Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ziyar ci hancina da sauri na d'ago kaina dan jin wani fad'uwar gaba da ya riskeni dan tabbas wannan k'amshin nasan shi, sai dai Ina tuna aina nasan shi, ban gama wannan nazarin ba saiga wani fari tas d'in balarabe ko nace ba fila tanin kyakkyawan gaske ya fito daga cikin wata k'ofa ido da baki da hanci na sake ina kallon sa dan nina san kyawun sa ya tafi da ganina yana dad'a tun karo gurin niko Ina dad'a yi masa kallon 'kurillah. wata irin tsawa ne naji an daka man sai da na zabura wani mahau kacin mari naji an watsa man wanda ya d'auke man gani na wucin gadi kafin nadawo hayyacina an k'ara aza man wani......✍️

❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_23--24

Wata kalan zabura nayi saboda azabar marin da nasha, muryar gimbiya safiyya ce ta maido ni hayya cina kad'an k'arfin murya take maganar inda take fad'in ke d'in Yar gidan uban waye da har kika isa kisa man miji gaba kina kallo? nace waye ubanki a duk fad'in garin nan dama Nigeria yar nan? Wata kalar shaka tamun idon ta a juye bakin ta har kunfa yake tsabar masifa nacin ta, da sauri iya ta k'araso gaban ta ta durkusa cike da girmama take rok'on ta akan tayi hak'uri sai kirari take faman yi mata tana bata baki dan ta hak'ura amman sai wani sham k'amshi take sai cewa take bazan hak'ura ba sai na daina ganin inwar yarinyar nan a gidan nan, cikin wata kalar murya mai amo take fadar ina jakadiya kizo kifitar man da ita, agidan can ta koma gefen sa ta zauna tana faman kad'a kafa, cikin wata kalar murya mai tafe da sanyi hade da tsantsar taushi naji yace " kibar ta kawai, wannan ba girman ki bane, wani mere baki tayi kafin tàce in takoma inda tafito kenan, adai-dai nan jakadiya ta karaso, cikin isa gimbiya safiyya ta nunani gamida fad'in "lallaine bana son wacce yarinyar ta k'ara minti d'aya cikin gidan nan, da sauri jakadiya ta nufo ni da nufin tayi waje dani, muryar sarki Mahmud muka tsinkayo Yana fad'in "duk kubar nan bana son hayaniya. da hanzari jakadiya ta bar falon itama iya ta taso da nufin barin falon nima na mara Mata baya can na tsinkayo muryar nan tasa mai sanya nutsuwa da tsantsar dad'in sauraro yana fad'in idan kika tafi waye ne zai had'a man tea d'in, duk muka ja muka tsaya nida iya, yakai minti biyar kafin yace wacce ta kawo shi tazo ta dauki a bunta tunda ba zata iya had'a man ba, Aiko iya tayi gaba abunta niko wani tsoro ne ya ziyar ci ruhina dan na gargad'u da marin gimbiya safiyya. wata uwar harara ta wurga man kafin da hanzari na taso na k'arasa gaban sa cikin sanyin jiki na had'a masa tea d'in na mi'ka mar, hannun sa yamiko man da nufin ya amsa hannun nabi da kallo araina Ina Raya tsabar kyau na wannan hannun idona nakai akan jajayen la'b'ban sa da yake motsawa a hankali harda wani d'an lumshe ido nake tsaar tunanin yaman dad'i, ouch shine abunda naji ya furta yayin da ya d'ago dara daran idon sa yana kallo na gamida dafe cinyar sa, sai alokacin na lura da ashe tea d'in gaba d'aya na sa kar masa shi acinyar sa da sauri na kai hannu na akan cinyar nasa da nufin in share mar. buro uba nan shine furucin da ya ankarar dani abunda nake shirin aikata wa, wani mahaukacin tsorone ya ziyarci ruhina da sauri na k'am'kame sarki Mahmud ina neman ceto dan da gaske naga wu'ka ahannun gimbiya safiyya gadan gadan nita haro, cikin wani irin ihu na k'ara k'am'kame sa da kyau dan bazan yarda ta sabar taniba, gaba d'aya na runtse idona, ina jiran saukar wu'ka a cikina amman ga mamakina sai naji shiru ahankali nasoma bud'e idona, acan gefe na hangota yashe ga alamar ma suma tayi, sai alokacin na ankara da irin tabar gazar da na tafka, aiko da sauri na cikasa shid'in ma ni yake kallo dan alokacin ganin yake tom mima zaiman? dan shidai ba da taka ta mata yake ba bare yagane kalar hukuncin da zai d'auka a kaina, da hannun sa yasa ya janye ni gefe sanan ya je kusa da ita ya duka Yana kallon ta, tabbas da gaske suman nefa tayi, caf aiko wannan yarinyar ta jan yowa kan ta ruwa. wani dan danja naga ya danna kafin daga bisani sai ga jakadiya ta shigo cikin falon batare da wani dogon zance ba yace kikaiwa wannan yarinyar gurin fulani tabar ta can guri ta kafin na zo. tom tace gamida fad'in amga ma ran ka ya dad'e hannu na ga ta kama da sauri iya da isowar ta kenan ta mara mana baya, sai faman fad'a take tana cewa ked'in ce y'ata kin fiye sanyi da yawan nawa yanzun Allah dai yasan kalan abunda zaki jawa mutane kuma banga kalar gargad'in da banyi maki ba hafsat niko dai faman fiki fiki nake da ido duk na yi kalan rashin gaskiya. wannan matar ce da ta fiddoni cikin falon take tambaya ta, ca tayi "wai mai yasamu gimbiya safiyya ce nagan ta some? ido ta kafeni dasu tana sauraron amsa, nima ita d'in nake kallo cikin in,ina naso fad'a masu abunda ya faru, dukansu ido suka zare gamida dafe k'irji suna kallo na baki a sake, cikin tsantsar mamaki wannan matar tace "bara kiga na koma daga ciki dan ma kar gimbiya safiyya ta farfado tazata ko dani a cikin tawa garki, ayau d'innan ko abin cina ya'kare a gidan nan da sauri ta bar gurin. cike da ta kaici iya ta kafe ni da ido kafin taja tsaki ta kara gaba tabbas na hango tsantsar bacin rai a idon iya, nan take nima nasha jinin jikina dan bansaba ganin ta a irin wannan yanayin ba, gaba ta shiga niko na biyo bayan ta tafiyar ba wani armashi har muka isa can kusa da fada acan na hango wasu kyawawan tsun tsaye masu kyau da sheki sai kyalli suke faman yi niko sai suka ban Sha,war kallo anan natsaya kallon su.




canna tsinkayo muryar iya tana fad'in ikon Allah wai hafsat yau she kika zamo hakam da sauri na tadda ta muka k'arasa shiga phart d'in fulani, kasancewar tana tare da jama,a shine fa iya tace man na zauna a d'akin danake har kuma ajima, itako sai ta koma sashen mai martaba, bacin na na zauna akan gadon na shiga tunanin wannan kyawun na sarki Mahmud gaskiya zan,iya cewa banta'ba zaton da akwai kalarsa ba, anan na shiririce har dare yayi sanan tashi nagabatar da ibada.


tun a waccen ranar nakai kwana biyar ban saka fulani a ido ba nidai ganinan narasa matsaya ta a gidan idan naga baba jummai na girki zanje na taya ta akullum tare dani ake girkin tom, yau ma kamar kullum ina juya kayan miya, har sun fara soyuwa k'amshin kayan miyar ya doki hancina nan take naji kaina ya fara juya wa saiko amai yarufe ni kafin na ankara tuni na wanke jikin baba jummai dake gaf da shigowa d'akin da a man,a tsorace ta taroni sai cewa take ke Yar nan mai yake damun kanki, cikin yunkurin amai nake nuna mata ciki na Ina shaida mata banson k'amshi kayan miyar da ake suya, mamaki ne k'arara afuskar baba jummai, cikin sanyin jiki baba jummai ta d'ago ni ta watsa man ruwa a fuska sanan ta wanke man idona adaki na ta zaunar dani sanan ta dawo da gyara gurin bacin ta sake wasu kayan miyar duk da cewa aman bai kai gurin girkin ba amman hakam dai ta sake wasu dan tsantsar tsan tseni da baba jummai take da, bacin ta kammala had'in komai na girkin saiko ta tarar dani d'akin sannu tayi man kafin tace man daman bakida lafiya ne? a a nace da ita sanan naci gaba da fad'in" yanzun na kai kwana, biyar kenan aduk sanda zanji k'amshin suyan kayan miya sai naji duk cikina yasoma hautsina nan take nake jin amai ya taso man, cikin tsantsar mamaki baba jummai ke kallo na tana gyada kai zama tayi sosai akan gadon nawa kafin tàce man kewai yanzun shekarun ki nawa? cikin sanyin murya na bata amsa da cewa sha bakwai shiru tayi kafin tàce man yaushe rabon da kiga al,adarki wata, irin kunya ce ta rufeni jin ta tambayi al,adarmu na mata amman ganin ba wasa afuskar ta yasa na bata amsa da cewa daman tun a satin can yadace na gansa amman yanzun gashi har sati ya zagayo ban gansa ba., cike da nazari baba jummai tace lallaine wannan zancen ba wanda zan barwa kaina ni kadai bane tilas ne fulani tasan da wanan zancen tashi mutafi shine furucin ta a kaina,


Tafe muke nida baba jummai zamu nufi phart d'in fulani dagani har ita ba mai yin magana kowa da zancen dake ransa baba jummai tana tunanin itako wannan yarinyar a ina tasamo ciki dan tabbas wannan ciki ne da ita lura da yarda ta ciko sosai ta k'ara yin haske kalar mai yaron ciki, niko ina tunanin wace kalar maganar ce za a shaida wa fulani sanan kuma mai isa nake yawan jin tashin zuciya, wani k'amshine ya ziyarci hancina wanda yasa na lumshe idona batare da na shirya hakam ba danko sosai naji dad'in k'amshin jinake kamar na rumgume mai wannan k'amshin idona arufe dan hakam bansan wanda ke gaba naba, sai jin wata tattausan murya nayi tana fad'in karkaso ma da hanzari na bud'e idona dan muryar mai martaba naji sai alokacin naga ashe wani dogari ne zai mareni mai martaba ya hanasa ashe har mun k'araso sashen fulanin baba jummai na hango tana a k'yarma kuma banga kowa a kusa da ita ba, kallo na na mayar agurin dogarai d'in naga duk sun zuba man ido sai alokacin na rula ashe akan takalmin mai martaba d'ora kafata shiko yazo fitowa ba tare da mun san dashiba nida baba jummai muka doso gurin shine fa wanna dogarin yaso duka na shiko mai martaba ya hana, kallona namayar gurin mai martaba yasha nad'in rawani baki wanda yaka rawa fuskar sa kyau da annuri , inda yake kallo nabi da idona sai alokacin na zabura gamida durkusa ina tuba dan tabbas akan ta kalmin sa na d'ora kafata bacin na durkusa ne da nufin tuba shiko ko inda nake bai kallaba ta kalmin nasa masu tsantsar kyau da tsada ya sanya ya k'ara gaba.

fadawa suka soma yi masa kirarin jinjina ga sarkin mai adalci ga talakawan sa, gaisheka sarkin da baya da tozarci ga talaka wan sa gaisheka sarkin da ke k'aunar talaka wansa, gaba yayi suka take mar baya niko hancina namika ina shakam k'amshin sa mai dadin sha'ka itako tuni baba jummai ta k'arasa gurin fulani dan isar mata da sa'kon dake ranta wata matace ta katsan tunanin dana ke da fad'in ke kizo inji fulani da sauri na dawo cikin hayyacina sannan nabi bayan ta a zaune na tarar da fulani da sallama na shiga cikin falon ba kowa sai ita da baba jummai da jakadiya, ido fulani ta kafeni dasu kafin tàce "waye wanda yata'ba koda rike hannun ki a rayuwar ki bare har yakai ga jikin ki da kika samu ciki? da sauri na dafe kir jina gamida waro idona kafin na ce ciki?......✍️

❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_25--26 wani mugu tsoro ne ya ziyar ceni jin furucin fulani a kaina cikin wata fad'uwar gaba na shiga zare ido na tabbas yau na raina wayau na, tom ni yanzun waye ne zance uban ciki na? cikin rawar murya nace ba ban ba wanda ya ta'ba ta'bani ni sai dài kawai injin tashin zuciya ne, bak'in k'ofar naga fulani ta kafa ma ido juyo wa nayi dan ganin abunda take kallo yarima faruk ne a tsaye ya kasa k'araso wa aciki sanan nid'in yake kallo ga alama yaji abunda muke fad'i, nima shid'in nake kallo ido cikin ido muke kallon juna k'arara na hango bacin rai afuskar sa kafin fulani ta katse mu, da fad'in tom yanzun na gano bakin zaren, shiru tayi sanan naga baba jummai ta bar falon, itama jakadiya nan naga itama tabar falon dan hakam nima na mik'e da nufin nabar falon kallon da fulani tabini da shi ne yasa na fasa tashin, takon da naji ne yasa na d'aga kaina dan ganin ko waye yarima faruk ne yak'ara so shigowa ciki gafan fulani ya gurfa na har k'asa Kai naga ya d'ukar a k'asa kafin naji muryar fulani tana "fad'in lallaine faruk kaine ka shigo da wannan yarinyar gidan nan sannan kaine kawai ta sani a gidan nan bacin hakam kuma nid'in banason kakawo man wani uzurin agaba na, ido ta kafa masa kafin tace faruk kar inji kar ingani tabbas kar kabari zatona yazamo gaskiya, cikin tsananin rud'ani yarima faruk ya shiga girgiza mata kai kafin ya juyo kansa gareni cikin tsantsar rud'u yace man keee waye uban cikin ki? tsoro ne k'arara afuska tadanko sosai na tsorata da ganin fuskarsa, cikin rawar murya nace ban sani ba nima. kamar ya baki sani wlh kisar da ummana cewar niban sanki ba ban ta'ba ganin kiba sai agidan yari kuma tau sayin ki naji shine fa har nasa aka sanyo ki cikin bayi, please kisanar da umma ta komai hafsat, dan kar ta zargi wani abun a tsakanin mu cikin rawar murya nace tabbas umma ni bansan ko waye uban cikin dake jikina ba sai dài abu d'aya nasani shine tabbas cikin ba shege bane dan ko, sai da aka d'aura auren mu dashi sanan, amman fa ban san shima.

wani kalan kallo ne yarima faruk ya bini dashi kafin yace ke "amman kin cika cikakkiyar ma hau kaciya watom yanzun ko waye ma yazo yace maki shine mijin naki zaki iya amince mar? ido nabisa dashi kafin nace nifa sai kuma nayi shiru dan kunyar fulani ce ta kamani ganin ta kafe ni da ido, shiko yarima wata harara ce yabini da shi kafin yace kefa me? ca fa yayi na taimaka masa na aure sa Wannan daren niko sai...shiru nasake yi saime? cewar yarima ganin na ki d'ago kaina yasa umma tace "yanzun ba wannan ba duk naji bayanin ku sai dài ban gamsu ba kuma kasa aranka zan tsanan ta bince akanka har sai na gano gaskiyar lamarin sanan kuma daga wannan ranar na hanata ko wanne aiki anan sashen nawa zata dawo har sai ta haihu zansa ido sosai akan ta dan nagano bakin zaren har kaima tabbas, shiru tayi kafin take ce ma yarima bacen dagani cikin sanyin jiki ya mik'e gamida fad'in dan Allah ummana ki yarda bani da hannu aciki kuma sosai zan binci ko waye shi sanan kuma tilas yasake ta danko wannan ba tsarin gaskiya yabi ba, yak'ara sa zancen yana mai fita daga phart d'in, aransa yana Nazarin wannan lamarin, tom waye wannan da yayi masa shigar sauri hakam dan tabbas tunda yaga wannan yarinyar aransa yaji wani abu akanta kuma yayi guri akanta wani kalan shu,umin murmushi ya saki gamida cewa tilas inada HUJJATA akanki HAFSAt muje zuwa nid'in nine dake sanan yasake sakin wani murmushin gefen baki cikin k'asaitar sa yabar gurin (tom fans mai yarima yake nufi ne?)



Tun awaccen ranar fulani ta umarce ni da natsaya anan sashen ta d'aki guda ta ware man da dukkanin abunda zan buk'ata. ba laifi Ina samun kulawa sosai kamar kar asan da cikin shike nan sai ko wani bak'in kwadayi ya taso man ga yawan son 'Kam shim turaren mai martaba, ga kuma kwana biyu banji shiba, tun sanan da fulani ta gargad'i yarima faruk akaina saiko ya daina shiga haraka ta, amman fa aduk sanda yazo sashen idon sa akai na yana yi man wani kalan kallo na zan rika kine, niko ko ajiki na danko banga laifin da nama saba.


yauma kamar kullum ina zaune afalon fulani babba itako tana can karamin falon ita da kuyangin ta suna hirar su danko fulani bata da matsalar rayuwa ta d'auki kuyangin ta kamar abokan shawarar ta, dan hakam suke sakewa da ita, kallo nake hankali na kwance, sanye nake da doguwar riga tad'an kame man daga gurin mazauna na ta baje daga k'asa sai can ta saman ta a bud'e take na d'ora kafata akan hannun kujerar dake kusa dani wani kalan k'amshin ne ya daki hancina sosai na sha'ka gamida d'ago kaina fes na sauke idona akan sarki Mahmud wanda shigowar sa kenan acikin falon bakin sa d'auke da sallama can cikin makoshin sa idan ba ka saurara da kyau ba baza ka fahim ta ba idona na d'ago da nufin kallon sa danko ina son kallon jajayen la'b'ban sa suna mini kyau caraf idona suka gane man inda yake kallo watom na shanuna da suka ciko suka tam tsam su yake kallo da sauri na duk'e cike da wata kalar kunya da ta kamani, a gefe kuma haushi naji tom shi meye nasa na kalle man jiki, muryar sa mai saukar da nutsuwa da saukar da kasala na tsinkayo yana fad'in kiyi man iso gurin umma ta kai na d'ago sai alokacin na tuna ashe ban kwashi gaisuwa ba gurin sarki da hanzari na duka sanan na gaida sa yi yayi kamar bazai amsa ba idon sa acan gefe sanan ya amsa muryar sa acan ciki. niko mik'e wa nayi da sanyi na nasoma tako na kamar mai yanga na karasa karamin falon fulani dan isar da sa'kon mai martaba jikina ne yabani ana kallo na dan hakam da gayya na k'ara juya mazau naina har na k'arasa isa ciki har k'asa na durkusa dan girmama wa ga fulani sanan na isar mata da sa'kon mai martaba cike da farin ciki ta tashi zaune danko tana jin dad'in yarda danta ke kulawa da ita baruwan sa da sarautar sa aje sarautar yake gefe yabata hak'k'in ta sosai, aiko nan take duk kuyangin suka bar falon duk wacce tazo fita sai ta kwashi gaisuwa agurin sarki bacin sun kammala fitane shiko sai ya k'araso falon, jakadiya ce ta shiga yi masa kirari kafin itama ta fice, cikin sanyin murya da girmama wa ya gaida mahaifiyar sa itama cike da farin ciki da sakin fuska ta amsa, bacin sun d'anyi hira game da yanayin da ake ciki da ganan yasoma tambayar ta yaushe ne yarima faruk zai fitar da matar da zai aura yaci gaba da fad'in shifa ya matsu yaga d'a ko na dan uwansa ne, cikin damuwa yace umma yaya Ali har ya koma ga Allah bai aje d'an kansa ba. nima yanzun na kai shekaru hud'u amman shiru umma kinga ko ai ya dace yanzun shima faruk d'in ya yi aure ko maga d'an sa itama batula karatun ya isa hakam ta dawo gida ta fitar da wanda take so ayi mata auren Allah yasa kar suyi irin namu ameen ya k'arasa maganar fuskar sa d'auke da da muwa. cikin rarrashi da kwantar da hankali fulani tasoma yi masa nasiha mai shiga jiki, sosai ya sauke ajiyar zuciya sanan yace umma ta kiyi man addu,a Allah ya k'addara inga d'an kaina a duniyar nan, cikin jin dad'i umma tace ameen ameen Mahmud yakai kusan awa d'aya a tare da mahaifiyar sa suna ta hirar su kafin ya bar sashen niko alokacin inacan nasoma barcin da yazame man jiki.






Da kimanin k'arfe d'ayan dare na farka sosai nake bud'ar hancina dan tabbas kalan k'amshin da nakeso shi nake sha'ka ga wani dumin jiki mai tsananin taushi da yayi man rumfa sosai nake jin dad'in kwanciyar juyin da nayi yayi dai dai da farka wata anan ne nagane ajikin mutum nake kwance da sauri na zabura dan tsananin tsoron da ya kamani cikin taushin murya naji ance ki nutsu sosai man, da sauri na bud'e idona sai dai bana ganin ko waye amman tabbas ina ji ajiki na kamar murya da k'amshi yarima faruk da sauri nace Yaya faruk dan Allah kabar nan nifa na fad'a maka inada auren wani akaina kaga ko banda aure bai dace kashigo man d'akiba harda rumgumata bare kuma da auren akaina. cikin wata kalar murya wacce na gaza fahim tar ai na nasanta, na ji ance dan Allah hafsat ki taimaka man wlh zan iya rasa raina akan abunda nakeji please aikin san nid'in mijin kine shiru yayi niko jin yayi shirune yasa nace daman kasan da zama na kashare ni? cikin waccen muryar mai muyar fassara wa yace ina sane dake dan hakam ne ma nasa aka maido ki gidan sarauta sanan kuma duk wani motsin ki akan idona kike yinsa yanzun ba wannan ba, ina zoben da nabaki? shiru nayi danko ban san inda na yada shiba jin nayi shiru ne yasa yaci gaba da fad'in wannan zoben da kike ganin shine hujjar ki akaina dan hakam ki kula hannu na ya kama ya sanya mani zoben wani yàr naji ajiki na lokacin da ya ta'ba man hannu, ahhh shine abun da na furta, a sanda naji saukar hannu wansaakirji na kara matso sa nayi sosai danko nid'in inajin dad'in wannan abun sosai yake shafa ta sai fad'in yake kina da tes hafsi, na kwad'aitu da ni,imarki tun awaccen ranar, niko sai k'ara shige masa nake ina fad'in dan Allah kabarni naga fuskar ka ko sau d'aya ne ina alokacin ya soma shiga ta bakin sa ya sa ya rufe man nawa daga nan nima na lula duniyar da ya jamu, sai can gurin ukun dare sanan ya barni sosai ya k'am'kame ni yasoma sanya man albarka cikin kunnuwa na yake rad'a man kina da testing ban gajiya dake hak'uri na ya'kare akanki tabbas kwanan nan zan kusan toni dake, cikin dan sheshshekar kuka na soma magana, jin muryar kuka atare dani yasoma rud'ewa yana fad'in me kuma ya faru? nace dan Allah kabarni naganka danko nidai zuciya ta tabani Yaya faruk ne kai awaccen ranar kaga irin fad'ar da umma ta yi akan cewa kaine ubn cikin jiki na ka musa tom akan meye zaka mun hakam yanzun idan Allah ya kawo abunda ke ciki lafiya mai kake so nace masa tunda nima ban san ko waye mijina ba, cikin tsantsar rud'u yace man me kikace ciki kike da eh shine amsar da na bashi da mugun hanzari naji an.....✍️



❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma

Please Login or Register in order to submit comment