Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli fateema ta kuma kallon dijama tace "khadija wnn k'anwarki ko?"

Dijama tayi dariya tace "k'anwatace uwarmu d'ayan ubnmu d'aya fateema ne sunanta."

Senior rukayya tayi murmushi cike da burgewa domin kuwa sunyi matuk'ar burgeta, tace "kunban sha'awa kamarku d'aya."

Anan fateema ta gaida ita, ta amsa tana dariya had'ida dafa k'afad'arta tace "Abba ya kawo mana ke nan mana."

Batace komaiba illah tayi dariya, dijama tace "yawwa Anty kizo mutafi ki gaida Abba da momy nabasu lbrinki."

Cikin minti biyar senior rukayya ta sanya uniform d'inta tafito tabiyosu dijama."

A bakin mota suka hangosu tsaitsaye alamar fitowar su kawai suke jira zasu tafi."

Senior rukayya taje ta durk'usa ta gaida momy da Abba,

Suka amsa mata cike da kulawa, tare da yimata godiya kula da takeyi da dijama."

Abba yaciro dubu biyar ya mik'a mata dakyar ta amsa had'ida yimashi godiya."

Sukayi masu sallama suka bud'e mota suka Shiga, idon dijama ya cika da hawaye,
Ganin zasu tafi subarta."

Khalil da ya tsura mata ido yana kallonta ya kasa d'auke idonshi daga gareta ganin zubar hawayenta da yayi, bai San lokacin da ya bud'e mota yafitoba, cikin sauri ya nufota yana Neman ya rungumota ya lallashe ta ta daina kuka."

Tana ganin hkan tayi saurin Jada baya tana wurga mashi kallon tsana, had'ida ya tsine bki cike da tsiwa tace "wai meye hakan ne?"

Gskya yya Khalil INA ganin yau kamar ba kanka d'ayaba,
Karka mnta dijamace fa 'yar k'auye Wanda ka tsana a kan komai a ryuwarka to meye nason ka tab'ani?"

Kafa rik'e girmanka kafa sanni sarai bana barin bashi idan naga ana neman a shiga hak'k'ina."

Turus yaja ya tsaya yana kallonta a maimakon yaji haushi. Kalamanta saima ya tsinci kansa da yana sakar mata murmushi."

Ya sanya hannu a Aljihu ya ciro kud'i masu ywa wad'anda shi kanshi bai San adadinsuba ya mik'awa Senior Rukayya yace "kici gaba da kula da ita ynda ya kamata zandawo wani sati."

Senior Rukayya tana wani rangaji da rangwad'a had'ida kashe murya,
Duk a tunaninta da Mahmud take magana,
tace "kula da k'anwarmu ai dolene baka da Matsala indai wnn ne,"

Jin ta canza murya tana wani fari da ido,
Khalil ya d'aga idonshi ya d'orashi a kanta, yana mata kallon tsaf, saman ta da k'asanta."
Ganinta yayi wata 'yar ramammiya tsaye take wuri d'aya kamar 1 bata da inda namiji sai tab'a yaji d'an taushi a jikinta gaba d'ayanta bata da wani abun burgewa."

Ido biyu sukayi da ita yayi saurin gauda idonshi daga kallonta domin shi har ga Allah irin wad'an nan matan haushi suke bashi, duk Neman matansa baya son irin wad'an nan, Wanda zaka dinga dambe da k'asusan jikinta,
Kuma irinsu sai zurfin tsiya kamar kafad'a rijiya idan kashigesu."

Dijama ta wurga mashi harara tace "kadawo wurin wa?"
Wlh Allah ko kadawo bazan fitoba mugu kawai, ko ka d'auka na mnta tsanar da kakeyi mun, tare da muguntar da kakeyimun?" ta murgud'a bki tace "karka kuskura kadawo domin bana buk'atarka."

Abba da ke cikin mota suna hango shi,
sun dai gansu Suna magana amma basajin abunda
Suke fad'i."

Fitowa Abba yayi ya kira sunanshi,
Khalil yayi saurin juyowa da sauri yana kallon dijama ya wuce yanufi mota ya tayar,
Gaba d'ayansu suna d'aga mata hannu itama tana d'aga masu idonta yana zubar da hawaye."

Tafiya sukeyi ba Wanda ke magana ko wannensu da akwai abunda yake tunani a ranshi,

a hakan har suka isa Gida, cikin farfajiyar gidan wurin ajiye motoci khalil yayi parking yafito ya bud'ewa Abba da momy k'ofa suka fito batare da sun kulashi ba, suka nufi cikin gida,

Yana ganin tafiyarsu ya koma mota yafigeta da k'arfi ya nufi gidan Ahmad."

Kai tsaye suka shiga babban falon gidan kowanne ya nufd'akinshi domin watsa ruwa ya huta."

Abba bayan ya kammala wankanshi sanye yake da jallabiya, ya kwanta rigigine a kan gado yana tunanin abubuwan da suka yita faruwa tsakanin khalil da dijama da irin magagganun da khalil yayita yi."

Momy ta turo k'ofa tashigo da sallamarta, ya amsa mata ta nemi wuri ta zauna a kusa da shi."

Ta dubeshi cike da kulawa tace "Abban yara, katashi Inaso zamuyi magana.".

Abba ya mik'e zaune had'ida da kallonta."

Itama d'in shi take kallo suka fuskanci junansu,
Snn tayi kyaran murya ta kwantar da murya cikin lumana, tace "Abba yarah, meka fahimta tsakanin khalil da Ummie?"

Abba yace "ban fahimci komaiba illah sakarcinsa da yakeso ya fito mana dashi abunda bazai tab'a yiwoba."

Domin bai isa ya sanyani na karya Alk'awarin dana d'aukarwa d'an uwanaba, kafin yabar duniya,
Tun lokacinda aka haifi Ummie na d'auketa nayi mata hud'uba, na sanya mata suna nana khadija,
marigayi ya furta da bakinshi 'yace "Allah ya rayaki Nana khadija matar mahmud,

Ya juyo ya kalleni mukayi ido biyu da shi, ya dafa kafad'ata yace "yaya ko bayan bana raye,
nana khadija matar mahmud ce Mahmud shine mijin khadija."

A lokacin naji dad'i nayi murna, sosai, hankalina bai kuma kwanciya ba sai bayan mutuwar d'an uwana naga ynda Mahmud yake kula da ummie da irin son da yake nuna mata, bayan gaba d'ayansu ba wnda yasan da wnn mgnar har zuwa ynxun da nake fad'a mki."

Karyane khalil yaxo daga baya ya karyamun Alk'awarin da na d'aukarwa d'an uwana. Bai isaba wlh sai dai soyayyar ummie tasan ynda zatayi dashi, ko kuma keda kike mahaifiyarshi ki lurar dashi kibashi hak'uri, Dan wlh ko hkri bai isa na bashiba."

Momy taga Abba ya d,auki zafi sosai, taja doguwar ajiyar zuciya tace "Allah yabaka ikon ai watar da wasiyyar d'an uwanka."

Yace "Amin cike da sanyin murya."

Ta kuma kallonshi cikin taushin murya tace "har ynxun bazanyi k'asa da murya ba wurin nemawa khalil Alfarma a wurinka akan ka amince ya fitar da matar da yakeso a aura mashi ita,
domin samun kwanciyar hankalinshi da namu baki d'aya."
Idan har kayi dibo da yanda yake yiwa 'yan mata wani kalar kallon a gaban ni da kai ya isa ya tabbatar maka da khalil ba irin mazan da za'a jamasu dogon lokacin da zasuyi aure ba."

A razane ya d'ago kai ya dubeta, yace "wai ni ko hajiya Bilkisu meyake damunki ne?"
Sau nawa kikeso nayita fad'a mki khalil bai isa aureba,

Kina hana saurayi mai lafiya yak'i kallon 'yan mata?"
Ko kuma so kikeyi da zarar yaga macce ya rik'a sunkuyar da kanshi k'asa,
Ki kuma zuwa kicemun kina ganin yaron can baya da lafiya mutashi tsaye munema mashi magani."

To bari inyi maki mai kankaf, ko bayan raina banyafe khalil yayi aure yanzunba har sai ya kammala karatunshi ya samu aiki Wanda zai zama madogara gareshi da iyalinshi baki d'aya."
na gama magana tashi Dan Allah kitafi d'akinki ina buk'atar Hutu."

_tofah Abba ya d'auki zafi_🤔

Bata kuma yin maganaba illah ta mik'e tsaye ta nufi d'akinta ranta duk a dagule."

*****************

Akwana a tashi ba wuya, mahmud har yayi wata uku da fara trening d'inshi,

A kullum Yusra da sonshi take kwana take tashi,
Duk wata hanya da macce zatabi domin ganin taja hankalin d'a namiji a waya ko a chat amma a banza takeyi."

Kullum da sabon photon da take tura mashi a chat tare da kalaman soyayya masu sanyi,
wanda da ita da wanda yake zindir basuda wani banbaci."

Duk lokacin da mahmud ya bud'e pic d'inta sai ya runtse idonshi saboda tsaraicinta da yake gani, tareda tsine mata Albarka, daga k'arshe yyi blocking d'inta,
Dama kuma baya d'aukar kiran wayarta."

Hakan da yyi mata ba k'aramin d'aga mata hankali yyiba, a rayuwarta bbu d'a namijin da ya tab'a wulak'antata kamar Mahmud,
kuka takeyi sosai irin yanda soyayya Mahmoud ta addabeta a zuciyarta"

Idan ya San wata ai bai San wataba."

K'arfe d'aya da rabbi na dare tashiga shirya birthday d'inta gobe takeso zatayi shi misalin k'arfe biyar na yamma kuma harda mahmud take buk'atar yazo,
Ko Dan saboda ta kalle kyakkyawar fuskarshi taji sanyi a ranta."

Tunda k'arfe 6:30am ta dura d'akin daddy baiko tashi daga barciba ita ta tasheshi, tana shiga shaida mashi yau ne ranar zagayowar ranar haihuwarta."

Zumur ya mik'e zaune yana murmushi yana fad'in happy birthday my daughter, ya janyota zuwa jikinshi, yace mekikeso na shirya maki natayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki?"

Ta kuma shagwabe masa a jiki tace "daddy Abu d'aya nakeso kayi mun."

Yace fad'eshi shalele kinfi k'arfin komai gareni."

Tace "daddy so nakeyi mahmud yazo yau d'in nan domin ya tayani murnar zagayowar ranar haihuwata idan kayi mun hakan daddy to ka gama bani gift d'ina na wnn shekarar wanda zanfi jin dad'insa a kan komai."

Murmushi daddy yayi ya d'anyi Jim kad'an yana tunanin fitowar mahmud a yanzun suna cikin trening dai dai yake da rugujewar wata uku da yayi yana wahalar trening d'insa
Kuma bayason ganin b'acin ran shalele gwara ya faranta mata rai,
Ran kowa ya b'aci daga ciki kuwa har da ranshi."




_BARKA DA JUMA'A DA FATAN KOWA YA WAYI SAFIYAR JUMA'A LAFIYA_
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅





Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)





*24*






Can kuma yaja dogowar ajiyar zuciya ya kalli Yusra ya sakar mata murmushi,
da ya tuna _weekend_ akeyi su mahmud a yanzun basa aikin komai sai hutu."

Yace "shalele indai wnn ne bkida matsala kisanyawa ranki kamar kina tare da mahmud a yanzun hkan."

Barima kijiyewa kunnenki."

Ya lalubo wayarshi a k'ark'ashin pillownsa,
Yashiga contacts d'inshi,
ya danna lambar shugabansu mahmud wanda yake kula da duk wani motsinsu da lafiyarsu."

Hands free ya sanya wayar ynda zata iyajin maganar da ke fitowa daga cikin wayar."

Cikin girmamawa oga yake gaida Alhaji Atiku,
Cike da kulawa yake amsawa,
Snn ya shaida mashi yana buk'atar mahmud Hassan yazo Abuja yanzun nan yana nemanshi."

Zubewa k'asa oga yayi kamar Alhaji Atiku na ganinshi, yashiga bashi hak'uri,
Yana cewa "idan wani laifi yayi ranka ya dad'e ina rok'ar mashi Alfarma dan Allah ayi mashi hak'uri kar a d'auke manashi a nan,
Yaron hazik'ine yana da kwaxo sosai wurin trening gashi da son Addininshi."

Ranka ya dad'e mahmud yana Neman yafiyarka tuba yakeyi bazai sakeba."

Alhaji Atiku ya saki dariya, yace "ba abunda Mahmud yayimun sai Alheri,
Neman da nake masa sak'o nkeson na bashi _hand to hand_
Batare da kowa yasan komaiba, karka damu gobe zaidawo gareku, abunda nakeso da kai kabashi mota lafiyayya ayimata full da mai.
wanda zai iya kawoshi Abuja ya kuma maidashi batare da wata matsalaba."

Oga ya sauke ajiyar zuciya yace "angama ranka ya dad'e."

Snn Alhaji Atiku ya kashe wayar, yana kallon shalele had'ida kashe mata ido d'aya,
Dariya suka saki gaba d'ayansu ta kuma fad'awa jikinshi ta rungumeshi tana fad'in nagode daddyna kana faranta mun rai, kana yimun duk abunda nkeso, Allah ya k'ara maka yawancin rai da nisan kwana ."

*****************

Mahmud yana zaune tare da sulaiman suna hirarsu kamar ynda suka saba idan basuda aikinyi."

_massage_ yagani ya shigo a wayarsa, kamar bazai duba ba kuma dai ya tsinci kansa da yanaso yaga ko wanne irin sako ne."

Bak'uwar number yagani karon farko dariya yaga anfara sanyawa kamar haka."

_Hhhhhhhh sweetyna kenan na fad'a maka duk abunda nakeso sai na sameshi, kashirya zuwa garin Abuja ynzun nan domin tayani murnar zagayowar ranar haihuwata wanda na shiryashi domin kai, domin inyi tozali da kyakkyawar fuskarka mai cike da Annuri, byee sai kazo_

Cikin bak'in ciki da takaici ya gama karanta massage d'in d'aga kansa da zaiyi yyi ido biyu da ogansu,

Yace "mahmud Hassan sak'o daga _commondent General_ ya mik'a mashi key d'in mota yace ynzun nan yana nemanka garin Abuja."

Idon mahmud suka rikid'e zuwa launin ja, ya d'aga kai ya dubi ogannasu sai da yayi kamar ba xai karb'i key d'in ba,
Tunawa yayi da hud'ubar da Abba yayi mashi, "kayiwa Alhaji Atiku biyya tamkar shi ya haifeka, KA kuma d'auke shi tamkar ni mahaifinka, karka sab'a mashi ko kuma KA b'ata mashi."

Sai da ya runtse idonshi sann ya bud'esu, yasanya hannu ya karb'i key d'in motar a hnnun ogan nasu, snn
Oga yyi tafiyarshi."
Mahmud ya mik'e tsaye had'ida kallon sulaiman wanda shima shi yake kallo,"

Sulaiman yace "aboki mai yake faruwa ne?"
Mahmud yayi murmushin yak'e wanda yafi kuka ciwo yace "Abokina ba lokacin da zanyi maka bayani, kayimun Addu'a sauka lafiya, amma kuma yau zandawo komai dare,
Yana kaiwa nan ya wuce ya shiga mota ya tayar ya d'auki hanyar Abuja."

A yau Yusra cike take da murna da farin ciki, duk Wanda yasan Yusra ya kalli fuskarta a yau yasan farin cikinta na yau daban ne."

Hotel ta sanya aka kama mata naji da gani wanda ake Alfahari da ita a cikin garin Abuja."

Gaba d'aya friends d'inta saida ta gayyatosu da abokanen holewarta maza da mata, tana shaida masu masoyinta wanda zata aura, yana kan hanyar tahowa."

Gaba d'aya holl d'in anzagaye shi da babban kalanda mai d'auke da pix d'inta Dana mahmud wanda tasanya aka had'a mata shi,
Sunyi masifar yin kyau dama Yusra kyakkyawa CE, to bare kuma mahmud."

K'arfe biyar da rabi kowa ya halarci wurin daga ciki kuwa harda ita,

kid'e kid'e kawai kakeji yana tashi ko wacce budurwa rungume da saurayinta ana holewa wasu kuma suna manne da juna suna shan shisha."

A can sama take zaune tana kallon kowa d'aya bayan d'aya tana d'an kurb'a lemo a hannunta,
tanayi tana kallon agogon dake d'aure a hannunta, lokaci na tafiya har ynxun sweety bai k'arasoba to ko lfy?"

Tashiga tmbyar kanta."

Mahmud da gudu yakeyi ba kakkautawa Allah dai ya tsareshi ya shigo garin Abuja lafiya."

Kai tsaye gidan Alhaji Atiku ya nufa, ya tarbeshi cike da murna da farin ciki, anan yke shaida mashi dalilin kiran nashi, da yyi
shalele ce takeyin birthday,
Ta d'aga hnkalinta sai kazo ka tayata murna."

Murmushi yak'e kawai yyi baice komaiba,
Amma cikin zuciyarshi jinta yakeyi kamar ta fashe saboda bak'in ciki."

Alhaji Atiku baidamu da yanayin da mahmud yake cikin saba,
Illah ma sai dariya yakeyi domin yasan yau shalele zatayi barcin farin ciki, taga abin sonta

Batare da b'ata lokaciba ya shiga yimashi kwatancen inda take,
Yace " Idan kuma bazaka ganeba bari na had'aka da sojoji suyi maka rakiya."

Yayi saurin girgiza kai yace "nasan wurin ranka ya dad'e."

Alhaji Atiku yasaki dariya yace yau kuma fannin aiki KA mayar dani, KA ajiye daddyn a gefe kenan."

Bai tanka mashiba illah ya mik'e tsaye ya fito, had'ida ce masa daga can zan wuce."

Bai jira amsar Alhaji Atiku ba ya Juya ya fita a fusace, yana jinjina son zuciya irin ta wnn mutumin."

Alhaji Atiku yana ganin fitar mahmud cike da b'acin rai
ya mere baki yace "indai shalele tasamu abunda takeso duk wnda ranshi zai b'aci matsalarshi."

****************

A guje yaja motar yanufi hotel d'in, ynda yashiga wurin a guje mutane sai k'ok'arin kauce masa sukeyi."

" *YUSRA*."!!!
Yashiga filin da ake tsakiyar taron,
Ransa a b'ace daga jin yadda amon muryar sa take fita zaka San yana cikin mummunan b'acin rai."

Yusra yaci gaba da kiranta har sai da ya isa inda take yayin da kowa hankalinsa ya koma kansa ana kallonshi, wurin yayi tsit."

Sai mmki akeyi wnn ai shine mijin da tace zata aure wanda aka manna photunansu."

Kallonshi takeyi cikin wata siga ta so da k'auna, ganinshi da tayi taji sanyi a ranta, dama tasan za'ayi hakan saboda ta fahimci mahmud yanada zafi idan ranshi ya b'aci."

Murmushi takeyi tana shan ( _Juice_) d'inta tana kallonshi dama ta zaci hakan daga gareshi Dan hka bata damuba, bare ta amsa kiran da yake Mata."

Wnn ya k'ara k'ular dashi yaje har gabanta suna kallon juna, abinda takeso kenan ta kashe masa ido d'aya tana masa murmushi, tana shan juice d'inta."

Tuni zuciya ta kuma k'uleshi tsakanin tsanarta da haushinta da kuma k'inta suka k'ara d'arsuwa a zuciyarsa bai San lokacin da ya d'aga hannu ya kwad'a mata mariba, y kuma d'auki wani cup a wurin dake cike da juice ya watsa mata a fuska da k'arfi."

Saida ta razana tayi saurin mik'ewa tsaye a firgice, duk kunya ta isheta gashi jama'a kewaye dasu,

Ranta ya b'aci ta harareshi,
Meye haka mahmud?" Wnn wani irin wulak'ancine hakan a gaban bainar jama'a."

Nafad'a maki har abada bazaki tab'a samunaba,
Saboda bana sonki bana k'aunarki, bakya cikin tsarin Matan da nkeso na aura, dakeda banzar rayuwarki Baku tab'a ban sha'awaba, karki sake yin kuskure da gaggaci a kuma kirana, domin zanyi mki abunda yafi wnn."

Ya d'aga kai ya kalli kalandar pix d'insu da aka zagaye wurin dasu,
ya nufi wurin ya shuga yagawa yana zubarwa k'asa."

