Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*





_____________________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_____________________________________






*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

- *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_







1️⃣&2️⃣




```Barkan mu da kara haduwa awani littafin, Allah yasa ku ji dadin shi, kuma Allah yasa ya amfane mu duk.```
```Wannan littafin it's a work of fiction, so in ka/kin ga ya zo similar da rayuwar ki/ka, kasan it's not intensional.```


```Am dedicating this page to my fam "my Mummy, my Daddy and my brave lil sis Nana Hauwa. I love you all loooooooadssssss.```




_Bismillah_






Zaune suke a balcony, suna hira, sai kanin ta ya taba ta, ya ce "aunty Olamide, yau she zaki koma school ne"? Ya fada yana yatsuna fuska.
"Gaskiya kam aunty, yaushe zaki koma". Kanwan ta ta tambaye ta, ta na daga gira.
"Mu kam mun gaji da mita ko Farida". Kanin ta AbdulHakeem ya tambayi Farida.
"Ooooh owk, kun gaji da ni ko, zan bar maku gida nextweek. Amma ku sani, kafun in koma, sai na gasa ku".
"Otobe! (Baki isa ba) mahaifiyar su ta fada.
"Kawai haka ki dinga takura ma yaya na, nextweek dinnan yayi yazo ki koma, ko yara na zasu ji sakat".
"Haba Mummy, harda ke yanzu kin gaji da ni"? Ta fadi kaman zatayi kuka.
"Ae sosai ma, addu'a na yanzu Allah ya kawo miji kiyi aure, kinga zamu samu kwanciyan hankali, ba mai mana mita, kije can kiyi da mijin ki".
"Kai Mummy è ni fe mi ni (baki so na ne)"?
"Of course ina son ki mana, your trouble is just too much".
"Shikenan, tunda my trouble is too much, bari in bar maku wajan, kuma ba abunda zai kara hada ni daku, in ba gaisuwa ba, da major things, har in koma school".
"Da mun ji dadi ko Boder (yaya)"?
"Sosai ma". Abdulhakeem ya amsa.
Afusace ta bar wajan, ta shiga dakin ta tana huci.



*WACECE OLAMIDE*
Kaman yanda kuka sani, Olamide sunan yarbawa ne, although sunan ta Faiza, amma kun san yarbawa da son amfani da sunan yare, shekarun ta ashirin, tana aji uku a jamia, a B.U.K.
Yarinya ce mai hankali, ga son jama'a, ga lada bi da biyayya, tana ba kowa girma, ba babba ba, ba yaro ba. Gashi tana da fara'a sosai, ga wasa, da duk qualities masu kyau dai, amma fa Olamide akwai masifa, ga uban mita.
Mahaifin ta ya rasu tun tana primary school, alokacin shekarun ta shida, toh tun lokacin mahaifiyar su ta zama ko mai nasu da ita da kannan ta.
Sunan mahaifin ta Alhaji Abdullahi, sunan Mahaifiyar ta Alaja(Hajiya) Fausat. Kannan ta biyu, da Abdulhakeem da Farida.
Shi Hakeem, kaman yanda suke kiran shi, shekarun sa sha'takwas, yana aji daya ajamia, a ATBU Bauchi, Ita kuma Farida shekarun ta sha'shida, tana secondary school ne, tana ss2.
Although su yarbawa ne, amma suna zama a arewa, anan ma aka haifi mahaifan su, harda su, in short nan duka Familyn din su suke, kawai dai muna yarbawa ne, dan basuma san hanyar garin yarbawa, although dai sun iya yaran kadan kadan. Suna zama ne a jahar Niger, agarin Suleja, sunma zama yan gari awajan, amma kun san bayarbe da kishin yaran sa.

~Wanan kenan~

Data shiga ciki, su ka fashe da dariya.
"In dai Mide tace, duk abaki take yi, da kan ta zata fara magana da mu". Mummy ta fada.
"È ma dalon( kar ki damu) mun saba Mummy". Hakeem ya fada yana dariya.
Ita kuma Farida, tayi shuru, kaman bata wajan.
"A'a goggo Farida, lafiya?
Naga yanzu muka gama dariya, ina magana kuma ki kayi shuru, kaman na tuna maki da wani abu".Hakeem ya fada.
