Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan abu ya sosa ran Sa'ade, ta wuce daki tana share hawaye da bayan hannun ta.
Kamar Maimartaba ya san za'ayi haka, da daddare sai ga kyawawan akwatuna manya guda biyu Fanna ta shigo mata dasu, tace tsarabarta ce inji Alanguburo. Ta ce Fanna ta bude mata. Tsala-tsalan dogayen riguna na 'yammatan larabawa ne a ciki kala-kala harda masu ado na sarauta a jikin su, takalma da jakunkuna na yammata masu karshen tsada a daya akwatun kalar kowacce daga cikin dogayen rigunan.
Ta cire biyu a ciki ta bawa Fanna, amma sai Fanna tace bazata karba ba Fulani ta basu irin nasu. Wadannan 'ya'yan gidan kawai suke sanya su. Don haka sai ta dauki guda uku a ciki tasa a kayan ta na tafiya makaranta da zummar zata kaiwa Raheemah a matsayin nata tsaraban.
Tunda suka dawo hutu wajen kwana arba'in bata kara sa gimbiya Humairah a idanun ta ba, sai yau a cikin mota da zasu koma makaranta. Da ta gaisheta ko amsawa bata yi ba don Fulani Hibbani ta kara ja mata kunne akan mu'amala da ita, ta gaya mata duk abinda Alanguburo ya sayo mata a Saudiyyah irin wanda ya saya mata ne ko banbancin kala babu. Wannan ya kara rura wutar kishin Sa'ade a zuciyar Humairah, ta kudiri aniyar kuntata mata wannan zangon fiye da na baya.
****
Da Allah ya tashi taimakon Sa'ade, satin su biyu da komawa aka yiwa dalibai canjin dakunan kwana, inda aka dauke ta daga dakin su Humaira kuma cikin ikon Allah ba'a kaita kowanne hostel ba sai na su Raheema.
Murna wajen su abin ba'a cewa komai, a daren ne ta samu ta baiwa Raheema tsarabar data ajiye mata, ita kuma ta bata labarin zuwan ta Askira, tace ta damu baban ta da labarin ta ne ta yi ta rokon sa kan ya sa a kaita, shi kuma ya amince, amma cikin rashin sa'a sai bata samu ganin ta ba.
Nan aminci ya kara kulluwa, suka hade kai suka zama kamar 'yan biyu, gasu dama tsayin su daya, sai dai Raheema baka ce sosai cikakkiyar Kanuri, yayin da Sa'ade take jajawur kamar Fulani Bilkisu.
Kawancen Sa'ade da Raheema ba karatun Sa'ade kadai ya taimaka ba, ya taimaka mata a sauran fannoni na rayuwar diya mace, tsafta, kwalliya, da iya magana, hatta tafiyar ta Raheema gyara mata take don tace tana tafiya gaba-gadi babu tsanaki. Ta koya mata magana a hankali cikin nutsuwa da yadda zata dinga gyara da kula da sassalkan gashin kanta na Shuwan usli. Rayuwar Sa'ade ta yi ta samun cigaba islamically, educationally, socially and morally a makarantar EL-KANEMI COLLLEGE OF ISLAMIC THEOLOGY.
Balle yanzun da bata da tension din Humairah, kowa son ta yake a dakin su, kowa so yake ace shi abokin ta ne. Ga hannun ta a bude, kyauta gare ta kamar 'yar siyasa. Kwakwalwar ta ta bude a lokaci daya kamar kiftawar ido, take grasping ilmi na kowanne bangare wanda nan da nan ya kara canza ta.
Dama Alanguburo ya ce mata tunda ta kayar da mutum daya, to nan gaba zata kayar da goma ne, to ba goman kadai ta kayar ba talatin ta kayar, ita ce ta dauki na goma a ajin su, Raheema ta dauki na farko.
Don haka da karfin gwiwarta ta dawo gida wannan hutun. Amma har ta kwana ta wuni, bata ga Fulani ba haka bata ji shigowar Alanguburo sassan su ba. Ta gaji da kallon kofar dakin Fulani ta tambayi Fanna, sai Fanna tayi murmushi ta ce.
