Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi masha Allah, sosai dukan mu muka hau dinning table, kowa nacin abinda yaso, niko sai faman juya cup nake, wani had'ad'den k'amshi ne, ya ziyar ci hancina, wanda bana gajiya da sha'kam sa, sosai nake jin dad'in k'amshin.




idona na lumshe kafin na bud'e su, fes na sauke su akan prince Mahmud wanda ke shigowa cikin dinning room, d'in don mik'a gaisuwa ga fulani, hannun sa sakale cikin na gimbiya safiyya, wacce keta faman watsa man harara, niko ba hararar ra bane damuwa ta, kamar yarda naga prince baiko kulani ba, wani d'an bacin raine ya ziyar ceni na d'an kauda idona gefe, wata zuciyar ta ce man tom ai d'akin gaida sa, dad'an hanzari na rusuna, dai dai zai nufi d'akin fulani, na gaida sa.




ido yad'an bini dashi alokacin fulani ta Kai cikin d'akin, k'asa yayi da kansa dai-dai sai tin kunne na, cikin muryar rad'a yace man" karda na fito d'akin nan na tarar dake da wannan shigar ban amince ba, yana karasa fad'in hakam yayi gaba abinsa, ido nabi kaina da shi inason gano illar wannan shigar rigar na kalla wacce baza ta gaza kasa da cibiya taba, sai wandon wanda yad'an matse daga sama ta k'asa ko abud'e yake yad'an kame man daga sama saiko gyalan da na yane iya kaina da shi, gby batula na kalla wacce kusan duk shigar iri d'aya ne Amman ita baiyi mata fad'a ba sai ni, d'aki na nufa Ina d'an tunzura baki,




itako gimbiya safiyya sai faman kad'a kafa take adole ita ga wacce miji ke yayi, ganin hafsat ta nufi d'aki tana tunzura baki sai ta zata ko ca yayi ya sake ta, ranta fari tas take wani sham k'amshi tana kallon yaran aranta tana aiyyana kalan rok'on ta zata yi masau.





shiko sarki Mahmud ita yabi da kallon k'asan ido, yana santin wannan dress na hafsat aransa, sai ca yake gida gidan mutane agama kalle man ke tun kan na ankaro......bara na dawo har kagama kare mata kallo muryar fulani ta maido sa cikin hayyacin sa kansa tad'an sosa kafin yace um..um...daman ca zanyi Ina tweens? cikin daure war fuska fulani tabi yarima da kallo kafin tàce kasan ko wace hafsat agurina? da mamaki yabi ta da kallo kafin yace"a a.



tom ka bud'e kunnuwan ka da kyau danko yanzun zan sanar da kai wacece hafsat a gurina.........✍️

❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_* 38--39





Ido ya kafe ta dasu kafin yace wacce hafsat? Cikin yanayi dake tabbatar da abunda ke cikin ranta tace "hafsat taka, mamaki ne shimfide afuskar sa, kafin yace "tom ummata Ina sua raron ki, kamar daga sama sukaji sallamar yarima faruk tare da gby batula, zama suka yi kafin batula tace, "yaya Mahmud mai keda muwar safiyya ne ? Na ganta zaune afalon fulani sai faman harare 2 take, murmushi ya d'anyi kafin yace"bara na zo umma na, cikin muryar tsokana umma tace "tom nima bara naje gurin maza na kafin ka dawo. da sauri ya dawo ya zauna danko , sosai yake son jin alakar dake tsa kanin, fulni da hafsat, d'insa.






nafasa umma murmushi itama tayi kafin tàce tom ku ara man kunnuwan ku da hankulan ku,.





Akasar itofiya da akwai wani gari mai tarin albarka da yalwar arziki, mutanen dake cikin garin yawan cinsu manoma ne wasu kuma makiyaya, dan hakam ako wanne lokaci baza arasa abinci ko kudi da sauran bukatun na rayuwa agarin.




Abdullah bin Adam shine sarkin garin kuma shine mahaifi agare mu, yasha bakar wahala gurin neman aihuwa duk inda yaje zancen d'aya ne, baida matsala da zata hana sa aihu wa , lokacin ne bai zoba, ahakam har ya Tara matan aure hud'u bacin kwar kwara da sad'aka kai harda barori.


sosai yake buk'atar ganin d'an sa, dan hakam da zarar ance Masa ga mai bada maganin aihuwa zai masa masauki daga nan ya soma sanyo nasa buk'atar, ahakam wataran wani saurayin makaho ya sauka a garin.



tare da k'anwar sa, Yar jagora, a gidan sarki akai masu ma sauki, sarki da kansa yasa aka Kira mar su fada ya soma tambayar su awanne gari suke anam ne yake shaida wa sarki cewa sud'in acan kyauyen garin suke su marayu ne basu da uwa basu da uba, dan hakam yace suzo cikin gari ko zasu samu abinci, tom shine fa Allah ya kawo su, gidan sarki, sarki yayi masu maraba sosai da masuki mai kyu, daga karshe yanemi auren k'anwar makaho mai suna binta. danko alokacin uwar gidan sa ta rasu, bacin yasa mu amincewar binta da wanta makaho aka sha biki binta ta tare agidan sarki. inda daga k'arshe aka yiwa kawu nuhu masaukin na karramawa a gidan sarauta.



sarki ya hanasa bara tun aranar da aka Kai ta cikin gidan amatsaya ta matar sarki saiko tasoma ganin tasko baga matan sarki ba baga sad'aka da baroriba sosai ta soam rama danko tayi k'ank'anta da shanye wahalar da take ciki jakadiya ce kawai take taimakon, ta take son ta fisabilillah.




Adik sanda aka 'bata mata rai sai ta nemi yayan ta ta sanar dashi, tom shiko sai dài yata bata baki Yana kwantar mata da hankali sosai.




Ahakam dai take ta hak'uri, sai kuma wani ciwon ya taso ta agaba sosai take ta faman shan wahala takai wata biyar tana fama da wannan lalura mai wuyar magani duk ta Kare kishiyoyin ta ko da rashin tausayi ba mai kula wa da ita sai fa shi sarkin saiko k'anwar sa goggo maryo ahakam dai har ta Kai wata tara da wannan ciwon wanda aka rasa gane kansa.


tom awatan taran ne saiko ta samu lafiya sosai abun mamaki kamar kar ta warke saiki cikin ta tasoma girma kafin duk su gama gane dalilin hakam saiko ga haihuwa, Ashe fa duk wannan ciwon na ciki ne kuma yaki nuna alamar da za, agane,. aiki ranar da ta tashi da nakuda goggo maryo ita ta soma gano hakam, saiko ta tsaya tsayin daka har Allah ya sauke ta lafiya, ta sankato yarta mace watom ni kenan, sak mahaifina na dauko da labari ya riski sarki saida ya suma dan murna sosai ya soma yanta bayi da sauran kyau tu tuka,

ya rumgume ni Yana ta zubda hawaye tun aranar aka soma shagali,


ranar suna naci sunan kaka ta sa,adatu sai ake man sa,ada sarki da kansa yace adinga kira na da sa,ada.



tun daganan kiyayyar ta dani da ma kawu nuhu ya karu azukatan, sauran mutan gidan, sosai nake ganin gata agidan danko duk wanda ya ta'ba ni jakadiya, tare da goggo maryo ba zasu kyaleba, hakama a fad'a sosai ake nunan so.




shekaru na biyu, kwatsam kuma saiga haihuwar y'an biyu, ga ummata Wanda ba wanda ya ganta da ciki sai dài haihuwar su aka ga tayi, sai dài wata muguwar kiba da tayi sosai nonu wanta suka k'ara girma sa, Adda cikin yasoma fitowa alokacin haihuwar tazo.




Aiko sosai aka soma nuna mata bak'in ciki kishiyoyin ta suka Soma farau tar rayuwar mu nida 'kanne na Zaidu da zainul abideen.



tun asannan bata sake samun ciki ba kuma yaran sai faman bacewa suke ana gane su, ta kai tsawon shakaru biyar sanan kafin kuma tawayi gari da kalar matsanan cin ciwon da yasa ko mai bata iya yiwa kanta, sai fa da aka ankara cikin ta yasoma fitowa kafin ayi wani yunk'uri akai harta haihu ta samu yarta mace mai tsananin Kama da goggo maryo tom shine fa yasa goggo maryo take son Aisha k'anwar mu kuma autar mu danko harta Kai shekaru shida bata sake samun wani cikin ba, ana hakam kwatsam wani dare tan biyu suka hau kuka sosai saida sarki da kansa yace mu dawo d'akin sa aranar mu kwana, acan tsakar dare muka koma can ba wanda yasani, itako Aisha aranar ad'akin kawu nuhu ta kwana danko ta shaida ma umman mu idan dare yayi baida yarda zaiyi ya kewa ya, tom shine fa tàce cikin y'am biyu surink'a zuwa suna taya sa barci, tom aranar suka ki zuwa, suka kama kuka shine fa ita Aisha taje, can d'in dan tayasa barci, da
sauran hidimar dare .




