Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guda da ita.
Wani jan haske ya fice daga cikin takobin, ya shige cikin jikin Rauziyya.
Da farko tamkar babu wani abu da zai faru.
Rauziyya ta sake ɗaga hannayenta sama waɗannan takubba suka sake dira, ta sake afkawa Marganu amma a banza.
Bata isa tayi yaƙi da Marganu a haka ba. Akwai babban sirri a jikinsa wanda yake hana komai tasiri akansa.
Abu ɗaya da za'a kira wannan yaƙi da suke a wannan lokaci shi ne, Marganu yafi ƙarfinta, dole ta koma ta sake shiri.
"Kun makara, ISRABIL ya gano wane ne shi!"
Abin mamaki ba Marganu ne yayi wannan magana ba. Wannan abu dake gefen zuciyarsa shi ne ya furtawa Rauziyya waɗannan kalmomi.
Mamaki da kwakwanto suka bayyana ƙarara akan fuskar Rauziyya.
Mene ne wannan abu wanda ke gefen ƙirjin Marganu, sannan tayaya ya gano cewa, suna farautar ISRABIL?
Inda ace abin ya tsaya iya mamaki da kwakwanto, to da da sauƙi a daidai lokacin hannun Rauziyya ya fara haske yana kumbura.
Zogi da raɗaɗi ya addabeta, kafun tayi wani yunƙuri tuni hannun yayi bindiga ya tarwatse.
Ta zamo mai hannu ɗaya.
Marganu yayi tsalle ya bayyana a gabanta, kafun tayi wani yunƙuri tuni ya caka mata takobin-haske a ƙirji.
Sirrin haske dake cikin jikin Marganu ya fito ya shiga cikin takobin dake hannunsa, sannan ya shiga cikin zuciyar Rauziyya.
Idanuwanta suka koma kalar wannan launi na takobin Marganu, fatar jikinta ma ta juye izuwa haka.
Rauziyya ta fara wani irin nishi, jikinta ya fara ɓari.
Ranta na daf da fita, hazo-hazon wani shirgegen aljani ya fara bayyana a wannan waje.
Duk wannan abu dake faruwa, Firziyya tana can cikin wannan kogo tana kallo.
Sannu-a-hankali siffar aljani Barzasa mai gidan Rauziyya ta bayyana a wannan waje.
Aljani Barzasa yana gama bayyana a wannan waje, ya dubi Marganu a fusace.
A wannan lokaci gangar jikin Rauziyya ta gama yin sanyi. Idanuwanta suka sandare, ta daina motsi.
Wannan lokaci ne Rauziyya ta ƙarasa mutuwa.
Barzasa na ganin ya fusata. Zuciyarsa ta fara tafarfasa tamkar zata ƙone.
Ya durƙusa kan gwiwowinsa yayi ta jimamin mutuwar sarauniya Rauziyya.
Kafun ya ɗaga kansa ya dakawa Marganu wani irin wawan harara tamkar fusataccen zaki.
"Ka kashe mini sarauniya! Jininta ba zai tafi a banza ba! Yau zan kashe ka sannan nasha jinin ka!!!" inji Barzasa.
Marganu yayi dariya ya ce, "Kashe ISRABIL sai cikakken shiryayye. Edwan tayi kaɗan, haka ma shugabanta Barzas."
Barzasa yayi murmushin mugunta ya ce, "Yau zaka ga salon yaƙi wanda baka taɓa tsammanin akwai mai kama dashi a duniya ba!
"Yau zaka ga dalilin da yasa sauran aljanun duniya suke tsoron zuwa tsaunin Barzasa.
"Wucewa da kayi ta cikin birninmu a shekarun baya, sa'a kawai ka taka, bana nan!
"Amma yau gani ga ka... Babu abinda zai raba mu, idan ba mutuwa ba.
"Yau zaka ga ɗalasimin-taswira wanda babu mai mallakinsa a duk duniya face NI!!!"
Marganu yayi murmushi ya nuna Barzasa da takobinsa ta haske ya ce, "Nima yau zan nuna maka babban sirrina wanda babu wanda yake saninsa face matacce.
"Ka tambayi gawar wannan shaiɗaniyar zata sanar da kai.
"SIRRIN ISRABIL" Abin mamaki wannan kalma ta ƙarshe ba Marganu ne ya furta ta ba.
Wannan abu dake gefen zuciyarsa shi ne ya furtawa Barzasa.
Barzasa yayi murmushin mugunta ya ce, "A filin yaƙi ba'a surutu. Abu guda ake shi ne ZUBAR DA JINI!!!
"Yau zan yi nasara akan ka, kuma zan bayyanar da babban sirrina ga duniya, wanda zai sa a sake tsorata da lamarin mu!!!"
Barzasa yana gama faɗin haka, ya fiddo wata takarda daga cikin aljihunsa, ya warwareta.
Abin mamaki, akan wannan taswira hoton wani ƙatoton daji ne.
Barzasa ya cilla wannan taswira sama. Kafun ta faɗo ƙasa tayi haske, sannan ta zubo ƙasa.
Wannan waje da suke tsaye akansa ya fara haske yana girgiza.
Kafun daga bisani wajen gaba ɗaya ya ɓace ɓat!
Wannan taswirar daji wadda ya cilla sama haskenta ya maye gurbin wajen.
Da farko abin a matsayin haske yake, kafun daga bisani ya juye izuwa na ainihi.
Ga shi dai Marganu da Firziyya suna tsaye a wajen, ba wai ɓacewa suka yi ba.
Amma an canja musu waje.
Wani gabjejen jeji ya bayyana mai yawan dogwayen bishiyoyi da tsaunika.
Ihu da kururuwar manyan dabbobi na tasowa daga cikinsa.
Barzasa yayi murmushi ya nuna Marganu da takobin dake gadon bayansa wadda zata kai kamu arba'in ya ce.
"Wannan shi ne ƙarfin ikona. Zan iya sauyawa abokin gabata muhalli koda yana so ko baya so. Na kaishi inda nake so sannan na hallaka shi!
"A yanzu kaima nayi amfani da haka akanka, yaro!"
*****
Yau *15/05/2023*
Babi na gaba zaizo *18/05/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 125: *Lokacin Tafiya Yayi*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U-M-S
*
Marganu ya nuna Barzasa da takobinsa ya ce, "Cikakken jarumi shi ne wanda zai iya fafata yaƙi a duk inda ya tsinci kansa!
"Koda daga cikin wannan duniya zaka fitar damu, hakan ba zai na fasa yaƙi da kai ba... Yau zan rushe wannan ƙabila ta ku wadda take shan jinin mutanen da basu ji ba, ba su gani ba."
Marganu yana gama faɗin haka ya ruga da gudu kan Barzasa.
Kafun ya isa inda Barzasa ke tsaye wannan abu dake gefen zuciyarsa, ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
Dukda cewa Marganu baya ganin wannan abu amma yasan cewa abun ya disashe.
Ko kaɗan hakan bai ɗagawa Marganu hankali ba, domin a imaninsa indai yana tare da takobinsa. Sai inda ƙarfinsa ya ƙare.
Barzas ya caka hannunsa a cikin ƙasa ya zaro wata zabgegiyar takobi mai zanen taswira akan ƙarfenta.
Marganu na ƙarasowa gabansa ya kai masa wawan sara da takobin dake hannunsa.
Barzas yayi murmushi ya ɗaga wannan takobi tasa sama, ya juyata a cikin iska.
Take wannan daji gaba ɗaya ya juya. Marganu wanda ke tsaye a gabansa ya kawo masa hari, ya juya.
A da Marganu fuskantar Barzas yake amma a yanzu dajin ya juya, Marganu ya juya masa baya.
Barzas ya sari jikin Marganu da takobinsa. Lafcecen sara ya bayyana a gadon bayan Marganu tun daga wajen kafaɗarsa har kusa da ƙugunsa.
Jini yayi feshi sannan ya fara zubowa ƙasa. Marganu ya kwarara uban ihu.
A gaggauce ya juyo zai sake afkawa Barzasa. Barzas ya sake kaɗa takobinsa wannan daji ya sake juyawa. Marganu ya sake bashi baya.
Barzas ya ƙara kafta masa sara a gadon baya. Wani lafcecen sara ya sake bayyana a gadon bayan Marganu.
Kafun kace me wannan, jini mai tsananin yawa ya fara zubowa daga gadon bayan Marganu.
Babbar matsalar yaƙi da aljani mai sarrafa taswira irin Barzas shi ne, zai iya sauyawa abokinsa muhalli.
Bayan wannan a duk sa'adda aka kawo masa hari, zai iya sauya taswirar wajen gaba ɗaya ya juya, harin dake tunkaro shi ya koma baya.
Idan yaga dama zai iya amfani da taswirar yayi ta sauyawa abokin-gabarsa muhalli yana bashi baya, ya yaƙe shi yadda yake so.
Kamar yadda wannan aljani yake amfani da taswirar wannan daji, yana juya dajin, yadda Marganu zai kawo masa hari ta gaba amma dajin yana juyawa Marganu zai bashi baya.
Waɗannan raunika dake gadon bayan Marganu suka ci gaba da zubar da jini, wani irin mugun jiri ya soma diban Marganu.
Barzas ya bushe da dariyar mugunta, ya nuna Marganu da tsinin takobinsa ya ce, "Ban taɓa ɗaukar alƙawari ban cika ba. Duk abinda na saka a gaba, sai nayi nasara.
"Tun sa'adda ka wuce ta cikin birnin mu, nayi arba da yanayin jininka. Daga wannan lokaci na ƙwallafa raina akan sai nasha wannan jini naka.
"Tabbas a yau babu abinda zai hana ni, shan jininka. Yanzun nan ma kuwa!"
Barzas yana gama faɗin haka ya sake zaro wata taswira a cikin aljihunsa. Abin mamaki kan wannan taswira kuwa, hoton wani gabjejen tsauni ne wanda kana ƙura masa idanu tunanin tsaunin Barzasa zai zo kanka.
Barzas ya cilla wannan taswira sama, take tayi haske sannan ta ɓace ɓat.
Wannan daji da suke cikinsa ya fara girgiza yana haske, kafun daga bisani ya ɓace ɓat.
Tsaunin Barzasa da birnin sarauniya Rauziyya ya maye gurbin wannan waje.
Abin mamaki a tsakiyar wannan ƙaton gidan bauta suka bayyana, ga jama'a sun cika shi tirim, ga gunkin Barzasa wanda har a wannan lokaci ba'a gyara shi ba.
Koda jama'a suka sake yin arba da Marganu a hannun Barzas sai suka cika da tsananin mamaki.
Wannan mutumin wanne irin hatsabibi ne?
Sau nawa ana kawo shi wannan waje domin a yanka shi amma har yau an gagara?
Koda suka yi arba da gawar sarauniyarsu a gefen Barzasa sai duk suka durƙushe kan gwiwowinsu, suka sunkuyar da kawunansu ƙasa.
Barzas yayi tsawa duk suka nutsu suna sauraron abinda yake cewa.
"Rauhanatul-Ziyya Edwan ta mutu a hannun wannan taƙadirin yaro.
"Amma abinda bai sani ba shi ne, jininta ba zai tafi a banza. Tun da ya kasheta yau, shima yau ce ranar mutuwarsa.
"Zan yi amfani da wannan dama na sanar da ku babban sirrin da zan samu, bayan na sha jinin wannan yaro.
"Kuma za ku ga dalilin da yasa na dage akan lallai sai nasha jinin sa.
"Wannan siffa da kuke ganina da ita, ba ainihin siffata ba ce.
"Ba zan taɓa komawa ainihin siffata ba, face na zuƙi jinin ISRABIL.
"Idan na zuƙi jinin ISRABIL zai kore ƙaramin jinin dake cikin jikina, sannan nasa ya maye gurbin nawa.
