Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shimfide afuskar ta gidan ko Ina sai murna ake da zuwan gimbiya batula cikin falon nakoma na zauna ina kallon irin yarda gidan duk ya rud'e da murna, sosai aketa faman farin ciki.


, cikin tsantsar takun k'asaita ta k'araso cikin falon ganin ta yasa naji wani farin ciki sosai ya kamani da kalar ta fiya namasu tsohon ciki na tare ta sosai na rumgume ta dan har ga Allah inason jinin fulani sosai na k'am'kame ta da kallo ta bini kafin itama ta k'ara rumgume ni gamida shafa ciki na, ta sunkuyar da Kai ta sumbaci ciki na, sanan tace man tace man "yauwa sister kema barka da gida, sanan ta sakeni kafin ta ruga da gudu gudu sauri sauri ta rumgume fulani cike da d'oki suka rumgume juna kafin su zauna akan kujerun falon sosai suke ta hirar yau she rabo da wani kalan yare wanda nidai ban ta'ba jin fulani tayi sa da kowa ba, sosai suke ta shaukin ganin juna, sai fa can ta je tayo wanka ta canjo kayan jikin ta sanan ta hau dinning kafin ta koma ta konta.

aranar duk muna ta murna a gidan sosai har dare, mai martaba da kansa ya shigo falon tare da gimbiya safiyya danyi wa gimbiya batula murnar kammala karatun ta, sosai ake ta hira niko idina nakan la'b'ban sa danko har ga Allah inason wad'annan la'b'ban nasa suna burgeni han kalina ya tafi can gurin kallon sa Ina ayyan araina shid'in kyakkyawa ne sai jinayi an kaiman rankwashi akai da sauri na juyo dan ganin kowaye gimbiya safiyya ce da wannan aikin, kallo nabi sa dashi kafin na juyo da idona araina narasa komeye nayiwa wannan baiwar Allah ta tsaneni da yawa, ganin zata ta kurani na tashi da nufin barin gurin danko gara nabar gurin zaifi man.


fulani ce ta d'ago Kai gamida fad'in yadai yata zaman ya gundure ki ne? eh nace sannan na nufi d'akina duk da ido suka raka ni, shiko sarki Mahmud idon sa a'kasa sai dài fa tafiyar ta na masu ciki shine ke burgesa, idon sa fes akan ta, sai dai fa idan baka sani ba baza kace ita yake kallo ba, dan ko idan sa a'kasa yake, sosai yake kallon ta aransa take ayyana lallaine yau d'innan zai ziyar ceta danko ya lasa zumar ta ta ratsa shi sosai yake jin yarinyar a jinin sa shi yasan zuwa yanzun tabbas ya kamu da sonta., jin shirun yayi yawa yasa gimbiya batula tace yadai d'an uwa ta fad'i hakam gamida tabo sa sai alokacin yad'an kallo ta sanan yace, " no ba damuwa k'anwata.


