Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nabila ta fada tana murmushi.
"Amin" suka amsa tare.
"Baby, kin ga 6 something yanzu, bari muje mu hada breakfast din, mu maki wanke wanke, kar mu bar maki plates." Olamide ta fada.
"Ai kuwa, the earlier we start, the better." Nafisa ta fada.
"Sai me in kuka bar mun wanke wanke?" Nabila ta fada, tana turo baki.

Basu bata amsa ba, Olamide ta riko hannun Nafisa, suka tafi kitchen, Nabila na biye da su.

Suna breakfast, suna hira, magana daya biyu, sai Nabila ta fada masu yanda zata yi missing din su, su kuma su ita fada mata maganganun da zasu yi calming din ta. Haka suka ita yi, har suka gama hada breakfast din su, suka ci, Nabila ma ta ci da su, sannan suka yi mata wanke wanke, duk da ta nuna masu bata so, amma haka suka yi. Da suka gama clearing din komai, suka koma daki, itama ta koma dakin ta.
Da suka shiga, Olamide ta samu wayar ta na ringing, ta yi suri ta dauki wayar, sunan mummy ya fito a screen din, ta daga cikin murna.
Sun yi 20 mins suna magana, tayi tambayar Farida, Mummy tace tana nan tana shirin school. Daman Hakeem ya koma school shi ma, so mummy da Farida suka rage a gida, Mummy ta masu addu'an Allah ya sauke su lafiya, tace ta ba Nafisa wayan, daga nan suka yi sallama, suka kashe wayan.
Ai ko bai fi 5mins ba, kiran Abdallah ma ya shigo. Cikin kunya, ta daga.
"Assalamu alaikum ifemi."
"Waalaikumus salaam qalbin Abdallah. Kin tashi lafiya, ya gajiyan jiya?" Abdallah ya tambaya.
"Lafiya kalau. Kai fa?" Olamide ma ta tambaya.
"Same alhamdulilah, but I kept dreaming about Mrs Abdallah Umar Muhammad Yero. I can't wait for you to be mine yide am (my love)."
"Me too ifemi, I can't wait. But meye ma'anan yide am kuma." Ta tambaye shi confusedly.
"Aww, ashe sai na dinga koya ma yide am fulatanci." Abdallah ya fada, su biyu suka yi dariya. Olamide ta ce "ae mana, kar azo ana zagi na."
"Haba qalbin Abdallah, bazan taba zagin ki ba, ko wani naji yana zagin ki, mai raba ni da shi sai Allah, sai ni na zage ki?
Toh maybe am mad then. So yide am means my love. Or ain't you my love?" Abdallah ya tambaye ta.
"Aww, ashe ma'anan shi kenan. Of course am your love yide am." Ta fada a kunyance kaman yana ganin ta.
Suna cikin waya, ita kuma Nafisa sai kallon ta take, Nabila ta shigo, tace ma su su fito, yanzu zaa kai su gareji. Nafisa ta tashi, ta dauki handbag din da suka sa kayan su, da side bag din ta, ta ma Olamide signal da hannu ta dauki nata bag din, da wani amebo leda. Olamide tayi nodding kan ta. Sai ta ce "uhmm ifemi, yanzu yaya Farouq zai kai mu gareji, zamu yi waya anjima."
"Okay, kinn ki in kai ku park din. But anyways, in kuka isa park, ki kira ni. Bye, mi yidi ma yide am. Meaning ina son ki masoyiya ta." Abdallah ya fada.
"Bye, mo ni ife re emi na ifemi. Meaning I love you too my love."
"MashaAllah, zan koya maki fulatanci, keh kuma ki koya mun yarbanci. I really love the way this words came out of your mouth, although am not seeing you. Anyways bye qalbin Abdallah." Abdallah ya fada, sai ya kashe wayar.
Ba abun da Olamide ke yi inba murmushi ba, gaskiya Abdallah na faranta mata rai sosai, Allah yasa iyeyen sa su yarda, saboda ta san from her side, bata da matsala, mummy zata yarda, dan a familyn su, akwai wayanda suka auri wasu kabilan.
Ita ma ta sa hijab din ta, ta dauki side bag din ta ta rataya a kafada, sannan ta dauki amebo ledan, suka bar dakin tare da Nafisa.


