Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kala......


¤¤¤¤¤¤


Yau satin Nafi d'aya a makaranta, har a wannan lokacin itadai bata fahimtar me ake a aji, sai dai tana kokari sosai a gun karatun da ake koya mata.

Yau aka kawo musu wani sabon malami na Computer bayan yayi introducing d'in kansa ne ya fara tashin mutane one by one dan tabbatar da abinda suka sani a gun waccan malamin nasu.

"Ke tashi." abinda Nafi taji malamin ya fad'a kenan idanunsa ns kanta, a tsorace Nafi ta kalleshi sai da ya kara ce mata ta tashi kafin ta mike jikinta duk ya fara rawa, Malamin ya kalleta yace "List 3 input of computer."

Nafi ta zare ido cikin tsoro, 'yan aji kam gani sukau ba wanda ya samu saukin tambaya irin tata.

Nafi tai shiru sai wasa da hannunta data shiga yi, zufa sai keto mata take a cikin jikinta.

Ran malamin yakai kololuwa gun tashi gani yake kamar yamata tambayar yara taya za'ai wannan tambayar ta gagari 'yar Js 3?

Ranshi ya b'aci yace " get out. " ya fad'a tare da nuna mata hanyar waje.

Batasan me yace ba sai dai ganin ya nuna da hannu yasa ta had'a hannayenta biyu tashiga bashi hakuri.

Dariya 'yan aji suka saka mata, ran Malam ya kara b'aci ganin taki fita, a zuciye ya d'au bulsla ya fara zuba mata, Nafi kam ta daku sannan yace " ya bata nan da sati d'aya zai kirata a gaban class ya mata tambayoyi, inta kuskura ta kasa to wlh ba shakka sai tayi dana sani mai tsanani."

Nafi kam zama kawai tai tana hawaye.......


Ni kaina ganin halin da Nafi take ciki sai dayasa hannuna ya fara rawa wanda na kasa cigaba da rubutun nan......


*LYSM MY FANS*😍😍😍😍


*THE INNOCENT TEAM*


*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*Hi Fans please Vote me on Wattpad As_AyusherMohd*


{ *28*}

Nafi kwance a saman gado, ba shakka taji zafin dukan da aka mata sosai, ita kad'ai ce a d'akin tana kwance Ferry ta shigo, kasancewar ba magana take mata ba yasa Nafi tace " Sannu da dawowa. "

Kallan da Ferry ta mata yau ba kamar yanda ta saba mata ba, wato kallan banzan data saba ba, yau kallanta tai cikin mutunci, Nafi tai murmushi sannan ta gyara kwanciyarta, jitai Ferry tace " Nafisa ya akai kika kasa bada amsa d'azu? Baici ace duk dakikantarki kinkasa ba. "

Nafi ta mike zaune sannan ta kalleta fuskarta cikin farin ciki, tace " Bansan amsar na Ferry. "

Ferry ta shiga cire kayanta tana cewa " to in dai haka ne lalai zakici doka a gun malamai, ya kamata ki samu Jibiya ta koya miki tun kafin a gama raina ki. "

Nafi ta jinjina kai cikin farinciki tace " Nagode Ferry. "

Ferry ta harareta tace " karkiyi tunanin sanki nake yanzu, ni bana kawa da wacce bata kile ba, bana kawa mara kwalliya, ba kuma na kawa mara aji. "

Nafi ta sauko daga sama tace " Ferry nikam kina burgeni wlh, duk da ba kulani kike ba inasan tsarinki yana birgeni. "
Ferry ta d'aura towel sannan tace " abinda yake b'atamin rai kenan da mata irin ku, sam bakwa abin mace, bakwa kwalliya, yanzu kamar ke sam duk abinda mutum zai miki ban taba ji kin d'aga ma wani murya ba, komai sai dai ki bada hakuri, ke ba dutse ba."
Taja tsaki ta zari kwandon wankanta tai waje.

Nafi ta bita da kallo ba shakka abinda ta fad'a gaskiya ne, to amma ya zatai? Bayan haka halinta yake?