"Hmmm boder ba zaka gane ba. Kasan baku zaku kwana da aunty Faiza ba, tunan nin masifan da zan sha nake yi". Ta fada kaman zatayi kuka.
Tana maganan, Mummy da Hakeem suka fashe da dariya. Hakeem na dariya har ya fado daga saman kujeran da yake zaune.
Cikin fushi tace "wallahi boder matsala ta da kai kenan. Kai zaka jawo fada, amma ni zan sha masifa".
"Toh ni nace ki sa baki ne?
Ai da nake magana, baki ji nace Farida kisa mun baki ba"
"Toh ai kaima ka san bazan iya shuru ba" ta fadi tana goge fake hawaye.
Ita ko Mummy sai kallon ikon Allah take.
"Eya, amebon(gulman) ki ne yayi yawa. Kinga bani ke saki ba kenan. Kuma indai masifa ne, yau zaki sha shi buhu buhu. Amma in baki son ki sha masifa, ki bi Mummy dakin ta, ku kwana tare". Hakeem ya fadi.
"Toh ai boder Hakeem baka sani ba, nightwear dina na dakin". Ta kara fada tana yi kaman mai kukan gaske.
Wani sabon dariya Abdulhakeem ya kara yi.
"Wato aunty Mide ta zama doodo agidan nan kenan".
"Idan ma akwai abun da ya fi haka, toh ta zama shi, ni dai anu è ni tiyo fe won mon gbo( tausayin wanda zai aure ta nake ji)." Farida ta fada.
"Wanda zai aure ta ko ya'yan ta, ai ya'yan ta kam sun shiga uku". Wannan karon Mummy tayi magana.
"Bari kawai Mummy".
Haka suka cigaba da hiran su.

Ita kuma Faiza (Olamide), data shiga daki, taje ta zauna akan gadon ta, don daman kowannan su (ita da Farida) na da gadon sa.
Ta zauna tana ta huci, wai ita ce suke kira mai mita, da masifa, ai zasu ga masifa da mita kuwa, dan yau din nan, sai Faiza tayi kuka, shi kuma Hakeem, sai idon sa ya raina fata, dan zata jijjiga su sosai kafun ta koma. Tana cikin tunani, lokacin sallan magrib ya yi, ta tashi ta shiga toilet din dake hade da daki, ta yi alwala, sannan ta fito tayi sallah.

Suma acan waje, suna jin kiran sallah, ko wannan su ya tashi. Mummy ta wuce dakin ta, shima Hakeem ya shiga dakin shi, yayi alwala, sannan ya wuce masjid. Ita ko Farida, tana bakin kofa, ta kasa shiga daki. Tasan indai ta shiga dakin nan, toh akwai problem, dan yau mai ceton ta sai Allah, ko in Mummy ta nuna mata bacin rai.
Sanda taga Olamide ta fara Sallah, kafun tayi sanda ta shiga dakin, ta dauki hijjabin ta, ta fita da sauri, ta wuce dakin Mummy. Nan ma ta samu Mummy ta fara sallah, sai ta shiga toilet din Mummy, ta yo alawala, kafun ta fara sallah.

Olamide na idar da sallah, tayi addu'a, ta nike Hijjab, da sallayan data yi amfani da shi, ta sa kowannan su a mazaunin sa. Data gama, ta zauna saman gado, ta fara dariyan mugunta. Ta ce "zaki gane ai yarinya, bani ba"?





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

"Umma ta, yau fa naji jiki sosai, ji nake kaman ban taba aiki ba arayuwa na" Wan saurayi ya fadi. Kana ganin shi, kasan wanan bafulatani ne, ga shi dogo, amma fa ba sosai ba, dan normal dinan, shiba siriri ba, kuma ba shi da kiba, normal size din nan ne. Ga kyau mashaAllah ba'a magana, gashi fari ga dogon hancin nan kaman pencil, ga idanuwan sa manya manya, yayi fitting din shi sosai.
"Yau aka fara?
Ai kaidaman ba ranan da bazaka dawo daga aiki bakayi complain ba, kuma kullum aikin ke maka wuya". Matar da ya kira Umma ta amsa mai. Itama matan, ba'a magana, tana da kyau sosai mashaAllah, gata ita ba fara ba, kuma ba baka ba.
"A'a Hajiya, bana son kina ma auta na haka fa".wani dattijo ya fada. Toh kana ganin dattijon nan, ka ga saurayin, saboda suna kama sosai, har ya baci. Amma babancin shine, shi wanan ya fara tsufa, shi kuma wanan saurayi ne.
"A'a Abba, kasan wanan yaron is very lazy, abu kadan sai yace ya gaji, yana abu ne kaman mace. Ina ji ma matar ka, saboda ita zata dinga aikin na miji agidan ku". Yayan saurayin ya fada, shi wanan yana kama ne da Umma sak.
"Abba na ka kyale su kawai". Ya na fada, ya tashi yana mika, sanan ya wuce dakin shi.
"Lazy woman kawa" yayan shi ya fada.
"Subhanallah, auta na ba woman ba ne, man ne, kuma a very strong man".
"A'a Alhaji adai fadi gaskiya. Ai wanan ya ma fi woman lazy". Tana fadan haka, yayan shi ya fashe da dariya.
Da ya shiga daki, ya cire tie din dake wuyan shi, ya na yi yana hamma.
"Gaskiya I need to get married, atleast in ina da aure, irin yau dana dawo agajiye, ita zata cire mun tie, ta fara tarba na tun daga bakin kofa, ta amsa briefcase dina, ta hada mun ruwan wanka, kafun in gama shafa mai, ta kawo mun abinci. Gaskiya aure kam akwai jin dadi, no wonder Yaya Sudais na kiba, amma I wonder why almost everyday yana gida, instead ya bari nima in mori su Umma, amma sai yazo suna hada hannu da Umma suna tsokana na". Ya fadi yana murguda baki kaman mace.
Daya gama cire kaya, ya shiga toilet, yayi wanka, yana gama wanka, yayi gab da an kira sallah, kawai yayi alwala kafun ya fita, ya yi dressing, ya fesa turaruka, ya fita parlor, nan suka hada hanya da Abba, saboda by that time Yaya Sudais ya tafi gidan sa.


*WAYE WANNAN SURAYIN?*
Sunan shi Abdallah, shakarun sa 25, medical doctor ne, kuma yana zaune ne da iyayen sa a jahar Gombe. Bafulatani ne gaba da baya. Su biyar iyayen sa suka haifa, Sudais ne First born, sai Bilkisu, sai Wasila, Fadila, sai shi Abdallah, autan su.
Familyn su ba Familyn masu kudi bane, amma alhamdulilah, akwai rufan asiri sosai, gashi kuma Allah da ikon sa, duk yaran suna da aiki masu kyau, hatta matan, Saboda Alhaji Umar Muhammad Yero baya barin yaran sa suyi aure basu gama karatu ba, sanan sai ya san yanda zaiyi, su samu aiki a wanan kasan tamu da samun aiki nada wuya.
Sunan Mahaifin sa kaman yanda na fada Alhaji Umar Muhammad yero, sunan Mahaifiyar sa Hajiya Rukayya Muhammad Yero.
Abdallah akwai shagwaba tamkar na mace, ba ranan da bazai dawo daga aiki baiyi complain ba, kuma kullum complain din na chanzawa.
Shi mutum ne da baya cika son hayaniya, indai ba da Familyn sa ba, amma in ya fita wajen, zaka rantse bai ma iya magana ba, saboda tsabarage miskilanci irin na sa. Amma agida kam, sai a slow, dan akwai tsokana agida, ga shagwaba. Yayyin sa Mata duka na biye masa sosai, dan duk abun da yake so suke mai, ba su son suga ran sa ya baci. Amma Umma da Hamma Sudais, kullum cikin tsokanan sa suke.
Suna da extended family sosai, kuma every end of the month, suke meeting, nan suke haduwa da duka cousins din su, aunties da uncles. Awannan meeting din ake hada wasu daga cikin su su auri juna, amma if you are so lucky, za'a bari ka auro daga waje, but she must be fulani. Tun lokacin daya fara aiki, shekara biyu kenan, ya san dole fa wata rana ayi tambayan mata, ko kuma ahada shi da cousin din sa, shi kuma kaf cikin su ba wanda ta mai, so duk sanda zasu yi meeting, either yace baya jin dadi, ko kuma ya daure fuska, ko ya zauna shuru kaman baya wurin don kar ma ayi noticing din shi.


~Wanan ke nan~

Da suka dawo daga masjid(shi da Abba), basu tsaya ako ina ba, sai a dinning.
"Umma ina abincin ne, karfa ulcer ya kamani yau" ya fada ashagwabe.
"Kai Auta, ai yanzu zata kawo, ka dan yi hakuri kaji, kuma In Sha Allahu bazaka kamu da ulcer ba". Abba ya fada yana jan hancin shi.
"Kama mutu ne ba ulcer ba. Kana zaune anan ba zaka zo ka taya ni dauko abincin ba, amma kana mu maganan ulcer, ya dadde bai kama ka". Umma ta fadi tana dauke da kuloli.
"Haba Hajiya, auta ne fa"? Abba ya fadi yana zaro idanuwa nan nashi kaman zasu fado,dan mashaAllah, Abba kam akwai manyan idanuwa, kuma kaman yanda kuka sani, magaji mafiyi, so Abdallah ma akwai su mashaAllah.
"Fada mata Abba, ni na rasa abun da yasa ta tsane ni" ya fada yana faking din kuka.
"Mtchwwwwww" Umma ta ja tsaki, sanan tace "ka tashi kaje kitchen, zaka ga plates da spoons, da cups, ka kawo su dinning".
"Duk wannan ni kadai zan dauka, haba Umma nifa na miji ne, kuma mata aka sani da shigan kitchen ko Abba na "? Ya fada ya na kallon Abba.
"A'a ni ban san da wanan ba, saboda baya cikin Alqur'ani ko hadiths".
Tunda yaji Abba ya fadi haka, ya san Abba bazaiyi bailing din sa ba, ya tashi ya tafi kitchen, ya kwaso abubuwan da Umma tace ya kwaso, daya bayan daya, sanan Umma tayi serving dinsu.
Cikin natsuwa, suke cin abinci, har suka gama, nan ma shi ya washe plates ya kai kitchen, sanan suka dan taba hira, kafun kowanan su ya wuce dakin sa.






〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


Farida na idar da Sallah, sanda Mummy ta bari tayi addu'a, ta ce kilode (meya faru), me yasa bakiyi adakin ku ba"?
"Wallahi Mummy Aunty ce, mon beru (ina jin tsoro)."
"Manta da ita, ba abunda zata miki kinji ko"? Mummy tayi magana tana daga gira.
"Toh Mummy Allah yasa. Kinga ma na manta ban dauki night wear dina ba".
"Karki damu, in muna cin dinner kije ki dauka kinji".
"Toh Mummy na". Ta fada
Da Hakeem ya dawo, yaga parlor, ya ga wayam, shima ya shige dakin sa.
Abun ba wuya, har ankira Isha, nan ma yaje masjid, Mummy da Farida su kayi tare adakin ta, ita kuma Olamide tayi adakin su. Kowanan su na idarwa, yayi addu'a, duk suka fito daga dakunan su. Daman suna idar da Isha, suke fitowa dan suci dinner.
Farida na ganin Mide, ta manne ajikin Mummy, tana tsoron karta cafko ta, itako ko ajikin ta, dan kitchen straight ta tafi, ta fara kwaso kuloli, da kayan da zasu ci abinci da shi, ta kai parlor, tasa masu a tsakiyan parlor akan center Capet.
"Yau kuma ba'a dinning zamu ci ba"? Hakeem ya tambaya.
Mide ta mai shuru, kaman ba da ita yake ba.
Farida ce tace "ka manta ta ce bazata yi magana da kowan nan mu ba".
Hakeem ya fashe da dariya, ya ce " ai na manta ta zama kurma".
"Ni kam ba ruwa na, ka ga dai saboda da kai yanzu ina cikin trouble ko".
A fusace ta ce "kuyi shuru ku ci, ko kuma ku tashi mana anan".
"A'a e ma binu (a'a kiyi hakuri), ba zamu kara ba" Farida ta fadi.
"Ni kam zan cigaba". Hakeem ya fada yana dariya.
Abun ya bata mata rai sosai, sai ta ja tsaki ta bar wajan. Tana tashi, Farida da Mummy suka kalli Hakeem, Farida ta ce "shikenan ka ja mana wani masifan, kai baka san aunty Mide sai da rarrashi ba, ga shi ban dau nyt wear dina ba" ta fada kaman zatayi kuka.
"Ni kam Farida ki daina damun mu da maganan night wear, ba zaki rasa adaki na ba. Kai kuma Hakeem, ka san yanda zaka lallabi yayar ka, ta daina fushi, dan kai kaja komai".
Ya ce "toh" yana wani hura hanci.
"Amma Mummy kin san ba zata saurare ni ba yau, sai dai gobe in Allah ya kai mu".
"Allah ya kaimu". Mummy ta fada.

"Amin" Hakeem da Farida suka amsa.


Aranan, ran Olamide abace tayi barci.






