Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_





```Dedicating this chapter to zeexee's novel group one and two, I love you guys so much, Allah ya bar mun ku.```





3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣





_Bismillah_





*BAYAN SATI BIYU*



"Mun yi magana da adda Zee, kuma kin san surprising thing din?" Ya tambaya.
"A'a ban sani ba, sai ka fada."
"Ina fada mata, tace mashaAllah, at least someone in our family has liver." Ya fada yana dariya, itama ta fashe da dariya.
"Wato kai ne first to break the rules."
"Exactly, haka hamma ma ya fada, wai zasu bani award."
"Gaskiya kam ya kamata." Ta fada.
"Hmm, kin san me?" Ya tambaye ta.
"A'a." Ta amsa.
"Naji dadi lokacin dana kira Hakeem, kuma ya mun magana with respect, amma fa yayi warning dina, wai in na sake na bari aka wulakanta ki, ko kuma na saki kuka, toh indai shi ya ji, sai ya manta da cewa na girme sa, shi zai mun tatas." Abdallah ya fada yana dariya.
"Haba! Gaskiya ne, ashe yana so na, baya son bacin rai na." Olamide ma ta fada tana murmushi kaman yana ganin ta.
"Gaskiya yana mugun son ki, ya mun warning fa da yawa, wasu are a secret."
"Toh ai tsakani na da kai ba secrets." Olamide ta fada.
"Haqqun babu, amma wannan tsakani na da junior bro dina ne." Abdallah ya fada yana danna dariyar sa.
"Toh shikenan, ai nima ina da snr bro yanzu, ga snr sisters."
"Oho dai, nima ina da junior sis ai." Abdallah ya fada.
"Ca'an ta matse maku. Ni dai yanzu su Abba suka rage a picture din, yaushe zaka masu magana." Olamide ta fada worryingly.
"Me kike ci na baka na zuba ne sweety, kinga yanzu yayyi na sun yarda, kuma they are in support, kinga na su Umma minor ne, ga adda Wasila kuma, amma karki damu zamu yi maganin ta." Ya fada
"Na ji, amma wallahi ina tsoro. Athough mummy ta yarda, bata da wani matsala, amma kasan without su Abba, our relationship is still in the root, shi yasa na damu, ina son in san position din relationship din mu." Tana gama magana ta numfasa.
"Kar ki damu, bana son inga ki cikin damuwa, kawai mu ci gaba da addu'a, sannan face your book, kinga kun fara test, ba zan so ki samu matsala ba, cause I won't be happy about that." Abdallah ya fada seriously.
"Toh naji, amma gaskiya hankali na bazai kwanta ba sai naji reaction din su suma." Olamide ta fada.
"Kar ki damu, keh dai ki ci gaba da yin addu'a, everything will be alright, In Sha Allah kaman yanda muka yi nasara akan sauran, haka zamu yi nasara akan su Abba ma." Abdallah ya fada.
"Amin. Kaga gobe ina da test, bari inyi karatu." Olamide ta fada.
"Okay toh, Allah ya baku sa'a ke da habibty, ayi karatu fa da kyau, amma kar kiyi stressing din kan ki, sannan kuma ki kwantar hankalin ki, everything will ba alright In Sha Allah." Abdallah ya fada in a comforting way.
"In Sha Allah naji, kar ka damu, zan yi focusing."
"Yauwa Olami. Bari in bar ki kiyi karatu, sai fijir yide am, meaning good night my love."
"Good night, Allah ya tashe mu lafiya." Olamide ta fada, sannan ta kashe wayan.




Ran da Olamide ta fada ma Mummy, Mummy taji dadi sosai, dan Olamide bata taba mata maganan saurayi ba, she was so happy, especially ma data ce he is ready for marriage, no wastage of time. Lokacin da ta fada mata bafulatani ne, Olamide was somehow expecting ta nuna damuwa, but to her surprise, bata ce komai ba, she was just so happy.
Data fada ma Hakeem ma, he was happy, yayi supporting din ta.
Da suka yi waya da Abdallah, ta fada mai, yaji dadi sosai a ranan, yana ta gode ma Allah, bai iya rufe baki ba, yana ta murna. Nan yace ta bashi numbern Hakeem, ta ce mai zata tura mai. Suna gama waya, ta tura mai, ta kira Hakeem ma ta fada mai.

Tana cikin tunani, taji hannun mutum a fuskan ta, sai ta zabura, Nafisa ta fashe da dariya, tace " matsoraciya, toh ni ne, wani irin tunani kike haka."
"Bakomai, am just thinking of how me and ifemi are making progress in our relationship." Olamide ta fada tana hugging din Nafisa.
"That's good, Allah ya bar ku tare, am really happy you guys are making a progress, yanzu dai hankalin ki ya fara kwantawa." Nafisa ta fada.
"Ae a'a, ae saboda mummy bata da wani objection, sun zama friends da Hakeem, yayyin sa suna so na. A'a, saboda iyayen sa basu sani bako, bamu san me decision din su ba, are they going to like me or not." Olamide ta fada disturbed.
"Ki daina damun kan ki, yanda na sauran yayi sauki, haka nasu ma zai yi sauki In Sha Allah." Nafisa ta fada tana murmushi.
"Allah yasa, amma wallahi hankali na ya ki kwantawa, duk da cewa shi ma yana kwantar mun da hankali, amma wallahi hankali na yaki kwantawa." Olamide ta fada.
"Kar ki damu, ki ci gaba da addu'a, yanda aka samu na sauran a sauwake, haka na su ma In Sha Allahu." Nafisa ta fada.
"Toh naji habibtyn Mide, na gode sosai da kulawan ki gare ni, Allah ya bar mu tare." Olamide ta fada tana hugging din ta.
"No godiya. Sannan dan Allah muyi focusing akan karatun mu, kinga fa har an fara test, kar mu zo muyi slacking please." Nafisa ta fada.
"In Sha Allah, success is our's."


Haka suka fara karatun test din su, cikin kwanciyan hankali, da suka gaji, suka kwanta barci, da niyan zasu tashi cikin dare su ci gaba.




〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


Da suka gama waya da Olamide, sai yaji hankalin shi ya dan kwanta, saboda ya samu ya dan kwantar mata da na ta, amma gaskiya shi ma bazai yi karya ba, hankalin shi bai wani kwanta ba, ji yake kaman ba zasu yarda ba, gashi su suka ce mai ya auri koma waye, indai ta kwanta mai, amma kuma sai ya ji hankalin sa bai kwanta ba.
Yana ta tunani kala kala. Amma tunda yana son ta, yana iya yuwuwa su yarda, gashi ai sun san Ustaz ma (Abokin sa, da suka hadu lokacin da yaje serving), kuma sunce yana burge su, then it will be easier, balle ma ba a garin yarbawa ta tashi ba, inma a garin ta tashi, it's still the same, mutum mutum ne, kuma Allah ya hallice mu duka, kuma a lokacin daya hallice mu, bai ce wani ya fi wani ba, inba muminai da suka fi kusanta dashi ba. Allah said he created us in different tribes, different colours, different nations, e.t.c, the who are we to argue, bamu da ikon nuna babanci tsakanin junan mu, amma Ina'a, mun bari cultural ethics, cultural norms din mu da values, sun bata mana tunani. Da iyaye zasu hada hannu, su gane, su bar yaran su, su auri wanda suke so, indai ta/ya na da hali, kuma ga addini, toh za'a samu zaman lafiya sosai. Amma yanzu kam addu'an shi bai wuci ace iyayen sa basu cikin iyayen da suke toya hakkin yaran su saboda *BANBANCIN KABILA* ba, Allah yasa suyi accepting din decision din sa whole hearted, Allah yasa su so choice din sa, kar su toye mai hakkin sa, saboda idan haka ya faru, toh fa zai shiga cikin babban matsala.
Yanzu dai zai fada ma yayyin sa ne tukun, inma hamma Sudais, da Adda Fadi zasu zo ranan ne, su ma su sa baki, sai suyi fixing din date, su hadu a gida su fada masu. Gashi ma Allah yayi, jibi Friday, kuma dukan su ke zuwa, amma yaga adda Wasila ma ta fara zuwa, kar ta zo tace an ware ta, why not su bari Saturday ko Sunday, zai fi.

Haka ya ita tunani, har barci barawo ya dauke shi.




Cikin dare, ya tashi ya shiga toilet, yayi alwala, ya koma daki ya shimfida sallaya, ya fara nafil, yana yi yana addu'a, Allah ya basu nasara, saboda idan su umma suka yarda, then bukatan su ya biya, kawu Dajjo kuma zasu san yanda zasu yi da shi.

Bai daina nafil ba, tun 3:00am daya tashi, sai daya ga lokacin fajr ya kusa, yayi raka'a taini fajr, kafun ya fita parlor, nan ya jira Abba, suka tafi masjid tare. Da suka dawo, yayi morning routine din sa, ya shirya cikin suit, farin lab coat din sa a hannu, ya fita ya je dinning, ya samu Umma ta dafa mai yam and egg sauce (miyan kwai), sai kuma ga tea, amma bata dafa mai lunch din da zai kai wajan aiki ba. Sai yayi deciding, ya kai abincin wajan aiki, ya kada shayin, yayi toasting din bread.

Daya gama, ya shiga dakin iyayen sa, ya masu gaisuwa, kafun ya sallame su, suka mai addu'a, kafun ya koma ya dauki briefcase din sa, da farin lab coat din sa, ya fita waje ya dan yi warming din mota, kafun, ya fara driving, yayi horn mai gadi ya bude, sai asibiti.





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️



By 3:20am, su Olamide suka tashi, suka yi alwala, suka yi nafila bibbiyu, suka yi addu'a, kafun suka kara jawo handouts din su, da jottern su, saboda idan suna da lectures, suna dan jotting, sai kuma wani extra jottern da suke jotting din duk abun da suka karanta.

Suna ta karatu, suna daukan break, suna nafil, har lokacin salatul fajr ya kusa, suka yi raka'a taini fajr, kafun suka yi sallah, tunda test din sai 11am, suka koma barci for sometimes, kafun suka sake tashi, suka gyara dakin su, Olamide ta girka masu breakfast, daman ita keda girki.
Da suka gama ci, Nafisa ta yi wanke wanke, Olamide kuma ta shiga wanka. Tana gamawa, yayi daidai da Nafisa ta gama wanke wanke, itama ta shiga wanka.


By 10:30am, suka bar gida, suka tafi cikin campus. Suna sauka, kiran Nabila ya shigo ma Olamide. "Assalamu alaikumu!" Olamide ta fada.
"Waalaikumus salaam. Ina kuke ne?" Nabila ta tambaya.
"Yanzun muka iso, muna ma sallaman mai keke ne, ina kike?" Olamide ta tambaye ta.
"Gani a karkarshe bishiyan da muka saba zama." Nabila ta amsa.
"Okay toh gamu nan zuwa." Olamide ta fada, sai ta kashe wayan.

Da suka gama sallaman mai keke, Nafisa ta tambaye ta, tace "ina tace take ?"
"Wai tana karkarshin bishiyan da muke zama." Olamide ta amsa.
"Okay." Nafisa ta fada.

Suka je suka same ta a inda ta fada masu, suka mika na junan su hannu, suna sallama.
"Kun san ban yi barci ba, kwana nayi ina karatu, yaya ma yaki yin barci, wai in banyi barci ba shima bazai yi ba." Nabila ta fada.
"Ban gane yayan ki bai yi barci ba, yaya Faeeq ko?
Saboda mijin ki na Gombe, ya zaayi kice baiyi barci ba." Nafisa ta fada.
"Miji na mana, after every 30mins yake kira na, gashi yana morning duty ne, kar Allah yasa yaje yana gengedi a office."Nabila ta fada.
Maganan ta ya basu dariya, sai Olamide tace "yayi mana highest in yaga bazai iya daurewa ba, ya shiga wani ward ya kwanta."
Duk suka kara fashewa da dariya. Da Nabila taga dariyan ba mai karewa bane, tace "toh ya ishe ku, ku daina ma heartbeat dina dariya."
"Oho dai mun dai yi." Nafisa ta fada tana mata gwalo.
Zata daki Nafisa da wasa kenan, Olamide tace "kuzo mu tafi inda za'ayi test fa, kar muzo muyi missing. Inya so ma in muka isa, sai ku ci gaba da dukan juna."



Da suka isa inda za'ayi test din, har an fara shiga, suma suka yi joining din queue, aka rarraba su, kuma ga two seats interval tsakanin dukan su.

Test din yayi hot sosai, duk wanda ya fito, sai yayi complain.
Nafisa ta fara fitowa, sai Nabila, Olamide ce last.
"Kai habibty, nayi zaton ba zaki fito ba". Nafisa ta fada.
"Ko ni, nayi zaton sai kinga karke pen din ki ne." Nabila ma ta fada.
"Ae din, koma meye." Olamide ta fada tana murguda masu baki.
"Kuga fa muje muyi sallah da wuri, saboda mu samu gaba a hall din da zamu yi wannan lectures din, kunga dai mutani dayawa sun zo test, haka za'ayi cunkoso a lectures ma yau." Nabila ta fada.
"Toh suka amsa mata."



Nasan maybe wasu are lost, basu gane me Nabila ta zo yi ba a wannan pejin.
Kaman yanda dai na fada a baya, cewa bayan bikin ta da two weeks zata dawo, domin ta ci gaba da karatu.



Da suka idar, suka nufa hanyan hall din lectures din su, suna tafiya cikin sauri. Luckily for them, sun samu space a gaba, saboda mutani basu fara shigowa ba sosai, suka samu wuri suka zauna su uku.






〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Da Abdallah ya isa asibiti, ya je yayi signing, sannan ya shiga office din sa, ya fara aiki, amma hankalin sa baya kwance, yana ta tunani kala kala, da kyar ya samu yayi aikin ranan.

Da suka yi closing, su uku (Abdallah, Farouq and Asim) suka hadu a karkashin wani bishiya, duk suka zauna a saman benci.
Sai Asim yace "Abdallah, yana ga yau din nan, kaman hankalin ka a tashe yake?"
"Gaskiya I noticed that too. I hope dai ba akan Olamide bane?" Farouq ya tambaya.
"Ni kam, tun daka hadu da ita, yau kana dariya, gobe kuma hankali a tashe." Asim ya fada worried.
"Ba zaku gane ba wallahi. Ni kadai na san yanda nake son ta, ni kadai na san yanda soyayyan ta ya gama mamaye zuciya na, wallahi ina son ta fiye da yanda kuke misali, ina son ta, ina son ta, ina son ta." Abdallah ya fada.
"Then what is the problem?" Asim ya tambaye shi.
"Exactly, meye matsalan?" Farouq ma ya tambaya.
Sanda Abdallah ya numfasa, ya ce "matsalan shi ne ban san yanda zan yi confronting din su Abba ba da wannan maganan ba, sannan ina tsoron amsan su. Wallahi ina ji a jiki na kaman ba zasu yarda ba, ina ji kaman zasu raba ni da masoyiya ta, kuma in aka yi haka, ba karamin cutar dani aka yi ba, dan koma wa zan zo in aura, indai ba ita ba, sai dai muyi auren, ba dan naso ba." Abdallah ya fada, idanuwan sa sun yi ja'a. Da mace ne, data yi kuka, amma tunda namiji ne, yana ta kokarin dannewa, saboda shi kadai yasan abun da yake ji.
"Hmmmm this is serious. Amma baka ce mana adda zee da hamma Sudais ma sun yi accepting din relationship din ku ba, then itama mahaifiyar ta ma tayi accepting, sannan kuna communicating da kanin ta, toh ai kunyi mai wuyan, am pretty sure su abba ma baza su zama problem ba In Sha Allah, ka daina damun kan ka please." Farouq ya fada.
"Yes please, ka kwantar da hankalin ka, Olamide taka ce In Sha Allahu, yanda Nafisa ma tawa ce da yardan Allah." Asim ya fada yana murmushi.
"Na gode maku sosai, Allah ya bar mu tare. Amma kun san me, ko ita ma hankalin ta a tashe yake, wai tana tsoro, and have been trying to make her cool her mind down. Kuma In Sha Allahu ran Saturday ko sunday nake son nida su hamma Sudais da adda Fadila mu fada masu, ku taya mu da addu'a, Allah yasa su yarda.
"Amin kar ka damu, In Sha Allahu zasu yarda. Kuma ka cigaba da kwantar mata da hankali ita ma." Farouq ya fada.
"Zamu taya ka da addu'a, your love will win In Sha Allah, and it will be an eye opener to other parents with this character, su abba zasu sa other parents su yi realising cewa tribe is not a fault in marriage In Sha Allah, now cheer up young man." Asim ya fada.
"Na gode maku, Allah ya bar mu tare." Abdallah ya fada.
"Amin suka amsa mai."





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


Da su Olamide suka tashi, driver din gidan su Nabila ya zo daukan su, ya sauke su Nafisa har gida, sannan ya wuce da Nabila gida.
Su Olamide sun mugun gaji, duk abun da suke, a gajiye suke yin shi.






```Thanks for reading.```



Comment
Like &
Share.



~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_






3️⃣5️⃣&3️⃣6️⃣





_Bismillah_






"Na samu wace nake so." Abdallah ya fada, kan sa a kasa.
"MashaAllah, shi ne sai ka wani kira yayyin ka?" Umma ta fada.
"Toh ai shi ne, I don't see the need for this." Abba ya fada.
"There is need for it." Abdallah ya kara fada.
"Then what is it." Abba ya tambaye shi.
"Gaskiya dai yarinyan na da hankali, ga kamun kai, ga addini, she is very loving. Ai sun hadu da adda Fadila lokacin bikin Farouq, kuma she can testify to her character." Abdallah ya fada.
"Yes I can, tana da hankali sosai wallahi, data zo gida na, kaman na hadiye ta, she is so loving." Adda Fadi ta fada.
"I don't still see the need for you guys coming here." Abba ya fada.
"Kai! Abba kai dai be patient. Amma dan Allah zan so ku duba alamarin nan da kyau kafun ku bada amsa." Hamma Sudais ya fada.
"Toh muna sauraron ku." Umma ta fada.
"Toh da farko dai ba a Gombe take ba, kuma, kuma, kuma."
"Kuma me?" Umma ta tambaya.
"Uhmm bayarbiya ce, amma tashin arewa." Abdallah ya fada kan sa akasa.
Ai umma da abba, sun ji maganan ne kaman saukan aradu. Ji suka yi kaman an zuba masu ruwan sanyi, sai kallon Abdallah suke.

Da Abdallah ya ji shuru yayi yawa, sai ya kalli yayin sa pleadingly, su ma su sa mai baki.

"Abba yana ji kun yi shuru ne, gaskiya according to what the both of them told me, tana da hankali sosai, gashi ma dana ga hoton ta, I thought ma Fulani ce, ba zaku ma san bayarbiya bace." Hamma Sudais ya fada.
"Umma! Abba! Dan Allah say something, am sure zaku so ta, tana da hankali sosai wallahi, she is every sister's dream for her brother, and she is also a gem every house hold wants." Adda Fadi ta fada.
"Me kuke son mu fada, ai wannan maganan ya fi karfin mu. So kuke a dinga zagin mu cikin family kullum, ku kenan burin ku a dinga zagin abban ku ako wani family meeting?" Umma ta fada.
"A'a, kwanciyan hankalin ku nake nema, kuma kullum ina cikin neman yanda zan faranta maku rai." Abdallah ya fada.
"Kana son ka faranta mana shi ne kake son ka kawo mana yarinya marasa dabi'a cikin gida, shi ne ka ke neman yanda zaka zubar ma mahaifin ka dan sauran mutuncin shi da familyn ku suke gani, kana son faranta mana, shi ne kake neman sa mana hawan jini?
Toh ka sani ba'a gidan nan ba." Umma ta fada ta tashi daga inda take zaune, shi ma abba ya tashi, domin shi yama rasa abun da zai ce.

Su Abdallah na ganin iyayen su sun tashi, suma suka taso da gudu. Abdallah da hamma Sudais suka je wajan abba, ita kuma adda Fadi, ta je wajan umma.
"DanAllah abba kayi magana, wallahi ina son ta, kuma tana so na, gashi tana da hankali, kuma tana da tabi'a mai kyau. Ku bata chance, zaku ji dadin ta." Abdallah ya fada.

"Wallahi umma tana da dabi'a. Ki bar ganin bayarbiya ce, tama fi wasu fulanin hankali. Wallahi umma zaki ji dadin ta, dan Allah ku ba soyayyan su chance dan Allah." Adda fadi ta fada. Da umma ta wani harare ta, ta cire hannayen ta a jikin ta, ta ce "in kika gama, ki wuce gida, ki gaida mun namesake dina da Irfan." Umma na gama magana, ta wuce dakin ta.

Shima abba, duk rokon da su Abdallah suke yi, sai shiga ya ke ta kunne dama, yana fita a na hagu, dan daman sun rike shi ne, sai ya balla hannayen su, cikin sukuni ya bar wajan.

Zai bar parlorn kenan, Abdallah yace "kar ka manta, ku kuka ce kowa na samu, indai ta zauna mun, then you guys will support my decision." Abdallah ya fada idonuwan sa jazur.

Abba bai ma bashi amsa ba, ya bar parlorn, ya wuce daki.


Su Umma na barin dakin, Abdallah ya tsuguna kasa, yaji jiri na daukan shi, ya dafa kai. Su Hamma Sudais da Adda Fadila suka zo kansa da gudu.
"Common be a man, kayi hakauri ka basu time. Kasan basu taba ganin irin haka ba a family, kai ne na farko, so they have to think, kafun su iya baka amsa." Adda Fadila ta fada.
"Gaskiya kam, you should give them time, kaman yanda Fadila ta fada, ka kyale su for sometimes, In Sha Allahu everything will be alright, yanzu kam they are in shock." Hamma Sudais ya fada.

Suna cikin lallaban shi, wayar sa ya fara ringing. Da kyar ya iya ciro wayan daga aljihun sa, ya duba screen, yaga sunan Adda Zaynab ya fito.
Da kyar ya iya daga kiran. Muryar sa kaman zai yi kuka, ya ce "assalamu alaikum adda!"
Adda Fadila ta mai signal ya sa a speaker, sai ya sa.
"Waalaikumus salaam mijin Faiza, amma ya naji muryar ka haka."
Sanda Abdallah yayi nishi, sai yace " Adda am not good at all, nothing went well. Gwanda Umma ma tayi magana, tayi objecting. Amma kin ga abba, bai ce komai ba, he just stood up and left." Abdallah ya fada idanuwan sa cike da ruwa.
"Subhanallah! Ya za'ayi kenan?
Ina hamma da Fadila ma tukun?" Ta tambaya.
"Gamu." Su biyu suka amsa.
"Me kuke yi da baku sa baki ba." Adda Zaynab ta tambaya.
"Ban gane me muke ba, ke kin tambaye shi kuma yace maki bamu sa baki ba?" Hamma Sudais ya tambaye ta.
"Kayi hakuri Hamma, amma dai you all know it that I hate to see auta miserable, that why I said that. Amma toh yanzu ba abun da zamu iya yi ne?
Ko in masu

Please Login or Register in order to submit comment