Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kanina hafis ya jefeni a gefen ido har saida guri yayi shaida, naci kuka sosai har naje na shaida wa umman sa sai koroni tayi gamida cewa dama ya cire man idon ai nayi gadon makanta sai na rinka yawo da sanda niko jin wannan furucin sai na ce ALLAH ya tsare ni insha Allah sai dài shi hafis ya zamo makaho ai ina fad'a maki iya aranar saiga babur ya kad'e hafiz Nan take idon sa d'aya ta tsi yaye, jim na d'anyi dan tuna wa da kalar ukubar da naci koma nace nake kanci, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo man hannaye na nasa na share kafin naci ga ba da cewa iya wannan ranar ita ce silar lalace war rayuwa ta itace silar rabani da ragowar farin cikin da yarage man a wannan ranar ne nakara yawan makiya a duniyar nan wani hawaye ne amai zafi yasake zubo man take bakina ya soma daci kukane yaci karfina iya da kanta ta share man hawaye na sanan tace man na bari har abun ya fad'a man sai inci gaba wannan kenan......✍️

🌀HUJJATA🌀





BY


HAUWA MUSA RIJAU





Chapter. 9--10




*AM SORRY MASOYA NA ZAKUGA NASA JARUMAH NAYI POSTING AMMA HUJJATA NE NAYI KUSKURE NE INA FATAN ZAKU GANE INA ALFAHARI DAKU MASOYA NA*



Da sauri iya ta tsiya yo man ruwa ad'an karamin cup na amsa ba musu na sha dan alokacin wani kalan zafi zuciyata take man ganin lokacin sallah tayi ne iya tace man mutafi mu sauke farali sanan bacin mun gabatar da zuhur sai iya ta kawo man wata da mammiyar fura da taji kindirmo tasha k'ank'ara tayi sanyi sosai tace man ungo wannan yata Kisha dan nasan wayewar garin yau ko mai bakici ba, sosai na kar'bi furan nasha sanan na d'an Sami nutsuwa kafin naci gaba iya tabini da ido sanan tace y'ata sai mai ya faru?




