Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Asim yai shiru kafin daga bisani ya shiga office dinsa, shiru yai yana tunani kafin yace " in nasai company din nan lalai ba karamar garabasa zan samu ba, yanda zan nunama Abba nima na fara abin kaina ba wai dashi na dogara ba."


Ya danyi murmushin mugunta yace " gaba ko Ashraf ya kwace company dinsa nidai inada makafa" wayarsa ya zaro ya duba account dinsa, million 30 ne a ciki kansa ya dafa cikin takaici yace ina zan samu kudi bayan ko rabi bandashi?"

Sauri yai ya kira Anisa yace " kanwata wannan takardun haryanzu sunanan a inda suke?"

Ta mike tare da dubawa tace " eh."
Ajiyar zuciya yai yace " guda nawa ne ma?"

Ta fito dasu tace " da alama ma ya kara wasu a gun da guda biyar ne yanzu kuwa sunkai 8."

Yace " ganinan zanzo yanzu in amsa."

Tace " amma yaya....."

Yace " karki damu bazai gane ba, inma ya gane sai musan karyar da zamuyi ko kuma yau da yamma kiyi kuka ki kirashi kice barayi sun shigo."

Tace "to."

Can kuma yace " a'a ba haka ba yau da daddare zansa a shigo gidan sai ki bar kofar a bud'e muyi kamar yan fashi ne suka zo."

Tace "yauwa hakan dai yafi."

Shiru yai yana tunani dole duk da haka yana bukatar wasu kudin ya tabbata wannan bazai isheshi ba, fitowa yai ya samu Secretary dinsa yace " yana bukatar account book na Company din nan."

Nan yai waje dan amsowa, Asim yai murmushi yace " ko na dau kudin Company ba abinda Abba ya isa ya min."


Nace hmmmm

*********


Nafi kam sunyi waya da Ferry tace " Little ta kaimata kudin, harta je kasuwa ma ta siy musu."

Nafi tace "to ina amarya?"

Ferry tace " tana gun dangin mamanta taje sallama."

Jin ance mamanta yasa jikin Nafi yai sanyi, haka dai sukai ta waya har suka gama, Nafi tana kashe wayar ta kwantar da kanta kan kujera tace " ko ina ni tawa uwar?"







*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*_Gareku 'yan Group d'ina The Queen Bee & Ayusher Fan Club.....Really luv u ol ❤_*

*76*


Ashraf na tasowa daga gun aiki ya wuce ban gareb Mumy, bai sameta a falo ba sai Afra ce tace mai tana d'aki tun jiya batajin dadi, nan ya wuce d'akin.

A kwance take sai dai jin kwankwasawa yasa ta mike ta bud'e, Ashraf ya shigo tare da zama a kasa ya gaisheta, ta amsa a hankali sannan ya kalleta yace " Mumy tambaya nazo da ita."

Gabanta ne ya fadi dan itakam tsoron tambayoyin Ashraf take, ya kalleta yace " gidajen Dady na waye?"

Kallansa tai bakinta yadan motsa kadan tace " wasu nawa ne wasu kuma nashi ne."

Kallanta ya sakeyi yace " asibitin Dady ya akai shima yaje hannunsa?"

Gabanta ne ya fadi ta kallu Ashraf cikin dan rawar murya tace " Mahaifinka ne........"

Katseta yai yace " sanda Abba yaki taimakama Dady har abin yazama ajalin Mahaifinki bakiji haushin Abba ba?"

Kallansa tai sai dai ta kasa magana, Murmushi yai sannan yace " Kince bakyasan kawu saki yai kika aureshi a dole saboda Dady meyasa kina aurensa kika hada zuri'a dashi bayan a fadarki ba sanshi kike ba ga haushin ya yi sanadin mijinki?"

Idanunta ta runtse a hankali hawaye ya zubo mata, Ashraf ya mike tsaye yace " no matter what i can't understand u Mumy, ke kanwar Dady ce, sannan matar Abba ta da sannan matar Kawu ta yanzu, duk inda na duba kina tsakiya."

Mikewa yai jiki a sanyaye yai waje har yaje fali ta fito da sauri tace "MUHAMMAD."

Tsayawa yai jiki a sanyaye idanunsa sun rukid'e, tace " zo."

A hankali ya koma d'akin ta zauna a bakin gadi shikuma ya zauna kusa da ita a kasa,Mumy tace " Ashraf duk na fahimceka sannan koma wanene dole ne indai yanada zarfafa tunani yai mamakin wad'an nan abubuwan."

Ashraf cikin zafin rai yace " bayan mahaifinki ya rasu ba shine dalilinki na fara kula Kawu ba har ya jawo zargi tsakani........."


Batasan sanda ta mareshi ba, bai dago ba sai dai yana ji dole ne ya fada mata abinda zai kona mata rai ko dan ta sanar dashi abinda ke b'oye.

Mumy ta share kwallarta tace " Kana nufin da aure na nai tarayya da kanin mijina? Dan kawai in rama abinda yamin kome?"

Ashraf a ransa yace " kiyi hakuri nima maganar ba har raina na fada ba."
Jin yayi shiru tacigaba " Tunda nake ban taba shakkar wani abu ba kamar ka, gashi dai ni na haifeka amma ina tsoron halayenka na zuciya da fadar magana ta yadda kai ra'ayi, ko Mansir da nasan zai iyayin ko menene a rayuwarsa bana shakkarsa sai dai ina tsoron abinda zai maka."

Kallanta Ashraf yai, tai murmushin takaici sannan tace " tabbas idan nace maka banji haushin Abbas ba alokacin nasan dole bazaka yarda ba ko ince ba ma mai yarda da ni."


Tai ajiyar zuciya kafin ta cigaba " Bayan rasuwar mahaifina ga mahaifiyataba kwance yasa ya Hisham ya kirani cikin fishi yacemin Ruma haryanzu kina tunanin Abbas nasanki?duk abinda ya mana?"

Kallansa nai cikin kunar abinda ya faru sannan nace " Yaya amma......."

Ya Hisham ya katseni da cewa " Abbas dukiyarsa ce kawai ke rudarsa in bakiyi wasa ba nan gaba kadan kema zaki rasa matsayinki a gunsa."
Kalamannan sun tsorata ni matuka wanda yasa na kalli Mansir wanda yake zaune a falon, Mansir yai ajiyar zuciya yace " ke kanwar Hisham ce ta jini dolene ki taimakeshi ya samu ya farfado dan kuwa makarantar da Abbas ya bashi ba abinda zata iya mai."


Na dau kudirin taimakama ya Hisham wanda hakan yasa nabarmai gidajen da Abbas ya dinga bani kadan kadan tun farko da ya sai karamin gida na haya dama ni yaba, tun daga nan yake bani kusan duk shekara.

Bayan naba yaya ne nace zan dawo gida sakamakon hakurin da Abbas yai ta zuwa yana bawa yaya.

A wannan lokacin shine Mansir ya daukoni dan Abbas baya kasar a lokacin.

Ban taba tunanin Mansir ya shiryamin gadar zare ba ya kaini Tahir guest Palace da sunan dauko abu ashe yasa a dau hotonmu a ba Abbas.


Ashraf ya kalleta yace " amma wa yasa?"

Tace " Driver din Abbas yanda yasan in har Abbas ya gani dole yai zargina saboda yasan yaron bazai kai karya ba, sai dai abinda bai sani ba, Mansir da Ya Hisham sun riga sun siye zuciyar yaron."

Tai dan hucci sannan ta cigaba " maganar gidaje kenan."

Maganar asibiti kuma wannan tabbas nasan laifinane dan nina sanar ma yaya zan sa Abbas ya bashi asibitin sai dai a ranar da zan sanar da Abbas a ranar yai hatsarin mota, gashi a lokacin ya Hisham ya gama sanar da matarsa da wasu nashi na kusa akan an bashi asibiti, bayan rasuwar Abbas ne yaya ya samen yace ban kyautamai ba sai dana bari kowa ya sani ashe ni ko fadama Abbas banyi ba.

Jiki na yai sanyi, shine mansir ya bamshawara akan tunda kai yaro ne sannan d'anane ba wani abun bane in na dauka na ba yayana.

Sunje sunsa anyi rubutu irin na Abbas wanda ni kuma nai shaidar hakan.

Kwallarta ta goge tace " Ashraf nasani nayi ba daidai ba sai dai ina tsoron abinda ya samu Abbana ya samu dan uwana, iyayenmu duk sun rasu shi kadai ya ragemub wanda nakeji bazan iya yarda abin duniya yasa in rasashi ba.