gabanin asuba wuta ta kama sosai a sashen umman mu, duk wani abunda ke ciki bai fita ba, sosai sarki ya soma mamaki danko shid'in yasan da wata a'kasa tom dan hakam sai yahana mu fita daga sashen sa yace mu zauna anam har ya kamo bakin zaren.




daga karshe ma, sai ca yayi mutafi gidan goggo maryo kafin yasa ayi masa bincike, Aiko sosai ya gano dasa hannu matan sa da wasu daga cikin barorin sa, shine fa kaf d'insu ya salla masu kafin ya maido umman mu suci gaba da zama.



, suko sauran jama ar gidan sarauta a tunanin su duk mun k'one har fa ca suke ko ya barsu ai basu da asara tunda sun halaka mar mata da Y'ay'a.


, tom sai dài fa tun a sannan ba,a sake sanin inda kawu nuhu da Aisha suke ba neman duniyar nan anyi masu amman an rasa su, munyi kuka sosai na rashin su mun hak'ura, suko sauran matan sarki sai ca suke ai ko yabar su basu da asara danko sun raba sa sa matar sa da yaran sa bai kula su ba saida ya gyara sashen umman mu sanan muka koma muka ci gaba da rayuwar mu, suko tuk wanda keda sa hannu , aciki wannan lamarin antura sa gidan kaso matan sa ko yabar su da halinsu.




tom shine fa niko tun awaccen ranar da aka rasa Aisha da kawu nuhu nake ta bakin ciki danko na k'walla fa raina ga yàr uwata sosai nake sonta shine fa naci burin sai na samo ta, duk wani binciken da yadace ayi anyi amman ba,a sa meta ba, dan hakam duk muka hak'ura, wataran wani malami yazo garinmu bakar fata ne d'an 9j ya sauka agidan mu bacin nazo fada gaida abbana saiko ya ganni anam ne yake cewa Abba na Aiko a kano yaga wani makaho da Yar jagoran sa, muna kama sosai da ita, nan fa aka had'o sa da dogarai suka zo har kano dan neman su, Aisha Amman ba agane suba, naci kuka har na gode Allah danko na k'walla fa wa raina yàr uwata.






tom shine fa sa,Adda naje makka dan sanar wa ubangiji na buk'atar dake raina Allah yahada ni da mahaifin ku ban 'kisa ba danko Ina ta burin ko ta wannan hanyar ce zan hadu da yàr uwata, tom har Allah yasa akayi auren har nasamu karuwa da yayan ku da Kai Mahmud har kawo kan, batula mai sunan ummata ban ci karo da Aisha ba.




Akullum Ina ta adduar Allah yasa nagan ta da raina itam hakam tom aranar da na fara ganin hafsat tabbas yanayinta d'aya da sister na Aisha Kai harda maganar su da tafiyar su, sai dai fuskar ce ba, iri d'aya ba, tum ganin farko da na yiwa hafsat na ji fad'uwar gaba danko lallai raina ya motsa da ganin hafsat.




tom shine fa nake jin tsantsar k'au narta araina, sai ga shi ajiya da kanta take fad'a man tarihim ta, abunda yasani kuka jin rasuwar kanwata Aisha shine nake wa bak'in ciki.




ta k'arasa maganar tana sharar hawaye kafin tàce tabbas nayi bak'in ciki da rashin Aisha amman kuma na gode Allah da yasanya naga yarta da idona.