niko tun sa Adda nashigo d'akin wani kalar barci mai nauyi ne yayi gaba dani, can cikin barci na juyo naji ni shim fid'e a kirjin mutum da hanzari na bud'e idona sosai nake kallon kowaye sai dài fa ban ganin kowaye danko bana barci da haske adakin mamakine ya kamani ganin yarima baya nan kuma tabbas wannan kalan k'amshin sa ne danko yanzun na soma gane da banbanci a tsakanin k'amshin yarima da sarki Mahmud, shiru nayi ina nazarin mai zai faru cikin kunnuwa na naji yasoma rad'a man "kin tashi sarauniyata? mik'a na d'anyi kafin na tashi zaune danko fitsari nake ji sosai wayar da nake game da ita na lalabo amman ban ganiba, hannu na naji ya cafko sanan ya d'auke ni cak sai a toilet yana tsaye har na kammala naso yad'an shigo daga ciki ko nagan sa ta hasken toilet din amman sai yaki yatsa daga cikin duhun ahakam nad'an fito kafin yak'ara dauka ta sai akan gadon ya dire ni, cikin sanyin murya nace "Kai din mai karfi ne sosai.
cikin muryar rad'a yace man "aikin ga zahiri danko ga ajiya ta nan tun adaren farko., ido na rufe kamar yana ganina danko kunya ce ta kamani cikin kunnuwa na, na tsinto muryar sa yana fad'in "zaki iya d'aukar lalura ta ayau? danko bazan iya hak'uri ba, cikin mamaki nace "yanzun ba ka ganin abinda ke ciki zai iya samun matsala "akanme? Yace dani saboda kaid'in babbane, kana da nauyi, kar cikina ya fashe. ina jiyo sautin murmushin sa kafin yace waye ya fad'a maki cikin mutum yana fashe wa idan ana wannan abin? sai dài fa inke din raguwa ce, cikin d'an tsoro nace nidai zan iya shanye wahalar idan har abin cikin bazai samu matsala ba, d'an murmushi yayi kafin yace shine fa nake jin farin ciki idan natuna ki kuma nakan gode wa Allah da yasa uwar Y'ay'ana ta zamto mai k'aunar su, k'ara k'am'kame ni yayi sanan yace man bara nabaki sweet naki kafin na furta komai sai jin la'b'ban sa nayi acikin bakina sosai yake tsotsar la'b'bana kafin ya sanya hannun sa cikin mara ta yana juya sa sosai yake shafa ta, duk ya riki tani danko ni nasan shid'in bai da wasa gurin nunan so tsantsar sa, ban san sa adda Nima na biye masa ba banyi aune ba sai jinsa nayi cikina k'ara k'am'kame sa nayi gamida sake masa ragamar tafiyar, tuni ya soma sakin layi sai ce man yake "kece sarauniyar nabaki karagar na d'ora ki akan mulkin jani ahan kali hafsina!!!!! niko sai mamaki ne nake.


bacin komai ya natsa yana rik'e da hannu na sai faman saman albarka yake yana fad'in Allah yabaki zuria d'ayyiba ya shayar dake kogin kausara, ameen nace dashi sanan nace "kace man kabani karaga kadora ni akam mulki dan Allah nidai zuciya ta ta fara sarka man wani Abu akan ka. name kenan? ya tamba yeni cikin dan damuwa nace tom Ina kasamu mulkin da ka d'ora ni akai ? cikin dan murmushi ya rad'a man akunne ai idan munzo Wannan gurin kece sarauniyar kin gane ko, ya fad'a yana mai langa'be Kai cikin jin kunya nayin saurin boye wa, a kirjin sa shiko yak'ara rungume ni sosai.







yanzun kam tafiya ta nisa sosai danko ni nasan ciki na yayi girma sosai akan na sauran wasu masu cikin dana ke gani yanzun zama da kyer nake gimbiya batula tana matuk'ar sona duk abinda nake so shi take yiman sosai take kulani tasha, tambayar fulani akai na, sai cewa take itama ahakam ta ganni nima din aranar da ta tam bayeni ca nayi insha Allah zan sanar da ita koni wace amman sai na haihu shima yarima ba laifi yana tausayi na sosai, danko tun aranar da gimbiya batula ta dawo shima muka wayi gari muka gansa, inaji fulani tana tambayar sa yaushe ya dawo saice mata yayi da biyun dare ya dawo, niko sai hararar nabisa dashi danko ina tunanin dawo war sa kenan yazo man da jarabar sa.



share sa nayi danko arai na kuduri aniyar duk abunda na haifa ya dauko fuskar yarima tom lallai anan ne zan gane shine ubn d'ana.





yau laraba tun safe na tashi da yawan fi tsari ga wani abu mai kauri dake fado man agaba sanan aduk sanda zai fado sai naji yanka war mara tom a hakam dai na daure Ina ta Sha,ani na Amman na lura duk hankalin fulani na a kaina. gimbiya batula sai faman k'ok'arin ganin take naci abinci sosai, danko ko abincin ban damu dashi ba ayau, zuwa dare abin ya soma damuna amman ganin dare ne sai na soma kannewa dan kar hankalin fulani ya tashi itam d'in lokaci zuwa lokaci takan leko ni da kanta hakam ma jakadiya tana zuwa tana tambaya ta abinda ke da muna alokacin da zasu kwanta ma sai da suka leko ni ganin Ina barci na yasa suma suka nufi nasu d'akin.