"Fulani ta tafi kasar India zata haihu".
Ta rasa a wane yanayi ta karbi zancen, haihuwa? Daman ciki gare ta? Tana farin ciki da jin zata samu karin mutum a kusa da ita, amma wani gefen na zuciyarta yana kishi. Idan ta tuno dama fa Fulani ba wai tana son ta bane, inaga ta samu dan kanta da ta haifa a gidan sarauta? Ai wulakanci gareta zai koma mode activated.
Ta kyabe baki tareda cewa "Allah ya sauke ta lafiya".
Hutun nasu dama ba mai yawa bane, na sati biyu ne, har sati biyun ta cika Fulani bata sauka ba balle ta dawo, suka koma makaranta zuciyar ta cike da kewar ta, bata san tana son ta har haka ba, sai yau da ta nemi ganin ko inuwar ta cikin gidan ta rasa. Shima Alanguburo Fanna tace yayi tafiya zuwa kasar Amsterdam (Neitherlands) shi da Ya Gumsu kaiwa babban dan Ya Gumsu dake karatu a can ziyara.
Rayuwa ta mikawa Sa'adatu Hashim a makarantar EL-KANEMI da budi da nasara da cigaba ta kowanne bangare. Wani sihirtaccen kyau ke bayyanarwa Sa'adatu wadda zuwa yanzu Sa'ade ya bace bat da taimakon Raheema, dama itace in an tambayeta sunanta sai ta ce Sa'ade Hashimu, bayan ba haka yake a rubuce a rijista ba. Raheema ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ta mantar da ita rayuwar ta ta kauye, ta yi adopting rayuwa mai cike da cigaba, wayewa da aji daidai na shekarun su, kaunar su da juna abin akwai sha'awa da burgewa a ciki.
Ranar wani visiting ne Raheema ta kira ta don ta gaisa da 'yan gidan su, fuska fal far'a take gaida Abban Raheema da mamanta, Bakin Babarbare mai zanen bare-bari akan fuskar shi ya sha manyan kaya na kamala, bayan sun gaisa ya sa musu albarka sai ya kasa dauke ido akan Sa'ade yana tunanin inda ya san wannan fuskar. Tabbas ya san fuskar amma ya rasa ta inda ya santan. Yana ta kokari ya tuna amma ya kasa. Har Sa'ade ta yi musu sallama ta koma cikin dalibai 'yan uwan ta.
Su dama ba'a zuwa musu visiting daga ita har Humairah, aiken kayan abinci kawai ake musu daga gida a kowanne visiting. Amma yau tana tsaye cikin daliban da ba'a zo musu ba ta hango shigowar motar data bata mamaki, bakar 'Land Cruiser' ce mai tsayi dauke da rubutun 'Biu Emirate'. Ba ta tafi wajen motar ba ta tsaya a inda take tana kallon su, don ta san ba wajen ta aka zo ba sai dai ko Humairah.
Wasu hamshaqan 'young ladies' ke fitowa daga motar tare da kyawawan 'ya'yan su kanana maza da mata, matan su hudu ne, daga inda take tsaye ta hango Humaira ta nufo su, duk jan ajin ta yau sai da ta hada da gudu-gudu ta rungume babbar cikin su.

"Yaa Maira! Ashe da gaske zaku zo?"

Ya Maira itace babbar 'yar sarki Yusufu, sunan sarautar ta kenan 'YaMaira' a matsayin ta na babbar 'ya. Sai mai bi mata a dakin Ya Kirjinoma wato Mairam Murjanatu, sai kanwar Murjanatun Mairam Naja'atu 'yar Hibbani, wadda Humaira ke bi a haihuwa.
Ya Maira tana aure ne a masarautar Biu yayin da Murjanatu ke auren Ambasadan Najeriya a Turkiya, ta zo ganin gida ne tareda 'ya'yan ta ta tadda Ya Maira ta zo daukar Naja'atu su zo wa auta ziyara kamar yadda ta alqawarta mata, sai ta biyo su, don itama ta jima bata ga Humairan ba.
