Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsantsar mamaki gby batula da barisster zainab suka shiga tafa hannu niko wani kalan kuka ne yazo man, amman sai na had'e kukan, d'akin nawa nakoma na haye gadon na kwanta ruf da ciki ina zullamin rayuwa.




shima yarima shiru yayi kafin shugaban gidan yarin yazo yatafi dasu jakadiya gamida bada umarnin ayi masu horo mai tsanani,
gby ba tula tare da barisster zainab suka shigo dakin suka soma bani baki gamida kwantar man da zuciya shima yarima dakin sa ya nufa yasoma nazarin rayuwa.



Suko su sarki mahmud suna saudiya acan babban asibitin kasar sosai sun sami kulawa su duka. ita fulani hawan jinine matsalar ta, shiko sarki mahmud a tsaran bayan sa wu'kar ta huda sa anan akayi masa aiki, ita dai kam gby safiya tafi kowa rauni danko ita hanjin ta ya hud'e sosai ake 'ko'karin ganin an shawo kan matsalar ta.






a nan gida nigeria ko an rad'a wa yara suna saifullah da saifuddin muna kiran su deen da saif sosai nake cikin damuwa danko zuwa yanzun nasan waye mijina kuma har ga Allah inason sa danko inna tuna irin yarda ya aureni batare da yasan koni d'in wace ba, sanan kuma bai kyamace niba, tilas zanso sa araina, yau kimanin wata biyu kenan da faruwar wannan lamarin yarana sun soma wayau sai tsantsar kamar su da mahaifin su ke kara fitowa niko a yanzun nasoma gogewa sosai jinin sarauta ya soma ratsani idan ka sanni ada a yanzun baza kace nice ba sosai jikina yayi fresh. lokaci zuwa lokaci muna gaisa wa da fulani danko yanzun sosai sun samu lafiya, cike nake da dokin ganin fulani , iyace yanzun ke kula da yaran harma dani kaina sai faman gyarani take sosai ta bani wannan tsumin ta had'o man wannan had'in na kayan frut da sauran kayan gyara har hadin kaza take man tun ban maida hankalin naci har nasoma ci da kaina nasha ko na shanye a hakam dai muke rayuwa, kullum sai fulani tayi fama dani gurin goyon yaran danko nidai bana son goyo amman ita ko, iya sai ca take idan nagoya su zasu fijin dumin jikina, duk da cewa a gidan har rige rigen goyon su ake kuyangin gidan dan ma gimbiya batula bata barin ana dogon yawo dasu.





gaskiya a yanzun bana da matsalar da ta fice son ganin fulani acan kasan raina ko harda mijina ina kewar sa.




yauma kamar kullum kwance nake akan tafkeken gadon gimbiya batula, itako tana can tana wa deen wasa shiko sai faman wangale baki yake, wayar ta dake kusa dani tayi 'kara, alamar ana kira, na d'aga na kara a kunne na, zazza'kar muryar sarki mahmud ne ta doken a dodon kunnena, yana doka sallama, cikin wani yanayi da naji ya ratsani na amsa sallamar cike da tsantsar farin ciki da ya ziyarci ruhina,



Shiru mukayi duka kafin yace baki iya gaisuwa bane? adan kunyace nace "am sorry ina wuni, cikin kasa da murya ya amsa kafin yace, hafsat!!! yaja sunan sai da naji tsikar jikina ya tashi, "na am, na amsa cikin muryar kasala, "anya ko kin damu dani? yau kimanin watan mu uku anam sai dai naji muryarki awayar ummata, daga karshe sai naji kince a gaida ni, shiru mukayi mu duka sai ca yayi tom bara na kashe tunda ba kida abun cewa, cikin sanyin murya nace "ya jikin naka, bai tanka ba sai wata iska da naji ya huro man, kunyace taka mani ina shirin yanke wayar na tsinkayo muryar sa yana fad'in karki kuskura ki katse man waya, fuskata na biye kamar ina gaban sa, sautin murmushin sa na tsin kayo, kafin yace "bara na kira vidio call ki nuno man yara na, inga kalan gir man su, cikin sauri nace mar bara naje na kar'bo su, ina kafin duk na yun kura na tashi tuni ya kira vidio call din tilas a hakam na bud'e gamida amsa mar sallamar.