Ya kuma yimata kallon bnxa ya watsar,
Gaba d'aya jikinta a waje yake tamkar tsirara take,

yace "banida abinda zanyi da macce irinki bakya cikin irin matan da zan zab'awa 'ya'yana a matsayin uwa,
Na tsaneki yusra na tsaneki,
Yana gama fad'in hakan ya juya yatafi had'ida yin wurgi da table d'in dake gabanta wanda aka jera mata kek da lemunmuka,

Tana ganin yayi tafiyarshi tabishi cike da bacin rai idonta yana zubar da hawaye, tana fad'in "kayi kad'an Mahmud aurena ya zame maka dole idan kaga ka auri wata a duniya to nice,

'Ya'ya kuwa in har zaka haifi su to ka tabbatar da nice uwarsu,
Idan bana cikin matan da kakeso, ni Kai kana cikin tsarin irin mazan da nkeso."

Kuma ni yusra ina samun abunda nkeso kota halin k'ak'a don Haka ka sanyawa rywrka nice matarka."

Snn wnn cin mutumcin da kayimun a bainar jama'a a ranar da nake liyafar murnar zagayowar haihuta bazan mnta dashi ka d'au bashi."

Wnn shi zaisa na nanuna maka isata, in kuma maka dole ka shirya rywar aure dani kota girma kota arziki."

Bai sauratetaba ya shiga motar sa ya bule ta da hayak'i da k'ura yayi tafiyarsa yabarta cikin bak'in ciki da b'acin rai ga Wani rad'ad'in sonshi da ke mata zafi a zuciyarta idonta ya kad'a yayi jawur,

Ta kasa kukanma kunya kamar zata kasheta tayi da nasanin Zuwan da yayi,
Dakyar ta iya tanufi motar ta, tashiga sauran k'awayenta da jama'a da ke gurin suka taru suna bata hak'uri,
Amma bata saurare suba da k'arfi ta taja motarta tanufi gida Allah dai ya kiyaye ta isa gida lfya🤔
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅





Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)





*25*






A wann ranar ta d'agawa kowa hankali, mu samman mahaifinta da hankalinshi yyi mummunan tashi. Sai lallashinta yakeyi da ban hak'uri."

Sai da tasamu natsuwa ta tsagaita kukanta snn yashiga tambayarta, "shalele meya faru?" Waya tab'aki?" Meke maki ciwo?" Me kikeso?"

Rinannun idanuwanta ta d'aga sukayi ido biyu da mahaifin nata wnda take kwance a kan jikinsa,
"Daddy zaka bani abunda nakeso kamar yanda ka d'aukar mun Alk'awari?"

"Zan bki shalele duk abunda kike buk'ata."

Hawaye ya kuma ciko idanunta tace.

"Daddy Mahmud nakeso,
Daddy inaso ka aura mun mahmud nan bada jimawaba, daddy Mahmud yaci mutum cina ya wulak'antani cikin bainar jama'a sai dai duk da hakan bnji soyayyar sa ta ragu a zuciyata ba sai ma buri da shauk'in na mallaki namiji irin sa."

Yyi murmushi "haba shalele Dama akan wnn kike b'ata ranki?
Mahmud kinzama matarshi bazan gaji da fad'a maki hakan ba
Ki sa aranki kece matar mahmud,
Mahmud bashida wata mata bayanke ko yanaso ko baya so."

Abunda nakeso dake karki kuma kiran wayarshi, duk ynda kikeji a kan sonshi a ranki ki danne ki sanyawa zuciyarki dangana kibani nan da wata uku kigani a lokacin Mahmud, zai zama mijinki zaki mallakeshi cikin kwanciyar hankali da lumana."

Mik'ewa tayi tana tsalle tare da tsananin murna ganin tasamu abunda takeso, domin da zarar daddy yayi mata Alk'awarin zaiyi mata Abu tabbas ba makawa saiya matashi koda rayuwar wani zata salwanta."

Mahmud zan nuna maka iya karka, ta fad'a tana murmurshi snn ta tashi ta tafad'a d'akinta."

*******************

Allah ka d'ai ya saukeshi garin ibadan lafiya irin yanda yake gudu a mota."

Misalin k'arfe 10pm ya sauka, kai tsaye d'akinsu ya nufa ya Tarar da sulaiman a kwance yana waya da matarsa uwar d'ansa, abin sonsa, sai dariya yakeyi cike da jin dad'i."

Bai lura da Mahmud ba sai ganinshi yayi ya shigo ya fad'a toile."

Da sauri yayi mata sallama ya kashe wayar yashiga zuba ido yana jiran fitowar Mahmud."

Mahmud dake cikin toilet ya sakarwa kanshi ruwan sanyi sai sauke ajiyar zuciya yakeyi tare da lumshe idanuwanshi."

Sulaiman yaji shurun yayi yawa ya kwankwasa masa k'ofa,
Sai a lokacin mahmud ya sauke ajiyar zuciya yayi arwala ya fito da jallabiya sanye a jikinsa sai da ya fara gabatar da sallolin da ake binsa snn ya mik'e ya je kusa da sulaiman da ya k'ura mashi ido yana kollonshi ya zauna "

Sulaiman ya kasa hak'ura ya kalleshi cike da kulawa yace "abokina wai meyake faruwa ne?"

Mahmud ya juya ya kalleshi yayi murmushi, anan yashiga fad'a mashi duk abunda ke faruwa."

Sulaiman yace "babu abunda ya kamata muyi shine Addu'a domin bayan tafiyarka oga ya dawo yake tambayata katafi?"

Nafad'a mashi "eh katafi amma ranka baiso tafiyarba. Oga yayi murmushi yace "Allah ya tsareka, Allah yasa baka fad'a tarkon commondent ba, domin ya fiya Son kanshi."

Mahmud yace "komai son Kansa da yakeyi bazai tursasani akan nayi abunda bana so bana k'auna ba
Wlh in har saina aure "yarshi nafison na ajiye aikin sojan da nkeyi,
Dama ni bana ra'ayin aikin soja Abba ne da momy sukeson hakan, kuma na d'auki Alk'awarin duk abunda su keso znyi masu,
zanyi biyyah garesu koda kuwa ni banaso, kai koda daga aikatashi shine silar rasa rayuwata indai akan mahaifana ne naji na gani."

Yana cikin maganar ne wayar hannunshi ta d'auki k'ara yana dibawa yaga shugaban makaranta ne."

Sai da yaja dogon nishi ya kalli sulaiman yace "dijama ta janyo mana wata fitina wata k'ilama ya koreta daga makarantar."

Sulaiman ya saki dariya domin shi har ga Allah labarin dijama dariya yake bashi,
Yace ka d'auki wayar mana meyasa zaka yanke hukunci a kan abunda baka sani ba."

Jiki a sab'ule ya d'aga wayar had'ida yimashi sallama."

Tunkafin shugaban makaranta ya fara magana mahmud yafara da cewa "dan Allah shugaba kayi hak'uri karka koreta na fad'a maka duk lokacin da tayi wani abun abata kashi Wanda zai sanya dole ta shiga hankalinta, idan akwai ma abunda yafi duka ayi mata shi."

Shugaba yyi dariya yace "kwantar da hankalinka Mahmud ai yanda kasan Nana khadija a da yanxun ta wuce nan bbu wani Abu da takeyi a yanzun bayan karatu domin kuwa idan kaji yanda bakinta yake fitarda turanci sai ka rantse da Allah kace ba ita bace."

Abunda yasa nakiraka a dai dai wnn lokacin, kiranka nayi domin na fad'a maka gobe ne akeyi masu hutu Wanda nasan bakusaniba sai kuzo Ku d'auketa da misalin k'arfe 10am

Murmushi mahmud kawai yakeyi a fuskarshi godiya yashiga yiwa shugaba har lokacin ya kashe wayar,
Duk abunda ake fad'a sulaiman ya naji a waya, shima dariya yakeyiwa mahmud jin tunkafin shugaba yafara yin magana mahmud ya rigashi yana bashi hak'uri.'
Saboda anriga da ansan dijama matsalace,

Mahmud yace dijama anyi hankali?
Tab da sake wata k'ila dai kwanto ne tayi masu saboda dijama fitina ce."

Sulaiman yace nidai ina rok'on Alfarma da abani dijama na aureta nayi ta biyu da ita,
Koda dai nayiwa wife d'ina Alk'awarin baxan mata kishiyaba."

Mahmud yace "ai kuwa idan kanasonta na baka amma ka shirya rabuwa da matarka ta girma da arxiki idan ba hakan ba to zakuyi rabuwar rashin arziki,

Dan na rantse maka dijama saita cinnawa gidanka wuta dakai da mtarka da d'anka duk sai kun k'une tana gefe tana kallonku saboda fitina."

Sulaiman ya kuma sakin dariya yace " wnn

Please Login or Register in order to submit comment