Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baba yabini da shi cike da tausayawa sanan yace eh nine mahaifin ta, baba dattijo ya kafe abbana da ido sanan yace yanzun kana ga ka saike wa yarka hak'k'in haihiwa kenan? kafa tuna su Y'ay'a amana ne Allah ya dam'ko mana ahannun mu sanan kuma bai bamu suba sai da ya tabbatar basu fi k'arfin rik'o agare muba, tom mai zaisa ka wofintar da y'arka akan wani dalili marar tushe wai shi kanbun baka, wanda hakam wata kalar baiwa ce wacce Allah ya bata kuruciya ce ta hana ta fa himta, nina tabbatar maka inda uwarta nanan raye kuma har ta fahimci halin da yarta take ciki Ina tabbatar maka da yanzun yarka ta shigo cikin tarihim Y'ay'an da za,ayi fahari dasu, amam kai uba ka koreta dan kai Alissa finka tazamo maka annoba, kaico da wannan tunanin.....iya abu ne tace cikin tsawa nikam banga amfanin aihuwar hafsi aduniyar nan ba sanan insha Allah.....wuf anty ma,u ta rufewa iya abu baki kafin tàce ke Inna dan Allah kibari kiga Koda auren mutum d'aya ne acikin yayan ki, kinsan inhar kika furta mata ba dai-dai ba bazata barki ba sai ta rama kuma kinsan itadin fad'i da cikawa ne yanzun kiyi duba ga mudi daga fad'ar Allah yabi mata hak'k'in ta akan 'kazafin da suka mata kinaga ko kofarsa bai koma ba, katanga ta rufto masa sai ko gawar sa aka ciro can k'asa har kansa saida ya ta'be tom kema kifada itama tafad'a maki. cikin sanyin jiki iya abu tace, "a a nima fa daman nifina bazan zauna da itaba, sai dài ko nabar gidan., cikin sheshshekar kuka nace dan girman Allah baba dattijo ka tafi da ni can ko aikatau ne kasamo man sai na rika cin abinci anan. ido baba dattijo yabina da Shi jin abbana baice komai ba, sai yamik'e gamida fad'in daman yaro ne yaje ya kirani dan inkai wannan yarinyar ga fad'ar sarki dan adau mataki kanta, shine fa waziri ya umar ceni da na je na sulhun ta ku dan sarki yaje tafiya tare da amarya sa, tom yanzun Ina fatan ka huce zaka rika y'arka. cikin sanyin murya abbana yace nifa daman banyi fushi da y'ata ba kawai bak'in hali irin nata shi ne tsana, kayi hak'uri shine furcin baba dattijo sanan ya mik'e gamida fad'in ana jira na fada bara naje, Aiko ganin ya barni anam saiga iya abu d'auke da k'aton bakkon ta sanan kuma can saiga umman hamza itama dauke da k'aton bakkon ta kowa niki niki yake Jan sa sanan suka yi masa 'kerere aka sai cewa suke bamu ta karadar mu kaga ita sai tarike yaran naka, aiko yaran kananun da manya duk sai suka taso kowa sai fad'in yake mama sai dai na biki, ganin dik gidan ya rud'e aiko ba shiri abbana yamik'e gamida fad'in dattijo muje suka k'arasa can waje sun Kai minti biyar sanan abba ya shigo cikin gidan kafin Abba ya bani umarnin tashi naje na had'o dukkanin ka yana dake gidan su ummi inzo mutafi da baba dattijo, tom nace cikin sanyin jiki nace ohni hafsa yau kuma ina k'addara za ta kaini? cike da sanyin na wand ya zamo man halitta naje gidan na d'auko dukkanin kayana harda jaka ta ta islamiyya, na shiga har ciki na d'auka har k'asa na roki mama akan taban hoton ummi amma ta hanani sai ceman tayi inhar da gaske nake sonta mai isa nayi mata mugun furuci kicin kuka nace niban yiwa ummi mugun furuci ba dan Allah shine shaida na, amman tunda har tàce hakam nabarta da Allah acikin gaugawa.......dawani mugun hanzari mama ta rufe man baki sanan tace yo kisan bata ishe ki ba kenan? so kike sai kin Kare mana gidan sai hankalin ki ya kwanta, cikin sanyin jiki nace tom ni wlh karya take man hannu na mama ta damko tayi waje dani sanan tace umma ta gaida ashsha jeki kallo nabita sa shi sanan na nufi gurin baba dattijo cike da tausaya wa yace man mutafi y'ata Allah yazamo gatanki, ameen na furta, sosai mukayi tafiya kafin musamu adai dai ta gidansa nacan doruwar y'am kifi,







Tun bayan da k'addara ta had'ani zama da baba dattijo sai na samu shima d'in baida matsala hakam matarsa sai dài fa d'ansa babba shine keda matsalar danko mugun barawao ne na kin k'ari sanan iyayen sa na masiafar son sa sam basu son ganin bacin rai nasa, tun farkon shigata gidan akullum sai ya rarumo kayan wani wataran akamasa wataran yatsira amman ba ruwansa da shiga hurumin kowa tom ana hakam ranar da na cika sati biyu agidan da misalin karfe goman safe sai ga shi ya dawo gidan ba kowa agidan saini d'aya umman sa ta shiga makwaf ta abban sa ko yatafi aiki fadar sarki, Yana shigowa saice man yayi ke zonan kallo nabisa da shi dan ban tsammaci jin hakam daga bakinsa ba tunda tun shigowa ta gidan wani zancen baitaba shiga a tsakanin mu ba, dan ko na gaida sa baya amsa wa, badake nakeba kin wani tsure ni da ido kamar wata mayya, ciki sauri na k'arasa gaban sa d'an waige2 yafara kafin ya nuna man taga yace man da hanzari ki k'arasa Kai balle tagar can zakiga wata k'atuwar jaka ki miko man da sauri dan Allah, jikina ya soma rawa dan tunawa da maganar baba dattijo da yace ma matar sa asanda ya shigo da jakar, ki adana man wannan dan ajiyar mai girma ce aciki idan wannan ta 'bace zan iya rasa raina ko na dau wama agidan yari, da rawar jiki naga matar sa ta amsa ta Kai can d'akin ta adana, sanan ta sa katon kwad'o har guda uku ta datse d'akin da shi sanan ta ceman kar na kuskura na shaida wa marwan watom da dansu, tom ni yanzun mamakina waye ya shaida masa, jada baya na somayi Ina fad'ar dan Allah Yaya kaman rai bansa ba, please yaya wani wawan mari yakai man saida na kifa akan dutse da ke gabana, da sauri na tashi da nufin in tsere kamar yasan nufina yasha gaba na da k'arfi gamida ja man gashin kaina wanda saida hakam yasa na fita hayyacin na wucin gadi kafin yace zan iya kisa fa akanki maza jeki ki d'auko man tun kan iya ta k'araso tsananin azabar tasa nayi saurin k'arasa wa bakin tagar da sauri na afka ma tagar na balle ta sanan nasamu na shiga Aiko tana can na hango ta ajiye k'uryar d'akin da burcewa nayi kafin nasamu nutsuwar dauko ta, ga mama ki na Ina jefo kafata da nufin indiro sai ganin nayi iya matar baba dattijo da baba dattijo sunyi cirko cirko suna kallon mai shirin fitowa daga d'akin.





cikin rud'ewa da tsantsar jin kunya na fito rik'e da jakar kudin a hannun na, cike da mamaki suke kallo na Ina waige2 dan inga ta inda zai bullo watom shid'in wanda yasani dauko su saijin k'arar tsaya war mashin d'insa mukaji alamar yanzun ya dawo gidan kallon kallo muka hau yi dasu na marasa mai zance, da sanyin jiki baba dattijo ya k'araso gaba na yasa hannun sa ya kar'bi jakar hannu na sanan yace y'ata Ina nema maki Shirin Allah amam gaskiya lamarin ki yaban tsoro tilas zanbarki ki tafi inda kika fito, cikin rawar jiki da rawar murya nasoma kuka Ina cewa wlh ban ta'ba sata ba baba ka kalli fuskata itace shaida ta na marin da Yaya marwan ya watsa man dan in d'auko masa kudin amman nace aa shinefa har ya maren. cikin karaji ya fisgoni ya shiga jifga ta ko ta Ina han cina jini la'b'bana duk suka zubar da jini nan take ka mannina ya sauya sai jifga na yake son ransa amman baba dattijo bai hana sa ba, itama karan kanta uwar sa bata hana sa ba ganin da gaske zai man I'llallah na yun kura dan na kwaci kaina Amman Ina, saiko ya fare ni na kifa kaina da k'asa nan take ko kaina ya gauri katon iccen dake tsakar gidan Aiko da mugun hanzari na furta idan har, banida hakki akanka sai Allah yabiman bashina cikin wani kalar rad'ad'i na azaba na fad'i kasa a some, wani irin tsananin azabar sanyine yara tsani shine dalilin farko wana, taron da na hango ne makil da tsananin azabar sanyin sune suka sa na zabura da nufin, in mik'e tsaye juwa ta kwashe ni, saiko baba dattijo na hango ya ratso taron jama,a da kansa yazo ya mikar dani tsaye tsaye sanan ya shigar dani d'akin da ya zauna makwafin nawa sanan ya kawo man gurasa na kallesa kafin na girgiza kaina ganin ban ciba ya mik'e ya d'auko man fura mai sanyi na sha sanan yafito inaji yana ta faman magana Amman Ina banji yayar ta taaya ba, sai faman k'ara hayaniya ake saican a tsinkayo muryar matasan suna fad'in tilas fa abamu ita musa mata fetur mu konata dan bazamu bar annoba agari ana kalloba, cikin muryar ban tausayi yace dasu yanzun Kuna kallo zan tafi da ita gidan sarki dan ayanke mata hukunci, kacar yasamu suka amaince da cewa akaini gidan sarki dan ganin kalar hukuncin da za,a yanke man, ba bata lokaci baba dattijo ya taso ni gaba muka shiga motar makwaf cin baba dattijo sai gidan sarki, muna zuwa, muka tarar sarkin ma yaje tafiya, dan hakam waziri da kansa yace akaini gidan kaso har sai sarki ya dawo sanan a san abinyi, baba dattijo da kansa ya kaini har gidan yari ya Kira shugaban ma,aikatan gidan watom Abdul nan fa naji yana fad'in wai nama d'ansa mugun furuci, ya fad'i da mashin d'insa yana can ko ga nuwa baiyi dan nan take kafar sa ta cire fuskar sa ta canja yanzun hakam bai san inda yake ba, watom marwan kenan nan, naji baba dattijo da kansa yana fadar kuyi hattara da ita wannan d'in da kuke gani annoba ce, tom tunda aka kawo ni gidan da nufin sai sarki yada wo za,a san abinyi akaina. daga wannan tafiyar ne sarki bai dawoba sakamakon had'arin jirgi da sukayi sai mutuwar sarki mukaji, yau shekaru uku, kenan da zuwa na gidan kuma tun shigowa ta wannan gidan ban tarar da komai ba face jarabawa, wani kuka ne yazo man sakamakon tuna wa da irin wahalar danaci afarkon shigo wata gidan yarin.......✍️


💦 HUJJATA 💦













BY


HAUWA MUSA RIJAU







CHAPTER 15--16







Tun sa Adda nashigo gidan nan ba, abunda na tarar sai bakar azabar tsiya, da kunnuwa na naji Abdul shuga ban ma aikatan nagidan nan Yana ba binta shugaba umarnin akan karta saurara mun ta dokeni iya son ranta, nid'in annoba ce da sauri binta shugaba tace kaiko ayi d'an mutum kuma ace yazamo annoba? wannan wace irin yarinya ce,ita ? cikin tsawa yace horon ta na baki kuma duk Wanda ya hana ki kice masa itad'in annoba ce, (kinji dalilin da yasa suke Kira man annoba ba tare da sun san koni waye ba) tun a waccen ranar binta shugaba ta bani bakar wahala ta hanyar azabtar dani nice d'ebo ruwa acan gwanar masha ya, nice wankin kayan binta harma da wasun su masu son zuciya sanan nice shara na gidan nan, ki duba dik fad'i da girman wannan gidan wlh iya nasha share sa tas har idan bai sharuba ace sai na sake wani sanan duk na d'an kuskure naci duka agun binta ga kuma nuhu mugu da ke firgi tar dani da bulalar sa.

