Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yareema ya yi ajiyar zuciya, ya ce, In ki ka ce haka ba ki yi min adalci ba Saadatu, dukkanmu mun dade muna son juna, ba mu gane hakan ba ne har sai da Maimartaba ya ankarar da mu. In kuma da gaske ba ki sona din ne Saadatu, to gata ki gaya mata da bakinki.
Ta girgiza kai da sauri kamar yana gabanta, ta ce, Yaya Yareema!!! (In exclamation).
Ya ce, Yes, ki gaya mata da bakinki, sannan ne zan yarda cewa ba kya son nawa.
Murmushi ya subuce mata, ta kawar da zancen da cewa.
Karatu ya wuce ni da yawa, an yi min fintinkau, in ka dawo za ka koya min?
Ya ce, Karatun namu ai kala-kala ne, wanne daga ciki?
Ba ta gane hausarsa ba don haka ta ce, Courses din Applied Chemistry, inorganic, organic and petrochemistry. Tunda kai ka jawo aka wuce ni. Ta fada cikin shagwabar da ba ta san ta yi ba. Dr. Sageer ya yi ajiyar zuciya.
Anya Saadatu za ki bar ni in yi kwanaki biyun nan? Gabadaya kin rikita min lissafi, na kasa zama lafiya cikin nutsuwa tun barowata makarantarku. Ke kawai nake son gani, ke kawai nake son ji a jikina.
Ta kai tafin hannunta ta rufe ido kamar Yareema na ganinta, sannan ta ce, Kada in shiga lokacin Aunty Sultana. Prince sai ka dawo.
Ta yi maza ta kashe wayar ta koma ta jingina bayanta jikin allon gado, ta lumshe idanunta. Ba abin da ta ke son gani a daidai wannan lokacin sai Yareema Sageer.

Wayewar gari ke da wuya ta soma shirin shiga makaranta. Ba ta dade da zama a mazauninta ba, Said ma ya shigo suka hada ido, ta dauke kai. Yau fuskarsa a sake ba kamar jiya ba. Ya zo har gaban kujerarta ya ajiye mata tulin wasu takardu. Gabadaya notes din da ya shige ta ne ya je ya yo mata photocopying dinsu. Ba tare da ya ce komai ba ya koma mazauninsa.

A kwanakin biyu gaba daya ba sa magana da juna, ya kasa cire abin da idanunsa suka gane masa daga kwakwalwarsa, ita kuma ta kasa yi masa bayanin da ya kamata ta yi masa. Kunya ta ke ji a ce ita yanzu matar aure ce. Kwarai ta ji dadin photocopies din da ya yi mata, amma wata zuciyar na cewa ta dauka ta bishi har mazaunin sa ta watsa masa tsiyar sa, zuciya mafi adalci na cewa ta yafe masa muggan maganganun sa ya fada ne a bisa rashin sani.
A kwanaki biyun in ta koma gida ba ta komai cikin kwanaki biyun sai bitar karatun da ya wuce ta. Abin da ba ta gane ba ta kira Dr. Sageer ta gaya masa ta waya ya yi mata bayani yadda za ta gane. Yana yi yana kashe ta da kalaman soyayyarsa masu ratsa zuciya da ruhinta.
Yau kwanansa uku da tafiya kuma ya sauka a Abuja, amma bai kira ta ba. Ta wuce makaranta har yamma tana fama da assignments din da ta kasa solving gabadaya. Ta daga agogon hannunta ta ga karfe shidda, ko me ya hana direbanta zuwa har yanzu?
Ta dauki wayarta don ta kira shi sai ta samu cajin wayar ya mutu gabadaya, don jiya kusan kwana suka yi a kan waya ita da Yareema, kuma da asubah ta manta ba ta sanya cajin ba.
Gabadaya Dr. Sageer ya gama kwance kan Saade da soyayyah ba abin da ta ke jira sai dawowarsa a kashe wutar da ake rurawa a waya.
Da ta tuna yau zai dawo, sai ta ga ba za ta iya zaman jiran direbanta ba, sabida tana son yi masa girki na musamman, gara ta gangara da kafarta zuwa cikin quarters dai ba nisa, ban da Yarima da ba ya so tana tahowa ita kadai da yamma da da kanta za ta dinga komawa gida ko don ta motsa jikinta.
Ba ta jima tana tafiya a gefen hanya ba, motar Said ta yi parking a gabanta.
Shigo in karasa da ke.
Aah na gode, ka je kawai.
Ki yi hakuri ki shiga, ba zan barki ki bi jejin nan ke kadai ba daf da magriba.

Sai ta ji tausayinsa ya kamata, ya kasa cireta a ran sa, ta fi kowa sanin yadda yake sonta. Ko ya zai ji in ya ji ta yi aure? Sai ta ga gara ta shiga motar yau ta gaya masa gaskiya ko don ya daina kishi a kan abin da ba nasa ba, kuma ba zai taba zama nasan ba. Sannan babu yaudara a tsakaninsu har abada sai mutunta juna. Ba za ta taba mantawa da dimbin kirkinsa gare ta ba.
Don haka ta bude gaban motar ta shige, ya soma tafiya a hankali, Saade ta ce,
Da dai ka yi sauri maigidana yana hanyar dawowa. Ka yi hakuri ban samu damar gaya maka ba kana ta fushi, an yi min AURE!
Said ya taka wani wawan birki sai da suka jirkito dukkansu, Saade ta yi maza ta rike hannun kofar motar, ta ce,
Yaa Salam!
Said ya dube ta a sanyaye, ya rasa abun cewa. Sai ya ja motar suka karasa kofar gidanta. Har cikin get ya shiga da ita, tana kokarin fitowa motar su Yarima na shigowa shi da Dr. Ziyad ne da ya yi wa waya ya je ya dauko shi a filin jirgi.
Bakuwar motar samfurin henessyta dauki hankalinsa, kuma ba jimawa ya gane yaron, ya taba sauke Saade, kuma ya yi warning dinta tun a wancan lokacin amma shi ne shi ne bakin ciki, kishi da bacin rai sun hana Sageer tunanin abin da ya dace.
Dr. Ziyad bai gama tsayar da motar ba ya bude ya fito. Cikin takunsa na Yariman Askira ya taka ya isa gaban Said, sannan ya nuna shi da dan yatsa.
Wannan ya zama lokaci na karshe da za ka kara daukar min mata a mota, ko da da niyyar taimako ne. bana so, nagode. Ko kallonta ka sake yi ba taimako ba, kotu ce za ta raba ni da kai, na gaya maka, na kara gaya maka wannan.
Da sauri Dr. Ziyad ya karaso ya kama shi yana fadin, Haba Dr. he is your student, ba girmanka ba ne.
Saade tuni ta shige gida jikinta na rawa. Dr. Ziyad ya bi ta da kallo yana hadiyar miyau. Said tuni ya tsugunna yana bada hakuri, ya gaya musu direbanta ne bai zo ba, ya ganta tana dawowa da kafa, kuma sawu ya dauke shi ya sa ya ce ta shigo ya karaso da ita.
Dr. Ziyad ya ce, Is o.k, kana iya tafiya, mun gode.
Bayan wucewar Said ya kwace hannunsa daga na Ziyad ya ce, Da ka bar ni na dan sassaba masa kamanni, gobe ko da kudi aka hada shi bai kara daukar matar mutane a akwalar motarsa.
Cikin mamaki Dr. Ziyad ya ce,
Daga zuwa na Istanbul da dawowata kana nufin ka kara aure? Is she this girl da ta wuce ciki yanzun nan?
Dr. Sageer ya harare shi sosai da ya tuna waye Ziyad a kan mata, ya ce.
Babana ya aura min yarinyar da na ke riko ce tun da jimawa.
And now ina Sultana?
Mun rabu. Na mayar da ita kasarsu.
“This is serious, ashe za ka iya rabuwa da Rose? What a lucky girl, amma ta ciri tuta, ya ya sunanta?
Sageer ya zabga masa harara ya ce, Don Allah malam kama gabanka, ina ruwanka da sunan mata ta?
Dariya Ziyad ya yi, ya ce, Ina nan ina jiran ka, in ka gama kwasar amarci za ka zo neman new catch.
Da sauri Dr. Sageer ya ce, Waiyazu billah, sai dai wani Sageer din ba ni ba, kai ma ina maka fatan shiriya, kuma ina mai ba ka shawarar ka dauko iyalinka daga Istanbul ka dawo da su kusa da kai ya fiye maka wannan kazamtacciyar rayuwar.
Ziyad sai dariya yake yana mamaki, in wani ya ce masa Sageer zai bar mata saboda mace daya ba zai taba yarda ba, amma a sanin da ya yi masa shi kaifi daya ne, sannan ba ya taba fadin abin da ba haka yake a zuciyarsa ba.
Ko sallama Dr. Sageer bai bari sun yi ba ya shige falon gidansa ya kullo kofa ta ciki. Ya bar Dr. Ziyad a tsaye ya kasa tafiya. Ba abin da idanunsa ke hango masa sai kyakkyawar surar BAGGARA-SAADATU diyar Fulani Bilkisu, a lokacin data juya baya tana shigewa cikin gida.

******

A yadda ta hango bacin ran da ke kunshe fuskar Yareema ta san ba za su kwashe ta dadi ba. Tana shiga dakinta ta aje jakarta ta sunce ta daura tawul ta shiga wanka, tana tsakiyar wanka a shower sai ganin Yareema ta yi ya bude kofar toilet din ya shigo. Idanunsa sun kada, amma ganinta cikin wannan yanayin tuni ya birkita shi. Ko a Yankari bai taba samun damar ganinta yadda ya ganta a zahirin yau ba cikin hasken farin lantarki. Da kayan jikinsa da komai ya tafi zuwa gare ta.
Da sauri Saade ta ja da baya ta ce cikin karkarwar murya, na tuba Prince
Duka jikinsu rawa ya hau yi cikin wani yanayi, ita nata rawar jikin na tsoron abin da zai yi mata don huce bacin ransa ne akan Said, yayin da shi kuma nashi na tasowar wata irin soyayya ne da bai taba ji ba a rayuwar sa a kan kowacce diya mace.
Ka yi hakuri don Allah ba zan sake ba. Saade ta fadi cikin karkarwar murya, amma daga irin rikon da Yareema Sageer ya yi mata, ruwan yana sauka a kansu su biyu, tun daga sumar kansu har zuwa yatsun kafarsu, da yadda ya soma sumbatarta fiercely ya tabbatar mata ta hanyar da zai huce fushin nasa kenan.
All of a suddenga Saade,komai ya faru cikin shower.. gently, romantically yet abruptly(in an abrupt manner). Abin nufi, bata zaci abinda ya kawo shi shower din kenan ba, ta zaci ya zone don ya gaggaura mata mari a yadda ta gaidanun sa lokacin da ya gan ta a motar Saidu.
Sai ta ga alamarin ya juye zuwa zazzafar soyayya mara misaltuwa. Dukkansu sai da suka yiwani irin kuka(for emotion and satisfaction), wanda soyayyar juna, kewar juna da tsananin kauna suka kawo shi. Wata sabuwar rayuwa ce mai gardi da Saadatu da bata taba tsintar kanta a ciki ba.
Wani sabon yanayi ne a gangar jiki da ruhin Yareema Sageer, ya ji nan duniya bai iya kara sake hada jiki da kowacce diya mace bayan Saadatu diyar Mallam Hashimu da Fulani Bilkisu.
Kalaman mahaifinsa suka sake dawo masa a ranar da ya mallaka masa SAADE.

Za ta dauke dukkan kwadayinka daga kan sauran mata, in dai Bilkisu ce ta haife ta.
Allah ya saka da alkhairi Alanguburo. Allah ya kara yawan rai, Allah ya ba ni ikon rike amanar da ka damka min da gaskiya da amana, har zuwa ranar da muka daina numfashi.
Kalaman da Yareema ke yi a fili kenan, yana kankame da matar sa Saade, ruwa na sauka a jikkunansu daga saman shower. Ba ta san adduar me yake yi ba har da sunan ASKIRAMA a ciki, daga baya ta fahimci gode masa yake da ya mallaka masa ita ta zama cikon farin cikin sa.
Ko ita a yau tana gode masa da ya mallaka mata gwarzon dansa mafi soyuwa a gare shi, wato Dr. SAGEER YUSUF ASKIRA,Basaraken Askira daya cikin dubu, sadauki kuma jarumi a fanninnunawa matar sa kauna da soyayya.
A baya gani ta ke Mai Askira ya katse mata rayuwa, yayi mata aure ba a lokacin da ta shirya ba. Yanzu kuwa ta gane Askirama ya cika rayuwar ta ne, ya ingantata.Ya suturtata cikin alfarmar aure. Aure suttura ne, cikar mutunci ne, garkuwa ne kuma rufin asiri ga diya mace, sannan gata ne da ba kowacce mace Allah yake yi wa Rahmar sa ba. Don haka godiyar ta ga Allah madaukakin sarki da kuma godiyar ta ga Mai Askirainfinite ce.
Kaunar ta mijinta ta gama ratsa koina na sassan jiki da zuciyarta. Ta fara tantamar ya ya rayuwa za ta ci gaba da kasancewa ranar da babu wannanmuhimmiyar soyayyar ta Yareema Sageer a cikinta???

*****
DR. ZIYAD SAHEEB
Ya kasa zaune ya kasa tsaye a dakin barcinsa, ya rasa inda zai sa kansa. Shaidaniyar zuciyarsa na ci gaba da kawata masa surar sullubebiyar matar abokinsa, yarinya danya sharaf! Irin Africans din da kalar fatar jikin su ke da wuyar samu a cikin matan Nigeria. Ka kasa gane half-caste ne ko kuwa shuwa-arab ne?
Dr. Ziyad ya kudire a ransa, ko ta tsiya ko ta arziki sai ya samu rabonsa a tare da matar Dr. Sageer, da ma ai sun saba sharing yammata, ya san Sageer bai taba neman matar aure ba, amma shi kam zai gwada saarsa a kan tasa, zina ai duk sunanta zina, kuma su ma wadanda yake neman a baya ai wani za su aura watarana.
Don haka don an yi masa abin da shi ma yake yi ba laifi ba ne.Dole ya juyawa harkar su baya yana da wannan precious gem din a cikin dakin sa.
Ya san ba zai sha wahalar samun kan yarinyar ba, yadda yake farin balaraben Turkish. Ya fi Sageer kyau nesa ba kusa ba, ya kuma san yadda matan Nigeria ke son fararen fata.
Karfe takwas na dare ya kira Sageer a waya. Dr. Sageer na makale da Saade a lokacin suna karatun Organic Chemistry ana yi ana soyayya tamkar sun cinye juna wayar Dr. Ziyad ta shigo masa.
Kamar ba zai dauka ba, sai kuma ya dauka.
Akwai abinci ne a gidanka in shigo in ci? Cook dina ya yi tafiya.
Sageer ya ce, Za mu bai wa Uche ya kawo maka yanzu, ka daina zuwar min gida, ba gidan Sultana ba ne yanzu, gidan Saadatu ne.
Saadatu!
Dr. Ziyad ya fada a hankali, wane irin suna ne mai tafiyar da ruhi haka? Duk wayonka sai na dandana abin da ka ke dandanawa.
O.K no problem, a kawo.
Da haka suka ajiye wayar.
Yareema ya yi tsaki, sannan ya dubi Saade da ke kalmashe cikin jikinsa. Da ya sani bai daga wayar bama balle ya bata masa mood din sa.
Kin yi ragowar abinci ne?
Ta ce, Eh. Ba ta son abin da zai tada ita daga jikin Yarima sam a daidai wannan lokacin, tana cikin amarcinta, suna yi suna karatun su. Karatun ma ya fi shiga a haka (inji Saade). Ta ji wayarsu da abokinsa, kuma ta tabbatar dole sai ta tashin.
Daure ki hada masa abinci a basket ki ajiye a kitchen, zan kira Uche ya kai wa Dr. Ziyad.
Tana cuno baki ta mike tana fadin,
Ba shi da mata shi?
Ya yi dariya, ya ce, Yana da ita.
Me ya sa ba ta ba shi abincin ba?
Ba ta nan ne, tana Istanbul har yayan sa, ki taimaka.
Ta sake turo baki gaba, sannan ta mike zuwa kitchen din, wandon three quarter ne a jikin ta da yar farar shimi (armless) ta je ta yi yadda Yareema ya bata umarni ta dawo. Shi kuma ya kira Uche a waya ya gaya masa abin da zai yi.

Da safe Dr. Ziyad ya sake kiransa, Karfe nawa za ka shiga ofis yau kuma karfe nawa za ka dawo?
Wannan wata tambaya ce da Ziyad bai taba yi masa ba. Nan da nan ya sha jinin jikinsa.Hausawa suka ce wai Shege shi ya san makwantar shege.
“Why are you asking?
Zan zo mu yi lunch ne tare.
Yareema ya daure fuska sosai, ya ce, Look Dr. Ziyad, gidana gidan aure ne, ko da can ni nake zuwa gidanka ba kai ka ke zuwa gidana ba. Sabida ba matar aure a gidan ka. Ni ba zan hana a ba ka abincin gidana ba, amma na gaya maka gara ka dawo da Guneet Nigeria ya fiye maka wannan rayuwar.
Maganar gaskiya matar da nake so nake kishi nake aure yanzu, don haka ba zan kai abokai gidana ba. In waccan rayuwar ce ni na bari, na gaya maka na kara gaya maka na bari. Don haka muamalarmu yanzu za ta koma ne strictly official, (ta tsaya a ta ofis kadai).
Wani maketacin murmushi Dr. Ziyad ya yi, ko dama shi ya sake dulmiyar da Yareema a harkar neman mata bayan aurensa da Aisha-Sultana kuma ba karamin shaidani ba ne. Ya riga ya rantse sai ya kwanta da matar abokinsa ko da hakan zai kawo karshen abotarsu. Ya gani kuma ya yaba. Ko ana ha-maza-ha-mata kuma sai ya yagi rabon sa.

Tun daga ranar yake studying shige da ficen Dr. Sageer da Saadatu zuwa cikin makaranta da lokutan dawowarsu ta tagar dakin barcin sa. Tsayin sati biyu yana hankalce da duk wani motsinsu, ya fahimci duk ranar alhamis yana dawo da Saade da wuri wajen karfe biyu na rana, shi kuma ya koma ofis ba ya sake dawowa sai shidda na yamma.

Ranar wata alhamis wadda Saadatu ta kira fateful day, watanninsu ukku kenan da aure, a duka wadannan watannin ba su je Askira ba amma kusan kullum suna waya da kowa nasu.
Yareema ya dawo da ita gida, ya ci abinci sannan ya dau keys dinsa ya fice yana ce da ita zai rufe gidan ta waje, ko an buga kada ta bude, shi in ya dawo zai bude da kansa.
Uche zai kawo mata cefane ta kofar baya zai shigo, in ya gama shigar da su zai rufe ya koma baskwata.
Bayan fitarsa Saade ta shiga wanka, wankan ma a gurguje ta yi shi don hankalinta na kan karatun paper din da za ta zana gobe, wadda ta kasance last paper ta kammala aji biyu (level 2).

Ta fito wanka kenan daure da towel iya gwiwarta, ta shiga dakin barcinsu ta zauna a kan stool din mudubi ta janyo lotion dinta na Makari ta soma shafawa, kanta cikin shower cap. Tana yi tana bin wakar balarabiya Nancy Agram cikin wayarta da ke gefe, ta ji an murda kofar dakinta an shigo.
Tana juyawa da sauri don a zatonta Yarima ne ya yi mantuwa ya dawo, sai ta ga wani balaraben mutum. Ya ma fi larabawa kyau. Ba ta taba ganinsa ba, yana sanye da jallabiyya, kawai sai ta sa a ranta aljani ne.
Wata kara da Saade ta tsandara sai da Uche ya jiyo ta daga baskwata, ihu ta ke tana neman a kawo mata dauki da dukkan karfin muryarta. Dr. Ziyad ya karasa da sauri ya toshe mata baki, ya buga kanta da bango, sannan ya sa kafa ya tadiye ta ta fadi kasa.
Duk da ta ji azaba ba yar kadan ba har cikin kwakwalwarta hakan bai sa ta kasa hobbasar ceton kanta ba. Bedside lamp da ke kusa da hannunta ta dauka ta kantara masa a ka. Fitilar ta fashe a kan Dr. Ziyad jini ya wanke masa fuska, shi kuwa Uche tuni ya kira Ogansa a waya tun karar farko da ya ji Saade ta kwallara.

Rapist, at your home Oga!.
Abinda kawai ya gaya wa Sageer ke nan. Ya na so ya shiga ya taimaki Saade yana tsoron ko Ziyad na dauke da makami. Shi kam Uche matsoraci ne na karshe.
Duk da raunin da ta ji masa da fitila bai dame shi ba, ya dafe wajen da fitilar ta huda masa wanda tulin gashin kansa ya rufe shi. Sai jini da ke bulbulowa ta wajen, ya mike da mugun zafin nama ya dauke ta da mari haggu da dama. Saade ta nemi jinta da ganinta na wucin gadi ta rasa. Dr. Ziyad ya yi amfani da wannan damar ya fincike tawul din da ke jikinta
Saade ta sake yunkurawa tana ihu, ya sake sanya kafa ya tadiye ta, Uche yana daga bayan tagar dakin yana ta jera wa Yarima kira, ga shi ba shi da lambar police ko security din makarantar cikin wayar sa, wata zuciyar ta ce ya dauki dutse ya shiga ya kwada wa Dr. Ziyad, wata zuciyar ta hana shi, in ya zo da tsautsayi ya mutu shi ma kashe shi za a yi, a kan matar da ba tasa ba ai ya san shima maigidan nasa yana danawa a gidan Ziyad din, abinda suke yi ne tare yau aka yi masa har cikin dakin auren sa..
Yana wannan sake-saken jikin sa yana bari sai ganin hancin motar Yarima ferrariya yi ya shigo gidan da wani irin mugun gudu, kasa tsayar da motar ya yi sai da ta daki daya dalleliyar motar da ke fake a gefe, sannan ta tsaya cikin kudurar Ubangiji, bayan ya take birkin tsayar da mota.
Da gudu ya fito, jikinsa ba inda ba ya tsuma, hatta jijiyoyin kansa da makwallatonsa sun mimmike. Tsabar rudewa ya rasa ina ya jefa mukullin gidan, ga shi ya kulle ta ta waje. SaiUche yayi masa nuni da kofar kitchen ta baya. A lokacin Uche ya zargi ta kofar kitchen Dr. Ziyad ya shigo.
A guje Yareema Sageer ya danna kai gidansa, don tun daga Kitchen za ka fara jiyo ihun da Saade ke ta kurmawatana ambaton sunan Sageer da neman taimakon Allah.
A falo ya tsaya cikin gigita mara misaltuwa, yana son tantance daga inda ihun Saade ke fitowa. Daga karshe ya gane dakin barcin su ne. Tuni Ziyad ya kai ta kasa, yana ta kicin-kicin cire jallabiyyar jikinsa zai haike mata.. domin ya gama galabaitata da duka karfin kokawar ta ya kare, sai ambaton sunan Allah take hawaye masu zafi na kwaranya, ya yi nasarar cirewar kenan ya ji an ba shi (one blow one die) daga keyarsa.
Da ma ga shi jiki ba jiki ba, siriri ne sai tsayi kamar falwaya, sai da ya tuntsira daga kutufo dayada Dr. Sageer ya yi masa, Yareema ya bi shi ya dinga buga kansa da bango yana naushin hancinsa da

1 Comments On MASARAUTAR MU
avatar
zainabaliyu

1 year ago

Reply

I really appreciate masarautar mu, thank you

Please Login or Register in order to submit comment