Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

28/03/2020, 21:32 - Messages to this group are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info.
03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: *Asslamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa BARAKATUHU.*


💕
*A dalilin yawan kira da neman tsoffin Littafaina da Masoyana keyi yasa na yanke shawarar kokartawa in rubuto muku su online don farin cikinku saboda dominku ake rubutun*💞

*Zamu fara da littafina mai suna RAHIMA saboda yawan tambayarsa da ake in Sha Allah.

Littafin *RAHIMA* na *sayarwa ne*, don haka ga masu son karantawa za'ayi adding dinsu a group ne bayan sun biya *300* kacal ta daya daga cikin wadannan bankuna.

A- *0598537268*
GT Bank
B- *6016142358*
Keystone.

Nagode.




....*RAHIMA*doc by Jami

*ONE*

Na
*Saliha Abubakar Abdullahi Zaria*

1

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Gaba daya yau cikin garin Kano an tashi cikin fatsakin rana ne duk da cewan an shiga watannin da ya kamata a rinka samun ruwan sama ko da yaushe. Al'amarin sai addu'a kenan domin wasu jihohin da kauyaku tuni sun sami ruwan sama, banda wannan ma sau da yawa hadari zai hadu a sararin samaniya tamkar ruwa zai sauko kafin kiftawar ido amma cikin hukuncin Allah sannu a hankali hadarin sai ya washe garin yayi haske , abu gwanin ban tsoro.

A kalla a kan jera kwanaki ana hakan kafin Jalla sarkin sarauta Yai nasa hikimar a saukar da ruwan kamar da bakin kwarya, wani lokacin har a yini a kwana ana shekawa. Idan anyi dace da wannan baiwa, garin ya kanyi sanyi, duk inda mutum ya taka zai ji taushi da kamshin kasa wanda sansanyar iska ke yadawa ko'ina, alamun an samu ni'imar Allah kenan don zafi zai ragu matuka, daga nan kuma sai manoma su dukufa su koma gona, malamai da sauran jama'a kuwa mu ci gaba da adduar samun damina mai albarka don kasarmu ta Kara samun yalwar abinci da kyakkyawar ci gaba, Allah yasa mu dace, ameen.

Duk da cewan ranar tayi yawa wacce ta haddasa zafin dake bugawa ta ko'ina bai hana jama'a bayin Allah zirga-zirga da kaiwa da komowar su wajen sana'oinsu ba, matan aure a gidajensu sun dukufa neman na kansu, halayen Kanawan Dabo dake burgeni kenan. Ba dai kaga suna zaman kashe wando ba mazansu da matansu, babba da yaro sun san hanyar da zasu maida taro sisi, sisi ya zama sule, sulen nan ya koma naira ba tareda girman Kai ko kyashin juna ba.

A daya daga cikin wadannan gidajen dake unguwar Yakasai ne Hajiya Kaltume, dattijiya 'yar kimanin shekaru hamsin da biyar ke zaune cikin dakinta tana 'yan kulle-kullen kayan sana'arta, kamarsu kuka, kubewa busashahiya, maggi vedan da mai tauraro, tana sayarda omo, gishiri da suga, ga dakakken yaji da take masa hada-haden kayan kamshi, tafarnuwa dasu magi harda soyayyar gyada,kana ta durasu cikin robobi ko kwalabe tana saidawa.

Sha biyu da rabi dai-dai babban danta Dr Haseeb yai sallama ya shigo gidan ya tarad da ita ta baje kayan a gabanta tana ta faman kulli, ganin haka ya kara tamke fuska ya murtuke babu alamun walwala ko kadan. Itama sanin halin likitan yasa ta daure nata fuskar, ko banza Dan fari ne,daman can ba sakin fuskar yake samu ba. Ya gaisheta ta amsa a ciki. Ya gyara zamansa tare da kurawa tafukan hannunsa idanu na 'yan dakikoki ya saki ajiyar zuciya. An ce tsakanin da da mahaifi sai Allah, ajiyar zuciyar da yayi yasa uwar ta dago Kai ta kallesa tace "Kai lafiya, wani abu na damunka ne?"
Ya kada kau "Komi lafiya ba abinda ke damuna, sakon da kika bari a gida ne yasa na garzayo inji ko lafiya kike son ganina da hanzari?"
Kafin ta bashi amsa Saida ta kulla kullin gishiru uku, hakan ya kara tunzura shi nan take ya kasa daurewa ya bara "Wai Hajiya don Allah me yasa kike son wahalar da kanki ne? Meye naki na zama kina wadannan kulle-kullen?"

Ta kallesa ta kau da kai kana ta amsa " Tun shigowarka na lura ranka a bace yake, amma so nawa zan fada maka cewan ni rayuwata ta duniya iyayena basu yi min tarbiyyar zaman banza ba tunda kuruciyata, nasan muhimmancin dogaro da Kai ta hanyar neman na kaina, naga Kuma amfanin sana'a tun duniya na kwance kudin nada daraja ba yanzun da muke muna sana'a ba, muna buga-buga."
03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: ....RAHIMA..doc by jami
3

Karfe biyar na wannan ranar yana kwance cikin dakin barcinsa, tunanin al'amarin 'yanuwansa kaf suka addabesa, ya juya can, ya juya nan....
Aka bude kofar dakin a hankali, ta shigo da dauke da cup data doro bisa faranti mai dauke da tatacciyar abarba ta tsaya gefensa ta mika masa, bai karba ba Saida ya tashi zaune, maimakon ya sha ya rinka karkada 'yan kololon kankarar da aka jefa cikin juice din don yai sanyi. Kafadarsa ta dafa tace "In tambayi Daktan wani abu?"
Ya dago ya kalleta yana shafar goshinsa da yatsunsa biyu wanda alama ce ta nuni da yana cikin damuwa, ita tasan haka don ba banza kawai take takamar ta fahimci halin wannan murdadden mijin nata da suka kwashe shekaru shidda suna tare ba.
Kafin ta bata amsa Saida ya kurbi juice din ya hadiye sannan Y
Ya dago ya kalleta yace "Meye?"
Ta amsa "Lafiya na ganka cikin wani yanayi tunda ka dawo?"
"Ba wani abu ya bata amsa a taikaice kafin ya ci gaba batun auren Rabi'u ne ya taso, Ina ganin karshen watan nan za a daura auren ayi bukin kowa ya huta."

Zuwaira ta bugi kirji "Wane Rabi'un, ba dai autan Hjy ba, karatunsa fa?"

"Saurara! Ya fadi ba tareda kallonta ba, Hjy na ganin danta ya girma don haka gara ayi auren, idan da halin ci gaba da school to, but for now ayi auren dai...
Ta so taji karin bayani daga bakin maigidan nata amma tsawon minti goma sha biyar ta fahimci iyakar abinda zata ji kenan daga bakinsa, taja jiki ta fita ta koma kicin.