```Ya kuka ga wanan salon?
Allah yasa dai kunji dadin shi.```




Thanks for reading, karku manta da sharhi, saboda sharhi is life🤪🤪🤪🤪🤪.

Comment
Like & Share




~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

- *MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_








3️⃣&4️⃣



```Dedicating this page to those who commented on the first chap, I love you guys loooooooooooods.```






_Bismillah_






Around 3:30 am na dare ya tashi, yayi sallan dare, yana yi har lokacin Fajr yayi, ya yi raka'a taini fajr, sanan ya fito parlor, suka hada hanya da Abba, suka je masjid.
Da suka dawo kuma, tunda yana da dutyn safe, ya fara shirye shirye.
"Ya ilahi, gaskiya I need a wife. Da ina da mata, duk wannan shirye shiryen ita zata mun. Kawai sai dai inji tana tashi na, ta ce qalbi ka tashi kayi wanka, ta cire mun kayan da zan sa, ta sa mun coat dina da briefcase di na waje daya, ta ciro mun covered shoe dina, shima ta sa mun a one side. Ina fita kuma ta mika mun ina sawa, in ta gama dressing dina, sai tace qalbi muje dinning ka ci breakfast. Ba kaman Umma ba, da zata dinga mu fada. In kuma na gama cikin breakfast, sai ta rike mun briefcase, ta raka ni har mota, sannan ka fun in shiga, tayi hugging dina, sai in shiga mota, ta mika mun briefcase, ni kuma in diga mata flying kisses, sannan in kuna mota, ita kuma ta dinga waving dina har in bar haraban gidan mu". Ya fadi ya na wani irin smile.
"Amma gashi yanzu ni ke komai. Da ma lokacin da adda Fadi take nan ne, maybe data mun. Duk da cewa muna fada sosai, dan ita nake bi, still na san zata mun". Ya fada with frustration.
Haka ya ita surutun shi shi kadai, har ya gama shiri, ya fita ya je dinning, ya ga ba kowa. Tun dama da kyar suyi breakfast tare inba weekend ba, ko kuma ran da yake da dutyn rana. Rai abace, ya shiga kitchen. Yana son ya fara girka indomie, yaga note akan kula. " ka ci, ba dan halin ka ba". Yana ganin handwriting din, ya san na Umma ne. Sai ya saki murmushi, ya dauki abincin, ya kai dinning, ya ci. Sanda ya koshi kafun ya kwashe kwanonin, ya kai kitchen. Daya gama kintsa komai, ya je dakin Umma, ya mata sallama, ta mai adawo lafiya, da addu'oi, ya je dakin Abba, shi ma ya mai, sannan ya fita, ya kama hanyar asibiti.
Yana driving yana bin kira'an sheik Abdulrahman Sudais, sai kawai ya fara addu'an Allah ya ba shi mata, shi ya fara gajiya da irin rayuwar nan, shima yana son yayi kyau kaman Hamma Sudais. Haka ya ita tunani har ya isa asibiti.



〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Around 4:00 Am, Mide ta tashi, daman ita kadai ta kwana, Farida ta kwana da Mummy ne, dan data shiga daki, data sha masifan da bazata taba mantawa da shi ba .
Da Mide ta tashi, ta shiga toilet tayi business din ta, sannan ta yi alwala, ta fito ta fara nafls. Da lokacin raka'a taini fajr yayi, tayi, sannan tayi sallan fajr. Tana idarwa, ta fara karatun alqur'ani, tayi azkar din safe, da wasu addu'oi, sannan ta ninke sallayan, tasa a mazaunin sa, kafun ta fita taje dakin Mummy. Ta shiga da sallama, Mummy da Farida suka amsa. Data shiga, ta tsuguna, ta gaida Mummy, Mummy ta amsa, ta sa mata albarka. Sai Farida ta ce "aunty mi (aunty na), e dakun(please) ki yi hakuri, bazan kara ba". Tayi magana kaman za tayi kuka.
Olamide ko tayi kaman ma bata san tana yi ba. Ta tashi zata fita, Mummy ta ce ta dawo. Cikin respect, ta dawo ta tsuguna gaban Mummy, dan daman Mummy da Farida na zaune ne akan sallaya, Farida na ma Mummy karatun ta da aka masu a islmiyya, ita kuma Mummy tana gyara mata.
Da Olamide ta tsuguna agaban Mummy, Mummy ta ce "wai ni wace irin zuciya gare ki?
Ba yafiya kwata kwata a zuciyar ki. Ya zaki kwana da mutum azuciyar ki, baki tsoron ki mutu, ko kuma shi wanda kika sa arai ya mutu?
Fisabilillah! Ai wannan ba hali bane, ko tun iwa re se (ki gyara halinki), kafun lokaci ya kure maki".
Ran ta abace, amma cikin sanyin murya ta ce "Mumny fa ni kadai kike ganin fault dina fa, baki ganin na su, barin ma Hakeem, kema dai kin ga abubuwan da yake mun, amma sai ki dinga cewa ni ke da fault". By this time, tana magana tana zubar da hawaye.
"Toh ai ke ce

Please Login or Register in order to submit comment