Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zo kusa da ita, a kuruciyar Sa'ade ba don komai bane sai don ita 'yar kauye ce. Tana kyankyamin ta ne kawai. Tasa a ranta daga yau kullum zata dinga wanka, don Fulani ta daina tsantsamin ta.
Ta mike ta sanya hijab ta tada birkitacciyar sallarta, wadda ko kadan ba daidai take yin ta ba, sannan babu wani karatun sallah na azo a gani, karewa ma "BA-SIM-MI'ARA" take karantawa a cikin sallahr.
Data idar da azahar da la'asar sai ta ja farantin abincin da Fanna ta ajiye mata, ta ci iya cinta kunnenta kamar ya gutsure don dadin naman tolo-tolo, data gama ta je ta wanke hannu ta dawo ta kwanta a gadon da tun dazu take son ta ji yaya yake? Wane irin laushi gareshi haka da tun dazu ya ke fizgar idanun ta? Wani barawon barci yazo yayi awon gaba da ita, sau biyu Fanna tana shigowa, ta fidda farantin ta kunna mata iyakwandishan wanda ni'imar ta ya kara armasa mata barcin.
****

Sai safah da marwa take a dakin barcinta, ta kasa barci, ta rasa abinda ke mata dadi. It's very unusual maimartaba ya shigo sassan matan sa. Amma yau sai kawai ta ganshi ya shigo har dakin barcin nata, ba zaton ta ba tsammani.

"Zuwa nayi ki gaya min abinda matsayi na bai kai na sani ba, wanda ya faru cikin rayuwar ki ta baya".

Ya fada yana mai zama a gefen hamshakin gadon ta.

Gabadaya ta zama upset, daga rana zuwa dare, fuskarta kamar jikakkiyar takarda, ta zama yellow, kasancewar ta jazur, damuwa kwance baro-baro, ga wani tsohon kwantaccen bacin rai da ya dawo mata sabo.
"Allah ya huci zuciyar ku, Allah ya huci zuciyar Askirama!".
(Askirama na nufin 'mai Askira' da harshen Kanuri).
Ta cigaba da fadin "Al'amarin bashi da muhimmancin da zaku san shi, shi yasa baku san shin ba. Sabida ban taba daukar sa da muhimmanci ba, ban kuma taba zaton wannan 'yar zata biyo ni ba, don nasan uban ta ko za'a dora masa wuka a makoshi, akan ya bani ita, ba zai taba bayarwa ba".
"Sai kuma mutuwa ta yanke muku dukkan kudirin ku ke da shi, akan baiwar Allah, wannan ya isa ya nuna muku cewa karfin kudura da irada naShi ne, bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwa ba, face abinda Ubangiji ya tsara masa".
Mai martaba ya fada mata a tsanake.
Ta sunkuyar da kanta, tana wasa da yatsun hannun ta, bata ce komai ba.
"Ki gaya mini duk abinda yakamata na sani akan yarinyar nan, tunda dai kin yarda sunnah ki kai kika haifeta, kada ki zama azzalumar Uwa, wallahi Allah bazai bar ki ba".
Fuskarta tayi jajawur kafin hawaye su cicciko idon ta.
"Ran ka ya dade bana son tuna labarin nan, bana so. Ba abun fade a cikin sa, me kake so ka ji? Yes, aure na yi na haife ta, amma ban taba son uban ta ba! Sau daya ya taba kwanciya da ni bisa fin karfi har na samu cikin ta. Kana so ka ji cewa Babana biyan bashi yayi wa ubanta da ni? Ya aura masa ni a matsayin filin sa da yake bin sa bashi?"
Maimartaba ya nuna abin bai bashi mamaki ba, a fuska da muryar sa babu komai, yace "to ita yarinya meye laifin ta? Bata zo duniyar ba lokacin, balle ta san laifin da babanta ko baban ki yayi miki da zaki rama a kanta. Ki yi a hankali, 'ya'ya amanar Allah ne a hannun mu, bar ganin ke kika haifeta, wallahi hakkin ta zai iya kai ki wuta. Ba kya tunanin hakkin ta ne yake hana wadanda kike ta haifa rayuwa? Tunda itama baki ji kanta ba a lokacin da Allah ya baki ita?"
