Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali wallahi, bata da wani abun da zaka tsana a jikin ta, although ran Friday nan na san ta, amma ta gama mamaye zuciya na. Ita ce ma tayi suggesting wai in fada a gida, duk abun da aka ce, sai mu sani in zamu ci gaba ne, ko kuma akasin haka. Amma wallahi I don't wanna loose her to another man, saboda duk namijin da ya same ta a mata, ba karamin nasara yayi ba, wallahi she is whom every man dream of, she is the dream of every man to become his wife and a mother to his children, amma matsalan shi ne akwai *BANBANCIN KABILA* a tsakanin mu, kuma when I mean banbanci, I mean a very big one. Although girman arewa ne, kuma according to what she told me, bata ma san hanyar garin su ba, saboda ko iyayen su basu sani ba". Sai yayi numfashi.
All this while, Adda fadi kallon sa take. Ita dai a rayuwar nan, bata taba gani ko ji kanin ta ya yabi wata ya mace ba, sai dai yayi shuru ko ana maganan mata, amma wai shi ne yau yake yaban wata haka, that means she most be soooo sweet, ya zama dole tayi supporting din shi. Amma wani banbanci ne haka a tsakanin su? Ta tambaye kan ta.
"Yana ji kayi shuru, wani banbanci ke tsakanin mu ne haka, ai su Abba sun ce zasu auran maka ko waye, indai ta zauna maka, kuma kana da assurance a kanta".
"Ae indai assurance ne, ina dashi, yaran mu ne matsala, amma in ku family dina zaku yi supporting dina, toh bani da case".
"In Sha Allahu zamu yi, ai you too have always supported us". Adda Fadi ta fada.
"Toh nagode. Bayarbiya ce, amma tana da zubin fulani, inba ta fada maki bane, ba zaki taba sani ba". Ya fada, expression din shi na nuna damuwa.
"Bayarbiya! Bayarbiya fa kace?" Ta fada tana zare manyan idanun ta.
"Ae, amma ai banga wani aibu aciki ba, wallahi tana da hankali. Kuma ai Allah ya halice mu, we are all one in the eyes of the creator. Wallahi you will love her, support din ki kawai nake bukata, in kika yarda, zan kawo maki ita har gida yau, saboda gobe da sassafe zasu koma kano. Kuma ma ba akano take ba, a Suleja take. Karatu ya kai ta Kano kuma acan Sulejan ma, sanannu ne".
"Hmm naji, Allah ne ya halice mu duka, kuma ba wanyanda suka fi kusan ta dashi inba mumine ba, so am ready to accept am sister in law In Sha Allah. Amma kawu fa?
Kasan yanda mutumin nan yake, yanzu zai sa iyayen mu agaba".
"Ki kyale ni dashi, shi din ba matsala bane, ai ya saba yi ana barin shi, this time around zanyi breaking din rules, kuma inyi maganin shi akan iyayen mu". Ya fada yana murmushi.
"Toh mashaAllah, kana da hoton ta ingani"?
"Ae, I snapped her without her knowing". Yana fadan haka, ya ciro wayar sa, ya shiga gallery, a camera, ya samo pics din, ya mika mata. Tana gani tace "wow mashaAllah, attention din ta ma was not on you, amma kalli yanda tayi kyau, gaskiya beauty ce. Kuma nima da baka ce mun bayarbiya bace, dana ce yar fullo ce. Gaskiya yarbawa ma nada kyawawa, kaman yanda ko wani yare ke da kyawawa, da kuma mashaAllah, kasan no one is ugly, everybody is beautiful in there own way, and beauty is in the eyes of the creator. I will like to meet her. Amma ba lokacin biki ne nan ba"? Ta tambaye shi.
"Ae, jiya ne ma, da aka gama daurin aure, me kika gani?"
"Naga bata yi heavy makeup bane, she looks simple but beautiful". Adda Fadi ta fada tana shafa screen din wayar.
"Am telling you, she doesn't like heavy makeup. Toh a bani waya na kar acinye mun wifey". Ya fada yana kwace wayar sa.
"A'a spicy ne, ai nima sister in law di ta ce. Kuma ni bazan yi irin naka ba, inta zo, zamu dauki hoto tare". Ta fada tana hura mai hanci.
"Oho dai, she is will be mine In Sha Allah".