mamaki ne ya kamani ganin yarda yayi kyau sosai ya kara haske duk da yad'an rame amman hakam bai hana naga ya kara man kyau ba,



ido ya zaro kafin yace, " eyen ba lallai kekam baki da matsala hala mai batula ke baki da kika canza lokaci daya hakam?

farin ciki naji ya kamani kafin nayi mik'a, gamida yin far da ido na sanan nace mar harna kaika yin kyau,


iyye ya fad'a gamida tafi yace lallai yarin ya kin girma, aa na ganoki watom kina bukatar mijin ki akusa dake kenan? tom agobe zansa, akawo man ke dan naga kin fara kyar kyara, kina bukatar zakaranki a kusa dake ya karasa maganar yana kashe man ido d'aya.


wata muguwar kunya ce ta kamani gane mai yake nufi da hanzari na aje wayar batare da na kashe ba sautin dariyar sa na jiyo yana fadin kin gudu ko ai zan kama kine.



Adai dai zan fita itako gby batula zata shigo dan daman ta fita dauko saif ne dan deen ne a hannun ta ina jin tana fadin laa yaya ta tafi tabar ka , waya bara na kawo ma tweens ka gansu daga hakam ban sake sanin yarda suka karata ba.






Zaune nake ina shan frut itako iya tana yiwa tweens wasa sai sallamar gimbiya batula naji wacce ban masan da fitar ta ba, tare take da wata mace fara mai d'an tsayi bacin mun gaisa dasu naji gby na cewa matar gani nan tana nuno ni, ban damu ba sai dai muka soma sabon gaisawa da matar sanan sai gby take fadin mije awan can dakin, tashi sukayi gamida fadin nabiyo su, ban musa ba danko suna gaba ina biye sosai nake mamaki ganin an shimfida katuwar leda sanan ta d'ora wata yar kujera mai kyau da tsari tace na hau kai na zauna ban musa ba danko na zamo yar kallo akai, umarni raban na rage kayan jiki na, na koma da gani sai bra da mini siket mai shara shar ina nan dai ina kallon ikon Allah, wai ashe gyaren jiki za,amun sosai gimbiya batula tasa aka gyara man jiki na sai kamshi da sheki nake duk inda na gifta sai nabar kamshina, kamar wata sabuwar amarya,





hakama gidan sai faman gyaran sa ake musamman fada sosai ake gyaran ta, anan nagane su fulani sun kusan da wowa kenan.






yau litini mun tashi da murna na dawo war mai martaba da mahaifiyar sa harma da gimbiya safiyya wacce ta kai wata agidan su, abban ta ne yaje har can gun sarki mahmud da ma haifiyar sa ya basu hakuri akan abunda ta aikata masu da'kyar suka hakura da sharadin zai hade su guri d'aya ya baiwa kowacce hakkin ta danko daman can bakin halin safiyya ne yasa har yanemi auren hafsat da rabon wadannan yaran, ma haifin ta yayi na,am da hakam sai dai yayi mata kyakkyawan gargadi akan ta kiyaye, kar yaji kar ya gani ta kuma yi na,am da hakam.




tom bara mu bisu dan ganin wanne kalan zama ne za suyi ga dai gimbiya safiyya ga sarki mahmud sanan ga kuma hafsat, atare zasu zauna, ko ya zaman zai kasan ce. ku mujee zuwa fans......✍️

❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_ 36--37




HAZIKAI STAR 🌟MASU AIKI da TSANTSAR HIMMA 💫





Wani kalan farin ciki na keji, koba komai yau zanga fulani, sosai na d'au ado cikin wata ran tsartsaiyar material, mai tsantsar kyau kalan sky blue, sosai ta haska ni ta fidda man asalin kalona.


, wata had'ad'diyar alkyabba gby batula ta sanya man, wacce ta k'ara maido ni kamar wata yàr sarki, nayi kyau sosai, saifa wanda ya ganni danni kaina nasan nayi kyau sosai.





Busar algaita da sarewa da ke tashi a gidan shine fa ya shaida man isowar su fulani.



Cikin takon k'asaita na iso falon hakam, yayi dai dai da isowar su fulani cikin falon, da sauri na rumgume fulani harda, Yar k'walla ta danko da gaske nayi kewar fulani.



sosai itama ta rumgume ni, tana shafa bayana, kafin musaki juna itama gby batula ta rumgume ta.