Bata ce komai ba amma tabbas kalaman sa sun shige ta, daga zaunen da yake ya kamo hannun ta. "Bilkisu ki karbi amanar da Allah ya baki da hannu bibbiyu, na yafe jin labarin auren ki da mahaifin ta tunda na lura yana tono miki bacin rai ne, wanda kika riga kika manta. Abu daya nake so ki rike a ranki shine wannan yarinya dolen ki ce, bata da sauran gata sai ke, wani dan uwan baban ta da kika ce akwai a Damaturu ba shi shari'ah ta bawa rikon ta ba kasacewar ta mace, kuma kina raye, sannan kina da halin rike ta. Ni na karbi yarinyar nan kamar sauran 'ya'ya na..... idan ni da nake kishin Baban ta ya riga ni samun ki, na karbi 'yar sa zan rike da amana, ke mai zai hana ki kwatanta tausayi da adalci irin na UWA ki karbi marainiyar Allah???"
Sai ta fada jikin sa tana kuka sosai, jikin ta yana tsuma, ya rike ta sosai a jikin sa yana cigaba da lallashin ta, Fulani Bilkisu ta san maimartaba yana son ta, amma bata zaci son ya kai har haka ba, duk da bata taba haife masa rayayyen Da ba. Shi gashi yau ya karbi nata da hannu bibbiyu, wanda bai taba sanin da wanzuwar sa ba. Idan bata yi masa biyayya ba kuwa, hakika ta cika butulu, wadda bata godewa ni'imomin Ubangiji gareta ba.
"Zaki kula da ita ko Bilkisu? Zaki bata kaunar duk da ya kamata ki bata?"
Ta gyada masa kai, ba tare da ta ce komai ba. Sai rungume shi data yi sosai a jikin ta.
"Ka yi min alfarma Askirama kar ka gayawa kowa cewa 'ya ta ce, don Allah, kace 'yar kanwata ce na karbo, ina gudun gorin kishiyoyi, tunda cikin su babu wadda ta san na taba aure kafin na zo gidannan".
"In don wannan ne kada ki damu, amma akwai wadanda sun riga sun ji a fada, zan gargadesu don duk na san su".
"Nagode.... Nagode Askirama. Alanguburo (Allah ya kara maka yawan rai)".
****

Duk da haka sai da ta kwashe kwanaki uku bata nemi Sa'ade ba, bata shiga dakin ta ba, bata nemi sanin halin data ke ciki ba. Fanna dai ta gaya mata tana nan lafiya kuma tana kokarin koyar da ita tsafta da sauran abubuwa.
Sarki Yusufu ya san halin kafiya irin na Bilkisu, don haka bai gushe ba yana cigaba da lallashin ta akan Sa'ade. Tana nuna masa komai lafiya, alhalin bata kara sanya yarinyar ma a idon ta ba.
A rana ta hudu sai gashi ya kara dawowa da kansa da safe kafin ya fita zuwa zaman fada. Tana karya kumallo ita kadai a 'dining table' din falon cin abincin ta. Ta mike cikin girmamawa ta same shi a kujerun da suka kawata falon, suka gaisa kamar yadda suka saba cike da kewar juna kasancewar ba ita tayi girki ba, kwana biyu kenan basu hadu ba, cikin hikima irin ta manya ya ce,
"Yaya kike cin abincin ke kadai babu 'yar tayin hira? Maza kirawo min ita mu gaisa, sabida ita na shigo".
Fuska a turbune tace "bata tashi daga barci ba"
"A taso ta"
Ba yadda ta iya dole ta juya cikin kasaitaccen takunta ta nufi dakin da ta san ta ce a ajiye mata Sa'aden kamar wani kayan wanki.
