Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakinsa. Saade ta yi amfani da wannan damar ta ja jiki da rarrafe ta shige toilet dinta ta rufe.
Ta kifa kai jikin jacuzzi tana girza wani irin kuka jikinta yana ta rawa da kakkarwa, wanda sautin sa yake fitowa tun daga karkashin zuciyarta.

Me wannan mutumin ko aljanin zata ce ya zo ya yi mata? Kisa ko me??

O.k tunda ta ganshi ya tube wando ya kuma tsiraitata to raping dinta ya zo yi. Rape, rape, rape dai da ta ke jin labari!!!

Wani mugun tsoro ya shige ta, ta ji ba abin da ta ke so a halin yanzu ban da ta bude ido ta ganta a gaban uwarta.
Ba ta san ya suka kare ba. Ta kasa fitowa daga toilet. Banda tsuma ba abinda jikin ta ke yi ta dunkule a wuri guda a gefen kwamin wanka. Sanyi yana kada ta.
Ta dai ji karar shigowar motar security din Nigerian Turkish Nile University. Gabadaya kuma suka shiga motoci suka tafi har Yareema domin su yi report karkashin hukuma. Har Uche aka tafi, don shi ne zai bada shaidar komai.
Uche ya fada wa kwamishinan yan sanda duk abin da ya sani, cewa yana shigar da cefane ya kai wasu ya koma don ya debo wasu, sai ya tuna wayar sa ya barota a baskwata tana caji ya je don ya dauko, da wannan damar Dr. Ziyad ya yi amfani ya shigo gidan ta kofar kitchen. Ihun Saade da ya jiyo da lekawa da ya yi ta taga ya gansu suna dauki ba dadi.
Kiran Yarima da ya yi da daya makwabcinsu Dr. Wole da ya kira universitysecurity bayan shigowar Yarima.
Lokacin da hukuma ta matsawa Dr. Ziyad kan ya amsa laifinsa kada ya wahalar da hukuma, budar bakin sa sai ya ce shi ma Yarima yana neman mata, komai suke yi ai tare suke yi, don haka bai kamata ya kawo zancen nan ga hukuma ba tunda abin da yake yi wa matan wasu ne shi ma aka yi wa tasa..kuma sharing matan suke yi.

Yarima bai taba jin nadamar aikata zina a tsayin rayuwar sa irin ta yau ba. Lallai Ubangiji ya yi gaskiya, ita zina bashi ce, kuma bibiyar mai ita take yi, in dai ka yi ta a rayuwarka ko ba a yi da dan ka ba zaa yi da matarka ko kanwarka.
Kuka riris Yareema Sageer ke yi akan bencin kwamishinan yan sanda, ya kuma yarda gaskiya Ziyad ya fada. Amma shi tunda yake bai taba neman matar kowa ba sai watsattsun bisa titi, to why matar sa? Amma da gaske ya taba raping yar wani duk da baiwa ce tun a shekarun tashen balagarsa. Amma ai an yi masa hukuncin addini, me ya sa tun bayan nan bai daina ba? Sai ma hakan ya bude shafin rayuwar kaico a gare shi? Sai ya ji koma me Ziyad ya yi masa kamun Allah ne. Ubangiji Subhana yayi gaskiya da yace (in kayi zina da yar wani to hakika zaa yi da yar ka ko kanwar ka ko matar ka.).
Ubangiji Yana kyale mu mu yi ta saba masa, ranar da zai yi mana talala sai ya yi mana ita a kan abin da muka fi so fiye da komai a rayuwarmu.
Yana son Saade, yana kishinta yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Dr. Ziyad ya keta mata haddi, amma abin nan da Ziyad ya fada sai ya ji ba shi da sauran guts na neman hakki a kansa. In har ya yarda da fadar Ubangiji a kan zina. To ya yarda kawai kamun Allah ne tun a gidan duniya. Wani kamun sai an je lahira.
Ya yi kukansa mai isar sa a gaban Ziyad da kwamishinan yan sanda, sannan ya share hawayen sa ya mike yace a sake shi, ya janye karar sa, amma yana so hukuma tayi masa iyaka da Dr. Ziyad ba shi ba shi har abada! Kuma daga yau ya ajiye aiki a jamiarsu ta Turkawa (Nigerian Turkish Nile University).

Yana tuki a kan hanyarsa ta komawa gida yana hawaye. Hawayen nadamar duk abin da ya aikata a baya. Shi kansa ya san talala ce Allah ya yi masa da soyayyar Saade, soyayyar da ko a labarun hikaya bai taba jin wadda ta yi daidai da wadda yake yi wa Saadatu yar Bilkisu ba. Yau aibunsa ya janyo an shiga gonarsa an keta haddin sa.
Ya shigar da motar maadanarta, sannan cikin sanyin jiki ya kashe ta ya fito, kayan jikinsa duk sun baci da jinin hancin Dr. Ziyad, da sanyin jikin dai ya bude kofar falon don bai san a halin da zai riski Saadatu ba.
Falon yana nan yadda yake tun safe, kofar dakin barcinsu inda abun ya faru har yanzu a bude, ya leka can bai ganta ba sai ya fito zuwa nata dakin.
Tana kwance a kan gadonta tana kallon ceiling hawaye na bi ta gefen idonta. Fuskarta duk ta kumbura ta yi jazur. Ba ta taba shiga tashin hankali a rayuwarta irin yau ba. Ba ta taba ganin abin da ya tsorata ya firgitata tsananin firgitawa irin yau ba da aka yi attempting raping dinta da tsakar rana har dakin aurenta.
Dr. Sageer Yusuf, ya nufi Saadatu da sassarfa, ya dago ta daga kwanciyar da ta yi ya rungume a kirjinsa. Ga mamakin Saade shi ma kukan yake yi. Cikin wata kassararriyar murya tamkar ba tasa ba yake magana.
Saadatu did hedid he succeed???
Ya kasa karasawa sabida tsoron abin da zai fada din.
Ta runtse idonta ta kankame Sageer jikinta yana rawa.
No he didnt.
Wata irin kakkarfar ajiyar zuciya Yareema Sageer ya saki, wadda bai taba yin irinta a tsayin rayuwarsa ba.
Ko an yi ko ba a yi ba, ya ji abin da miji ko uba yake ji in an yi zina da yarsa ko matarsa. A fili ya ke furta, ASTAGFIRULLAH WAATUBU ILAIHI.
Saadatu ta fashe da kuka tana rokon Yareema ya maida ta Askira, ita ta hakura da karatun. Yareema ya ja lallausan duvet ya lullube su, ya kwantar da Saade saman kirjinsa.
Ki kwantar da hankalinki don Allah Saadatu. Aikin ma gabadaya na aje. Alfarma daya nake nema kada ki fadawa Fulani ko Maimartaba wannan kaddarar da ta faru, ni kuma duk abin da ki ke so zan yi miki, I promised.
Saade ta ce, In ban fada ba za ka maida ni Askira gobe?
Ya ce, Insha Allahu za mu koma gabadayan mu, amma sai na mika resignation letter, ki ba ni kwanaki uku.

Da wannan ya samu ya lallashe ta. Amma shi kansa Yareeman tsoronsa ta ke ji, ta daku a hannun Ziyad koina na jikinta ciwo yake yi, ba ta gaya wa Yareema ba ne don kada ta kara daga masa hankali, ganin mawuyacin halin da yake ciki, amma kanta ciwo yake sosai sabida yadda Ziyad ya buga shi da bango.
Duk yadda ya so ya samu yadda yake so a daren yau, Saadatu ta ki, shi kuma yana so ne ya yi amfani da soyayya ya gusar da tsananin tsoron da ya dankare mata a zuciya, amma ta ki bada damar hakan.
Ya gaji da kokawa da ita, ya mike ya kunna fitilar dakin. Sai kuka ta ke mai ban tausayi. Ya ce,
For Gods sake Saadatu, ni ma rapist din ne?
Kukanta ya karu, ta ce, Yau daya dai ai sai ka kyale ni in ji da abin da ya dame ni, I cantdo it, gida nake son tafiya.
Yareema ya dawo ya zauna daidai kafafun ta, ya debi kafafun ya aza bisa cinyoyinsa, ai kuwa ta saki wata kara don azaba, wannan ya tabbatar masa akwai targade a yatsar kafarta.
Sosai ya ci gaba da jan yatsun kafarta a hankali har ya gane mai targaden. Ba tun yau ba ya iya gyaran targade, tana kuka tana komai haka ya gyara mata. Sai lokacin ya lura cewa, goshinta ma ya kumbura sosai. Hawaye suka ciko idonsa, ya ce,
Im sorry Saadatu, ni na jawo miki, one is responsible for the consequences of what he have done. Amma ke kam ba ki da laifi, tsarkakakkiya ce aka wanke aka bani cikin girma da daraja.
Dole gobe mu je asibiti a binciki lafiyarki, in ma yayi kika boye min ayi miki wankin ciki.
Ni ba inda za ni, kuma na gaya maka bai yi ba. Ta fada cikin kuka, ciwo har cikin kokon kanta.
Kawai ka sa ni a jirgi in tafi Maiduguri, daga can sai a dauke ni a filin jirgi, bazan iya kara kwanaki uku a gidan nan ba.
Ya kara sassauta murya mai nuna ya fi ta damuwa da abin da ya same ta.
Na rage kwanakin ki ba ni kwana biyu mu tafi tare, in ma kin ce kada mu sake zuwa garin Abuja ba za mu sake ba!.
Da wannan ya samu ya lallashe ta ta hakura ta yi barci.

Washegari da asubah a firgice ta tashi tana tambayarsa aljanin nan ya sake dawowa? Ya kankame ta yana gaya mata, Relax Saadatu ba fa aljani ba ne, abokina ne Dr. Ziyad wanda yake karbar abinci a wajenmu.
Mamaki da tsoro ya kashe Saade a kwance, ta kasa cewa komai, har duniya ta yi lalacewar haka? Aboki kuma makwabci mafi kusanci ya nemi raping matar amininsa? Wannan wace irin rayuwa ce? Tsoronta ya nunku fiye da tunanin ta na cewa Ziyad aljani ne.
Abuja ta kara fice mata a ka, ba abin da ta ke so irin ta bude ido ta ganta a dakin ta na unguwar Fulani Bilkisu.

Da gari ya waye ya yi wanka ya shirya, sannan ya rubuta resignationletterdaga NTNU. Da ya zo fita ne Saade ta ce, bai barinta ita kadai sai dai su tafi tare, tana da paper din karfe takwas.
Duk da ba ta karanta komai ba, a matsayinta na matar Dr. Sageer wadda ko a kwance suke ba ya rabo da tisa mata karatun fannin su na Pure and Applied Chemistry, ta san ba za ta kasa rubuta wannan takardar ta Inorganic Chemistry ba.
Shi ma ya fi so su tafi taren, don haka ya taimaka mata ta yi wanka.
Tana fitowa daga paper ta same shi a mota yana jiranta, dukkansu ba mai walwala, suka nufo gida. A daren ba ta bari sai gobe ba ta hade kayanta tsaf ta daure. Lamarinta har da na shagwaba kuma, ya yi - ya yi su je asibiti a duba ta ta ki.
Washegari ya shiga don ya gama cike sauran takardun ajiye aiki, ya ce mata insha Allahu ba zai wuce awanni biyu ba. Da kyar ya lallabata ta yarda bayan ya ba ta mukullan kofar kitchen da na kofar shigowa duka a hannunta.
******

Yareema Sageer bai dade da fita ba Ya Gumsu da kanwarta Aunty Daja wadda ke aure a nan Abuja tana auren wani ministan yada labarai, suka zo gidan cikin wata zabgegiyar mota. Ya Gumsu ta zo auren babbar yar Aunty Daja ne Abuja tun shekaranjiya. Tun da ta iso ta ke ce da Daja a kai ta gidan Yareema, Daja na ba ta hakuri kan ta bari a kai amarya ko me za su yi sai su yi, ita ma ba ta bayan hada zuria da yar annamimiya Fulanin Askirama.
Suna sauka daga mota suka karaso kofar shiga falo, suka soma yi mata wani irin mahaukacin bugu, wanda ya karasa razana razananniya Saade, wadda da ma ta ke zaune a darare tana jiran dawowar Yareema da trollies dinta uku a gabanta. Ta gama sa wa a ranta yau komai dadin bakinsa a Askira za ta kwana.
Sai kuma ga wannan mahaukacin bugun, ba abin da ta kawo a ranta sai Ziyad ne ya dawo. Idanunta suka raina fata, hawaye ya soma malalowa. Ba ta so ta yi ihu ma kada ya san tana cikin gidan, sai mazari jikinta yake daga tsayen da ta ke, wani fitsari ya kwace mata. Amma me?
Sai ta jiyo murya kamar ta mata suna kiran sunanta. Ba ta yi wa Ya Gumsu farin sanin da za ta dau muryarta ba, amma sai ta ji tana fadin,
Ni da gidan Dana aka bar ni ina buga kofa da mutuncina na Gumsun gari da komai?
Da sauri Saade ta karasa ta bude kofar da mukullan da dama suke rike a hannunta. Ta gane Ya Gumsu, dayar ce ba ta sani ba. Tana kokarin yi musu barka da zuwa ta ji wani lafiyayyen mari ya sauka a kan kuncinta, Aunty Daja ma ta kai mata nata.
Shegiya karuwa yar karuwa, tsintattun bisa titi. Idan ba Bilkisun ce ta haifa min Yareema ba, ba kuma ita ta ajiye ki a gidan nan ba, to sawunki a likkafa ki kama hanyar gidan ubanki, tunda an ce kina da shi.
Idan na ganki a masarautar Askira sai na sa an nakasta ki yadda ba Yareema ba babu wani namiji da zai kwashe ki. Fice mana a gida ki san inda dare ya yi miki kafin in sassaba miki kamanni.
Ta hankado ta waje, Daja kuma ta dauki hijab dinta ta jefo mata suka dinga hankada ta har kofar fita gidan, bayan Daja ta kara zazzabga mata mari. Farar fuskar nan ta yi jawur tayi kitumur kamar gauta. Marukan da ta sha sun kai goma. Yatsunsu ya kwanta lambam a kan farar fatar fuskar Saade.
Kuka ma wani lokacin rahma ne ga dan Adam, a lokacin da zuciyarsa ta rasa abin yi. To Saade ta kasa ko da fidda hawaye, tana nadamar yarda da aure da soyayyar Yareema Sageer alhalin tana da masaniya kan cewa, mahaifiyarsa ba ta kaunar tata kamar ajalinta.
Ya yi amfani da dukkan dabarunsa na wayayyen Da namiji ya sanya soyayyarsa a zuciyarta, ya ribace ta ya kassara zuciyarta. Yau mahaifiyarsa ta yi mata wulakancin da ko ita mayya ce dole ta hakura da Yareema Sageer sai a wannan lokacin ne ta ji hawaye masu dumi sun zubo mata.
Ya ya za ta yi ta je Askira? Duk da Ya Gumsu ta ce kada ta je din, amma ba ta da inda ya fi can, tunda uwarta tana can, za ta bar masarautar Askira ne only ranar da babu Fulani a can ko ranar da ita ma Askirama ya kore ta.
Ko kudin mota babu a tare da ita, daga ita sai hijabin sallarta. Amma ta tabbata za ta iya kai kanta Askira, idan ta ganta a Maiduguri. Ko da da rarrafe da jan ciki ne.
Tana wannan tunanin tana kuka, ba ta san cewa ta hau bisa titi ba ta bar tafiya a gefen hanya.
Daidai lokacin da shi kuma ya fito daga NTNU yana sharara gudu don tafiya gida, ya hango wata mace na tafiya tsakiyar titi kamar bata ji ba ta gani, motoci na ta kauce mata, wasu su bi ta da zagi, wasu su kunna mata fitilar zagi, amma ba ta ko san suna yi ba.
Ya sakar mata kakkarfan horn don ta sha gabansa, ta juya a firgice sai ya ga Saade. A hankali ya sauka a gefen titi, ya fito da sauri ya bi bayanta yana kiran sunanta.
Saadatu Hashim, Saadatu Askira ina za ki je haka?
Muryar Said abokinta, Saidu-Saidunta. Yau da shi ta aura wa zai yi mata wannan wulakancin da cin zarafin? Wani hawayen ya sake zubo mata, ta sa fuska cikin hijabinta tana kuka.
Said ya hau waiwaye cikin tsoro. Har zai ce ta shiga motarsa ya kai ta inda za ta je ya tuna gargadin Yareema Sageer.
Kada ka kara daukar matata a motarka ko da da niyyar taimako ne.
Said ya naushi hannun damansa da hannun hagu, ga shi kuma ba zai iya tafiya ya barta a kan titi ba, ko da kuwa supreme court Dr. Sageer Askira zai kai shi a dalilin hakan. Da ganin halin da ta ke ciki tana tsananin bukatar taimako, ba zai barta ta ragaita a babban birni irin Abuja ba.

Wane irin taimako zan iya ba ki?
Said ya fada cikin tsoro, yana tsaye nesa-nesa da Saade yana kuma waiwayawa dama da hauni kada Dr. Sageer ya zo ya same shi.
Kudin mota.
Ba ta san lokacin da ta furta ba.
Ina za ki je? Ya tambaya da sauri.
A hankali ta ce, Garinmu Askira.
In aka sauke ki a Maiduguri za ki iya zuwa har can Askiran?
Da sauri ta gyada kai.
Said ya ce, Zan sa ki a tasi zuwa airport, sai in bi bayanku, sai mu je in yankar miki ticket din Maiduguri.
Saade ta hau godiya, tana yi masa addua. Ji ta ke kamar ma ga ta ga Fulani a gabanta.

Hakan kuwa aka yi, Said bai bar airport din ba sai da ya tabbata jirgin Maiduguri ya daga da Saade. Ya kuma damka mata naira dubu goma, ya bar filin jirgin cike da tausayinta.
A ganinsa iyayensu sun cutar da ita da suka aura mata babban mutum kamar Dr. Sageer, ba zai ba ta kulawar da in shi ya aure ta zai ba ta ba, ban da kishin balaI bai san komai ba (a ganinsa).
Tunda jirgin Azman ya lulluka sararin samaniya ya doshi arewacin Nigeria, Saade ta kankame jikinta wuri guda tana kuka, ba ta san ya ya za ta iya rayuwa babu Sageer ba. Amma ta tabbata Ya Gumsu ta raba su kenan, ba za ta kara bari su rayu inuwa guda ba.
Ya taba cewa yana fuskantar barazana akan auren su, wanda ya sanya shi tabbatar da auren su a lokacin da bai shiryawa hakan ba, yanzu ta tabbatar ba komai bace barazanar, Ya Gumsu ce. Har gobe bata yi naam da zaman su tare ba.
Wannan tunanin kadai na matukar tayar da hankalin Saade, ta rasa inda za ta tsoma zuciyarta ta ji dadi. Wani irin sanyi ta ji yana shiga har cikin bargonta. Ba jimawa hakoranta suka soma karo da juna, kafin a yi haka zazzabi mai zafi da ciwon kan da ta kwana a ciki sun hadu sun rufe ta ruf.

Ta sauka a filin jirgin saman Maiduguri cikin mawuyacin hali. Ba ta gaya wa kowa tana tafe ba balle a san da zuwanta a zo a dauke ta, sannan ba wayarta a hannunta ta baro ta a kan gadonta. Duk da cewa ta haddace lambar Fulani, amma ta ga gara ta bi motar kasuwa ta karasa Askira, tunda akwai kudi isassu a hannunta.
A nan airport ta samu wani mai taxi yana faman binta da nacin tambayar ina zaa kai ta? Ta ga cewa, zuwa tasha da neman motar Askira karin wahala ne a gare ta, ga shi da ma ta yi matukar jigata, sai ta juya ta ce da shi,
Nawa zan ba ka ka kai ni har Askira?
Mai taxi ya yanko kudin da a tunaninsa ko rabinsu ba za ta biya ba. Amma sai ya ga babu musu ta amince. Ya bude mata kofa ta shiga ya rufe, ya ja mota suka naushi hanya.

******

ASKIRA EMIRATE
Lokacin da suka shiga garin Askira magriba ta kawo kai. Ita ta dinga nuna masa hanya har kofar fada. Ya ajiye ta ta mika masa duka dubu goman, sannan ba tare da ta kara cewa uffan ba bayan godiya, ta durfafi cikin gida.
Amma me? Tana saka kafa a soro na farko hajijiya ta soma dibarta, ga yunwa ga wahalar zaman mota. Ga wani irin masifaffen ciwon kai da ke sakadarta, taku biyu ta yi a soron farko Fadawa na zazzaune sai gani suka yi mace ta fadi a wajen, sakamakon kafafunta da suka kasa daukarta, duhun yunwa da na hajijiya kuma suka mamayi ganinta.
Taimakon Allah ne kadai ya kawo ta Askira lafiya.
Fadawa biyu sun shaida ko wace ce, kasancewar cikinsu akwai direban fada da ya ke kai su El-Kanemi. Cikin kidima suka kira bayi mata, su uku suka dauke ta ranga-ranga sai Unguwar Fulani Bilkisu.
Ba aladar Askirama ba ce bin dakunan matansa, amma Fulani Hibbani wadda ita ce mai girki, sarkin gulma da daukar zance ta shigo yanzun nan ta same shi yana cin abinci, kamar ta manta shi din ne ta ke magana da shi, tsabar gulma da ke cinta.
Mai Askira ashe abin da Yareema ya yi ke nan? Ya sako yar Bilkisu bayan ya yi mata shegen duka? Ta dawo rai a hannun Allah Anya shi ma ba giyar yake sha ba kamar matar.
Sauran maganar makalewa ta yi a bakinta ganin wata irin zabura da Askirama ya yi. Kafin ta ankara kuma ta tsinto shi a bakin kofa bayan ya saka takalminsa na gashin dawisu.
Fanna tare da dukkan kuyangin Fulani suna kan Saade, sai firfita suke mata bayan an samu ta farfado, tana kwance shame-shame bisa cinyar Fulani, tambayar duniyar nan Fulani ta yi mata, amma ta ki cewa komai. Fulani ta soma fusata, amma ta yi kokarin hadiye fushinta.
Ba za ki gaya min ina Yareeman ba? Ya san kin taho? Ke da wa ki ka zo? In sakinki ya yi ki yi mana bayani.
Kallo daya Fanna ta yi wa sauran kuyangin suka hau darewa suna barin falon, ta yi hakan ne ganin irin rikicewar da Fulani ta yi har ta manta cewa suna tsaye. Ko sakin Saade aka yi ba za su so a ji ba, a wannan gidan na gulma da jiran kiris a kan duk wani abu da ya shafi uwargijyarta.
Gyara kimtsi kimtsi gyara Zakin Askira.
Suka jiyo kuyangi na fadi daga waje, tabbacin Alanguburo ya durfafo unguwar da kansa. Kamar kiftawar ido kuma sai ga shi a kansu, sabida saurin da ya shigo da shi ba irin tafiyar sarauta da yake yi ba.
Lafiya Bilkisu? Me ya faru?
Ya tambaya cikin matukar kidima

1 Comments On MASARAUTAR MU
avatar
zainabaliyu

1 year ago

Reply

I really appreciate masarautar mu, thank you

Please Login or Register in order to submit comment