Cikin sanyin jiki da sanyin murya naci haba, tunda ga waccen ranar sai k'iyayaya mai karfi wacce ta lunka nacan baya ta k'ara hau hawa ga ahlina ba Mai son Koda ganina bare jin murya ta har mahai fina wace kalar tsana suke man wacce ban ta'ba ganin anyi wa wani irin ta ba, can dama inada wani hali niko wanda ban son sa sai dài ba yarda na iya tunda ance hali zanen dutse wannan halin shine nid'in banda rashin kunya ga babba kuma ban iya musu da manya ba, Amma fa sai dài idan naga za a cutar dani nakan janye jiki na da Kai sanan kuma idan yaro ne sa,a ta nakan rama abunda yayi man wannan duk sun kasance halina ne azamanin kuruciya. tom hakam yasa nake da yawan bakin jini ga iyayen yara, kowa fa nagidan mu ya fita haraka ta musamman iya abu dan acewarta gara ta ga ranar mutuwar ta ta taganni akusa da ita, kasan cewar yaranta biyar mata sai akan hafiz ta fara samun namiji kuma yanzun na zamo silar makan tar sa, ahakam nake rayuwa ba ruwan baffa na dani ba mai bani abinci agidan dan acewar su baza su zauna suna dafa man abinci Ina hadiya ba sanan in dawo Ina illata masu yara, wannan duk bai dameni ba dan na kanje kofar hasana mai abinci inyi mata wanke2 tabani kanzon shin kafa ta sammani mai inci, sanan kuma babar ummi duk abunda taraba takan sammani, duk da kasancewar su mad'in talakawa ne aman bakamar mahai fina ba, niduk ba abun da yafi d'aga man hankali irin makantar hafiz, aduk sanda na kalli yaron tausayin sa nakeji, shiko kullum sai caa yake sai yaga baya na, tom ahaka dai nake rayuwa, ba Wanda yasan cina da sutura ta kowa baida mu da Sha anina ba, sannu sannu har ta Kai ko gidan na shigo da har karamin yaro ce man yake muguwa mai bak'in hali, duk yawan cin su kannai nane, ganin hakam niko abun ka da kuruciya sai na tsiri ramawa duk wanda yace man mai bak'in hali nan take zance mar bak'in hali ya dauwa ma akan ka, suko iyayen su sukama ni suta jifga wani sa,ilin ma manyan yannin mu su ake sawa suyi ta jifga ta Ina ihu ba mai cetona sai, Allah saiko hasana ko babar ummi kasancewar duk gidan mu d'aya saidai kowa da nasa phart d'in amam munfi makwaf taka da su unmi hakam ne yasa shaku wa mai karfi ta shiga tsakanina da ummi sosai , haka ma babarsu ummi ta d'auke ni tamkar yarta nima akai akai nakan je gidansu ko nace phart din su dan hakam duk lokacin da nayi laifi dazarar nasamu hanyar tsira tom gidan su ummi zan shiga na buya. wata rana da ta shigo cikin tarihin rayuwa ta wacce bazan manta ba, ranar mun taso makaranta nida ummi alokacin muna pramary 6 duk agajiye muke kasan cewar aranar class d'in mu munyi p, e dik mungaji ga daman Koda na bar gida ko ruwa ban shaba kuma da man ba mai bani kud'in tara, sai dài nayi aikatau, d'an abinda za,a sammin ba wani abunda zai wada ceni bane tunda mutane ma son kansu yayi yawa, to aranar ma mun makara dan na tsaya yiwa anty ma,u wanki kuma Yaya auwalu yasa nayi masa jidar ruwa arijiyar dake k'ofar gidan mu, dan hakam amakare naje makaran tar ga yunwa ga gajiya tom ahakam muka taso duk na gaji sosai, Ina karasowa dakin ummata na shiga Wanda tun bayar rasuwar ta shi yazamo ma kwafin nawa dan ba wanda ya shige sa, aciki nake rayuwa ta bacin ita mariyar tawa tace tagaji da wahalar banza akai na, bacin nacire uniform dina sai nafito tsakar gidan inana zare ido dan tunanin ta Ina abinci zai fullo man? Ina cikin wannan tunanin na tsinkayo muryar ya sani yan ceman ke hafsi maza ki d'auki wancan boket d'in kidebo man ruwa nayi wanka sanan ki tara man wasu a banbun can zan wanke mashin dina ne, cike da tsantsar tausayawa kai nace please yaya kabarni na d'an samu abunda zan sanya bakina, rabon da naci wani abinci tinfa jiya da dare ko shima babar ummi ta sammun....wani mugun mari yasa kar man a kumatu saida naga gifta war taurari, cikin matsa nan cin kuka nace mai nayi maka Yaya ko dan dai an ganni marai niya sai ata cuta ta, da wani kalan hanzari umman hamza ta fito daki sai cewa dake rufa makanka asiri wannan da kake gani anno ba ce dan hakam ka iya kanka da ita kar ta janyo man asara, kallo na bita da shi cike da wani kalan bacin rai da jin furucin ta akai na. ban tanka ba ban kuma tafi ba, mariya ce wacce muke sa,a d'aya da ita takaraso gaba na cike da mugun izgili ta sharara man mari gamida fad'in shegiya muguwa wlh ahir dinki damu kuma insha Allah sai waccen rijiyar ta zamo ajalinki tunda kinzamo muna annoba agida, da mugun kallo nabita sanan nace dik abunda zaku fad'a kaina Allah ya fiku kuma da izinin Allah sai dài ke rijiyar ta zamo ajalin ba dai niba, Aiko da hanzari ummanta ta nufato ni da nufin ta zaneni ,rige rigen gudu muke dani da mariya dan azatom ta itad'in zata daka, Aiko a bisa k'addara ta ruga da gudu dan neman hanyar tsira Aiko garin neman hanyar gudu sai ko tafice da gudu ta wajen gidan, niko d'akina na nufa da mugun gudu dan neman mafaka,Ina can k'uryar d'akin sai jin nayi an zuba wani uban ihu, sai karar afka war mariya rijiya muka jiyo. wani kalan sheshshekar kuka ne yazo man nan take itama iya zufa ya karyo mata duk da cewa sa an sanyi ne, cike da ruwan hawaye a fuskata naci gaba, aranar sai da naji na tsani kaina ban ta'ba tsamma nin illar furuci na ya Kai haka ba, babar mariya ko duk ta rud'e sai surutai take aiko nan take aka ciro mariya ta zamo gawa, duk nabi na tsure Ina sauraron abunda zai biyo baya, har akayi addu,ar sati bawanda ya sake shiga hurumina agidan dani da babu duk d'ayane nima da kaina haushin kaina nakeji dan banga dalilin biye wa mariya ba, Ina cikin wannan tininin ne na tsinkayo muryar umman hamza ta na fad'in lallaine saika sauwake man danko bazan iya zama da annoba agida daya ba, idanko kaki tom tilas ka za'ba koni ko ita, cikin dakiya da k'arfin zuciya irin na uban da ke boye son d'ansa aransa Abba ya kirani bacin naje yake shaida man na had'a inawa inawa na bar masa gidan sa, cike da kuka mai tsuma zuciya na bar masa gidan sa dan Allah yagani Ina k'aunar ahalina duk da kalan tsanar da nake fuskanta atare dasu, tafe nake da kaya na Ina gaf da barin gidan na tsinkayo muryar ummi tana Kira na tsayawa nayi cak batare da na juya ba, cike da tsagwàron tausayi tarike man hannu batare da tace dani komai ba, tafara tafiya dani da nufin komawa gidan dani, gane abunda take nufi ne yasa na fisge hannu na gamida cewa kibarni ummi meye amfa nin irin Wannan rayuwar tawane? saurin rufe man baki tayi, sanan tace man am sorry my lovely sister dan Allah kizo mi tafi gidan mu wani ba wa Yan uwan kiba, kuma insha Allah nayiwa kaina alk'awarin zanyi k'ok'arin ganin farin cikin ki Koda hakam na nufin San hadu da ajalina ne, jin furucin ta yasa nizubar da wasu kalan hawaye masu zafi, na bi bayanta dan cika burin ta, bacin mun shiga gidan nasu abban ta da umman ta suka soma yi man nasiha mai ratsa zuciya sosai wadda tasani zubar da hawaye nayi masu alk'awarin in Sha Allah zan daina biye masu zanbar shiga hurumin su.





suko anasu ban garen kullum burin su su 'kun tata man daga mai duka na in mun had'e a hanya sai mai nemar na kastani, aranar ma anty ma,u ruwan batur tasamo dan ta watsa man afuska kamar ummi tasani tace man da k'arfi maza kauce gatanan tafe zata ingi jeki ganin ta nu fato ni da mugun gudu, Aiko da hanzari na duk'e ruwan suka watsu k'asa saiko k'asa ta Kama ta farfasa, tunda ganan na soma Shan jinin jikina dasu.


awata rana Ina k'ofar hasana Ina karkaran kanzo saiko ga Anty ma,u munyi arba da ita tazo sayen abinci gurin hasana daga mai zaya ce man sai cewa tayi man kedai akwai asararriya anan ta kaiman zuguri kafin tàce niko burina a yanzun in ganki da d'an shege kin giya a bayan ki, shine kawai zai wanke man zuciya ta daga abuda kika yi wa kanina hafiz. saijin muryar ya sani nayi abaya na Yana fad'in niko narison naga tana yawon sata, gida gida Kinga da zarar ankama ki shine zaisa nayi farin ciki, kuka na fashe dashi kafin nace nabarku da Allah, da sannu abunku zai koma maku, insha Allah, daga hakam nabar gidan ma na koma sashen dana ke watom sashen su ummi, dikfa da hakam ban kullaci kowa araina ba musamman abbana cike nake da d'okin ganin sa, adik ranar da nayi sa ar ganin sa, aranar dokine fall raina, kwana kad'an da wannan sa,insa da yam uwana sai labari ya riskeni nacewa ankama Yaya sani tumu dumu yasaci man man kud'ad'e, magana har tayi nisa cakar aka samu aka rufe maganar bacin an mayar da kud'in an gama wannan da y'an watanni saiga anty ma,u itama tayi abun kunya wanda ake ta rad'e rad'en mijin hasana mai abinci shi yayi mata shi, tun awaccen ranar itama hasanar takama kanta dani, bata ko son in je kofarta ganin hakam ne yasa nima na janye mata.



sannun sannu har mun kusa kammala karamar sakan dari watom j secondary School kenan ahakam rayuwa take tafi mana badadi danko anam bawai wani dad'i bane nakeji sai dài nakam ji dad'in inna tuna karatun da nake kanyi boko da arabi, asa ilin da rayuwa ta ta barbare man asanda muka shiga ss1 alokacinne, Ashe a waccen ranar da muka sami sabani da y'an uwana har sukaman mugun furuci niko nace akansu zai koma, tom Ashe hasana mai abinci ta kwashe dik yarda mikayi, shine fa suka Yankee shawara kashe ni ta hanyar sawa abinci huga dan naci na mutu, da matar yayan su ummi aka had'a baki gurin saman guba ga abinci abisa kuskure ummi ta dawo tana Jin yinwa kawai sai daikar abincin tayi ta hauci sai bacin dataga ci ne taje Shan ruwa taji ,murya k'asa k'asa adakin jimmai matar yayan ta, ana cewa kar kiji komai ainan da minti 30 zata sheka barzahu d'an nasa was abincin guba kuma nasan kwanon tane aciki ake saka mata a binci ai kawai kunemi abun sadaka dan koni ta isheni.




Cike da hanzari ummi ta koma marafi ganin abincin kwano na ne ta d'au ko taci sai ta hau godiyar Allah da Allah yasa banice naciba sai tayi hanzari ta fad'a d'aki ta tauki biro da takarda tayi rubutu akai ta saman a cikin jaka ta ta islamiyya ta na kammala wa tace ga garinku nan Allah sarki ummi masoyiya ta gaskiya wacce ninasan har abadan zai yi wuya nasamu wacce zata maye mani gurbin ta wani kuka ne mai karfi yazo man cikin sheshshekar kuka nake fad'in alkhairan ki subiki ummi......✍️

💦 HUJJATA 💦







By.



HAUWA MUSA RIJAU




CHAPTER

11--12







Kuka nake sosai dan sai nake ga kamar yanzun ne ummi ta rasu mutuwar tata ta dawo man sabuwa fil, nakai wani lokacin Ina darzar kuka kafin iya ta dakatar dani ta hanyar rarrashi tace man y'ata kiyi hak'uri ita kanta ahalin yanzun muna kyaukya ta mata zaton samun rahamar ubangiji, dan hakam kiyi hak'uri karkija wa kanki wani ciwon kuma, ajiyar zuciya na sauke sanan nayi d'an jim kafin naci gaba da cewa.






tun sa,adda ummi ta shiga d'akin sai bata fito ba ga babarta najiran ta dan zata aike ta. niko alokacin ban karaso ba dan na d'an tsaya karasa wani rubutun da na tabbatar koda naje gida ba lallaine na samu sawar k'arasa shiba, dan hakam na tsaya k'arasa wa, acan kuma gida jin shirun yayi yawa hakam yasa babar ummi ta shiga d'akin namu dan ganin mai ya tsayar da ummi ba tazo kar'ban sakon nata ba. cikin muryar ta mai sauri take kiran ummina!! ummi!!! ta k'arasa Kiran sunan tana mai yaye labulen, turus taja ta tsaya sakamakon hango ummi ta tayi dun 'kule acan k'uryar d'akin ta cure guri d'aya idon ta kafe asama kanta da kafar ta sun had'e guri d'aya alamar ciwon ciki take, da hanzari mama ta k'arasa ciki tana fad'in ni AI mai nake shirin gani hakam? da sauri ta k'arasa gaban ummi tana girgiza ta, ganin tana ta'ba ta k'arasa fad'a wa akan hannun mama, kamar anturo ta. da hanzari mama ta k'ara girgiza ta amman ina bata motsi sai ma wani haske da takara nan take mama ta fahimci ummi bata da rai wani uban ihu mama ta rusa sanan ta soma Kiran innalilahi wa Inna ilaihi raji,un ummi mi nake Shirin gani hakam? nan take jama,ar gidan suka hallara kowa sai tofa albarkacin bakin sa yake sai cewa suke tom dama ai sun san hakam zata kasance, taya zata dauko annoba ta aje gidan ta sanan tace zataga yarda take so, cike da k'arfin zuciya mama tàce dan Allah kubarni inji da rashin y'ata karku zo ku canja man tunani cikin sanyin jiki duk suka soma koke koke a dai-dai sanda na shigo gidan na tsinkayo muryar jummai matar yayan ummi tana fad'in tabbas ni naji sa,adda hafsi ke cewa ummi lallaine inhar tace bazata bar mata idrisu dan gidan alh mamman ta aura ba itako sai dài gawarta ba dai ita d'in ba, cikin muryar kuka ta Kare fashe wa da sabon kuka na muna furci sanan taci gaba da cewa inajin ummi tana fad'in haba hafsi ki tuna kalan halaccin da nayi maki sanan kice ni Zaki yi wa hakam? dan Allah hafsi na kibarni da idirisu sai cewa hafsi tayi tinda ma abunki na kafiya ne tom yau d'innan bazaki kwana duniya ba, tana kawo wa nan azancen ta sai ta aza hannun ta saman kanta ta rafsa wani uba uban ihu gamida fad'in hafsi Allah ya tsine maki albarka, ace duk kusancin ki da ummi duk halaccin ummi akanki sai da kika aika ta mata mugun furuci. tana kuka tana fad'in Allah sarki ummi Allah yaji k'anki, jin furucin Allah yaji k'anki shi yasa nayi saurin karasowa gidan sanan nakama kafar mama, cikin kuka nace mama dan Allah kar kice man babu ummi 'kwakwal wata bazata iya daukar rashin ummi ba dan Allah mama me nake jin jummai na fad'a akan Yar uwata, cikin halin bacin rai mama ta hankad'ani na fad'i ta shige d'akin da gawar ummi take batare da ta tanka niba., kuka nake sosai Ina fad'in mutuwa mai isa kika man hakam mai isa baki d'au keni ba, cikin k'arfin kuka nace ummi mai isa kika tafi kika barni. bawan da ya kulani duk gidan saima ceman suke muna fuka duk wannan kukan muna furcine wacce tayi sanadin mituwar uwar da ta haifeta tom waye zata ragawa.






Sai sanan su baba suka k'araso aka shirya ummi muna kallo aka tafi da ita gidan ta na gaskiya nayi kuka iya kuka nayi bakin cikin mutuwar ummi kamar raina zaifita amman mutanen nan saida suka yi sanadin tunzura mama har ta fara tsana ta baba shima kansa bai wani kula da lamari naba har tsawon sati d'aya Ina nan dai ba mai kulani ba mai kallon inda nake ga bakar yunwa ga rashin dad'in zuciya na rashin masoyiya dik na wani kalan ya mutse wa, ana hakam saiga yaya habu yayan ummi watom mijin jummai shida kanin sa ibro shima Yana da mata sai dài shi matar sa bata da matsala bana mance sa adda mukaje makarantar islamiyya malamin mu yakoya mana wankan janaba, da mikazo gurin matar yaya ibro itace tamana bayani yarda zamu fahimta, sanan ko alokacin da muka fara Al,adar mu na mata, itace ta koyar damu yarda zamuyi har muka fahimta, tom....muryar Yaya habu ne ta katse man tunani na ceman yayi inbashi hankali na, cikin nutsuwa nabi shi da kallo sanan nace inajin ka Yaya.






ido ya kafe ni dasu muskar sa murtuk alamar ba wasa yace man mai ya had'aki da ummi har kika yi mata mugun furuci? cikin muryar kuka da ya taso man nace Yaya wlh Allah ba komai tsakanina da ummi sai alkhairi tunda nake da ummi ban ta'ba samun matsal da ita ba bare har ta kai dana yi mata wani furucin akanta....ban k'arasa rufe baikina ba yaya habu ya watsa man mari wanda saida ganina ya d'auke sai cewa yake zaki fad'a ko ba zaki fad'a ba, ana hakam saiga mudi mijin lantana shima d'annan cikin gidan ne , da ga zuwar sa sai ya hauni da duka kota Ina tun Ina ihu har nakai ko motsi bana iyawa Amman bakina bai mutu ba sai cewa nake wlh ni banyi ma ummi furucin komai ba, daga karshe nace idan har nayi mata furucin Allah kar yabani ikon ganin daren yau idan ko har banyi mata wannan furucinba tom Allah yabi man bashina akan dik Wanda ya zalinceni sanan daga hakam sai ban sake sanin inda kaina yake ba tsawon wani dogon lokaci, mama ce ta watsa man ruwa masu mugun sanyi da shiga jiki da wani mugun zabura na farka, amman Ina farkowa sai cinkaro nayi duk gidan namu ya hargitse kowa sai faman koke koke ake daga karshe saiga babban d'an gurin mudi da wani mutum mai d'auke da wata zafgegiyar bulala da manyan kaya ajikin sa.







cikin d'akin da nake ya shigo ido yakafe ni dasu sanan ya maida kallon sa ga ya,u d'an gidan mudi kafin yace Wannan d'in itace?, eh ya,u yaba shi amsa sanan mutumin yace yanzun kubata abinci taci sai asan abinyi, cike da tsantsar mamaki mutumin yake kallona sanan yace ke yanzun ace duk girman gidannan kece kika zamo annoba? yanzun ance mutum uku kikayi wa sana din barin duniya sanan kin zamo silar lalace war wasu sanan kin zamo silar halakar wasu cikin halain rashin fahimta na dafe kirjina sanan nace wa kuma na kashe yanzun muryar mama na tsinkayo tana fad'in mudi kece kika zamo silar mutuwarsa ayau.....✍️

❄️ HUJJATA ❄️







By

HAUWA MUSA RIJAU





CHAPTER 13--14


Bissi millahirrah manirra him.




Allahumma salli ala Muhammadun wa ala ahli wasallim 💓











ILOVE YOU ALL MY LOVERS








Kallo nabi iya da shi kafin nace iya bara muyi sallah, Kinga yanzun lokaci na gudu kamar yanzun nefa mukayi sallar zuhur Amman ga shi yanzun har la,asar ta gaba to. cike da duban k'ofa iya tace sosai ma aike dai yar nan Allah dai yasa mugama lafiya da wannan duniyar, shine fa zakiga nan take muna cin ye lokacin mu da Allah subhanahu wata ala ya bamu, bara nima na d'auro alwala sai muyi atare kinga ma karu da juna. tom nace da ita sanan nima na mik'e na d'auro alwala muka yi jam,I tare da iya, bacin mun idar na koma can najin gina da bangon sanan na bi iya da kallo itama d'in ni take kallo, naci gaba da fad'in,










Wata kalar zabura nayi gamida kallon mama sanan na dafe k'irji na cikin in,in,niya nace ni... ban...kashe...kowa...ba..wlh cikin sheshshekar kuka naci gaba da fad'in nidai dan Allah ku kashe ni na futa kuma kufuta meye amfanin rayuwata ba ummi acikin ta dan Allah kuka sheni na k'arasa fad'in Ina mai rushewa da kuka, cikin tsantsar tausayi wannan mutumin mai babban rigar yace dan Allah ku duba lamarin wannan yarinyar ku barta na lura cewa ita d'in k'addara ce ke bibiyar rayuwar ta, idan kunyi duba zuwa ahekarun ta wannan ai bata gaza Sha hud'u ba ko sha biyar, dan hakam kuyi hak'uri da ita sai kudai na shiga hurumin ta, kunga sai a zauna lafiya. da sauri ya,u ya tari num fashin sa da fad'ar mudai dan Allah baba ka tai maka karaba mi da wannan annobar, ko wlh muzamo ajalinta, ido na kafesa da shi arai na nake tuna ranar da ya,u yarik'e wa ummi hannu yana fad'in son ta yake babar ta takama fad'a har take gargadin mu da kar mu yarda ana rike mana hannu tàce mana idan namiji yarik'e wa mace hannu indai shid'in ba d'an uwanta bane shi tom d'an iska ne kuma lallaine Allah zai konasa amman yau harni yake Kira da annoba, ganin nakafe sa da kallo sai yada baya gamida fad'in dallah malama ki daina man irin Wannan kallon, aikin ga dai ban tanka kiba tom nima kidaina kallona dan Allah karki k'ullaceni nima ki zamo sana din barina duniya ehe aikin dai ga da wannan tsohon nake. baki na bud'e da nufin nabasa amsa. sai kawai na hango ya,u ya bud'a da gudu acan na tsinkayo muryar sa Yana fad'in al,kur, an bazan tsaya kice kece ajalina ba kiman asarar kaina kawai baba thoho ya d'auki mataki akanki ko kije can keda Allah, daga nan ban sake jin duriyar sa ba, mama itama tabini da wani kalar kallo wanda azahirin sa, kallo ne na sai naga k'arshe ki, amman acikin kwayar idon ta nake hango tsantsar tausayi na aciki kwafa tayi sanan ta kalli baba tsoho kafin tace masa nikam gara karaba mu da wannan annobar tin kan takarar damu sanan itama ta ficewar ta, shiru mikayi na d'an lokaci kafin baba tsoho yace y'ata waye mahaifin ki? cikin sanyin murya gamida ajiyar zuciya nace yana can cikin gida can yanisa sanan yace man muje in gansa, gaba na wuce shima ya maraman baya agefen katangar gidan na hangosa ya kishin gida ya kunna radio yana sauraro, sai ga ninmu sukayi ram gam ramgam nida baba dattijo cikin sakin fuska baba dattijo yamik'a wa baba hannu sukayi musa biha, sanan ya nunani gamida cewa "Ina fata kaine mahaifin wannan? kallo

Please Login or Register in order to submit comment