Da suka shiga parlor, suka samu, Farouq da Nabila na jiran su, su Olamide suka gaishe shi, sannan dukan su suka fita, Farouq ya sa ma kofar key, suka shiga mota, Nabila a gaba su Olamide kuma a baya. Farouq yayi horn, mai gadi ya bude mai gate, ya fita, sai gareji.

Luckily, suna zuwa, akace mutum biyu ya rage motan ya cika, sharp sharp aka yi loading kayan su, nan suka ita hugging din juna, Nabila harda kwalla. Da suka shiga motan, ta yi waving din su, Farouq ya riko hannun ta, suka matsa ma motan ya samu hanya ya wuce, suka ita waving din juna, har motan su ya bace masu, sannan still hannun Nabila cikin nasa, ya bude mata gaban motan ta shiga, sannan ya je driver side, shima ya shiga. Sanda ya ita rarrashin ta, kafun tayi shuru, shima ya ja motan, suka koma gida.

Su Olamide kuwa, motan su na barin gareji, ya kama hanyar barin Gombe, ta ce "kai Habibty, gaskiya garin Gombe nada kyau fa sosai."
"Bari kawai. Am going to miss this state, duk da cewa bamu san ko ina ba, still garin ya kwanta mun. Balle ma, muma fa nan zaa kawo mu, zamu ga garin, har ya ishe mu."
"Hahhhh habibty, wallahi kin ban dariya, wai nan za'a kawo mu." Olamide ta fada tana dariya, data ga mutani na kallon ta, ta rufe fuskan ta da tafin hannun ta.
"Toh daa karya nake, kema dai kin san nan zaa kawo mu, inda rai da rabo In Sha Allah." Nafisa na rufe baki, wayar ta ya fara ringing, sunan Asim ya fito, sai ta kalli Olamide, ta daga mata gira, tace " bye sweety, ki kira ifen ki."
Nan Olamide ta tuna yace ta kira shi in suka isa gareji. Sai ta dauki wayar ta, ta fara kiran Mummy, ta sanar da ita motan su ya tashi, suna hanya, mummy ta yi masu addu'a, sai ta kira Hakeem ma, tace mai ga shi gari kusa kusa suke da school din sa, amma ba halin su hadu. Suka dan yi hira, kafun yace mata yana da lectures, zai tafi school, ya masu addu'an safe trip, ya kashe wayar. Zata kira Abdallah kenan, kiran Ummin Nabila ya shigo. Ta daga, ta gaishe ta, ta ita masu godiya, tace ta ba Nafisa, tace Nafisa na waya, ta masu addu'a, suka yi sallama, ta kashe kiran, sannan ta kira Abdallah, har kiran ya katse, bai daga. Yana tsinkewa, bai fi 2mins ba, kiran sa ya shigo, ta daga, tayi sallama, ya amsa. Ya ce "sai yanzu kuka isa gareji, this is 8 something fa qalbin Abdallah, gashi na ita kira, ana ta ce mun line busy, da wa kike waya haka ne?"
"Da mutani nake waya."
"Toh su mutanin basu da suna ne?" Abdallah ya tambaya.
"Nace maka mutani, ka bar wannan zancen, and wish us a safe trip."
"A'a gaskiya bazan iya barin zancen nan ba, why is it so hard ki fada mun sunan su?" Ya tambaya.
"Nothing." Olamide ta amsa.
"Then tell me please, inba haka ba, my mind won't be at rest." Abdallah ya fada.
"Nifa bana son kishi wallahi ifemi. Kuma da mummy, da Hakeem, da Ummin Nabila muke waya."
"Toh what was hard there yanzu. Kuma gaskiya indai kishi ne, sai dai kiyi hakuri, dan ina matukan kishin ki, amma in the right way."
"It's better be in the right way gaskiya, dan ni kam bana son bakin kishi. So wish me safe trip."
"Toh yide am, Allah ya sauke ku lafiya, ya tsare maku hanya, ya kare ku daga sharin karfe, da duk wani sharrin dake kan hanya."
"Amin my young doctor." Olamide ta amsa, tana murmushi har kunne.
"Yauwa qalbi, nima yanzu zan shiga office, so ina Samu break, zan kira ki."
"Okay toh, Allah ya baka saa, banda kallon yan mata." Tana fada haka, ta kashe kiran, tana murmushi.
Shima yayi murmushi, dan yaji dadin maganan ta sosai, wato tana kishin shi, shine take cewa bata son kishi. Daman baya kallon su, gashi yide(love) tayi warning din sa, gashi islamically, it is said to lower your gaze, so abun yazo daidai.

