
Sai dai kafun yayi hakan, gagarumin baƙin hayaƙi ya cika wannan waje.
Nan take aka gabza musu naushi shi da sarki Kuffuru.
Cikin tsananin mamaki suka miƙe zaune, wannan baƙin hayaƙi yana gama yayewa suka hango Aymanul Faris da jaruma Riya suna ta gudu goye da gimbiya Jaanu.
Nan take Marganu da Kuffuru suka take musu baya da gudu, sai dai kafun su riske su. Tuni Aymanul Faris ya fiddo dawakan nan na haske sun hau.
Kamar walƙiya haka suka ɓace musu lokaci ɗaya.
Sarki Kuffuru ya kwarara uban ihu, ya juya wajen Marganu.
Marganu yayi murmushi ya ce, "Mu sake haɗuwa a karo na gaba!"
Nan take jikinsa ya saje da kalar hasken wannan waje ya ɓace ɓat!
****
Yau *03/06/2023*
Babi na gaba zaizo *05/06/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 134: *Babbar Matsala*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
U-M-S
*
Aymanul Faris da jaruma Riya suna tsakiyar gudu a cikin wannan daji bisa dawakansu dauke da gimbiya Jaanu, aljani Ranganu ya bayyana a saman kansu, cikin gaggawa yasa hannayensa ya dauke su gaba daya ya tashi da su sama.
Daga wannan lokaci basu san abinda ya sake faruwa ba, kawai farkawa suka yi suka gansu a cikin birnin Darul Barban. Ga Hajriya da wata likita tsaye akansu.
Aymanul Faris ya yunkura zai mike tsaye, wannan likita ta dakatar da shi da hannayenta.
“Kayi hakuri akwai mummunan duka a gadon bayanka, idan ka ce zaka mike daga yanzu zaka warware maganin da na saka maka a wajen,”inji likitar.
Aymanul Faris yana jin haka ya koma ya kwanta, hawaye suka taru a idanunsa ya dubi Hajriya ya ce, “Mama! Ina matata da kuma Arya?”
Hajriya ta dafa kafadarsa ta ce, "Ka kwantar da hankalinka, ɗana. Matarka da Arya suna nan lafiya. Idan ka warke zamuje inda suke."
Aymanul Faris yana jin haka ya gyada kai, sannan tunanin abubuwan da suka faru suka fara dawowa kansa
An yiwa Arya fyade!!! Wannan shi ne abinda ya tsaya a zuciyar Aymanul Faris, ya gagara rike hawayensa ya fashe da kuka.
Hajriya tana ganin haka ta baiwa wannan likiya wani umarni, take likitar ta baiwa Aymanul Faris maganin barci, take ya fara minshari.
Saida Aymanul Faris ya shafe kwanaki uku kwance a cikin wannan daki yana jinya, sannan wannan rauni dake gadon bayansa ya warke.
A wannan rana da sassafe ne, Aymanul Faris ya farka daga barci.
Idanuwansa suna budewa, tunanin Arya ya fara fadowa ransa.
Cikin gaggawa Aymanul Faris ya sauko daga kan wannan gado sannan ya tunkari kofar fita daga cikin wannan daki, saura kadan ya iso bakin kofar yaga an turo kofar ciki.
Lamarin da yasa ya tsaya kenan domin mai shigowa. Matarsa Riya yaga ta shigo cikin dakin.
Koda ta ganshi tsaye bisa sawayensa sai gagarumin farin ciki ya lullubeta ta ruga da gudu ta rungume shi akan kirjinta tana mai tsananin farin cikin ganinsa a cikin koshin lafiya.
"Mama ce tazo nazo na kiraka, idan jikinka yayi sauki. Kazo ka sameta a dakin da ake jiyyar Arya!"
Aymanul Faris yana jin haka yayi gaggawar cewa, "Kiyi maza, ki kaini wannan daki."
Jaruma Riya ta juya da sauri ta nufi wani bangare dabam na wannan gida, Aymanul Faris ya take mata baya.
Bayan gajeren lokaci suka iso kofar shiga wani katoton daki, wanda musamman aka gina shi domin yiwa mutane jiyya.
Aymanul Faris yasa hannunsa ya bude kofar shiga dakin, sannan suka kunna kai izuwa cikin dakin.
Tun daga nesa suka hango gimbiya Jaanu kwance akan wani gado, an lullube jikinta da bargo iya kirjinta zuwa sama kawai aka bari.
Idanuwanta a rufe suke wanda hakan yasa Aymanul Faris yayi tunanin ko barci take.
Barban, sarki Ranganu, Hajriya da likita Laziyya suna kewaye da wannan gado wanda take kwance akansa.
Koda suka ga Aymanul Faris ya shigo cikin wannan daki, sai suka buda masa ya karasa gaban wannan gado.
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki bisa ganin Barban a wannan waje amma son ganin halin da masoyiyarsa take ciki yasa ko kyakkyawan kallo bai yiwa Barban ba.
Aymanul Faris ya karasa gaban wannan gado ya tsaya, ya mika hannunsa guda ya taba fuskar Arya.
Jikinta yayi sanyi tamkar babu wani abu dake damunta.
Aymanul Faris ya dubi Ranganu ya ce, "Mene ne abinda ke faruwa da masoyiyata?"
Ranganu ya dubi Laziyya ya gyada mata kai. Nan take Laziyya ta fara yiwa Aymanul Faris bayani.
"Kayi hakuri, tau'rin. Marganu ya yiwa Arya fyade mai karfi wanda yasa jini ya balle mata. Ba don jaruma Riya tayi mata aiki na gaggawa ba, da tuni ta dade da mutuwa.
"Wannan fyade da Marganu yayi mata ya illata ta sosai. A yanzu ko tafiya ba zata iya yi ba, dole sai anyi jiyyarta tsahon lokaci."
Aymanul Faris yana jin wannan batu ya kwarara uban ihu ya durkushe kan gwiwowinsa, yana tsinewa Marganu.
Ranganu ya dafa kafadar Aymanul Faris sannan ya tashe shi tsaye suka fuskanci juna ya ce, "Kayi hakuri, tau'rin. Tabbas Marganu ya cutar da masoyiyarka.
"Inda ace abin ya tsaya a iya jiyyarta ne da da sauki. Kayi sani cewa, kasancewar ba kaine mutum na farko da zai fara mu'amala da jinin Arya ba yasa gagarumar matsala ta afku.
"A halin yanzu dole ne mu jira zuwa kwanaki arba'in domin mu tabbatar da cewa, wannan fyade da Marganu yayi mata ciki bai shiga ba.
"Idan fa ciki ya shiga komai ya tarwatse, saboda an sirka mata jini. Hakan zai sa koda jininta ya shiga cikin jikinka ba zai farkar da babban sirrin dake cikin jininka ba..."
Aymanul Faris yana jin haka ya tari numfashin Ranganu ya ce, "Haka ba zata faru ba. Ba zan iya jira zuwa kwana arba'in, ba tare da na dauki fansar abinda ya yiwa Arya ba."
Ranganu ya dafa Aymanul Faris da hannunsa guda ya ce, "Ka kwantar da hankalinka babban jarumi, ka saurari bayanan da zan yi maka."
Aymanul Faris yana jin wannan batu ya cije baki ya sunkuyar da kansa cikin takaici.
"Shin ka san cewa, wannan Marganun da yazo birnin Damashkar yayi barna ba cikakken Marganu bane?
"Idan na tuna wannan batu shi ne yake saka min farin ciki, naji kamar cewa, juna biyu ba zai shiga ba.
"Dukda cewa da wuya juna biyu ya shiga, dole muna bukatar sake tsarkake jinin Arya."
Aymanul Faris yana jin abinda Ranganu ya ce, "Tayaya zamu iya tsarkake jinin nata?"
Ranganu ya ce, "Kayi sani cewa, gangar jikin Marganu tana cikin wata tukunya a daular Gorgon tana zukar sinadarai. Duk ranar da ya kammala zukan wadannan sinadarai zai farkar da babban sirrin jikinsa na haske. Wannan wanda ka gani a birnin Damashkar somin-tabi ne kawai akan na ainihin.
"Kasancewar Marganu ya hada kai da ma'abota Bankai yasa suka bashi kyautar takobin Bankai mai mataki na dari wato ta sarauniya Yilan.
"Marganu ya hade takobinsa ta haske da takobin Bankai a waje guda, hakan yana bashi damar ya kai saran Bankai-mai-tafiya kuma mai dauke da sinadarin haske.
"Ya gwada hakan akanka sannan ya gwada akan sarki Kuffuru. Dukkanku wannan hari yayi tasiri akanku, ba don kun sami taimako na gaggawa da tuni ya kashe ku.
"Ganin wannan abu da ya faru shi ne yasa na yanke shawarar ba zamu bari kayi tarayya da jinin Arya wanda aka sirka ba, dole muna bukatar a tsarkake shi.
"Saboda idan muka yi kuskure, ka farkar da tau'rin wanda bai kai na Samudul Ansari karfi ba. Babu abinda zai iya yiwa ISRABIL cikin kankanin lokaci, ISRABIL zai gama da kai.
"Don haka dole ne mu sake tsarkake jinin Arya."
Ranganu yana zuwa nan a zancensa yayi gyaran murya domin sake tattaro hankalin Aymanul Faris.
"Marganu baida wani bambanci a wannan lokaci da ma'abota Bankai, abinda ya bambanta su kawai shi ne, ISRABIL.
"Kuyi sani cewa, duk wani sharri na takobin Bankai ko kuma na ma'aboci Bankai akwai maganinsa a cikin dakin bauta na daular Gorgon wanda ke saman tsaunin Hajarul Gorgon.
"Na gudanar da bincike akan Arya, wanda ban so na sanar da kai shi daga yanzu ba.
"Tabbas Marganu ya gurbata mata jini, hakan zaisa koda jininku ya hadu, tau'rin ba zai farka a jikinka ba.
"Hanya daya da zaka sake tsarkake wannan jini nata shi ne, dole kaje saman tsaunin Hajarul Gorgon, ka shiga cikin wannan gidan bauta ka dauko tukunyar dake dauke da sinadarai Yirlish.
"Amfanin sinadarin Yirlish shi ne, kashe duk wani dafi da ma'aboci Bankai ya samar.
"Kun karanta a tarihi Samudul Ansari ya sha wani tsumi a jikin wata ma'abociya Bankai sa'adda dafi ke daf da zagaye jikinsa.
"To, ku sani cewa wannan tsumi da ya sha daga sinadarin Yirlish aka samar dashi.
"Kasancewar jinin Marganu ya hadu da na Arya hakan yasa dafi ya shiga jikinta.
"Dafin zai ci gaba da zagaye jikin Arya har zuwa tsahon lokaci.
"Kasancewar jininta yana da karfi yasa dafin ba zai kasheta ba, amma zai ragewa jininta ƙarfi. Ya zamana cewa jinin baida wani amfani a duniya.
"A lissafin da na gudanar wannan dafi zai gama zagaye jikinta ne a ranar da Marganu zai fito daga cikin wannan tukunya da yake zuƙar sinadarai a cikinta.
"Saboda wannan dalili dole ne ta kowanne hali, Ayman kaje saman wannan tsauni ka ɗauko tukunyar dake ɗauke da sinadarin Yirlish a yiwa matarka wanka dashi."
Aymanul Faris yana jin wannan batu yayi shuru yana tunani, daga can ya numfasa ya ce, "Ina so kayi min izini yanzun na tafi daular Gorgon na ɗauko wannan sinadari."
Ranganu yayi murmushi ya ce, "Shiga daular Gorgon yana da ƙa'idoji waɗanda idan ka kiyaye su, zaka sami nasarar abinda kaje nema. Amma dukda sai kasha baƙar wahala."
"Faɗa min dokokin," inji Aymanul Faris.
Ranganu ya sake yin murmushi ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Kayi sallama da wadannan masoya naka, zamu tafi izuwa wajen da zanyi maka bayanin dokokin,"
Aymanul Faris yana jin haka ya ƙarasa gaban Hajriya ya risina a gabanta, ta dafa kafaɗarsa da hannunta guda suka yi sallama.
Aymanul Faris ya rungume matarsa Riya sannan ya sumbaci hannun Jaanu.
Ranganu ya ɗauke shi a gadon bayansa, suka lulluƙa a cikin gajimare suka ɓace ɓat!
A cikin fadar aljani Ranganu suka bayyana.
Kai tsaye Ranganu ya kai Aymanul Faris cikin wani ƙaramin ɗaki dake gefen wannan fada tasa.
Aymanul Faris yayi arba da tarkace kala daban-daban a cikin wannan ɗaki da kuma zane-zanen taswirori.
Ranganu ya dafa gefen ƙirjin Aymanul Faris da hannunsa guda, take wannan baƙin hayaƙi ya soma shigowa cikin wannan ɗaki.
Hayaƙin yana cika wannan ɗaki Aymanul Faris ya dawo hayyacinsa. Wata nutsuwa da kamala tazo masa, ya fuskanci Ranganu sosai.
Ranganu ya nunawa Aymanul Faris wata taswira da aka rubuta DAULAR GORGIN a samanta da manyan baƙaƙe.
Ya nuna wata hanya dake gefen wani ƙaramin kogi ya ce, "Ta wannan hanya zaka shiga daular Gorgon.
"Kamar yadda wannan taswira ta nuna, tun daga kan wannan hanya har zuwa kan Hajarul Gorgon babu babban birni guda daya da zaka wuce ta cikinsa, kaga kenan ba zaka fuskanci matsalar abokan gaba sosai ba.
"Idan kaje gindin wannan tsauni sannan ka haye kansa. Zaka haɗu da masu tsaron gidan bautar ma'abota Bankai guda biyu.
"Wannan baƙin hayaƙi zai iya kashe maka guda ɗaya, kai kuma sai kayi ƙoƙari ka kashe guda.
"Babbar sa'ar da ka taka ma ita ce, kana tare da Saif-Al-Barzaƙ.
"Doka ta farko: Kada ka kuskura ka shiga wannan daula idan ba ta wannan hanya da na nuna maka ba.
"Doka ta biyu: Kada ka kuskura ka yaƙi ma'abota Bankai da wata takobi dabam, idan ba Saif-Al-Barzaƙ ba.
"Doka ta uku: Kada ka kuskura ka ce zaka wuce wannan tsauni kaje gidan sarautar Marganu kace zaka farmake shi saboda ba zaka yi nasara ba.
"Doka ta huɗu: Kana ɗauko wannan tukunya ka dawo birnin Darul Barban cikin gaggawa.
"Idan ka kiyaye waɗannan dokokin kamar ka samu nasara akan wannan aiki da zaka je ne. Fatan nasara!"
Ranganu yana gama yiwa Aymanul Faris waɗannan bayanan bai jira yayi tambaya ko ya nemi ƙarin bayani ba, ya dafa shi suka ɓace ɓat daga wannan waje.
Aymanul Faris da Ranganu suka bayyana a wani waje mai nisan gaske da wannan daula.
Ranganu ya fiddo wani ingarman doki wanda bai kasance na sihiri ba, ya baiwa Aymanul Faris.
Nan take suka yi sallama ya sake yiwa Aymanul Faris fatan samun nasara ya ɓace ɓat!
Aymanul Faris ya haye saman wannan ingarman doki, ya tunkari wannan hanya wadda Ranganu ya ce ta ita ce kaɗai zai shiga daular Gorgon salim-alim.
Aymanul Faris ya ci gaba da gudu akan ingarman dokinsa har ya hawo saman wannan hanya.
Bai fuskanci matsalar komai ba, har yazo wata iyaka wadda aka yi gajeren gini sannan aka kafa tutar mutum ta gashin maciji.
Aymanul Faris ya fiddo wata hula koriya da Ranganu ya bashi ya saka akansa.
Ai kuwa yana saka hular wasu macizai na sihiri suka bayyana akanta suka fara yawo akansa. Idan ka ganshi zaka ɗauka ɗan ƙabilar Gorgon ne.
Aymanul Faris yayi ta ratsawa ta ƙauyukan dake kan hanyar, yana wucewa ba tare mutum ɗaya ya tsayar dashi ba. Saboda duk a tunaninsu ɗan ƙabilar su.
Yana wuce ƙauyuka guda uku ya hango Hajarul Gorgon a can cikin dokar daji, tazararsa da wannan tsauni tana da nisan gaske amma saboda girma da tsahon tsaunin yana hango shi.
Aymanul Faris yana ganin haka ya ƙara azama, ya yi ta cin hanya.
Sai da ya kwana uku yana tafiya sannan ya iso gindin wannan tsauni.
Saida Aymanul Faris ya tsaya ya gyara makaman yaƙinsa, sannan ya fara hawa kan wannan tsauni.
Dokin nasa yayi ta tafiya akan wannan tsauni a hankali tamkar mai hawa lanƙwasashshen bango.
Ai kuwa bai yi nisa da fara hawa tsaunin ba, ya fara cin karo da dakarun Gorgon.
Aymanul Faris ya zaro Saif-Al-Barzaƙ duk wanda ya ɓullo masa sai ya aika masa saran takobi-mai-tafiya ya gama dashi.
Kafun a jima Aymanul Faris ya hallaka wajen dakaru ashirin.
Lamarin da yasa suka daina ɓullowa suna shan gabansa kenan, ya ci gaba da tsala azababben gudu har ya hawo saman wannan tsauni.
A saman wannan tsauni Aymanul Faris yayi arba da ƙatoton gidan bauta kamar yadda aka sanar dashi.
Amma saɓanin dakaru guda biyu kamar yadda Ranganu yace a wannan lokaci dakaru guda uku ne.
Biyu daga cikinsu ma'abota Bankai ne amma ɗaya kuma ga dukkan alamu BES ce.
Jikinta yana lulluɓe da manyan alkyabba wadda take fitar da haske mai razanarwa.
Koda waɗannan dakaru guda uku suka yi arba da Aymanul Faris sai suka rugo daga inda suke tsaye suka ƙaraso inda yake.
Ma'abota Bankai ɗin guda biyu suka kewaye shi, ita kuwa BES ɗin sai ta tsaya ta ƙura musu idanu.
Ba tare da ɓata lokaci ko kuma kace-nace ba, suka afkawa Aymanul Faris da mummunan yaƙi.
Ai kuwa take ya zaro Saif-Al-Barzaƙ ya tare su.
Nan take suka fara gwabza azababben yaƙi a saman wannan tsauni.
A wannan rana Aymanul Faris ya ganewa kansa sharri da muggan hare-haren Bankai kamar yadda yake jin labari.
Ba don a fusace yake wannan yaƙi ba, da babu yadda za'ayi ya tsira da rayuwarsa daga sharrinsu.
A wannan rana takobin Saif-Al-Barzaƙ bata wani tasiri akan wadannan dakaru saboda manyan ma'abota Bankai ne.
Bugu da ƙari kuma gashi babu tau'rin a tattare da wannan takobi.
Koda sa'a guda ta shuɗe babu wanda ya samu wata nasara ta azo a gani a cikinsu sai suka daka tsalle baya, suka bar Aymanul Faris a gaban BES.
BES ta zaro takobinta Bankai mai mataki na sittin da shida, bayan wannan babban mataki na takobin akwai sirrin haske na musamman a tattare da ita.
Tun kafun ta iso gaban Aymanul Faris ƙawanyan haske suka fara bayyana a wannan waje.
Tana isowa gaban Aymanul Faris suka ruguntsume da azababben yaƙi mai ban tsoro wanda yayi matuƙar bata mamaki.
Saboda wannan takobi dake hannunta tamkar haske haka take.
Da zarar ta kawowa Aymanul Faris sara da takobin, idan ya kai takobinsa ya kare.
Sai kaga takobin nata ya ratsa ta cikin takobinsa tamkar haske, amma kafun ta riske shi zai kauce cikin zafin nama.
Lamarin da yasa wannan budurwa cika da tsananin mamaki kenan.
Wanne irin zafin nama Aymanul Faris yake da, wanda yake bashi damar kaucewa saran takobin Bankai mai babban mataki?
Haka dai suka ci gaba da gumurzu, ita tana ta ƙoƙarin kaiwa Aymanul Faris sara shi kuma yana kaucewa. Har tsahon ɗan lokaci.
Waɗannan ma'abota Bankai dake tsaye a bayan wannan budurwa suna ganin haka, suka kewayo ta bayan Aymanul Faris cikin sanɗa.
Nan take suka haɗa takubbansu a waje guda. Ɗaya mai mataki na arba'in, dayar kuma talatin. Idan aka haɗa Bankai mai mataki na saba'in kenan.
Cikin shammata suka jefa wannan takobi cikin iska. Maimakon ta faɗo ƙasa kamar yadda kowa zaiyi tsammani, kawai sai ta saje da kalar wannan waje ta ɓace ɓat!
Aymanul Faris yana cikin kare hare-haren wannan budurwa kenan, yaji an caka masa takobi ta baya.
Wani irin azababben zogi ya rufe shi, a daidai lokacin kuwa, wannan budurwa ta kawo masa wani wawan sara zata datse masa wuya.
Aymanul Faris ya daka tsalle gefe guda ya kaucewa wannan sara nata.
Sai dai yana dira ƙasa wani azababben dafi ya soma yiwa gaɓoɓin jikinsa sallama.
Da farko daga ƙasusuwan kafaɗarsa abun ya soma, sannan ya sauƙo kan ƙasusuwan damatsansa da hannayensa.
Hatta Saif-Al-Barzaƙ sai da ta yiwa Aymanul Faris nauyi a wannan lokaci, ta suɓuce zata faɗi ƙasa ya taro ta.
Cikin ƙarfin hali ya taro takobin.
Dafin ya

Please Login or Register in order to submit comment