can cikin barcina naji wani kalan mugun azababben ciwon mara ya taso man aiko ba shiri na zabura na mik'e akan gadon aiko da yak'ara kwanta na tuni na diro k'asa da sauri na dafe mara na, Aiko sosai fa abun yake da muna, saiko naso karanta inna lillahi wa Inna ilaihira jiun, danko ban ta'ba zaton da kalar wannan azabar aduniya ba, nakasa zaune na kasa tsaye nama rasa maye mafita sai mafam kiran Allah nake, da nasamu na Kai zaune sai ko na kaza tashi, inanan inata fad'in sunan Allah saiko naji an turo kofar da sauri nace dan Allah ko waye yazo ya taimaka man, da mugun hanzari naji an dagoni kafin inji saukar muryar sa a kunnena cikin rud'ewa yace hafsat!! mai yafaru? baki da lafiya ne? wani kalan yankawar marace tazo man yasa narike sa, ganin tabbas haihuwa zanyi yasa ya ce man ki kwanta ki kalli sama, na yunk'ura Dan cikon umarnin sa Amman sai nakasa, cikin wata kalar wahalalliyar murya nace masa mutuwa zanyi dan Allah idan namutu kar kabari ashe ganta man d'ana dan Allah kasanar dashi cewa kai ne uban sa, da sauri yace man "bazaki mutu ba hafsat! insha Allah saikin goya a bunda kika haifa da bayan ki, tashi ki gur fana aizaki iya ko? eh nace dan a sannan abun yad'an lafa man, aiko kamar karna gur fana saiko naji wani kalan ciwon mara mai tafe da wani k'aton nishi, k'am'kame masa kafad'a nayi sosai nayi nishin shiko sai faman shafa man baya yàke Yana fad'in kisake yin nishin yanzun zaki haihu aiko da sauri na sake yin nishin saiko ga sankacecen da ya fado asaman rigar sa, yana shirin janye yaron sai ganin yayi nasake rike sa sosai gamida wani nishin aiko saiga wani d'an yasake dan nowa jinayi kamar ancire man kaya ajiyar zuciya nasauke gamida zauna wa acan gefe, dukan mu shiru mukayi ni ina kallon yaran dake ta faman wuntsila suna kuka shiko kansa yasoke ya soma kukan nagane hakam ne ta hanyar hasken daku sasshiyar tochilan waya ta data kasnce man nayin game, acikin kukan yake ta fad'in alhamdulillah hakam yayi dai dai da shigowar gimbiya safiyya ad'akin dan tabbas ita d'aice nasan mai irin Wannan halin aduk gidan da sauri ta fado d'akin Jin kukan jarirai hakam yayi dai da isowar fulani adakin dagani har shid'in Wanda nake zatom yarima faruk ne duk munyi sha'be sha'be da jinin haihuwar tom amman abun tambaya anan mai ya kawo gimbiya safiyya ad'akin cikin wannan tsohon daren.......✍️


❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_ 32--33


HAZIKAI STER 🌟 masu aiki da kaifin basira da tsantsar himma💫





Kina nan araina har kullum kece fitila ta Anty Fatima Rabiu Allah ya k'ara d'aukaka da k'arfin gani🙏






Jin jinan ban girma ga reku dukka masoya na masu bibiyar wannan littafin Ina sonku a duk inda kuke Allah yabar k'auna ❤️ ta fisabilillah.




Had'e mu yayi mu duka dani da yaran ya rumgume sosai yake godewa Allah, sai ya koma kamar wani zararre sai faman fad'in yàke "Allah nagode ma da ka a zur tani da kyautar abunda mulki da kudi basa saya.


Fulani ce ta janyo yaran bacin ta kunna hasken d'akin ko,ina ya game da haske.



Bura uban nan, cewar gimbiya safiyya, a sanda ta yi arba da sarki Mahmud k'am'kame da hafsat wani kalan ashar ta ruga gamida kaiwa hafsat raruma sai ca take daman anam ake zuwa cin a mana ta? da yawan darare nakan farko naga baka nam idan nayi magana sai kace man, uzuri ne ya fidda ka, wlh baka isa kace man ka aje y'ay'an shege awaje ba...... marin da yarima faruk ya d'auke ta dashi shine ya hana ta k'arasa maganar, wanda iso war sa kenan gurin danko haya niyar gimbiya safiyya ta tada sa. kuncin ta tarike gamida binsa da kallo, cikin dakiyar murya yace "kisake shegan ta wad'annan yaran kiga ikon Allah, danko sai kin yi nadamar kasan cewar ki anan.


Cikin karaji da juyewar tunani tace "ance shegu sud'in ba shegu bane yanzun agaban ka yake fad'in ya godewa Allah da ya azurta shi da yara tom idan sud'in ba shegu bane uban waye ya d'auro masa aure da uwar tasu? da wani kalan hanzari yarima faruk ya d'aga hannun sa da nufin ya zafga mata wani marin, fulani ce ta da katar dashi gamida fad'in" kabar ta kawai aiba a had'a farin ciki da bak'in ciki dan hakam share ta, barin gurin yayi danko bazai iya jure ganin ana shegen ta yaran yana kallo ba, dan ko shid'in da yake ta'ba shirme, baya so ya aje shege bare d'an uwansa da ya zamto kamili sosai, awani gefe na ransa sai faman mamaki yake Ashe daman sarki ne mijin hafsat, shine ta ke fad'in ko shine har suke tuhumar sa ita da umma, lallai ko biri yayi kama da mutum, ahakam yabar gurin.




Itako gimbiya safiyya sai k'ok'arin take ta kai ga jiki na, shiko sarki Mahmud ya na k'am'kame da jikina kamar wani zai kwace masa ni.




Niko nayi suman zaune dan mamaki danko ban ta'ba zaton sarki Mahmud shine miji na ba a duk inda tunani na ya tsaya bai fice gurin yarima faruk ba, cafkar da a kayi wa hannu nane yasa na dawo cikin hayyacina, da sauri na kai duba na ga gimbiya safiyya dake k'ok'arin ganin ta shake ni cikin azama sarki Mahmud ya fisgo ta jikin sa duk jini hakam ya jata, da nufin ya turo ta a waje ya rufe, d'akin yabar ta can, ina kafin duk ya kai k'ofar ta rarumo wu'ka sai dài jin yayi ta soka mar ita a bayan sa, sai ca take zan kashe ka in kashe kaina danko bani da amfa ni ga rayuwar ka, tilas ko yau d'in nan sai na kashe ka na kashe kaina.






fulani dake zaune rumgume da yaran da hanzari ta taso har tana Shirin jefar da yaran jakadiya dake ta kokarin ganin ta gyara gurin ita da sauran kuyangin da suke aikin atare, da mugun hanzari jakadiya ta cafe yaran. nima da mugun hanzari na riko hannun sarki Mahmud dake shirin dafe gadon danko sosai jini kemar zuba agurin kasan cewar yayi man nauyi atare muka fad'a kan gadon da shi.


duk fa a binda ake gimbiya batula bata da labari danko barcin ta take sosai, amman fa cike take da mamaki aran ta, watom ita gimbiya batulan danko bata yi zatom a gidan wani zai iya auren hafsat ba, danko tayi yarinya, a zatan ta, ko yarima faruk ne ya janyo masu rigimar tasa da ya saba, a kullum, so take tasan dalilin zaman hafsat a gidan, amman har a yau bata samu mai bata wannan, amsar ba.


dài dai sa,adda fulani ta k'arasa gurin gimbiya safiyya, ta jiyo sautin ta tana fad'in "zan kashe ka in kashe kaina, da ganin wannan ranar gara min ganin gawar mu duka nida kai.



da mugun hanzari fulani ta k'arasa a ciki tana isah, gimbiya safiyya tana luma wa cikin ta wu'ka sai ca take mu mutu atare zaifi man amman bazan iya jure ganin wata atare da kai ba. da gudu ta k'arasa ga d'anta tana fad'in dan Allah Mahmud kar katafi, janye ni tayi daga jikin sa kafin ta d'ago sa, ana hakam sai ganin wuta akayi ta tashi agurin sosai duk muka rud'e fulani ce ta fito da gudu tana Kiran jama,ar gidan sauran masu kula da gidan sune suka yi saurin kawo wa muna d'auki da sarki Mahmud.


da mugun gudu gimbiya batula ta k'araso gurin, janyo d'an uwanta take, amman ina bata iyasa, kacar dogara wan dake nan suka samu suka kashe wutar.

wani kalan kuka ne yazo man a yayin da nake tuna hakam idona cike da hawaye nake kallon barisster zainab wadda itama ni d'in tàke kallo danko ayau d'innan ba sai gobe inason kowa ya san HUJJATA, (ina fatan masu karatu zasu fa himci inda HUJJATA ya dosa) kallo nabi barrister zainab, da shi, kafin inci gaba da fad'in, "bacin an kashe wutar saiko aka dauko gimbiya safiyya, dake kwance cikin jini tare da sarki Mahmud aka nufi hospital dasu awani kwararren asibiti aka Kai sarki Mahmud danko yana cikin wani hali itama kanta fulani asibitin ne aka nufa da ita danko tabbas tana cikin buguwar zuci.




Niko tuni na some ban ma san inda yaran nawa suke ba nid'in ban San inda nake ba bare wasu yara na, can nasoma, jiyo sautin kukan gimbiya batula tana fad'in lallaine da akwai wata a k'asa danko ba yarda za ai ace su duka an kashe su kuma an jona musu wuta. Wannan kukan da take ne shi ya mayar dani cikin han kalina, tuna abinda ya faru ne yasa na soma kuka, sosai sai ca nake mai zanji da gani a yau, duk gidan an hallara phart d'in mu, acan daga farko na hango su binta shugaba ita da kande, suma d'in ni suke kallo, da ganina sai ca sukayi daman taya za,a samu lafiya tunda ga anno ba a gidan.




Sai alokacin natuna a she na haihu wani kukan ne yasake zuwa man danko ban san ko wanne irin hali fulani take ciki ba bare shi kansa uban gayyar, shiko yarima dan tsabar rud'u bai tsaya ako ina ba sai gurin al'kali, itako gimbiya batula sai ca take lallaine sai anbin ciki laarin danko ya za,ayi duka gidan ace sun tafi ba fulani ba Yaya Mahmud ba gimbiya safiyya, dan tun farko na fad'a maku ita din bata san wainar da ake toya wa ba.






Bacin ta gama fad'ar ta sai ko ta juya da nufin barin gurin adai dai nan sai ga yarima faruk dauke da wasu kalan kaki suna ta tsintar duk wanda ke gurin ana jefa sa gidan yari saifa can rana sannan jakadiya ta k'araso gurina tace man nazo na gasa jiki na bacin ta yi man duk abinda ya dace saiko ta taimaka man na gyara jiki na ta gyara man yaran sai tabarni dasu dan ganin nasamu nutsuwa, tom ina nan Ina nazarin yanayin da su fulani suke ahakam mun kai kwana biyar, kullum sai jakadiya ta bamu kyakkyawan kulawa tare dani da kyawawan yara na masu tsananin kama da juna, kuma sud'in sak sarki Mahmud suka d'auko bacin na ri'kasu sai na fashe da kuka sosai danko Ina tuna ko wanne irin hali mahaifin su yake ciki? tom ina nan nefa sai ga ki watom ke gimbiya batula, atare da barisster zainab anan ne nake jiyo zancen kuma wai fa harda al'kali ya nason zaiyi binci ke a kaina.



Anan ne na fahimci watom ana zargin da sa hannu na cikin Wannan lamarin wasu hawayen ne nake sake share wa ina kallon gimbiya batula kafin nace nifa zama gidan yari ba zai dameni ba, Amman fa inason sanin halin da fulani take ciki sanan kuma na tsani ana kallon yarana wasu kala alhalin saeki Mahmud shine uban su Ina da kuma HUJJATA akan hakam amman sai Allah yayi dawo war fulani lafiya da shi kansa sarki Mahmud harda ita kanta gimbiya safiyya, nasan Allah zai fidda yarana cikin zargi ana kallon sud'in y'ay'an kuyanga ne, wace sarki bai aura ba, wasu kuma suna kallon su a matsaya ta shegu .




