Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kira Yareema gefe ta ce tunda jikin da sauki, kuma an ce gashi ya rage za a dinga yi mata, ko zai nema musu sallama su koma gida? Sai a yi hiring professional din da za ta dinga yi mata gashin a gida?
Sun yi yawa a asibiti, kuma ba wanda zai yarda a ce ya koma gida. Don wani hotel suka kama a nan kusa da asibitin mazansu da matansu.
Yareema ya amince da shawarar Yaa Maira, ya nema musu sallama a washegari. Daga asibitin koyarwa na Maiduguri aka dauko physiotherapist din da za ta dinga kula da Ya Gumsu a gida ana biyanta.
Yareema bai samu nutsuwa ba tun saukarsa Abuja, don haka bai kira Fulani Bilkisu ba. Amma ko me yake yi Saadatu na manne cikin ransa. Minti bayan minti, sakan bayan sakan son Saadatu karuwa yake a zuciyarsa. Tamkar nisa da suka yi da juna wani medium ne na linking zuciyoyinsu wuri guda.
Haka kuma yake ga Saade, wadda ke can tana fama da kanta, amma kullum hankalinta yana kan mijinta Yareema Sageer. Ko yana cin abinci? Ko yana cikin irin damuwar da ta ke ciki? Ko shi ma Ya Gumsu ta mare shi a kan ta? Tambayoyin da ta ke yawan yi wa kanta ke nan ba ta da mai amsa mata. Domin Fulani ta lafiyarta ta ke ba ta mata zancen Yarima sam-sam.
Sun dukufa ita da Fanna wajen kula da ita da dafa mata duk abin da suka san za ta iya ci ko da loma daya za ta yi masa.
Dr. Zainab ma na kokari a kanta matuka, ta taimaka aman ya tsaya, amma kullum cikin tashin zuciya ta ke, don haka Fanna ta samo mata goro tana taunawa.
Ta rame ta yi duhu, da ganinta za ka san a satin nan ta yi jinya ta sosai. Tana kwance a dakinta suna labari da Zarah Fulani ta shigo ta same su. Ta ce,
Saade su Yareema sun dawo fa, an sallamo Ya Gumsu, don haka ki daure, ki kwarara jikinki yanzun nan ki je ki duba ta, ko da kuwa ba za ta amsa ba.
Saadatu ta fiddo ido cikin razana, Fulani ta lumshe mata ido tare da girgiza mata kai, ta ce,
Do as I said, sai Fanna ta raka ki.
A sanyaye ta mike ta soma daura laffaya a jikinta.
Fanna ce ta yi mata jagora suka tafi unguwar Ya Gumsu. Wata kuyangarta ta shiga ta yi musu iso, sannan ta fito ta shiga da su har tankareren falon da Ya Gumsu ta ke kwance. Gabadaya yayanta maza da mata suna zaune a falon tun daga kan Yaa Maira har zuwa auta Ahmad.

Yareema Sageer na zaune a gefen Ya Maira daga kan tattausan kilishi, ya mike santala-santalan kafafunsa da waya a hannunsa yana latsawa. Sanye yake da alkyabba ruwan zuma wadda ta sha aiki da zare ruwan gwal. Duk hirarrakin da suke yi ba ya sanya musu baki domin gabadaya hankalinsa yana ga son ganin Saadatu, da sabon matsayin da zai kalle ta da shi na mother of his children.
Lokacin da wata baiwa ta shigo ta isar da sakon cewa ga matar Yarima nan za ta shigo duba Ya Gumsu ko kadan bai ji su ba. Text messages yake rubutawa yana aikawa wayar Saade mai dauke da alkawurruka na soyayya da kauna masu wuyar samuwa daga bakin mazan aure a wannan zamanin. Duk da ya san cewa ba ta tare da wayar tata ta baro ta Abuja.
Kamar cikin mafarki, kamar daga sama ya tsinkayi sassanyar muryar Saaden na sallama a falon. Ya riga kowa dagowa a rikice, a mamakance, sannan excitedly yake dubanta. Da shi ta fara hada ido, ta yi saurin sunkuyar da kanta. Idanuwan yayye da kannen Yareema suka yi mata caaa wanda hakan ya sa kafafunta hardewa kamar za ta fadi. Kafin Fanna ta riko ta Yareema ya riga ta. Babu wanda ya ga sanda ya mike cikin zafin nama ya taro Saade, ya ruko ta har gaban Ya Gumsu, ya zaunar da ita daidai kafafunta yana fadin,
Ya Gumsu ga Saadatu ta zo duba ki!.
Kunya a wurin Saade kamar ta ce kasar ta tsage ta shige. Amma da yake dukkaninsu wayayyu ne ko a jikinsu, murmushin kauna suke mata dukkansu.
Yaa Maira ta ce, Barta ta zo nan kusa da ni ta zauna Yarima, dawo nan gefe na Saadatu.
Cikin jin nauyi ta zame daga hannun Yarima ta tsugunna har kasa ta ce, Ya Gumsu sannu da jiki, Allah ya kara afuwa.
Ya Gumsu ta daga mata kai alamar ta amsa, sannan ta rike hannunta cikin nata. Tana ta motsin maganarta wanda da alama so ta ke ta bai wa Saade hakuri.
Saade ta girgiza mata kai tana hawaye, Allah ya ba ki lafiya Ya Gumsu, da yardar Allah za ki fadi duk abin da ki ke son fada. Mun yi laifi a yafe mana.
Sai kuka, Yaa Maira ta zo ta kamata ta tayar da ita daga gaban Ya Gumsu, ta ja ta suka zauna tare, ta ce, Ba ki mata laifin komai ba Saadatu kin ji, kuma ta yafe muku duniya da lahira, Allah ya yi muku albarka.

Kowannensu da kalar kulawar da yake nuna mata a falon, duk suka yi mata sannu da jiki.
Awaisu ya yi sallama ya shigo, ya duba Ya Gumsu da jiki sannan ya dubi Yareema da ke gefe kusa da Yaa Maira yana hagunta Saade na damanta (babbar Ya, UWA). Tana ta tsokanar su;
Princess Saa Allah ya sa ki haifo min mai kama da ni ba mai irin hancin Yareema ba (pointed noise), kin san in hanci ya cika tsayi muni yake komawa.
Ahmad ya ce, Kai Yaa Maira! A dinga yi ana tsoron Allah, ko makaho ya shafa ya san Yaya Yareema ya fi ki kyau nesa ba kusa ba.
Awaisu ya katse hirar tasu da cewa, Yareema bakinka na Neitherland sun iso airport din Maiduguri, zan je in taho da su. Gidanka zan sauke su ko guest house din Maimartaba?
Yareema ya harare shi, ya ce, Awaisu! Kana shiga lokacina fa, this is family time, ka je ka ji da customers dinka kai kadai. Duk inda ka ga ya dace, ka kai su.
Family ba za su ji dadi ba sai da kudi. A nemi kudi a bai wa family Malam, ina zan sauke su?
Gabadaya aka yi dariya ban da Yareema da Saade wadda ke satar kallon Yareema ta kasan idonta, tana mai alhinin muguwar ramar da ya yi cikin sati guda kacal. Duk da haka kyawunsa da kwarjininsa suna nan, sai ma abin da ya karu.
Sai lokacin Awaisu ya lura da Saade a falon tana daga gefen Yaa Maira, ya ce,
Aah! Madame, are you here? Dole idanun Yareema su rufe, ga masoyiya a kusa me zaa yi da kudi? Don Allah ki yi masa magana ya gaya min inda zan kai bakin turawanshi.
Saade ta yi dan murmushi ba ta ce komai ba, sai ma kara kasa da ta yi da kanta, gabadaya ta takura domin duk motsin da ta yi sai ta ji kaifafan idanun Yareema a kanta. Maganar Turawa da Awaisu ya yi ita ta sa Yaa Maira tunawa da Aisha-Sultana.
Da sauri ta ce, Yareema, ina Sultana? Ban ganta ta zo duba Ya Gumsu a Abuja ba?
Ai kuwa duk suka tattaro hankalinsu a kanshi, sai yanzu duk suka tuna ba su ganta din ba, including Saade ta dau ido ta dora masa, ita dai ta san sun yi tafiya tare, kuma ya dawo shi kadai bai kara yin zancenta ba.
Yareema ya dubi Yayar sa Yaa Maira sannan sauran kannensa maza da mata, sannan matar sa Saadatu da aminin sa Awaisu, ya ce,
Dukkanku ba bare a nan. Ba wanda zan boye wa sirrin gidana, muddin wanda ya dace ku ji ne. Aisha-Sultana (Rose) mun rabu. Na maida ita kasarsu.
Gabadaya suka sa salati domin babban zunubi ne saki a masarautar, tun daga iyaye da kakanni.
A kan wane dalili? Askirama ya sani? In ji Yaa Maira.
Yareema ya yi ajiyar zuciya, calmly ya shiga ba su labarin halin da yake ciki da Sultana tun komawarsu Abuja da ta sarki shan giya ta kuma cire mahaifa ba da izininsa ba. Ya ce,
Na yi ta hakuri ne da shan giyarta saboda nobody is perfect. Dukkanmu masu sabo ne in one way or the other. Sabida ni ma kaina din Im not perfect either. Amma sallah fa? Ba zan iya jure rayuwar aure da wadda ba ta sallah ba, sabida yayana da lahira ta.
Ya ci gaba da gaya musu yadda Askirama da kansa ya zo har gidansu ya same ta drunkard, ya ce,
bai ce in sake ta ba, amma bacin ran da na gani cikin idanunsa da gaisuwata da ya daina amsawa ya sa na ga duk son da nake mata gara in hakura da ita. (Ya boye musu abu guda daya, cewa ba zai iya adalci tsakanin kowacce mace da Saadatu ba, don ya sirranta soyayyar da yake wa matarsa ga yan uwansa, wanda hakan shi ya kamata ga duk namijin da ya san ciwon kansa).
Yaa Maira ta fahimce shi, amma sai ta ce, Wani hanzari ba gudu ba, Sultana ba ta ce ta yi RIDDA ba, sakin da ka yi mata saboda shan giyarta zai sa ta kullaci musulmi, ta ga cewa, tukuicin soyayyarta gare ka kenan, ta baro kowa nata da addininta ta biyo ka a karshe ga abin da ka saka mata da shi.
Ban sake ta saboda giya kadai ba. Na gaya miki ta karbi musulunci, amma ba ta sallah, mene ne marabarta da addininta na baya? Addinin ma da babu shi sam domin kuwa ba kirista ba ce, bayahudiyya ce (Jew). To cut it short, na yi nadamar aurenta tun farko, ban taba zaton Alanguburo zai amince ba, amma tashi guda ina fada bai turza ba, sai ya amince.
Had I know akwai Saade, kamar yadda ya ce tun farko ita ya so na aura ba zan taba yin wani aure ba.
Saade ba ta san lokacin da ta mike ta yi kofar fita ba, inda ta baro Fanna, kunya kamar ta yi ya ya. Tana ji Yaa Maira na fadin, Ka kore ta ka ji dadi. Saadatu dawo kin ji, yanzu zan sa Awaisu ya tattara shi su tai su ba mu wuri.
Ina! Saade ta kai kofa. Cewa ta ke, Yaa Maira zan dawo ne, idan na kara jin sauki.
Yareema ya daga murya yadda za ta jiyo shi ya ce,
In zo zance anjima bayan isha?
Ai saade kadan ya rage ta zura da gudu, suka dinga yi mata dariya.

Tana komawa unguwar su ta tadda Fulani ta dafa mata lafiyayyen faten acca da ya ji ganyen alayyahu da kabewa, ta zuba a faranti tana firfitawa da kanta tana jiran shigowarsu. Tana shigowa ta nufe ta da sauri.
Allah Sarki UWA! Saade ta fada a ranta, ta karbi cokali tana shan faten Fulani na tambayarta jikin Ya Gumsu, ta ce, ita ma tana jira Askirama ya shigo gida ne su shiga tare su dubo ta.
Saade ta tambayi Fulani, Ya ya aka kare ne da zancen auren Hanne?
Ta ce, An kai zancen kotun musulunci an yi mata gaiba, mun rabu a kan cikin watannin in ta gama iddah za ta dawo nan gabana, yaron a kai wa iyayen mijin. Plan dina akan ta shi ne a kai ta El-Kanemi, ta samu kwalin kammala sakandire sai a sama mata UNIMAID. Ta zauna hostel in sun yi hutu ta zo nan wajena ta yi hutun, har Allah ya ba ta mijin aure.
Saade ta gode wa Fulani, godiya maras adadi, tsarin da ta yi a kan rayuwar Hanne ya yi mata.
Ta ce, Su Raheema ko waya?
Ta ce, Kusan kullum muna magana da Maman, Raheema ta koma makaranta (university of Heartfordshire) wannan watan za ta kammala daga nan ku sha biki. Zan tambayi Maman lambarta na UK tunda yanzu akwai waya a hannunki.
Ta kyabe baki ta ce, Ni da na ji zafin maruka ina na tuna da wata waya?
(Tana nufin marin da su Ya Gumsu suka yi mata).
Fulani ta ce, Mari?
Nan ta gaya mata duk yadda aka yi, amma ba ta manta rokon da Yareema ya yi mata ba na ta boye zancen Dr. Ziyad ga iyayen su, it will create a serious problem idan suka ji, tunda dai mun bar NTNU din gabadaya shi ke nan. In ji yareema Sageer.
Sai dai tana tantama idan hukuncin da Yareema ya yanke musu is geniune, da gaske Abuja ta fice mata a ka, shi ma kuma Yareema haka, Dr. Ziyad yayi shattering zuciyar sa into pieces ya karya masa zuciya, ita kuma ya jefa tsoron rayuwar Abuja mai tsanani a tata zuciyar.
To amma makomar karatunta ta ke hangowa, shekaru ukun da ta kwashe cikin wahala da fadi-tashi sun tashi a banza ke nan? Above all aka ce sabo turken wawa. Ta saba da NTNU. Babu wata jamia da za ta bi bayan Nigerian Turkish Nile University a wurinta.
Fulani da ta ji duk abin da ya faru tsakanin Saade da su Ya Gumsu, sai ta jinjina kudirar Ubangiji. Ya Gumsu mai ja da ikon Allah dare daya yau gata ta zama sai dai a kwantar a tayar. Shin wannan bai ishi dan Adam ishara ba ya yarda cewa shi ba a bakin komai yake ba? Duk mulkinsa da izzarsa bai wuce talalar Ubangiji ba a duk lokacin da ya so? Bai isa ya sa, bai sa ya hana abinda Ubangiji ya hukunta ba?

Matar nan ta jima tana cutar da ita, da harshenta, da bakin ta, da hannunta, da komai nata. Don ma dai kowa ya tabbatar cewa ba ta yin asiri ta tabbata da in akwai abin da ya fi shi sai ya Gumsu ta yi mata. Wannan sai Hibbani, shi ya sa ita din ba ta wasa da addua da tsayuwa gaban Sarki Allah a tsakiyar kowanne talatainin dare.
Ta nisa ta dubi yarta Saade, ta ce, Saadatu marriage is not a bed of roses. Babu wani aure da ba shi da kalubale, ki sa a ranki Gumsu ita ce kalubalen aurenki, kuma ga yadda abubuwa ke tafiya na fahimci tsoron Allah ya kama ta. Ki cire ta a ran ki ki yi wa mijinki mai sonki biyayyah, komai za ta yi miki ta yi kadan ta raba wannan auren tunda har ga zuria a tsakani.
So ni da Ya Gumsu yanzu mun zama JINI DAYA. Kun riga kun yi tiding wannan barakar da ke a tsakani. Ni kuma ko me ta yi mun a baya na yafe mata. Allah ni ma ya yafe mini, ina kuma rokonsa ya ba ta lafiya ta koma taka kafafunta a doron kasa.
Kuma tunda kin warware ki soma shirin komawa dakinki tun kafin Yareema ya zubar da kawaici da kunyar da ke tsakanina da shi.
Dazu ya roke ni Fanna ta raka ki dakinsa na gidan nan yana son gaisawa da babynsa tunda Askirama ya hana shi shigowa nan. Ni kuma bazan yi abunda in Askirama ya ji zai yi fushi da ni ba.
Tunda har ya cire kunya ya fadi gaisawa da baby kin ga daga hakan wata rana abin da zai gaya min sai ya fi haka.
Saade ta soma tirjiya, har da buga kafa na shagwababbun yaya,
Ni wallahi ba yanzu zan koma ba, abin da jinyar Ya Gumsu suke yi? Ko na koma ba shi da lokacina.
Fulani ta ce, Duk inda yake in dare ya yi ai zai dawo gidansa ne Saadatu. Dare mahutar bawa, don haka na gaya miki ki soma shiri, ba za ki kara kwana uku a sassan nan ba. Yau din nan zan bai ma Askirama baki, har ga Allah Yareema tausayi yake bani don ba shi da laifi.
Saade har da hawayenta ita ba za ta koma yanzu ba sai Ya Gumsu ta warke.
Warkewar da babu wanda ya san ranarta sai Allah?
In ji Fulani cikin lallashi.

Kamar yadda ta alkawarta da yake yau ita ke da Mai Askira, tare suka je suka duba Ya Gumsu. Da lokacin kwanciyarsu ya yi ta yi ta ba shi hakuri kan ya sassauta wa Yareema, cikin alamarin nan ba ta ga laifinsa ba, tunda shi bai ma san Ya Gumsu za ta je Abuja ba, kuma sanda ta je din Saadatu ta tabbatar mata shi ba ya gidan, sannan abin da ya faru da Ya Gumsu kadai ishara ce babba, Allah ya nuna musu su dukkansu a daina jayayya, a bar wa Allah ikonsa.
Zuciyar Maimartaba ta tausasa, shi ya sa yake son Bilkisu amma matansa sai su ce wai kyawunta ne. Me ake da kyau in ba hali? Ai ga Hibbani nan kyau har kyau, amma ban da gulma, tsugudidi da daukar zance ba ta iya komai ba.
Ya ce ya yarda a je a gyara musu gidansu kafin su koma. Ya kuma kira Yareema don ya ji yaushe za su koma Abuja. Yareema bai boye ba, ya ce da Askirama ya ajiye aikinsa da NTNU, wani zai nema.
Cikin mamaki Mai Askira ya ce, A kan me?
Yareema ya runtse ido, tuno cewa Ziyad ya ga tsiraicin Saade kadai yana kona zuciyarsa yana tafasa ta ba dan kadan ba.
Ya ce, Allah ya kara maka yawan rai a taya mu addua Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare mu bakidaya. Zan yi mata transfer zuwa babban reshen jamiar tasu da ke Ankara (capital of Turkey) ta karasa shekara biyunta. Ni ma zan yi wasuprojects (applied research) da jamiar na tsawon shekara daya.
In mun gama sai mu dawo Askira da zama gabadaya, bazan kumazama a garin da ba Askira ba, ina so in bude jamia tawa ta kaina (private university) tunda ni da ita duka fanni daya muke karanta sai mu hadu mu tafiyar da jamiar. Kafin in samu lasisin budewar (licence) shi ne abu mai wahala,domin a nan Askira nake so in bude jamiar ba a maraya ba.
Askirama mutum ne mai ilmi kuma wayayye, sosai ya fahimce shi, yana alfahari da haihuwarsa a kullum. Da daya ne tamkar da goma wanda yake barranta kansa da sarauta when it comes to neman ilmi, duk ya fi yan uwansa maza talent da jajircewa a kan harkar ilmi. Ya yi addua ya sa musu albarka, ya ce, gobe insha Allah za su je Abuja su mika neman visa da neman tranfer din shi da Saade, in sun gama komai zuwa sati daya za su tashi zuwa Turkiya daga Abuja ba za su dawo Askira ba sai bayan shekara daya.
Askirama ya ce bai yarda ba, idan watan haihuwa ya kama wa zai kula da ita? Yareema ya yi alkawarin zai kula da Saadatu kamar yadda zai kula da kansa. In watan haihuwar ya kama zai daukar mata Fanna, in kuma ta kammala karatun kafin nan tunda semester biyu ne kawai zai dawo da ita ta haihu a gabansu.
All he need is to be isolated shi da Saadatunsa. Shi kadai ya san irin ragaitar da ya shiga a wadannan kwanakin da suka yi nesa da juna. Ba ya son hayaniyar gidan Sarauta ko kadan. Da kyar Maimartaba ya amince da wannan tsarin na Yareema, amma yana adduar ta gama karatun kafin watan haihuwar ta ya tsaya ta zo ta haihu a gaban su. Yana da jikoki kusan guda 20 amma na Yarima isspecial domin babu kamar sa cikin duka jikokin da zai haifa ko ya haifa a baya. Yana masa adduarsamun nasara akan duk abinda ya sa gaba kuma ya gama rubuce-rubucen da zai je ya yi na tsawon shekara guda a ANKARA UNIVERSITY wanda zai bashi damar hawa Professorial Chair.
*****
Kin faya nawa, kin faya yanga Saade, don kin ga Askirama na biye miki, shin sau nawa zan aiko Fanna ta gaya miki Yareema na cikin mota tun dazu yana jiran ki zaku wuce ne? Duk wani shiri da za ki yi meyasa tun jiya baki yi shi ba?
Saade ta cuno baki hadi da marairaice murya Fulani gashi na fa nake gyarawa kawai, ya ce baya son ganin sa a cukurkude, nikuma bana so kowa ya taba min kai, shine nake tajewa da kaina.
Fulani ta karbi katon matajin dake hannun ta tace bari ni in taje miki, in ba haka ba zaki yi awa guda kina abu daya. Ta taje mata, ta tufke mata shi da murtukekiyar kalbaa tsakiyar ka. Ta kawo katon hair-bound kalar kayan jikin ta wato sky-blue ta zagaye mata shi. Fuskar Saade ta fito tsam, tayi cute da ita. Fulani ta taimaka mata ta nannada laffayar. Sannan suka fito.
Ko kusa bata gaya mata kasar zasu bari ba don ta san halin shagwabar Saade da rigimar ta, cewa zata yi bazata iya shekara babu Fulani ba.
Sun bata lokaci suna sallama, kamar kada su rabu,finally suka rabun. Saade na kwallah Zarah na kukan sai ta bi ta, da kyar Fulani ta rarrasheta da cewa asibiti zata je ta dawo, kafin Fanna ta raka ta wajen Ya Gumsu.
An jinginar ta jikin pillow bakin da ya karkace ya sha gashi ya koma daidai. Amma har yanzu bata motsa daya hannun yadda ya kamata amma kana iya gane abinda take cewa. Sauki dai yana ta samuwa cikin yardar Ubangiji da kulawar yayan ta.
Idan Allah ya baka yaya masu jin kan ka ya baka komai na duniya. Kishiyoyin ta ma baa bar su a baya ba wajen nuna kulawar su akan iftilain da ya same ta.
Ya Gumsu na ganin shigowar su ita da Fanna ta mika mata hannun ta mai lafiya, da sauri Saade ta karasa ta zube gaban Ya Gumsu. Hannu ya Gumsu ta dora a kanta tana shi mata albarka tare da cewa cikin harshen barbarci.
Wa gafurne kla awodune nyiro dikkuna samma so ro, Nadimtikna.(Ki yafe min na yi nadama a akan duka abinda na aikata, na yi nadama).
Saade tace baki yimin komai ba sai alkhairi Ya Gumsu, Allah ya baki lafiya.
Ta

1 Comments On MASARAUTAR MU
avatar
zainabaliyu

1 year ago

Reply

I really appreciate masarautar mu, thank you

Please Login or Register in order to submit comment