A satin nan Nafi har sai da ta rame tsabar karatu kala biyu, ga na lesson d'in da ake mata gana computer, a wannan zaman karatun da jibiya take koya mata anan ta fahimci Nafi batai wani karatu ba ganin duk yanda taso tai pronounce d'in kalmomi abun yake gagara, sai dai hakan yasa ta kara tausayama Nafi sannan ta jajjirce wajen kara koya mata.

Yanzu kam suna 'yar magana sama sama da Ferry.

Sati d'aya ya cika, malam ya kira Nafi gaban black board ya shiga zuba mata tambaya, tambaya 5 ya mata da kyar Nafi ta amsa biyu, wannan dalili yasa Malam ya yanke mata hakunci akan ta dawo gaba kusa da Ferry da zama sannan duk karshen week sati biyu zai dinga mata tambaya.

Nafi kam duk ta rame saboda karatu, sam bata samun damar tunanin gida ko wani abu, sai dai ta rasa dalili duk sanda ta tashi daga bacci sai zuciyarta ta rage mata kwana d'aya akan kwanakin bikin Ashraf.





*A KANO*

An kai lefe sannan anata hidimomin biki, sai dai sam Ashraf abin nan baya gabansa, tabbas yasan a ransa yanasan Aneesa sai dai bayajin wani farin ciki game da wannan auren.

Ita kad'ai take kid'anta take rawarta, duk dinkunansa sai Habib ta samu sukaje suka siyo, sam Ashraf baya walwala bare farincikin wannan auran.

Duk yanda Aneesa taso daurewa karta nunamai jin haushinta sai data kasa tamai magana, sai dai duk sanda tamau magana kanta abin yake komawa, karshe tazo tana bada hakuri.


Gida ya fara taruwa da mutane, little kam sai rawar kai dinkuna tayi yakai kala 10 ta musu kuma anko da Nafi kala 5, murna kam ba'acewa komai agunsu Umma.


Yau saura kwana biyu a fara hidimomin biki Mumy ta kira Ashraf zuwa falonta, bayan ya zaunane Mumy ta kalleshi cikin kuluwa tare da tattara hankalinta kansa, ta fara magana cikin kulawa " Ashraf yau saura kwana biyu a d'aura maka aure da 'yar uwarka."

Ashraf kansa na kasa sai dai baice komai ba, tace " Muhammad! "
D'agowa yai cikin mamaki dan bai tab'aji ta fad'i wannan sunan ba d'an sunan baban mahaifinsa ne.

Mumy ta kalleshi tace " kayi hakuri abinda na maka. "

Kallan mamaki yake binta dashi, yace "name? "

Ta kalleshi idanunta a raunane tace " Ashraf na sani sarai abinda na maka shekarun baya masu yawa shine yasa ka zama haka, sam bakasan 'yan uwanka, kanka kawai ka sani, ba ka tunanin maganar da zaka fad'a ko zai b'atama wani rai. "

Ashraf dai kallanta kawai yakeyi, Mumy tai ajiyar zuciya tace " bazaka tab'a fahimtar me yasani na auri kanin mahaifinka ba daga rasuwar Abbanka ba har sai lokacin da kasan komai na gidan nan da kuma abinda ke cikin zuciyar kowa na gidan nan. "

Ashraf da mamaki yace " Mumy. "

Ta sakar masa murmushi tace " na sani nayi laifi a gareka, na rashin sanar dakai komai danai har sai sanda aka haifi Little, sai dai inaso ka sani komai nai a rayuwa to tabbas d'an kai nayi shi, ban tab'ayin wani abu dan in farantawa kaina rai ba, a ko da yaushe kai nake fara sawa a gaba akan komai na rayuwata kafin inyi tunanin kaina. "


Shiru tai sai dai ta kawar dakanta gefe kad'an alamar so take ta b'oye kwallar ta, Ashraf kam kalaman Mumy sun tab'ashi sai dai haryanzu gani yake koma meye dalili shi bai fahimci dalilin auranta da kanin Abbansa ba."

Mumy ta d'anja hanci sannan tace " Mahaifinka na tsananin san kaninsa, sannan babban burinsa bai wuce yaga ya had'a zuri'a dashi ba, nasani da yana da rai sai yafi kowa farin cikin wannan abun duk da yasan shi kanin nasa ba sanshi yake ba. "


Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace " Mumy me kike nufi da basanshi yake ba? "

Mumy tai murmushi tace "la ba haka zan fad'a ba subutar harshe nai. "

Ashraf yai shiru sai dai tabbas yasan da wani abu.

Mumy tai saurin wayancewa da cewa " Ashraf kasan me ake nufi da aure ba sai na sanar dakai ba dan Allah ka rike matarka yanda ya dace, Aneesa na sanka kowa ya sani. "

Ashraf bai amsa hakan yasa Mumy tace " Ashraf maganar aiki. "

Kallanta yai sannan ya daure yace " Mumy me yasa kike so im fara aiki a company d'in Abba? "

Mumy tace " saboda hakkinka ne."

Ashraf yai murmushi yace " idan na fara aiki a wani matsayi kawu zai zauna? Sannan ni a wani matsayi employees na company d'in zasu d'auken?"

Mumy da mamaki tace " Ashraf me kake nufi? "

Yai murmushi sannan yace " zan fara aiki a company d'in Abba sai dai bawai a matsayina na magaji ba inasan ne in amshi hakkina da kokarina bawai dan ni d'an Abba bane. "

Mumy ta jinjina kai tace " kana nufin zaka fara aiki a company d'in daga farko? Tun daga kan interview?"

Kai ya d'aga Mumy tai murmushi lalai ta yaba da tunanin d'an nata ta sani sarai dama yanada hangen nesa sai dai bata tab'a tunanin zaiyi tunani haka ba.




¤¤¤¤¤¤

Nafi ce zaune tana shafa mai Ferry ta kalleta tace " Nafi yau tunda kika tashi naga kamar bakida lafiya. "

Nafi ta kalli Ferry tace " Ferry dan Allah tambaya. "

Kai Ferry ta d'aga mata alamar eh tanaji.
"Yayanane zaiyi aure a satin nan, na rasa meke damuna sam duk sanda na tuna sai inji raina yana b'aci. "

Ferry ta kwashe da wani dariya tace " Innocent Feenah dama haka kike? Oh a ido kamar.... "


Nafi tace " ban gane ba, wani abun ne? "

Ferry ta fara tafi tace " Innocent girl, yayan naki uwa d'aya kuke ko uba? "

Nafi ta girgiza kai, Ferry ta kara sa dariya sannan tace " gaskiya Feena kin tashi daga Innocent kin koma green snake. "

Nafi ta mata kallan mamaki tace " ni na tambayeki abu ma baki amsa min ba kin bige da dariya. "

Ferry tace " Good haka nakesanki in abu bai miki ba ki fito ki fad'i gaskiya, sannan zancen yayanki ai ba komai bane sanshi kawai kike. "

Da sauri Nafi ta mike ta zura hijab d'inta tai waje tana cewa " Ni? Wacce ni? Ni kaza?????





*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*Hi Fans please Vote me on Wattpad As_AyusherMohd*


{ *29*}




Yau ce ranar da za'a fara gudanar da event, da sassafe Little da Habib sukazo suka d'auki Nafi, sunyi murna sosai da ganin juna sai dai Little ta damu da ganin yadda Nafi ta rame sosai, hatta Habib yaga haka, nan suka taho a hanya Little nata tsokanarta akan ta bata labarin makaranta, Nafi kam sai dai tayi dariya kawai.


Haka sukai ta tafiya, Little duk ta isheta da labarin biki, Nafi kam shiru kawai tai sai yake da takeyi, daga kazaure zuwa kano ba wani nisa ne dashi ba amma saboda Little ta kyaleta da zancen bikin nan sai Nafi ta tsiri yin bacci a hanya, hakan yasa Little ta kyaleta sai dai ta maida akalar hirar tata ka Habib.

Har suka iso gida Nafi dai idanunta a rufe suke.
Tunda suka shigo kuwa tasan lalai biki yazo, dan gida ya cika da mutane, nan Habib yai parking su kums suka fito.


Sun fara zuwa b'angaren Mumy suka gaisheta, cikin farin ciki ta kalli Nafi tace " 'yar makaranta kin iso? "

Nafi ta d'aga kai, Mumy tace " kije kiyi wanka kice abinci ki huta dan yanzu kinsan da baki dayawa a gidan hutu bazai samu ba anjima. "

Nafi ta amsa da to fuskarta cikin farin ciki, b'angaren su suka wuce tana isa ta fad'a toilet tai wanka kafin ta fito Little ta d'auko mata kaya a cikin sababin da Ashraf ya mata bata sa ba.

Nafi tai murmushi sannan tasa kaya, taci abinci sosai daj gaskiya tayi rashin abincin gida, ta gama kenan Ashraf ya kira Little a waya, Nafi tanaji Little tace "Hello Yaya! "
Taji gabanta yaa fad'i, jitai Little tace "eh ta dawo." sai kuma taji tace to amma yaya..... "
Jin shiru yasa Nafi tasan ya katse wayar dan shi dama baya jira.
Little tabi wayar da kallo sannan tace " wai kije ki gyaramai d'akinsa, yaba Habib makullin d'akin sannan inkin gama ki ajiye a gunki zai amsa. "

Nafi tai murmushi sannan tace " To. "
Little cikin b'acin rai tace " Nafi bakiji haushi ba? "
Ta kalleta tace name?

Little ta ja wani dogon tsaki tace " yau kika dawo bai tambayeki makaranta ba, sai ya saki aiki? "

Nafi ta d'an harareta kad'an tace " ke kuma menene naki??? "

Little ta kama baki cikin mamaki tasan Nafi indai abu ya mata ko bai mata ba bata tab'a magana sai dai tai kasa da kai, cikin mamaki Little tace " ba komai nawa. "

Nafi ta mike tare da wanke hannu tai waje ranta wasai, farin ciki take zataga Ashraf.


Da isarta b'angaren taga kofar a bud'e sannan ga kayayyaki nan a waje da alama gyara ma ake, nan ta tsallaka ta shiga falo, mata ta gani su hud'u suna ta jera sababbin kaya a falo, Nafi ta gaishesu, sai dai kowa kallanta yake cikin mamaki, wata daga cikinsu wacce kana ganinta kasan kanwar Umms ce ta d'aure tace " Yarinya ke kuma wacece? Kuma me kikeyi a nan. "

Kallansu tai sannan tai kasa dakai, a zahirin gaskiya batasan me zatace ba bata kums san me zata kira kanta ba a gidan nan.

Jitai ance " me kike anan ba aiki yasa ki ba? "

Da sauri ta d'ago ta kalli inda ake magana Habib ne tsaye a bakin kofar d'akin Ashraf, a hankali ta wucesu zuwa gunsa.

Habib ya mika mata makulli sannan yace " gimbiya meye naki na tsayawa? "
Ta kalleshi tace " gaishesu nai. "

Habib ya d'an matso kad'an yace " ki kiyaye kula mutane irin wannan kar abu ya rutsa dake kisani a tashin hankali. "

Da mamaki ta kalleshi, ita zatai abu to shi kuma meye nashi na shiga tashin hankali??? Ta bud'e baki da niyyar tambayarsa kawai taga ya wuceta ya fita.

Bayansa tabi da kallo sannan ta shige d'akin Ashraf ta rufe.


Ba shakka yan jere sun sha mamaki, wacce wannan zataxo ta shige d'akin Ashraf??

Itakam Nafi tana shiga ta cire hijabinta ta shiga gyara, ba laifi d'akin yayi kura, ta dad'e tana gyara d'akin kafin ta nufi toilet, ta wankeshi tas sannan ta wanke towel d'in dake ciki.

Tana gamawa taji bayanta yad'an amsa, murmushi tai har hakoranta suka fito tace wato jikinki ya fara sanyi ko? Ai in a riga ne aikin dayaci uwar wannan ma batajin wahalarsa.

Air freshener ta fesa a d'akin, sannan ta jawo mai d'akin ta kulle tare da zare makullin, sallama ta musu basu amsa ba itadai tai gaba.


Yau Arabian nights za'ai, bayan magrib kowa ya shiga yin kwalliya ta gani ta fad'a, Nafi kam tana zaune tana karatu, Little wacce kawayenta sukazo sunata shiri.

Kallanta Little tai tace " Nafi wai meye hakan? "
Tace " name?"

"kina ganin kowa yana shiryawa amma ke kina zaune sannan ga kayanki nan na fito dasu banga alamar kinada niyar sa wa ba. "

Nafi ta kalli kayan, riga ce da wando sai doguwar riga ce baka (after dress) sai dai an bita da kwalliyar duwatso rigar tayi kyau sosai.

Nafi cikin mamaki ta kallesu, kowa riga da wando yasa yanata kwalliya, tace " Little kinsan dai bazan iya fita a haka ba. "

Little tai dariya tace " muma ce miki mukai a haka zamu fita? "

Ta fad'a tare da ware mata after dress d'in tace "wannan zamusa. "

Nafi tai ajiyar zuciya tace " zakuyi kyau nikam ba dani ba. "

Little ta d'aga wayarta tace " shikenan bari na kira yaya nacemai kince wai ke bazaki iya zuwa gun bikinsa ba. "

Da sauri Nafi ta mike ta kwace wayar, kawayen suka sa dariya.
Nafi tai ajiyar zuciya tace " naji zan saka kuma zani sai dai ina gefe.

Little ta d'aga mata kafad'a alamar wannan kuma ruwanki.

Little da kanta ta zauna ta shiga yima Nafi kwalliya, itakam Nafi bataso gani take kamar ba mai bukatatarta a guri meye nata na wani kwalliya? Nafi tayi kyau sosai, dan zan iya cewa tun datazo birni bata taba yin kyau irin na yau ba, mayafin abayar Little ta nata rolling dashi, tayi kyau sosai da sosai, ba wani kwalliya na kuzo mu gani bane sai dai inkaga Little lalai bazaka tab'a cewa ba a birni take ba.

Dukansu wando Ja suka saka, hakan yasa suka sai takalmi ja flat, sannan yar karamar jakar dake rataye a kafad'arsu ma jaa ce, sunyi kyau sosai dan ankon shigar su kad'ai sukai.

Sun fita reras dasu, Little na rike da hannun Nafi, tun a gida ma duk wanda ya kallesu sai ya yaba musu, nan suka shiga d'aya daga cikin motocin da aka kawo na d'aukar mutane zuwa gun da za'ai event d'in.


¤¤¤¤¤


A can b'angaren Aneesa kam tana can gidan Aminiyarta ankira mai kwalliya tana tsantasara mata, ganin an kusa gamawa yasa ta d'au waya ta kira Ashraf.

Sai data kusa katsewa ya d'aga, cikin salon jan hankali tace " Hubby ka shirya? "

Yace " ku mata ai kune aka sani da shiryawa ni wani shiri zanyi? "
Tai murmushi sannan tace " ka taho ta gidan su Abida sai mu tafi.
Cikin mamaki yace " ban gane ba? "
Ta kara shagwab'e murya tace " ba dama kai zaka kaine ba? Ai tare zamuje gun. "

Yace " So? "
Tace " so shine nake fad'ama ina gidan Abida kazo mu tafi tare. "

Yace " ni na kasa fahimtarki, meye zaisa sai nazo mun tafi tare? "

Mikewa tai ganin yana neman disgata a gaban kawayenta tai d'aki tace " yaya haka fa akeyi. "

Yai d'an tsaki yace " in haka akeyi sai akace dole sai nayi? "

Mamaki ya kamata tace "Yaya ka tab'a ganin Amarya taje gun biki daban ba tare da ango ba? "

Yace " sai a fara a kanki dan ni kam ba driver bane babu kuma dalilin dazai sa inzo in d'aukeki keda kawayen ki bayan inada abinyi. "

Idanun Anisa ne suka canza kala tace "yanzu dai kana nufin bazaka zo ba kenan Yaya? "

Yace " ba wai bazan zo ba gaba d'aya, sai dai zaki iya zab'a in har nazo na kaiki to kuwa ina ajiyeki zanyi tafiyata. "

Aneesa ta furzar da wani iska ta bakin ciki tace " shikenan zamuzo a motar Abida. "
Bai amsa ba ya kashe wayar, bin wayar tai da kallo ranta a b'ace sai dai dan karsu gane yasa ta fito tana zumbure zumbure.

Abida tace " Neesa ya akai? Ko keda Angon ne?"

Ta kara tab'e fuska tace " wai suna tare da abokansa su kuma shine sukace wai inyi hakuri mu tafi dake akwai abinda zasu bashine da bazai samu damar zuwa d'aukana ba. "

Sukasa mata dariya, Abida tace "sai kiyi hakuri ai uzuri ne. "

Aneesa ta harareta sannan ta zauna akacigaba da kwalliya.


An gama kwalliya suka taso suka taho, Amarya tayi kyau sosai da sosai dan maganar gaskiya Aneesa dama kyakyawace.

A gun event kuwa, Amarya ta iso sai dai ango shiru, gashi ba dama ta shiga ta zauna ita kad'ai.

Duk yanda Aneesa ke kiran layin sa san bai d'aga ba.

Little ta taho rai a b'ace ta zauna kusa da Nafi tace " Nafi wlh yaya nema yake ya ja mana magana."

Nafi tace " name? "
Little tai ajiyan zuciya tace " an nemeshi an rasa kuma Habib yace " wlh yana cikin gun nan dan tare suka shigo. "

Nafi da mamaki tace "an kirashi a waya? "
"tun d'azu ake kiranshi amma shiru bai d'aga ba, gasu Mumy can da Umma kamar zasuyi fad'a. "

Nafi wacce duk jikinta yai sanyi tace " a nemeshi mana to ko wani abun ne ya sameshi."
Harararta Little tai tace " yaro ne shi? "

Nafi ta mike da sauri bata ce komai ba kawai tai baya da sauri.

Sauri takeyi tana tafe tana addu'a Allah yasa ba abu ne ya sameshi ba, duk ta gama rikicewa, sai kutsawa cikin kuryar gun ga gun ba kowa sai dai akwai fitilo suma masu d'an duhu.

Nafi tana tafe tana waigewaige, saura kiris ta fa d'a kwata, Allah ya taimaketa sai dai takalminta d'aya ya fad'a, zare d'ayan tai ta rike a hannu.

Ko kulawa batai ba haka taketa tafiya, yanzu kam har gudu take had'awa d'ashi jikake tim.

Kafarta ta bige wani dutse ta fa d'i, mikewa tai batare data dubaba ko kula da kafarta wacce taji ciwo sai jini yake batai ba.

Daga can bakin wani pool ta hango mutum a tsaye ya kurawa ruwan ido, tana ganinshi ta baya tasan shine, da gudu ta karasa inda yake.

Ta tsaya kawai tana hakki, Ashraf ya juyo gabansa jin alamun mutum, Mamaki ne ya kamashi yake kallan Nafi.

Idanun ta suka zubo da hawaye, tasa hannu ta share da sauri tare da cewa " ba abinda ya same ka? "

Kallanta yai daga sama har kasa, kayanta duk sun b'aci, yabi kafar ta yabi da kallo duk jini ya b'ata kafar.

A hankali ya matso daf da ita har tanajin numfashinsa, yasa hannu kamar zai rankwasheta a kai, da sauri ta runtse idanta kam.

Ya girgiza kai batai auni ba taji ya sureta.
Idanu ta bud'e cikin mamaki da tsoro, a can kan kujera wacce ake hutawa in anyi wanka ya ajiyeta sannan ya karasa bakin ruwan ya debo ruwa a hannayensa ya fara zuba mata a kafa.

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*Wattpad As_AyusherMohd*

*Gaisuwa gareku Aminan Arziki Mom Hamra, Mom Farhan, Agra, Mom Farouk and Fresh LUSM*

{ *30*}


Gaba d'aya Nafi ta kasa d'auke ido daga kanshi, har ya gama d'ebo ruwa ya wanke mata duk da rad'ad'in da takeji sai leb'e kawai da take ciza, sannan ya kalli inda ta yanke, sosai gun ya shiga ciki da alama karfe ne ko kwalba ya mata wannan aikin, hannu yasa a aljihunsa ya ciro handkerchief sannan ya d'aure mata gun dashi.

Mik'ewa yai tsaye sannan ya kalleta yace " zaki iya

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment