Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'aton gwangirin da ake diban ruwan da shi na nufi hanyar rafin da muke zuwa d'iban ruwa watom rafin kwanar Masha ya.



tafe nake zuciya ta fal 'kunci Ina tuna yau nema naji dad'in zaman wannan dunyar, acan wani sashe na zuciya ta Yana raya man cewa aiko adaren jiya kin yi farin ciki tunda har kinyi aikin lada, wani d'an murmushi nayi Wanda bazai wuce saman la'b'bana ba da hanzari kuma naji wata irin fad'uwar gaba tazo man hannu nasa nadafe kirji na gamida Kiran na shiga uku ni hafsa, cike da kalan damuwa a zuciya nake tambayar kaina tom waye mijina? oho wata zuciyar ta ban amsa, ban ankara ba sai ganina nayi gaf da nuhu mugu, da wani kalan hanzari na sake hanya dan nasan gamona da shi ba dad'i rike yake da zafgegiyar bulalar sa na shin imani ga dik Wanda yataka doka, cike da wata irin murya Mai Kama da tsawa yace, ke Ina Zaki kika nufato nan? nan take jiki na yasoma k'yarma cikin matsa nan cin tsoro nayi k'asa da idona dan bazan jure ganin wa dannan jaja yen idon sa ba. cike da muryar tsoro nace zanje rafin kwanar mashaya ne ind'ebo ruwa, cike da wata kalan dariyar mugun ta yace "shegiya binta bakida kyau bakida imani, nan take kuma ya tsa gaita sanan yabini da kallo kafin yace kece Mai laifi dan nasan dik masifar ta idan har baki tabota ba tom bazata zalunceki ba, maza bar nan muna fuka a sararriya, tom inban da asara kamar ke yarinya mai tsananin kyau da kuruciya ga kyan jiki sanan ace kin kre ryuwarki agidan yari a Kan kuma laifi mafi muni tir dake. ai inajin yace bar nan take da mugun hanzari na ruga da mugun gudu na bar gurin, adai-dai kwanar masha ya naci burki da wani kalan tsoro dan cin Karo da nayi da adodo Yana fitsari kuma ta gaban sa nake da mugun hanzari na kauda idona na juya da nufin na bar gurin da sauri ya shagaba na, gamida nuna man abarsa dake tsye kam, Yana wani mugun dariya gamida fad'in "yarinya aikin makaro dan ba a ganin wannan abar abanza tilas ne yau sai kin shata, da wani kalan hanzari na tofar da yawu Jin wannan furucin da yayi na ka zanta, kallo d'aya nayi mata ibisa kuskure Amman duk wani kalan tashin zuciya nakeji saboda abun ba kyan gani, gashi mugun kazamine bakin sa ma ba duk ya dafe da hayakin taba ga shi duk awani ya mushe da shi, yak'i kauda abarsa kuma yaki bani hanyar gashi lokaci naja ga binta shugaba Bata da tausayi bata da uzuri, cike da wani kalan tsoro nace "dan Allah kaban hanya na wuce, cike da rshin imani yabini da kallo sanan yace ke harni kike tofar wa yawu tabbas yau ko zakici ubanki.....kodai Kai kaci ubanka ba muryar nuhu mugu na tsinkayo ta baya na, da mugun hanzari adodo ya jada baya Yana neman hanyar tsira sai dài badama dan yasan duk inda ya nufa agidan yarin tabbas zaisa akawao marshi, cikin k'yarma da rawar murya adodo ke fad'in dan Allah kayi hak'uri oga nuhu bazan sake ba, cikin kaushin murya nuhu mugu yace "watom Kai ga dan iska kaga fara kyakkyawa shine harda wani fitar da a bunka kana nunawa wannan 'kank'anuwar yarinyar har kana fad'in zataci uban ta ko? Kai ga dan iska, kee yakirani da hanzari na dago kaina yace bar nan da hanzari na bar gurin cike da sauri na nufi rafin na debo ruwa na nufi hanyar da sata sada ni da gurin da binta shugaba take zaman jirana, tafe nake Ina sauri dan nasan sai naci azaba agurin binta shugaba, sauri nake sosai kowa na gidan Yana ta harakar gaban sa, audu mai shela na tsinkayo muryar sa Yana fad'in kowa na gidan nan mata da maza ana son ahad'u a babban ofishin dake gidan nan ayau za a zayi zabar kuyangi wadan da za akai gidan sarki dan hidimta wa iyalan sarki.