, kwana na uku da isowa Wannan gidan duk nabi na lalace na koma kamar baniba sanan ga bakar yunwa duk Wannan Yana cikin horon binta shugaba, Abdul da kansa yace asani adaki na daban dan ba mai irin halina duk gidan, tom shine fa naka sance d'akina daban da na Yan,uwa na Kai sati da kawo wa Ina can Ina fama da bakar wahalar da nasaba sai ganin nayi anzo Kira na da nifin anka wo man ziyara bacin naje na tarar da baba dattijo ne da kansa yazo ganina, shima yara zana da ganina sosai amman sai ya dake jaka ta mai d'auke da k'ur ani na itace yakawo man sanan yayi man nasiha kafin ya tafi, cikin sanyin jiki da rashi kuzari nima na bar gurin bacin na kammala dukkanin ayyu kana sai na shiga daki da nufin in gabatar da sallah acan ne nabude kur,anin da nufin inyi karatu saiko naga farar ta karda ta fad'o da hanzari na bud'e ta bacin na adana k'ur ani, cike da d'oki na bud'e ganin rubutun ummi ne sai ko nayi saurin karan tawa da rawar jiki danni ma ban san da wannan d'in ba, ga abinda tace ( aslm my bestie na nasan koda wannan letter zata riskeki tuni na dad'e da shiga cikin k'abari na amman dan Allah kiyi wasu Al farma guda uku na farko inason dan Allah karkiyi man kuka, sanan inason dan Allah duk wanda ya biki da mugun nufi kekam kibi shi da furucin alkhairi sai kiga mutane da dama sun karu ba furucin ki kuma agurin Allah Zaki Sami lada, sanan inaso ki zamo JARUMA kuma jajir tatta wacce zata zamo mai shanye damu warta dik rintse ki kasance mai tsaya wa tsayin daka gurin ganin kin gina wa kanki rayuwa mai kyau agaba duk da nasan da akwai kura agaban ki, sanan kuma kisani kasha cikina...bazan kaiba bare na baki wani labari sai dài nabar su da Allah watom jummai da iya Abu dan sune silar mutuwa ta guba....gubaaaa nabarki lafiya Allah ya....ha....d"a...fuskar............ )daga nan rubutun ya tsaya wani kuka ne na fashe da shi sosai naci na koshi ba mai rarrashina anan ne nagane lallaine da jummai da iya Abu suka kawa ummi guba a abinci taci, Ina tsaka da kuka a waccen ranar saiga binta shugaba har cikin d'akin tashigo tayi man dukan tsiya wai na dad'e ban fito, nayi aiki ba, wata zuciyar ta Umar ceni da in aikata mata mugun furuci amman tunawa da maganar ummi sai nayi hak'uri. tun a can nayiwa kaina alk'awarin zan ta furta alkhairi ga jama,a ko zan samu lada kamar yarda ummi ta buk'ata, sanan tun acan nayiwa kaina alk'awarin zan rinka sjanye da muwa ta har, I'llallah masha Allah, Wannan kenan.





bacin gama karan ta letter ummi da kwana biyu saiga wani bawan Allah an shigo dashi agidan kaso yana ta kuka sosai yana fad'in wlh shi bai yiwa kowa sata ba shima ganin yayi kawai mutum ya damka masa jaka kafin duk ya ankara mutumin ya bace wa ganin sa kuma Yana shirin karawa gaba sai ganin yayi an cafke sa. amman Ina ba wanda ya kula da ma abunda yake fad'a, har yagaji ya daina fadar komai can guraren yamma nazo tafiya kusa da shi na raba zan wuce sai wata zuciyar ta ce man mai zai hana in taimaka masa ta hanyar kyakkyawan furuci da kwarin gwiuwa na k'arasa tagaban sa cike da tsoron kar wani ya ganni nadan rage tsaho sanan nace masa kabar kuka d'an uwa insha Allah ba zaka kwana gidan nan ba da yardar Allah yau d'innan za,a fidda ka katafi ga iyalan ka, da sauri na bargun muryar sa na tsinkayo Yana cewa Allah ya amshi bakin ki yar nan, amen na furta. sai da safe nake jin binta shugaba tana bawa ta bawa labarin cewa ai harfa dare ya soma sai ga masu kudin da wancan mutum yayi wa sata sun zo sun tabbatar da cewa bashi bane wancan an kamasa da kansa yake shaida masu yarda abun ya faru, nan take aka fidda sa tare da kud'ad'e masu dama da nufin ban hak'uri ta bawa tace atom shikam gaba ta kaisa ai. nan take naji wani farin ciki ya rufe ni arai na nace ashe ma furucin alkhairi dad'i ne da shi, tunda ga waccen ranar sai nayi wa kaina alk'awarin zan zamo mai furta alkhairi Koda ancutar dani, sanan na yiwa kaina alk'awarin zan zamo mai juriya akan kowacce k'addara da Allah ya nufe ni da shiga cikin ta, tom sai kuma gashi adaren jiya Allah ya nufe ni da shiga cikin wata k'addarar.

