Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babba, ya za kiyi, dole ki dinga hakuri. Fushi fa ba abu mai kyau bane. Na san abubuwan da suke miki na bata miki rai, amma su fa a matsayin wasa suka duki komai".
"Toh ni bana son irin wasan. Kullum su ita tsokana na kaman kanwar su. Harda ke ma". Ta fada tana kallon Farida.
"Shekaru nawa kika san na girme ki da shi, shekaru hudu fa, amma in aka fara magana, ke kike leading. Gwanda ma Hakeem, age gap din mu ba yawa, amma ke fa. Ko shi din he has no right or what so ever to disrespect me".
Tana cikin magana, sai ga Hakeem ya shigo. Su na hada ido, ta dauke idon ta. Sanda ya gaida Mummy, sanan ya ce "Aunty ina kwana". Ta ki amsa mai. Ya kara cewa "na san na miki laifi, but I was only joking, wallahi wasa mu ke dake. Amma na ga kaman wasan mu na bata miki rai, saboda haka, ina mai baki hakuri, dan Allah kiyi hakuri, ki yafe mana".
Still tayi shuru, sai hawayen da ke zuba a idon ta. Abu kadan na sata kuka, she is always emotional.
"Haba Olami, ba zaki yafe masu ba, haba my first fruit, you were the first person who made me know how wonderful and exciting been a mother is. Ke ce first din komai na, dan Allah dari jin wan (dan Allah ki yafe masu)".
Cikin kuka, ta ce "na yafe maku, amma ku san irin wasan da zaku dinga yi da ni". Tana gama magana, ta tashi zata fita, Mummy tace ta dawo. Da ta dawo, Mummy ta ce da su, suyi group hug. Su kayi group hug dukan su, Mummy na sa masu albarka.




〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Yana isa asibiti, ya shiga office din sa, ya zauna. Kafun ku sani, har patients sun fara shigowa.
Ya na kiran next, wata budurwa ta shigo, yarinya akwai kyau ba laifi, gata fara. Tana shiga ta gan shi, ta fara gyara mayafin ta, tana gyara kayan ta. Shi ko ya riga ya gano ta, dan haka majority din yan'matan dake shigowa suke. Sai su dinga wani gyare gyare. Wasu ma har cewa suke, zasu iya samun numbern sa incase idan ciwon su ya kara tashi, sai su fada mai, it's either yayi kaman bai ji ba, yana next, wani ya shigo, su kuma su fita disappointed, ko kuma ya basu amsa rudely.
Daya ga gyare gyaren ta bai kare ba, ya ce "can you have a sit please, we still have other patients waiting out there".
Ta gyara murya, ta ce "uhmmm sorry". Sannan ta zauna.
"Toh me ke da mun ki"? Ya tambaye ta.
Ta fada mai abun da ke damun ta, ya rubuta mata magunnuna, ya bata. Ta fita kuma ya zama problem, ta ce "kaman na san ka ".
"Ya ce Allah ko"?
"Ae, dan na san ina ganin face dinnan sosai".
"Hanya kuwa, dan ni ban san ki ba".
" Okay, amma ka san Fadila Umar Muhammad yero"?
"Ae na san ta, ya akayi".
"Haba no wonder, kuna kama sosai. I think ina ganin hotunan ka awayan ta ne. Actually munyi BASUG(Bauchi state university) tare da ita ne, amma snr dita ce, dan tana level 4, ina 1, amma mun shaku sosai".
"Allah sarki, nagode".
"Uhmmmm na ce ba, kana iya bani numbern ka, kaga sai mu cigaba da zumunci ba".
"Numbern na ko na ta, dan naga ita kika sani".
"Na ka, ai ina da nata". Ta fada tana murmushi.
"Toh ai tunda kina da nata, alhamdulilah. Ita kika sani ba ni ba. Please here is the door. Next patient, ya fadi.
She was soo embarrassed, ta dau bag din ta, ta bar wajan.
Ba zata wuci 22 years ba, so ya girme ta.
Tana fita ya fashe da dariya, ya ce "ai ko mata sun kare, ba zan iya zaban ki ba. Na san mata ta na can itama ta kosa mu hadu. Ya Allah Kasa mu hadu very soon". Yana cikin addu'a, patient ya shigo. Bai bar asibiti ba, sai around 2:30 PM. Instead ya je gida, sai ya je gidan adda Wasila. Yana horning, aka bude mai gate. Mijin adda Wasila na da kudi sosai alhamdulilah. Ba ita ce first wife din sa ba, first wife din sa ta rasu, ta bar yayan ta uku, after shekaru hudu da rasuwan ta, ya auri adda Wasila yanzu shekarun su 8 da aure, yaran ta biyu, da Zaynab da Faiz. Su kuma yaran Mijin, da Jamila, Nana Hauwa, da Abdulazeem, amma suna kiran sa Azeem. Akwai zaman lafiya dosai, yaran na son ta sosai, dan bata babanta su da nata yaran ba, duk daya suke awajan ta.
Yana horn aka bude mai, gate, mai gadi na ganin shi, ya ce "a'a auta! Kai ne haka da ranan tsaka"?
"A'a bani bane, kai ne".
Yana fadan haka, shi da mai gadin, mai suna lawali, suka fashe da dariya.
"Kai auta baka gajiya da tsokana. Allah yayi dai yau ka zo Hajiya bata je wajan aiki ba yau".
"Ai na sani mallam, ba asibitin mu daya ba"?
"Awww haka ne fa". Lawali ya fada, yana sosa keya.
"Kar ka damu, in zan fita zamu hadu". Abdallah ya fada, ya je ya gyara parking. Shiko Lawali, sai washe baki yake.