nan fa naga kowa ya shiga murnar wasu harda taka rawa suke dan farin ciki niko sai abun ma yabani mamaki dan wannan ba bakon Abu bane danko ba yau aka faraba, Amman ni wannan bada muwa na bane, wannan shelar da akai shine fa ya kwace ni a hannun binta dan ita din babban gurin ta takasance jakadiya agidan sarki, sosai nake hanzarin dan naci gaba da aikin da ke gaba na dan ko ba komai sonake nayi wankin kayana masu datti wata kyakkyawa dattijiya naci karo da ita tana yiman murmushi mai tsaya wa azuciya Kai na d'an sukuayar gamida gaida ta dan nagane ta itace shugaban masu dafa abinci nagidan yarin, cikin sanyin murya tace man, y'ata maza kiyi hanzari ki tafi ayi dake ko kin dace ashigar dake gidan sarki ga yarima faruk can da kansa yazo dan fidda zakka agidan yari ki tafi muna fatan ashiga dake. wani d'an murmushi nayi kafin nace "iya kin mance ne mance ne aini kalar nawa laifin har abadan ban cancanci a fidda ni anan gidan ba, kin San fa saboda girman laifina ko shari,a ba atsaya ga laifina ba Kai tsaye aka nufato dani gidan yari kuma Kinga barana bare watar da zan fita kawai nidai gani nan ban san matsaya ta ba, tom iya mai kalan wannan hukumcin har shine za a fitar ka kaisa gidan sarki da sunan kuyanga? murmushi tayi mai sauti sanan tace no yata nasan halinki gardama bana ki bane kawai kitafi, gwangirin na aje sanan na koma d'akina na dauko dan karamin hijab d'ina, da yasha takura saboda rashin guga Amman fes yake dan bani da kazanta tafe nake cike da fargaba nak'ara sa kusa da wata Yar dattijiya na tsaya, can gefe ta matsa gamida cewa kinga dan Allah canza guri kar ahan goki kusa dani azata ko irin laifin mu d'aya dake, ido nabita da shi sanan naja can gefe na tsaya, cike da bacin rai na abunda suke man dukkanin mufa masu laifine dan duk wanda kagani a gidan kaso kasan ba ra,ayi bane yakawo sa amman dan tsabar son Kai sai suta aibata laifina, hawaye ne nashare gamida dago manyan dara daran idanuna danufin in kalli can gefena karaf idona suka sark'e da na wani kyakkyawan mutum mai tsananin kyau da cikar Kamala sai faman murmushi yake, nazata ni yake kallo ashe dan dazon mutanen dake cike agurin su yake bi da murmushi idon sa masu tsananin haske yad'ago da nufin yabada umrni saiko karaf idonsa yakai akan hafsi wani kalan shokin ne yaji jikinsa ya.....✍️

💧 HUJJATA 💧






BY

HAUWA MUSA RIJAU




Page 5-6
Wani kalan shokin ne yaji jikinsa ya d'auka ya dimauta da ganin wannan kyakkyawan yarinyar tsaleli Yar budurwa kamar wannan ace tana rayuwa agidan yari aiko abunda mamaki, ganin hankulan jama,a na kansa, sai ya basar da tunanin sa akan hafsi cikin halin ko in kula cike da k'asaitar sa da nutsuwar sa yaci gaba da abunda ke gaban sa cike ta k'asaitar sa ya bi wani dogari dake kusa da shi da kallo kafin yace" wace shugaban wannan gidan? cikin yanayi na girmama wa binta shugaba tace gani ranka ya dad'e shiru yayi mata saida ya mula dan kansa sanan yace kizaga ki nutsu ki d'auki masu nutsuwa da hankali dan ban son kaza mai banson marasa k'ok'ari dan hakam sai akiyaye, koma wa yayi ya ki shingid'a cikin k'atuwar motar sa mai kyau da tsada, mamakine niko ya kamani ganin yayi halin ko inkula da jama,ar bacin shine fa da kansa ya taramu agurin.

da rawar murya binta shugaba ta soma fad'in angama ranka ya dad'e aiko yanzun zan nemo masu hankali nan fa ta soma rawar jiki, do gari d'an iliya yace "bi a sannu shugabar mata na gidan kaso y'alla'bai Yana buk'atar ana tsu abin ciko masu nutsuwa, "an gama sarkin dogarai cewar binta shugaba, sannu ahankali ta soma tsintar mutane har ta k'araso gurin da nake, kallon sama da kasa ta man kafin tàce yo ke waye zai Kai ki gidan sarauta, ki zamo masu annoba nima hakam ta shafeni azata, ko nice na kawo ki, hannu tasa ta hankad'ani kad'an yarage na fad'i da zafin nama na rik'e wacce ke gefe na, wani kalan tsaki tayi sanan ta k'arasa ga wacce ke gaba na. duk abun da ake idon yarima faruk na akan mu, cikin yanayi na basar wa yace da Abdul d'aya daga cikin ma,aika tan gidan kason "ita waccen me ta aikata hakam da har naga ana hantarar ta? ya fad'a Yana mai nuna hafsi da yatsar sa
cikin halin ko in kula yake zancen da hanzari Abdul ya kalloni sanan yace caf wannan ai kabar ta kawai itad'in mai laifine ranka ya dad'e wannan da kake gani annoba ce, yanzun ma hakam ninan shakkar ta nake ko wani zance bana son ya shiga tsaka nina da ita. mamkine karara ya bayyana afuskar yarima faruk, sanan yace ita ko mai ta aikata hakam ne mai girma har tazamo abun gudu cikin al umma, kuma gata da kananun shekaru? yaci gaba da fad'in lallaine zanso sanin mai ta aikata hakam., Abdul yace ranka ya dad'e wannan ba komai bane idan ka shirya zan sanar da kai, kallon sa yarima yayi kafin yace no abakin ta nake son ji asaka man ita cikin kuyangi atafi man da ita.




kallo na bita da shi raina fal farin ciki dan nima banga abunga dalilin da zaisa inyi farin ciki agidan da binta shugaba take ciki ba, dan tariga da ta zan gwame ni, dan hakam har cikin raina nayi farin ciki da raba mana gurin zama da za,ayi da binta shugaba koba komai na d'an shaki iska kafin naga wacce zata zamo madadin ta.....muryar inno shugaban masu dafa abinci na tsinkayo tana fad'in angama ranka ranka shi dad'e insha Allah duk abunda kake so shi za ai, nan take naga ta nu fatoni cike da murmushi afuskar ta ta rik'o hannun na sanan tace mutafi y'ata yarima ya bada umarnin atafi dake gidan sarauta ki shiga cikin masu hidim tawa ga iya lan mai girma sarki Aliyu bin Abdul jabbar, Allah yak'ara masa lafiya.

cike da sauyawar fuska alamar 'bacin nabi iya da kallo sanan na langa'be Kai almar bana so, cikin yanayi na kasala da Jin muryar hafsi mai tafe da tsantsar sauti kamar anbusa sarewa yarima, faruk yace tilas ne dake za,a tafi, daga hakam ya shige amotar sa dogarai suka take mar baya dire ba yaja su suka bar gurin, cikin bacin rai binta shugaba tace lallaine na yi mugun bak'in cikin kasan cewar wannan muguwar yarinyar shiga gidan sarauta, amman nasan dakafar ki zaki bar gidan saboda ukuba , waye baisan fulani safiya ba kowa yasan halin ta dan hakam da kanki sai kin fison zaman gidan kaso akan zaman gidan sarauta, da hanzari iya tabi binta shugaba da kallo kafin tàce hattara dai binta akiyaye harshe fulani ba sa an yinki bane, da sauri binta ta waiga bata ga idon makusancin fulani ba duk taron barorine dan hakam sai ta sauke boyayyar ajiyar zuciya kafin tàce, "nifa daman gani nayi ita d'in annoba ce acikin al umma shine fa, amman inani Ina fulani ai ruwa ba sa,an kwando bane, sanan taci gaba da fad'in nima dai shegen shigar shugula ne dani Ina ni Ina shiga maganar yarima kuma fa ba ko sashe d'aya muke da itaba agidan sarauta itad'in tana sashen masu dafa abinci niko Ina sashen masu kula da lafiayar gidan da tsaftar gidan, Kinga tafiya ta sanan takama Sha,anin ta iyace ta bini da kallo kafin tàce ki saki jikin ki nidin Ina tare dake, in Sha Allah zan zamo maki gata sanan kuma ko acan muka tafi ba ruwanki da kowa ki zamo makauniya agidan sarauta kizamo kurma agidan sarauta ba ruwanki da abunda bai shafeki ba, mutafi abamu kayan da kuyangi ke sakawa kafin gobe mushiga gidan sarauta, kallo nabi iya da shi nama rasa abun fad'a, ganin da tayi nakasa gaba na k'asa baya yasa tace man mutafi y'ata kisake jikin ki, kar kizamo mai garda ma. tom nace da ita sanan tace mutafi d'akin da kike dan naga kalan kayan ki, tom nace da ita kafin na wuce gaba tabiyo ni abaya, tafe muke tana k'ara man k'arfin gwiwa har muka karyo kwanar da zata sada ni da d'akina, cikin wani kalan mamaki iya dake biye da ni tace "mai nake Shirin da gani yar nan kar dai ace kene mai wannan d'akin? cikin rawar jiki nabita da kallo sanan nace mai ya faru iya ya Salam shine furucin ta kafin ta d'an yi jim sanan tace tabbas ked'in Mai nasara ne kuma lallaine ked'in mai kashin arziqine tabbas da akwai alkhairi cikin rayuwar ki mai tafe da albarka. shiru tayi kafin ta ce man mu k'arasa ciki, da rud'ani na k'arasa ciki Ina mai zullumin da ko kwanto abunda yasa iya tace man hakam bacin mun k'arasa ciki na duba yar tsum makaron shimfid'a ta wani kalan kunya naji da tsoron abunda iya zata ce dan shaf na mance ban d'auke wannan zanin da na d'aura a daren jiya da ta kasance man Daren farko da mijin da ban San sa ba bansan sunan sa ba bansan ainahim shid'in waye ba.... muryar iya na tsinkayo tana fad'in "ke yarinya kalleni da kyau, nakasa d'aga ido in kalleta dan tsananin kunyar abunda idona yagane man watom itama iya shine tagani, cike da tsantsar kunya na sunkuyar da kaina k'asa adai-dai nan binto shugaba ta danno kanta cikin d'akin bako sallama gamida fad'in sai kifito ga shiru tayi sakamakon abunda idon ta ya gane mata, cike da tsantsar mamaki tabini da kallo niko ido nasake yin kasa da shi dan wata matsanan ciyar kunya da ta kamani cike da rud'ani na nufi shimfid'ar da nufin in d'auke ta da hanzari binta shugaba tayi saurin rike man hannu wani fad'uwar gaba ne ta riskeni sakamakon tuna wa danayi Wannan mutumin da yake amsa sunan mijina ya gargad'eni kar na kuskura na bari wani ya shigo d'akin nan dan duk wanda yaji wannan mayen kamshin yasan daga inda ya fito.....✍️


💦 HUJJATA 💦




By

HAUWA MUSA RIJAU








CHAPTER 7--8




Akun yace na d'ago kaina danufin in rok'i binta shugaba da tasakar man hannu na karaf idon mu suka sark'e da na iya wata kunyar ce takara kamani cike da jin nauyin ta na sadda kaina sanan nayi k'asa da murya nace shugaba ki sakar man hannun yayi man zafi da yawa, cike da bakar masifar ta da tazamo mata jiki tace man, yanzun ke da nake ganin ki sumui sumi kamar na, Allah Ashe kina nan kina guma Sheri cikin d'akin nan naki? cike da tsantsar tsegumi dake cinta ta tafa hannu gamida cewa "ahaf gaske dai yau d'innan da farar safiya kika man wanka da ruwa, sai kuma ta zabura cike da tsantsar masifa ta ce ke yar nan shin Ina son sanin waima da wasu kalan ruwar ne kika man wanka? ruwar meye? kar dai ace ruwan da kika yi wankan tsarki ne tunda ga Shai da mun gani a yanzu? Aiko in har zatona ya zamo gaske da kin d'auki al hakina y'an nan, saiko ta wani disgo ni da k'arfi sanan tace Ina magana kinyi man shiru. cikin rawar murya nace "dan Allah kibarni ni ban san wani wankan tsarki ba can, bare na watsa maki su, cikin d'aga murya tace keee......iya ne ta katse ta da cewa yaka mata kisarara wa kanki hakam sanan itama kanta ki shafa mata lafiya kinsan girman k'azafi kuma kinsan hukuncin k'azafi anam gidan dan ked'in shaida ce da ilu yayi wa jummai da habu k'azafi Kinga irin hukuncin da akayi masa dan hakam ki kiyaye, gaban ki yarima faruk yace Yana buk'atar kasan cewar ta gidan sarauta sanan yanzun ki fullo da wannan zancen, sanan ita ta karyata ki mai kike zaton zai biyo baya, nan take naga jikin binta shugaba yayi mugun sanyi har tana kashe murya gurin cewa aa daman naga wannan lamarin kamar tom bara dai mana tafi kinga daman Abdul ne yace man Yana son magana dake takarasa maganar tana nuna ni sanan tace, cikin dan saussauta murya kinsan nike inno nazamo mai shigar shigula amman za a kiyaye yo waye zaiso amar irin Wannan hukumcin da aka yiwa ilu ai abun ba acewa koami bara na tafi dai ana jirana, cike da kame kame tabar d'akin, anam ne na fahimci ita d'in duk tsananin ta tana tsoron hukuncin shuwa ga bannin ta, cikin muryar mai tafe da gaskiyar abunda ke ranta iya ta bini da kallo kafin tace y'ata daki sirine kana abinda kaso acikin sa hakam kuma kana kimtsa sa dan gudun bakon bazata sanan tabbas wannan k'amshin shizai k'ara tona asirin abinda mutane zasu shiga zargi akan ki dan hakam kikiyaye,.


tom nace mata ga mamaki na ita d'in batayi mani wani dogon bincike ba kawai tace man ki nutsu ki kar'bi dukkanin k'addarar da tazo maki, sanan karki kuskura kiyi wasa da damar ki, dan Ina tabbatar maki a cikin mata dubu ke d'in kinyi masu zarra, na yarda dake dan hakam kirike wancan yazamo maki hujja sanan nima nayi maki alk'awarin zan zamo maki hujja cikakkiya aranar tambaya dan nasan sai ta zo tabbas zata zo.

hannun ta nabi da kallo dan ganewa idona abunda take Fadi na rika ya zamo mani hujja cike da zare ido na dafe k'irji na gami da fad'in na shiga uku, dan ganin wannan frame dinne da battar da wancan mutumin mai amsa sunan mijina ya bani yace na rike su hujja sanan kuma kar na bayyanar da su sai lokacin yazo amman tun kafin aje ko, ina gasu nan zube akan sumuntin d'akin ,cike da hanzari na d'auke su gamida tura su cikin jaka ta sanan na maida kallon ga iya kafin nace mata na gode,

shiru tayi ta kafe ni da ido har saida na tsargu sanan dan kanta ta kauda kanta ga barin kallona cikin murya mai tafe da kwantar wa da mutum hankali tàce man wacece ke? mik'e wa nayi batare da na tanka ta ba na kwashe shimfid'ar sanan na kaita can gefe nazo da nufin na zauna gaf da ita sai ceman tayi tashi maza ki d'auki tabar man kije ki wanke ta. ahalin yanzun ke d'in y'an tattatace ba mai takura ki ba mai tsangwa marki dan kowa yasan ked'in kinzamo cikin ku yangi dan hakam kije Ina jiranki, tom nace da ita sanan na mik'e naje na d'auki boket d'in da ake, aiki da shi na d'ebo ruwan sanan na wanke su tas bacin na kammala nazo na zauna gaf da ita, cikin sanyin murya nace iya bara na fad'a maki ko


...WACECENI






nid'in sunana HAFSAT usman ma haifi na yakasan ce talaka ne sosai, wanda baida cin yau bare na gobe a kullum sai ya fita neman abunda zaici shida iyalan sa, shid'in haifaffafen garin rano ne ta jihar kano aman a unguwa uku yake zaune tare da iyalan sa ya kasance yana da matar aure guda biyu acan baya, mahaifina kyakkyawan mutum ne mai cikar Kamala Yana da takawa da tsantseni hakam ne yasa jama,a da dama suke son shi da yawan mutane Yana matuk'ar burgesu kasancewar sa mutum Wanda abun hannun jama,a bai gaban sa duk kudin ka ko matsayin ka baza kace ga randa abbana yaje bara agurin kaba amam ya yarda yaje yayi ma aikin kud'i kabiyasa dan ya rufa wa iyalan sa da kansa asiri kaf gidan mu ba mummuna kuma mafi a kasarin mu farfaru sunfi yawa, Yana da yara ba kwai acan farko nake maki zancen uwar gidan sa mai suna iya abu itake da yara hudu duka mata sai mai binta itako tana da yara uku duka maza, tom fa duk da hakam sai tsananin kishi suke da junan su. ga gidan namu gidan hayane taron mata barka tai acikin gidan, sai dài ko wacce da sashen ta ana hakam sai Allah yahad'a Abba na da umma ta agarin yawon bara da takewa baban ta jagora, ganin yarda take faman shan wahalar zama da mugayen maza agarejin yasa ya tausaya mata da kuma k'arfin son da yake mata yasa yayi kulla kulla ya aure ta, dan ganin yaraba ta da wannan yawon barar tun a farkon shigowar ta gidan tagane masu gidan basa kaunar ta, aduk sanda ta shigo cikin su, sai ha baici ya tashi sai suke cemata karuwar tasha taga ma wa tsewa da mazan banza ta aure masu miji, ko kad'an bata nuna bacin ranta dan basu gaban ta akoda yau she nasihar mahai finta shine take fama da shi inda yake ce mata Aisha ki rike mijin ki dan shine yancin ki na duniya da ma lahira shine alkhairin ki ara yuwa, karki biyewa son zuciya har yasa ki biyewa abokan zama kuta musayar yawu akan mijinku kije ki zauna zaman aure da zuciya d'aya Allah ya tai makeki arayuwa yayi maki albarka yabaki zuria d,ayyiba idan tatuna hakam ta kanyi ajiyar zuciya tace insha Allah abbana zan zamo maka farin ciki arayuwar ka, tun sannan take ta k'ok'arin ganin ta cika umarnin ma haifinta har kawo sanda ta fara haihuwar fari, da biyu ta fara har saida tayi biyu so hud'u amman ko d'aya bai tsaya ba, sai fa ana biyarne ta haifeni na fito kyakkyawan gaske ga kyau ga tsari sai dài ansamu aka si tunda umma na ta haifeni bata sake lafiya ba sannu sannu har aka yaye ni, tana cikin ciwo yau gobe lafiya shekaru na biulyu umma ta tàce ga garinku😭 bacin rashin umma na rikona ya koma hannun umman hamza watom mai Y'ay'a mazan duk cikin zuriar mu ba Wanda ya d'auko fuskar mahaifinmu kamarni sak fuskata irin ta mahai fina ne sanan ko magana da tafiya harda yanayi tsayin sa na dauko sai dài hakuri da rashin tsoro da rashin son hayaniya sune na dauko na ma haifiya ta.




tun sa adda na dawo hannun umman hamza na soma fuskan tar matsala tun bana iya tantan cewa har nasoma gane me ake nufi da rik'o tafi tafi harna soma sanin cewa bafa ita bace uwata duk agidan ba mai kulani ba mai sona aduk inda naje tsana da tsamgwa ma shike biyo wa baya, duk fad'in gidan da girman sa ba mai shiga sha anina, acewar su wai nid'in tafe nake da k"ashin tsiya tunda ko uwata ta dalilin haihuwa ta ta bar duniya, yakasance ko yaran su basa son na rabe su da naje kusa da yara yanzun ko zanyi kuka, dan basa raga man ko d'aya aduk sanda zamu hadu da yaran unguwa mutum d'a yace ke kulani watom itace, ummi . jim nayi Ina shesh shekar kuka gamida dafe kaina dan tunowa da nayi da ummi baiwar Allah mai sona dan Allah, wacce naji ciwon rasuwar ta fiye da na umma na, dan nafi shak'uwa da ita sanan itace farkon nuna man soyayyar gaske bacin mahai fina, tun da ummi ta kyalla ido akai na Allah yahad'a jinin mu sosai bata son ganin bacin rai na kowani taga zai cutar dani sai inda karfin ta ya kare, ko islamiyya zata saida ni inma boko zata sai da ni dan hakam har ana muna inkiya da hafsin ummi ko ace ummin hafsi duk fa wannan abunda da ake abbana ba ruwansa da lamarina, acan farkon rasuwar ma haifiyata Yana kulani sosai tom amman daga baya sai yayi watsi dani, wannan shine karin ta barbare war rayuwa ta,




Matsalar da na fara fuskan ta shine baki watom kanbun baka aranar da na gane lallai Ina d'auke ta wannan cutar mai wuyar magani itace ranar

Please Login or Register in order to submit comment