Ta murda kofar ta shiga a hankali ba tare da ta bari sauti ya fita ba, akan darduma ta same ta tana sallah, tana wani karatu a fili "basim-mi'ara, alu ambaki wau-zal, wa'aluba ilallan haakuri"..... sannan ta tafi sujjadah ba tare da ta yi ruku'u ba. Fulani ta mutu a tsaye, sujjadar ma guda daya tayi ta sallame sallahr. Kamar jikin ta ya bata da mutum a dakin, da sauri ta juyo, suka hada ido da matar data ke kwana tana wuni da ita a ran ta.
Da kyar Fulani ta hada sautin muryar ta waje daya, ta ce "sallahr me kike yi?"
"Asubah ce Inna"
"Asubah? Wa ya ce miki yanzu ne lokacin sallar asubah karfe goma na safe har ta wuce?"
"Ai i yanzu nake yin ta kullum, wataran ma sai na dawo daga talla ma nake hadawa da azahar inyi kafin Baba ya barni na fara zuwa makarantar A-BA-CA-DA".
Takaici ya hanata magana kawai ta juya a fusace tare da cewa "biyo ni".
Suna shigowa falon taga maimartaba a zaune cikin rawanin sa da jabba, da sauri ta tafi gareshi ta zube a gaban sa, ta lura shi mai kirki ne ba irin matar sa ba mai kama da mala'ikun daukar rai. "Baba ina kwana" yayi murmushi yana kallon ta da tausayi "Anan ba'a cewa Baba diyata. "Alanguburo" ake cewa. Tayi kokarin maimaita kalmar amma ta kasa. Yayi dariya kadan cikin tausayi yace "kina son makaranta?" "Sosai Alan...." sai ta yi shiru. Ya karasa mata "......guburo" ta maimaita a hankali "Alanguburo" "masha Allah! Makaranta wacce kike so? Ta kwana ko ta jeka ka dawo?" Ta saci kallon Fulani Bilkisu ta ga yadda take hararar ta, sai ta ga ai gara mata ta zabi makarantar kwana akan zama ita kadai cikin daki da idanun Innarta masu razanata. A hankali ta ce.
"Na fi son makarantar kwana Alanguburo"
"To shikenan tashi jeki abun ki, nan da sati biyu za'a kai ki, amma bazakiyi nisa da gari ba, nan cikin garin Maiduguri zan sa a nema miki mai kyau, ince ko kina kunna talbijin kina kallo?"
"Menene talbijin Alanguburo?" Ya nuna mata ita da hannu, ta ce "ai babu a dakin dana ke" ya ce "Innar ki bata kyauta ba, yau zan sa a kawo miki taki a jona miki a dakin ki". Ta hau murna sosai ta ce
"Nagode Alanguburo"
Yace "Allah Kawun jo".
****
Duk yadda ta so ta wuni cikin sukuni a ranar ta kasa, sallahr Sa'ade da karatun sallahrta kawai take tunowa. Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, wai dan musulmi ne yake irin wannan ibadar, me ake da rayuwar jahilci.
Ta so ta share, don a ganinta tunda Askirama ya ce zai kaita makaranta ta san zata koya a can, amma sati biyun da zata cigaba tana irin wannnan sallahr zuwa lokacin da zata koya din shin idan ta bari Allah ba zai tambaye ta ba? Tunda har ya nufe ta da gani, tamkar umarni ne ya bata kan ta yi mata gyara tana so ko bata so, ita ba jahila bace ta san muhimmancin sallah ga dan musulmi, balle wanda ka haifa a cikin ka.
Ta kira Fanna da zata wuce kai mata abincin dare, tace "kira min yarinyar can ta same ni a dakina yanzun nan". Fanna ta yi matukar mamaki don banda ita Fannan ba mai shiga dakin Fulani Bilkisu, itama gyara ne kawai yake kai ta shima ba kullum ba, sai lokacin da Fulanin ta bukata.
Har dakin ta kawo Sa'ade, sannan tayi bankwana ta juya, don ta gama aikin ta na daren sai kuma gobe.

A wannan lokacin ne Fulani ta yi mata kallo na sosai, tana durkushe gabanta kamar yadda ta ga Fanna na yi, da can a fizge take kallon ta, a 'yan kwanaki hudun kacal data yi cikin gidan har ta fara washewa, kamannin ta da ita sun gigitata, kallo daya zaka yiwa yarinyar ka san ita ta haifi abar ta, kamar ta yi kaki ta tofar. Anya akwai wanda zai yarda in aka ce ba 'yar ta bace? Ko dai ta bari Askirama ya fadi gaskiya ne? Amma in ta tuna gorin da zata sha wajen Ya Gumsu (most senior wife ta sarki) kuma wadda suke buga mugun kishi da ita fiye da sauran matan sarki sabida yadda take jin kanta matsayin uwar manyan 'ya'yan sa, amma ya zo yana fifita Bilkisu akan ta, wanda hakan ya haifar da zazzafan kishi a tsakanin su, sai ta ga gara ta bar ta a 'yar kanwar ta ce, ai is normal dan dan uwanka yayi kama da kai.
Ta yi ajiyar zuciya tareda dauke kanta daga kallon yarinyar tana jin kirjin ta na wani irin bugawa, inta kalli yarinyar sai ta tuno sanda Hashimu ya daure ta a jikin karfen gado ya haike mata, ko ta so ta ji tauayin ta abinda take tunawa kenan ta ganta bakikkirin a idanun ta, duk da an ce ya mutu, bata jin nan kusa zata yafe masa, ta hadiye wani kullutu daya tokare ta a kahon zucci, tana mai kautar da kanta ta ce mata.
"Kin yi sallahr Isha?"
"A'ah Inna, bari nayi sai can dare, an ce sallah cikin dare tafi lada"
Ta galla mata harara tace "inji uban wa? Ni kar ki sake ce min Inna".
Sa'ade ta yi shiru tana kikkifta ido. Ta nuna mata hanyar toilet da hannun ta "muje ki yi wankan sallah da alwalah akan idona na gani"
Sa'ade ta zaro ido.
"Kina nufin a gaban ki zan yi timbir?"
Ta sake galla mata harara cikin tsawa tace,
"Rufe min baki! Ko kin ga ana yi min musu a gidannan? Zaki wuce ko sai na hankada ki?" Sum-sum-sum Sa'ade ta wuce ita kuma ta bi bayanta.
Da kyar Sa'ade ta iya cire riga a gaban Fulani, tana yi tana kare kirjin ta, tace tayi wankan tsarki tana gani. Ai yadda ake normal wanka da soso da sabulu haka Sa'ade ta yi, alwala kuwa ba'a zancen ta. Fulani Bilkisu ta ji kwalla ta tarammata, ba na tausayin yarinyar bane na tunanin wai gudan jinin ta a duniya ne wannan ba arabi ba boko.
Zama tayi akan masai ta dinga gaya mata yadda zatayi wankan tsarki don ta tambayeta cewa ko ta fara ganin jinin al'ada ta tabbatar mata ta fara, sannan ta koya mata alwala, suka fito ta bata mayafi tace ta tsaya ta lura sosai da yadda take sallah. Sannan tasa ta tayi tana kallo. Akwai improvement sosai duk da haka wani abun sai kyalewa ta yi, ta san a hankali zata kara gyarawa.
Sannan ta zaunar da ita a gaban ta ta koyar da ita fatiha, falaki da nasi da ikhlas, cikin 'yan mintuna Sa'ade ta karanta mata su tiryan-tiryan, daga nan ta gane tana da saurin daukar abu muddin zata samu kulawa.
Sai karfe goma na dare ta sallameta. Bayan ta gaya mata wannan karatun data koya mata yanzu ta karanta ta tofa a hannayen ta ta shafe jikin ta da shi.
Daga ranar kuma bata kara nemanta ba, sai bayan sati guda, shi din ma kayane akwati uku maimartaba ya aiko mata dasu, atamfofi, lesuka da shaddoji na alfarma, ta sa telar ta tazo har sassan ta ta gwada yarinyar a gabanta, don har zuwa ranar ko kofar falo na biyu bata bari ta fita ba, Allah Allah take ma satin ya zagayo a kaita makarantar kwanan ta huta.
Ta manta cewa magana bata buya a gidan sarauta, abinda bata sani ba kuyangi suna magana a junan su cewa yarinyar nan da aka kawo daga kauye tun ranar da ta zo basu kara ganin ko inuwarta ba kuma basu san daga ina aka kawo ta ba ko aikin me ta zo yi. Har tsakanin kuyangin sauran matan sarki suna zancen har zance ya kai kunnen su Ya Gumsu, Ya Kirjinoma da Fulani Hibbani cewa Fulani Bilkisu ta dauko rikon 'ya daga kauye. Ya Gumsu tace "matar so an gaji da zaman kadaici an buge da tsinto 'ya'ya". Ita kuwa Hibbani cikin hila ta tambayi Askirama ko ya san da batun 'yar da Bilkisu ta dauko riko? Ba tareda ya bata hankalin sa ba ya ce 'yar kanwarta ce, kanwar tata ta mutu". Haka ta je ta fesawa Ya Gumsu, ita Ya Kirjinoma dama bata shiga sha'anin su, daga ita sai 'ya'yan ta take harkokin ta, tana da kamun girma sosai.
A cikin sati biyun kafin tafiyar Sa'ade makaranta akwai cigaba sosai a tare da ita, sallahrta ta gyaru, ga wanka ya kama jikin ta, Fanna ta koya mata yin Brush sau biyu a rana, safe da dare, ta zama kamar Yayarta. Har hira suke yi sosai in Fulani ta tafi girki Turakar Sarki. Tana kara gyara mata kome ta ga ta yi ba daidai ba, har dige-digen data ke yi a fuskarta da kwalli Fanna ta hana ta.
Sannan ta kiyaye umarnin uwargijiyarta da gaskiya na cewa kada ta bari kowacce kuyanga ta zo inda Sa'ade ta ke, bata yarda tayi alaqa da kowa cikin sassan ba bayan ita Fannar.
Ana i gobe sati biyun da Sarki yayi alkawari ya sake shigowa sassan nasu, wannan karon da daddare. Ya samu Fulani da kuyanginta kusan su duka goman ana bata labarai tana murmusawa. Yana shigowa duk suka mike, fadi suke in chorused "...zauna daidai mai Askira... takawar ka lafiya Askirama!"
Suka fice akan layi, shikuma ya zauna sannan ya soma yiwa Fulani fada.
"Haka kawai kin kama yarinya kin kulle a daki don mugunta, kin hanata ko zama cikin kuyangin ki, to wadanda kike gudun su san da zamanta sun riga sun sani, gara ma ki sakarwa yarinya mara ta yi fitsari".
Ita dai bata ce komai ba sai "Allah ya huci zuciyar Askirama (mai Askira).
Bai amsa ta ba ya ce "kira wo min Sa'adatu". Ta tashi tana tafiyarta cikin yauki na halitta ta nufi dakin Sa'ade.
"Ke ki zo ana kiran ki".
Ta ce da Sa'ade wadda ke luntsume tsakiyar gado ta kafawa talabijin ido tana kallon diramar larabawa. Irin yadda ta saki baki da hanci tana kallon ba karamin haushi ya baiwa Fulani ba. Kamar tayi fiffike ta shige cikin akwatun talbijin din a yi da ita. Ko maganar Fulani bata ji ba, sai da ta taka ta kashe soket din talbijin din, tayi firgigit tace "haba don Allah Inna ya zaki kashe mini.....?" Sauran maganar ta makale mata a makoshi sabida mugun kallon da Fulani ta jefe ta da shi. "Na ce ki zo, ko ke kurma ce ne?" Sa'ade ta sauko daga gadon ta bi bayan ta don tuni har ta fice, tana shigowa falon ta yi arba da Sarki, ai tuni ta washe ta daina fushin kashe mata talbijin da Fulani ta yi ta nufi wajen sa cikin tsananin murna.
"Alan....ina wuni?" Yayi murmushi ya yafito ta da hannun sa. "Zo nan kusa gare ni Sa'adatu" ta rarrafa gabansa ta zauna ya ce "Ah! Masha Allah, da alama Fulani tana kula da ke, gashinan kin yi haske kin yi kumatu" ta saci kallon Fulanin, hararar data ke mata yasa ta kasa fada masa abinda ta yi niyya, cewa ita bata wani kula da ita, Fanna ce take kula da ita, ita sai tayi kwanaki bata ko ga inuwar ta ba. Aka soma shigo da kwalaye da katon katon na kayan masarufi ana jibgewa a gefe. Daga ita har Fulani Bilkisu bin kayan suka yi da kallo don basu san ko na menene ba.
"An samo makarantar Sa'adatu, an gama komai, gobe za'a kaita, ita da zuwa gida sai karshen kowanne zangon karatu, sai kuyi sallama yau, don gobe da sassafe za'a kai su ita da Humaira".
Fuskar Fulani ta tattare cikin rashin jin dadi, bata son a alaqanta komai na Sa'ade da 'ya'yan gidannan, ba don komai ba sai don gudarwa kanta gori. Balle 'ya'yan Hibbani sarakan surutu, ita kuma Hibbanin uwar tsugudidi, in taji abu to tabbata Ya Gumsu ta ji ta gama. Amma ai da kunya tace masa bata so ya hada 'yar ta da 'yar sa, shi da yayi wannan kara ta mutuntawa in ba'a gode masa ba akalla baza'a kalubalance shi ba.
"Allah ya kaimu"
Kawai ta ce. Sa'ade ta dago cikin farin ciki ta ce "Alan....amma inna tafi sai bayan shekara zan dawo ko?" Cikin mamaki yace "ba kya marmarin ganin Innar ki zaki yiwa kanki fatan yin shekara a makaranta?" Ta sunkuyar da kai a ranta tana so ta gaya masa ita Innar ce bata son gani kusa da ita da wadannan muzuran idanun nata masu karkada mata 'ya'yan hanji, sannan kadaici yana damun ta, banda yanzu da aka jona mata talbiin take debe mata kewa.
"Wata uku zaku yi ku dawo hutu, na hada ki da 'yar uwarki Humairah don ki ji dadin zama kina ganin na gida a kusa da ke. Ki maida hankali kiyi karatu, ki kawo min sakamakon da zan yi alfahari da ke, kin ji Sa'adatu?"
Ta gyada masa kai "insha Allah zan yi kokari Alan....guburo, nagode, Allah yayi maka fin abinda kayi min".
Shi da Fulanin duka suka kalle ta jin abinda ta ce, don basu yi zaton tana da hankalin sanin an yi mata alkhairi ta bi da kyakkayawar addua irin haka ba.
Cikin daren Fulani ta kasa barci, ba kewar Sa'ade ta ke ba, damuwar ta na hada Humaira da Sa'ade da za'ayi ne waje daya, ta san Humaira da shegen kinibibi kamar na uwar ta zata iya jan Sa'ade a jiki ta ji sirrin su ta fesawa uwarta. Don haka ta mike daga kwanciyar ta ta sanya hijab kan rigar barcin ta ta nufi dakin Sa'ade.
Ta yi dai-dai sai sharar barci take abinta, santala-santalan fararen cinyoyin ta a waje, rigar barcin ta yaye can sama, gashin kanta da Fanna ta wanke mata dazu da shampoo sai sheki yake ga santsi, sai ta ganta exactly like herself when she was twelve years of age, a perfect replica of Bilkisu! Bata taba yi mata cikakken kallo irin na yau ba, kauyancin duk ya fara barin jikin ta, a maganarta kawai zaka ji shi.
Ta daddage ta daka mata duka a cinya, Sa'ade ta zabura ta tashi tana sosa wajen tana mutstsikar ido. "Haka kike kwana tsakiyar kwan lantarki sabida baki da hankali ko? Me yasa baki kashe ba?" Sa'ade ta zumburo baki "ni ban san ana kashewa ba" "daga yau duk sanda zaki kwanta ki kashe fitila mai haske ki bar dim, na ga alama ke kidahuma ce" Sa'ade ta kumburo kumatu bata amsa ba. Ta dora kafarta daya bisa gadon ta tsaya akan daya, sannan ta kama kunnenta na dama da kyau ta murde, Sa'ade ta saki tsuwwa don zafi, Fulani tace "idan kika gayawa wani a makarantar ku ko wadda zaku tafi tare ke 'ya ta ce sai na kabari ya fi ki jin dadi a gidannan, kowa ya tambayeki wacece ni a wurin ki ki ce ke 'yar kanwata ce, babar ki ta mutu, kin ji ni ko baki ji ni ba?"
Hawaye na fitowa daga idon Sa'ade ta ce "na ji!".
Fulani ta sakar mata kunnen, ta juya zata bar dakin. Sai ta tsinkayo muryar Sa'ade cikin rishin kuka.
"Amma me yasa kika tsaneni haka? Da har ba kya so a ce ni 'yar ki ce? Kawai saboda ni Babana talakane ba sarki bane?"
Wuta ta daukewa Fulani Bilkisu, ta kasa gaba, ta kasa baya. Bata taba zaton yarinyar zata iya yi mata wannan tambayar ba. Sa'ade tayi murmushi mai ciwo ta share hawayen ta da bayan hannun ta.....
"Ki nemo min dan uwan mahaifina na Damaturu, tunda kinsan inda ya ke, insha Allahu zan nesanta kaina dake kamar yadda kike so, zan koma wajen sa".
Bata bata amsa ba ta fita daga dakin, jikin ta yai matukar sanyi, bata zaci yarinyar nada hankalin gane abubuwa har haka ba, a shekarun ta goma sha biyu, ko ta yi mata bayani bazata gane ba, bata kin mahaifin ta don talaucinsa sai don rashin SO da zafin AUREN DOLE. Tunda itama 'yar talakawa ce futuk! Gaba da baya, inda halacci ashe kuwa bazata manta talauci sabida arzikin gidan aure ba.
Da maganganun da Sa'ade ta gasa mata ta kwana a ranar suna gasa mata zuciya. Shi yasa da safe ta ki fitowa balle ta ga tafiyar ta, bata so ta karasa karya mata zuciya, bata shirya karbar ta matsayin 'ya anan kusa ba kuma har abada bata jin zata iya idan ta tuna Hashimu ne Baban ta.
Fanna ce ta zo ta tashi Sa'ade ta taimaka mata tayi wanka, ta bata kayan makarantarta ta sanya, tuni an fidda kayan ta zuwa mota. Tun shigar ta gidan kwana ashirin da daya sai yau ta fito ta shaqi fresh air, daga iskar fanka sai ta A/C. Ta na ta wurga ido ko zata ga Fulani, amma ko motsin ta bata ji ba, ta san kuma bata isa ta shigar mata daki ba bisa umarni ba. Duk ta ji ba dadi da abinda bacin rai ya kwashe ta ta gaya mata jiya. Ta san a matsayin ta na uwa, ko me zata yi mata bata cancanci wadannan kalaman daga gare ta ba.
Kawai sai ta kama kuka. Jikin ta a sanyaye ta bi bayan Fanna suka fita daga shiyyar Fulani, kuyangin Fulani na ta kallon ta don su har sun manta tana cikin gidan. Da yake safiya ce basu hadu da mutane sosai a hanya ba sai bayi jefi-jefi amma matan gidan da 'ya'yan su ko jikokin su babu ko daya, kowa yana sashen sa.
Har suka shiga dalleliyar motar da direba da dogarai biyu ke ciki, daya na

1 Comments On MASARAUTAR MU
avatar
zainabaliyu

1 year ago

Reply

I really appreciate masarautar mu, thank you

Please Login or Register in order to submit comment