Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

tuki, daya na gefen sa. Sa'ade bata bar kuka ba. A jikin motar an rubuta da ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE". Gefen hagu dogarawa suka bude mata ta shiga, kafin su rufe kofar ta kamo hannun Fanna, idanunta narai-narai da hawaye tace.
"ki ce ma Fulani don Allah don Annabi ta yi hakuri".
Fanna bata san akan me ake aiken ta bada hakurin ba, ta dai lura akwai wani babban al'amari tsakanin uwargijiyarta da wannan bakauyiyar yarinyar. An raineta ne kawai a bisa bin umarni, babu tambaya, don haka tace "insha Allahu zan gayawa Fulani sakon ki".
Fanna na barin wajen ba da jimawa ba Sa'ade ta hango wata kyakkyawar budurwa na tahowa karkashin rakiyar bayi 'yammata tsararrakin ta, tafiyar ta kawai data banbanta da tasu ya sa ta gane itace Humaira da Alanguburo yace zasu tafi tare wato 'yar autar sarki. Duk da kayan makaranta ne a jikin ta irin wadanda ke jikin ta amma an dora farar alkyabba wadda ta sha aiki da zare ruwan gold mai matukar walwali akai.
Tun kafin ta karaso dogarawan nan suka bude kofar da azama suna yi mata kirari irin wanda 'ya'yan gidan kawai ake yi wa. Ta shiga barin dama, yayin da Sa'ade ke barin hagu. Da ta zo bakin motar sai kuyangar dake bayanta ta zare mata alkyabbar ta shiga daga ita sai kayan makaranta. Daga haka aka ja sullubebiyar motar a hankali suka soma tafiya, kuyangin nata basu bar wajen ba har motar su Sa'ade ta hau kwalta.
Tunda suka mika hanya sosai yarinyar take ma Sa'ade kallo na kurilla, ita kuwa tun gaisuwar farko data yi mata bata kara ce mata komai ba. Ta maida hankalin ta ga kallon hanya suna wuce bishiyu da dazuzzuka kamar walkiya. Sanda suka cimma garin Chibok ta ce da Sa'ade cikin ginshira.
"Me ye hadin ki da Fulani?"
Sa'ade ta tuna gargadin Fulani don haka nan da nan tace "ni 'yar kanwar ta ce, mahaifiyata ta mutu". Gimbiya Humaira ta yi mata kallon shakka don ita dai bata taba ganin irin wannan kamar ta kwabo da kwabo ba irin wadda ke tsakanin Fulani Bilkisu da yarinyar da ke gefen ta. Kamar kamannin sun zarta na matsayin data ambata din na kasancewar ta 'yar kanwa a gareta. To amma wace hujja gareta na karyatawa? Tunda ta san bata haifi 'yar a gidan su ba?
Sai ta dauke kai itama ta koma kallon gefen titi. A ranta tana fadin ita sam bazata yi mu'amala da 'yar kalen dangi ba mai maganar kauyawa.
****











EL-KANEMI COLLEGE OF ISLAMIC
THEOLOGY
Makarantar kwalejin kimiyya ce ta addinin muslunci wadda Larabawan Yemen dana Sudan suka bude a Maiduguri da hadin gwiwar manyan masu kudin jihar Borno. Itace makarantar da sarki Yusufu ke kai 'ya'yan sa maza da mata, tun daga kan babbar 'yar sa (Ya Maira) sunan sarautar ta kenan a matsayin ta na babbar 'ya, har zuwa kan auta Humairah.
A tsarin makarantar daga Lahadi zuwa Alhamis sune renakun karatu, Juma'ah da Asabar renakun hutu.
Malamin maths na fita na Qur'an na shiga, na English na fita na Nahawu ko Fiqh zai shiga, na chemistry na fita na Adab ko Tarikh ko Mutala'a zai shiga haka dai tsarin karantarwar su yake. Wato kimiyya cakude da ilmin addini tsantsa.
Sannan ana gama lessons karfe uku ake fara Islamiyya ga mai son haddan Qur'an zalla ake yi har zuwa biyar na yamma.
Malaman makarantar kuma yawanci larabawan Sudan da Yemen ne, sai kuma Yarabawa
Maza da mata basa haduwa sam, dan katanga ce makekiya a tsakanin su sannan kowane bangare da gate din shi.

Tunda aka kai Sa'ade da Humairah dormitory dalibai 'yan uwan su ke kallon su, ba don komai ba sai don irin tsadaddun kayan abincin da ake shigo dasu katan-katan ana loda musu a lokokin su, a karshe lokokin nasu ma sun yi kadan su kwashe kayan, sai Humaira ta ce da metron da masu jerawar su je da sauran ta bar musu. Ko kallon Sa'ade bata yi kada a ce tare suke, amma kayan abincin su ba banbanci haka takalmi da jakar makarantar su, wanda ya tabbatarwa 'yan dakin cewa tare suke din.
Gadon Humaira na gefen na Sa'ade, don haka ta yi amfani da wannan damar ta maida ita baiwar ta, komai tana daga kwance take sa ta ta yi mata, dauko wannan miko wancan, ko kofi zata yi amfani da shi sai ta sa Sa'ade ta wanke mata shi, kuma da yake Sa'aden ta iya kitso ita ke yi mata duk sati, basa yin wanki iyayensu ke biya a wanke musu shiyasa Sa'ade ta samu sauki, da har wanki da guga ita zata ce ta yi mata.
Girman kai irin na Humaira ya hanata alaqa da mutanen dakin, ita kadai take rayuwar ta ko a class don bata ga wanda ya isa tayi mu'amala da shi ba duk da cewa duk 'ya'yan masu kudi ne a makarantar amma a wurin Humaira in ba ka da jinin sarauta cikin jikin ka to baka isa mutum ba. Kuma duk makarantar ita kadai ce 'yar Sarki.
Sabanin Sa'ade wadda ta maida kanta abokiyar kowa a dakin nasu, in har bata hidimar Humaira to zaka sameta cikin jama'ar dakin suna hira da harkar arziki, ga ta da kyauta, haka take ta rabar da kayan abincin nata musamman ga wanda ta lura yana da bukata, cakuduwar ta da dalibai 'yan uwan ta wadanda suka fita experience da exposure ya sa ta fara samun wayewar kai. A aji kuwa duk ita ce koma baya a kowane darasi daga na boko har na addini, amma bata barin hakan ya kashe mata gwiwa, ya cire mata hope na cewa da sannu zata iya idan ta sanya jajircewa da bada himma.
Haka monitar ajin nasu Raheema Kyari ke yawan gaya mata, wadda tasu ta zo daya, sakamakon yawan tambayar ta abubuwa da Sa'ade ke yi idan bata gane ba ba tareda nuna jin kunya ko girman kai ba. Ba ajin su daya da Humairah ba ita 'yar JSS 3 ce yayin da Sa'ade ke JS 1. Don haka tafi jin dadin rayuwa a class fiye da a dormitory (dakin barcin dalibai) sabida babu Humaira mai takura mata, a nitse take karatun ta tare da likewa monita Raheema tana daukar ilmi daga wajen ta.
Malaman ko sun so yin korafi akan rashin kokarin Sa'ade sai su fahimci abin nata daga tushe ne wato bata samu foundation a makaranta mai kyau ba kamar sauran daliban makarantar, don in sun tambayeta wace makaranta tayi tana gaya musu a kauyen Tsanyawa ne, makarantar da maigari yasa aka bude, don a koyawa yara A BA CA DA sai su daga mata kafa musamman in suka lura da yadda take da kishin abun a zuciyarta, in aka koya abu bata gane ba har kuka take yi. Duk kokarin Raheemah na koyar da ita ba komai take ganewa din ba musamman darasin lissafi, da yawa a makarantar sun dauka Sa'ade baiwar Humairah ce, irin 'ya'yan bayi da ake hado 'ya'yan sarakai dasu su zo makaranta tare don su dinga hidimta musu, sabida haka Humairan ke nunawa.
Sannu-sannu bata hana zuwa, saidai a dade ba'a je ba, a hankali Kwakwalwar Sa'ade ta soma budewa, musamman a haddar Al'qurani da Ingilishi. Raheema ta taka rawar gani akan hakan don fisabilillah take kaunar Sa'ade sabida saukin kanta, baban Raheema babban dan kasuwa ne a jihar Maiduguri wanda sunan sa yayi fice akan sana'arsa ta fata.
Watarana Raheema ta kawo wa Sa'ade ziyara dakin su, sai ta same ta durkushe gaban Humaira ta sunkuyar da kai tana hawaye, Humairan na ta zazzzaga mata fada har tana fadin dama 'yan kalen dangi basu iya cin arziki ba, banda haka tun safe ta sa ta gyaran sittirunta amma tasa kafa ta fice yawon neman suna bata gyara mata ba, su ko Fulani Bilkisu ba wata tsiya bace a wurin su tunda sun san asalin ta balle su ya-ku-bayin data kawo musu gida suna cinye arzikin Babansu.
Ba fadan data ke mata ne yasa ta kuka ba, domin in da sabo ta saba, ambaton sunan Fulani data yi ta zaga ne ya tsaya mata a zucci. Ya kona mata zuciya. Fulanin da has never been nice to her in any way amma zuciyar ta na mata wani irin so, da bata taba jin sa akan kowa ba including Baban ta.
Rahima ta kama hannun ta ta cira ta tsaye suka bar dakin, Humaira ta sakar musu tsaki tana fadin "ya'yan mutsiyata, gayyar tsiya".
Can bayan dormitory suka zaga suka zauna akan duwarwatsun da ke wajen, Raheema ta ce "wai don Allah Humaira ke baiwar ta ce? Ko iyayen ki bayi ne a gidan su?" Bata san me yasa ta yarda da Raheema ba, tun sanda ta fahimci Raheemar na tausaya mata tsakani da Allah. Ta girgiza kai tare da share hawayen idon ta "ni ba baiwar ta bace, ana riko na ne a gidan su, kishiyar mamanta ce yar mahaifiyata a hannun ta nake".
Raheema tace "tabdi! Amma shine kike mata bauta tana miki wannan wulakancin? Ke ba baiwar ta ba iyayenki ba bayin su ba? To wallahi ki kama kan ki, ki nuna mata zaman kan ki ke yi ba zaman ta ba in ba haka ba watarana sai ta kai ga taba lafiyar jikin ki" da sauri Sa'ade ta girgiza kai.
"Zan yi mata komai saboda Baban ta!".
Raheema ta rasa abinda zata ce, sabida a amon muryar ta kadai ta fahimci akwai wani girmamawa da kauna na musamman data ke yi wa Baban Humaira, abinda ta fada har zuciyar ta ya ke. Wannan ya tabbatar mata Sa'adatu irin mutanen nan ne da basa manta alkhairin da wani yayi musu komai kankantar sa.
****
An yi jarrabawar karshen zango, as expected Sa'ade ta dauko na biyun karshe, ta yi kuka har ta gode Allah, amma a islamiyya ta yi dan kokari ba laifi musamman a hadda.
Damuwar ta yadda zata dauki wannan mummunan sakamako ta kaiwa Alanguburo, bayan ta yi masa alkawarin yin kokari iyakar iyawar ta.
Raheema ta ce ta bata lambar wayar wani a gidan su zata kira ta in ta koma gida, Sa'ade tace banda Fulani babu mai waya a sassan su, ita kuma bata san lambar ta ba, ko ta sani bazata yi karambanin bayarwa ba Fulani ta tsinke mata kunne haka kawai.
A daren ta hada musu kayan su da zasu tafi dasu gida a kananan trollies din su, sauran kayan abincin da suka rage Humaira tace ta fitar duka ta kaiwa metrons.
Ta yi sallama da 'yan dakin su cike da kewa suna fadi a ransu ai gara ta je gida ta huta da wannan bautar data sha ta gimbiya Humaira, wasu kuma suka ce a ran su watakila har a gidan ma irin bautar data ke mata kenan.
Kusan su ne na farko da aka zo dauka a washegari. Suna tsaye ita da Raheema a jikin bishiya suna hira, Humaira na daga zaune a gefe akan jijiyar bishiya tana ta harare-harare irin wanda ta saba da kallon kowa a wulakance. Zungureriyar mota kirar 4matic baka wuluk ta yi parking a gefe, da rubutu baro-baro cikin ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE".
"Ma'assalam Raheema, an zo daukar mu"
Ta fada tana jan trollies din biyu dake gaban ta, nata da na Humairah, Raheemah ta daga ido tana kallon inda ta nufa, tun kafin ta karasa dogarawa biyu suka yi wuf suka fito daga motar suka karbi kayan hannun ta. Ta karanta rubutun ta sake karantawa "ASKIRA EMIRATE" Ashe daga masarautar Askira suke, no wonder Humairah take mulkin data ga dama. Baban ta ya sha basu labarin masarautar Askira da irin dimbin arzikin ta da shaharar ta a yankin Borno.
Ta karasa da gudu ta cimma Sa'ade, ta rike hanayen ta, tana murmushi ta ce "ki gaida mun Fulani, i will give you a giant surprise insha Allah" Sa'ade ta yi dariya ta ce "Fulani zata ji, ki gaida Mama dasu Sarina (kannen ta)".
Raheema na juyawa ta kusa karo da Humairah, da sauri ta bata hanya sabida mugun kallon data sakar mata. Ta shiga gefen dama data saba zama dogarin ya rufe kofar. Ya zaga mazaunin sa ya zauna suka ja motar zuwa get, inda suka cike takardun daukar dalibai sannan aka basu dama suka wuce daga get din makarantar.
Tun daga kofar gida kuyangin Humaira na tsaye suna jiran isowar ta. Cikin rakiyar su suka wuce cikin gida kowacce ta doshi bangaren su. Fanna ta fara cin karo da a bakin kofar shiga unguwar Fulani Bilkisu da alama jiran karasowar ta take, tana mata murmushi tace
"sannu da zuwa 'yar gida na, yaya hanya kuma yaya karatu?"
Tare da karbar jakar kayan ta wadda Humaira ta hana kuyangin ta su daukar mata.
Suka wuce zuwa ciki, tsakanin ta da sauran bayin Fulani sai ido, don ba'a basu damar alaqa da juna ba, only Fanna. Ta kaita har dakin ta, ta hada mata ruwan wanka a bathtube sannan ta fita don ta kawo mata abinci.
Sa'ade tayi wanka ta ji dadin jikin ta, ta sauya kayan makaranta zuwa doguwar rigar atamfa exclusive mai hasken sararin samaniya, sosai tayi kyau, farar fatar ta ta yi tas, wanka da tsafta sun kama jikin ta, ita kanta data tsaya a jikin mudubin dogon yaro ta kalli kanta sai da ta razana, don gani tayi kuruciya kadai ce zai sa ta kasa cewa Fulani Bilkisu ce a cikin mudubin. Ta ga ta kara tsayi, hancin ta da idon ta sun kara fitowa dara-dara, tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta.
Sai data ci abinci ta koshi tayi sallar data kufce mata sannan ta hau gado sai barci.
Cikin barcin ta ji an dala mata duka a cinya, ta zabura ta mike zaune, Fulani ce tsaye a kanta ta ci gayu kamar mai shirin gasar sarauniyar kyau.
"Wa ya ce da ke ana barci bayan la'asar? Kidahuma kawai".
Ta zumburo baki tana mutstsikar ido. "Amma ko sannu da zuwa baki mun ba kin rufe ni da fada, don Allah Fulani me na yi miki ba kya so na?" Ta saki kuka har da na shagwabar ganin uwa, ba wai na zafin fadan da ta yi matan ba. She just felt relaxed by seeing her......after missing her for over ninety days. Fulani ta saki baki tana kallon ta don bata ga abun kuka ba don kawai tace ta daina barci bayan La'asar. Tsaki tayi tace "ba'a son naki, an ki a so ki din, ubanki ya ja miki, banda alfarmar Askirama wallahi bazaki zauna mun a gida ba, Damaturu zan kai ki". Sa'ade ta ida rushewa da kuka, it's painful uwar data haife ka ta bude baki tace bata son ka sabida mahaifin ka komai kazantar laifin uban naka ai mutuwa ma na kunyar idon Da.
Balle in ta tuna Uban nata da akewa kiyayyar ba ya duniyar ma. Ita Fulani wace irin zuciya gareta?
"Duk talaucin sa dai bazaki kankare cewa shi kika fara aure ba, tun da ga ni.....", sai bayan ta furta kalaman wadanda a zahiri a zuciyar ta tayi niyyar fadar su, ta yi maza ta toshe bakin ta da ta fahimci sun fito fili, amma ina! Already Bilkisu ta ji su.
Har ta kai bakin kofa gabadaya ta juyo, ta kankance idanu ta kai mata wani wawan mari, Sa'ade ta kauce amma saida ta samu bayan kunnen ta, dan kunnen ta ya fice ya karce gefen kunnen ta sosai jini ya kwanta a wurin tare da yatsun Fulani Bilkisu.
"Wannan ya zamo rana ta karshe da zan kara yin magana ki maida mun, mara kunyar banza! Mai mugun hali irin na uban ta!"
Sa'ade na kuka wurjanjan Fulani ta bude kofar dakin ta fice.
Tana zuwa falon ta ja ta yi turus! Ganin Askirama a zaune yana jiran fitowar ta.
Ya sauke nagartattun idanun sa akanta, ma'abotan kamala da ilhama, a hankali ya ce.
"Koma ki kirawo min ita, na jiyo kukan ta".
Bata da damar yin musu, haka ta koma jiki a sanyaye tace daga bakin kofa.
"Ki zo Askirama na kiran ki".
Without giving her a second look ta fice ta bar dakin.
Sa'ade saida taje toilet ta wanke idon ta don dai ta boyewa Alanguburo cewa kuka take, amma tana fitowa ta zauna a gaban sa idon sa bai sauka a ko'ina ba sai a bayan kunnen ta.
Ya kamo fuskar Sa'ade ya kalli ciwon sosai, yace "Sa'adatu ki yi hakuri kin ji? Ni na gaya miki watarana in wani daban yayi miki haka, sai inda karfin ta ya kare".
Sa'ade tayi murmushi duk da idanun ta sun kumbura, a ranta tana tantamar zuwan wannan ranar. Yau ta yarda da gaske Fulani ke kin Baban ta wanda shine mujazar nata kiyayyar. Amma bata ga laifin ta ba, laifin kanta ta gani, da ta ke kasa tankwara zuciyar ta ta mayar mata da magana. Wanda ko kusa bata cancanci hakan daga gareta ba.
"Alanguburo ka taya ni bata hakuri don Allah, ni na bata mata rai".
Ya yi murmushi ya ce "babu komai ta hakura, amma nan gaba ko me zata yi miki kada ki ji haushin ta, sannan kada ki tanka mata. Uwa ta wuce duk inda kike tsammani. Matsayin ta da darajar ta daban yake dana kowa a wajen ubangiji. Sai da Ya ce abi ta.....a bi ta.....a bita... sau uku kafin ya ce abi Uba. Ina fata kin fahimce ni?"
Hawayen nadama na zuba a idanun ta ta gyada masa kai, ta dago ta dubi Fulani da appealing look, amma sai Fulanin ta kauda kai idanun ta jazur, ko kusa bata yi nadamar ciwon data ji mata ba da jinin data fitar mata, ta ma so ya fi haka, tunda ita bata da kunya. Amma can a karkashin zuciyarta ta ji wani sashe daban ya darsa mata tausayin yarinyar. Sanin cewa bata da kowa da zata raba a rayuwar ta sai ita, amma duk kokarin ta ta kasa sanya ta a ranta. Watakila sai ranar da Sa'aden da kanta ta yarda cewa ba laifin ta bane duk abinda take yi mata akan baban nata. Ko kuma ranar da zuciyar ta ta gaji ta russuna ta karbi Sa'aden don kan ta.
"Je ki ki huta zan sa a kawo miki magani ki sha". In ji Alanguburo. Har ta mike sai kuma ta dawo gaban sa ta durkusa. "Ka yi hakuri Alan....ban cika alkawarin dana yi maka ba, ban yi kokari a makaranta ba, na yi duk iya kokarin da zan iya amma na kasa kamo kowa....a karshe nice ta biyun karshe".
Yana murmushi ya ce "to ai babu komai tunda kin kada mutum daya, a ta gaba na tabbata goma zaki kayar, a ta can gaba ashirin, a ta gabanta talatin, daga haka har ya zamo kece a saman kowa. Kada hakan ya karya miki gwiwa kin ji? Ba wanda aka haifa da iyawa, kowa a hankali yake zama gwani, je ki kwanta ki huta sosai kafin a kawo maganin, ko talbijin ban yarda ki kunna ba sai gobe".
Cikin jin dadi ta amsa tareda yi masa godiya, ta saci kallon Fulani ta ga harara kawai take zabga mata, ta wuce su zuwa daki kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Barcin da ya ce ta yi, ta so ta yi amma ta kasa, duk tunanin ta na yadda zata dinga yiwa Fulani biyayya ne, insha Allahu daga yau bazata sake bata mata rai da gangan ba.
*****
"Me ya kai ki? Me ya kai ki dora hannu a jikin marainiyar Allah Bilkisu? In da ya zo da tsautsayi kin kurunta ta fa? Wallahi bar ganin ke kika haife ta, akwai hisabi tsakanin 'ya'ya da iyayen su".
"Ku yi hakuri Askirama!".
Abinda ta iya furtawa kawai kenan, ya mike cikin bacin rai mai tsanani ya ce "ni kam ba abinda kika yimin sai kyautatawa, balle ki bani hakuri, tunatarwa ce kawai nake miki domin tana amfanar da muminai. Amma tunatarwar da kullum sai an maimaita maka ita, ban ga amfanin ta ba. Daga yau bazan kara yi miki magana akan 'yar ki ba, na tabbata kin fi ni son ta. Saidai bana bayan zulunci, ni shugaba ne mai adalci wanda Allah ya damkawa amanar duk wani talaka da ke cikin garin Askira babba da yaro, balle wanda ke cikin gida na karkashin iyali na don haka bazan lamunci duka ba, in kin so ko dakin ta ki daina shiga wannan ya rage naki, amma duk ranar da kika sake kai hannu a jikin ta zaki ga bacin rai na Bilkisu".
Ta tabbatar yau ta kure hakurin mai Askira, dole ta kwantar da kai tayi ta bada hakuri. Tsakanin mace da miji sai Allah balle Bilkisu da Sarki Yusufu mai Askira. Soyayyar su wata ajiya ce daga Allah. Wadda babu irin ta a wannan zamanin, soyayyar mazan jiya masu dattako da sanin yakamata.
Fanna ta kawo mata magani ta sha, arashin sanin ta har da maganin barci a ciki. Haka tayi ta barci kuma Fanna bata tashe ta ba saida lokacin sallah yayi.
****
Kwanansu bakwai da dawowa hutu, Sarki Yusufu da Fulani Bilkisu da Fulani Hibbani suka tashi zuwa kasa mai tsarki domin gabatar da aikin Hajji na wannan shekarar kamar yadda suka saba duk shekara, yana daukan mata biyu ne cikin matan sa su tafi da kwarkwarori biyu. Harkokin gidan suka cigaba da gudana kamar yadda suke gudana in sarki baya gari karkashin kulawar Wazirin gari Ibrahim.
Kadaici ya kara yi wa Sa'ade sallama, bata ganin kowa sai Fanna, bata zuwa koina daga dakin ta sai falon Fulani na karshe wanda babu mai shigar shi in ka dauke Fanna. Ta kagu a koma makaranta ko ta hadu da Raheemar ta su yi ta karatun su ya fiye mata wannan jin dadin mara 'yanci. Domin kafin Fulani ta tafi ta ja kunnen ta sosai akan kowa na gidan koda kuwa bayi ne, bata yarda ko magana ta hada ta da kowa ba sannan bata yarda ko kofar unguwar ta ta fita ba. Ko me take so ta gayawa Fanna zata yi mata.
Satin su Fulani biyu a kasa mai tsarki, rannan da Fanna ta kawo mata abincin rana ta hado mata da wata wasika da aka rubuta da fensir, tace "sakon ki ne daga kawar ki".
Tun kafin ta bude takardar ta gane rubutun Raheema wadda ta rubuta sunanta a bayan takardar. Raheema Kyari. Jikin ta har rawa yake wajen warware takardar. Ga abinda Rahima ta rubuta.
"Hi Sa'adatu,
Ni ce Raheema, na zo tun daga Maiduguri as i promised to surprised you, an hana ni ganin ki, don an ce ba'a bada umarnin ki ga kowa ba, sannan Fulani bata gari balle a nemi izninta.
Ina fatan ba za kiyi ta kallon talbijin ba, zaki yi ta bitar littatafanki ne kina koyar da kanki kafin mu koma hutu, na so in kwana uku tare da ke don muyi karatu sosai in koya miki mathematics, Allah bai yi ba, musamman Abba ya bada mota aka kawo ni, dana gaya masa masarautar Askira ne bai hana ba. Na so mu hadu, na so in ga Fulani, na so in gan ki, but some other time insha Allah. Mama da Sarina suna gaishe ki.
Yours sincerily,
Raheemah Kyari.

Har hawaye ta yi na bakin cikin rashin ganin Raheema, ta yarda Raheema mai son ta ce, mai kaunar ta ce. Tunda har ta iya biyo ta tun daga Maiduguri har Askira. A karshe ta dauki shawarwarin Raheema, ta daina kunna talbijin, ta mayar da littafanta da darussanta na baya ababen debe mata kewa kuma abokan hirar ta. Sosai take tsintar abubuwa masu muhimmanci, sannan ta dinga tisa haddar ta, Fanna ta kawo mata 'yar radio tana sauraren karatun Abdurrahman Sudaith a ciki. Cikin haka har Allah yayi wa Fulani da maimartaba dawowa daga aikin hajji ana saura kwana biyu su koma makaranta.
Suna dawowa shirin komawar su aka fara, aka yo musu provision har fiye dana wancan hutun, babu wanda Fulani bata yiwa tsaraba ba cikin unguwarta (sassan ta). Banda Sa'ade. Ko tsinke bata sayo mata ba.
Ita Sa'ade bata san ma an yi rabon tsarabar ba tunda tana cikin daki kullum, ta dai daidaici sanda Fulani take zaman falo ita kadai ta je ta yi mata sannu da zuwa. Tare da tambayar ta "an dawo lafiya?"
"Lafiya kalau, alhamdulillahi"
Kawai ta ce, ba tare da ta tambayeta komai ba, kamar lafiyar ta ko yadda ta sameta,
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On MASARAUTAR MU
avatar
zainabaliyu

8 months ago

Reply

I really appreciate masarautar mu, thank you

Please Login or Register in order to submit comment