Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_ 27--28


Damko hannu na, sanan ya talla bo man kaina, saitin fuskar sa, muna shakar num fashin juna, "da gaske kike ciki ne dake? "eh, hakam naji fulani tace, shiru naji yayi kafin naji saukar dam shin hawaye akan hannu na, cikin rud'ewa na riko hannun sa gameda fad'in "kayi hakuri inna takura ka akan hakam, bana son in haifi d'anda zai tuhu meni ne a kan uban sa, amman kayi hakuri insha Allah zan cigaba da hak'uri daga ni har abunda zan haifa.

wani kukan ne naji yazo man sosai nake shesh shekar kukan, arai na ina tuna kalan k'addarar da nake ciki, mahaifi na ya wofin tar dani, y'an uwana sun tsaneni, auren yazo man ahagun ce, mahaifiya ta bata raye, yau ga d'ana zaizo abaran shege.

cikin wani gunjin kuka na dafe cikina kafin na soma fad'in inason abunda zan haifa koda kowa zai guje mun ne bani da kowa sai wannan cikin, insha Allah bazan barshi ya zu bar da hawaye ba.

saukar tattausan hannun sa naji akan fuska ta yana sharen hawaye na kafin ya rungume ni k'am'kam ajikin sa, mun Kai second 30 a hakam, kafin ya cika ni. shiru naji ya gifta d'akin kafin naji motsin k'ofa, alamar yafi ta kenan. wani sabon kuka ne naji yazo man a raina nake nazarin waton, "shi wannan bawan Allah bazai ji tausayi naba? sai dài inma zan mutune shiko sai dài ya kwaso damuwar sa yazo neman tai makona, niko yanzun ba zai nuna man kansa ba, wata zuciyar ta ke ceman kema dai kin faye rashin fahimta, ai basai ya nuna maki kansa ba. kiyi amfa ni da han kalin kanki kiga duk a gidan nan wake da wannan muryar inaba yarima ba, wake da kalan wannan k'amshin inba yarima ba, ki nutsu da kyau ki gane. da sauri na share hawaye na, na zabura na zauna kafin nace tabbas zan d'aukar wa kaina mata ki ga yarima.,


kamar yarda ya shaida man wankan tsarki hakam nayo, sanan na d'ora Al wala naso mayin na fila, har sai da lokacin sallar asuba tayi, naga batar da farali, kafin nakoma can na soma nazari.


7:am na taso dan ganin tashin fulani, a adai-dai lokacine shima ya rima ya shigo falon, ido cikin ido nake kallon sa, banko yi nazarin in soma gaida shiba, sai dài kawai na k'araso gaban sa, da mugun hanzari na rik'e kafar sa ina rok'on sa, sai fad'in "nake dan girman Allah yaya faruk ka tai makaman, kafitar dani duhu. wlh bani da mafita inba naga uban d'ana da idona ba, kuma duk kalan nazari na a kanka ya kare, shiru nayi kafin naci gaba da fad'in "inma baka son kowa yasani ne tunda har da auren ka akai na,niko nayi alk'awarin zan rik'e maka sirrin ka.

shiru nayi ina shesh shekar kuka, ido ya kafe ni dasu kafin ya janye man hannu wana a kafar sa, ya zaga ta gefe na, sanan yabar falon.


a i don sa na hango tsantsar tausayi na kwance a kwayar idon sa.

, d'akin fulani ya nufa kafin can naga ya fito ya koma, can a akan kujerun dake falon ya zauna, ina gefe ina sharar hawaye shiko yana latsar wayar sa.


fulani ce ta fito cikin takun ta na k'asaita da Kamala, acan kan lun tsuma lun tsuman kujerun ta na alfarma ta zauna idon ta akan yarima dake faman murzar hannun sa yana had'e su alamar yana cikin damuwa. fulani dake kallon sa tana nazarin sa ganin baima san da isowar ta a falon ba sai ta k'ura masa ido kafin ta maida duban ta akai na, nid'in ma ban san da shigo war ta afalon ba danko azahiri itad'in nake kallo amman kuma tu nani na baya a kanta. namaki ne kwance akan fuskar fulani, cikin d'an fad'a fad'a tace wai me kuke 'boye manne? dukan ku kun tasa juna gaba sai faman tunani kuke, ido ta k'afa ma yarima kafin tace" Umar ka fito fili kasanar dani a binda kake boye man, game da hafsat. idon sa ya mayar akan ta sai alokacin ya d'uka ya kwashi gai suwa, nima sai alokacin na tuna abunda ya fiddo ni d'akina da sauri na d'uka gamida d'ago jajayen ido na na kafe ta dasu kafin nagaida ta.