Wani kalan kuka naji yazo man danko tun, sa,adda fulani ta soma labarta musu labarin ta na shigo cikin d'akin itama gimbiya safiyya tana gefe danko ganin na shigo itama sai ta biyo bayana.



duk abunda take fad'a a kunnen mu yake, sosai na k'am'kame fulani Ina faman kuka.



shiko prince ido ya kafeni dasu sosai sai faman cinzon gefen le'bensa ya ke, duk d'akin shiru makayi kafin, sarkin dogarai ya nemi iznin ga.sarki danko yayi baki, tambayar su waye yayi,


Sarkin dogarai yace mar, malamin da ya d'aura auren ka da hafsat ne yazo tare da wani dattijo, gane sirikin sane watom mahaifin hafsat da kansa ya fita yayi masa, iso har masaukin baki kafin ya gabatar da su ga fulani sosai suka gaisa da fulani sanan ta umarce prince Mahmud da yazo dani.



muna zaune jugum jugum nida batula da yarima faruk, saiga shi ya k'araso d'akin, da bango ya jingina kafin ya kafe ni da ido cikin muryar mai tafe da tsantsar taushi sanya wa rai nutsuwa, yace man hafsi na!! da ido nabisa cikin langa'be Kai nace na,am cikin k'asa da ido yace man taso mutafi ummata na Kiran ki,



cikin sanyina mai tafe da tsantsar yanga na taso gaf dashi na k'ara so, sosai ya k'am'kame ni kafin yarad'a man "congrats a cikin kunnuwa na Kai na langa'be gamida cewa "dami fa' dad'an murmushi ya ce man mutafi kiga.



sosai yariko man hannu tafe muke cikin salon burgewa da Sha,war kallo a falon da ake sauke baki muka k'araso muna tafe Yana rad'a man dadad'an kalamai niko sai shagwa'ba nake zuba mar, da sallama muka k'araso,,

gaban fulani na zauna idona fes akan Abba na da sauri nad'an ja baya kafin na dafe kir ji na nace abba na!! cikin tsantsar tausayi yace man hafsi!!!



shiru mukayi kafin Abba yace "tom masha Allah hafsat kiyi hak'uri dan Allah ki yafe man,



a matsayi na na mahaifi agere ki na kasa sauke hak'k'in da Allah ya d'ora man akan ki, dan Allah ki yafe man, kuka na sanya na farin cikin ganin ga ummata fulani ga kuma Abba na sosai nake murna. a gefe kuma ga za'bin Allah da yayi man na samun miji tamkar, prince Mahmud, cikin sauke ajiyar zuciya nace abba na ban ta'ba rike ka da wani kalan nufi araina ba, face na alkhairi, addua fa kayi man kace naje,, na tafee,, insha Allah zan tadda alkhairi,, tom Abba kalla kaga kalan alkhairin da Allah ya datar dani ga ummata fulani wacce take k'auna Yar uwa ce agare ni, sanan ga ido na k'urawa prince Mahmud shiko sai ya kanne man idon sa d'aya, kunya ce tasa na d'ukar da kaina.



danko naka sa k'arasa fad'in abunda ke raina, sosai Abba na yasan ya man Albarka.


sosai suke k'ara zancen ummata shida fulani watom Abba na, anan ne take tambayar sa kawu nuhu, cike da mamaki, Abba na ya ke tambayar ta daman bashine mahaifin Aisha?



Sosai ta labarta masa yarda zumunci su yake , kafin daga bisani ya shaida mata rasuwar sa, watom kawu nuhu.





fulani tayi bak'in ciki sosai ta kuma sahida masa duk ranar da za,a je itofiya zata shaida mar dan yaje yaga dangin Y'arsa kuma yayi na,am da hakam, sannan kuma ya shaida mata zai turo matan sa da yaran sa dan suzo suga masaukin hafsat.


kamar kar abba na ya tafi hakam naji bacin yasanya man Albarka sosai kuma ya nuna farin cikin sa da kasan cewar, d'an uwansa da kansa ya d'aura man aure sanan yayi man nasiha akan narike mijina danko shid'in za'bin Allah ne akaina sanan kuma ya Sanya wa yara na, albarka sosai yayi farin ciki da ganin yaran.





bacin iyayen nawa sun, nayi keawar mahaifi na,sosai.



fulani da kanta ta d'auko mai gyara ta gyara ni ciki da waje sosai danko saida nima naji ajiki na acan sashen sarki Mahmud aka ware man phart dina, wanda ke hade dana sarki Mahmud harma da na gimbiya safiyya.




sosai aka gyara man phart dina da kayan ado kala kala kalar na isassasun yaran sarauta d'in nan.


sa,adda na shiga phart d'in sai da na zufda hawaye dan murna.


sosai nake kuka danko ba abunda zance da fulani sai godiya, danko d'akin yarana ma ba, abinda babu, aciki gadon su daban na iya daban sanan ga kuma kayan more rayuwa ta ko wanne fanni, sosai fa nima na faso, sarki Mahmud da kansa yayi odar kayan d'akin na a dubai, wannan kenan.




zaune nake cikin d'akina nida batula misalin 9:pm danko yanzun mun zamo tamkar aminan juna komai namu atare muke duk da cewa itad'in ta girme man sosai amman shakuwar mu ta fice na abota ta kai matayin na jini irin na kusa d'in nan sosai,.




waya tace wacce prince ya bud'e man sabuwa fil ta d'au Kira ar k'ur ani alamar ana kira na.

d'aga wa nayi gamida kara wa a kunne na, zazza Kan muryar prince Mahmud na tsinkayo cikin kunnuwa na yana ce dani "kina Ina yanzun?

cikin kasa lalliyar, murya ta wacce jin tasa muryar yanzun tasau kar man da kasala, nace ina nan a phart dina, iska ya huro man kafin yace man kizo phart dina ina son ganin ki ,tom nace tashe batare da nasan phart d'in sa ba, danko awaccen ranar da na Kona sa da ruwan zafi a sashen safiyya ne.




cikin d'an kunya nace da batula please sister inason zanje gurin prince sai sai fa ban san hanyar zuwa gurin Saba,. Yar dariya tayi kafin tàce tom ai shi sai yazo da kansa ya d'auki matarsa,,


cikin muryar tsokana tace kagan sa kamar salihi, Ashe ja,irine wai har agaban filani, yake nuna maki soyayya baya ko jin kunya, sai fa angansa ya Kama kame kame.




"Laa keko kice kina Nan kina sanya wa mutane ido, aiko kibari ya rik'o ki kyayi mar bayani.


dariya tad'an yi kafin tàci gaba da fad'in, "keko sai wani sunne Kai kike sai kace bake ce nagani kina juya mar jikiba shiko sai wani luu yake Yana kara kafeki da ido.

"oh ni hafsat nace gamida fad'in kanki akeji bara kiga na isa gun mijina kar yagaji da jira.




Iyee masu mijin ta fad'a tana dariya na k'asa fita Ina fad'in ya son ranki kema kamar gone ne a gidan yarima anwar kuma dake da sarutar katsina d'akin kara.





zaune na tadda shi ad'akin sa sanye da tree quarter da t sheet sosai naga yayi man kyau, cikin takona mai tafe da sanyi na na k'ara sa agaban sa.

idon fes akaina, cikin k'asa da murya yace man ina yara na? "suna can gurin iya na bashi amsa, "mai isa baki zo dasu ba?, yace dani ido nad'an bisa dasu kafin nace acan fa suke kwana.


, janyo ni yayi sosai ya rad'a man kinsan fa yau anan zaki kwana, ido na waro kafin nace saboda m?, cikin kunnuwa na naji ya ce "saboda, aikin lada ko ba kyason lada? Kafad'a ta na mak'e sanan nace nifa kunyar iya nakeji, kawai sai da safe ta ganni naje bawa yara nono, haba prince abinda kunya.



ok tom bara nabiki can sashen naki kinga ni baruwa na, kinsan ko da safen dai zata ganni kuma tasan abinda kenan dai Kinga kunyar baki tsere Mata ba, kaina yarik'o muna fuskan tar, juna kafin yace yaushe ne zan raba ki da wannan kunyar? Shiru nayi masa, ok yace kafin yace sai Kinga kalan girma na, zaki daina jin kunya ta
bara nazo.


ido na rufe sosai danko na fahimci inda ya dosa,

shigar sa toilet keda wuya sai ga gby safiyya bako sallama ta fad'o d'akin, turus tayi danko bata zaci ganina anan ba.


, ido ta kafa man cikin takaici tace man "wannan anyi yàr bariki , shifa da kansa ya fad'a man baya son ki,, baya k'aunar ki, amman duk kinbi kin nace mar, harfa ce man yayi daga tayi so d'aya, kika mik'a kai, tom daman an saba bin maza, wama ya sani ko asiri kika mar danko nidai ban ga abunda zaija sa akan ki ba, taku tayo har gaba na, kafin tàce k'arya kike yar maba raciya, prince Mahmud nawa ne ni d'aya tal akayiwa shi kuma insha Allah sai na fidda ki gidan sa yaran kuma in rik'e su dan ko can daman nawa ne, kika yi mar shigar sauri kan su, tom kisa ido kiyi kallo da kafarki Zaki bar gidan.

, bora kawai ana kora tana k'ara lakewa, shid'in ma yanzun hakam yace, man zargin ki yake danko tun aranar da ya kusan ceki bai sameki abudurwa ba sanan kuma....keee wata irin tsawa ne yadaka mata kafin ya k'araso gaba na, yana tun Kara ta Ina ja da baya har sai da na jingina da bango kaina ke ta girgiza mar danko nama rasa bakin magana sosai nake ta sauke ajiyar zuciya danko har cikin raina nake jin zafin maganar da safiyya ta fad'a man, ganin ina kokarin zille mar yasa ya manne ni da bangon hannun sa yasa yazaga yo kuguna kafin ya had'e bakin mu guri d'aya, sosai yake sakar man zazzafan kiss, sai faman sauke ajiyar zuciya muke atare nida shi, kafin ya d'auke ni cak sai da yakai gaf da shiga dakin sa sanan ya juyo ya kalleta ta kafe guri d'aya sai faman kuka take tama rasa bakin magana danko aganin ta tozarci Mahmud yake son yayi mata a gaban kishiya, sosai ya kalleta kafin yace dani kike zancen sanan ya maido da ganin sa gurina nayi lamo ajikin sa, danko alokacin yariga da ya tono lagona, bazan iya guje.mar ba, cikin murya mai tafe da amo yace hafsat ki saki ranki ked'in ba matar cinne bace, danko kinsan matar cinne bata daraja.



Da ganan ya turo k'yauren adai dai nan itako zuciyar ta ciyo ta tasoma bugun ganbun sai ca take ni kake yiwa gori har kake ceman matar cinne? daga hakam bansake sanin komai ba, sai sautin sambatun prince da yacika man kunne sai caa yake please hafsi na kibar ni kar ki zautani da ni,imar ki nid'in naki ne ke d'ayan ki duk wace mace tana can bayan ki azuciya ta sosai yake zuba man samba tu kafin can cikin dare sosai ya samu gamsuwa. k'am'kame ni yayi yashiga sanya man Albarka danko nima nasan nayi kewar mijina.




asubar fari anam muka riski gimbiya safiyya abakin k'ofa hakam na nuna mana anam ta kwana.........✍️


💦 HUJJATA 💦


By

HAUWA MUSA RIJAU 💫


(Team Fasihai 5)


DASHEN ALLAH writer's Association (D.A.W.A)


Allahumma salli ala Muhammadun wa ala ahli wasallim 💓




Page:40--41







Kallo d'aya nayi mata nasan a some take, ra'ba ta nayi zan wuce naji saukar tattausan hannun sa aka fad'a ta, cikin muryar mai tafe da tsantsar k'auna yace man,




"da sauran lokaci fa, my star, juyo dani yayi ina fus kan tar sa, kafin yace "ki zo muyi wanka, ya fad'i hakam yana mai kafe ni da idon sa, cikin kunnuwa na ya rad'a man "Kinga nima sai na d'an k'ara, danko ban 'koshi da ke ba.


idona na runtse danko ina jin kunyar wad'an nan zancen nasa suna yiman nauyi a kunnena, cikin tsantsar jin kunyar sa na juyo,


kallon sa nayi kafin nace yaran nake tuna wa danko sai nake ga kamar zasu bu'kaci abincin su,


shifa bai ma lura da safiyya a gurin ba, sai alokacin ya hango ta can yashe, Kai ya girgiza kafin "yace ubangiji ya yaye maki wannan damuwar,


niko tsaki naja araina nake ayyana tabbas daga yau na daina shakkar ta danko idan har nace zan dinga shakkar ta to lallai ko zansha wahala,



ido na na mayar kansa wanda shiko ya sunkuya adai dai wuyar ta yana shafa ganin hankalin sa ya sauka akan ta niko sai, nayi yun k'urin barin falon,






hannu na yariko sosai gamida fad'in bana son musu, tilas na hak'ura na koma can a kusa da shi,



ganin lokacin Yana tafiya itako bata da nufin motsi kawai sai dauka ta yayi cak sai ad'akin nasa


sosai ya nuna man wata kalar soyayya mai wuyar fad'i danko nid'in nasan mijina gwarzon maza ne.



bacin mun gabatar da sallah sosai muka koma barci.


sai after 7:am muka farka, a shagwa'be nabisa da kallo, kafin nace

Please Login or Register in order to submit comment