Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kaina saina fad'awa tsohuwa."

Ganin ya nufota tayi saurin shigewa d'akin had'ida sanyawa k'ofar key."

Tsaye yayi yakasa tafiya yana kallon babban d'an ya tsanshi da ya somayin ja,
Yana tunanin dijama wato bata daina halintaba kenan lallai akwai aiki a nan gaba."

Yana nan tsaye wuri d'aya saiji yayi andafashi a bayanshi, Khalil yagani yace "brother lfy kayi tsaye a nan?"

Su momyn basu dawobane?"

Mahmoud yace "fita sukayi ne?

"Khalil yace "sunje gidan gaisuwa tare da Abba."

Ya mik'awa Mahmoud wani takarda Mahmoud ya karb'a yana dubawa yana cewa "takardar meye?"

Khalil ya yamutsa fuska yace form d'in islamiyar wnn bagidajiyar nan ne, wadda Abba yasanyani karb'owa, nagama cika komai sunanta ne kawai bansaniba,

Wlh bnsan abunda yasa Abba ya dawo da ita gidan nan ba, da zarar munyi ido biyu da ita jinakeyi kamar zanyi amai."

Mahmoud ya dubeshi yace "khalil 'yar uwarka face, gakya ya kamata ka canza hali Kuma ka canza rayuwa, kadaina ganin 'yan matan Jami"a kyawawa wayayi suna rud'arka har kake kyamatar jininka. To kasani asalinka k'auye a can Abbamu ya tashi a can ya girma har gobe mahaifansa suna k'auye."

Wani saurin ja da baya yayi yana duba bayansa, ganin baiga kowa a wurinba yace "haba brother bazaka gane bane, nagodewa Allah da bakowa a kusa dani lokacinda kake fad'in hakan daka sanyani naji kunya."

Ido Mahmoud ya tsora mashi yana mmkinsa domin yanda ya d'aukeshi sai yaga ya wuce nan."

Takarda ya mik'a mashi yace "ynda bakasan sunantaba nima bnsan sunantaba, kabari idan Abba ya dawo shida ya sanyaka saika tmbayeshi sunanta kagani sai ya fad'a maka."

Yana kawowa nan yayi tafiyarshi ya barshi nan tsaye zuciyarshi cike da mmkin khalil."

Khalil yabi mahmoud da kallo yace "ya za'ayi na tambayi Abba sunanta, nasan yanda yakejinta a gidan nan yana iya kafsamin a gabanta
Zan dai jira har lokacin da fateema dawo daga mkranta saina tambayeta."

Yajuya yanufi d'akinshi yana mamakin mohmuod ganin yanda shima yakeji da wann bagidajiyar a gidan nanโ˜น
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: ๐ŸŒน *DEEJAMAH*๐ŸŒน
( _'Yar gidan tsohuwa_ )๐Ÿ˜…





Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)





*13*







Da sauri shugaban mkranta ya nufo ajin har da tuntub'e. Yakeyi domin lbrin da ya isar mashi anjiwa 'yar ciyaman da 'yar kassila ciwo."

Ganin saurin da yakeyi yasa sauran malamai suka fahimci a akwai abunda ke faruwa, suka rufo mashi baya."

Ganin jinin dake zuba a bakukansu ya d'agawa malamai hankali. Anan take aka Shiga basu taimakon gaggawa."

Shugaban makaranta ya d'aga waya ya kira ciyaman da kassila yake shaida masu abunda ke faruwa."

Ko wannensu cikin tashin hankali suka bugawa jami'an tsaro waya, anan take mota biyu ta 'yan sanda kamar had'in baki, motar ciyaman da motar kassila."

Suka shigo cikin mkrantar sai jiniya kukeji kamar za'a tashi makarantar, 'yan sandan kowanensu da zungureriyar bindigarshi a hannunshi."

Sai tambaya sukeyi ina yarinyar da taji masu ciwo, a wuce da ita atafi da ita a hukuntata."

Dijama dake tsugune gefe d'aya sai Zarar ido takeyi ta karkace kai duk Wanda ke magana tana binshi da kallon tana kallon bakinshi."

Turanci kawai takeji yana tashi Wanda bata san abunda suke cewaba kallonsu kawai takeyi."

Can taga shugaban makaranta ya nunata da yatsa yana fad'i da Hausa yana cewa "kunganta can itace, yau yau d'in nan da zuwanta makarantar nan amma har ta fara dazamun bala'i."

Shekarata goma sha d'aya da bud'a makarantar nan hakan bata tab'a faruwa daniba sai zuwan wann fiti nan niyar yarinya."

Tsawa aka dokawa dijama Wanda yasa tayi saurin mik'ewa tsaye saboda ganin zungureriyar bindigar dake hannun d'an sandar."

Tashiga ja da baya tana "fad'in Dan Allah kuyi hak'uri karku harbeni sune suka fara tsokanata."

Fateema kuma babu abunda takeyi sai aikin kuka, Wanda a cikin mutanen wurin bbu Wanda ya lura da ita tana gefe d'aya a tsaye."

Kuma doka mata tsawa d'an sandar yayi, yace "ba kasheki zamuyiba tafiya zamuyi dake sai munji ko waye ubanki a garin nan snn mu d'aukar mki hukunci."

Haka aka sanya k'eyar dijama a gaba tare da shugaban mkranta aka sanyasu a mota aka tafi dasu."

Dijama sai Zarar ido takeyi wuk'i wuk'i a bayan mota, shugaban makaranta da juya ya kalleta sunyi ido biyu da ita sai ya wurga mata harara."

A zuciyarshi yana da yasani karb'arta da yayi a matsayin d'aliba."

Fateema na ganin antafi da dijama, ta kuma fashewa da kuka,
tayiwa wani malami magani tace "dan Allah uncle kabani Aron wayarka zankira Abba na na fad'a mashi abunda ke faruwa."

Zaro ido yyi cike da mmki yace "dama kinsanta ne?"

Ta d'aga kai alamar "eh tace yayata ce uwarmu d'aya ubanmu d'aya."

Uncle ya xaro ido waje yace "kina nufin 'yar Alhaji Hassan Adam CE?"

To ya akayi bansanta ba a cikin gidanku?"

Cike dajin haushin tambayarshi fateema ta turo baki tace "bazaka Santaba saboda ba'a garin nan takeba,
dan Allah uncle kabani aron wayar mana."

Yace "Ayyah fateema kiyi hak'uri banada waya a hannuna, amma nasan za'aje da ita ta nuna gidansu."




_kuyi hk'uri d wnn pls yau sai a hnkli_
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: ๐ŸŒน *DEEJAMAH*๐ŸŒน
( _'Yar gidan tsohuwa_ )๐Ÿ˜…





Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)





*12*






7:30am. Shiri sukeyi domin zuwa makaranta,
tasanya uniform dinta, wad'anda sukayi mata kyau sunfito mata da fuskarta sak 'yar fillo."

Fuskar nan tata tasha hoda da jambaki,
fateema dake gefenta zaune,
ta dubeta tace "dijama ki goge wnn kwanliyar ta fuskarki tayi yawa sosai idan mukaje Anty tana iya sanya hijabinki fari ta goge mki ita."

Ta murgud'a baki tace "bazan gogeba, a hakan zanje kuma bata isa ta gogemun kwanliya taba."

Fateema zata kuma yin magana tajiyo sautin muryar yaya Mahmoud yana fad'in "wai bazaku fitoba lokaci fa na tafiya, Allah duk kuka kuskura kuka bari na hawo saman nan sai jikinku ya gaya maku."

Da sauri fateema ta d'auki school bag d'inta ta goya. Bata kuma bi takan dijamaba don tasan halin yaya Mahmoud ba sauk'i ne dashi ba."

Dijama da ke k'ok'arin sanya sendel a k'afarta tana turo baki cikin magana k'asa k'asa tace "to idan ka hawo karka barmu da rai ka kashemu."

Ido fateema ta zaro waje tace "yayan kike cewa hakan lallai dijama bakisan halin yaya Mahmoud bane, tana fad'in hakan tayi saurin bud'e k'ofa ta fita, tabar dijama na sanya takalmi."

Tana gama sanyawa itama ta biyo bayanta, ta fito tana tafiya harda wani rangwad'a takeyi wai ita 'yar boko."

Gaba d'anyansu Suna babban falo zaune suna Brest fast, Abba da shirinsa na zuwa Office khalil shima da shirinsa zuwa makaranta BUK."

Mahmuod a tsaye da key d'in mota a hannunshi yana jiran fitowarsu ya kaisu, yadawo yana da inda zaije, har sun b'ata mashi time."

Fateema ta fara fitowa sann dijama ta biyo bayanta,
Abba na ganinsu cikin uniform yaji dad'i sosai sai murmushi yakeyi a fuskarshi,
Momy itama murmushin takeyi tana fad'in "iye 'yan matana lallai kunyi kyau musamman 'yata ummie."

Mahmoud dake tsaye gefe d'aya yanayi yana kallon agogon gwal dake d'aure a hannunshi."

Khalil ya d'aga kansa yana ya mutsa fuska yana kallon dijama. Da take k'ok'arin k'arb'ar flast d'in break d'insu. Wanda momy ke mik'a masu,

Ido biyu yayi da fuskar dijama datasha kwalliya,
mai zaiyi idan ba dariya ba,

Dariya yakeyi yana nuna fuskarta yana fad'in tab "mutumin k'auye baiyi ba wlh ke wai kwanliyace kikayi hakan ko meye?"

Brother wlh karka bari wnn abar ta shigar maka mota, ai sai kuzama abunda kwatance duk inda kuka gifta."

Cikin zafin rai Abba ya doka mashi tsawa da k'arfi yace "khalil tashi kafita karna na sab'a maka wlh."

Momy Itama tabishi da harara tana fad'in "ni bansan irin rayuwar khalil ba a cikin gidan nan."

Ta jawo hannun dijama dake tsaye wuri d'aya tana cije baki had'ida girgiza kai, ranta ya b'aci matuk'a."

Mahmoud dake tsaye a inda yake, ya had'e fuska,
yayi saurin waigawa ya wurgawa khalil harara cike da jin haushinsa."

Mmy ta rik'o hannuta tace "zo nan 'yata na gyara maki fuskarki karki damu da abunda khalili yayi mki hka halinshi yake."

Momy tashiga gyara mata fuskarta, ta goge mata janbakin da 'yar gira, ta kuma rage mata hudar fuskarta,
Sauran kwallin da tashafa a idonta ne yak'i goguwa. Gudun karsuyi latti momy ta barta haka suka tafi."

Bayan sunfita ne Abba ya maida kallonsa ga momy yace "nafara ganin take taken khalil a gidan nan a kan ummie zan d'aukar mashi mummunan mataki idan hakan ta kuma faruwa a kan idona."

Inason Allah yabani iko da nisan kwana nacika Alk'awarin da nayiwa d'an uwana kafin ya mutu,
na aurawa muhmud Ummie idan ba hakan ba a yanda naga khalil na kyamatarta a gidan nan da bbu abunda zai hana na aura mashi ita, domin kawai naga iya karshi."

Hak'uri momy kawai take bashi domin ganin ranshi ya b'aci sosai."

A bayan mota suka shiga mahmud bai kulasuba, fuskarshi a had'e, ya tayar da
motarsa yaja yanufi makarantarsu."

Suna shiga cikin makarantar yayi parking d'in motar shi a cikin harabar makarantar,
, tun kafin ya fito dijama ta rigashi fitowa harwani sauri takeyi k'asa na tashi,
Da sauri ya doka mata tsawa yace "ke 'yar k'auye da Allah malama ki dawo ki tsaya."
Kina wata tafiya k'ura na tashi sallan ki b'atawa mutane jiki da k'asa, 'yar k'auye kawai
Takkwala mai kwanyar kifi, kamar da gske sai kace ganewa kikeyi.
To bari na fad'a mki nan ba k'auye bane mudun kikayiwa malamai rashin kunyar da kikeyi a k'auye tsinanen dukan tsiya zakici kuma ba Wanda zai rama maki."

Juyowa tayi tana kallonshi ta sunkuyar da kanta k'asa, a rayuwar ta bbu abunda ta tsana irin yaya Mahmud ya kirata da mai kwanyar kifi, ta d'aukarwa kanta Alk'awarin cewa zata maida hankali tayi karatu Wanda yaya Mahmud sai yayi mmkinta,
a lokacin zata bud'e baki ta mayar masa da raddin takkwalar da yake kiranta da ita."

A fusace ya juya wurin fateema da mmkinsa bai gantaba sai ma hangota da yayi ta kusan shigewa class."

Gaba ya shige dijama na biye dashi, office d'in shugaban mkranta ya shiga ya gabatar da dijama, sann daga k'arshe gaban idonsa aka kaita class,
Aji d'aya aka ajiyesu da fateema kamar yanda ya buk'ata, saboda fateema ta dinga koya mata wasu abubuwa wad'anda bata saniba."

Sai da yaga shigarta aji sann ya shiga motarsa ya dawo gida."

Da shigarta ajin d'alibai sai kallonta sukeyi ganin yanda ta tsurawa silin roba ido sai kallo takeyi, gaba d'aya sai k'arewa ajin kallo takeyi da kujerun dake ajiye a cikin class d'in."

Fateema ta hango a can zaune tayi saurin bud'e baki tare da d'aga murya tace "lah fati Ashe aji d'aya aka ajiyemu ai kuwa naji dad'i."

Gaba d'aya ajin suka tuntsere mata da dariya, wata 'd'iyar chiyaman d'in garin,
Wanda suke mak'otaka da Abba, tace "amma dai ke 'yar k'auyece wlh."

Suka kuma shek'e mata da dariya, wata d'aliba daga cikinsu tace "dubi yanda ta shafa kwanli a idonta, ta fad'i hakan had'ida nuna idon dijama suka kuma shek'ewa da dariya."

Dijama taji haushi sosai, fateema ta mik'e tsaye ta kama hannun dijama da tayi tsaye takasa zama saboda jin haushi, ta zaunar da ita a kan kujera kusa da ita."

Dijama taja wuri d'aya ta zauna tana sake sake a ranta,

Malam mai English ya shigo ya fara yi masu karatu ta kashe kunne ta kwantar da hankalinta tana saurare kuma tana fahimta."

K'araurawa taji an buga alamar antashi break fast, hakan yayi dai dai da fitar malma mai English, d'alibai suka fara fita waje domin cin abinci."

Da sauri dijama ta duro a kan kujera ta shagaban 'yar gidan chiyaman
karon farko mari ta fara kai mata, ta cire hijabin jikinta tasha d'amara cikin d'aga murya tace "ubnwa kike cewa 'yar k'auye?" Tashiga nusarta, baji bagani, saida bakinta ya fashe da jini,
gaba d'aya ta b'ata gaban hijabinta,
D'aya yarinya wanda harda ita wurin yi mata dariya,
ta matso wurin dijama ta cimuimuye mata riga a bayanta,

Dijama tasanya k'afa ta bayanta ta shure mata baki, aikuwa yarinya ta kwatsa ihu ta duk'e ta rik'e bakinta da jini yaketa zuba."

Ihu 'yan aji keyi da gudu suka fita suka kira shugaban makarantar."

Babu abunda fateema keyi sai aikin kuka,
Dama kuka baya mata wuya, saboda kwata kwata fateema bata da fad'a batason tashin hankali,
sanyin hali ke gareta."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: ๐ŸŒน *DEEJAMAH*๐ŸŒน
( _'Yar gidan tsohuwa_ )๐Ÿ˜…





Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)





*14*






12:30pm Abba ne zaune a Palo ya dawo daga office Mahmud zaune a gefensa yana shaida masa cewa Alhaji Atiku ya kirashi a waya akan cewa ya xama cikin shiri satin nan ya shirya kayansa ya sameshi Abuja domin sunansa ya fito zasu wuce wurin trening."

"Alhmdulillahi Abba yace,
Yana murmushi cike da jin dad'i da farin ciki, ya dubi Mahmud yace "Alhaji Atiku mutumin k'irkine abokina ne tare muka tashi mukayi makaranta d'aya dashi,
A rayuwata ta duniya bbu abunda Alhaji Atiku zai nema gareni banyi mashiba indai baifi k'arfinaba, saboda yanda yake nunamun k'aramci da k'auna."

Mahmud inaso idan kaje ka kula da kanka,
Kabishi sau da k'afa kayi mashi biyayya kamar yanda kasan kanayi mun Allah yayi mka Albarka."

Bai rufe bakinsaba fateema tashigo ko sallama bbu idonta yayi ja alamar taci kuka,har ta gaji."

Mahmud ya dubeta cike da kulawa yace "fateema meyasameki?"
Abba yace "ina Ummie take?"

Kafin tabasu amsa sukajiyo jiniyar motar 'yan sanda a k'ofar gida,
Saiga Baba maigadi yashigo da saurinsa ya zube k'asa gaban Abba yace "ranka ya dad'e 'yan sanda na sallama da kai a waje."

Abba ya zaro ido cike da mmki yace "yan sanda?"
Meyafaru?"

Mahmud shima hakan,
Fateema ta kuma fashewa da kuka tace "wlh sune,
Momy ta taso tashiga girgixata tana tambayarta "sune suwa?"
Meya faru?"

"Sune wad'anda suka kama dijama suka tafi da ita,
Mahmud yayi saurin juyowa ya kalleta, ya kuma kallon Abba da momy, yace "dijama tayi halinta kenan tajanyo mana fitina."

Suka d'unguma gaba d'ayansu suka fita,
Mahmud ke gaba sai Sauri yakeyi Abba na biye dashi snn momy da fateema."

Yana tukarar motar ya hango dijama zaune a bayan mota sai zarar ido takeyi"

'Yan sandan na ganin Abba sukayi saurin fitowa suna gaisuwa gareshi kasan cewar Abba ta fito takarar d'an majalisa na jahar kano,
A garin na kano, kowa yasanshi babba da yaro, kuma Abba mutum ne mai yawan Alheri ga jama'a."

Tambaya yashigayi meke faruwa?"

Anan sukashiga yi mashi bayani cike da girmamawa."

Hak'uri Abba yashiga basu, snn dga k'arshe ya d'aga waya kira ciyaman da kassila yashiga bsu hkri ya kuma shaida masu da cewa 'yarsace ta aikata hakan a bisa kuskure."

Ko wannensu mmki ykeyi,
Gnin basu san dijamaba."
Anan sukayi sallma da cewa ko mai yawuce Allah ya tsare gaba."

Snn aka fito da dijama daga cikin motar,
Abba ya d'auki kud'i masu yawa ya mik'awa 'yan sandar suka amsa suna godiya snn sukaja motarsu sukayi tafiyarsu."

Mahmud yayi kanta da sauri, ya rik'o hannunta yashige da ita d'akinsa ya sanya key yashiga jifgarta yana dukanta ba girma ba arxik'i,

Ihu takeyi tana fad'in wayyo tsohuwa kizo ki ceceni,

Abba da momy sai dukan k'ofa sukeyi amma yak'i bud'ewa, rai b'ace Abba ya nufi d'akinsa ya d'auko extra key ya nufi d'akin mahmud ya bud'e ya shiga."

Ya daina dukanta ya sanyata kamun kunne yana zaune gefe d'aya yana kallonta hannunshi rik'e da bulala."

Yana ganin Abba ya shigo yayi saurin tashi tsaye yashiga ja da baya,
Abba ya rik'a dijama ya mik'ar da ita tsaye,
Tana ganin Abba ta fad'a jikinsa ta fashe da wani sabon kuka, tana fad'in "Dan Allah Abba ka taimakeni ka bayar dani wurin tsohuwa idan naci gaba da zama gidan nan yaya Mahmud kasheni zainyi."

Abba ya rik'a hannunta yana bata hak'uri had'ida juyawa ya wurgawa Mahmud harara snn suka fita."

Da fitarsu mahmud ya sauke ajiyar zuciya, ya fad'a kan gadonsa ya kwanta rufda ciki,
Ya shiga tunanin dijama, Sam bayajin dad'in rashin jin maganar da takeyi, babban abunda yafi b'ata masa rayuwa shine akan karatu dijama batason karatu ko kad'an rashin kunya da tujara yayimata yawa a kai."

Yashiga tunanin yanZun meye mafita wani mataki ya kamata ya d'aukar mata wadda yin hakan zai sanyata dole ta tsaya ta natsu tayi karatu, Wanda a ynxun ilimi shine gishirin zaman duniya." Idan bakada shi babban cinka da jaki kad'an ne."

Makarantar barci boarding school ta fad'o masa a rai,
Wani murmushi yayi ya kuma juya kwanciya yace "tabbas makarantar barci zan kaita inda bata ganin kowa da zarar tayi rashin ji abata kashi kuma dole ta tsaya tayi karatu ba Dan tasoba."

Hakan dai ya yanke shawarar kaita boarding school kafin ya bar garin hankalin kowa ya kwanta."

Mik'ewa yayi yashiga toilet yayi wanka ya fito ya canza kayanshi ya d'auki key d'in motarshi yajata yanufi gidan wani abokinshi Ahmad wadda shima k'anwarshi a makarantar barci take karatu.
domin ya tambaye shi abubuwan da yakamata a shiryawa dijama."

Abba na rik'e da hannun dijama suka nufi babban Palon gidan, inda momy take zaune,
momy na ganinta ta mik'a mata hannu alamar ta taxo gareta,
Cikin sauri taje jikin momy ta fad'a tana kuka."

Momy sai bubbugar bayanta takeyi tafad'in yi shuru Ummie daina kuka, barni da Mahmud duk yashigo falon nan saina rama mki dukanki da yayi mki."

Suna hakan sai ga Khalil ya shigo da littafai a hannunshi, yana fad'in " Momy meya faru yau a gidan nan ina shigowa unguwar nan ake fad'amun 'yan sanda sunzo gidan nan harda wnn ya nuna dijama da hannu don har ynzun baisan sunantaba,
suka gani a bayan motarsu."

Momy tace "bkmai akwai abunda ya kawosu wurin Abbanku."

Ya mere bki da dayaga ynda dijama ta wani shigewa momy ajiki ta lafe."

Haushi tabashi ya doka mata tsawa yace "Dan Allah malama ki d'aga mata k'afa karki gajiyar mana da ita."

Momy ta wurga mashi harara tace "ina ruwanka?" Meye nka aciki ina ganin dai k'afatace ba takaba."

"Momy to karta gajiyar da ke tasanya ciwon k'afarki ya tashi."

"Kaga Khalil ni banason tsangwama, kawuce kayi tafiyarka kayi abunda ke gabanka."

Momy taja hannu dijama suka tafi d'akinta cikin dabara da hikima tashiga yiwa dijama nasiha,
"Ummie na ya kamata a ce kin natsu kin fara sanin ciwon kanki, ki tsaya kiyi karatu domin ki hau wani mataki da mu kanmu zamu yi Alfahari dake."

Ki zubarda duk wasu halayanki na k'auye, ki tsaya kiyi karatu ki zama 'yar birni, maiji da kanta."

Ki daina tsokanar fad'a,
Tace "momy banice na tsokanesu ba, sune suka fara tsokanata suja cemun 'yar k'auye, kuma ni ynxun bnaso ana kirana da 'yar k'auye."

Momy tayi murmushi tace "tunda bakiso a dinga kiranki da yar k'auye sai kin tsaya kinyi karatu Arabic da boko, kindaina tsokanar fad'a, kizama kamar 'yar uwarki fateema."

Dijama tace inaso nima nazama yar birnin kamar fateema, ko Dan yaya mahmud ya daina kirana da mai kwanyar kifi yar k'auye, sai idonta ya kuma cika da hawaye."

Momy tadinga share mata,hawaye tare da yimata nasihohi cikin hikima da dabara

taja hannunta tasanya ta toilet ta taimaka mata tayi wanka
momy ta gyara mata gashin kanta, had'ida gyara mata jikinta man shafi kawai ta shafa mata da hoda, da kuma man Baki."

Ta d'auko mata wata dogowar riga ta atamfa tabata ta sanya had'ida d'aura mata d'an kwali ta zubo mata gashinta a bayan ta."

Dijama tayi kyau sosai tafara fitowa 'yar birni, dama kuma dijama kyakkyawace."

Momy tace "eyeh Ummie na kinga ynda kikayi kyau kuwa?"

Dijama taji dad'i tayi dariya."

"Maza kitafi wurin yar uwarki fateema k'arfe uku Khalil zaizo ya kaiku makarantar islamiya."

A guje tafita tana dariya tana jin dad'i."

Momy na ganin yanda tafita da gudu tayi murmushi ta girgiza kai "mai hali baya fasa halinshi."

Momy tafitoTanufi d'akin Abba, ta Tarar dashi yayi zaune a kan kujera yayi shuru alamar akwai abunda yake tunani."

Sallama tayi ta zauna kusa dashi, ta rik'o hannunshi tace "Abban yara lafiya?" Meke faruwa?"

Wani dogon nishi yaja ya dubeta yace "wato lamarin ummie ne narasa ynda zanyi da ita, akan ta natsu ta tsaya tayi karatu, hankalina ya kwanta domin ganin narik'e amanar da d'an uwana ya barmun."

Momy tace "ka kwantar da hankalinka, Ummie tayi mun Alk'awarin cewa ta daina duk abunda takeyi zata tsaya tayi karatu, domin kawai a daina ce mata 'yar k'auye."

Abba yayi murmushi yace "inko hakan ne danafi kowa murna da jin dad'i."

Momy tashiga kwantar mashi da hankali da kalamai masu dad'i, harya fara sakin jikinshi yana dariya, Hajiya Bilkisu kenan mace ta tagari A wurin Alhaji Hassan Adamu Tofa.
Uwa a wurinsu Mahmud da Khalil da fateema."
Da kuma _dijama 'yar gidan tsohuwa๐Ÿ˜ƒ_

Dijama na shiga d'akin su ta tarar da Fateema a kwance tayi wanka tayi kwalliya ta kwanta barci ya d'auketa."

A hankali ta fito ta janyo mata k'ofar ta rufe dan kar ta tasheta daga barci."

Ta sauko falo tanufi kicin tazobo abinci a plate ta tanufi wurin TV ta kwanna tashar MBC 3 suna shirinsu na kartom tanacin abinci tana kallo tana dariya."

Abba dake tare da momy suna hira, ya duba agogo hannunshi yaga k'arfe 3:15 lokacin zuwa makaranta islamiya yayi, da sauri yakira wayar Khalil domin yazo ya d'aukesu ya kaisu, saboda yau ne dijama zata fara zuwa mkranta."

Khalil dake d'akin wani abokinshi suna hutawa da 'yan matansu wayayyi yan boko masuji da Kansu suna zaune a gefensu suna hutawa, ko wannesu yayi matashin filo da Brest d'in budurwanshi ana kallo ana hutawa."

Khalil kansa a kan Brest d'in budurwarshi mai sona Yasmin 'yar wani hamshak'in mai kud'ice a anan cikin garin kano,

Hannunshi d'aya yana sanya cikin pant d'inta yana wasa dashi, ita kuma tashiga shafashi tana wani nishi."

Wayar Abba ta katse masu jin dad'i,

Yayi saurin d'agawa yaji Abba yana cewa "Khalil kana ina ne? To duk inda kake duk abunda kakeyi kamaza kazo ka kaimun su fateema makaranta yanzun nan jiranka nkeyi."

Da sauri khalil ya sauka a kan Yasmin yace "bbyna Abbana kekirana bara naje nadawo,
Kishirya zanbiyo ta nan na d'aukeki na ajiyeki gida tunda bada mota kikazoba.

Ya juya ya dubi abokinsa Auwal da yayi nisa tareda budurwanshi yayi murmushi yace "Auwal baka da sauk'i wlh."

Auwal ya d'ago rinannun idonshi, ya d'aga mashi gira yacika bakinshi da Brest d'in budurwanshi yana sha."

Dariya khalil yayi yaja hannun Yasmin ya canxa mata d'aki yace kijarani a nan tafi nadawo,

Ta dubeshi had'ida kashe ido tace "OK saika dawo my."

Yafito ya ja motarshi yanufi gida."

Kai tsaye cikin falo ya nufa. Da sallamarshi d'auke a bakinshi."

Wata kyakkyawar bby ya hango kwance a kan kujera da alama kallo takeyi barci ya d'auketa TV kawai ke aiki."

Kasa hak'ura yayi sai da yanufi wurinta, gashin ganta yayi tozali dashi Wanda d'ankwalin kanta ya zame, gashin kanta ya bayya ya rufe maya fuska."

"Wow khalil ya furta ya tsinci kanshi da durk'usawa saiti fuskarta yasanya hannunshi yashiga gyara mata gashin da ya rufe mata fuska."

Karan hancinta yagani har baka, Wanda yayiwa kyakkyawar fuskarta kyau yashiga k'are mata kallo yana fad'i a zuciyarshi "gata k'aramar yarinya gata da masifar kyau, kuma
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment