Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana ne?" Adda Zaynab ta fada disturbed.
"You should, ala in suka ga kema kin sa baki, maybe su yarda. Dan yanzu kam basu ma son su ga fuskokin mu, dan umma harta sallame ni." Adda fadi ta fada.
"You should also try your luck." Hamma ya fada, sai ya kalli Abdallah, yace " we are with you, everything will be alright In Sha Allah."
"Yes we are." Adda Zee da Adda fadi suka fada.
"Nagode maku sosai, Allah ya saka maku, ya raya zuriya, ya hada mu duka a jannah." Abdallah ya fada da jajjayen idanuwan sa.
"Amin amin autas." Suka fada.

"Toh auta, anjima zan masu magana, kaga by that time maybe sun sauko." Adda Zaynab ta fada.
"Toh. Allah yasa su ji naki." Abdallah ya fada.
"Amin" yayyin sa suka amsa, adda Zee kuma tayi hanging up.

Su Hamma Sudais sun kai 30mins, suna kwantar ma Abdallah hankali, da kyar suka samu ya daidaita.

Da suka wuce, shima ya koma daki, ya hau kan gado, ya jingina da pillow, sai tunanin Olamide ya fado mai. Me zai ce mata yanzu in suna waya?
Inma ya fada mata, hanya bai zai yi loosing din ta ba?

Haka ya ita tunani, har lokacin sallah yayi, yayi sallah acikin dakin shi.

Daya idar, yana cikin addu'a, wayar sa ya fara ringing. Ya duba wanda ke kira, sai ya ga sunan Olamide (my qalbi) boldly akan screen, nan ya fara jin heart din sa na beating, yama rasa mai zai yi, ya daga ne ko ya bari.





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️



Sanda Nafisa ta bari bayan 30mins, sai taje kusa da Olamide akan katifan ta, Olamide na ganin ta, ta juya fuska. Yanzu kam tama daina tunanin yanda iyayen Abdallah zasu yi reacting, haushin Nafisa take kawai, saboda ita baza ta iya fada mata haka ba, ko suggesting din shi baza ta yi ba.
Da Nafisa taga ta juya kai, sai ta juyar mata da kai tana kallon ta, tace "Allah sarki habibty, wallahi I care for you, I care about everything about you, bana son ganin hawayen ki. Kuma na fadi hakan ne saboda I really care about you. Kuma indai kin saurare ni da kyau, toh bance kuyi breakup ba, cewa nayi da baki son shi yanda kike son shi haka, dana ce maki kuyi breakup."
"Toh naji ki, sai da safe." Olamide ta fada, ta juyar da fuskan ta zuwa dayan gefen.
"Haba habibtyn Fisa, I really care about you, shi yasa kika ga na fada haka. Wallahi na tsani inga kina cikin damuwa, balle azo ga kuka, amma ina mai baki hakuri, kiyi hakuri da wannan stupid friend din naki, bazan kara ba." Nafisa fada.
"Toh naji." Olamide ta fada.
"Baki ce kin hakura ba." Nafisa ta fada.
"Ban hakura ba." Olamide ta fada.
"Haba habibty na, wallahi I care about you, kin ga idan kika ci gaba da haka, education din ki ma zai yi slacking. Bana son situation din da zaki dinga slacking a komai." Nafisa ta fada.
"Toh naji na hakura, shikenan?" Olamide ta fada ta juya kai tana kallon ta.
"A'a, ina son ki hakuran gaske, ba irin wannan ba." Nafisa ta fada a shgwabe.
"Wani irin hakuri ne yafi wannan, har ina amsa maki, toh na hakura, amma I don't want to talk to you." Olamide ta fada, ta tashi ta zauna.
"Haba habibty, so kike inyi ciwo, ya zaki ce kin hakura, amma baki son yin magana da ni, ki tuna fa I love you more than you can imagine, your happiness is my, and your sadness worries me too." Nafisa ta fada kaman zata yi kuka.
"I know you love me, and I also love you too, you mean a lot to me, but you should have consoled me, bawai ki dinga bani irin advice din nan ba at that moment. Wallahi alokacin nan, comfort nake so, ina bukatan ki kwantar mun da hankali ne. Ko kin san idan iyayen sa basu yarda ba, hakan na iya zama sanadiyan rabuwan mu, so I need comfort, not that type of advice. You can advice me that any day, banzan yi fushi ba, but I was hurt when you deed it at that time." Alokacin Olamide tana magana tana kuka.
"Ban san abun daya sa nake da saurin kuka ba, amma this is me." Olamide ta kara fada.
Nafisa bata san lokacin da ta yi hugging din ta ba, ta ce "am very sorry habibty, bazan kara ba, I just said it, ban yi tunani ba, danAllah kiyi hakuri." Nafisa ta fada.
"Nayi, amma Fisa na dauke ki as sister ta, ko kin mun laifi, bana iya fushi dake." Olamide ta fada.
"Am very sorry, banzan kara ba." Nafisa ta fada.


Da suka gama koke koken su, su dan yi hira, Nafisa ta ita kwantar mata hankali, su kayi barci.



Da suka tashi da safe, suka yi dutyn su, suna ta hira, ranan ya kasance Saturday, gashi basu da lectures, so suna ta huta duka gajiyan da suka yi tun monday. Ana cikin haka, Abdallah ya kira ta, ya sanar mata da cewa bayan asr zasu fada masu Abba, tun lokacin mood din ta ya canza, amma tana ta kokarin danne shi, not to make anyone around her worried.



Around 3 data ji shuru, sai Nafisa ta bata advice wai ta kira shi, da tana ta contemplating. Sai bayan sallan asr ta yi concluding kawai ta kira shi, kawai ta kira shi.





〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


Sanda wayan ya kusan tsinkewa, ya daga.
Daya daga bai yi magana ba, sanda ta ita sallama, kafun ya yi clearing din muryar sa kafun ya amsa.
"Baka amsa mun ba tun dazu ina ta salama." Olamide ta fada.
"Kiyi hakuri, yanzu na tashi daga barci shi yasa." Abdallah ya fada.
Allah ya ga baya son yin karya, amma ya ya iya, ba zai iya fada mata abun daya faru ba.
"Toh yayi, shi ne ka bar ni da damuwa ko?" Ta tambaye shi.
"Kiyi hakuri, su adda could not make it, shi yasa muka chanza timing din, sai duk ran da they are free again." Abdallah ya fada.
"And you didn't bother telling me. Kasan yanda na damu kuwa?
Gashi instead ace muna progressing, sai baya mu ke zuwa. Gaskiya ni bazan iya irin relationship din nan ba, our parents need to know about us. But if you don't want that, we can call it a quit." Olamide ta fada, sannan ta kashe wayar.
She was soo frustrated, ta rasa abun da yasa Abdallah yake mata haka. Shi ya sata agaba, sanda ta sanar ma mummy, amma ya sanar ma iyayen sa ya zama matsala.

Shi kuma Abdallah, data kashe wayar, ya rasa yanda zai yi da rayuwar sa, the pressure is too much, ya rasa abun yi, ji yake kaman ma ace he is not Abdallah any more.






```Thanks for reading```



Comment
Like &
Share.





~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_




3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣






_Bismillah_






Da su umma suka shiga ciki, Umma tace "wai ni alhaji me ke damun yaran nan ne in aka zo zancen aure?"
"Ai kuma ba ni zaki tambaya ba Hajiya, su zaki tambaya. Ina ganin sakewan dana masu ne yayi yawa." Abba ya fada rai abace.
"Gaskiya kam, sai ko wannan su zai yi aure ake meeting akan mu kullum." Umma ta fada.
"Hmmm bama wannan ba. Kin san me Abdallah ya fada?" Abba ya tambayi umma.
"A'a alhaji." Umma ta amsa.
"Kin tuna ran da na dawo nace baffa Dajjo ya mun maganan auren shi, kuma muka ce mai koma waya ya auro, in dai ta mai?" Ya tambaye ta.
"Haqqun na tuna. Kar dai shiyasa ya nemo mana bayarbiya. Yarbawan da basu da tarbiyan?"
"Shi nake gani nima ai, saboda da na kusan fita a parlor, yake cewa ai mun ce ya auri koma waye, indai ta zauna mai." Abba ya fada yayi tsaki.
"Toh shine yaje ya samo bayarbiya, yarbawan da kowa ya san halin su?
Be ma nemi yar arewa ba, yar kudu ya nemo." Umma ta fada takaici na kama ta.
"Ai shi ne. Ni fa when we said that, I only thought about someone from arewa, me zamu yi da yar kudu?" Abba ya fada ya dafa kai.
"Ai shi ne na gani. Me ma ya kai tunanin sa zuwa nan?" Umma ta fada.
"Oho masa." Abba ya fada.
"Ni kam gaskiya bazan yarda ba, saboda gaskiya yanda mutum ke jin labarin yarbawa, they are not people we can live with." Umma ta fada.
"Gaskiya they are not people to live with." Abba ya fada yana kada kai.
"At all. Kuma kar mu yarda gaskiya alhaji, saboda ban zan yarda ace mu zama abun zagi a gari ba." Umma ta fada.
"Ai baza mu yarda ba, ya ma san inda dare ya ma sa." Abba ya Fada.
"Ai kuwa." Umma ta fada.



Haka su Abba da Umma suka ita maganganu.




Abdallah ya kara kiran Olamide, bata daga ba, ya kira ta yafi sau bakwai amma ta ki dauka, sai ya kira Nafisa. Olamide ta tambaye ta ko shi ne, ta ce ae, Olamide tace mata kar ta daga. Har sau uku ya kira ta, itama bata daga ba.
Although ta so dagawa, amma Olamide ta ki, tace kar ta daga, inba haka ba zasu yi fada. Ita kuma gudun kar kawar ta tayi fushi, ta ki dagawa, amma ta kuddura a ran ta, anjima zata kira shi.


Rashin dagawan da suka yi, ya tada ma sa da hankali sosai, yaji ba abun da ke mai dadi. He felt so heart broken, ya rasa inda zai sa kan sa. Olamiden da ta kamata ta kwantar masa da hankali, ita ma tana fushi da shi.




Aranan kam Abdallah ya rasa yanda zai yi da kan sa, dan su abba ma sun ki kula shi. Inma ya masu magana ba kula shi suke ba. Abun duniya duk yabi ya ishe shi, ji yake kaman ya je tsakiyan compound din gidan su, ya dinga ihu, ko zai dan ji relief.



Bayan isha ya kira adda Fadila, yayi ringing sau uku, ta daga.
"Assalamu alaikum auta."
"Waalaikumus salaam. Wallahi tunda abun yau ya faru kuka koma gidajan ku ko, ke kadai kika mun magana normal. Ko qalbin Abdallah ma fushi take dani." Abdallah ya fada sadly.
"Don't be sad brother, your fav sis na tare da kai in every situation. Ka fada ma qalbin ka abun daya faru ne?
Indai ka fada ne, toh baka kyauta ba kwata kwata." Adda Fadi ta fada.
"No, ban fada mata ba, yama zan fada mata irin wannan abun, ita da tsoron ta kenan, shi yasa tace na fada masu, mu san inda muka dosa." Ya fada weakly.
"Kai ! Subhanallah, this is not good at all, gwanda ma da baka fada mata ba. Gashi tsoron ta yazo true, kuma am pretty sure in ta sani, maybe tace kuyi breakup. Kuma wallahi ba zan ga laifin ta ba, what is the need of staying in a relationship din da yan uwan guy din basu son ki. Amma yayi kyau da baka fada mata ba, maybe su zo su yarda in adda Zee ta masu magana.
"Toh Allah yasa su yarda, saboda da ta kira ni, ta tambaya ko na fada masu Abba, sai na mata karya nace a'a, shi ne fa tayi fushi, wai ni na takura mata, har sanda ta fada ma mahaifiyar ta, amma ni in fada ma su Umma ya zama matsala. Wai ina mata wasa da hankali." Abdallah ya fada.
"Allah sarki, ta matsu ne ta san level din relationship din ku, if it's going to make a progress or not. Amma it's still good da baka fada mata ba, muma sai muyi kokarin ganin su abba sun yarda, saboda gaskiya ni kam ina son ta, bazan iya jure rashin ka da ita ba, wallahi ta gama tafiya da zuciya na." Adda Fadila ta fada.
"Da zuciyar ki ko nawa. Ai irin soyayyan da nake ma qalbi, in su abba suka hana ni ita na auri wata, toh ko min son da nake mata ba zai taba kai na qalbi na ba, saboda she owns my heart." Abdallah ya fada.
"Allah sarki kani na, kar ka damu, komai zai yi daidai, ka kwantar da hankalin ka, saboda Olamide taka ce In Sha Allah." Adda Fadila ta fada.
"Amin, nagode sosai da support din ku, Allah ya bar mun ku." Abdallah ya fada.
"Amin amin." Adda Fadi ta fada.
"Toh mu kwana lafiya, bari in kira qalbi na." Abdallah ya fada.
"Toh, agaishe ta, mun ma dade bamu yi waya ba, maybe in kira ta gobe." Adda Fadi ta fada.
"Okay. Dan Allah in kun yi waya, ki kara kwantar mata da hankali please, kice mata ta daina damuwa, very thing will be alright In Sha Allahu." Abdallah ya fada.
"Toh naji, amma in kun yi waya, kai ma ka kwantar mata da hankali."
"In Sha Allah. Bye." Abdallah ya fada.
"Allah ya tashe mu lafiya, bye." Adda Fadila ta fada, sai ta kashe wayar.



Da suka gama waya, sai ya nemo sunan qalbin sa, yana gani, zuciyar sa ya fara tsinkewa, Allah yasa dai ta daga. Yayi dialing din numbern, ya ita ringing baa daga ba, Olamide ta gani, ta ki dagawa, sanda ya kira sau uku, Nafisa tayi forcing din ta ta daga. Rai abace ta daga, tayi sallama.
"Waalaikumus salaam qalbin na." Abdallah ya amsa sallaman ta.
Sai kuma shuru ya biyo baya, ba wanda yayi magana acikin su, da abun ya ishi Mide, tace "daman ka kira ni ne kawai, ba dan kayi magana da ni ba ko?
Toh na gode, bari in kashe....." Bai bari ta gama magana ba, ya ce " ba haka bane qalbi, wallahi I just became speechless ne, amma am sorry for the silence." Abdallah ya fada.
"Toh. Ina jin ka." Olamide ta fada without emotion.
"Daman na kira ne in baki hakuri qalbi na." Abdallah fada.
"Hmm ifemi kenan, lokacin da zan fada ma mummy, ka sani a gaba, in dai fada. Amma ka fada masu abba ya gagara. Toh me kake son inyi, dole nayi fushi ai. Ni wallahi gani nake kaman kana wasa da hankali na ne kawai." Olamide ta fada.