Bacin sunci sun sha sosai aka sake sabon gaisawa, motsi naji a k'ofar da sauri na kai duba na acan danko nazata sarki ne, sai dài fa Ashe iya ce d'auke da tweens. da fara,a fulani ta kar'besu sai faman washe baki take sosai ta rumgume su kafin tàce "masha Allah, kaga yara masu kama da uban su, wad'an nan ai duk Mahmud ne, nan fa kowa ke fad'in abunda ke ransa game da yaran.



niko sai mafan lek'o nake ko zan ga shigowar mai martaba danko na so ganin samuwar lafiyar sa, gane mai nake nufi ne yasa fulani ta d'anyi murmushi kafin tàce "inaga Mahmud nacan sashen sa danko atare suke da sirikar sa, watom uwar matarsa, kai nad'an sunne a lamar jin kunya. batula ce tace tom ni bara na kai masa tweens ya gansu kafin ya k'araso sashen mu.....kamshin sa ne, ya katse ta da hanzari ta soma takon ta na kasai ta ta rumgume sa, sai faman yare take mar, danko ad'an tsakanin nan na fahimci ita fulani tana yiwa yaran ta wani kalan yare wanda naji iya tàce yaren itofiya ne.






idonsa k'ur akaina nima d'in shina ke kallo, ido d'aya ya kanne man gamida huro man iskar bakin sa, caraf muka had'a ido da fulani, Aiko da sauri na d'ukar da kaina shiko kai yad'an sosa kafin "yace ummata har kun huta kenan itama murmushi tasakar mar, sannan tàce "eh ai har munci abinci, yana rike da hannun batula har ya zauna akan kujerar dake fuska ta, ta sosai naji kunyar sa ta kamani na rasa dalilin hakam, du'kowa nayi nad'an rage tsaho kafin na gaida sa, cikin muryar nan tasa kalan na miskilai ya amsa man, sanan ya soma tam baya yar fulani akan yaran, mik'a mar su tayi, kafin tàce kaga gasu nan masu Kama da Kai, murmushi yayi gamida kafa w yaran ido sosai zaka ga farin ciki a fuskar sa, bacin kowa ya na tsa, fulani take tambayar jakadiya, nan ne gby batula tasanar da ita komai ba abunda ta rage ta da shi.




, cikin tsantsar mamaki fulani ta kafe yarima da shigowar sa kenan da ido kafin tàce" tom ai duk abunda aka ce da shi da rabon sa danko shid'in bai tsayar da kansa guri d'aya ba, a yanzun aduniyar nan, ba iya dabba, kawai ake kiwo ba har da d'an mutum, kaga wannan sai ya zamo izna akan ka.



itako hafsat sai nace laifin ta saurin yarda, yanzun yarda yazo maki da suffar taimako kinga idan da shid'in baida kyawon hali Kinga ya 'bata, maki kuruciya ya kuma bata sunan abunda zaki haifa,kinga wannan zai zamo izna akan ki.




Shiru mukayi dukan mu muna sauraron fulani, kafin daga bisani taje fo man, tambaya wacece ke? shine tambayar ta akaina, cikin sanyin murya nasoma bata labarin rayuwa ta tunda ga farko har k'arshen ban rage ta da komai ba.






Sosai naga jikin su yayi sanyi musamman ma fulani wacce naga ta kafe ni da kallo, sosai kafin ta Sanya kuka, d'uka rud'ani ya kamamu har sarki Mahmud sai da naga ya rud'e, tambayar ta muka hauyi ko lafiya kafin nima na fashe da kuka sosai nace kiyi hak'uri umma inhar kema kanbun baka na yasa ki damuwa insha Allah zanbar cikin rayuwar ku, keda yarnki, insha Allah, kaina ta dafa tana girgiza Kai amman kuka yahana ta magana.




canta nisa ta kalli sarki Mahmud da yarima faruk sanan ta maido da duban ta akan gby batula, cikin d'an dashewar murya tace inhar kuka cutar da hafsat ko bayan raina ban yafe maku ba, ido ta mayar akaina kafin tàce hafsat ki rik'e su da amana kema idan kika ha,ince su Allah bazai barki ba, shiru tayi nad'an lokaci sosai sanan tace, "yanzun karfe nawa ne? yarima faruk ne ya kalli hannun sa kafin yace 8:pm yanzun.



kallo tabi sarki Mahmud da shi kafin tàce kakira man mlmn da ya d'aura auren ka da hafsat, cikin sanyin jiki sarki Mahmud ya doka wa mlm Ali Kira, ba 'bata lokaci ya d'auka cikin muryar sa ta isa da k'asaita, yace inason ganin ka a gidana, yanzun, tom shine abunda mlm yace.




cikin sanyin murya ya ce ummata ga mlmm nan ya iso , ashiga dashi fada shine umarnin ta, duk fada an hallara, ana jiran adalin sarki ya fito ayi masa, sannu da dawowa.


, sarkin fada ne yayi wa, malam Ali iso, harda fulani ta k'araso afadan, kowa afadan sai mamaki, yake ganin fulani afada, sunsan ko da akwai zance mai mahimmanci abakin ta.



sosai take kallon mlm Ali kafin tàce " Allah gafar ta malam a wacce ranar ce ka d'aura wa sarki Mahmud aure? cikin d'an kasa da Kai yace ranki ya dad'e adaren juma, a 7/1/2023 da misalin karfe 8:pm bacin mun kammala sallar isha, dubban mutane ne suka shaida auren nid'in ako ina zantsa da shaidar cewa lallaine ninan na d'aura, auren akan sadaki naira dubu goma yanzun hakam nasanya hannun jari da kudin, agidan gonar d'ana lawan yanzun hakam kud'in sun karu, inata son in sanar da sarki Amman ban samu ganin sarki ba, kabbara suka d'auka duka fadan, sarki Mahmud yayi shiru danko daman yasan so take ta wanke sa shida yaran sa, kallon ta yayi yad'an yi, murmushi, sanan yace "akara makalla Ina godiya da shaidar ka akaina insha Allah zan zo gurin ka har gida nida hafsat.



. murmushi fulani tayi kafin ta ce ai bazai tafiba, yanzun bara nazo, kallo tabi maman gby safiyya da shi watom sarauniya surayya danko da ita suka shigo fadar dan kafa HUJJAR auren d'an ta, kar wataran ayiwa d'an ta da yaransa mummun zato.



Sosai tayi farin ciki da wannan shaidun sanan ta shiga har sashen da nake Ina zaune Ina shayar da tweens saiko ga fulani da kanta bata ko tsaya aiken kowa ba, sanyo hijab dinki shine abunda tace man da d'an sanyi na, na sanyo hijab dina yaran ta amsa kafin ta shige gaba niko ina biye da ita, sai ababban falon na tarar da wasu mutane datti jai guda biyu sai shi gwaskan nawa, kaina sunkuyar kafin na gaida su, cikin kunnuwa na naji ance "waye nake gani kamar hafsat, da sauri na d'ago kaina aiko idona suka sauka akan baba Ali wan mahaifina ne uwa d'aya uba d'aya nidai sanina acan rano nasan sa, cikin muryar mai tafe da kuka nace baba Ali shima mamaki ne shimfide afuskar sa, kafin yace kardai ace kece wacce na d'aura wa aure da sarki Mahmud? cikin sunkuyar da kai gamida kukan da yazo man na soma sheshsheka kuka, sarki Mahmud ne yace itace mlm daman kasan tane? cewar sarki, shima baba Ali nid'in yake kallo kafin yace y'ata ce, nin sakar wa uban ta nono, shiru ne yabiyo baya kafin fulani tace ikon Allah, tom ai badamuwa daman Kaine liwanin auren, kaga shike nan, yaran ta Mika mar kafin tàce ga albarkar da Allah ya azurta su dashi nan shida ita, masha Allah shine furucin sa, uadauki yaran gamida Sanya masu albarka, sanan ,yabini da kallo kafin yace mai ya kaiki barin gaban abubakar da har aka d'aura maki aure bada sanin saba? kuma har yau bai shaida man ba?, shiru nayi ina ci gaba da kuka,,


fulani ce ta ce "takama ta kaje ka binciki, d'an, uwanka, danko inaga da akwai dalilin hakam.




tom insha Allah zanyi binciken duk abunda kenan zanne meki, ido na d'ago na kallesa sanan nace yanzun kadawo cikin garin kano ne? eh yace, sanan ya mik'e da Saif da ke ta faman dariya sanan ya mik'o wa fulani su gamida sanya masu albarka,.







Sai taran dare sarki ya fito fada fadawan sa suka rako sa harcan sashen sa, bacin ya yi duk abunda ya dace ya nufi masaukin sa ransa fall da kewar matar sa.




d'akin gby safiyya ya shiga yata rar da umman ta tana ta faman bata baki akan auren sarki da hafsat sai faman risgar kuka take tana fad'in itafa mutuwa zatayi danko bazata iya jure ganin kishi ga Mahmud ba, ganin bata ma kulasa ba yayiwa ummanta sai da safe ya bar d'akin, da rarrashi umman ta tasamu ta turo ta gurin sa, kwance ta tarar dashi akan gadon sa yana tunani idonsa a runtse,

tsaki taja kafin tàce "nina san bana ga banka danko yanzun waccan yàr cikin ka, itace tunanin ka, idon sa ya bud'e fes akan ta, kafin ya kafe ta dasu cikin muryar kwantar da hankali ya janyo ta a jikin sa, sanan yasoma cewa da ita, "safiyya ya ka mata, kisan cewa duk wani matsayi da hafsat ta taka a zuciya ta, kece kika bude mata k'ofa, kuma kece kika bata dama, sosai ya rumgume ta gamida fad'in zo kiji, mafarin lamarin ido cikin ido suke kallon juna, kafin yace awaccen ranar da nazo gurin ki da lalura ta, aranar kamar bazan kaiba danko ninasan Ina cikin wani mawu yacin hali, sosai nake rok'on ki alfarmar ki amince dani harda alk'awarin bazan yi maki kishiya ba har abadan na daukar maki, kika ki amin cewa, dani, kan kebaki ra,ayi, sanan nace ki rubuta cak kona nawane zan baki danko dama sai na biya kike kwana dani sosai kikace man aranar ke baki buk'atar d'a namiji. niko aranar ayarda nakeji idan ban kusanci ya mace ba zan iya shiga cikin mawuya cin hali, ganin ba ki tausaya man ba yasa naci alwashin tabbas idan na fito duk wacce na fara cin karo da,ita itace matar da zan aura cikin ikon Allah har na fita gidan nan banci karo da kowa ba, kasan cewar lokacin san yine, saiko zcy ta ta aiyana man naje gidan yari ganin ba nisa da gidan sarauta yasa na fito batare da kowa ya ganni ba, danko ko mai gadi ban amince da ya ganni ba, da sand'a na k'arasa cikin gidan, yarin, aiko Ina shiga acan daga gefen dama na na hango wani d'aki, mai tsayi da d'an fad'i araina nace nasan can za,a samu mutane da yawa., ina k'arasa wa bakin k'ofar d'akin, wata yarinya naci karo da ita zata koma daga ciki, sosai na mara Mata baya, nayi farin ciki da naga yarinya ce mata shiya, anan nasoma rokon ta, akan ta aureni, a cikin daren nan, dukda na hango tsoro sosai, a idon ta, amman Jin nace zan,iya rasa raina a hakm, ta amaince man danko ga alama yarinyar tana da tausayi a idon ta, nan take ta, amince man nakira mlm Ali ya d'aura auren acikin daren kuma acikin daren nasamu biyan buk'ata ta, na barota cikin halin tausayawa danko itad'in tabbas budurwace, k'arama ma.....dan Allah can naji cewar gimbiya safiyya ta ci gaba da fad'in basai ka fad'a man kasan cewar kasan wata mace ba, ahasale ta mik'e ta nufi hanyar barin d'akin.


janyo ta yayi ta fad'o jikin sa gamida fad'in so nake kisan kece mai laifi bani ba.


.
Baki ta tun zuro masa kafin tace "tom idan ma nice, mai laifin sai kana fad'aman kasan wata, ya mace? kanta ya d'ago yasai ta sa da nasa, kafin yace, "ba wai Ina fallasa sirrin aure na neba, a a so nake kisan ita d'in mai daraja ce a gurina, sanan kuma dan kar wataran ayi mata gorin mani abun tabbas nina shaide ta itad'in bata ta'ba zina ba, atun farkon ta.



cikin d'an fusata tace "nidai ba wannan ba, yanzun kace nice mai laifin har kana fad'a man da bakin ka, tom yanzun inason kabani dama na gyara laifina. cikin nutsuwa yace "ehen ta Yaya? zaki gyara abunda kika bata, da d'an fara,a afuskar ta tace idan har zaka iya aikata abunda zan fad'i maka, insha Allah niko zaka sameni, mai kokarin gyran abun da na bata.



