Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aah Alanguburo muna cikin Nigeria. Na kawo ta ta ga dabbobi ne, a nan Yankari Game Reserve.
Askirama ya yi dariya, idan yana magana da Sageer mantawa yake shi Sarki ne. He so much love him, zai iya komai don ya faranta masa ko da kuwa kara masa wata mace ne bayan Saade in dai har zai nutsu ya tsaya a kan matansa na aure.
To a ga dabbobi da kyau. Ina gaida Giwayen Yankari.
Dariya Yareema ya yi, sannan suka yi sallama cike da begen juna.
Ya koma dakin, Saade na kwance har yanzu yadda ya barta abincin da aka kawo musu ko tabawa ba ta yi ba. Da ya duba sai ya ga bacci ne ya dauke ta, ga busasshen hawaye a fuskarta, ya tsugunna ya sumbaci goshinta, sannan ya hau kintsa kayansu da ya yi watsi da su a dakin daren jiya.
Jinya sosai har ta kwanaki uku cif! Yareema ya yi ba shiga ba fita, ko kofar falo ta ki fitowa sai a rana ta uku ne ta yarda ta ci abinci ta koshi, amma a tsayin kwana uku oldenburger fresh milk kawai ta ke sha a Yankari.
Ranar da ta dan soma walwala, Yareema bai yi kasa a gwiwa ba ya sake kalallame ta ya maimaita laifinsa.
Sai dai wannan karon ita kanta ta san da bambanci. So sweet, so gentle. Kafin su bar Yankari cikin kwanaki bakwai Saade an zama manyan mata. Ta iya dauke wa mijinta Yareema Sageer Yusuf Askira lalurar da mata hudu ba za su iya dauke masa ba. Sun dinke sun zama miji da mata na haqiqa mafiya kusanci da juna, maabota soyayyar da biro ya yi kadan ya bayyana ta.
Sai a na i-gobe za su tafi ne suka zaga wild life na cikin Yankari Resort, Saadatu ta ga dabbobi iri-iri a fili, wadanda sai a talabijin ta ke ganinsu. Ta baro Yankari with nostalgia, ta sanya zamanta na amarci na dan lokaci a Yankari cikin kundin tarihinta as the beginning of the beginning na kafuwar rayuwarta da maigidanta Yareema Sageer Yusuf Askira.

******

ABUJA
Sun dawo Abuja ranar lahadi da yamma. Saade ta saki baki tana kallon yadda aka canza komai na gidan da ROYAL ONE. Duk abin da ke cikin gidan zubin na sarauta ne, sarauta ta zamani mai tafiya da boko.
Ta karaso cikin main parlour tana latsa cushion din Royal Chairs din da suka yi wa dakin kawanya. Komai ya burge ta beyond her taste, beyond her expectation. Da Yareema ya ce za a yi refurbishing gidan ne shi ya sa suka tafi Yankari ba ta taba zaton gyaran zai kai kayatuwar haka ba. Once again, she simply fall in love with her humble abode (ta fada a matsananciyar soyayyar gidanta).
Tunanin me ya kamata ta fara gyarawa ta tsaya yi. First of all zata gyara zaman kujerun. Su kalli juna madadin yadda aka ajiye su. Ta daga kai tana kallon hoton kyakkyawa Fulani Bilkisu cikin alkyabba da aka kafa mata a bangon gabas maso kudu na falon, ta saki murmushi ita kadai murmushin farin ciki. Ta matsa a hankali zuwa ga hoton, ta kai hannu ta shafi fuskar Fulani a hankali tana murmushi, lebbanta suka furta,

Ina kewarki Fulani ba dan kadan ba.

Ba ta san Yareema ya shigo jaye da trollies dinsu ba, yana tsaye daga bayan ta, ya ce, Me ki ka ce?
Ta juya ta yi masa wani kallo na kasa-kasan ido, sannan ta zumburo dan bakinta gaba ta ce, Na ce ne Im missing her Prince, don Allah yaushe za mu je Askira?
Dariya ya yi tare da mika mata kwalin wayar da ya sayo a hanya yana fadin,
Ke da Askira sai na ga kina daga kafa da kyar, kina tafiya da kyar, sannan kina tashi da kyar.
Ya karaso ya kama hannayenta ya sanya mata kwalin wayar, ya ce,
Call your Mum, anytime.
Har da dan tsallenta don farin ciki, ta makale a gefen kafadun Dr. Sageer ta na fadin,
Na gode Prince.

Dakin barcin Sultana na da nan ya kai mata kayan. Ya ja hannunta suka shiga dakin. Saade sai da ta rike numfashinta sakamakon ganin irin dankara-dankaran Royal furnitures da Maimartaba ya zuba mata. Wanda sai yayan sa su Ya Maira kadai zai iya yi wa. Hawayen farin ciki suka zubo mata, ba ta san sanda ta juya ta rungume Yareema Sageer ba.
Ka taya ni godiya ga Alanguburo, Allah ya kara yawan rai, ya kara nisan kwana mai albarka. Ya gama yi min duk wani gata a rayuwa.
Yareema ya rike ta sosai a cikin hannayensa, sannan ya ba ta kyakkyawar sumba saman idanunta. Yace.
Nima ya gama min kowanne gata a rayuwa, tunda ya bani ke a lokaci mafi dacewa. When my heart was bewildered. Na kasa tunkarar ki in ce ina son ki, haka na kasa tunkarar kowa don ina ganin Im not good enough to have you.
Bansan ni da ke wa Askirama ya fi so ba.
Dariya ta yi ta zame daga cikin rikon sa, cikin jin dadin kalaman sa, aah Prince. Blood is thicker than water, ni ce ma yakamata in ce Im not good enough to haveyou, ni da ba yar kowa ba, ba yar sarau!. Yarima yayi saurin toshe mata baki da nasa in such a waythat hakan ya sa ta hadiye abinda ta yi niyyar fada cikin cikin ta, ya kuma kalubalance ta da cewa;
watarana ruwan yana fin jinin kauri Saadatu.

A daren ranar suna cin abinci yake cewa, Saadatu in na tafi na barki ke kadai a gidannan sai maaikata, babu matsala? Zan sake yin tafiya ta tsayin kwanaki uku.
Da sauri Saade ta sake cokalin hannun ta, damuwa ta bayyana karara a kan kyakkyawar fuskarta. A dan zaman da suka yi tare a Yankari game reserve ta saba da Yareema Sageer fiye da tsammani, ya shiga zuciyar ta fiye da kintace. Tace tana son shi ma bata baki ne and is not enough to express the feelings
Zuwa ina kuma Prince?
Muryarta ta nuna tsantsar damuwar data fada.Yareema Sageer ya kamo hannunta ya dunkule cikin nasa, suka zauna a tare a gefen katafaren gadon Saaden, ya sassauta murya cikin lallashi,
Its a promise ba zan wuce kwana ukun ba, zan kai Aisha-Sultana ganin gida ne.
Wani abu ya zo ya tokare a kirjin Saade, wanda a nata sanin yafi komai zafi a zuciyar diya mace, a hankali ta janye jiki daga gare shi,sannan cikin karayar murya ta ce,
A dawo lafiya!.
Yareema ya sanya fuskarta cikin tafukansa, yana kallon fararen kwayar idanunta, ga mamakinsa idanunta sun cika taf! Da kwallah, kada dai Saadatu ta fara kishinsa? Babban burinsa kenan ta so shi irin yadda shi yake sonta.
“Look at me Saadatu, na yi tafiya da ke mun yi kwanaki bakwai, ita ma tana da hakki a kaina, so ki yi hakuri in je in rakata, na yi miki alkawarin ba zan wuce.
A hargitseSaadatu ta mike.
Ka ji na ce wani abu ne Prince? Ko na ce Aunty Sultana ba ta da hakki a kanka? Ko me ye damuwata a ciki don ka dauki matarka kun tafi kun bar ni jiran gida?
Ta juya masa baya a kokarin ta na boye hawayen ta.
Yareema Sageer yana daga zaune yana kallonta ban da murmushi ba abin da yake yi. She never talked to him in this manner (cikin tsiwa). Saade ba ta ankara ba ta ji Dr. Sageer ya sure ta yana juyi da ita a tsakiyar dakin, kafin ya dire ta a tsakiyar gadon su ya koma samanta, ya dora mata dukkan nauyinsa gabadaya.
Say it againba ki da damuwa don na dauki matata mun tafi Korea, to su wadannan hawayen kuma na mene ne, ya ya sunansu? Zan so kwarai in san maanar su.
Saade ta runtse idonta hawayen na ci gaba da bulbula. Kamshin INVICTUS da ya riga ya kama Yareema ya soma hargitsa ta. Yana tada tsigogin jikin ta. A hankali Yareema ya soma kissing dinta from head to toe, lungu-lungu, sako-sako, kusfa-kusfa, kafin dan lokaci Saadatu ta fice a hayyacinta.
Abin da ya biyo baya mai nauyi da girma ne da ya shallake tunaninsu. It was kind of gentle romance da ya gudana da hobbasar Yareema shi kadai, yayin da Saade ta sakar masa komai, gangar jiki, zuciya da ruhi, sai yadda ya ga damar sarrafa ta.
Daren ya zamo cikin dararen tarihi a rayuwar amarcin ta, dare ne da daga Sageer har Saadatu, bazasu taba mantawa ba.

Washegari suka yi shirin shiga makaranta. Saade ta yi tsaf cikin doguwar rigar atamfar chiganvy kalar pusher pink, ta yi lullubi da mayafi kalar kayanta wanda ya ciza sosai. Kallo daya Dr. Sageer ya yi mata yana shigowa dakin nata yana daura agogon hannunsa na danyar zurfa samfurin (Gucci) na maza, ya girgiza kai ya ce,
Ai da sake. Ba ke ba fita da irin wadannan mayafan Saadatu, ko dai ki sa hijab ko ki koma gado ki nade ki kwanta.
Saadatu ba ta kula shi ba, don ba wai ta huce daga fushin tafiyar da ya ce zai yi da matarsa ba ne, duk da duniyar soyayyar da ya dauke ta ya luluka ta daren jiya, yayi shawagi da ita a sararin samaniyar soyayya sky-blue mai haskaka zuciya da ruhi,still kishin hakan na makale a kasan zuciyar ta.
Ya ce, reporting kawai zai je ya yi a ofis ya je gidanta ya dauke ta su wuce airport. Hijabin sallarta ta dauka ta saka akan atamfar jikin ta sannan ta biyo bayansa suka fito.

Suna tafe a shimfidadden titin da zai shigar da kai cikin jamiar NTNU, a hankali Yareema ke jan motar tamkar ba ya so. Kwanakin nan da ya yi da Saade cikin rayuwarsa su ne kwanaki mafiya daraja da farin ciki da zai iya tunawa. Kwanaki ne da ba zai taba mantawa da su ba. Sannan kwanaki ne da suka bude sabon shafin tsaftatacciyar rayuwa da bai taba samun kansa a ciki ba.
Sannan wadannan kwana ukun da zai yi ba tare da ita ba suna nufin komai. In ya ce komai yana nufin komai. Amma su kadai ne za su ba shi madauwamin kwanciyar hankali tare da Saade, ba zai iya hada rayuwarsa da ta kowace mace a yanzu bayan ita ba.(ASKIRAMA ya yi gaskiya).
Aurensa da Sultana aure ne da bai san a rukunin da zai sanya shi ba. A yanzu ya gane kwanciyar hankalinsa da na Maimartaba shi ne kawai rabuwa da Sultana duk da Askirama bai furta hakan ba sabida principles din gidan sarautar Askira ya san abinda yafi so kenan. Don ya tabbata ba za ta taba yarda ta bar alcoholism ba.
Ta fannin sa abubuwa sun dade da canzawa, ko yace suna kan canzawa, tun kafin shigowar Saade cikin rayuwar sa ya dade da nisantar zunuban sa. Abinda ba shi da tabbas a kai shine abinda gobe zata haifar.
Amma ya dade yana tuba akan laifuffukan sa na baya. Tuban da Ubangiji yayi alkawarin karbar sa wato tuban da aka yi da niyyar bazaa sake komawa izuwa zunubin ba. Cikin matakan da ya dauka don kare kansa har da nesanta kansa da Dr. Ziyad.
Ko Maimartaba bai gayawa ba, don ya san zai dakatar da shi ne daga hukuncin da ya yanke a kan Sultana, zai ce zai yarda da kowanne irin hukunci amma ban da rabuwar aure, sabida ba ya cikin aladar sarautar Askira.
Shi kuma ya yi laakari da fadar Ubangiji (S.W.T) ne da ya ce, Na hore ku da auren abin da ya yi muku dadi daga daya-daya, biyu-biyu, uku-uku ko hurhudu. Amma in kun san ba za ku yi adalci ba, to ku zauna da guda daya.
Shi kam ya tabbata bai iya yin kowanne adalci tsakanin Saadatu da Aisha-Sultana. Musuluncin da ta karba a yanzu ya gane don ya ba ta lasisin aurensa ne kawai, daga sanda ta same shi kuwa ta nade shi cikin tabarma ta jingine a gefe. Don haka ya amince wa ransa rabuwarsu ita ce mafi alkhairi.

Har gaban department din su Saade ya shiga da motar, inda babu mai wucewa sai staff only. Yana tsayawa ta bude kofar za ta fice, cike da dokin shiga aji, ta yi kewar karatunta sosai, ta san abubuwa da yawa sun wuce ta, amma ta tabbata Said zai dora mata komai.
Yarima ya rike hannunta tana shirin fita.
Haah! Saadatu har murna ki ke zan tafi in ba ki fili ko?
Ya fada da marainiyar murya, har cikin ransa yake jin rabuwar nan da zai yi da Saade har tsayin kwanaki uku. Kwarai bai yi karya ba tana murna da tafiyar sa ta wani fannin ko don kwarzaba irin tasa, ta san za ta samu hutu da nutsuwa na dan lokaci ta yi karatu sosai na abin da aka wuce ta.
Amma in ta tuna da matarsa zai tafi sai ta ji gara ya zauna ya yi tumurmusar nata da ya tafi wajen mai jan kunnen tasa. Amma ko kashe ta zaa yi ba za ta iya gaya wa Yareema tunaninta ba. Ta san kuma da gaske ne kamar yadda ya ce matarsa ma na da hakki a kansa, ba don ita kadai aka halicce shi ba.
Ba ta ankara ba ta ji hawaye sun zubo mata. A hankali ta ce,
Ni ba murna nake ba, hasali ma I will really miss you.
Cikin jin dadin kalaman ta Yareema ya mika mata hanky dinsa ya ce, To share hawayen, ki bar wayarki a kunne, zuwa asubahi in mun sauka zan kira ki. Me zan sayo miki? Kasar Korea ta Kudu za mu je ni da Sultana.
Ta kasa sabawa da ambaton Sultana da yake yi, don ji ta ke kamar ya fi kowa iya fadar sunan. Wasu hawaye suka sake zubowa, wadanda ba ta san dalilinsu ba. Yareema ya sa hannunsa yana shafe mata hawayen da tafukansa sai a idanun Said da ke fitowa daga lecture hall. Dr. sageer ya gan shi ta karshen idon sa amma ita Saade bata lura da shi ba, da gayya ya kara rungumo Saade yana mata magana cikin kunnen ta.
Zan iya tafiya?
Ta tambaye shi bayan ya gama dauke mata hawayen fuskarta da tafukan hannun sa.
...Only if you give me a farewell kiss (za ki tafi ne only in kin ba ni sumbar bankwana).
Wani irin murmushi ne ya subuce a siraran lebbanta, wanda Said bai taba gani a tare da ita ba. Ji ya yi kafafunsa na neman kasa daukarsa ya juya ya koma cikin aji da mugun sauri. Har yana cin tuntube a bakin kofa saura kadan ya kifa.
Prince ka bar ni in tafi aji, ka ga malam ya shiga. Kuma nan kan hanya ne, mutane suna iya hango mu ko daga lecture hallne.
Kin yi alkawarin in na dawo komai zai canza Saadatu? Za ki daina fushi da ni, za ki dinga gaya min duka bacin ranki? Zamu shimfida sabuwar rayuwa ta amana, soyayya da fahimtar juna?
Da sauri Saade ta gyada kai.
Yareema ya ratsa yatsunshi biyu cikin nata ya matse su sosai sannan ya sake su a hankali. Ta kasa dago ido ta dube shi, domin wata irin soyayyar Sageer da ta ji tana shigarta tana mamayeta a hankali. Ta bude kofar motar ta fice rungume da folder dinta.
Ba ta waiwayo ba sai da ta kai kofar lecture hall dinsu.
Har yanzu yana nan a inda ta bar shi, kanshi kwance bisa sitiyari, bai dauke ido a kanta ba. Ta sakar masa lallausar murmushi, sannan ta juya ta shige aji.
Yau sai ta ji ta kasa zuwa ta zauna kusa da Said yadda suka saba, wanda ya tattara hankalinsa duka ya dora a kanta tana shigowa. Ta dauke kai ta nemi gefen wata kabila mace ta zauna.
Mai miji kamar Yareema Sageer, ji ta yi ta daina son ganin kowanne namiji a duniya sai shi. Tafiyar da ya yi kuma tamkar ya tafi tare da ruhin ta ne. Gabadaya ta rasa kuzarinta da walwalarta.
Malamin Baireshe ne, yana ta bayani a kan applied chemistry, Saadatu ba ta jin muryar kowa sai ta mijinta Yareema Sageer cikin kunnuwanta yana rada mata tausasan kalamansa. Har ya yi awanni biyunsa ya gama ko alifun ba ta rubuta ba.
Said daga inda yake zaune ban da satar kallonta ba abin da yake yi, yana yi yana rubutu, ta yi wani mugun kyau, ta yi fresh da ita. Yana ta mamakin abin da idanunsa suka gane masa yana faruwa cikin motar Dr. Sageer Askira da kanwar tasa Saadatu.
Ba ta taba yin kama da mutanen banza ba, yarinya ce mai tarbiyyar babban gida, amma anya abin da ya gani cikin idanunsu ita da Yayanta Dr. Askira bai yi kama da mashahuriyar soyayya ba? Soyayyar ma irin wadda ba ta taba faruwa sai da physical relationship a tsakani.
Bayan fitar Malamin, Saade dole ta taso ta cimma Said a mazauninsa don ya ba ta notes din da ya wuce ta. Ta yi masa sallama, ta ce,
Said kwana biyu?
Ya daga ido ya dube ta a hankali, sai kuma ya dauke kai. Mamaki ya kama Saade.
Said ba ka gane ni ba ne?
Kawai sai ya tattara takardunsa ya bar gurin.
Saade mamaki ya kashe ta a tsaye, ta bi bayansa yana fita daga theater din.
Said! Said!! Ta daga murya tana kwala masa kira.
Juyowa ya yi ya jefe ta da wani mugun kallo, sannan ya dakata har ta cimmasa. Suka yi kallon-kallo na yan sakanni kafin Saade ta tuna cewa ita yanzu matar aure ce, ta yi saurin kawar da idonta.
What happened Said? Ina magana kamar ba ka san ni ba?
Said ya rasa me zai ce mata, idanunsa sun kada sun yi jazir don kishi. Saade ta soma shaka, don ta tsani wulakanci. Ta kankance ido ta ce,
In dai don notes dinka ne, ka rike abunka kada Allah ya sa ka ba ni, kada ka manta kanwar Dr. Sageer ce ni, zai karba min a hannun kowanne malami.
Said ya yi murmushi mai ciwo, ya ce, Kwarai, na shaida hakan tunda kuwa kina ba shi reward a cikin mota, abin da ya fi notes ma zai karba miki.
Kan Saade ya kulle, ta ce,
Me ka ke nufi?
Ya yi mata wani irin kallo zuciyarsa na zabalbala, ya ce.
Kin ba ni mamaki Saadatu, ina miki kallon yarinyar kirki, mai hankali da tarbiyya, yar manyan mutane, yar babban gida, amma ashe kallon kitse nake wa rogo, duk abin da ya faru cikin motar da ta kawo ki tsakanin ki da wanda ki ka kira Yayanki na gani.
Abin da ban sani ba shi ne, da gaske biological brother dinki ne ku ke aikata wannan assha?
Saade ta kai yatsu ta toshe kunnuwanta ta juya da sauri ta bar wurin. Ba ta san me za ta ce masa ba, tunda ashe duk amincin da ke tsakaninsu ba zai iya shaidarta ba, zai iya yi mata mummunan zargi irin wannan.
Ranta ya yi mugun baci, har ta ji ba ta bukatar fayyace masa gaskiyar ko wane ne Dr. Sageer a gare ta a yanzu. Ya je ya yi ta yi mata kallon yar shan minti a mota, damuwarsa ce. Daga yau ba za ta kuma shiga shirginsa ba.
Ba su gama lectures ba sai yamma lis. Direbanta ya zo ya kai ta gida bisa umarnin Yareema. Ta fito daga motar goye da jakarta irinta yan sakandire (school bag), ta gaya masa gobe karfe takwas zai zo ya shiga da ita.
Uche ta taras ya yo cefane himili guda yana shiga da su kitchen. Ta yi masa sannu, sannan ta ce daga yau ta hutashe shi girkin gidan, aikinsa ya koma share-share da goge-goge kafin ta dawo makaranta ya yi duk abin da zai yi ya gama ya wuce baskwata. Sai kuma cefane da aike da zai dinga yo wa lokaci zuwa lokaci.
A ransa Uche ya ce, Tunda dai ba za ki sa a kore ni ba ai shi ke nan. A fili kuma ya ce, Yes Ma!. Don haka yana gama jera mata komai a firji da store ya bi ta kofar baya ya koma baskwata ya ci gaba da aikin fulawoyin gidan.
Wanka ta yi, sannan tayi sallar magriba ta yi lazimi zuwa isha. Ta kawo sallar isha da shafaI da wutiri, sannan ta roki Allah ya sauki Yareema lafiya, Ya kuma dawo mata da shi lafiya. Ta koma kitchen ta hau aiki, ta gyara komai zuwa yadda ta ke so, ta ke buri tuntuni kitchen din ya kasance (da a ce nata ne).
To shi Allah buwayi ne, gagara misali. Abin da ba ka taba zato ba ko tsammani ya riga ya rubuta shi cikin littafin kaddarorinka.
Noodles kawai ta dafa guda daya ta shige daki, ta ci ta koshi sannan ta yi shirin kwanciya.
Da asubah tana idar da sallah ta janyo wayarta da ta saka a caji ta kunna. Wayar ta cika taf da caji. Tana kunnawa kamar jira yake, sai ga kira daga international number.
Saade na amsawa, tana jin muryar Yareema sai ta saka masa kuka.
Prince yaushe za ka dawo? Jiya da kyar na yi barci, tsoro nake ji.
Hankalinsa gabadaya ya tattara ya mika mata, ya ce, Ki yi hakuri Saadatu, mun sauka lafiya on transit a Amsterdam, yanzu za mu jau jirgin South Korea, insha Allahu jibi i-yanzu muna tare. Mun fara shirin tarbar mai sunan Maimartaba, da ni ki ke so ya yi kama ko da ke?
Ba ta san sanda ta yi murmushi ba, ga hawaye shabe-shabe a idon ta.
Ina gaida Aunty Sultana, ka gaya mata ni ban ce ina son mijinta ba aka aura min, ta daina fushi da ni.


1 Comments On MASARAUTAR MU
avatar
zainabaliyu

1 year ago

Reply

I really appreciate masarautar mu, thank you

Please Login or Register in order to submit comment