Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

littafinta tana dubawa ko da dai ba komai tasani a cikin littafinba tana karanta wqni wuri wani wurin kuma bata ganewa."

Kiran sunanta shugaban karanta yayi yace tabiyoshi."

Yana tafe tana bayanshi saida ya shiga office dinshi ya zauna snn ita kuma ta duk'a

Ya dubeta da kyau yace khadija bakyajin magana, dama yayanki ya fad'a mun halinki,

Ynzun muka k'are waya dashi yace zaizo ya d'aukeki ya bar garin nan dake yakaiki wata k'asa kiyi karatu a inda bakisan kowaba, kuma ba wnda zaije wurinki."

Ido ta zaro waje ta turo baki idonta ya fara zubar da hawaye. Tana fad'in "Dan Allah malam kayi hak'uri kakirashi a waya kabashi hak'uri na tuba bazan sakeba."

Kuka takeyi Sosai snn malam yace tayi shuru,
Zai kirashi yabashi hak'uri. Amma da sharad'in bazata kuma rashin jiba,

Da Sauri ta d'aga kai tace "eh tayi mashi Alk'awari."

Anan shiga yimata nasihohi a kan ta tsaya tayi karatu da amfanin ilimi ga rayuwar d'an Adam.

Jikinta duk ya mutu Tayi mashi Alk'awarin daga yau zatayi karatu, amma kuma ya kuma jawa prefet kunne karsu daketa."

Murmurshi kawai ya d'aga kai yace xanfad'a masu, snn yabata umurnin ta tashi tawuce aji."

Tun daga ranar Dijamah tashiga karatu baji ba gani tare da taimakon senior rukayyah."

Hankinta ya kwanta karatunta kawai takeyi sai dai wani lokacin idan ta tuna da gida,
Taji kewar tsohuwa, zataja wuri d'iya inda ba mai ganinta taci kukanta har tagaji snn ta share hawayenta ta koma cikin mutane ta zauna."

Duk wani rashin jin magana ko tsiwa duk ta zubar dasu babu abunda ta Sanya agaba sai karatu,
Musamman idan ta tuna da kalaman da yaya Mahmud yake furta mata " takwala mai kwanyar kifi, bata gane karatu,

A kullum idan ta tuna da wad'an nan kalaman nashi sai ta kuma maida hankali a kan karatu domin so takeyi ta nuna mashi ba kwanyar kifin ke garetaba."


Burin ta d'aya ne a yanxun ta ganta tafarajin turanci domin wani lokacin yaya mahmud harda turanci yake zaginta amma bata sanin abunda yake cewa."

Yanzun ba laifi ta fara ganewa,
Dama dijama tana da k'ok'ari da saurin gane karatu, rashin jine yayi mata yawa, bata Samun lokacin zama tayi karatun."

D'aliban makarantar kuma tun daga lokacin da suka ganta tayiwa prefet dukan tsiya kamar mai Aljanu kowannensu ya shiga tsoronta, yana taka tsantsan da ita, ko aikin house akeyi bnda dijama domin kuwa gaba d'aya makarantar shakkarta sukeyi."
A cewarsu Aljanu ke gareta masuyiwa mutum shegen duka."

Wnn dalilin yasa tasamu sauki takeyin abunda takeso ba wanda zai hanata."

Hatta da shugaban makaranta lallab'ata yakeyi baya son ganin b'acin ranta. duk abunda take buk'ata zaiyi mata, domin kawai a zauna lafiya."

***************

5:30 Mahmud ya tashi yyi sallah yayi wanka snn ya sanya k'ananun kayanshi wad'anda suka kuma fito mashi da mazan takarshi ta d'a namiji."

Yana cikin shirinsa saiga wayar Alhaji Atiku yakirashi a kan yayi sauri yafito shi kad'ai ake jira, zasu wuce ibadan wurin trening,

yana kashe wayar mahmud ya kira number Abba ya shaida mashi yanzun zasu wuce, Abba da momy suka yimashi Addu'a sosai snn ya kashe wayar cike da jin dad'i yafito janye da akwatin kayanshi ya nufi harabar gidan inda yakejin hayaniyar mutane da alamar abokanan tafiyarsu ne."

Koda yafito an kammala shirya komai shi kad'ai ake jira, ya bud'e murfin mota ya shiga tareda addu'a a bakinshi."

Anan suka tayar da mota suka d'auki hanyar Ibadan."

Cikin Amincin Allah da yardarsa suka isa garin Ibadan lafiya, a barikin sojoji suka sauka
aka basu masauki cike da girmamawa da karamci."

Shalele na farkawa daga barci misalin k'arfe 10:30am hankalinta na wurin Mahmud domin a daren jiya tayi mafarkinshi suna cikin wani lambu suna shanawa cike da so da k'aunan junansu."

Toilet ta fad'a tayi wanka tafito ta tsantsara kwanliya ta Jan hankali, batare da tayi sallah ba, domin yusra sallah bata dametaba saitaga dama takeyi."

Tana fitowa kai tsaye d'akin Mahmud ta nufa, tana tura k'ofa, taga baya nan babu alamun kayanshi."

Cike da tashin hankali da firgici tashiga diba ko INA a d'akin amma bbu alamarshi,

Ta koma da baya da baya idonta yana zubar da hawaye kai tsaye ta nufi d'akin daddy a lokacin yana tare da mmy mahaifiyarta suna hutawa."

Kai tsaye tashiga d'akin batare da tayi tunanin wani abuba, ko sallama babu,kai tsaye ta fad'a d'akin, ta Tarar da momy kwance a kan jikin daddy tana shafarshi."

Ganinsu hakan bai dametaba, kai tsaye ta fad'a kan gadon tayi wurin Daddy da yana ganin shugowarta yayi saurin janye momy daga kan jikinshi, Ya janyo rigarsa ya sanya yana kallonta yayi mata nuni taxo gareshi."

Tana hawa kan gadon momy ta dubeta cike da takaici da jin haushi domin ita kanta rashin tarbiyar yusra yana damunta, gaba d'aya Alhaji Atiku ya sakantata,
bata da tarbiya ko kad'an,
Mik'ewa tayi tsaye ta kai masu harara snn ta fita ta bar masu d'akin."

Tana ganin fitar momy ta fad'a kan jikinshi ta fashe da kuka mai sauti. Tana fad'in "daddy yayi tafiyarshi dama yana fad'amun baya sona wai ni nakasasshiyace, daddy meye aibuna wanda Mahmud baya sona?
, mena rasa Wanda bn caccaci so a wurin Mahmud ba?""
Pls daddy Dan Allah ka taimakamun Mahmud ya zama nawa mallakina ni kad'ai."

Bubbuga bayanta daddy yakeyi cikin sigar lallashi da kwantar da hankali, yace "daina kuka shalele,

"Mahmud ba tafiyarshi yayiba suntafi wurin trening,
So nawa kikeso na fad'a maki cewa mahmud ya zama naki."

Ki daina d'aga hankalinki kina zubarda hawayenki a kan wani Mahmud can,
waye mahmud? Waye mahaifin mahmud?"
Alhaji Hassan, duk a k'ark'ashin ikona suke."
Ko Alhaji Hassan kikace kinaso, wlh sai kin aureshi bare d'ansa."

Kud'i mulki k'asaaita basu sanyaki zubar da hawayeba, k'aryane wani d'a namiji yasanyaki kina zubar da hawayenki a banxa."

Tashi kitafi d'akinki, kibani nan da wata biyar a lokacin sun kammala trening sunfito da sakamako mai kyau kinga a lokacin sai ayi maganar aurenku da shi."

Sai a lokacin ranta yyi sanyi, tad'aga daga kan jikinshi sukayi ido biyu suka sakarwa junansu murmushi, tace "daddy kabani number shi."

Wayarshi daddy ya lalabo ya shiga contact dinsa ya lalabo number mahmud ya bata,

Ta karba ta Sanya a wayarta tana dariya tana jin dad'i snn tafita."

*****************

Mahmud sunfara trening cikin nasara, da taimakon Allah,

Mahmud mutum ne mai son Addini. Domin duk abunda sukeyi da zarar lokacin sallah yayi zai ajiye yayi sallah, wnn dalilin yasa a cikin barikin na sojoji suka nad'ashi a matsayin limamin masallacinsu"

Baidamu ba illah yaji dad'i hakan da akayi mashi,
Zamanshi a bariki yana fahimta mutane da dama wad'anda 'ya'yan musulmai ne, amma basa son ibada sunfi maida hankali wurin aikata Sab'o kamar xina da shaye2."

Dan haka baidamu da ya zauna a cikinsuba,
Abokinshi d'aya ne sulaiman,

Sulaiman mutum ne mai son Addini, Dan haka abotansu tazo dai2 da mahmud."

Da zarar sundawo daga wurin trening idan sukayi wanka sukaci abinci sukayi sallah,
Basuda wurin zama sai a bakin massaci tareda sulaiman zasu fara fira."

Sulaiman zaifara bashi lbrin matarshi fareeda da d'ansu d'aya Ammar irin ynda yayi kewarsu, mahmud yana tausaya mashi domin ya fahinci yana matuk'ar son iyalinshi."

Shi kuma Mahmud ba wanda yake tunani tana sanyashi dariya sai dijama,
Hakan zai zauna yayita bawa sulaiman labarin dijama,
Sulaiman yana dariya wani lokacin harda rik'e ciki."

Saboda yawan labarin dijama da yake yawanyi ko a d'akin barcinsu gaba d'aya d'akin ba wanda baisan dijamah ba, a bakin Mahmud."

Wani lokacin yana bawa sulaiman labarinta yana dariya,
Sulaiman ya dubeshi yace "Ayyah k'anwar nan taka ba 'yar gida za'ayiba kuwa?"

Mahmud yyi murmushi yace "karufamun asiri duk Wanda ya aure dijama dare d'aya zata kasheshi da fitinarta."

Sulaiman ya kuma sakin dariya yace "ni kuwa sai naga tsantsar soyayyarta da k'aunarta a tare dakai,"

Wata kalar dariya mahmud yasaki Wanda baisan yanayintaba,
yarasa dalili duk lokacin da ake mashi hirar dijama saiya tsinci kansa cikin farin ciki."

"Dole naso dijama saboda 'yar uwatace jininace, duk a cikin k'annena babu Wanda nkeso sama da dijama saboda tunda aka haifeta Allah ya d'oramun sonta, amma soyayya irin ta 'yan uwantaka ba Irin taka da fareeda ba."
Ni har yanzun ba'a haifamun matar da zan aura ba,
Ya k'are maganar yana dariya."

Sulaiman zaiyi magana kenan, wayar Mahmud ta d'auki k'ara, yacirota a Aljihunsa yana dibawa yaga bak'uwar number ce d'agawa yayi had'ida yin sallama."

Yusra dake gefe d'aya kwance akan lallausar gadonta,
tanajin tattausar muryanshi ta lumshe ido ta janyo pillo ta rungume tasaki ajiyar zuciya snn takashe murya tace "hello honey nasan zakayi mmkin ganin kirana a dai dai wnn lokacin
Ba abun mmki bne dan masoyiya ta kira masoyinta kasani " *ina sonka*."

Dogon tsaki yasaki had'ida fad'in shed'aniya kawai Allah ya shiryeki,
Yayi saurin kashe wayar shi"
Ya maida kallonshi a kan sulaiman dayaga tarin tambayoyi a fuskarshi."

Anan yashiga bawa sulaiman labarin duk abunda ke faruwa,

Sulaiman ya girgiza sosai snn yace "kadage da Addu'a muma zamu tayaka, domin irin wad'an nan matan shed'anune."

Mahmud yace "Allah yafita."

*****************

Yau ake zuwa visting makarantar su dijama,
Mahmud yana lissafe, da kwanakin

Ya d'aga waya yakira Abba yake shaida mashi,

Abba yayi dariya yace kwantar da hankalinka mahmud ga momynka can a kicin tana shirywa dijama lafiyayyen abinci yanZun tamutafi."

Dariya Mahmud yayi yace "to Abba Allah ya k'ara girma, dama na d'auka Momy ta mntane, kar a k'i jemata safiyar gobe kuganta ta dawo d'auke da a kwatin kayanta."

Abba yayi dariya yace " shikenan kun renamun ummie na baZatayi hnkaliba kuke nufi."

Suka saki dariya gaba d'auqnsu, snn mahmud yayi mashi sallama yakashe wayar."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅





Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)





*21*





Momy ta kammala shirinta tsaf, cikin wata atamfa Holland. Green colour Wanda tayi mata kyau matuk'a."

Abba da fateema kuma suna palo suna xaman jiranta."

Fitowarta daga d'akin kenan,
yayi dai dai da shigowar Khalil,
Sanye da wata dakkiyar shadda Wanda tayi mashi kyau,
ta mayar da shi kamar wani babban mutum,

Daga wurin d'aurin auren abokinshi yafito."

Abba ya d'aga kai ya dubeshi yace "yawwa Khalil tunda Allah yakawoka mutafi kayi driven d'inmu, xuwa makarantarsu dijamah."

Tunani yashigayi wai dama bata gidan ne?"
Gske kwana biyu yaji gidan ya xama normal ba hayaniya ba k'auyanci"

Ba yanda ya iya tunda umurnine daga wurin Abba,

Yashiga mganar zuci, yana fad'in, Amma gskya Abba dakasan halin da nake ciki yanxun da ka barni natafi na sauke buk'ata ta, dan wlh Allah a matse nke."

Ya riga da ya ajiye 'yan matan da zai huta dasu,
A gidan Ahmad yanxun hakan uzurce yake kud'i yazo d'auka. Ya koma wurinsu."

Ba yanda ya iya hakan ya kalli Abba ya mirgina kai, yace "to Abba."

Had'ida duk'awa ya d'auki kulolin abincin da momy ta shiryawa dijama yanufi mota dasu."

Driven yakeyi sannu a hankali, yanda Abba ya umurce shi yayi,

gaba d'aya hankalinshi yana wurin baby's dinshi, wad'an ya ajiye suna zaman jiranshi,

gasu sabbin kamu ne a wurin dinner abokinshi ya samosu

Yana cikin tunanin hakan,
sai ga kiran Ahmad a
Wayar shi,
Yana kallon wayar na ringing a gefen hannunshi amma ya k'i d'agawa,

a hankali yake satar kallon Abba dake gaban mota zaune a kusa da wayar."

Karo na biyu Ahmad ya kuma kiran wayar saida ta kusan tsinkewa bai da niyar d'auka,
Abba ya juya yana kallon screen d'in wayar yaga an rubuta ( _Best friend Ahmad_ ). Abba yace meyasa bazaka d'auki kiran Ahmad ba?"

Kasan cewar mahaifin Ahmad abokin Abba ne sosai,
Abban yana matuk'ar ganin natsuwa da kamala Ahmad.

Domin a duk inda Ahmad ya ci karo da Abba,
sai ya cire hular kanshi ya durk'usa har k'asa ya gaida Abba cike da girmama da natsuwa."

"Abba yace "Ka d'auka mana."

Gaban Khalil ya yanke ya fad'i Dan yasan maganarda Ahmad zaiyi mashi,
Ya kai hannunshi zai d'auka kenan wayar ta tsinke,

Anan take ya sauke ajiyar Zuciya yaci gaba da driven d'inshi yana addu'a Allah yasa kar ya kuma kiranshi."

Kiran ya kuma shigowa a karo na uku."

Cike da fad'uwar gaba cikin sanyin jiki ya d'aga wayar had'ida yi mashi sallama cikin natsuwa kamar wani na Allah."

Yanayi yana satar kallon Abba,
"Yana fad'in inajinka abokina "Dan Allah sababin kayan nan da nakawo maka, ka ajiyemunsu Karka bari kowa ya kwada mun kayana,
daga ciki kuwa har da kai,
Saboda kasan kafini girma, da zarar kasanyasu bud'ewa zasuyi,
Kuma sanin kankane bana sanya kaya idan har suka bud'e."

Yanzun ina kan hanya zan kai Abba da momy unguwa ynzun zan dawo."

Ahmad najin hakan ya gane maganar abokinshi a Inda ta nufa,
Yace "karka damu abokina a inda ka ajiye kayanka suna wurin bantab'a maka ba,

Saboda nima inada irinsu yanzun,hakan sanye nake dasu a jikina, kai dai
Sai kundawo Allah ya tsare INA gaida Abba da momy, sukayi sallama ya ajiye wayar."

Ya kuma satar kallon Abba,
yaga ya maida hankalinshi a karatun jaridarshi yana murmushi a fuskarshi,

Shima murmushin yyi ya sauke ajiyar zuciya yaci gaba tuk'in motarshi sannu a hankali
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅





Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)





*22*






Dijama da tunda safiya ta waye Senior Rukayya ta bata labarin yau 'yan gida suke zuwa _visiting_

Murna takeyi da tsalle zata ga Momy da Abba,
senior Rukayyah sai dariya take yi mata, irin ynda take tsalle kamar wata 'yar baby."

Can kuma sai tab'a fuska
Senior Rukayya ta tambayeta "meya faru."

tajuya Ta kalli senior rukayya dake yi mata kitso tace "Allah yasa Abba yazomun da tsohuwa dan nayi kewarta da yawa,
A Daren jiya harda mafarkinta nayi."

senior rukayya tasan da lbrin tsohuwa a bakin dijama.
Da zarar an zauna zaman fira,
dijama batada lbrin da takeyi sai na tsohuwa da yaya mahmud, Dan haka duk cikin fad'in makarantar duk Wanda yasan dijama to yasan tsohuwa da yayanta mahmud,"

Senior rukayya tace "daina b'ata fuska khadija,
zagiga tsohuwa insha Allahu."

Anan senior Rukayya ta gyara dijama tayi mata kitso da kunshi, tayi mata wanki da goga,
ta kaita tayi wanka ta tashirya mata cikin uniform d'inta wad'anda sukayi mata mugun kyau, fuskarta tafito farinta ya Kuma k'aruwa, duk sauran wann k'auyancin ya fita a jikin dijama."

Wanda a yanzun duk wanda ya San dijama a da ya ganta a yanzun da wuya ya iya ganeta, saboda tafara zama dijama yar boko."

Senior Rukayya tana kammala shiryata sai ga kira a bakin k'ofa,
. cewa khadija hassan tafito yan gidansu suna nemanta."

Cike da farin ciki wanda ya kasa b'oyuwa a fuskarta tabi bayan d'an aiken cike da murna da jin dad'i."

A can ta hango momy da Abba da fateema zaune a mota, cikin farfajiyar makarantar, Suna ganinta suka saki murmushi gaba d'ayansu suka bud'e murfin motar suka fito, amma bnda Khalil da hankalin shi baya wurin ya tafi wurin kallon wata prefet da ya ganta ta cika dam,
K'irjin nan nata cike yake da dukiyar Fulani, hakan hips d'inta sun bayyana cikin hijabinta." Kallonta kawai yakeyi yana lashe baki, a nan take gabanshi ya mik'e cikin wandonshi yayi saurin sanya hannu ya rik'e had'ida d'ora kanshi a kan sitiyarin mota yana sauke numfashi a hankali."

A guje ta Rugo ta rumgune momy tana dariyar jin dad'i sann tasaketa taje wurin dady shima ta rumgumeshi cike da murna, snn ta rumgume fateema tana dariya tace "sister nayi missing d'inku."

Fateema tace "muma hakan munyi missing dinki sister."

Anan ta shiga waige waige momy tace "mekike nema ummie?"

Ta turo baki tace "ina yaya mahmud banganshi ba, bayan shi yace da zarar nayi wata d'aya zaizo yacireni a wnn karantar ya mayardani gida kusa daku."

Momy ta rik'a hannunta tace "eyyah ummie Yayanki baya gari, yayi tafiya ya tafi wurin trening d'in soja kiyi mashi Addu'a Allah yabashi sa'a."

Dijama ta turo ido waje tace "soja tab lallai kuwa zai k'aro mugunta."

Suka sanya dariya gaba d'ayansu snn suka nemi wuri suka shinfid'a k'atuwar darduma suka zauna gaba d'ayansu Suna dariya, momy tana yaba Kyan da taga dijama tayi kamar ba itaba."

Khalil da ke zaune cikin mota,
cikin ma wuyacin hali,
ya d'aga kai yana kallon su momy,
A can ya hangosu zaune wuri d'aya sai fira sukeyi suna dariya harda Abba a hankalinsu a kwance,
tareda wata 'YAR farar yariya kyakkyawa."

Yace "ko ina kuma momy tasan wancan yarinyar 'yar beauty?"
Meyasa bazasu aiketa ta nemo masu Wanda sukazo nema ba suyi su sallameta mutafi."

Cikin jin haushi ya bud'e murfin motar ya fito ya nufi wurinsu."

Yana zuwa a gefen dijama ya zauna had'ida k'ura mata ido yana mata kallon tsaf, samanta da k'asanta, yake kallo irin kallon nan nasu na 'yan duniya,
bai San lokacin da ya d'aga hannunshi ba ya shafi gefen fuskartaba yace _fine girl_

Yana murnushi yace momy INA kika San wnn beautyn tana da kyau."

Dariya suka saki gaba d'ayansu,
Dijama da Dama ta tsaneshi ta harareshi ta murgud'a baki tace baraka kallah, masha Allah,
karka cinyemun kyau sai gani sai hange."

Yanayin ynda take tsiwar yayi matuk'ar yi mata kyau, sai gani yayi ta kuma burgeshi,

Yana murmushi ya kalli Abba da momy yace "momy wnn yarinyar ta burgeni sosai, ina kamu"

Duk lokacin da Abba ya bani umurni Na nemo matar aure to itace zab'ina,
Momy 'yar k'awarki ce?"

Momy tayi dariya tare da fateema, ganin bai gane dijama bace wacce ya tsana saboda k'auyancinta."

Abba kuma yanajin hakan sai da gabanshi ya yanke ya fad'i, dajin kalaman khalil akan dijama,
Meyake son faruwa ne a nan gaba a cikin familynsa?"

Murmushi ya k'akaro ya dubi khalil yace "baka ganeta bane k'anwarka ce fa dijama."

Da sauri khalil ya kuma juyawa yana kallonta cike da mmki, ya kuma kai hannunshi zai kuma shafar gefen fuskarta Wanda tafi burgeshi."

Da sauri dijama taja da baya tana harararshi cike da tsiwa tace " _dant touch me_🖐🏿


* *tofah 'yar gidan tsohuwa da turanci*🤗🤗


*iya comment d'inku iya typing d'inku*🤷‍♀
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅





Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)





*23*





Ta mik'e da sauri tabar mashi wurin, ta koma gefen Abba ta zauna a kusa da fateema."

Khalil ya kuma kallonta cike da burgewa,
Da murmushi d'auke a fuskarshi yanunata da hannu yace _are you a dijama 'yar gidan tsohuwa_?"

Ta langwab'e kai cikin tsiwa, tazaro ido tace _are you seprise_?"
Had'ida murgud'a mashi baki."

Kuma zaro ido yayi waje cike da mmki, yana kallon d'an k'aramin bakinta mai tsiwa."
Pink colour shar dashi,
Ya langwabe kai yana kallonta, had'ida lashe Baki, domin jiyakeyi kamar yaje ya kamota ya rungumeta ya tsotse d'an k'aramin bakinta yakeji."

Abba yace " _Gud_ ummie na yau xanyi baccin farin ciki,
A yau ganau nake ba jiyau ba, da kunnuwa na guda biyu naji ummie nah tana zaro turanci, kai Allah Na gode maka ina ma mahmud yana kusa da yafi kowa farin ciki da wann ranar."

Dariya tasaki tace "Abba saboda Mahmud kawai na dage nakeso na iya turanci, saboda ya daina cemun mai kwanyar kifi,
Kuma ya daina zagina da turanci, saboda kawai dan yaga banajin abunda yake cewa."

Abba yayi murmushi yace "Allah yak'aro ilimi mai yawa mai amfani ummie nah "

Ta amsa da "Amin Abba nah,
Can kuma ta marairace fuska tace "Abba tsohuwa fa?"
Duk Na kwanta bacci sai inyita mafarkinta."

Abba yayi murnushi yace "tana nan lfyarta k'alau jiya ma nadawo daga tofar."
_Next month_ idan za'a kuma zuwa visiting zanje Na d'auko mki ita muzo tare ki ganta."

Khalil ya nisa ya d'auke idonshi daga kallon dijama da yakeyi tun d'axun,

ya maida kallonshi a kan Abba yace Abba"mai yasa kace brother zaifi kowa murna da ganin dijama hakan?"

Abba yace "saboda yafi kowa son yaga ta tsaya tayi karatu, wanda zata inganta rayuwarta,dashi,

Mahmud ya shirya d'aukar ko wanne irin mataki domin ganin Ummie tasamu ilimi mai yawa mai amfani wanda ko ina ne a cikin fad'in k'asar nan Dama wajenta."

"Kai fa?" Abba ya tmbayeshi."

Snn kuma dijama ta shice shi ya raineta tun tana k'aramarta, yafi kowa shak'uwa da ita duk a cikin family."

Khalil yayi shuru yana tunanin wani Abun,
Jin da yayi Abba yace dijama ta mahmud ce gaba d'aya yaji ranshi ya b'aci,
Yaja doguwar ajiyar zuciya, yace "Abba dijama bata brother bace,
Dijama ta kowa ce a cikin family 'yar uwar kowace kowa yana da dangantaka da ita, bashi kad'aiba
Amma Abba idan kana fad'in dijama ta brother ce sai naga kamar a kwai wata manufa."

Abba ya tsure shi ido yana kallonshi, yana kuma karanto wani Abu a tare dashi,
Sai da ya d'auki minti biyu yana kallonshi snn yace "eh ba k'arya kafad'aba Khalil akwai wata manufar,
Kuma Karka kuskura ka tambayeni ko wacce manuface, amma abunda nakeso Na fad'a maka shine duk abunda kake na sartawa ryuwarka akan ummie da mahmud to hakan ne babu ko tantama."

Kai kuma sai ka cire naka banzan tunanin da kakeso kafara a yanzun."

Abba ya kalli dijama da ta mayar da hankalinta a can wurin fateema suna fira suna dariya."

Yace "ummie Na tashi ki d'auki kayanki kije ki kai hostel ki ajiye kidawo muyi sallama tafiya zamuyi."

Cikin shagwab'a tace "Abba ni xan biku mutafi, yaya mahmud yace da zarar nayi wata d'aya zai zo yacireni a makarantar nan gaba d'aya."

Momy ta rik'o hannunta cikin sigar lallashi take cemata "yi hak'uri ummie idan Wanda ya kawoki ya dawo shi da kansa zai cireki mu nan da kika ganmu bama da ikon cireki batare da mahmud ya aminceba."

Khalil yanajin furucin momy ya mik'e tsaye a fusace yanufi mota ya bud'e ya shiga ya rufe had'ida d'ora kanshi a kan sitiyari yana tunanin wai meke shirin faruwa dashine?"

Runtse idonshi yayi, amma babu abunda yake gani sai kyakkyawar fuskar dijama, tare da d'an
k'aramin bakinta."

Tafiyar da yyi a fusace Zuwa mota, Abba da momy suka bishi da kallo, suka juyo a tare suka had'a ido suka kalli junansu, ko wannesu da tambaya a bakinsa."

Fateema ta katse masu tunani tace Abba wai meyake damun yaya khalil ne naga kamar yayi hushi yatafi."

Momy tace "kije ki tambayeshi mana ai gaya can a mota saiya fad'a mki

Dijama da bata kula dashiba, tace "sister tayani mud'auki kayan nan mutafi d'aki Na ajiyesu."

Anan suka Shiga d'ibar kayan shopping d'in da Abba yayi mata tareda d'aukar kulolin abinci suka nufi hostel dasu."

Senior Rukayya tana kwance a kan gado, kasan Cesarwar ba 'yar garin nan bace bata sa ran za'a zo mata visiting, taga dijama ta shigo da kaya nik'i nik'i kamar Wanda za'a bud'awa wani k'aramin shago."

Da sauri ta duro daga kan gadon tashiga taimaka masu suna ajiyewa bayan sun gama ajiyewa
Senior rukayya ta

Please Login or Register in order to submit comment