Wani kilishi mai taushi baiwar da suke tare ta shimfida musu, ta koma motar ta soma fiddo sundukan abinci na alfarma da picnic coolers masu dauke da ababen sha masu sanyi. Nan suka baje suna ta hira, kai bazaka ce 'ya'yan kishiyoyi bane sabida shaquwa da kaunar da ke tsakanin su sabanin iyayen su da ke zaman kishin kwatar kai.
Naja'atu ta juya idanun ta kan Humaira, "Hummy ina yarinyar da ake kawo ku tare ne 'yar kalen dangin da kike cewa? Kin ji uwar rikon nata ta haihu ko?" Humaira tace "wai wannan 'yar mutsiyatan nan, ni rabon da insa ta a idona tun ranar da muka dawo hutu, da yake an raba mana daki". "Wace yarinya kuke magana ne? Menene kuma kalen dangi?" Inji Mairam Murjanatu. (Mairam title ne na kowacce 'yar sarki). Humaira ta ce "yarinyar da Fulani Bilkisu ta dauko riko, da fari cin uban ta nake yi as if na samu baiwa, sai kuma aka zo aka raba mana daki aka barni da cizon yatsa".
Murjanatu tace "dadi na da ke Humaira baki da kirki, albarkacin zaman tare ai ko gaisawa kya dinga yi da ita, ni na rasa inda kika dauko wannan fadin ran naki, na san dai ba daga Fulani Hibbani ba haka ba daga Alanguburo ba". Dama can Murjanatu tafi kowa saukin kai cikin 'ya'yan sarki kai bazaka ce ita 'yar gidan bace. An raine su akan yiwa wanda ke sama da su biyayya! Wannan ne ya sa Humaira ta kira wata junior din ta tace ta je ta zo mata da Sa'adatu Hashim. Ya Maira bata ce musu komai ba. Sai dai itama tana son ganin 'yar da Fulani Bilkisu ke rikon.
Suna tsaye itada wata 'yar ajin su Falmata wadda itama ba'azo mata ba, yarinyar da aka aiko ta zo ta same su, tayi mata nuni da inda suke zaune tace "ki je in ji Princess Humaira".
Saida ta ji gabanta ya fadi don ita har ta manta da matsalar Humaira, tace da Falmata "ina zuwa" sannan a hankali ta soma taku cikin nutsuwa zuwa inda suke zaune.
Tunda ta doso su taji gabanta na faduwa, duka fuskokin bata san su a gidan ba banda Humaira amma ta gane iyalin Sarki ne. Haka suma suka zubo mata ido cikin tsananin mamaki a fuskokin su, hatta gait (takun tafiyar ta) irin na Bilkisun Askirama ne. Is it possible dan kanwarka yayi irin wannan kamar da kai har fiye da dan da za'a ce kai ka haifa?
Har ta tsugunna ta soma gaishe su an rasa mai magana a cikin su, sai kallon ta suke with astonishment, duk sun mata kwarjini irin na su na 'ya'yan Saraki ta kasa ko duban fuskokin su. Ya Maira....ji tayi zuciyar ta na bugawa, tana da wata baiwa ta sunsunar kaddara. Haka kawai jikin ta ya bata akwai wani babban al'amari da zai zo ya kasance tsakanin su da yarinyar nan wanda bazata ce menene ko na menene ba.
So she became mute, kamar an dinke mata baki, ko gaisuwar Sa'ade bata iya ta amsa ba. Murjanatu ce ta kawar da mamakin ta ta amsa mata gaisuwa, sannan ta ce Yaya karatu? Ina fatan kina kokari? Kuma kina jin dadin makarantar taku?" Sa'ade tayi murmushin da ya fidda beauty point a barin hagu tace "ina yi ranki ya dade, kuma ina jin dadin makaranta" tana ta kallon yaransu cikin sha'awa kasancewar Allah ya sanya mata son yara kamar me, Murjanatu ta nunawa baiwar da suke tare daya daga kulolin abincin da suka zo da su tace ta dauka ta bita da shi har kofar hostel. Sa'ade tayi ta godiya, ba don yunwa take ji ba sai don karamcin Mairam Murjanatu, a ranta tana fadin ashe akwai mai kirki irin Askirama cikin 'ya'yan sa, at the same time tana ta karbar sakon harara mai zafi daga Humaira.
Har ta kule basu daina kallon bayan ta ba, Murja ta ce "Allah mai iko, dole Fulani Bilkisu ta dauko yarinyar nan daga cikin dangin ta, ku dubi kama don Allah har zuba take" Humaira ta kyabe baki ta ce "Ya Murja yanzu ne ta kile fa, da in kin gan ta ko kin ji maganar ta ko kin ga yadda take tafiya sai kin kusa yin amai. Kawaye take bi kamar mayya suna kilar da ita, banda haka bazaki so ki ganta sanda aka kawo ta makarantar nan ba".
Murjanatu tace "to ai sun taimaketa, yanzu wannan yarinyar ina ne baza'a shiga da ita ba ko wanene ba za'a iya aurawa ba? Kin ce Alanguburo na son ta, ki zuba ido ki ga irin mijin da zai zabo mata, kin san shi dai da so wa 'ya'yan sa da 'ya'yan rikon sa babban gida". Kishi ya kara turnike Humaira tace "insha Allahu tsohon hakimi zai bata gidan kishiyoyi goma taci uban ta". Ya Maira tace "ka so wa dan uwanka abinda kake so wa kan ka".
Haka suka maida Sa'ade da uwar ta topic of discussion har lokacin tafiyar su. A cikin hirar tasu naji Murjantu na gayawa Humaira Fulani Bilkisu ta haihu 'ya mace, amma bakwaini, 'yar tana cikin incubator har yanzu acan kasar India basu dawo ba.
Ya Maira tace "dama Alanguburo ya daina asarar kudin sa, sunan wannan din ma matacciya, wadanda ta haifa lafiya ma basu zauna ba balle bakwaini mai cutar sikila.
Raheema ta shigo da nata kabakin abincin, nan ta ga abincin alfarmar dake gaban Sa'adatu, tace "yanzu dama 'yan gidanku sun zo shine baki kira ni ba?" Sa'ade ta girgiza kai "ba waje na suka zo ba, ni ban san su bama, arzikin Humaira na ci suka bani wannan din". Nan suka zauna suka soma dibar garar dadin su. Yau kam sun wuni cikin farin ciki marar misaltuwa.
A haka zangon karatun ya kare, akayi hutu suka dawo gida.
Wannan karon ma bata tadda Fulani a gida ba, Fanna dai ta ce mata ta haihu, bata dawo bane don 'yar bata isa haihuwa ba aka haifeta sai ta yi kwari tukunna a asibiti.
Ta kasance cike da farin cikin jin labarin haihuwar nan, ashe itama zata samu dan uwa a duniya, wanda zata kira "kanin ta". Babban abun farin cikin ma diya mace. Sai dai damuwa ta biyo bayan farin cikin da Fanna tace 'yar mawuyaci ne ta rayu. Sai ta ji tausayin Fulani, yadda ta lura Alanguburo na son ta, sai take musu fatan samun rayayyen Da a tsakanin su.
Da tayi sallah sai ta samu kanta da daga hannu tana addu'a. "Ya Allah ka raya abinda Fulani ta haifa".
Haka tayi wannan hutun ma cikin kadaici da kewar Fulani, amma da yake yanzu ta auri littafan ta sai komai ya zo mata da sauki.
Tana son karanta littafan hikaya na turanci, duk da turancin nata baida karfin fahimtar kowacce kalma, sai take yi tana duba kamus na hausa da turanci, haka ta karbo su kala-kala daga library ta taho dasu gida musamman na ZAYNAB ALKALI da ABUBAKAR GIMBA.
A wannan hutun saida Sa'ade ta maida kanta 'yar karamar Farfesa a Ingilishi sabida karatu da duba dictionary. Kullum Fanna ta shigo kawo mata abinci abinda zata tarar tana yi kenan. Har ce mata take "ki dinga ajiyewa kina hutawa kada kan ki yayi ciwo". Sai tace da Fanna "da haka ne zan kayar da kowa Fanna, idan na iya turanci, idan ka iya shi kowanne darasi zai zo maka da sauki". Fanna sai tace "to ALLAH ya bada sa'a".
Har suka koma makaranta Fulani bata dawo ba.
In ka lissafa zaka ga cewa watanni masu yawa kenan basu ga juna ba, wanda hakan ya sanya matukar kewar junan su a zukatan su. Ga Fulani, ba damuwa tayi ta ganta ba don ta san tana lafiya amma somehow tana jin kewar ta a can kasan zuciyar ta. Saidai hankalin ta ya dauku ga son rayuwar abinda ta haifa wadda ke tsakanin rayuwa da mutuwa, don haka bata cikin kwanciyar hankali ko kankani. Shi kam Alanguburo ya gama fidda rai da rayuwar yarinyar kamar sauran wadanda suka gabata.
Amma bai fasa karfafawa Fulani gwiwa ba kan tayi hakuri ta barwa Allah ikon sa. Da sun haihu ko basu haihu ba, soyayyar da yake yi mata bazata taba raguwa ba, sannan ba ga Sa'adatu Allah ya basu ba?"
Bata cewa komai idan ya fadi hakan, amma a ranta cewa take "yar Hashimu ce ba tawa ba, da sannu Allah zai bar min tawa".
A sannu kuma sai Allah ya soma baiwa 'yar koshin lafiya sabida tsananin kulawar data ke samu daga likitoci da adduar uwa, tayi bul-bul kamar ba bakwaini ba, amma still sikila ce.
Sun dawo gida ranar wata Lahadi, sati biyu da komawar Sa'ade makaranta. Nan aka yi ta shigowa Fulani barka kamar za'a tsaga sassanta don yawan al'umma, kishiyoyin ta dake jiran gumbar sadaka dole suma suka yi lullubi suka zo barka don ganewa idon su abinda ta haifo ba don barkar ta Allah da annabi bace, "yarinya kamar Murjanatu" inji Ya Kirjinoma cikin al'ajabi. Hibbani tace "wannan dan gajeren hancin ai na Ya Maira ne, Murjanatu mai dogon hanci zaki hada da wannan burtuntunar, ai komai nata na Ya Maira ne" Ya Kirjinoma tace "in zaki tsoraci Allah, Murjanatu ce sak wannan". Fulani tayi murmushi bata ce komai ba, amma burtuntuna da aka kira 'yar ta ya sosa mata rai. Ta san kadan da aikin Hibbani, in ta kwabo maka magana ko zaka mutu ita babu ruwan ta.
Amma abin mamaki Ya Gumsu bata shigo ba, tana can bakin ciki na neman kashe ta, don bata taba zaton 'yar zata rayu ba.
Haka 'ya'yan gidan maza da mata na nesa dana kusa suka yi ta tururuwar zuwa barka har wajen kwanaki talatin mutane basu tsagaita ba. Daki guda sai da ya cika taf da kayan barka na uwar dana 'yar mai suna "Zarah"
Cikin kuyangin Fulani aka warewa Zarah masu kula da ita su biyu, dattijuwa da budurwa, dakin Zarah yana jikin na Fulani, yayin da na Sa'ade ke kallon nasu.
Suka cigaba da rainon ta cikin tsananin kulawa.
*****
Kayan su suke hadawa itada Raheema kasancewar gobe hutu, suna yi suna hira, Sa'adatu tace "wannan hutun ina duban hanyar ki, na san daga Fulani har Alanguburo in suna gida, baza'a hanaki shigowa ba".
"To Allah yasa Abba ya barni, ya ce min ma shi kallon sani yake miki" Sa'ade tayi dariya, "ba dole yayimin kallon sani ba tunda nima 'yar sa ce?"
Haka suka yi ta hira har suka kammala hada duk abinda suke bukatar zuwa dashi gida.
****





Yarinyar dake tsaye yau a gaban ta wata siririyar budurwa ce, cikin shekaru na tashen balagar diya mace. In bata manta ba tana kamar girman ta aka yi mata auren fari, auren dolen da ya zamo silar zuwan ta duniya.
Tana tsaye daga bakin kofa sanye cikin uniform din ta na makarantar sakandire, kyakkyawar fuskar ta kunshe da sassanyan murmushi, wanda kai tsaye ta fassara shi da murmushin farin cikin abinda yarinyar ta shigo ta tarar tana yi (breastfeeding her baby).
Ta tako a hankali cikin tafiyar data banbanta da ta SA'ADEN da ta sani watannin baya, mai tafiya tana hada hanya, wannan Sa'adatun a nitse take tafiya. Her gait, her serene smiles duka suna kara tabbatar mata da cewa, ta fito ne daga cikin mahaifar ta kwatankwacin diyar dake rungume a hannun ta a yanzu, wato Zarah.
Banbancin dake a tsakani shine; wannan soyayyah ce ta kaita ga haifar ta, yayin da waccan kiyayya ce silar nata zuwan duniya.
Ta yi nisa a wannan tunanin har bata san lokacin da Sa'ade ta karaso gareta ba, kokari take ta karbi 'yar daga hannun ta wadda ta saki nono tana kallon Sa'aden da kyawawan idanun ta. Sa'ade blushing ta ke from ear to ear, ta dauka Fulani zata hana ta daukar diyar ta, amma ga madaukakin mamakin ta sai ta ga ta sakar mata.
Ta dauki kanwar tata tana ta murmushi. "Beautiful!" Ta fada cike da kauna. Fulani ta cigaba da bin ta da kallo ba tare da ta sani ba, duk wani kankanin canji dake tare da Sa'aden a watannin data kwashe bata ganta ba saida ta zaqulo shi cikin idanun ta.
"Ashe kilewar diya mace ba wuya muddin zata je makaranta!" Fulani Bilkisu ta fada a zuciyar ta. Tana son comparing soyayyar data ke ji akan Sa'ade da Zarah. Sai ta ga cewa ratar dake a tsakani mai tsananin fadi da girma ce, ta haifi Sa'ade ne kawai amma babu ko digon soyayyar ta a zuciyar ta, sai tausayi da kyautayi irin na zuciyar musulunci.
Yanzu ne ta san kaunar uwa akan dan ta, da ta haifi 'ya da wanda take so. Can wani lungu na zuciyarta kuwa kururuwa yake yana objecting: idan soyayyar Sa'ade da ta Zarah, bata zo daidai da juna ba, sai dai ace ta Zarah ta rinjayi ta Sa'ade, amma ba wai ace babu burbushin ta ko kankani a zuciyar ta ba.
Bata ankara ba sai ganin 'yar ta tayi a bayan Sa'ade, tasa tawul din da aka nannade ta a ciki tagoye ta tsam ajikin ta, ta soma dan jijjigata sabida dan rikici data ke yi irin na jarirai. Sai tasamu kanta da kasa cewa ta sauko mata 'yar ta, ta mike ta shige turakarta ba tare da ta ce da ita komai ba. Dama kuma tana so ta huta din, gashi ta sallami kowa tace bata son ganin kowacce baiwa a bangaren ta sai gobe da safe in Allah ya kai mu. Sai ganin tsayuwar Sa'ade ta yi a gaban ta ba zaton ta ba tsammani.
Sa'ade saboda jin dadin Fulani ta bar mata Zarah sai ta nufi dakin ta goye da ita, roba ta samu ta hada ruwan dumi ta saukota ta soma yi mata wanka, ta gama ta nade ta cikin shawul ta fito kan gadon ta ta dauki basilin din ta tana shafa mata.
A lokacin Fulani ta shigo, ta bude baki da zummar yin fadan don me ta yi mata wanka bayan ba'a jima da yi mata wanka ba? Amma sai ta ga yarinyar na ta bangala dariya Sa'ade kuma ta himmatu wajen yi mata wasa a cute kumatunta. Sai suka bata sha'awa, ta juya silently ta fita. Ta dauko set din kayan baby na sanyi ta dawo ta watsawa Sa'aden ta sake juyawa ta koma.
Shikenan daga wannan ranar Sa'ade ta kwace rainon Zarah daga hannun Fulani da masu rainon ta, kayan yarinyar ma saida ta san yadda tayi suka dawo dakin ta. Tsakanin ta da Fulani shine kawai idan ta bukaci nono.
Hausawa suka ce wai "Mai Da wawa ne", wannan kyautatawa da kauna ta Sa'ade ga Zarah a hankali yake hakurkurtar da zuciyar Fulani Bilkisu, daga mummunan kullacin Mal. Hashimu dake cikin ta, wanda ya hanata ganin farin Sa'ade har ta kaunace ta matsayin 'ya 100%.
A hankali ta soma rage fada, da tsawa da hantarar da take yawan yi mata, ta soma yi mata magana jefe-jefi cikin sanyin rai.
Satin ta uku a gida sai ga Raheema Kyari, wannan karon ba'a hanata shigowa ba, Kuyangar data rako ta sai ta hada ta da Fanna, ita kuma Fanna tace ta jira daga waje, ta nemo izni tukunna.
"Kawa kuma daga Maiduguri?"
Fulani ta fada cikin mamaki.
"Haka ne ranki ya dade, sannan ta tabbatar min ita aminiya ce ga Sa'adatu sannan ta san da zuwan ta".
Fulani ta hadiye fushin ta wanda tayi aniyar saukewa akan Sa'ade bayan tafiyar bakuwar, ta ce Fanna ta shigo mata da yarinyar.
Cikin sallama da shiga ta mutunci da kamala Raheemah ta shigo, tunda ta shigo Fulani ta kura mata ido. She looks so much like her father wanda ta yi wa farin sani. Mikewa tsaye tayi ba tareda ta san lokacin da ta yi hakan ba, hatta tsagin fuskarsa biyu-biyu dogaye gasu nan kwance a fuskar Raheema.
Da ta gaisheta da kyar tayi controlling razanar ta ta amsa,
"yaya sunanki?"
"Raheema Kyari Babagana"
"Kyari?!"
Ta fada da amon muryar da ya baiwa Raheema mamaki, "eh, sunan Babana kenan" "daga wane gari kike?" "Daga Maiduguri na zo, acan muke zaune, amma mu 'yan asalin Damaturu ne".
"Shikenan dangin ubanta sun biyo ta, a lokacin da na fara sanyata a raina".
Fulani ta ayyana a zuciyar ta, ta kuma kudiri aniyar kin gayawa Sa'ade kowacece Raheema a gareta.
"Shiga nan dakin, tana ciki"
Ta fada tare da nuna mata dakin, ta kuma tashi ta bar musu area din gabadaya zuwa turakar ta.
Sa'ade sai ganin Raheema ta yi ta shigo da sallama, zo ki ga gudu da murna wajen Sa'ade, saura kadan ta kada Raheema. Ita kuwa sai dariya take. Ta dauki Zarah dake tsakiyar gadon ta tana fadin "masha Allah, beautiful baby". Hira kamar ta kashe su. Fanna ta shigo wa da Raheema abinci na musamman suka ci tare cike da farin ciki.
Can da yamma Raheema ta ce "Sa'adatu ki zagaya da ni mana in ga masarautar taku in samu abun baiwa su Sarina labari". Sa'ade tayi dan jimm! Kafin tace "ni bana zuwa ko'ina, daga daki sai daki, Fulani bata bari na". "Amma meyasa?" Inji Raheema. Ta dan kyabe baki "i don't know. May be sabida kishiyoyin ta". Daga haka suka bar hirar.
Washegari Fulani ta sa aka yiwa Raheema sallama ta girma, aka maida ita har Maiduguri.
****
Ya Gumsu ta shiga turakar mai Askira cikin kwalliya ta kasaita a matsayin ta na mai girki ranar, abinci yake ci tana gefen sa tana masa firfita, cikin hila irin ta matan da

1 Comments On MASARAUTAR MU
avatar
zainabaliyu

1 year ago

Reply

I really appreciate masarautar mu, thank you

Please Login or Register in order to submit comment