"Haba qalbi, me zai sa inyi wasa da hankalin ki, you are too specially in maki haka." Abdallah ya fada.
"Am not! Because if I was ba zaka dinga mun haka ba. Kullum sai kace you love me, amma you are finding it hard ka fada ma su abba mu san inda muka dosa. Bana son situation din da zan zo in sake da yawa, su zo su ce basu son ka auri kabila." Olamide ta fada.
"Kar ki damu masoyiya ta, hakan ba zai faru ba, ina son ki kara hakuri, nida siblings dina mun na plan ne akan yanda zamu fada masu da baza'a samu damuwa ba." Abdallah ya fada.
"Ni kam ban yarda ba, gani nake kaman kana wasa da hankali na ne kawai. Amma ba damuwa, I will be patient, but you should know, next time ba zan ji komai ba, we will just find our ways kawai." Olamide ta fada.
"Hakan ma bazai taba faruwa ba In Sha Allah. Ki kwantar da hankalin ki please, saboda kwanciyan hankalin ki shi ne nawa." Abdallah ya fada.



Da kyar ya samu ya shawo kan ta, har suka dan taba hira kadan kafun tace ta gaji barci take ji, suka yi sallama, ya kashe wayar.

"Ya ilahi, Allah kaga niyya na, bana son yin karya, amma ya na iya, this is the only way I can keep the love of my life. Bana son situation din da zai raba ni da ita. Na san yanzu dai su Abba are in shock ne, amma they will come around, har su zo su yarda da soyayyan mu. Kuma In Sha Allah zan yi duk a bun daya kamata, har su zo su gane ina son qalbi na, kuma qalbi na nada hankali, ga illimin addini, ga dabi'a mai kyau, ga respect. Kuma ai ko wani yare nada salihi da dan iska, ba yarbawa kadai keda su ba. Nama rasa abun daya sa iyaye suke irin wannan tunanin, kuma na rasa abun dayasa aka sa ma yarbawa lakanin nan. Ya Allah please guide me through, I hope our love conquers." Abdallah ya fada yana thinking aloud.


Haka ya ita tunani, har barci ya dauke shi.






〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️





Olamide kuwa da suka yi sallama ya kashe wayar, ta kalli Nafisa dake kwance kusa da ita, tace "na kasa yarda da shi, ina jin shi ajiki na kaman karya yake mun, kaman akwai abun da yake boye mun, saboda da safen nan fa ya kira ni ya fada mun wai bayan zuhur zasu hadu, amma in kira sa bayan asr kuma yace mun basu hadu ba, wani wai yana barci ne, kuma muryar sa bai yi kamada wanda yayi barci ba sannan yanzu kuma yana wani ce mun wai suna planning din yanda zasu masu magana just imagine habibty, is this not suspicious?" Olamide ta fada.
Ita kuma Nafisa inba kallon Mide ba, ba abun da take.
"Habibty fa dake nake." Olamide ta fada tana daga mata gira.
"Toh me zan ce?" Nafisa ta tambaye ta.
"Mele." Olamide ta fada tana murguda mata baki.
"Toh, amma you should trust him, relationships don't work without trust." Nafisa ta fada.
"I know, but am just finding it hard, saboda yanda yake magana ma zaka san there is something he is hiding, but I will put my trust in Allah, dan na san he is the only one that will never disappoint me." Olamide ta fada.
"Yes he is. Ki kwantar da hankalin ki kin jin bibtyn Fisa?"
"Naji bibtyn Fa'iza."

Suka ci gaba da hira, Nafisa na ta bata advice, har suka gaji, Nafisa ta koma kan katifan ta, kowannan su tayi barci.






```Thanks for reading and been patient, wallahi abubuwa suka mun yawa .```





Comment
Like &
Share.





~Zeexee ce~ 🖊️🖊️🖊️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight💜💖: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*BANBANCIN KABILA*
_(Short story)_
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

*-RAYUWAR HUSNA*

*-MAHAKURCI MAWADACI* _(2020)_




```Dedicating this chap to my sweet and lovely cousins aunty Jamila and Jamila. I love you guys sooo much💕💕💕💕❤❤❤❤❤.```



3️⃣3️⃣&3️⃣4️⃣





_Bismillah_





Ranan Friday, tunda short day ne, Abdallah ya dawo da wuri, nan ya samu, har sisters din sa, da matar hamma Sudais da jikokin gidan duka sun zo, amma banda na adda zee, saboda basu countryn.

Ya na fita daga motar sa, kananan yaran suka zo suna mai oyoyo, one after the other ya rinka daukan su.
Manyan kuma, suka zo suna gaishe shi. Haka suka bi sa a baya, ya gaishe da kowa da kowa, kafun ya tafi dakin sa, saboda yayi wanka, sannan ya chanza kaya.

Daya gama komai, sai ya koma parlor, ya samu kowannan su a parlor, suna hira. Ya kira baban cikin su, Jamila (yarinyar mijin Adda Wasila), ya mika mata leda cike da su chocolate, sweets, chewing gum, da dai sauran su, ya ce ta raba masu.
Ya kalli umma a shagwabe ya ce "umman auta, ina jin yunwa fa".
Adda Fadila na jin haka, ta ce "ai ba sai ka fada ma umma ba, ko ni sai ka fada min, bari in kawo maka. Anan zaka ci ko a dinning?" Ta tambaye shi.
"Anan zan ci." Ya fada a shagwabe.
Yana fadan haka, ta tashi, ta wuce kitchen, ta je kawo mai abinci.
"Kai auta! A lan an kwaso gajiya ne ko?" Abba ya fada yaba shafa bayan sa.
"Sosai abba na, na gaji." Abdallah ya amsa.
"Sannu Uncle auta, ai kana kokari sosai." Aunty Aisha matar hamma Sudais ta fada.
"Ni kam ku bar shagwaba shi, wai ku baku san ya isa ace yana da yara ko yaro ba ne da zaku dinga wani shagwaba shi kaman baby." Adda Wasila ta fada.
"Ai shi ne, ji yanda kuke yi dashi." Umma ta fada, sai ta kalli Abdallah, ta ce "kai kuma ka tsaya a wajan a dinga maida ka yaro."
Tana gama fadan gakan, sai ga Adda Fadila niki niki da Abincin Abdallah a kan tray, sai ta tura stool, tasa a gaban shi, kafun ta ajiye abinci, ta ce "A ci lafiya auta."
Suna hada ido da Umma, taga irin hallon da take mata, sai ta kau da kai.
Umma tace "ku kuka sani, in yaso ku maida shi dan shekara biyar."
"A'a Hajiya ya ishe ki haka. Yaro ya kwaso gajiya, instead ki lallabe shi, kina kara mai gajiya akan gajiya. Ya samu masu mai kuma kina complain. Kar ki damu, inya yi aure, ya rage ni dake, zaki san value din auta. Ko auta." Abba ya fada yana kallon shi.
"Sosai ma, idan na auri Ola...." Sai yayi shuru, ya ma manta, bai san lokacin da sunan ya fito daga bakin sa ba.
"Ka auri wa?" Adda Wasila ta tambaya.
"Babu, ina auri all my wives nake son fada." Abdallah ya fada yana murmushin dole.
"All your wives kuma?
Ashe mata da yawa zaka aura a rana daya." Umma ta fada.
"Kai Umma, ai uncle auta ba haka yake ba, kawai dai wasa yake. Kuma ai yana da ikon auran matan hudu." Aunty Aisha ta fada.
"Toh ai shi ne, in yaso ya aure su a rana daya, but the fact still remains, zaki yi missing din auta." Adda Fadila ta fada tana murmushi.


Haka suka ita hira, Umma da adda Wasila na zolayan Abdallah, kafun shima hamma Sudais yazo, teams din suka cika 3-4, wannan team din na zolayan Abdallah, wayannan kuma na bada amsa.

Daman idan 6:pm yayi, ko wannan su ke komawa gida. So by 5, Abdallah ya ma hamma Sudais da adda Fadi text, yace su hadu a balcony, shi zai yi kaman yayi fushi, ya fito, su kuma su biyo shi.

Haka ko aka yi, adda Wasila na dukan shi a baya da wasa, ya hada rai, ya tashi ya bar wajan, suma suka biyo shi a baya. Da suka fita, suka yi dariya

Please Login or Register in order to submit comment