WANNAN itace HAFSAt

shiru nayi dan na samu kaina da Jin kunyar fad'a wa iya adaren jiya an d'aura man aure da wanda ban ma san saba. cikin kamalar ta na tsinkayo muryar iya tana fad'in a jiya waye ya shigo a d'akin nan? sai da na zabura a sakamakon jin tam bayar bazata da naji iya tayi man ad'an diriri ce, na sunkuyar da kaina k'asa sanan nace nima bansan saba, shiru ta d'an yi kafin tace kina da wauta da saurin yarda yanzun y'ata da ga ganin mutum baki san saba baki san shid'in waye ba kawai har kin bashi kanki wata irin kunya ce ta rufeni har sai da na boye fuska ta a cikin cinyoyina, kafin na tsinkayo muryar iya tana fadar y'ata inason kibani hankalin ki ki saurare ni da kyau cikin natsuwa na d'ago dara daran idanuna na sauke su akan iya, itama d'in ni take kallo, cikin sakin fuska tace man y'ata ki fa himcine nid'in bawai Ina zargin ki bane da wata manufa , aa a labarin ki da kika bani ked'in kamila ce dunta har babar ummi ta shaida maki illar wani yarik'e wa mace hannu matuk'ar shid'in ba d'an uwanta tabane tom, mai zai sa ki amince wa wani har ya kai ga sanin ki y'a mace? cikin tsantsar jin kunya iya nasoke kaina ban sake cewa komai ba, itama iyar aranta tasan cewa wanda idon ta ya gane mata tabbas shid'in ba mazina ci bane, amman tom abunda take son sani mai yakawo sa d'akin Wannan yarinyar har kuma wani abun ya shiga tsakanin su, ganin yarinyar ta soke kai alamar jin kunya sai ranta ke bata kodai shid'in ya garga d'eta akan kar ta fad'a wa kowa. dan hakam sai ta bar zancen cike da rashiñ jin dad'i, ganin na yi shiru, sai iya tace tom bara na sanar dake wani abu gameda gidan sarauta dan yanzun can zamu fuskan ta kafin nayi maki bayani gameda kanbun baka.


A GIDAN SARAUTA.



Gidane mai cike da taron jama,a kama daga kuyangi bararori fadawa da sauran su, sarki ALIYU bin ABDUL JABBAR shine tsohon sarki Mai rasuwa.......✍️


💦HUJJATA 💦












BY
HAUWA MUSA RIJAU 💫





CHAPTER 17--18






Sarki ALiYu bin Abdul jabbar shine tsohon sarki mai rasuwa, shine babban d'a ga sarki Abdul jabbar wanda duka duka su hud'u ya haifa sarki ALiYu shine babba, sanan sarki Mahmud shine akan ka raga yanzun sai yarima faruk sanan autar sa gimbiya batula su wad'annan sune y'ay'an tsohon sarki wacan, bacin rasuwar sa aka nad'a sarki ALiYu wanda Allah baisa yata'ba haihuwa har ya koma ga Allah matar sa na farko fulani binkisu, sunyi zama na dogon zamani da ita kafin daga baya ya auri yar sarkin misra gimbiya safiyya wacce du du zaman su bai gaza watanni biyar ba Allah ya d'auki ransa, tom bacin rasuwar sarki ALiYu sai aka nad'a sarki Mahmud wanda alokacin baya ko nan Nigeria, Yana can Dubai acan yayi karatun sa kuma bacin ya kammala sai yayi zaman sa dan garin yayi masa dadi. rasuwar yayan sa ne yasa yazo da nufin gaisuwa sai kuma aka hanasa komawa da nufin ya gaji yayan sa, yaso zamewa sarautar amman Ina manyan sa suka nuna mai mahimmanci ta agaresa alokacin ason ransa a baiwa yarima faruk amman Ina manyan sa suka nuna mai shi yafi can can ta ganin baida mata ne yasa suka Yankee shawarar idan gimbiya safiyya ta cika idda sai a aura mar ita, har cikin ran fulani sa,ada bataso hakam ba, watom mahaifiyar su sarki Mahmud kenan,


dan tasan ko waye safiyya, itad'in ta kasance irin yaran nan ne masu son jiki da tsantsar kazanta sanan ga mugun son girma da raina nagaba da su kuma ga muguwar kissa itad'in bata ganin kowa da gashi komai tsufan ka sai ta zafga ma rashin mutunci ta k'ara gaba wannan ba damuwar ta bane duk da kasan cewar ita din balarabiya ce amman hakam bai sa take halayya na dattako da nuna itad'in jinin sarauta ce, dan ansan jinin sarauta da karamci amman bada safiyya ba dan ita bada muwar ta bane dan ta taka ka iya son ranta wannan shine isa fulani sa,ada bata so auren ba, amman ganin mafi yawan magaba tansa sunyi a manna da hakam sai tace Allah yasa hakam ne alkhairi sanan kuma tabawa d'an nata k'warim gwiwa akan hakam.



shima aban garen Mahmud bai so hakam ba dan shi ara, ayinsa yafison yar k'asar sa Nigeria mai cike da Al,adu irin na bahaushiya mai yanayi irin na hausa fulani Wannan shine ra, ayinsa tom amman ganin duk manyan sa sun yi amanna da hakam shima sai bai ja ba, ya hak'ura, kasan cewar shid'in mai yawan hak'uri ne baida d'agawa baruwan sa da tauye hak'k'in talaka sanan uwa uba baida yawan magana sai buhun k'asaita shid'in tsayayyen sarki ne adali ga jama,arsa duk wani wanda yake karkashin ikon sa Yana jin dad'in kasan ceawar hakam dan bai da cuta alamarin sa, Wannan shiyasa talaka wansa keson sa.



tun bayan da gimbiya safiyya ta kammala takaba saiko aka d'aura auren, su da sarki Mahmud, gimbiya safiyya ta yi farin ciki da murna hakam dan acewar ta daman shine kalan mijin da yadace ta samu amman tun farko bata samu ba sai a yanzun Allah yabata har tana cewa ita d'in mai sa,a ce, a wani sa,in har cewa take ba afarin ciki da mutuwa amman ita Kam tayi farin ciki da samun hammud ama tsayin miji.




shiko a fanni sa baiyi farin ciki da hakam ba dan can daman bata gaban sa bare yanzun da yagane halin ta, ko d'aya halayyar ta basu cikin tsarin sa,

amman dan ya kasan ce bai son rigima sai bai tanka taba, d'aya daga cikin halayyar ta da ya tsana shine sai ta turo masa kuyanga har cikin d'akin sa da nufin ta gyara mar, idan ya nuna rashin jin dad'in sa akam hakam saiko ta hau fushi itama, har ya kance mata anya ko kina kishin mijin ki, sai cewa take itad'in tasan ko waye mijin ta, har abadan tasan matan banza basa gaban sa, da wannan take rufe mar baki. hakam ma idan batayi ra,ayiba ko sunna zaiyi da ita sai ya biyata sanan zai kusance ta, shid'in ko ya kasance mai yawan buk'ata ne tom da wannan take karya masa lago, sanan abincin sa ko sai dài kuyangi su dafa mar yana da za'ba'b'bun kuyangi su biyu dake kula da lafiyar abincin sa sanan bacin sun kammala da akwai wanda ke kula da lafiyar abinci nasa kafin yaci, duk fa kuyangin dake gidan sarauta sun fahimci kalar hak'urin da sarki Mahmud keyi da gimbiya safiyya, da akwai watan acan zamanin da nake jakadiya agidan sarauta kin san jakadiya bata da shamki adakunan gidan sarauta tom wani uzurin ya taso gurin fulani watom mahaifiyar su, kenan tace man naje na isar mata da sa'kon tana son ganin sarki Mahmud shine fa dana k'arasa dakin sa baya can saiko naje can d'akin matarsa watom ita gimbiya safiyya kenan , Ina fad'a maki yar nan tun da na tunkaro nake jin maganar sarki Mahmud Yana ta yiwa gimbiya safiyya magiya akan ta yi hak'uri ta bashi hak'k'in sa, duk fa yarda yaso aranar saiko ta ki amin cewa. ba nayi masu la'be bane a a Ina jiran naji ya d'an natsa ne sai na nemi iso agurin sa, amman jin abun yaki karewa tilas na juya harfa cewa yayi yabata gida da ran tsartsaiyar motarsa amman matar nan saiko takafe akan sai dai in ya amince zai Kai ta America,

shiko inda abunda ya tsana tom zuwa America ne, dan acan ne yarima faruk yayi karatu kwata kwata tarbiyyar sa bata cikin tsarin islam saifa da fulani ta

Please Login or Register in order to submit comment