nima d'in kallo tabini da shi cikin yanayi na damuwa tace"hafsat!! keda Umar!! ya kamata kudai na wahalar da kanku kusani duk fa duniyar nan bamai iya hana k'addarar sa ta riske sa, amman karku sanya yau darar kanku da abunda zaku haifa, dan cimma wata manufa taku. sanan inhar itad'in bata san meye gidan sarauta ba, tom ai kai kasan ni danko inhar ka batawa sarautar ku suna kaicon ka.


shiru mukayi dukan mu, niko sai faman kuka nake danko tabbas abun na ta'ba man zuciya ta tabbas inason cikina tunda shi kad'ai nake da shi aduniyar nan tom amman waye uban sa? fes sauke idona akan yarima wanda shima d'in ni yake kallo kafin ya maido duban sa ga fulani cikin girmama wa yace gaida ta sanan yasoma bata baki akan cewa "kiyi hak'uri ummata ni nasan insha Allah gaskiya zatayi halin ta, shiru yayi, kafin ya ci gaba da fad'in, ummana!! daman nata'ba yiwa kaina alk'awarin, duk ranar da buri na yaci ka akan wata bukata da nasa gaba, insha Allah zan yanta bayi goma, kuma alhamdulillah a daren jiya anyi man albishir da hakam yanzun ma har nasoma shirye shiryen tafiyar insha Allah da zarar na dawo, zan ware wad'an da zan yanta.


Allah ya kiyaye shine furucin fulani da ga hakam saiko tabar falon, niko inacan ina sharar hawaye, shima yarima tashi yayi da nufin barin falon saida yazo gaf dani sanan ya d'uka saitin fuska ta, ido ya bini da shi kafin yace "Allah ya baki mafita.


daga hakam yabar gurin idona bisa da shi har ya'bace wa ganina kafin na koma d'aki na nasoma kuka sosai danko da gaske ina cikin da muwa, ganin hakam ba mafita bace a gareni yasa na hak'ura na fauwa lawa Allah lamari na, tun awaccen ranar ban sake sanya yarima a ido naba, sanan shiko cikina sai ya soma girma danko alokacin mun kai wata biyar da shiga gidan sarauta. hakam a ban garen fulani tana kokarin ganin ta rage man damuwa kafin ta had'ani da doctor Maryam, sosai take kula dani da abunda ke ciki na, balai fi nasoma walwala tunga nasan banda mafita bacin hakam.





Yauma kamar kullum ina kishin gid'e, a cikin babban falon fulani Ina shan a gwaluma, wani kalan k'amshin ne hnaci na ya shako man mara dad'in shaka wanda yasan ya na d'ago kaina da hanzari dan ganin daga ina k'amshin ya fito, ga wani wahalallen amai da ya taso man, aiko caraf idona acikin na gimbiya safiyya jin aman ya taso man da gaske hakam yasa na mik'e da nufin na nemi gurin yinsa, aiko da k'arfi ta ca kumo man wuya kafin ta sauke man mari afuska ta cikin zafin marin da hautsi nar da cikina yake man naji aman ya yunk'uro man kafin duk na ankara na wanke jikin gimbiya safiyya da amai yunkurin nake idona duk awaje dan ban san mafita ba, aiko da mugun hanzari ta tashiga wanka man mari ga k'amshin turaren ta nata azab tar dani, agala baice na tafi luuuu zan fad'i dan ko nagala 'baita ga azabar mari ido na a rufe Ina sauraron kalar fad'uwar da zanyi ga mamakina sai najini ajikin mutum, ga mayen k'amshin nan da nake mayata, k'arar marin da naji ne yasa na bud'e idona taoro ne ya kamani ganin na kwance ajikin........✍️


❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_ 29--30

Tsoro ne ya kamani ganina kwance akan k'irjin sarki Mahmud, da hanzari na yunk'ura da nufin zame wa na zauna kan kujerar dake cikin falon k'ara rungume ni yayi kafin ya maida duban sa ga kuyangin dake falon. kallo d'aya yayi masu aiko da hanzari ko waccen su ta kama gaban ta, danko sun san abinda yake nufi.


, idon sa k'ur akan gimbiya safiyya wadda keta ruga ashar akaina, sai kokarin ganin ta cafko ni take shiko hakam yasa ya zafga mata mari, da wani kalan tsoro da mamaki k'arara afuska ta ta kafe shi da kallo cikin muryar rud'ani, tace "my, yau ni ka wanka wa mari akan wata kuyanga? idon sa fes akaina a lokacin ya direni akan kujerar sanan ya sanya hannun sa cikin aljihun sa ya d'auko wani kalan hamki chif mai kyau da k'amshi ya mik'o man kafin yace man sannu, sai alokacin ya maido da kallon sa akan ta cikin muryar sa mai tsananin taushi da ratsa zuciyar mai sauraro, yace"yanzun ke wannan shine kalan adalcin dake tsakanin shugaba da kuyangin ta? wannan shine kama girma atsakanin ki da wacce take k'asa da ke, ya kamata ki rik'e marta barki sanan na mareki ne akan rashin imani da kika nuna ba wai dan wata kuyanga ba, da ga hakam ya k'arasa gaban fulani dake can farkon falon tana kallon ikon Allah, cikin girmama wa ya d'uka ya kwashi gai suwa, kafin su k'arasa ciki.


da ido fulani ta kafe sarki Mahmud kafin tàce mai ya faru? d'an murmushi yayi sanan yace shirme ne kawai irin na mata, sanan ya mik'e yace "zan shiga fada ummata kiyi man addu,a cikin murmushi da soyayya irinta da da uwa ta dafa kansa sanan tace "ubangiji yayi maka jagora Allah ya dafa maka akan dukkanin lamuranka, cikin murmushi ya ce "na gode ummata, sai yad'an dukar da kansa kafin yace ummata ya fad'i hakam yana mai langa'be Kai, gane me take nufi, yasa tad'an yi murmushi sanan tace" ubangiji ya baka zuria dayyiba murmushin ya sake yi sannan ya ce ameen ummata Allah yashim fid'a maki mashin fidi mai kyau acikin aljanna ferdausi dimun da iman. amenn ameeen d'ana. daga nan ya taso yabar d'akin, a falon ya tarar dani kwance duk fuska ta ta d'an hau kallo yabini da shi, adai dai lokacin jakadiya ta k'araso cikin falon ganin mai martaba da kansa yasa ta d'uka ta kwashi gaisuwa sannan ya umarci jakadiya da tayi hanzari Kiran doctor Maryam dan ta duba lafiya ta., kafin shiko ya bar falon Yana fitowa fadawa suka mara masa baya sai fada,.


Fulani ce tsaye akaina niko sai juya hannu nake, da sauri fulani ta rik'o hannu na gamid kafe yatsa na da kallo sanan tace man ina kika samu wannan zoben? idona suna lumshe wa suna bud'e wa, nad'an kalleta sannan nace "shine wanda yabani yace man narike sa HUJJATA danko ranar da buk'atar hakam ya taso.


sosai ta kafe ni da kallo kafin tàce man shiwaye wanda ya baki cikin rawar murya mai tafe da zazza'bi nace shine wanda ya aureni cikin tsantsar mamaki filani ta kafeni da ido sosai take kallo na, sanan tace wa jakadiya kira man doctor Maryam a waya ta, da sauri jakadiya ta yi calling d'in nomber doctor Maryam, sanan ta k'ara wayar akunnen fulani, bacin doctor ta kwashi gaisuwa ga fulani sai take fad'a mata tazo da hanzari hafsat ba lafiya, ba wani bata lokaci saiga doctor Maryam bacin gwaji da sauran aune aune da tamun nan ta bani tarkacen magun guna na masu ciki sanan tayi man suran allura kafin tàce man ki samu hutu sosai ki nutsu ki rage tunani da damuwa, kaina d'aga mata, kafin narike wa fulani hannu sosai nake kuka nace " umma dan Allah ko kinsan ko waye mai wannan zoben? ki taimakan umma ki sa nar da ni nid'in ma rai niya ce ma hai fiya ta tabar duniya, mahaifi na ya wofin tar da ni, sanan yanzun wanda yake amsa sunan uban ciki na ya banza tar dani.


dan Allah umma ki tai ma kan ki sanar dani waye mai wannan zoben ko naji aanyi. cikin tsantsar tausayi, tace "kidai na kuka hafsat danko Allah yara baki da kuka, kisawa ranki kina cikin mata masu sa,ar zuwa duniya tabbas ked'in mai nasara ce. yanzun ba wannan ba hafsat ki nutsu ki fad'a man tsakanin ki da Allah ked'in wacece? Ta k'arasa maganar tana mai kafe ni da Ido,




Kafin taci gaba da fad'in amman fa ba yanzu ba kibar shi sai kin ware idan kinsamu lafiya.



tom nace gamida runtse idona daga nan sai wani kalan barci mai nauyi yayi gaba dani , itako fulani sai faman gadi na take ta hana koda jakadiya ce ta zauna ainda nake wannan kenan.










Gimbiya safiyya ce cikin falon ta, tana Kai komo danko tun ranar da uwar ta ta haifo ta ba,a ta'ba bata mata raiba irin waccen ranar, itace har tayi lalacewar da sarki Mahmud zai zafga wa mari akan da daki kuyan ga, kuyan garma, kusan yar cikin sa danko a haihuwar kaji ai yahaife ta, tom wai mai hakam ke nufine? wata zuciyar ce ke shaida mata cewa aiki kamar ciki ne da ita, wata kalar zabura tayi sanan ta soma danna wa iya Kira, da hanzari iya ta shigo har tana shirin fad'uwa da sauri ta d'uka ta na rawar jiki kafin tàce gani, da wata kalar tsawa ta daka mata sanan tace ita waccen yarinyar wace ita?, da rawar jiki iya tàce ban gane wacce kike nufi ba,. bazaki gane ba, har sai na kasheta ko na illa ta akan me ye zata rumgume man mijina shima a yau da idona na hango ta kwance akan kirjin mijina sanan akanta ya zafga man mari, tilasa ne sai na illa tata ko na kashe ta sanan zan fuce abunda tayi man. da rawar jiki iya ta soma fad'in tuba take ranki ya dad'e Amman ko inda take bata kulaba, cikin fushi ta nufi phart d'in ta kuyangin ta suka mara Mata baya.




Tun a waccen ranar da ya iso k'asar ya kasa sanin ainahim abunda ke damun sa, tabbas yasan ya kamu da son yarinyar kuma so mai tsananin gaske yake mata so kalan wanda ke yado mai d'ore wa har, abadan, amman sai daifa ina mafita? taya hakam zai faru? meye hujjar sa akanta? ya Salam shine abunda ya furta gamida dafe kansa, wata kyakkyawan yarinyar ce tazo gurin sa ta na k'araso wa ta haye mar cinya gamida fad'in "prince lafiyar ka? , hannun sa yasa ya d'ago ta kafin yace tina yaushe ne zaki kama gaban ki nace maki na daina na tuba wa Allah insha Allah bazan sake zina ba, please kibarni Tina., cikin wani kalan mayen kallo tace my prince tilas saifa ka aure ni danko duk duriyar nan ba nami jin dake man sugar sai fa kai, nid'in da kaina saba kaine ka koyar dani sirrin so da kulawa bazan iya jure rashin ka ba ko nan da can. da sauri yarima faruk ya rik'o hannun ta sanan yaturo ta waje kafin ya maido gidan ya rufe sannan ya fad'a duniyar tunani danko shidai ba wacce yake gani idan ba hafsat ba, yarinya mai tashen kyawu da kuruciya ka tsantsar kalo da class hannun sa ya nausa gamida fad'in hafsat yangar ki ta tafi dani sosai, cikin sanyin jiki gamida bacin rai ya janyo filo ya rungume sosai sannan ya sauke ajiyar zuciya Yarima faruk kenan.





Zaune nake afalon fulani yanzun kam na saduda na sada kar damko fulani sosai take bani kulawa tana kamtar man da hankali gamida cire man da muwa, kallo nake suko kuyangi sai Kai komo suke suna ta Shirin zuwar gimbiya batula da ta kammala karatun ta acan kasar Egypt wacce akesa ran dawo warta ayau sai faman murna muke, wata daga cikin kuyangin fulani mai suna saratu tana gefe na tana yanke man farce na, niko sai faman shafar ciki na da yafito yaman girma ajiki nake duk ya baje man kota ina, hira take man niko Ina d'an yin murmushi, Wannan myen kamshin wanda bana gajiya da shi shine yaman sallama a hancina idona na d'ago na sauke su fes akan sarki Mahmud da shigowar sa falon kenan, shima d'in idan sa akaina yake, Yana takon sa kalan na k'asaita da salon burgewa jajayen la'b'ban sa naka fa wa ido banko kyafta wa, inason wad'annan la'b'ban nasa suna bugeni, na shaga la sosai da kallon sa banyi aune ba sai na tsinkayo muryar sa mai tsananin taushi gamida debe kewa yana cewa "kibarni hakam karki cinye ni, wata kalan kunya ce ta rufeni sosai nasanya Hanna yena na rufe idona cikin salon sa na burgewa yace man ke bakya gaida kowa ne? a kunya ce na d'ukar da kaina kafin nace "Ina wuni' ban gansa ba, shine amsar da ya bani kusa da inda nake zaune ya k'araso ya zauna gamida fad'in gaisuwar ma sai da na roka, fuskar sa gaf da nawa saida na tsora ta danko tsoron k'arara a fuska ta na juyo dan ganin saratu dake kusa dani, sai dài naga wayam ashe tuni tabar gurin shid'in ma kara ma tsoni yayi sosai har muna iya jim num fashin juna kafin yace man na kula kina son wad'an nan, ya fad'a yana mai nuna la'b'ban sa sanan yaci gaba da fad'in tom gasu nan ki cinye su sosai yake kokarin hade bakin mu guri d'aya ido na waro gamida ja da baya shiko sai kara matso ni yake da gaske tsoro ne k'arara afuska ta danko ganin nake anya kodai sarki ya zare ne ko ko hauka yake baya ko tunanin wani zai iya shigowa atarar damu a hakam girman sa ya zube, cikin rawar murya nace please "kabar ni banaso. shima da kalar murya tawa yace niko inaso sosai ya shafo cikina kafin yace daman ked'in matar aure ce? Shiru nayi damko duk sai nake ga kamar bashiba ganin ban tanka ba ku yasa ya bar gurin ya koma asalin sa sanan yace man ina ummata cikin rawar murya nace sun fita ita da jakadiya, ido ya kafeni dasu kafin yace tun yaushe ne? Adai dai nan su umma suka shigo falon da sallamar su kafin shima ya amsa cikin nutsuwar sa ganin na adiririce yasa umma tabi shi da kallo shiko sai yadn sunkuyar da Kai gamida sosa wuyar sa sanan yayi mata sannu da zuwa gamida tambayar yaune isowar auta eh tace mar sannan ta fad'a daga ciki shima ya mara mata baya, da sauri ta juyo sanan tace anya ko Mahmud kayiwa danka adalci daka sama masa uwa agidan yari alhalin baka san ko itad'in wacece ba.........✍️


❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_ 31--32


HAZIKAI STAR 🌟


Da d'an hanzari ya d'ago kansa ya kalli fulani, dan jin furucin da baiyi zato ba, duk da yasan hakam zata faru tom sai dài baiza ta a yanzun fulani zata tuhume sa ba. cikin sanyin jiki ya ce " ummata kin san HUJJATA kuma kece ma kika kara man k'warim gwiwa akan hakam. shiru yayi yana sauraro jin furucin ta, kai ta d'ago kafin tàce "tabbas nine na baka dama akan hakam danko hujjar ka mai k'arfi ce, sai dài fa gaskiya ina jiye maka ranar gori wa y'ay'an ka kasan fa abun duniya baya boye watan danka ya zamto sarki tabbas sai ma'kiya sunyi masa gori akan cewa uwar su ma agidan yari ka aure ta, wanima ca zaiyi ko auran baka yi da itaba, a sad'aka ka zauna da ita, gaskiya Mahmud duk mutum baya kauce wa k'addarar sa amman fa banji dad'in auren ka agidan yariba inama ace d'auko yarinyar kayi kazo nan aka d'aura auren kaga hakam zaizo da sauki amman ko yanzun ina maku fatan alkhairi Allah ya Sanya alkhairi ga auren naku. cikin kasa da murya yace ameen ummata, shiru sukayi kafin umma tace "ina taya ka murna nasamun karuwar cikin da hafsat keda Allah ya ingan ta, Kai yadan d'ukar kafin yace "ameen ummata, ido ta bisa da shi sanan tace tabbas kaid'in bana zargin ka har abadan nasan Allah yatsare man kai da aikata zina, amman inason mlm d'in da ya d'aura auren ku dan nazamo shaida, ta k'arasa maganar tana fad'in angon gidan yari, murmushi ya d'anyi kafin yace ummana tsokana ne dukan su day murmushi a fuskokinsu, sanan fulani da d'an kame fuskar ta sanan tace kad'an yi man alfar ma d'aya Mahmud da sauri shima ya d'ago kansa ya kalle ta sanan yace" ummata kin fice hakam a gurina kiyi yarda kike so dani nid'in alfarmar kine nid'in mai biye wa Umar nin kine. cikin farin ciki da hakam umma tace" Allah ya yi maka albarka d'ana so nake kabar ta anan harta haihu, sanan insan ko ita wacece kafin munemi iyayenta. "an gama ummata yarda kike so hakam za, ayi, taci gaba da fad'in yanzun tasan Kaine mijin ta? "aa ya bata amsa, tom kad'an dakata har ta haihu danko Inga cikin yanzun kamar ya kai wata bakwai kenan, ido ya d'an waro aransa yana tuna yaushe ma akayi abin, har yakai bakwai, cikin cika umarnin uwa yace "insha Allah zanyi yarda kike so. jin tayi shiru yace tom bara na shiga fada jin bata tanka ba, yasa ya d'ago kansa cikin sa,a itama shi take kallo kansa ya dukar Yana sauraron ta danko yasan da akwai magana abakin ta, cikin muryar mai sanyi tace "sanan kuma ka d'aga mata k'afa kar ka yawan matse mata kaga yanzun cikin nata ya danyi nauyi kasan mace mai tsohon ciki tana buk'atar futu. gane mai take nufi ne yasa yad'an dukar da kansa aransa yake fad'in "yanzun har umma ta gane yana zuwa gurin hafsat? murmushi ya d'anyi sanan ya dukar da kansa k'asa kafin yace za,a kiyaye, insha Allah kafin tàce Allah ya tsare ya yi maka jagoran ci akan lamuranka ameen yace sanan ya mik'e ya nufi fada asanda ya fito ina nan ainda ya barni, cikina yabi da kallo sanan ya d'anyi murmushi mara sauti kafin ya bar falon kuyangi sai duka mar suke shiko sai murmushi kawai yake yana fitowa fadawa suka mara Masa baya.







Da misalin 5:pm motocin gidan masu tambarin gidan sarauta suka faka a babban katon garejin faka motoci na gidan, ina can daga sama ina kallon, wata kyakkyawan yarinya tsaleli Yar fara tas naga ta fito cikin d'aya daga cikin motocin na alfarma fara ce tas tamkar fulani, ga wata irin haiba da kwar jini kalan na sarauta sosai takun ta ya burgeni wasu kuyangu naga sun mara Mata baya suko dogarawa sai faman kwasar gaisuwa suke, sosai take ta fara,a da murmushi

Please Login or Register in order to submit comment