Da ido gimbiya batula ta bini, kafin ta soma fad'in taf cakwakiya tom indai ko har da gaske ne kike ked'in matar sarki Mahmud ne tom lallai ko da sauran k'ura danko nina san itad'in gimbiya safiyya baza ta barki ba.



Barisster zainab dake kallona sake da baki tace " Nina san hakam zata faru wacce kalar shawara ce bamu bawa safiyya ba akan ta kama mijin ta sosai dan guje wa irin Wannan ranar, k'ara kallona tayi kaifin ta soma fad'in "kekam yarinya, Allah ya baki sai ki dage ki rik'e mijin ki danko ni na san ba k'arfi ba ko iyawarki ya baki, shi sai dài ikon Allah danko samun sarki Mahmud a cikin dubun maza sai antona infa da gaske kike amma gaskiya ina shakka akan hakam kiduba duk haduwa irin ta safiyya sai da ya turje wa auren ta bare ke Wannan yar,mi tsitsiyar dake.

Nima ido nabi barisster zainab dashi kafin nace " nid'in yanzun damuwa ta shine insan halin da fulani da mai martaba suke ciki, danko nasan dai basa kasar ko na fad'a ina mai kallon gimbiya batula.

muryar yarima faruk na tsinkayo Yana fad'in Innalillahi wainna ilaihirra ji,un, da hanzari muka tun karo sa mu duka shiko, yana gaf da shigowa cikin falon fulani har suna cin karo da juna, sai k'ara mai-mai ta kalmar yake. ido cikin ido yake kallon batula kafin ya dafe kirjin sa. niko sai cewa nake please yarima mai yake faruwa........✍️


❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
_*❄️HUJJATA❄️*_
_By_
_*HAUWA MUSA RIJAU*_
_(AMINIYAR D. A. W. A)_
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
```Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*Page*_ 34--35



HAZIKAI STAR 🌟 masu aiki da tsantsar himma.




Kansa ya dafe yaci gaba da mai-mai ta kalmar sosai ya kafe gby batula da ido, dukan mu sai tin inda yake kallo muka bi da ido, ga mamakin mu ashe ba gimbiyar yake kallo ba, jakadiya ce ita da sauran kuyangi sun kai su hud'u sai faman kyarma suke. shiko idon sa sun kad'a sunyi jazur sosai yake kara kallon su. cikin san yin jiki gimbiya batula tace wai meye yake faruwa? kallon su din yake gamida cewa "su fad'a maku abinda suke fad'i da bakin su, a she lala cewar zamani har ya kai ace bawa zai zaman zagin sarki da bakinsa? duka shiru mukayi danko na soma gano bakin zaren, ajiyar zuciya na sauke, tunda na gano cewar matsalar ba ta su fulani bane, har gby batula atare muka sauke ajiyar zuciyar da ita, tsawa ya daka masu gamida fad'in nace ku mai-mai ta, abun da kuke fad'a. da rawar jiki jakadiya ta fara fadin dan Allah kayi hakuri ranka ya dad'e mun tuba waya ya daga yakira shugaban gidan yarin, aiko da sauri ta soma kuka tana rokon gafara suma sauran sai faman zare ido suke.


cikin tsawa gby batula tace wai meye ku ke fad'a ne da kuka kasa mai-mai ta wa, cikin rawar murya yawale ra soma fad'in daman..daman.. um...umm jakadiya ce tace wai..."ke ki nutsu ki sanar damu karkisa yanzun in sa acasa man ke muna fuka, cikin rawar murya tasoma fad'in "daman ca tayi wai yaran hafsat na yarima ne wai ta sha kama sa ad'akin hafsat amman yanzun gashi anli'ka wa sarki mahmud su, dace ko aranar da idon ta taga yarima rumgume da hafsat shine fa muko mukace ai tunda har taga fulani tayi biris da su tasan d'anta ne yayi cikin shine jakadiya tace ai Allah kadai iya y'ay'an da yarima yayiwa ciki ko yanzun dubun sa ne tacika har ya farma hafsat da take annoba, shine fa ina juyo wa da nufin in tam bayi abunda ta aika ta, shine fa mukayi ido hud'u da yarima, zai shiga sashen fulani sai salatin sa muka jiyo.


cikin

Please Login or Register in order to submit comment