Karfe shidda kanninsa suka yi sallama gidan babban Yaya, ya fito falonsa suka zauna, Hayatu da Rabi'u suka zamo daga Kan kujeru domin su gaishe shi, ya amsa musu cikin fara'a har suka ji mamaki dalili da a zatonsu bom zai tashi!
Ba bata lokaci ya fara magana "Ba wani abu yasa na nemeku ba sai don inji daga bakinka bayan na Hajiya dangane da batun aurenka."
Rabi'u ya gyara zama ya fara kare kansa "Wallahi Yaya ban taba tsammanin abu ya zama haka ba, yes nasan mun fara sa mutunta juna tun shigowarta makarantarmu don shekara daya kacal na wuce ta, duk da ba course dinmu guda ba muna fahimtar fannin karatun junanmu da inda muka dosa. Da farko relationship dinmu tamkar yan uwa har a kan kiramu wa da kanwa, cikin ikon Allah myka shaku da juna fuye da zatonku, Kuma wallahi bamu taba furtawa juna batun soyayya ba sai watanni biyu da suka wuce har muke ganin zamu iya zama abokan rayuwa, sai dai ko da muka gasgata muka yanke shawarar bamu kawo batun aure kusa ba don gaskiya na fada mata sai na kare karatu ta amince saboda itama tana shaawar karatun sosai. Ashe muna namu ne Allah na nasa, kwatsam kakanta na wajen uba ya tada kayar baya cewa shi sam bai San da batun wani karatu ba aure ya sani, Kuma dole Rahima ta fidda miji ko yayi mata na dole. Ta taho ta zayyane min batun cikin tashin hankali da rashin sanin madafa, na tausaya mata kwarai, sannan naga ga alkawarin auren juna da muka shine naga ya dace dole inyi wanu abu a kai in taimaka ayi aurenmu in yaso ma ci gaba da karatun later."
Hayatu ya daka masa harara "Kaji dan ka iya, watau ma har ka riga ka tsara yadda za'ayi, in hakane meye na neman shawarar ko yardarmu, ba ka shirya ba? Yaro da shegen rigiman tsiya, muna zamanmu lafiya ka tayar Mana zaune tsaye."

Rabi'u ya gyada Kai "Kunji Yaya Hayatu da kayi naka wa ya hanaka ko shawara wa ka dauka, gashi nan saboda zara ka kasa zama da mace guda sai biyu duk sun hana maka sakat "

Haseeb yai gyaran murya "Ni ban kiraku gardama ba, shawara na taraku muyi, Kai Hayatu hakuri za muyi ayi abinda ya dace, Hjy ma na goyin bayansa. Amma Kai Rabi'u Ina son kasan cewan wallahi ba da son raina za ayi auren nan ba, na amince ne gudun bacin ran mahaifiyarmu Kuma bamu san alkhairin dake ciki ba so karka damu ba zaka ji kunya ba in Allah yaso. Yanzun su waye ne iyayenta, wace unguwa take?"
Baki yaki rufuwa saboda murna, Hayatu ya kallesa ya bushe da dariya yace "Ka daina wani murna in har munji bata da usuli batun aure ya tashi ehe, uhhmmm Kai muke saurare:
03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by Jami
2
Dr Haseeb yai murmushi bayan jin kalaman tsohuwarsa yace "Tuni na amince da batunki Hajiya shiyasa na sayo miki wadannan kayan masarufin yadda kika bukata bisa yarjejeniyar aunarwa za ki rinka yi ba ki zauna kina irin wahalar nan ba."
Itama tayi 'yar dariya " Ina wahala a nan? Ku fa likitoci kuka ce mutum ya rinka motsa jininsa, Kuma idan kace sai tiya ko mudu zan rinka sayarwa kenan sana'ar tawa bata talaka ba ce, in kuwa hakane to ci gabanmu ragagge ne domin talaka shine jigon kowacce irin sana'a, ni don Allah ka bar wannan zancen, Kai kenan kullum kazo gidannan da sabon tsirkun da zaka kirkiro alhali ni din nan ban gaza ba da sauran karfina, to Wai ma Ina wahalar take? Mai aiki fa ka ajiye min musamman babu abinda ni keyi kullum sai dai in wanke goma in tsoma biyar, inci mai kyau, insha mai kyau, in daura zanin da wata yarinyar macen bata daura na, inyi barci na ya isheni, in bautawa Ubangijina gwargwadon karfina, bani da sauran buri a duniya da ya wuce illa inga auren Dan autana, baya ga shi sai rokon cikawa da imani. Haba wace wahala, lokacin da akayi ta can da anyi yanzun kuwa albrkacinku sai godiyar Allah da fatar Allah ya baku masu yi muku fiye da yadda kuke yi mana."
Ya amsa "Ameen Hajiya, shikenan ba zan kara magana kan hidimar sana'arki ba Allah ya bada sa'a, amma don Allah ki rinka samun isashshen hutu, bayan haka nace ki tambayeni duk abinda kike so cikin ikon Allah ba zai gagara ba."

Hjy. Kaltume ta tattara kayan gabanta ta ture gefe tace "Bari dai in tsaya muyi maganar nan sosai don na fahimci hira kake ji yau, shin me yasa kake son maida hannun agogo baya ne? Na fada maka Kai kadai, na gaya maka tare da 'yanuwanka, yau ma zan Kara fada maka ni ban raina hidimar da kake min ba, iyaka nafi amincewa da in nemi nawa na kaina, ba sai na jiraka ba balle 'yanuwanka da basu da hali. Ranar da Allah ya hore maka kayi inyi murna da farin ciki, ranar da baka dashi sai inyi amfani da nawan da kuke rainawa, kaga na rufawa kaina asiri na rufa muku, banda wannan yau da gobe bata bar komi ba, koda nike mahaifiyarku ba lale Allah ya tara min duk masu jin kaina ba, idan Kuma har na samu hakan nasan irin matan da zaku auro? Wata matar ita ke hana da ya kula da iyayensa yadda ya kamata duk da ni alhamdulillah matanku na kwatanta min da'a. To idan duk muka ture wannan batun, ka duba kaga kaine babba, Allah bai ba 'yanuwanka rufin asiri irin naka ba, kai kake dawainiya dani, kayi dasu da dangina, ka taimaki dangin mahaifinka, Ina tausaya maka kwarai da gaske don ka zama hannu guda ba wani mai tallafa maka, ga iyali ka fara tarawa dole in rinka taimakonka, misali ko haihuwa matarka tayi na baka gudumuwar zanin goyo ban taimaka maka ba?"
Dole yayi murmushin da har kyawawan hakoransa suka bayyana yace "Wallahi Hjy kin ban dariya, amma insha Allah ba zan sake shishishigi cikin hidimominki ba, Allah Kuma ya kara taimakawa."

"Yauwa yanzun naji batu, to tunda naga ka saki ranka yanzun sai muyi maganar dalilin nemanka."
Ya amsa "Ina saurarenki, Allah yasa lafiya."
" Lafiya kalau, batun kaninka Rabi'u ne, kasan na fara yi maka bayanin neman auren da ta fara kwanaki ko? To shine jiya ya taho min da maganar cewan wai iyayen yarinyar sunce inda gaske yake ya fito."

Haseeb yai kasake na wani lokaci kafin ya furta "Har yanzun yana nan yana shirmen nasa kenan?"
Tace "Wane irin shirme Kuma, yaro na neman raya sunnar manzo?"
"Hmmmm hjy Rabi'un guda nawa yake ne? Ni fa karatu na turasa makaranta yayi ba soyayya ba, don Allah Ina zai kai mata yanzun?"

"Ban gane ina zai kai mata ba, bai isa auren bane ko yaya?" Ko kuwa don ka turashi karatu sai yaki aure, maza da mata nawa ke yin auren su ci gaba da karatun nasu?"
Ya kada Kai "Kwarai ana yi amma ga Wanda ya shirya, yana da muhallin da zai aje matar yanada kamu sayar domin ciyar da ita da daukar sauran lalurorin yau da kullum na shi kansa da ita matar da ya aje. Rabi'u karatu yake Hajiya, duka -duka 200 level yake a jami'a, me zai hana ya hakura ya kare sauran shekara dayan, ya samu abinyi kafin muyi wani batun aure?"

Ta fara harzuka "Da yawan yajin aikin da ake yi a jami'oi ne zai gama karatun nan da shekara gudan? To naji, yanzun ya kake son ayi da iyayen yarinyar, me zamu ce dasu?"

Ya amsa "Ace musu bai shirya ba sai ya gama karatunsa tukunna."
Tace "To ita Kuma yarinyar da aka ce za a aurar da ita yanzun ne fa?"
Ya bata amsa da "Ta nemi wani ta aura tunda iyayenta sun matsu su aurar da ita, shi Kuma Allah ya bashi wata nan gaba idan lokacin auren nasa yayi."

Ta fusata "Na fahimci ka shiryawa kowacce tambaya zanyi maka, kawai ka fito fili kace ba zaka taimakawa danuwanka hidimar aurensa ba fakat."

Ya Kara ladabtar da kansa "Ko kusa ba haka bane Ni a ko yaushe shirye nike in yiwa 'yanuwana kowanne irin taimako suka bukata daga gareni. Ba wai baba son Rabi'u yai aure bane, tunanina mene na gaugawa,hanzari ba nasa bane, ya bi a hankali mana har Allah ya bashi daidai shi."

Hjy Kaltu ta juya masa baya "Kai kake da lokacin surutu, da kake gaya min wannan zancen wofin kaninka da kuke uba daya nawa suka yi aure? Gaba dayansu babu Wanda ya haura shekaru ashirin a cikinsu, me yasa baka hanasu ba, wane irin gudumuwa ce baka basu ba, sai yanzun yaro ya Kai shekaru da biyar a duniya ya isa aure kace zaka tauye masa hakkinsa?"

Yace Yi hakuri ban tari numfashinki ba, wadanda kike magana na amince musu ne saboda kowannansu nada shago a kasuwa, sunada abinyi,tunda sun nuna su kasuwancin suke so fiye da karatun, na tabbatar Kuma zasu iya daukar takalihun matansu, amma Kya hada da wannan ahi ba karatun ba, shi ba aiki ko wata katamammiyar sana'a ba? Idan Kuma kina ganin banyi magana Kan auren su Hamisu ba na Hayatu shima na hana shi ai amma shima don rashin sanin ciwon Kai matar shekararta biyu ya sake auro wata, gasu nan banda tashin hankali me suke yi?"

Ta juyo a fusace "Ka rufa min bakinka kaji, ai fa tunda ba Kai ya shafa ba yanzun zaka rinka kawo min kabli da ba'di, to shima da ya auri mata biyun ai ance matar mutum kabarinsa da yaje yana neman na banza a waje ai gara ya tara cikin gidansa. Kai wai ya za ayi daman ra'ayin rikau dinka ya zama irin na kowa? Naji ta bakinka, tashi jeka, kaga kyaun sana'ar da kake mita, ni zan tsaya, Allah kuma zai taimakemu ayi wannan auren da yardar Allah autana ba zai kunyata ba, idan ba zaka jagoranci harkar auren ba ai ba Kai kadai bane, kaninka na Nan, Allah dai na gani na baka hakkinka na kasancewa babba."

Da ya tabbatar da al'amarin yai nisa gashi bai son bacin ranta ko kadan har dai in ya tuna can inda aka fito da can dole ya fara lallashi yana bata hakuri yace "Tunda abin ya zama haka ba komi Hajiya, daman ni naso ace ya kara sanin ciwon kansa ne yasan wahalar ya nemi na sa yadda idan yai auren zai fi rike matar da daraja da mutunci amma tunda an matsa insha Allahu ba damuwa za ayi yadda kika ce cikin yardar Allah. Zan nemi Hayatu mu tafi gidan iyayen yarinyar cikin satin nan in yaso duk yadda muka yi dasu Kya ji, anjima ki turo min Rabi'un yai min bayanin unguwar, Allah yasa mana hannu."

Dadi ya rufeta cikin murna tace "Insha Allah yau dinnan zaka ganshi yana dawowa gida zan turo maka shi, Allah yai maka albarka."

"Ameen nagode, idan babu wani abu Ina son komawa asibiti amma shi Rabi'un ya sameni a gida."
Ya ciro kudi cikin aljihunsa ya ajiye a gabanta bisa tabarma, ya mike kana yai mata sallama ya fita tana sanya masa albarka.
03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami
4
Rabi'u yace "Yaya Haseeb, Rahima da iyayenta 'yan usulin jihar nan ne, gidansu na unguwar rijiyar lemu, muna iya kiranta marainiya don ta rasa mahaifiyata tun lokacin haihuwarta.
Bayan Allah ya amshi ran mahaifiyarta ne kanwar uwar dake shayar da nata jaririyar 'yar kimanin watanni uku ta dauketa taci gaba da shayar dasu gaba daya.
Kasancewa mahaifinta daman matansa biyu sai abin yazo masa da sauki domin ta samu saukin maraicin diyarsa da aka mutu aka barin masa, ko sa yake ita ce diya kwara daya tilo da mahaifiyarta ta bari su bakwai ne cif wajen mahaifinsu, sunan mahaifiyar nata aka mayar mata don tunawa da marigayiyar.
Sunan mahaifinta Aliyu ana kiransa Ali mai goro, data girma ta isa shiga makaranta saita shiga da suna Rahima Mamman Mai yadi, sunanta marikinta kenan, kowa dai ya san Mamman Mai yadi na Yakasai, tsakanin gidansa dana Hajiya bai wuce loko biyar zuwa shidda ba, bayan wannan Rahima yarinya ce mai hankali da zurfin tunani Ya Haseeb.
Hayatu ya kallesa "To ai ka bari har mu bincika muji wa kunuwanmu tukunna kana mu zartas da hukunci, Kai daman ya za ayi ka Fadi wasu aibunta tunda kana sonta."
Rabi'u yace "Balle ma bata dasu, yarinya ce mai da'a wace ta samu dimbin kyawawan tarbiyya nagari Kuma nagartacce."
A nan dole Haseeb yai murmushin da bai shirya ba yace "A nan kan Ina bayan Hayatu Rabi'u, idan har mun bincika mun tabbatar da yarinyar da halayen daka fadi babu shakka kayi sa'ar Mata, idan kuma munji sabanin haka sai dai kayi hakuri. Yanzun sai ku koma gida, idan Allah ya kaimu gobe zanyi abinda ya dace sai kaje kaci gaba da adduar Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Duk yadda muka yi goben za kuji insha Allah."
Sunyi sallama cikin farin cika da murna.
Kamar yadda ya dauki alkawari, ya binciko dukkan abubuwan da suka dace ya sani ya Kuma ji ta gamsu saboda aure tsakanin Rabi'u da Rahima tabbas ba makawa.

Baiyi sanya a gwiwa ba nan da Nan ya nemi Baffansu Rabi'u da kanin Hajiyarsul watau kawunsu yai musu bayanin halinda ake ciki. Suma basu bata lokaci ba suka amince, suka hadu su hudu suka nufi gidan Mamman Mai yadi a matsayin mabidan auren wa dansu diyarsa.

Ba wai ta fannin saye da sayar da yadiddika kadau yasa sunan Alh. Mamman yayi fice ba, ah ah duk wani Mai hulda dashi ta cinikayya ko harkokin yau da kullum ya shaidi mutym ne Mai son jama'a da mutunta su, ya iya hulda da mutane kwarai da gaske.

Ta fannin iyalinsa kuwa matarsa uwar 'ya'yansa Habiba ita kadai ya mallaka, tunda ya aureta suke zaune lafiya, zaman so da kauna da mutunta juna sai bai taba sha'awa ko tunanin karo wata matar ba, gashu sun hayayyafa, Allah ya azurtasu da diya takwas, biyar maza uku mata. A zahiri diyanta bakwai ne amma tunda matarsa ta amshi marainiya Rahima ta shayar da ita yarinyar ta shiga zuciyarsa, yaji yana tsananin sonta, irin son da da mahaifi har bai son yaji wasu su furta bashi ya haifeta ba, itama kanta Rahimar Saida tayi wayo ta fara sanin ciwon kanta ne ta fahimci cewan ba sune mahaifanta ba, ta Kara tabbatar da hakan yanzun da aka ce mahaifinta na wajen Uba ne yai ruwa sa tsaki wajen hanata ci gaba da karatunta.

Hausawa kance wani ma yai rawa ballantana dan makadi, su

Please Login or Register in order to submit comment