Cikin tsantsar mamaki yace, "tom ina sauraron ki, hannun sa ta d'an matse gamida fad'in kasaki hafsat kaga zamu dawo kamar da niko insha Allah zan gyara laifina.



Ido yad'an bita dashi, aran sa yake cewa a yanzun aiko da ca za ai nazaba, a tsakanin ku, sai dai ko nazabe ta, danko a yanzun itace zuciya ta., d'an girgiza shi tayi kafin tace "kayi shiru, cikin muryar mai tafe da rainin wayau, yace "yanzun kina ga idan na bar hafsat yaran fa, waye zai rika man su tamkar ita? da d'an hanzari cikin alamun nasara tace "niba daman ai yara nane kakai mata danko ara nar idan da na amince da ko nice da haihuwar su, kaga ai yara nane, ta k'ara sa maganar tana, yarfa Hanna yenta.



murmushi yad'an yi kafin a ransa yace wai yaran ta, (fans wai hakane?😂)




kallon ta yad'an yi kafin yace "tom yanzun inga alamar kin fara kokarin gyaran.


ta ina kake son sanin hakam? tanan ya fad'a gamida nuna mata gadon. fuskar ta tad'an saki kafin tàce ;I'm ready,, sosai ta saki jikin ta yayi yarda yaso da ita, bata hana sa ba kuma bata katse sa ba, sosai ya samu nutsuwa wacce rabon da yasamu kalar ta tun adaren farkon su, rumgume ta yayi gamida sanya mata albarka, itako aranta sai faman murna take danko a tuna nin ta da safe zai sallami hafsat, aranar sanyi barcin farin ciki.







niko a ban gare na, inacan d'aki nida ya rana, aranar ma koda naba iya su, asan da a zamu kwanta caa tayi na tafi dasu 'kilan, abban su zai bu'kaci ganin su, da yàr kunya nace "laa iya aiba zan Kai mar suba, ca dài tayi na tafi dasu, badan naso ba, tilas na tafi dasu aiko rashin sabo kacar na samu sukayi barci, danko suna d'an ta'ba rikici.


tun sa,Adda na sanya prince Mahmud, a idona nan fa na soma jin wata muguwar sha,war sa musamman idan na kalli la'b'ban sa, dan hakam na shiga d'aki da sauran lokaci, amman fa kamar jira nake naji ni ad'akin, sai tunanin sa ya hanani sakewa, sosai nake buk'atar ganin sa a kusa dani, tunfa abun baya da muna, har nasoma duban a gogo kamar wata wacce take sauraron isowar wani, sako.





ahakm dai nasamu barci ya d'auke ni, amman kuma ina barkawa da jarabar na farko danko marata naji tayi man nauyi, har da d'an ciwo na keji take man, Aiko sosai na soma addu,ar kar Allah ya san yani, cikin bayinsa masu muyuwar Sha,awa danko da abun bazai man kyawo ba, sai na tashi, duk raina aja gule, amman hakam na daure naje na d'ora wa, fulani girkin ta, (domin ko tun sa Adda nazo gidan indai Ina nan ban fita ba tom nice ke girka wa fulani abin da zata ci) saiko sa,adda ciki na ya tsufa sanan da kanta ta da katar dani.




tom ko yanzun ma inacan ina d'ora mata abun kari sosai na had'a mata kalan abunda take so bacin na kammala nayi wanka kafin na dau ado cikin wasu kalan riga da wando kalan na y'ay'an birni zubin na yaran sarakai tilas idan ka ganni zan burge ka, gby batula ce keta Kod'a man kwalli yata kafin suma tweens iya ta gyara su tsaf cikin wata jar shadda, wad'an da akayi wa dinki kalan na sarakai sosai suka haska , k'asan cewar su farare tas kamar uban su, fulani tana ganina sai cewa

Please Login or Register in order to submit comment