Abdallah na sallama, yaran suka zo da gudu. "Oyoyo uncle! Oyoyo Uncle". Suke ta fada, suna hugging din sa one after the other. Bisa duka alamu dai yanzu suma suka dawo daga school.
Sai ya tambaye su Mummyn su, suka ce tana sama, yanzu muma muka shigo". Zaynab kenan, ta amsa.
"Toh Jebu, je ki fada mata best din ta ya zo".
Zaynab ta bata rai, ta ce "best din Ummi ko best din Zaynab".
"Toh best din Zaynab".
"Yauwa uncle auta". Tana fada ta bar wajan da sauri, kar ya buge mata baki.
"Zaki dawo ai yarinya". Ya fada.
"Me ka kawo mana". Nana Hauwa second born din gidan, shekarun ta 14, tana jss3 ta tambaya.
" Ku da kuka je school, bai kamata a kawo maku kayan dadi ba, kar yazo ya dagula maku lissafi".
"Kai! Uncle auta, ka iya zuki". Jamila babban cikin su, wanda shekarun ta 15 yanzu, kuma tana ss1 ta fada, ta bar wajan da sauri, dan ta san halin shi, yanzu zai bubbuga mata baki.
"Ai da ke da Zaynab, mai kwace ku sai Allah. Ni na maku kama da autan ku ne?
Wannan munmunan autan na ku" ya fada yana kallon Faiz.
"A'a kar ka bari mu fara, ka daina ce ma handsome dina ugly tohm". Adda Wasila ta fada.
"Ko dan gaisuwan nan babu, sai fada? Ko kema kin shiga group din su Umma ne"? Ya fada yana bata rai.
"Na isa?
Ai ban isa ba. Toh autan mu, ka zo lafiya? Ya aiki yau"?
Ya amsa mata, daga nan suka fara hira, suka ci abinci. Suna gama ci, suka kara taba hira. Suna cikin hira, ta ce "Abdallah!" yana jin yana yin yanda ta kira sunan shi, ya san akwai magana kenan.
"Na'am adda". Ya amsa.
"Yaushe zaka yi aure ne?
You are not getting any younger".
"Hmm adda kenan, zan yi, lokaci ne bai yi ba. Ko nima na kosa inyi, amma har yanzu ban samu wace ta mun ba". Ya fada.
"Kar ka tsaya ruwan ido, inba haka ba, ka kwaso nonsense. Kuma kana wani cewa baka samu kowa ba, yan'matan dake family fa?
Ga yaranan kyawawa, ga kyaun hali, amma kace baka samu ba"?
"Ba haka bane, I don't just have interest in them. Basu zauna mun a rai ba. Amma na san My wife na can tana jira na, lokacin haduwan mu ne kawai bai yi ba".
"Toh Allah yasa ahadu soon, inba haka ba, kawu Dajjo ya hada ka da wata acikin family".
"Ba amin ba, In Sha Allahu soon zamu hadu".

Bai bar gidan ba sai 5:PM.


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


"Toh goge hawayen ko". Mummy ta fadi.
Olamide ta goge hawayen ta, ta ce "Mummy ban san abun da yasa nake kuka haka ba, kuma bana iya controllimg din shi".
"Kya koya ai, in kika yi aure, zaki koya".
Olamide ta sa hannu agoshi, ta ce " Mummy abu kadan kice aure. Ni kam ba yanzu zanyi ba, kuma ma fa bani da ko mashin shini".
"Hmmm, bari in bar maku dakin". Hakeem ya fada.
"Nima haka". Faiza ta fada.
"Dawo nan munafs. Yanzu in kuka fita, ba abun da zaku yi in ba munaf ba". Olamide ta fadi
"Kul, ma ban be awon omo mi ni munafukai( kar ki kira mun yara na muna fukai)". Mummy ta fada.
"Toh alhaja Mummy". Olamide ta fada.


Ko wanan su ya fara morning duty din sa, da suka gama, suka ci breakfast, Farida ta je school, su kuma suka koma dakin su.


"Aunty Mide, ina son in danyi wani dan talk da ke" Farida ta fada.
"Ina ji, kuma ki fadi sensible thing, inba haka ba ki sha mari".
"Am serious fa". Ta fada tana making serious face.
"Toh am all ears darling Faree".
"Daman akwai wani ne, cousin din su Eyman, ya ce wai yana so na, baki gan shi ba, yana da kyau sosai fa". Farida ta fada.
"Zo, matso kusa". Olamide ta fada.
Farida ta matso kusa da ita. Sai Olamide ta taba wuyan ta, ta ce "gashi jikin ki bai yi zafi ba, toh me zan ce yana damun ki".
"Aunty fa am serious. Ai kin san Eyman, wanan kawa ta din nan yar Maid, kin san how much I love kanurai ai".
"Ki tashi anan kafun inyi ball da ke. Kina ss2, intsead ki dinga tunanin yanda zakiyi passing din third term exams din ki, kina tunanin na miji, ko ni nan banda saurayi, kuma ina 300l. Common ki tashi kije kiyi assignment dinki kafun inyi ball da ke".
Afusace, Farida ta ce "ko dan wanan halin na ki, ba zaki samu saurayi ba". Tana fada ta bar dakin.
Ita ko Olamide, maganan ya dame ta, maybe maganan Farida gaskiya ne, shi yasa haryanzu bata samu saurayi ba. Amma kuma to hell, ta san lokaci ne baiyi ba, dan in lokaci yayi, ko cikin rami aka sata, sai sun hadu da mijin ta".





Thanks for reading, ayi sharhi abeg, because sharhi na oxygen ooooohh🤭🤭🤭🤭🤭.




Comment
Like & Share.





~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*






_____________________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
______________________________________







*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*







5️⃣&6️⃣




```Am dedicating this page to my washi Wasila, aka washi buje🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭. I love you wujiga wujiga``` 🤣🤣🤣








_Bismillah_






Abun ba wuya, yau Olamide ta koma school. Faridan data ce tama fi kosawa ta wuce, ita ta fara kuka, wai zata yi missing din ta. Kuka take sosai, har ta sa Mide ma kuka. Hakeem da Mummy ko sai kallon ikon Allah suke. Har gareji suka raka ta, nan ma sanda suka yi kuka. Daman ko man fada da argument din da zasu yi, basu iya rabuwa da juna, Farida da Mide na mugun son juna. Shima Hakeem, ya na son sisters din sa kaman ran sa. Ita kuma Mummy, kwanciyar hankalin ta bai wuci taga kan yayan ta a hade ba.


"My Faiza! Welcome back to school dearie". Kawar ta Nafisa ta fada.
"Oyoyo my Nafy". Olamide ta fadi, sannan suka yi hugging din jun.
"Nayi missing din ki like crazy wallah". Nafisa ta fada.
"Awwwn, nima fa nayi missing din ki. All those fight, wasan da muke a kan hanya kaman yara, ko kuma duk wanda yayi approaching din mu, mu sille shi tas, sannan mu zo muna tsoron kar azo akama mu, da dai sauran su".
"Wallahi fa kawa ta. Ko kuma randa bamu jin yin girki, mu ita shan garri hhhhhhhhh".
Olamide ma tayi dariya, ta ce "ai Nafy muna tsiyan mu yanda muka ga dama. ".
"Am telling you bea".
"Toh yanzu dai mu bar surutu, ki taya ni daukan kaya".
"Aww nama manta, wallahi ganin ki da nayi yau, yasa ni nishadi sosai mama na".
"Allah sarki, nima am soo happy to be with you again mama na" sai suka yi dariya. Daga nan, Nafisa ta taya Olamide daukan kayan ta, har cikin dakin su. Daman a off campus suke. Tun suna level 1 suka hadu, lokacin Olamide na neman abokiyar zama, ita kuma wannan na neman daki. Haka dai suka hadu, tun lokacin suke zama tare, sai Allah yayi kuma halin su yazo daya, ga shi department din su daya. So komai nasu tare suke yi. Ita dai Nafisa yar Bauchi ce, ita kadai iyayen ta suka haifa. Mahaifitar ta fulltime house wife ce, mahaifin ta kuma yana aiki ne a ministry of works. Although ita kadai ce, iyayen ta basu shagwaba ta ba ko kadan.
Da suka kai komai ciki, suka gyara ko ina. Daman tun jiya which was saturday Nafisa ta dawo, ita kuma Mide ta zo yau which is sunday.
"Allah sarki kawa ta, na san kina jin yunwa ko, bari in kawo maki abinci".
"Kaman kin sani Fisa baby, ban ci komai ba ahanya".
"Ai nasan halin ki". Nafisa ta fada, sannan ta kawo mata rice and stew, da nama, sai ta hada mata Fresh, strawberry flavour cikin jug, sannan ta sa mata agaba, da cup din da zata dinga sha da shi.
"Nagode sosai habibty, Allah ya bar mun ke. Kin ga bari in cire hijjabi, sai inyi justice akan abincin nan. Dan Allah kema kawo chokalin ki, muyi justice tare". Olamide ta fada, tana cire hijjab.
"Ai habibty, kema kin san ba zan ki ba, sai munga karke rice din tab, if possible ma mu cinye naman".
"Gaskiya ne, nima na kawo stew ai, ga kuma soyayye nama".
"Nima na kawo soyayya. Mu cinye na stew dina yau". Nafisa ta fada.
"Allah ya bamu sa'a toh".
"Amin mama na. Gwanda muji dadin mu yanzu, kafun lokacin scarcity ya hantayo".
"Gaskiya kam". Olamide ta fada.
Su biyu suka rike spoons, Nafisa ta ce "it's time mr rice, 1, 2, go".
"Bismillah suka fada atare, sannan suka fara ci.

Sanda suka ci suka koshi, har su ka kasa tashi, sai suka kalli juna, suka fashe da dariya.
"Gaskiya Mide muna tsula tsiya".
"Bari kawai, am soo happy Allah yasa mun hadu".
"Ko ni fa. Tunda mukayi two weeks, na kosa adawo, na fara missing din ki. Kinsan agida banda abokiyar hira in ba Ummi ba".
"Allah sarki my habibty. Ai nima in fada maki, sanda muka samu matsala da su Hakeem last week".
"Ai na san za'a rina. Ai ba vacation din da baza kuyi fada ba".
"Kyale su, yaran nan sun raina ni ne. Amma yau da zan dawo, kinga yanda muke kuka ne, ni da abokiyar, kaman irin za'a kai amarya dakin ta". Sai su biyu suka fashe da dariya.
"Yauwa ga ruwa nan nayi plugging, ki duba in yayi zafi kiyi wanka ko habibty"?
"Yes Mummy habibty". Mide ta amsa.
Olamide ta duba ruwan, taga tayi zafi, sai ta juye, sannan ta shiga toilet tayi wanka, kafun ta fito, aka kira sallah, ta yi alwala. Da ta fito, ta shirya cikin night wear din ta, ita kuma Nafisa ta shiga tayi alwala, itama tazo suka yi sallah. Da suka idar, kowanan su ya ninke hijjabin sa, Olamide ta ninke masu sallaya.
"Gobe zamu fara registration ko"?
"Ae, it's going to be stressful wallahi".
"Gaskiya it's going to be. Kinga muna idar da sallan isha, zan yi barci".
"Nima haka, amma zan dan karanta wani sabon book ne, mai suna Uncle sadiq".
"Toh, waye marubuciyar"?
"Eyman".
"Aww, harta fara wani"?
"Ae ta fara".
"Kai! Ni dai gobe zan fara karantawa". Olamide ta fada.
"Toh Allah ya kaimu. Yauwa kina karanta izzar mulki ma by Hafsat Khalil, da mijin Zarah by Phateema lawal"? Nafisa ta tambaya.
"Ae, mai zai sa inyi missing?
Kin karanta Mahakurci mawadaci by zeexee"? Olamide ta tambaya.
"Dole na ai, na karanta. Yanzu ma tafara wani, mai suna babancin kabila". Nafisa ta fada.
"Ai na fara katantawa". Olamide ta amsa.
"Toh masha Allah, novels din su nada dadi fa sosai".
"Gaskiya kam". Suna cikin hira, aka kira isha, sannan ma suka yi sallah, Olamide ta hau katifan ta, ita ma Nafisa ta hau nata.
"Sai da safe" Olamide ta fada.
"Allah ya tashe mu lafiya". Nafisa ta amsa.
"Amin. Kar dai ki dade, kinsan akwai sallan dare ko"?
"Ae, bazan dade ba In Sha Allahu". Nafisa ta amsa.





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Da Abdallah ya koma gida, Umma kadai ya samu cikin parlor, tana kallo.
"Assalamu alaikum my darling Umma, na same ki lafiya"? Ya fada yana hugging din ta.
"Waalaikumus salaam my troublesome son".
"Kai Umma, kin iya ruining din moment, wai troublesome son, abun da zaki ce My handsome son, ko my cool and quite son" ya fada ashagwabe.
"Ohh ni Rukayya! Ya zan yi da kai ne, shagwaba sai kace mace"?
"Toh ni Umma wani shagwaba na maki yanzu"? Ya kara magana ashagwabe.
Da Umma ta daga hannun zata dake shi, ya tashi da sauri. Ta ce "zan kama ka ai. Ai ni da ace kai mace ce ko, ai da anga uwar shagwaba da laziness, da mijin ka ya sha wuya. Amma alhamdulilah, tunda kai na'miji ne, kaga inka fara samun responsibility akai, maybe ka dai na".
"Umma ai in fada maki, mata ta shagwababiya ce, sai dai mu ita zuba ma juna shagwaba. Kuma dan Allah Umma kar ki buge ni, yau din nan na dawo agajiye ne, aikin nan is not easy at all".
"Ni kam rashin kunyan ka har ina, Allah dai Ya shirya mun kai. Kuma tun da ka shigo, nake ta jiran ka mun complain, naji shuru, nayi zaton ka chanza ne, amma ina mai hali baya chanza halin sa. Kai da tun 2:30 ka bar aiki, sannan kaje gidan Wasila, sai ka zo yanzu kace ka gaji. Aiki kaje mata ne"? Umma ta tambaya.
"Kai Umma, ni dai kawai baki sona. Abu kadan ina fada, shikenan zaki fara mun fada, ina Abba na ya ke, dan shi kadai ke sona yanzu". Ya fada ashagwabe.
"Gani nan dan albarka". Ya ji muryan Abba. Daya juya, yaga yana shigowa ne daga waje, he was thinking maybe yana dakin sa ne. Bisa duka alamu, fita yayi.
"Oyoyo Abba na mai so na". Ya fada yana kallon Umma, sannan yayi hugging din shi.
"Can ta matse muku". Umma ta fada.
"Oyoyo my Auta. Ya aikin yau, hope dai bai gajiyar da kai ba ko"? Abba ya tambaye shi, hannun Abdallah acikin nasa, suka zauna tare.
"Ai Abba na ka bari kawai, na jijjigu yau sosai".
"Allah sarki Auta na, sannu. Ka dinga hutawa fa". Abba ya fada.
"In Sha Allahu" ya fada, yana ma Umma gwalo.
"Au ni ko, zaka sani ai".
"Abba kaga Umma ko, ban mata komai ba fa". Ya fada kaman zaiyi kuka.
"Kayi hakuri ka kyake ta, kishi take, kasan ba mai nuna mata irin wannan son".
"Haka ne, Hamma Sudais bai zo ba yau, shi yasa". Abdallah ya fada.
Umma ta kada kai, taki amsa masu, dan ta san indai ta amsa, haka zasu cigaba da tsokanan ta.
"Kaje kayi wanka, ka warware gajiya. Then In Sha Allahu yau bayan Magrib, ina da magana da ku". Abba na gama magana, ya bar parlorn, ya wuce dakin shi.
"Toh Allah ya kai mu".Umma da Abdallah suka fada atare.
Shima ya tashi, ya bar parlorn, ya je dakin sa.

Yana gama wanka, yayi alwala, ya fito, yayi dressing cikin ash jallabiyan sa, ya fesa turare, sannan ya fito parlor, suka hada hanya suka tafi masjid tare.
Da suke hanya, dan masjid din na can kasan gidan su ne, Abdallah ya ce "Abba, akan me zaka mana magana, ka dan bani clue mana".
"A'a, ka bari in muka koma gida zaka ji". Abba ya fada ba sign din dariya afuskar sa.
"Toh Abba". Abdallah ya amsa.
Daga nan ba wanda ya kara magana acikin su, har suka isa masjid.
Suna idarwa, suka kama hanyan gida.
Acan gida ma Umma ta idar da sallah, tana jiran su aparlor. Tana ta tunani, mai Alhaji yake son fada masu ne haka, Allah yasa dai su ji alheri.
Har suka dawo gida, basu ce ma juna komai ba, nan hankali Abdallah ya tashi. Wanan da Abba bai danyi hira da shi ba ahanya, toh abun da Abba zai fada, must be very serious.

Suna isa gida, suka yi sallama, Umma ta amsa. Ko wanan su ya samu wuri ya zauna, sanan Abba ya gyara murya. Ya fara magana. "lokacin da na fita, Baffa Dajjo ya kira ni, yace inzo gida, naje. Da muka gaisa da shi, sai ya ce mun wai yana da magana ne akan Abdallah". Ya fada yana kallon Abdallah.
"Kuma gaskiya maganan daya mun, ya taba ni sosai. Kuma dai kun san yanda yake, inya fara yarba ma mutum magana, especially mu da yake ganin mu as low class". Abba ya fada.
Ran Abdallah ya baci sosai, dan yasan mutumin nan, ba abunda bazai iya fada ba, kar Allah yasa ma yayi embarrassing din abban sa ne.
"Kuma dai kun san shi, bayi da mutunci".
"Ae" Umma da Abdallah suka amsa.
"Maganan akan auran Abdallah ne". Abba ya fada yana kallon Abdallah. "Wai yaushe zaka yi aure ne, wai shi yanzu yana expecting kace ga wanda kake so, amma shuru. In kuma baka samu bane, wai baga yan mata nan da yawa acikin gida ba, mai ya hana ka zaban daya acikin su. Na ce mai ban sani ba, sai fa ya hau ni da fada, wai bamu iya training ba, duka yaran mu da nasu salon, Sudais kawai ya auri yar family, wai kar mu bari ya maka na dole. Ni yanzu ina son ka fada mun ne, baka da kowa ne"?
"Allah sarki Abba na, ban ji dadin abun da Kawu Dajjo ya maka ba, kuma In sha Allahu zan nema. Wallahi Abba na, dukan su ne basu da features din da nake so, they are just indecent. Sai ma sun zo asibiti, su dinga misbehaving. Amma nasan In Sha Allahu na kusan samun wanda ta mun, In sha Allahu ba zan baku kunya ba".
"Hmmmmm, gaskiya bana jin dadin abun da mutumin nan ke yi. Ya bi ya raina mu haba. Ni kam kar ma ka kawo mun wata yarinya cikin familyn nan gidan nan". Umma ta fada.
"Gaskiya ko ni am not in support ka auri yaran nan. Allah ya kawo maka ta gari".
"Amin ya rab".
Aranan dukan su sun yi shuru, ba mai ma wani magana. Duk basu ji dadin abun ba.
Shi kuma Abdallah, abun ya masa yawa, ga takaicin abun da kawu Dajjo ya ma Abba, ina

Please Login or Register in order to submit comment