Ashraf ya kalleta sannan yace " Mumy kina tunanin saboda kunyi amfani da dukiyar da take gado na nake fadar haka? Ko kadan dukiyar nan bata gabana dan wlh zan iya barinta in dauki matata in bar garin nan, sai dai abinda ke damuna ya zakuyi da zunubin da kuka daukarma kanku? In ni ina raye zan iya yafemuku Abba fa? Ya kuke tunanin Little da Habib zasuji in suka ji komai?"

Idanu ta runtse tace " Nasani munyi ba daidai ba sai dai ba yanda zamuyi tunda abu ya riga ya faru."

Ashraf yai shiru kawai yana kallanta, ta nisa sannan tace "maganar zuri'a kuma dana hada da mansir nasani shine babban kuskuren dana tafka a rayuwa sai dai ya zanyi? Allah ya riga ya rubuta akwai 'ya'ya a tsakaninmu dashi."

Mikewa Ashraf yai ya shafi kansa sannan yace " kujira hukuncin da Kuto zata muku dukanku, banaji zan iya yafe muku dan kun ci amanar Mahaifina sannan hukuncin da za'a muku shi kadai ne zai sa a kama kawu akan babban laifin daya aikata."

Yana kainan yai waje.

Sama ya kura ma ido zuciyarsa na tafasa lalai shikam ya gaji da jin abubuwa kala kala, sai dai yanzu komai ya ware mai kuma tabbas ne ya gurfanar da kawu gaban hukuma ko da kuwa komai nasa zai kare.


************

A ranar kuwa da daddare Asim ya turo 'yan fashi suka sashe takardun nan Ashraf kam ya nuna da gaske yaji ba dadi sai dai a ransa yana mamakin lalai Asim sam kansa baya ja, ace mutum duk yanda aka nemi ayi amfani dakai ba ka wani tunani sai ka bi?


Anisa kam kuka tasa wai ita a dole tana tayashi bakin ciki, ya jawota jikinsa yace " karki damu Nisa sai dai please karki fadama kowa abinda ya faru banasan azo ana kace nace."

Kai ta daga alamar to.

******

Asim yaje ya ga filaye manyan gaske sannan ga gonaki, nan ya ba wani dilallinaka sasu a kasuwa, bai wani tsula musu kudi dayawa ba wanda hakan yasa aka sai dasu cikin kankanin lokaci, ya amshi kudinsa Million 20 cif ya hada da nasa yaga million 50, takaici ya kamashi ganin ko rabi bai hada ba, gun Umma yaje ya mata bayani har ta gamsu itama ta dauko tata kadarar aka harhada aka saida, ansamu an hada 90 million, nan fa ya shiga neman yanda zaiyi ya samu ragowar gashi yaje yaga Company din ya birgeshi sosai wanda ya kara rinjayarsa, sannan ance akwai mutane da sukeso dayawa, nan ya samu Zakari ya bashi 90m yace zai ciko nan da 2dyz.


************


Nafi kam tun daga ranar da Ashraf ya tafi ya barta washegari bayan sunyi waya da Ferry akan shagalin biki Ferry take tambayarsa Ashraf, Nafi tai ajiyar zuciya tace " Ferry sam yanzu ya canzamin, jinake zuciyata kamar zata fashe."

Ferry tai tsaki tace " wato nema kike ki koma Nafi ko?"

Cikin mamaki tace " bangane ba."

Ferry ta kara ja mata tsaki tace " kin manta yanzu Feenah kike ba Nafi ba? In ya canza miki kema ki canza masa an fada miki kowani namijine yake so yaga an like masa?"

Nafi tace "Ferry bazaki gane bane yaya na cikin......"

Ferry tace " ni kin bani kunya ma wlh shiyasa yake miki abinda yaga dama tunda kin gama nunamau shine rayuwarki gaba d'aya."

Nan ferry tasata a gaba da fada.

Tundaga wannan rana Nafi bata kara bari sun hadu da Ashraf ba, sai dai tana ganinsa a b'oye ganib hankalinsa kamar a kwance yake yasa itama ta kara kwantae da nata.



**********


Yau Ashraf na zaune a office Salin ya kirashi ya sanar dashi tabbas Auwal Max an ganshi yanzu ma suna tare da wanda yasa ya nemoshi suna hanyar zuwa kano tare.


Dadi sosai ya kama Ashraf ya kira dan sandan nan abokinsa yace " ka nemomin Dan siyasan nan dana ce maka?"

Yace " haryanzu dai ranka ya dade ba labari."

Ashraf yai ajiyar zuciya.

Nan sukai sallama, Ashraf ya kalli Dan Litti dake tsaye yace " ana azahar kazo mu tafi."

Yace " ok sir, amma maganar Asim."

Ashraf ya kalleshi yace " ya? Ya d'ebi kudin company din?"

Dan litti yace " inaji dan d'azu Zakari ya kira yace yakaimai cikon kud'in."

Ashraf ya hada hannayensa yace " good, kace ya bashi takardun company din ya kuma yi signing."

Dan litti cikin mamaki yace " amma in akai haka ba a bashi company din ba?"

Ashraf yai murmushi yace " ai dama so nake ya zama nashi."

Dan litti yamai kallan mamaki sannan yace " ko da yake Ina ni ina sanin abinda Kake tunani?"

Dariya sukama juna kafin Dan Litti ya fita.



Nace Hmmm


*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*77*


Ana azahar Dan Litti yazo suka fita shida Ashraf, gidan Salim suka wuce.

Falo suka nufa inda Salim yace musu Auwal max na ciki, Ashraf ya kalli Dan Litti yace " dole ne ka hade rai ka maida abu serious."

Dan litti ya jinjina kai sannan suka shiga.

Ashraf da sauri ya isa gun Auwal ya kama hannunsa cikin nuna tsananin kulawa yace " Uncle kana lafiya? Badai abinda ya sameka ko?"

Auwal cikin tsananin mamaki ya ke kallan Ashraf.

Ashraf yace " ko ba Auwal bane?"

Yace " nine Auwal Max"

Ashraf ya zaunar dashi sannan ya zauna a gefensa ya kama hannunsa yace " nine Asim, babban d'an gidan Mansir."

Sai a lokacin Auwal ya saki fuska, Ashraf ya kara rike hannun sa Yace " Abba ne yace in tabbata na samoka kafin Ashraf ya fara samunka."

Auwal yace "Ashraf D'an....?"

Ashraf ya karasamai " dan Abbas marigayi."

Idanu Auwal ya zaro cikin tsananin tsoro yace " ya akai ya sanni?"

Ashraf ya dan saki fuska cikin yanayin damuwa, Dan litti yace " bincike yake akan abinda ya faru a baya."

Auwal cikin tsananin rud'ewa yace " inalilahi ya zanyi? Nikam na shiga uku, banda masifun da suke afkuwa akaina yanzu kuma wannan?"

Ashraf ya kalleshi yace " karka damu Abba yace inkula dakai sannan yace in tambayeka ranar meya faru? Har dakai akai hatsarin ko yaya?"

Auwal ya kalli Ashraf yace " mantawa yai? Ai na sanar dashi komai."

Shiru Ashraf yai yana tunani, sai jin Auwal yai yace " bayan mun shiga mota ai ko layin bamu fita ba na sa matata ta kirani a waya akan batada lafiya dan nasan yallabai zai barni, aikuwa tana kira yace inje shi bari yaja motar, da alama dai Mansir ya manta da hakan."

Ashraf yai dariya yace " da alama kasan yanzu abubuwa sunmai yawa dole ne mantuwa ta dinga shiga."

Auwal ya jinjina kai, Ashraf yace " amma ai ba wata hanya da Ashraf zai gane kaine ka lalata birkin ko?"

Auwal yai shiru yana tunani kafin daga bisani yace " kai, babu sai dai in mahaifiyarka."

Cikin mamaki Ashrad yace " Umma?"

Auwal ya jinjina kai yace " ita kadai ce ta ganni lokacin da nake aikin, bayan ita gaskiya ba kowa."

Ashraf yai murmushi yace " ai bakomai indai Umma ce, amma Dady fa?"

Auwal yace "Dady?"

"Hisham nake nufi."

Auwal yai dariya yace " shi ai bashi ya sani ba shine dai ya bani kudin aikina."

Ashraf yace " nasan wannan wai nufina baku kara haduwa ba?"

Auwal yace " ina zanganshi nida na koma garinmu?"

Ashraf ya kara rike hannunsa yace "karka damu Abba yace inkula dakai ba abinda zai faru."

Auwal yai ajiyar zuciya sannan yace "tunda na taho gabana ke faduwa sai yanzu hankalina ya kwanta."

Ashraf yamai murmushi.

Auwal ya kalli Ashraf yace " Amma kafi kama da Abbas, sam baka kama da mansir."

Ashraf ya shafi fuskarsa yace " duk ba jini d'aya bane su? Kowa haka yake cemin wai nafi kama da Marigayi, shikuma Ashraf din inka ganshi abin mamaki kamarsu d'aya da Abbana."

Auwal yace " ikon Allah, ai nikam bazan taba mantawa da Abbas ba, naci amanarsa na yaudaresa shiyasa nake ganin ishara kala kala."

Ashraf yace " karka damu ka kwantar da hankalinka."

Auwal ya daga kai.

Ashraf ya kalli Dan litti yace " ka maidashi gidana na Darmanawa."

Dan litti ya amsa da to, sannan ya kalli Auwal yace muje ko?
Ashraf ya mikamai kudi yace kasai mai abinda zai bukata na nan da sati d'aya.
Kallansa Auwal yai yace "har sati zanyi anan?"

Ashraf yace " tsoro nake kar mu maidaka Ashraf ya sa a kamaka."

Jin zancen kamawa yasa yace "to ai ba laifi satin ma."

Nan sukai waje Ashraf ya bishi da wani kallo na takaici, sannan ya zaro wayarsa dayai recording ya sa a computer ya yanke maganar daga inda yace " _Nine Auwal Max_"


Ya tura ma Kawu da d'aya wayarsa.


Kawu wanda ya fito daga meeting kenan ya ga anturo mai email yana bud'ewa yaji muryar Auwal da abinda yace.

Mamaki ya kamashi, meye hakan kuma????


Bai kawo komai ba yai gaba.

Salim ya kalli Ashraf yace " amma kana tunanin zaiji wani abu dan yaji suna kawai?"

Ashraf yai wani murmushi yace " it won't be fun in na turamai komai a lokaci d'aya, so nake naga yanda hankalinsa zai fita daga jikinsa a kowace rana, yana wannan case din ga kuma na d'ansa."

Salim ya dafa Ashraf yace " U are very smart Ashraf sai dai please kayi a hankali dan ina tsoron wannan kawun naka."

Ashraf yace " karka damu Uncle, sannan ina tunanin Mumy ne, in barta anan ko inkaita wata kasar, kar ya hanani komai saboda ita."

Salim yai shiru sannan yace " tabbas kayi tunani dan kuwa zai iya cewa zai mata illa inkaki bin umarninsa."

Ashraf yace " shi nake tsoro."

Uncle yace " ka sata kawai ta tafi umara, taje ma ta nemi yafiya tai ibada ko ta samu rangwame."

Ashraf yace " nagode Uncle."

Nan ya fito.


**********


Su Asim an mallaki company murna a wannan rana ba'a magana, dashi da Anisa da Umma da sauran kannansa sunje sunga guri kowa ya yaba sannan ya kira mahaifinsa ya sanar dashi.

Mamaki ya kama Kawu a ina Asim ya samu kudin siyan Company? Sai dai haka ya karasa company din dan tabbatarma idanunsa.

Mamaki sosai yakeyi ganin wannan katon guri wai mallakin d'ansa ne, ya kalli Asim cikin zargi yace " ina ka samu kud'i?"

Asim yai shiru yana tunanin karyar da zaiyi, sai dai kafin ya furta komai sai ga wasu mutane ne nan su hud'u sanye da kayan 'yan sanda sunzo kusa da Asim.


Nan fa kowa ya matso ana san ganin menene.

Na gabansu ya zaro id card dinsa yace " I am Sergeant Kabir."

Asim ya mai kallan banza yace " me ya damen da sunan ka?"

Ankwa ya ciro yace " u are under arrest."

Asim ya kalli Kawu sannan ya kallesu yace " ban gane ba, me nai?"

Kabir ya cafki hannunsa ya fara kokarin sa mai ankwa Asim na turgewa.

Kawu ya rike hannun Kabir yace " me yai?"

Kabir yace " an kai kararsa akan d'eban kudin company dayai "

Kallan mamaki Kawu yama Asim yace " me kenan?"

Asim ya shiga jijiga kai yana cewa " Abba ba Company dinmu bane, ai ba wani abun bane in na ranci kudi a ciki."

Hankalin kawu ya tashi yace " ku tsaya ayi magana."

Kabir yace " i am sry sir, bayan wannan yana dauke da laifin satar kayan da ba nashi ba."

. Asim cikin rud'ewa yace " mena sata kuma?"

Kabir yace " filayen daka saida takardun ba na gaskiya bane bayan kuma ka riga ka amshi kudin mutane."

Asim ya rikice ya kalli Kawu yace " Abba."

Kawu wanda gaba d'aya yama rasa abinyi yace " yanzu me kuke bukata?"

Kabir ya karasa datsamai ankwa yace " am sry sir dole ne ya biyomu."

Yana kai nan yaja hannun Asim.


Umma wacce ta saki wani ihu tare da bin bayansu tana kira sai dai ina.....Sunyi gaba, Anisa ma kuka take sosai, Umma ta matso gun Kawu ta rikemai kwallar riga tace " malam ka wuce ka amsomin d'ana."

Kawu ga runtse ido cikin takaici, Umma ta kara rikicewa tana masifa.

Kawu ya fizge jikinsa yace " me yasa kwatakwata kwakwalwar yaron nan kamar ta kifi take? Bashida hankali ne ko me? Ke ma kina ina da kika kasa bashi shawara,?in har bazaki iya dashi ba ai sai ki sanar min, yanzu wani irin abune wannan?"


Ya fada cikin tsananin takaici.



Nikam nace 🤷‍♀ ko a jikina.
Lol masoyan Asim amin afuwa, duk da banaji yanada masoya.....Lol





*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*78*


Asim kam duk ya gama rikicewa sai rokon Kawu yakeyi, Umma kam kuka kawai takeyi tana itadai a anso mata d'anta.

Sun isa police station akasa Asim a wani dan karamin d'aki dan yin bincike kafin a rufeshi.

Kawu ya karaso a tasa motar ya umarci a barshi ya fara magana da Asim, ba musu kuwa suka barshi.

D'akin ya shiga ya kalli Asim yace " ina kasamo filayen gidaje da gonaki haka?"

Gabansa ne ya fadi, ta ina zai iya cewa satarsu yai? Cikin rawar murya yace " siya nai."

Kawu ya bugamai wani kallo yace " Asim kana wasa dani, wlh akan kai kadai bazan yi asarar abinda na tara da kyar ba, zan iya yanke tsakanina dakai in har naga kana neman zubarmin da kemata."


Asim ya kara rikicewa yana rokon Kawu akan yai hakuri, kawu yace " kasan nawa kaci kudin company kuwa? Banda zubarmin da mutunci dakai, dole haka nan nizan yi kashin wad'an nan kudin, kafi kowa sani dukiyar Abbas a karkashin Ashraf take ba ni ba ai."

Asim ya sauka kasa ya rike kafafun Kawu yace " Abba dan Allah ka taimakeni, bazan iya zama a wannan gurin ba, kafi kowa sani kaf 'ya'yanka bamai maka biyaya dayin abinda kakeso farat d'aya kamar ni, saboda haka ko aure ban taba sha'awar yi ba karma matata tazo tanemi samin wani ra'ayi."


Abba ya kwace kafarsa da karfi wanda hakan yasa Asim fad'uwa, yace " na rasa wace irin kwakwalwar tumakai gareka, mema ya kaika siyan wani company? Meka rasa na rayuwa?"

Asim kuka kawai yake yana rokon kawu, kawu ya nunashi da yatsa yace " wannan damuwarka ce da alama zaka ziyarci prison."

Yana fada yai gaba yakai wajen kofa Asim yace " wato ka gama shan mangwaro shine kakeneman yadda kwallan?"

Kawu ya juyo ya kalleshi, Asim yace " me kake tunani Abba? Bansan komai game da kai ba? Nafa sani kaine ka sa aka lalata birkin Ashraf a sanda ya b'ata, ba kasheshi kaso kai........."


Kawu ne ya matso cikin zafin nama ya toshemai baki tare da jinginashi da bango, yace " bakada hankali ne? Me kake fada haka?"

Asim ya dan shiga kakari saboda yaji matsar, Kabir da yake zaune yana kallo da jinsu a d'akin da ake ganin komai through computer ya mike tare da kallan su ya kashe abin CCTV din da microphone din sannan ya kira Ashraf ya sanar dashi komai.

Wani Murmushi Ashraf yai yace

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment