Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dage sanan aka samu sassauci dan hakam ganin lallaine baza ta yarda ba ahakam ya hak'ura, harta cemar aiyana da damar zai yi fushi tunda yana da kuyangi, cikin muryar sa wacce ta dashe da azabar ciwon mara dan idan har bai samu biyan buk'atar sa ba tom sai abun yakoma mar ciwon mara mai tsananin gaske wanda komai rashin imanin ka sai ka tausayawa masa ya kalle ta sanan yace nan daine halaliya ta idan naje wa kuyangi bazan so suhaifo man abunda bazai gaje niba dan hakam inga bai dace inje gare su ba, kawai ki amince man, aiko tako hanasa nid'in ma da bacin rai na fito shashen nata.




shiko yarima faruk mutum ne mai son wayewa da kyakkyawar mace sanan akwai sa da basar wa ga jama,a sai dài kamar d'an uwansa yake watom sarki Mahmud dan shima bayada walakanci wa al,umma sanan Yana da son jama,a ga Fara,a da son kulawa ga jama,a sai dai fa gaskiya Yana da wani hali Wanda ya zamto mar jarabbata dan gaskiya Yana da shashancin rayuwa watom yawan kula mata duk ya kyalla idon sa yaga kyakkyawa tom yakam yi amfani da kyau nasa ya ja ra,ayin yarinya sanan har sai yaga ya biya buk'atar sa sai ya daina kulaki ita fulani da kanta tasha turani gurin malamin su dan a samo mar addu,a mai sanya nutsuwa amman sai kiga ya nutsu kafin daga baya kiga ya koma yar gidan jiya.


sanan ita kankin kanta gimbiya safiyya tabbas tana da tsananin kishin mijin ta, zakiga kamar bata kula da damuwar sa tom, amman ko abinci aka kammala tana tsaye ake, yin saving nasa bacin kin gama saiki kama gabanki itako tana gadin sa sai ya kammala sai ta kira ki kikwa she kayan sai itama ta kama gaban ta, kuma karkice wata tsiyar ne zata kulla masa a a , Yana cin abinci tana daga lar waya, shine fa aikin ta, tom a irin Wannan rayuwar sarki Mahmud ke akai yanzun hakam, yau shekarar su uku da aure kuma sune shekarun sarautar sa.




Sai gimbiya batula itako ruwa ne masu aiki sannu bata son takura kuma bata iya takura kowa sanan ita komai nata akan lokaci take yinsa kamar dai yarima faruk suna girmama lokaci suna ba lokaci hak'k'in sa dan hakam ita da kuyangin ta bacuta ba cutar wa, a hakam take rayuwar ta. wannan shine irin gidan da zamu fuskan ta yanzun hakma.



Ajiyar zuciya na sauke gamida kallon iya sanan nace iya kince ada ked'in jakadiya ce tom yanzun mai ne dalilin ki na shigowa gidan yari kuma a matsayin mai dafa abinci na gidan yarin? sanan ita gimbiya safiyya har iyau tsahon zaman su bata haihuba? shiru iya tad'an yi nawani lokacin kafin tàce da sannu Zaki san dalilin hakam, lokaci na zuwa, cikin sanyin jiki iya tàce man y'ata huturu ta gaba to yanzun, mu tafi muyaba tar farali insha Allah gone zanyi maki bayani dan gane da kanbun baka da abunda yake nufi amman sai mun shiga gidan sarauta sanan,



cikin mutuwar jiki nima na tashi na gaba tar da sallar magrib sanan na zauna zaman yin lazumi wanda rabon dana yisa har na mance ranar ma. bacin na kammala na yiwanka aranar jina nake wata daban kamar baniba. hakam ma da dare, da nazo gurin kwanciya sai daren jiya ya fado man a raina wani d'an murmushi ne ya subu ce man dana tuna da muryar sa mai tsananin taushi, da hanzari na zabura tunowa da muryar yarima faruk tabbas muryar iri d'aya ce, dan aduk inda na tsinkayo muryar nan bazan mance taba, tafe k'irji na nayi wata zuciyar ta ke rayaman cewa ke hafsi mai yarima zaiyi dake bacin kinji ance acikin turawa yayi karatun sa, sanan koma ba wannan ba ked'in aiba kyakkyawa bace irin wacce yake buk'ata nan take nayi na,am da wannan zancen na zuci har barci ya kwashe ni, da farar safiya na farka cike da godiyar Allah da ya k'addaro man, zuwa gidan sarauta a yau kuma, bacin mun k'arya can saiga mota tazo kwasar mu sai agidan sarauta.


Kumujeee zuwa gidan sarauta fans........✍️


❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_





💦 HUJJATA 💦





By

HAUWA MUSA RIJAU 💫






19--20



Wani wawa keken gida naga motar ta nufa mai dogayen bishiyu da doguwar ka tanga, wani k'aton fili ne fetal wanda aka tana da dan ajiye motoci gidan cike yàke da had'ad'dun motoci na alfarma sanan ga wad'an su korayen bishiyu masu kyau da kalar bur gewa gidan gidane da ya amsa sunan sa, ko acikin gidan sarakuna tsarin gidan na daban ne, duk inda kake zaton tsari da haduwa GIDAN ya fice hakam, lallaine zancen iya hakkun da tace gidan sarauta yatara jama,a da yawan al,umma, tabbas nagaha kam dan saida zamo cikakkiyar ba k'auya ta ko wanne fanni bazance ban saba ganin jama, aba lura da inda nafito watom gidan yari, tom Amman sai dài fa da ban ban ci dan ko shi gidan yari gida ne na tarin masu laifi kowa da nasa kalar wahalar da zai riska agidan yari ga rashin yanci, nan ko sai dài ace bauta a gidan sarauta, tom gamu dai mun shigo bamu san kalar wainar da zamu toya ba agidan.




Bacin motar ta faka a ma,ajiyar ta duk muka fito dan karasa wa acan gurin shuga bar bayi na gidan dan gabatar mana da kalan aikin da zamu dosa, iya ke gaba Ina biye su binta shugaba duk sun shiga gaba, niko Ina can bayan su dan nid'in Allah baiyi ni da kazar kazar ba, idan baka san ni farin saniba sai kazata yanga ne dani gani ba wata mai kauri ba nidai gani nan dai, jiki na ne yaban ana kallo na, Aiko nan take nashiga waige2 aiko caraf ido na acikin na yarima faruk ya kafeni da dara daran idon sa masu saka y'ammata cikin rud'u da saukar da kasala Aiko da hanzari na kawar da kaina danko bazan iya cigaba da kallon sa ba.

hannu yasa ya yafito ni alamar inzo aiko caraf idon iya ya sauka a kansa adai dai sa Adda yake dago man hannun alamar nazo, cikin d'an diriri cewa naso na basar, amman iya ce tace man naje ta furta hakam ne batare da ta kallo inda nake ba, sannan ta d'ora da cewa kar ki manta ked'in matar aure ce dan hakam ki nutsu kisan me ke gaban ki tayi gaba abinta nid'in ma naso in share amman tunawa da nayi nid'in baiwa ce shiko d'an sarki ne dan hakam sai na nufesa dan amsa Kiran sa, tako nake cikin nutsuwa har na k'arasa gaban sa salla ma namar naja na tsaya, shiko ko inda nake bai kallaba sai ma wani kara kauda Kai da yayi, d'ago kaina nayi dan na kallesa saiko naga ifan sa akan wata kuyanga suke, nan nefa na tuna ashe nima d'in kuyanga ce a yanzun, tuna hakam yasa nayi saurin kaiwa kasa gamida da fad'in "ranka ya dad'e gani. yi yayi kamar bazai amsa ba, kafin can bacin ya shaki iska karan kansa ya d'ago idon sa masu matuk'ar haske da kalar zaiba yazuba su a kaina, saurin dukar da kaina nayi kafin nace na masa Kiran shugaba na, (wannan duk Yana cikin hud'u bar iya) wani murmushi ya sake mai sauti Wanda hakam sai da yasani fad'uwar gaba, dan tunawa da sautin murmushin Wanda ke amsa sunan miji agareni, tabbas wannan sautin murmushin shin naji waccen ranar, ban kara tsinke wa ba, da lamarin sai da na tsin kayo, muryar sa Yana tamba yata, sunana kafin nace mar sunana hafsat, ido yad'an bini da shi kafin yace muje daga ciki, nima shid'in nake kallo sanan na marai rai ce ido, ganin ba wasa a fuskar yasa na mara Masa baya.

wani katon phart naga ya nufa mai d'auke da tsari da kyawon kallo k'ofar shigar sa ma abun kallo ne gawa su filawoyi zagaye acan daga farko har k'arshen ginin Kai abunfa da akwai kyan kallo, tafe yake cikin yakon kasaita kalar na y'ay'an sarakai masu isa da sarautar su, bayi maza da mata sai kwasar gaisuwa suke shiko gigan naku sai faman basar wa yake, ahakam naga ya k'arasa ga wata k'ofa can nima na nufa kafin da hanzari naga an bud'e mar ita yasa kai nima na mara mar baya, wani katon basa muden mutum na hango ya nufatoni gamida da dakan wata uwar tsawa wacce ta sa nayi saurin ja da baya kafin yaci gaba da cewa"ke ina Zaki anam? kafin nace wani abu yarima ya juyo kallo d'aya yayi masa, nan take naga ya sha jinin jikin sa hakam na nufin ya gane mai kallon yake nufi da yarima yayi masa, cikin girmama naji ya soma fad'in "tuba nake yarima Allah huci zuciyar yarima sanan yaci gaba da fad'in muna yiwa bakuwar yarima barka da zuwa, hannu naga yarima ya d'aga masa kafin yaci gaba da tafiya niko na mara masa baya.

wani katon falo naga ya shiga mai matuk'ar kaya tarwa da kyau da tsari inma tsaya kwatanta maku tsarin falon 'bata lokacine kawai ku 'kiyasta yarda tsarin zai kasance.

wasu mata nagani masu dogayen riguna wasu a tsaye wasu kuma a zaune sai hidima suke a sassan falon wasu na can 'bangaren madafi wasu kuma acikin falon, wata hanya Naga ya mik'e niko sai naja can gefe na raku'be, sai kuma duk naji na takura dan bana son kallo gasu kuma duk matan sun zuba man ido, kaina a 'kasa najin gina da bangon falon ina wasa da zara zara ya tsun hannu na, can na tsinkayo muryar wata mace tana fad'in ana Kiran hafsat cike da nutsuwa ta na mik'e suko matan dake falon suka bini da ido, hanyar danaga waccen yarinyar tabi nima anam nabi, mun danyi ta Kai tacciyar tafiya kafin mu k'arasa cikin wani falon daban Wanda yasani sakin baki dan duk a tunani na bai ta'ba kawo man da akwai irin Wannan daular ba a duniya, ta'bani akayi hakam shi yasa nayi saurin dawo wa hayyacina, cikin d'an jin kunya na duk'e kaina bacin na hango idon yarima k'ur a kaina, d'an tsaki naja araina dan na fara gajiya da kallon nan, muryar sa na tsinkayo yana fad'in " baki iya gaisuwa bane? kaina na d'ago da nufin ganin wa zan gayar cikin sauri da hanzari na yi saurin dukawa gamida fad'in barka da safiya ranki ya dad'e, dan alokacin duk ba,afi karfe 11:am nasafe ba, wata kyakkyawan dattijiya ce na gani tad'an kishin gida akan wasu y'an tum tum irin nagidan sarauta ga kuyangi zagaye da ita suna mata hira, ganin yarima ya yi gyaran murya yasa duk suka mik'e, suka nufi can hanyar da muka fito, har alokacin kaina a'kasa yake nakasa jure kallon wannan kamilar dattijiyar danko tayi man kwar jini da yawa, muryar ta mai cike da nutsuwa da k'asaita na tsinkayo tana fad'in barka dài y'ata, shiru ne yad'an ratsa falon kafin na tsinkayo muryar yarima Yana cewa" ummana ga hafsat nan na za'bo ta dan ta zamo mai yimana girki Kinga iya mai tafa mana abinci har yau bata samo wacce ta yarda da tsaftar taba, aduk sanda xa,a had'a ta da mai taimaka mata, sai ta raina da tsaftar ta, shine fa nake ga kamar hafsat zata iya dan nayaba da kalar tsaftar ta. sautin murmushin dattijiyar na tsinkayo kafin naji tace " faruk kenan watom Inna fahim ceka ita wannan hafsat d'in kana son taka sance akusa da lami surink'a girki tare kenan? Kai yad'an sosa kafin yace hakam nake nufi, itama kanna nasa da tafa kafin tàce d'ana kenan kar kadamu yarda kake so hakam za,ayi yarima da kansa yace Abu amusa ai hakam ba zata sa'bu ba, takarasa maganar tana murmushi, shima murmushin ne shimfide afuskar sa idon sa akaina, d'ago kan danayi muka had'a ido ya wani kafeni da ido Yana lasan la'b'ban sa, kaina kawar gefe kafin na tsinkayo muryar umma tana fad'in" sai dài fa kasan ta zamo y'ata koba komai zan samu mai debe man kewa tunda kaga batula tana makaranta sanan kuma bana son yawan zuwa sashenka wannan dokata ce, Ina kallon sa yad'an turo baki gamida fad'in "nikam ummana waye zai dinga gyara man d'akina waye kuma zai gyara man gadona, murmushin ta na k'asaita ta saki sanan tace d'ana dan albarka ai na shaida wa aminu ya koma sashen ka ya dinga kula da gyaran d'akin ka, da sauran bukatun ka, na yau da kullum, kafar sa yakama bubbuga wa k'asa kamar wata mace yana fad'in Kai, ummana aminufa gardi ne, dikan mu saida yabamu dariya Amman sai muka murmusa, ummane ke fad'in tom kaifa wanne kalan ne kai? shima cike da murmushi ya tafi Yana fad'in umma zanzo ki ara man ita ta gyaran daki anjima.


kallon ta ta mayar akaina kafin tàce yata sunanki hafsat ? "eh ,nace da ita taci gaba da fad'in tom ga daki can ta ban garen masu dafa abinci yanzun zansa akaiki ki futa kafin anjima zangaba tar dake ga sauran kuyanki, shiru ta d'anyi kafin tàce zaki iya tafiya, wata Yar abu mai jar wuta naga ta danna nan take naga wata Yar dattijiya ta bayyana da sauri ta durkusa gamida fad'in ranki ya dad'e na amsa Kiran shugaba ta, cikin k'asaita, umma tace ki tafi da ita can sashen masu dafa abinci kibata daki mai kyau sannan ki had'a ta da lami kafin na nemesu, tom an gama ranki shi dad'e shine abunda ke tace kafin tàce man mutafi yarinya tana gaba Ina biye har tacan wani sashen, wani d'an madai daicin daki ta nuna man mai d'auke da gado da katifa da wadrop da sauran kayan amfanin yau da kullum, bacin na shiga cikin d'akin can naja na tsaya Ina Kare ma d'akin kallo cikin raina na sauke ajiyar zuciya kafin nace Allah na godema yau kuma anan k'addara ta maidoni.......✍️

❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_21--22




Tun sa,Adda na fad'a d'akin nake Kare wa d'akin kallo Ina jinjina ikon Allah wai nice yau agidan sarauta har agaban fulani uwar sarakai. kai lallai ubangiji man yasha,u ne, cikin san yina na fad'a toilet na darje jikina sosai wanda rabon da nayi kalar wannan wankar har na manta, sosai na wanke ko ina na jiki na na sanya makilin da burosh na wanke hakora na tas sanan nazo gaban diresin mirro na kalli kaina amadubi wanda shima rabon da naga kaina a madubi tun bayan da na tsinci kaina agidan yari tom acan ma ina naga wani madubi, bare na kalli kaina saiko idan aiki yabi dani tacan gefen gilas d'in dake cikin ma,aikatar, ido na mayar akan miron Ina kare wa kaina kallo, tabbas nid'in inada kyau da kyan tsari nid'in doguwa ce dai dai sanan inada hips ga dimple dina dake lotsawa koda magana nake sanan inada manyan dara daran ido masu kalar madara, nid'in farace tas mai kalar farin Yan Nigeria masha Allah ga siririn dogon hancin na da yayi wa madai dai ciuar fuskata kawanya, ya k'ara fidda man da zaga yayyen baki na nid'in nasan inada kyau daidai misali duk inda za,a ambaci kyawawa nasan tilas zanshiga ciki, ajiyar zuciya na sauke gamida hamdala ga Allah kafin na k'arasa gaban wadrop na d'auko wata doguwar jar riga mai ado da siton wacce keda bu d'ad'd'en hannaye sosai rigar ta kar'beni galen ta nasa na yane jikina da shi sanan nagabatar da sallar, a zuhur dai dai na kammala naji anturo k'ofar. ido nabi ganbun d'akin dashi, wannan dattijiyar ce wacce aka had'a mu da ita ajiya, "masha Allah shine furucin ta a kaina taci gaba da fad'in tabbas tafiyar mu zata zo d'aya dake y'ata danna ga alamar ked'in mai tsafta ce, taso kiga y'ata aikin shigo akan sa,a a wannan gidan fulani da kanta ta amince dake amatsaya ta amin tacciya har ta amince dake akan kizamo amai dafa wa mai martaba abinci lallaine ked'in mai sa,ace cikin sanyi na na mik'e gamida "fad'in tom baba mutafi tana gaba Ina biye duk raina tunanin ta inda zanga iya nake tafe muke baba jummai sai faman zance take niko hankali na nacan ga iya, ababban falon ta umarceni da na zauna kafin amana iso ga fulani, jakadiya ce take shaida Mana cewa sarki ya kawowa fulani ziyara dan hakam mujira, mun kai kimanin 30: minutes kafin abamu umarnin k'arasa wa acan falon fulani, wani maya taccen k'amshine ya ziyarci hancina kafin wata irin fad'uwar gaba ta riskeni tunawa da wannan k'amshin mutumin dake amsa sunan miji agare ni, da hanzari na d'ago Kai jin furucin dake yawo akunne na "ke kinutsu shine abunda ya furta, yarima faruk idona ya gane man zaune agefen fulani, yakafe ni da shu,umin kallon nan nan nasa na jaraba, boyayyar ajiyar zuciya na sauke dan nagane inda kamshin ya fito watom ga yarima faruk,


Fulani ne ta d'ago kanta ya sauke idon ta akaina kafin tace cikin muryar nan tata na k'asaita wacce yarima ya gado agareta "ki nutsu kibani hankalin nan hafsat watom inason kutafi acan phart din mai martaba tare da ke da kande kuyi masu hidima acan nari gada yasan ko wacce kande dan tasan takan girki sosai dan hakam ke zaki zamo mai taimakon ta girki da wanke wanke da sauran aikin da baza, rasa ba, shiru tayi na d'an lokaci kafin taci gaba da fad'in sanan kuma na tsani cin Amana karki yarda nakamaki da wannan halin tabbas idan kin kiyaye zamu zauna lafiya idanko kinki zaki d'an dani azaba agidan yari. saida naji fad'uwar gaba dan tunawa da gidan yarin, muryar fulani ce ta maido ni hankali na, jinayi tana fad'in keko jummai anan zaki cigaba da aikin dafa abincin zaku iya tafiya, yarima faruk ne ya ka tseta da fad'in dan Allah ummana kibar hafsa anan tayi aikin anan gurin ki, shiru tayi ganin, hakam ne jakadiya tace xaku iya tafiya mai girma fulani ta sallame ku, cikin hanzari baba jummai ta mik'e sanan tace man mutafi na sada ki da gidan sarki d'in, gimbiya safiyya uwar gida agurin sarki Mahmud mai dogon zango tana can tana jira, cike da sauri muka far sashen fulani wani babban titi muka hau kafin mu d'anyi tafiya matsai kaiciya sanan muka riski wani katon gida mai d'auke da wata kafceciyar fada wacce tatara taron mutane sosai ashe sashen fulani wasa ne anan ne Al, umman suke awata yar, siririyar hanya muka nufa wacce muka d'anyi tafiya mai dan tazara kafin mu isa acan wata k'ofa mai tarin glas da wani kalan kafet mai garai garai da tsantsar kyau da sha,awar kallo acan nasake baki gurin kallon ban ankara ba na tsinkayo muryar jummai tana fad'in ke yar nan kiyi da jiki inafa da aiki sosai da d'an hanzari na cimma ta kafin taci gaba da fad'in ki daina nawa mu k'arasa ciki wani k'aton falon muka riska mai kyau da tsari idan nace kyau tom kunsan abunda ake nufi da kyau dan inma fad'a maku tsari da haduwar falon ma k'au yan cine (dan hakam kumuje zuwa, labari fans) acan gefe na dan dosana kafin abamu daman zama wata farar matace nagani acan gefe itace ta umarce mu da zama kafin ta fad'a wani sashen can naga tabi yàr kofa sanan ta 'bullo kuma ta wata k'ofar da ban taai second uku da zama kafin tàce wacce acikin ku za,tayi aiki anan da sauri naga baba jummai ta nuna ni ido matar takafe ni dasu kafin tàce taso mutafi gimbiya safiyya ta umar ceni da na kaita sashen masu dafuwar abinci dan hakam tashi mutafi.

angama jakadiya ta Amana agurin gimbiya safiyya cike da kulawa da mutumci baba jummai ta bar sashen niko wani ban garen aka nufa dani katon kicin ne agurin daga can gefen sa akwai d'a kuna guda biyu ajere d'aya daga cikin d'akin naga ta kwan kwasa kafin naci ki ya fito wani mugun farin ciki naji ya ziyar ceni ganin iya ce ta fito daga d'akin itama iya da murmushi d'auke a fuskar ta ta rik'e man hannu cikin d'okin ganin ta na fad'a jikin ta, ita wannan matar da ta rakoni murmushi ne take kafin tabar gurin. y'ata iya tàce dani tana cigaba da murmushi sanan taci gaba da fad'in tunfa d'azun nake ta adduar Allah yasa a maido ki nan muyi aiki atare" cikin doki nima nace wlh tun a dazun iya nima nake ta d'okin ganin ki, tom mutafi kichin zan dafa wa mai martaba na,a na,a da green tea yanzun mutafi kiga acan kichin d'in wasu kalan na urori ne masu kalan wayewa da iyawa dan wad'annan idan baka iya ba sai su iyama Ina iya cewa wad'annan na urorin sai agidan masu da shi ko yan gata, Danni dai aiya zamana ban ta'ba ganin suba, iya ce tace man yar nan matso kusa ki koyi aiki ban son kigaza ad'akin miji insha Allah, tom nace da ita wasu gwan gwani naga iya ta d'auko sanan ta wanke towa tas ta d'ora akan na urar girki data jona ruwa naga ta zuba sanan ta zuba wasu kalan da kakkun garin ganye koraye baifi mintoci biyar ba naga ta tace su awwni gurin daban sanan ta d'auko wani flacks mai kyau ta zuba ta fa sasshen ruwan tea d'in aciki kafin ta d'ora akan wani tire mai kyau da kyalli duk Ina gefe ina kallon ta sanan ta mik'o man kafin tace mutafi itace agaba niko Ina baya can wata kalar kofa mai ruwan zaiba muka nufa muna tafiya kafar mu na lutsewa acikin wani lallausan kafet mai dadin taka har acan cikin wani katon falo mai kyau da tsari sanan muka dan jira sakamakon wani dan danja da naga iya ta danna, can aka mana iso acikin dan wani ma dài dài cin falo muka shiga, acan gefe da akwai wani karamin dining room. a saman table d'in na d'ora tiren najuyo da nufin inbar gurin sautin wata irin murya ce ta dake ni wacce nake zaton isowarta kenan agun, cikin muryar mai amo take ceman idan kintafi uwarki ce zata fita mar tea d'in ta zubamar? cikin wani facin rai wanda bansan inada shiba na juyo da nufin mayar da martani amman Ina tuni iya taka tse mani hanzari gurin cewa tuba muke ranki yadade sarauniyar kyau gimbiyar gimbiyoyi na farko kuma na karshe agurin sarki Mahmud Allah yaja zamanin ki, da wani murmushi tayi far da ido kafin tàce taci darajar ki da sai nasa ankoyar da ita yarda ake girmama mutane da sauri iya tàce tuba take kuma godiya take, cikin sanyin jiki na k'arasa gurin dining table d'in na ja na tsaya Ina jiran mai Martaba ya fito dan in cika umarnin wannan matar da ke amsa suna gimbiya safiyya wacce dagani itad'in masi faffiyace.



Na Kai 10: minute a tsaye kafin naji wani shu,umin k'amshin ne

Please Login or Register in order to submit comment