Throughout lokacin da Abdallah yake aiki, yaki kallon female patients, sai dai yaji complains din su, ya karbi card, ya rubuta masu magani, ya mika masu, next patient ya shigo. Haka ya ita yi, har lokacin break yayi, suka hadu da Asim, suka fara zuwa masjid, suka yi sallah, kafun suka aiki wani cleaner, ya siya masu drink da biscuit. Saboda basu son cin abincin a waje, gashi ba wanda ya kawo lunch daga gida acikin su. Never the less, by 2 something zasu bar wajan aiki. Kuma gaskiya sunyi missing din Farouq Sosai, click din su bai yi complete ba without him.


Da Mide tayi cutting din call din, ta dinga murmushi, kaman ya na ganin ta. Bai fi 5mins ba, Nafisa ma ta gama waya. Sai ta kalli Mide, taga fuskar ta na dauke da murmushi, kuma if she could recall, she have been smiling like this for the past 5mins. Ta taba goshin Mide tace "naji jikin ki ba zafi, balle ince high fever ke damun ki."
"High fever kuma, me kika gani?"
"Ae high fever. Keda tun dazu kike ta murmushi, kinga abu na damun ki." Nafisa ta fada.
"Kema haka, saboda kema murmushin kike." Olamide ta fada tana murguda mata baki.
"Kya ji da shi ai." Nafisa ta fada.
Olamide ta sa kan ta saman cinyan Nafisa, tace "barci nake ji, amma in aka shigo garin (Bauchi), dan Allah ki fada mun, saboda ina son inga garin ku."
"Ai dole na, dole na tashe ki kiga garin habibtyn ki. Wai gani zan wuce gida, amma bazan shiga gida ba, this is too bad."
"Baki so zuwa gidan ku ba dai." Olamide ta fada.
"Haba habibty, kema fa kin san tun da muka koma, bamu samu munyi concentrating a karatun mu ba, sai ince mu kara zuwa gidan mu?
Ai sai dai mu kwashi carryover wannan semestern. Moreover ma Abba bazai bari mu zo ba, baki ga ma da kyar ya bari inzo Gombe din nan ba. Cewa fa yayi, inba bikin habibtyn ki bane, ba zaki ba. Sanda na ita explaining, Ummi ma tasa baki, kafun ya bari." Nafisa ta fada.
"Toh naji Hajiya, ni dai in muka iso BH, ki tashe ni." Olamide ta fada, tana gyara kwanciya.
"Toh naji kasa." Nafisa ta fada.
"Oho koma meye, endavour to wake me up, kar kiyi barci fa."
"Naji Mrs Yero."
"Yauwa Mrs meye naki ma. Kinga Bila nata Mrs Ardo, ni Mrs Yero, naki fa?"
Sanda Nafisa tayi wani irin murmushi, kafun ta ce "Mrs lacca ce." Nafisa ta fada tana rufe fuska.
"Toh! Harda guntun kunya?
You try Mrs lacca. Yanzu abun yayi sweet. Ardo, Yero and Lacca. Anyways kar ki manta ki tashe ni." Olamide ta fada.
"Naji uwar mita." Nafisa ta fada.
Olamide bata amsa mata ba, dan tasan inta amsa, haka zata ci gaba da jan ta da surutu, har su iso garin (Bauchi), gashi barci take ji.






Abun ba wuya, har sun iso Kano. Daman da suke hanya, Ummin Nabila ta kira Olamide, tace Faeeq zai zo daukan su, ya kai su gidan su Nabila, in suka huta, ya maida su. Kaman tace a'a, sai ta tuna, yanzu Ummi zata ce suna son juna ne, kuma bata son hakan ya faru, tace mata taji.
Suna sauka, daman Faeeq na jiran su, suna sauka, ya hango su, yana ganin Mide ya bata rai, sanda yaga Fisa, ya yi murmushi, yana jin dadi, alanbaran yaga masoyiyar sa, masoyiyar da bata ma san yana yi.

Da sauri, yaje inada suke tsaye, taje ta side din Nafisa, ya ce "sannun da zuwa arewa angel." Sai ya kalli Olamide ya wani harare ta, itama ta maida mai martani. Nafisa ko murmushi kawai tayi, dan ta san yana neman tsokanan habibtyn ta ne. Sai kuma yace "kawo jakar in rike maki Fisa."
"A'a na gode yaya Faeeq." Nafisa ta fada tana mai faking din murmushi.
Yayi yayi da ita, amma haka taki, dan ta san duk abun da yake yi, yi yake dan yaba Mide haushi.

Da suka isa motan, Nafisa da Olamide suka zauna a sit din baya, sai Faeeq ya kalle su, yace "kun san niba drivern Ku bane. Maybe wannan yar yarbawan ta koya maki halin nan, dan gaskiya na san ba haka kike bane."
Maganan shi ya bata ma Nafisa rai sosai, bata son yanda yake ma habibtyn ta. Rai abace, ta fita ta shiga gaba, ta zauna.
Duk yanda yaso ya ja ta da jira, taki amsa mai, sai kuma ya koma yana ta neman tsokanan Olamide, ita ma ta ki amsa mai, daya gaji, yayi shuru.




Da suka isa gidan su Nabila, an tarbe su da kyau, duk da ba Nabila, ummi bata nuna masu banbanci ba, suna shiga, suka gaida kowa da kowa, da shike basu gama komawa ba (yan biki), Ummi tace suje dakin Nabila, suka je, nan suka kira wayanda zasu kira, suka sanar masu sun sauka. Da suka fada ma Nabila suna dakin ta, ta fara kuka, wai ita tayi missing din su, in short tayi missing din komai. Through wayan suka ita rarrashin ta, har tayi shuru. Ummi ta aika akawo masu abinci daki, suka ci suka koshi.
Basu bar gidan ba sai bayan asr.







```Thanks for reading y'all, I appreciate.```




Comment
Like &
Share.



~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_






2️⃣9️⃣&3️⃣0️⃣





_Bismillah_




Da suka koma gidan su (a school), suka gyara ko ina, daman Ummin Nabila ta riga ta basu abincin da zasu ci da daddare. So da suka gama, suka shiga wanka one after the other, sannan suna alwala.

Bayan isha, suka ci abinci, suka kai plate kitchen, kowanan su ta kwanta saman katifan ta, suna dan taba hira kadan, kiran Abdallah ya shigo. Tayi murmushi, ta kalli Nafisa, sai Nafisa tace "na san mai kira, you don't have to behave like this, ki daga kar ya katse."
"What am I doing din, bana son shishigi fa." Olamide ta fada, ta murguda ma Nafisa baki, sannan ta daga wayan.
"Asslamu alaikum!" Olamide ta fada.
"Waalaikumus salaam qalbin Abdallah. Ya kike, ya gajiyan yau?"
"Am fine alhamdulilah, gajiya ma ya koma gidan sa." Ta fada tana dan dariya.
"Baki da dama qalbi. So nace ba, yaushe zaki fada ma mummy, saboda mu san level din relationship din mu.
"Have patience, yau fa na dawo, ka dan bari ko jibi, a lokacin na dan yi settling."
"Jibi kuma qalbi, I don't think I can be that patient, why not gobe ki fada mata please, wallahi I want to know the level of our relationship, ina son in san wani matsayi zamu sa soyayyan mu, mu sani idan zamu yi taking din shi further." Abdallah ya fada yana shafa kai kaman tana ganin shi.
"Toh naji, In Sha Allah gobe zanyi kokarin inga na fada mata. Kai ma, ya kamata ka fada ma su Umma da Abba, ka san dai there decision will also be needed."
"Kar ki damu, amma inaga ba yanzu zan fada masu ba, sai naga na fada ma siblings dina, kin ga zasu samun baki, alokacin da zan fada masu. Kema dai kin san ni zan fara auran wace ba Fulani ba, so a hankali zan bi su. Kuma kinga idan suka yarda, in kika shigo family, ba zasu bari a wulakanta ki ba, kuma zasu duke ki tamkar 'yar su ta ciki." Abdallah ya fada.
"Ban gane ba, ai ba haka muka yi da kai ba, iyaye fa muka ce zamu fada ma?" Olamide ta fada tana kokarin danna fushin ta.
"Na sani, amma irin haka bai taba faruwa a familyn mu ba, ni ne fa na farko, kinga in ina son su yarda, dole sai na bi a hankali. Shi yasa nake son yayyi na su sani, saboda in lokacin fada masu Abba yayi, suma su sa baki, kar abun ya zo masu kaman shock."
"Hmmmm naji." Olamide ta fada, without any emotion.
"Bazan taba yaudaran ki ba, bana son muyi aure azo ana wulakanta ki ne, ina son kowa ya dauke ki da mutunci, ba zan so ace Umma ko Abba zasu sa ki agaba, kinsan aure is a life time commitment, so bana son situation din da zaki dinga samun sabani da surukan ki." Abdallah ya fada calmly.
"Toh na ji, Allah yasa hakan shi ne mafi alheri."
"Amin." Abdallah ya amsa.
Daga nan, suka ci gaba da hiran su. Da suka gama, ta ajiye wayar ta, ta kalli inda Nafisa take, taga tana waya, sai ta kwanta da kyau, ta fara tunanin maganan da suka yi da Abdallah.
Allah yasa dai kar su samu matsala, dan tana ji a jikin ta kaman soyayyan su ba zai taba zuwa ko ina ba, tana ji kaman ita da Abdallah sun kusan rabuwa. Tana tunani tana hawaye. Wai meke sa ake nuna banbanci ne tsatanin mutani, me yasa iyaye basu son yaran su su auri outside yaren su ne, kar Allah yasa irin haka ya faru da ita, kar Allah yasa a raba ta da Abdallah, saboda in aka yi haka, gaskiya ancuce ta, saboda bazata taba mantawa da shi ba.


Da Nafisa ta gama waya, taji shashakan kuka, ta tashi ta je katifan Olamide da gudu, ta daga kan ta. "Habibty me ke damun ki, ko iyayen shi basu yarda bane, dan naji kuna maganan iyaye?" Nafisa ta tambaya.
Sanda tayi kukan ta, har hankalin Nafisa ya tashi, itama idanuwan ta sun yi ja'a, sannan ta ce "a'a, amma ina jin shi a jiki na kaman baza su yarda ba." Olamide ta fada, wasu sabon hawayen na zuba.
"Kar ki ce haka please, tunda bai ma fada masu ba, just be positive, nifa I thought basu yarda bane, kuma kun rabu. Please stop crying, I will cry too if you continue crying." Nafisa ta fada tana goge mata hawaye.
"Naji habibty, amma ina jin tsoro kar hakan ya faru." Olamide ta fada.
"In Sha Allahu hakan bazai faru ba. Toh me ma ya fada maki daya saki kuka haka, nifa indai tun ba'a kai ko ina ba, zaki fara koke koke in kuka gama waya, ni kam ku rabu." Nafisa ta fada jokingly.
"Ji bakin ki, kema ki rabu da Asim mana." Olamide ta fada tana hararan ta, sannan ta labarta mata komai.
Data gama, Nafisa tayi hugging din ta, ta ce "kar ki damu, wannan hanyan da zai yi using ma is okay, kinga idan yayyin sa suka sani, kuma yayi convincing din su suka so ki, toh baza'a samu matsala ba." Nafisa ta fada tana comforting din ta.
"I know, but am just scared wallahi, am very scared." Olamide ta fada, idanuwan ta suka kara cikowa da ruwa.
"Don't be please, don't be scared, just pray for the best." Nafisa ta fada tana hugging din ta.

Haka Nafisa ta ita consoling din ta, har ta daina kuka, suka dan yi hira, sannan suka yi barci.


Cikin dare, suka tashi suka yi sallah, tun daga lokacin suka fara shirin lectures, saboda by 7:30am suna da lectures. Suka ita shire shire. Da suka gama shiri, kowanan su ta dau side bag din ta, tayi slinging din shi a shoulders din ta, duka fita, nan suka hadu da su Hafsat, suka gaisa, su kama hanyar school.




〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️



Shi kuma Abdallah, tunda ya dawo daga aiki, bai wani yi hira dasu ( umma da Abba) ba, saboda yau daga aiki straight gida ya dawo. Yana ta aikin tunani, ya rasa daga inda zai fara, koya fada masu Umma ne ko a'a, nan wata zuciyar ta bashi wai ya fara fada ma yan'uwan sa, amma banda adda Wasila, saboda kanwar Dajjo ce, zata bata alamarin, so hamma Sudais da adda zee kawai suka rage ya fadama, tunda ya gama da side din adda Fadila.
Haka dai ya ita sa'ke sa'ke a zuciyar sa, lokacin sallah yayi, suka tafi tare da Abba.
Although iyayen sa sun yi noticing din shuru shurun da yake yi, basu wani damu ba, saboda daya dawo, ce wa yayi, shi ya gaji sosai, so suma basu wani dame shi ba.

Da suka dawo daga sallan Isha shi da Abba, dinning straight suka nufa, nan ya je kitchen, ya taimaka ma Umma, har suka yi arranging din dinning, suka ci abincin su in peace, ba hayaniya. Da suka gama ma, ya kwashe plates, ya kai kitchen, shi ma yaje ya same su a parlor, dan ya masu sai da safe.
Daya shiga parlorn, Umma da Abba na zaune, suna kallon Islam channel, sai yace "Umma na, Abba na, sai da safen ku."
"Sai da safe kuma?
Yau din ba hira ne, ko gajiyan ne?" Abba ya tambaya.
"Toh shi ne nima na gani ai, wani irin gajiya ne haka?" Umma ma ta tambaye shi.
"Normal gajiya ne fa, am just tired ne kawai, and I will like to rest." Abdallah ya fada.
"Toh shikenan Allah ya tashe mu lafiya." Umma da Abba suka fada.
"Amin ya amsa masu, ya koma daki, alokacin ya kira Mide, suka yi magana.

Da suka gama waya, ya fara tunani, hanya tayi trusting din shi on these kuwa, hanya ba gani take kaman baya son ta ba?
Ya ilahi, this is not easy at all, he is trying to do everything in his power, yaga bata samu matsala da iyayen sa da yayyin sa ba. Indai na sauran family ne, shi bai damu ba, amma iyayen sa are a big part of his life, and he will like them to accept what he wants without problem, amma in suka ki, ya shiga uku, dan bazai so saba ma su ba.

Ahaka ya ita tunani, har ya fara jin barci, ya tashi yayi alwala, ya dawo ya kwanta akan gadon sa, yayi azkar, bai san lokacin da barci barawo ya dauke shi ba.


Cikin dare, ya tashi, ya ita nafils, yana ta addu'a, Allah ya taimake shi, Allah yasa soyayyan su yayi winning, kar Allah yasa a raba su, Allah yasa siblings din sa da iyayen sa su yi accepting din su. Haka ya ita addu'a harda hawaye.
Da lokacin fajr yayi, suka hada hanya suka tafi masjid tare.
Da suka dawo, ya fara shirin aiki, saboda yana morning duty ne, ya shirya cikin suit, ya dau briefcase din sa, da coat din sa, ya shiga kitchen, ya hada ma kan sa shayi, ya zauna a dinning ya shanye, ya dauki lunch din sa, sannan ya je dakin su Umma ya sallame su, daga nan, ya tafi asibiti straight.







```Thanks for reading, nasan pejin yayi kadan, kuyi maneji please.
```


Comment
Like &
Share.



~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖:

Please Login or Register in order to submit comment