"Idan na samu jinin ISRABIL zan iya ladabtar da daular Gorgon.
"Idan na ladabtar da Gorgon zamu koma cikinta mu ci gaba da rayuwa.
"Babu yadda za'ayi ace daula kamar Gorgon tana ƙarƙashin ikon mu, ba mu gagari duniya ba."
Barzas na gama faɗin haka ya zaro waɗansu abubuwa guda biyu masu tsananin tsini kamar allura ya tunkari inda Marganu ke kwance.
Niyyarsa ita ce yana zuwa zai caka abubuwan biyu a daidai inda zuciyar Marganu take, ya zuƙi jininsa.
Dukda cewa an sauya muhalli amma har a wannan lokaci Firziyya tana cikin wannan kogo tana kallon abinda ke faruwa.
Ita dai tana nan a wajen da take wato cikin kogo, amma a duk sa'adda aka sauya muhalli tana ganin Marganu da Barzasa kamar hotuna.
A wannan lokaci tsaunin Barzasa, Marganu, shi Barzas ɗin da duk mutanen dake wannan waje a matsayin hotuna take kallonsu.
Barzas yana zuwa gaban Marganu ya ɗaga waɗannan abubuwa zai caka su a ƙirjin Marganu, bisa mamaki sai yaga ƙirjin Marganu ya fara fitar da wani irin haske.
Hasken ya fara yawo a jikin Marganu, cikin ƙanƙanin lokaci ya gauraye ko'ina da ina. Tsahon daƙiƙu ashirin kacal kafun ya ɓace ɓat!
Barzas yayi mamaki na 'yan daƙiƙu, kafun ya caka waɗannan abubuwa guda biyu a ƙirjin Marganu.
Tsinin abubuwan ya nutse a cikin ƙirjin Marganu.
Cikin gaggawa Barzas ya saka ƙarshen abubuwan a cikin bakinsa domin ya fara zuƙar jinin Marganu.
Bai kammala saka su a cikin bakinsa ba, yaga sun yi haske sun tarwatse.
Barzas ya ja baya cikin tsananin mamaki.
Kafun Marganu ya farfaɗo Barzas ya matso da kasko guda daga kaskon dake wannan waje, ya saita wuyan Marganu da wannan kasko.
Ya zaro zabgegiyar takobinsa ya datsa wuyan Marganu.
Takobin tana nutsewa a wuyan Marganu, itama tayi haske sannan tarwatse.
Saboda tsananin mamaki saida Barzas ya daka tsalle gefe guda, idanuwansa cike da mamaki da al'ajabi.
Wannan takobi da ya yiwa Marganu yankan rago da ita, tana da tsohon tarihi da kuma cikakken sirri.
Ko a mafarki bai taɓa tsammanin za'a samu halittar da zata gagara yiwa illa sai Marganu.
To, amma inda ace iya rashin illata Marganu ne da da sauƙi. Gashi takobin gaba ɗaya ta tarwatse ta hallaka.
Kafun Barzas ya sake wani motsi, Marganu ya bude idanunsa ya miƙe tsaye.
Jikinsa sumul babu alamun waɗannan raunika da takobin Barzas ta ji masa a gadon baya.
Haske ne kawai yake ta ratsawa ta cikin jininsa da kuma jijiyoyinsa.
Marganu ya zaro takobinsa ta haske, sirrin haske ya fito daga wannan ɓangare na gefen zuciyarsa ya shiga cikin takobin.
Barzas yayi kasake yana kallon abin al'ajabi, Marganu ya daka tsalle ya dira a gabansa.
Marganu ya ɗaga takobinsa zai sare wuyan Barzas amma sai ya dakata.
"KAYI MUBAYA'A KO KUMA KA MUTU!"
Abin mamaki ba Marganu ne yayi wannan magana ba, wannan abu dake gefen zuciyarsa ne ya baiwa Barzas umarni.
Barzas ya murtuƙe fuska ya juya ya dubi mutanen dake tsaitsaye a bayansa.
Fiye da shekaru dubu yana matsayin abin bautar ƙabilar Edwan, abin kunya ne a gare shi a gaban idanunsu ya zube ya yiwa yaro Marganu mubaya'a.
Saboda haka ya girgiza kai ya afkowa Marganu, sai dai kafun ya iso Marganu ya sare gefen wuyansa.
Gangar jikin Barzas ta fara kumbura, zata tarwatse.
Cikin gaggawa Marganu ya caka hannunsa a ƙirjin Barzas ya finciko dunƙulen wani abu, sannan ya jefa shi cikin jakar tsafinsa.
Gangar jikin Barzas ta tarwatse izuwa filla-filla sannan ta zubo ƙasa.
Faruwar haka keda wuya, tsaunin Barzasa gaba ɗaya yayi girgiza tamkar zai ruguje ƙasa.
Jama'ar Edwan gaba ɗaya suka zube kan gwiwowinsu suna masu dukan kirazansu suna kiransu kaitonsu.
Ashe ababen bauta ma suna mutuwa?
Nan take tsaunin Barzasa yayi girgiza ya ɓace ɓat! Marganu ya bayyana a cikin wannan daji wanda Barzasa ya fara kawo shi da farko.
Shima dajin ya ɓace ɓat! Marganu ya bayyana a wannan waje wanda suka fara gwabza yaƙi da sarauniya Rauziyya kafun Barzasa ya bayyana.
Marganu ya juya bayansa inda Firziyya take ya jiwo ƙamshinta, ya duba inda abokin tafiyar Rauziyya ke tsaye wato Darwazu ya ganshi tsaye riƙe da takobi yana karkarwa.
Tun da Darwazu yake a rayuwarsa bai taɓa ganin hatsabibanci irin na Marganu ba.
Abinda yasa yake karkarwa shi ne, yasan cewa ba zai iya yaƙar Marganu ba.
Marganu ya ƙwalawa Firziyya kira, nan take ta fito daga inda take ɓoye.
Firziyya tazo bayan Marganu ta tsaya.
Darwazu ya dubi Firziyya cikin tsananin mamaki. Lokaci na ƙarshe da yayi arba da ita sa'adda sarki Kuffuru zai kaita kurkukun azaba-uku ne.
Koda yake mamakin me zaiyi? Wannan hatsabibanci da ya gani a wajen Marganu babu wanda ba zai iya kuɓutarwa daga kurkuku ba.
Marganu da Firziyya suka ƙarasa gaban Darwazu suka tsaitsaya.
Fuskar Marganu babu tsoro ko alamun sassauci ya dubi Darwazu ya ce, "Tambaya ɗaya zaka amsa min, na ƙyale ka kayi tafiyarka!
"A ina zamu riski sarki Kuffuru?"
Sarki Darwazu yana jin wannan tambaya ya fara yin zuru-zuru da idanu, ya rasa amsar me zai bayar.
Su kansu a wannan lokaci, basu san inda sarki Kuffuru yake ba.
"Ban sani ba," inji Darwazu.
Har Marganu ya zare takobinsa zai sare shi, caraf Firziyya ta dakatar dashi ta ce, "Wannan baida laifin komai, ka ƙyale shi kawai ya tafi. Ga dukkan alamu mahaifina yaudarar su yayi."
Marganu yayi shuru yana tunani kafun ya nunawa Darwazu hanya ya ce, "Mun sallame ka!"
Sarki Darwazu ya juya ya nausa cikin daji, ya bar wannan waje.
Gimbiya Firziyya ta sake rungume Marganu cikin tsananin jin daɗi da ƙauna bisa ganin yadda ya kuɓuta daga sharrin Rauziyya da kuma Barzasa.
Marganu da Firziyya suka koma gindin wata doguwar bishiya suka zauna a ƙarƙashin inuwarta domin su huta.
Gimbiya Firziyya ta dubi Marganu ta ce, "Ya masoyina! Shin a haka zaka yaƙi mahaifina?"
Marganu ya ɗan haɗe fuska ya ce, "Ban gane a haka ba? Me kike nufi?"
Gimbiya Firziyya ta ce, "Saboda idan zaka lura dukkan abokan gabarka da ka kashe a yanzu, ba wai jarumtakarka ko kuma ƙarfin damtsenka bane. Wani iko ne na musamman yake ganin bayansu."
Marganu yana jin haka ya haɗe fuska ya dubeta ya ce, "Babu abinda kika sani akaina. Na hore ki da irin waɗannan maganganun. Daga ranar da na aureki, ba za ki sake zuwa filin daga ba. Don haka ki kiyaye shiga irin waɗannan maganganu."
"Ka gafarce ni, ya kai masoyina!" inji Firziyya cikin sanyin murya.
Marganu ya gyada mata kai sannan ya kishingiɗa a cikin wannan bishiya ya rufe idanunsa ya fara barci.
Yana rufe idanunsa tunanin abubuwan da ta faɗa masa ya fara dawowa ransa.
Shi kansa bai san wannan abu wanda ke cikin jikinsa gefen zuciyarsa ba.
Karo na farko da ya fara jin motsin abun, sa'adda ya hallaka Duksum ne. A wannan lokaci abun iya tarwatsa ruhin Duksum yayi.
Amma a halin yanzu abun har fara furta maganganu sannan yana iya raba haske izuwa cikin jikinsa.
Wai shin mene ne wannan abu?
Marganu da kansa yana buƙatar amsa.
A tunaninsa babu mai amsa masa wannan tambaya idan ba Isika ba, don haka cikin gaggawa ya dafa hatimin haske dake kan damtsen hannunsa.
Hatimin yayi haske mai ƙarfi sannan ya kirawo Isika. Nan take Isika ya bayyana a wannan waje cikin gaggawa.
Marganu ya nuna masa wannan abu dake gefen zuciyarsa sannan ya tambaye shi, mene ne wannan abu?
Isika yayi shuru ya kasa kunnuwa yana jin abinda wannan abu yake furtawa.
"SIRRIN ISRABIL" ita ce kalmar da Isika yaji wannan abu yana furtawa.
Isika yayi murmushi ya ce, "Ya shugabana! Amsar wannan tambaya taka a bayyane take. Wannan abu da kake jin motsinsa a gefen zuciyarka shi ne babban sirrin ainihin sunanka ISRABIL!
"Tuni labari ya riski daular Gorgon cewa, abinda suka shafe zamani mai tsaho suna jira ya bayyana wato kai kenan.
"A halin yanzu, sun ɗaukaka sunanka a wannan daula sannan sun haɗa maka gagarumin tsumi wanda za'a saka ka a cikinsa kayi wata guda.
"Wannan abu da suka yi shi ne yasa wannan sirri ya farfaɗo daga jikinka, yanzu kawai jira yake a tsuma shi.
"Idan zaka tuna, ba kai kake kiran abun ba, sai yaga ka kusa halaka sannan yake bayyana. Bayan haka ba kai kake turo sirrinsa izuwa sassan jikinka ba, shi ne yake tura kansa."
Marganu ya gyada kai, "Haka ne!"
Isika ya ci gaba da bayani, "To, idan aka tsuma ka a cikin wannan tsumi da suka samar yanzu, jikinka ya zuƙi sinadaran da suka tanadar wannan abu zai tarwatse ya mamaye ko'ina da ina na jikinka.
"Ya zamana cewa a duk lokacin da ka gama dama, zaka yi amfani da abun sannan zaka iya tura sinadarin sirrin haske izuwa duk inda kake so a jikinka!"
Marganu yayi shuru yana tunani, daga can ya kalli Firziyya sannan ya sake kallon Isika ya ce, "Ina sarki Kuffuru yake a halin yanzu?"
Saida Isika ya ɗan sauya launi sannan ya ce, "Ya shugabana! Ina tunanin yaƙi da sarki Kuffuru a yanzu, mun makara..." Bai ƙarasa rufe bakinsa ba, Marganu ya murtuƙe fuska ya dakatar dashi.
"Saboda me?"
Isika ya ce, "Saboda sarki Kuffuru ba iya su Rauziyya ya yaudara ba, muma ya yaudare mu. Ya ƙyale mutum-mutumi a cikin tawagar su Rauziyya domin ya ja hankalinmu mu kai musu hari.
"Hakan ya bashi damar sake samar da wata runduna dabam mai kama da ta su Rauziyya. Yanzu maganar da nake muku, suna daf da kaiwa Hodon hari.
"Da zarar sun kama Hodon, sarki Kuffuru zai zamo sabon sarkin masarautu guda tamanin da uku.
"Ta ya ya zamu yaƙi babban sarki mai mulkin masarautu guda tamanin da uku, ba tare da cikakken shiri ba?"
Marganu yana jin wannan batu jikinsa yayi sanyi, ya fara tunani akan wannan al'amari.
Marganu shi ne ya gwabza yaƙi da hatsabibai irin su Rauziyya, shi yasan wahalar da yasha. Ba don taimakon wannan abu da ya samu ba, da ba zai kai labari ba.
Ya ya abin zai kasance ga hatsabibin mutum kamar Kuffuru, sannan ace bayan hatsabibancinsa, ga taimakon masarautu tamanin da uku.
Samun nasara kam, ba zai yiwu ba. Sai dai su yi tunanin ragas kawai.
Idan sarki Kuffuru yana taƙama da mulkin waɗannan masarautu guda tamanin da uku. Marganu zai iya zuwa daular Gorgon ya taka matsayinsa na ISRABIL.
Idan yana matsayin ISRABIL zai juya wannan daula kamar gidansa, hakan zai bashi damar yaƙi da sarki Kuffuru.
"LOKACIN TAFIYA DAULAR GORGON YAYI!" inji Marganu.
*****
Yau *18/05/2023*
Babi na gaba zaizo *20/05/2023* da yaddar ALLAH.
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 126: *Shiga dajin Husum*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
U-M-S
*
Ad: *Akwai 126-156 available a WhatsApp, ga duk mai buƙata yayi magana 08136093283. N400 kacal*
*
~Fadar sarki Ranganu, birnin Jai'zin.
*
Sarki Ranganu na zaune bisa ƙasaitacciyar karagarsa ta mulki a cikin fadarsa. Yana sanye da fararen tufafi wadanda aka saba kallonsa da su kullum.
Jim kaɗan Aymanul Faris da matarsa Riya suka bayyana a cikin wannan fada.
Sarki Ranganu yana ganinsu ya basu umarnin zama akan waɗansu kujeru dake gefe ya ce su zauna.
Ba tare da gardamar komai ba, Aymanul Faris da matarsa suka zauna sannan suka fuskanci Ranganu.
Sarki Ranganu yasa wata hadima ta kawowa su Aymanul Faris abinci mai rai da lafiya, sannan ya basu umarnin cin abinci.
Bayan sun gama ci sun sami nutsuwa.
Sarki Ranganu ya dube su ya ce, "Ina taya ku farin ciki bisa shiga wani babi na rayuwa. Ubangiji ya tabbatar da soyayya a tsakanin ku har abada."
Aymanul Faris da Riya suka yi farin ciki bisa jin wannan addu'a da Ranganu yayi musu.
"Bari na sanar da ku dokokin shiga waɗannan dazuzzuka guda huɗu," inji Ranganu.
Aymanul Faris da Riya suka gyara zama suna sauraronsa da kyau.
Sarki Ranganu ya fara magana da cewa, "Daga lokacin da kuka shiga dajin Djinn amfanin tsafi a wajenku ya gama amfani. Saboda idan ba zaku manta ba, komai na Samudul Ansari bada sihirin tsafi aka samar dashi ba, don tau'rin baya amfani da tsafi. Da zallar jarumtaka aka halicce shi.
"Daji na farko babu komai a cikinsa face wannan ƙatoton dodo kamar yadda kuka

Please Login or Register in order to submit comment