Suna cikin magana, Mijin Adda Fadila ya fito, lokacin sallah zai tafi masjid, sai suka tara hanya da Abdallah, yayi da Adda Fadi, bayan sallah, zai je ya dauko ta, ita kuma tace ya bari sai bayan Asr, alokacin yaran ta sun dawo, kuma ta girka mata abu, gashi yace ba ita kadai zata zo ba, yace mata toh, amma daga masjid, ba zai dawo ba, sai ya kawo Olamide.

A hanyan masjid, Abdallah ya fada ma mijin Adda Fadi komai, ya taya shi murna, bai ba nuna wani shock ba, da Abdallah ya ce mai bai nuna damuwa ba, da shi yace mai bayarbiya ce, sai yace mai, ai Allah ya halice mu duka, kuma daya halice mu, bai ce wannan yaren sun fi wannan yaren ba, ai yarbawan ma mutani ne, in saboda kawu Dajjo ne, kar yaji komai, dan duk abun da Allah yace "Be, it shall be."
Abdallah ya ji dadin maganan sosai, sai godiya ya ke, har suka isa masjid.

Suna fita daga masjid, suka koma gida tare, Abdallah bai shiga ciki ba, ya bude gate, ya fita da moton sa, sukayi sallama, yace sai ya zo da yanma, shi kuma yace Allah ya kaimu, Amin ya amsa, ya ja motar sa, ya bar gidan.
Gida ya wuce direct, ya gaida Umma da Abba, sannan ya koma dakin sa, ya cire kayan daya sa, yasa jallabiya, ya hau kan gado, ya fara barci, da niyyan zai kira Olamide inya tashi, dan daman still a gaijiye yake.




〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Yanda Olamide tayi shuru data gama karanta msg, duka su Nabila ke noticing, sai Nabila ta taba ta, tace "Lafiya kuwa?
Daga karanta msg kuma sai ki kwanta kaman marasa lafiya, ko rasuwa akayi ne?"
"A'a ko daya, na gaji ne kawai, kin san stress." Ta fada tana mika.
"Wani irin stress kenan daga karanta msg?" Nafisa ta tambaya.
"Normal stress mana, wallahi habibty, you can ask silly questions."
"Bawani silly, gaskiya ta fada. Koma me ke damun ki, ki fada mana, we are all friends, ain't we?" Nabila ta tambaya.
"We are. Am just scarred, what if addan sa tayi poising din shi akai na, what if ya daina sona idan tayi poising din zuciyar shi." Ta fada, idon ta ya cika da ruwa.
Sai suka yi hugging din ta.
"I don't think Abdallah will do that, he loves you more than you think, just be positive and stop been negative". Nabila ta fada.
"Like she just said, stop been negative, and be positive, hope for the best".
Sai suka sake ta. Ta daga kai ta kalle su, tace "what will I do without you guys, you guys have be come a part of me wallah, Allah ya bar mu tare. In Sha Allah I will think positive.
Suna Nana ko sai kallon ikon Allah suke.

Ana cikin haka, aka kira zuhur, suka tashi suka yi sallah, suna idarwa, suka ji muryan wasu suna sallama. Daman da aka kira Sallah, Nabila ta koma dakin ta. So tana jin sallama, ta fito, taga kannan Farouq su biyu ne, daman sun saba, sai sukayi hugging din ta.
"Ku zauna, ina ta expecting din Ku tin dazu, me ya hana ku zuwa?"
"Aunty ki bar shirmanmiyan nan Hafiza, kin san ta ai, inba'a ci kwalliya ba, ba'a fita, shi yasa muka dade, hakan ma Umma ta koro mu". Kanwar sa mai suna Nusaiba ta fada.
"Nikam Allah ya yaye maki wannan cutar, dan in kika yi aure, kuma zaku fita da mijin ki, sai dai ya bar ki a gida". Nabila ta fada.
"Uhhmmmmm uhmmmmm, su aunty anyi aure, har ansan logic." Hafiza ta fada.
"Toh kar insan logic ne,
Mtchww. Yauwa kawaye na guestroom, muje ku gaishe su.

Suka gaisa da su Olamide, aka kawo ma su abinci, suka ci, amma still hankalin Mide bai gama kwantawa ba, amma ta kasa nuna ma kawayen ta. Shi daya bar gidan Nabila by 11:30, ace har almost 2:00 pm, bai kira ta ba, hanya kuwa?
Hawaye taji ya jiko idanun ta, sai ta tashi ta shiga toilet kaman zata yi fitsari, ta fara kuka, a hankali, yanda baza su ji ba.
Bata kai 5mins ba, aka kwankwasa kofar toilet, Nusaiba kanwar Farouq, tace "Adda wayan ki na ringing".
Olamide najin haka, ta fito da sauri, ta karbi wayar, tana ganin wanda ya kira ta, ta yi wani irin murmushi, sanda tayi hamdallah, kafun ta daga wayar.
"Assalamu alaikum! Ta fada zuciyar ta na bugawa, although taji dadi ya kira ta, amma bata san sakamako ba.
"Waalaikumus salaam qalbin Abdallah."
Olamide taji wani irin dadi a zuciyar ta, sai ta amsa mai da "na'am ifemi". Tama manta da akwai mutani a dakin. Suko sai kallon ikon Allah suke.
Abdallah ko data kira shi da sunan, sai yaji wani irin dadi na ratsa shi.
"Qalbin Abdallah guess what?"
"Ifemi I am not good at guessing, just tell me".
"Toh shikenan, bazan so inga zuciya na a wahale ba, so, adda Fadi is ready to receive her in law to be In Sha Allah, tace muzo bayan Asr".
"MashaAllah, naji dadi sosai, I thought bazata yarda ba, I thought this will be the last time da zamuyi magana, but mashaAllah she accepted me the way I am".
"Alhamdulilah, she is sooo ready to accept you, ko mijin ta ma yana expecting din zuwan ku. So ku shirya keda habibty, by 4 dot zan zo".
"Toh shikenan, sai kazo".
"Please takecare of my heart, dan bana son inga zuciya na a wahale. Take care of Abdallah's qalbi".
"Okay, you should also take care of mine". Tana fadan haka, ta kashe wayar, sai a lokacin tayi realizing ma akwai mutani a dakin, wani kunya ya kamata, zata koma toilet, Nafisa ta jawo ta. "Dawo nan marasa kunya. Wato ifemi, daman nasan pretending kike, akwai kalamun soyayya sosai abakin ki, sai ki dinga cewa zamu koya maki in lokaci yayi, ai yanzu kam sai dai ki koya mana." Nafisa ta fada tana hararan ta.
"Haba habibty, kya dan tsake ni ai, kin wani rike ni kaman kin kama barauniya, dan Allah tsake ni. Kuma ni bana pretending. Then duk abunda nake yi, awajan ku na koya, especially Nabila".
"A'a kar kiyi karya da ni, mu dai sai mun zo lectures ko Fisa?"
"Gaskiya kam".
Suna na kan teasing din ta, suka ji muryan Farouq ya dawo, da sauri Olamide ta riko hannun Nabila, ta kai ta bakin kofan daki, ta tura ta waje, sai tace "je kiji da mijin ki." Ta fada tana mata gwalo.
Kannan Farouq ma suka fita gaida Farouq. Tayi facing din Nafisa, ta ce "kin san Nabila ce power din ki kuma bata nan, toh ki shiga brain din ki. And yes wai mu shirya by 4 dot zai zo ya kaimu."
"Toh mummy Olamide, amun afuwa, kar a cinye ni. Kuma in kika sa wasa, bazan je ba".
"Haba habibtyn Mide, am sorry my sweet miyan kuka".
"Baki ma ga abunda zaki kira ni ba sai miyan kuka, ba damuwa". Nafisa ta fada tana faking hurt.
Daman kan gado suke, sai Olamide ta riko hannun ta, ta ce "haba habibtyn Mide, ban san ki da fushi ba, ki yafe ma troublesome habibtyn ki."
"Naki, sai an bani cin nose."
"Kaman me?"
"Kaman shawarma". Nafisa ta amsa.
"Amma fa sai mun koma school In Sha Allah".
"Naji bakomai". Nafisa ta fada tana murmushi.
"Amma in na mutu ki yafe mun."
"Ai dole na, Allah yasa mu cika da imani, ya jikan magabata."
"Amin".





Around 4dot Abdallah ya shigo gidan Farouq, ya fara parking, daman Farouq ya san da zuwan shi, sai ya shiga ciki suka gaisa, kafun ya mata text wai gashi nan ya zo. Sanda suka shafa almost minti 10, kafun suka fito. Suka sallame cousin din Nabila, da kannan Farouq, saboda maybe kafun su dawo sun wuce, kuma ma daga yau ai shikenan, sannan suka ma Nabila da mijin ta sai sun dawo.

Da suka fita, Abdallah ya ce su tsaya a inda suke, bari ya kawo motan nan. Suka jira shi, ya kawo motan inda suke, ya bude ma Olamide gaba, akunyace ta shiga, ita kuma Nafisa ta bude bayan da kanta, ta shiga. Sanda suka daidaita zama, sannan yaje gate yana horn, gateman din gidan ya bude gate, suka fita sai gidan Adda Fadi.
Su Olamide sai kale kale suke, shi kuma duk exciting place din da suka wuce, sai ya fada masu sunan, ya kasa boye murnan sa. Nafisa kawai ke magana, ba yanda bai yi da Olamide ta sake ba, amma taki. Ita kuma a bangaren ta, kunya take ji, shi ya hana ta sakewa.
Daya ga yayi yayi bata sake ba, sai yayi tunanin abun da zai fada, yasa tayi magana, wani idea ya zo mai, yace " kin ga garin ifen ki, kuma where you will be staying very soon In Sha Allah".
Tayi murmushi, tace "Allah yasa." Saboda maganan tashi ma kunya ya bata.
Daya ga kaman baza yi magana ba, yayi shuru, domin ya gane kunya take ji.
Haka ya suka yi shuru, har suka isa gidan. The only time din data yi magana, shi ne da suka wuce wani shago, ta ce ya tsaya, dan daman sunyi da Nafisa, zata siyan ma yaran Adda Fadi abu. Daya tambaye su me suke so ya siya masu, tace bakomai, sai yace bakomai ne kuma tace ya tsaya, sanda taga da gaske yake ta fada mai, yace su zauna zai siya, tace mai a'a, ita zata siya, because it's a gift from her, and zata so ta siya da kanta. Sanda yaga ta dage, shine ya kyale ta, amma yace mata Afra ta fi son chocolate, shi kuma Irfan ya fi son sweets, but suna son biscuit, but those are there best.
Da suka isa, instead yayi horn, ya mata flashing, ta fito, ta bude karamin kofar, ya shiga ta wajan, ya bude gate, ya shigo da motar sa ciki, ya gyara parking, sannan ya fita, Nafisa ta fita, sanda Olamide tayi addu'a, ta fito. Tana fita ita da Nafisa suka taka har inda Adda Fadi take, suka gaishe ta, ita kuma tun fitowan su, take ta kallon su, shi kuma Abdallah ya je rufe gate.
Da Olamide taga sun gaishe ta bata amsa ba, ta kara gaishe ta, dan alokacin har tayi give up, sai taji tace "common, you guys shouldn't just stand there, give me hug." Adda Fadi ta fada hannun ta a bude.
A kunyace sukayi hugging din ta. Ta riko hannaye su, tace su shiga ciki, su Afra da Abban su na can.

Suka shiga, Abdallah na biye da su, kuma ya ji dadin yanda Adda Fadi ta tarbe su.






```Thanks for reading, and always been patient, zeexee loves you guys.```





Comment
Like &
Share.




Zeexee ce 🖊️🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*




*SAKON TA'AZIYA ZUWA GA PHATEEMA LAWAL*

Ina me miki ta'aziyan rasuwar kakan ki, Allah Ya ji kan ta, Ya mata rahama, Ya gafarata mata zunuban ta, Ya haskaka kabarin ta, Yasa aljannah ce makomar ta. Sorry for the lose sister, Allah ya baku hakurin rashin ta, Amin.


```Dedicating this chap to those who post my book. Thank you soooo much, I can't thank you guys less, I really appreciate your efforts.```






2️⃣5️⃣&2️⃣6️⃣






Da suka isa gidan Nabila, Abdallah yayi horn, aka bude mai, ya shiga.

Da za su fita acikin motan, Abdallah yace "kinga lokacin sallah ya kusa, da mun dan yi hira. I can't wait for you to be mine, then I won't need any permission to be with you. Dan Allah kaman yanda kika yi alkawari, in Kika koma school, dan Allah ki ma mummy magana, nima zan ma su Abba magana. Kin san annabi Muhammad (SAW) yace; shi bai ga abun daya fi dacewa da mutani biyu dake son juna ba, inba aure ba. So why should we take long on a mere relationship, mu fahimci juna, even if it's for 2 to three months, if we are okay with each other, we should take it further, amma idan vice versa ne, kai Allah ma ya kiyaye, In Sha Allahu zamu fahimci juna. Amma still ya na da kyau iyayen mu su san muna cikin relationship. Am going to miss you so very much, sai na kara zuwa kano In Sha Allah."
"Kar ka damu, zan fada mata. Addu'an shi ne iyayen mu su yarda, ni dai na san side dina ba problem, domin a familyn mu, zaka iya auren kowaye, in as far as yana da addini, kuma yana amfani da shi, sannan in suka yi bincike akan shi da familyn shi, kuma ya zauna masu, toh they are good to go. Gaskiya ne maganan ka, ko ni ma bana son long relationship. Nima zanyi missing din ifemi (my love), amma I will wait for the right time. Kazo fa, inba haka ba, inyi fushi." Ta fada tana rufe fuskar ta wai ita mai kunya.
"Toh shikenan Olamin Abdallah, aka qalbin Abdallah, In Sha Allah, baza'a samu matsala ba ta side din su Abba ma. Karki damu, in iyayen mu suka yarda, maybe wannan hutun naku, akai goron tambaye. And In Sha Allah I will come."
Wani irin kunya ya kama ta, a kunyace, tace "toh, Allah ya tabbatar mana da mafi alheri. Kaga ana kiran sallah, bye".
"Okay bye, take a very good care of my heart please".
"In Sha Allah."
"Toh habibty, nagode da kika bamu time din ki, Allah ya sauke ku lafiya, ya bar ki da Asim."
"Sai yanzu kuka san dani kenan. Amin, nida yaya Asim dina."
"A'a habibty, ai muna sane da ke. Amin, Allah ya bar ku tare."
"Amin. Toh bye". Nafisa ta fada, sannan suka fito daga cikin motan, Olamide nata waving din shi, har ya fita.


Da sallama suka shiga, suka samu Nabila da kannan Farouq a parlor. Nafisa taje tama Nabila side hug, amma sai taga tayi shuru, bata yi reciprocating, su kuma kannan Farouq suka fara dariya, abun ya ba Nafisa haushi, sai tace "meye haka dan Allah?"
Alokacin Nabila ta dago kai ta kalle su one by one, ita da Olamide, sai tace "ai da kun kwana ne kawai."
"Ban gane damu kwana ba?" Wannan time din, Olamide tayi magana.
Suko kannan Farouq, kokarin danne dariya suke, amma yaki dannuwa.
"Ae mana, da kun kwana. Ku da kuka san gobe zaku wuce, amma kuka dade haka, kuma fa kun san duk da cewa zan dawo in the next two weeks, am still going to miss you. Saboda ku ne fa naji bana missing din gida, amma nasan daga gobe kam shikenan, komai zai dawo square one, gobe zan san ae na bar gida, instead ku dawo da wuri ku kwantar mun da hankali, amma sai yanzu kuka dawo." Ta fada tana hawaye.
Olamide da Nafisa suka kalli juna, kawai Nafisa ta fashe da dariya, ita kuma Olamide taje kusa da Nabila tayi hugging din ta, tace "haba my black queen, ki daina kuka please, bada gangan muka ki dawowa da wuri ba. Naso mu dawo tun 6pm, amma Adda Fadila ta ita jan mu da hira, kuma wallahi we thought about this, tambayi Fisa. I know you are going to miss us, and we too will, na san yau din nan, we are meant to be with you, make you forget your worries, but man propose, God dispose, wani sain ba yanda kayi plan abun ke zuwa ba, so ina me baki hakuri, nice sillan haka, so am sorry. Amma if you can stay with us har 10:pm yau, we will pet you, till you get tired ko habibty?"
"Ae mama Olamide. Amma kin san har na fara jin haushin maganan ki, I was even ready to answer you back, ashe shagwaba kika, iye, su bila an iya tada hankalin mutum." Nafisa ta fada tana daga ma Nabila gira, Nabila bata san lokacin data fara murmushi ba, yanda tayi murmushin, ya basu dariya, sai suka fashe da dariya, daman kannan Farouq na danna nasu, kawai sai suka yi bursting at the same time.
Sanda suka yi ma ishi, kafun Olamide tace "bari muje muyi sallah ko uwar shagwaba."
"Ai kuwa, dan in muka biye maki, baza muyi ba." Nafisa ta fada.
"Toh ai nima ban yi ba, daman ina jira ne ku shigo. Amma yaya kam tun 6:25 ya fita, sai kuma my marasa tausayi cousins, masu mun dariya." Nabila ta fada tana hararan su Nusaiba.
"Su kuma suna jiran driver ne inya kawo dinner, su tafi dashi. All the time din da nake complain, suke ta dariya."
"Toh kin ga laifin su ne?
Ko nima nayi dariya bale su." Nafisa ta fada.
"Ni kam a bar surutu, muje muyi sallah." Olamide ta fada.
"Toh uztaziya". Nafisa ta fada.
"Ba zan biye maki ba, saboda baki ki a ita surutu ba har gobe." Olamide ta fada, ta bar wajan, sannan kowan man su ta mara mata baya, amma banda Nabila, dakin ta ta wuce.

Suna idar da sallah, yayi gab da drivern gidan su Farouq ya zo. Nusiba da Hafiza suka yi hugging din su Olamide kaman sun san su daa, harda su we are going to miss you. Suma su Olamide suka raka su har cikin compound, inda suka shiga mota, sai Hafiza tace suyi exchanging din numbers dukan su, suka yi exchanging din numbers.



Sun idar da sallan isha, har sun ci abinci, su uku suna zaune a guestroom, Olamide ta jawo ledojin da Adda Fadi ta bata, ta mika ma Nafisa nata.
"Ina kuka samo wannan ledojin kuma?" Nabila ta tambaya.
"Adda Fadila ta bamu." Olamide ta amsa.
"Very good, nama manta ban tambaye ki how far ba, amma tunda naga haka, nasan it went smoothly." Nafisa ta fada.
"Gaskiya kam it deed, am so happy for you habibty. Kinga yanda ake tarerayan mu ne?
Gaskiya ita da mijin ta akwai kirki. Ga yar su ma Afra, very funny wallahi, kuma akwai saurin sabo, kawai dai Irfan that's second born din ta, ya ke makale da ita, baya barin a taba shi, but everything went smoothly."
"Allah sarki gashi da har kin fara damuwa, kinga this alone is a good sign, gaskiya naji dadi data tarbe ku da kyau, saura iyeye yanzu. Kar ki damu suma din zasu iyi accepting In Sha Allah".
"Allah yasa, dan ni yanzu wallahi duk wanda ya raba ni da shi, zai zama babban enemy na, wanda baya son ganin farin ciki na." Olamide ta fada.
"Kar ma ki damu, In Sha Allahu yaya Abdallah na qalbin sa ne." Nafisa ta fada ta na shafa mata baya.
"Naji dadin yanda

Please Login or Register in order to submit comment