Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidansa abincin ma dazasuci nema yake ya gagaresu.

Da yake Ruma na gidan ita ta kira Abbas ta sanar dashi halin da ake ciki nan ya je bankin ya biyasu kudinsu sannan makarantar da yake masifar so ya mallakama Hisham duk dan ya farantamasa, sai dai kwanansa d'aya da bashi makarantar Allah ya d'auki ran Abbas."


Ashraf yai shiru kafin daga bisani yace " asibitin fa?"

Salim yai ajiyar zuciya yace " Ashraf wannan sai bayan rasuwar mahaifinka sukazo min da takarda akan Abbas ya mallakama Hisham asibitinsa da aka gama ginawa ko fara aiki ma ba'ai ba."

Ashraf cikin rashin fahimta yace " ta yaya ya bashi makaranta mai girma irin wannan ya sai mai gida sannan ya kuma bashi asibiti?"

Salim ya kalli Ashraf yace " nima da naki yarda da bada takardun asibitin to amma abin mamaki rubutun mahaifinka ne."

Cikin fada Ashraf yace " zasu iya sa expert su kwaikwaya ai."

Salim yace " yes shiyasa naki yarda sai dai mahaifiyarka itace tace tabbas Abbas ne ya rubuta."

Shiru Ashraf yai kafin yace " gidajensa fa?"

Salim yace " bansan wannan ba gaskiya sai dai bayan mutuwar Abbas naji jita jita akan bai daina safarar bindigogi ba zai iya yiwuwa da su ya siya ko kuma gadon Ruma ne."

Cikin mamaki Ashraf yace " gadon Mumy?"

Salim yace " ban tabbatar ba amma tunda kace gidaje dayawa nasan tanadasu dan Abbas tun yana da rai yake siyan gida da sunanta sannan da ya rasu aka bata gadon wasu."

Ashraf yai shiru baice komai ba, Salim ya dafashi yace " Ashraf mahaifinka burinshi kai rayuwa mai dadi ba wai ta wahala da kunci haka ba."

Murmushi Ashraf yai yace " Uncle kana tunanin zanyi rayuwa mai dadi bayan duk 'yan uwana makiyan Abba da ni suna zagaye da ni?"

Salim baice komai ba sai kallan Ashraf dayake yi.

Ashraf ya sake murmushi yace " ka binciko min inda Auwal Max din yake?"

Salim yace " eh to wanda yake binciken yace yana zariya sai dai yace in kara mai 1day ya tabbatar da shi din ne."

Kai Ashraf ya jinjina sannan ya mike yace " kace kafin Abba ya rubutawa matata wasiya munyi tafiya zuwa wani kauye dashi ko?"

Salim ya jinjina kai yace " kwarai kuwa saboda bazan manta lokacin ba nayi mamaki kwarai daya kawon wasiyyar da daddare."

Ashraf yace " Malam Mahmud ko?"

Salim ya daga kai alamar eh.

Ashraf yai godiya kafin yai waje.

Mota ya fad'a ya d'aga wayarsa sakon Nafi ne yaga ya shigo kamar haka " _Yaya dafatan kaci abinci?_"

Ya dade yana kallan sakon kafin ya ajiye wayar ba tare da ya mata reply ba.


Makaranta ya wuce, yai sa'a kuwa yana zuwa Malam na kokarin fita, nan ya ajiye mota ya karasa suka gaisa, Malam yai murmushi yace " Muhammad daga ina haka?"

Ashraf yai murmushi yace " gaisawa nazo muyi."

Malam yai dariya yace " nagode da baka manta da wannan tsohon ba."

Nan sukai dariya, Malam yace " Ina Matar taka?"

Ashraf yace " tana nan."

Malam yace " yarinyar fa nake nufi."

Ashraf yadan sosa keya.

Malam yai murmushi yace " da alama tana nan."

Ashraf ya kalleshi yace " malam tambaya nazo da ita."

Malam yace " Allah g yasa na sani."

Ashraf ya nisa sannan yace " kafin Abba ya rasu munyi tafiya ni da kai da shi ko?"
Malam yace " Hakkun."
Ashraf yace " Malam zaka iya tuna abinda ya faru a lokacin?"

Malam yai murmushi yace " shekarun da yawa na dai san munje zagaye da taimakon bayin Allah dake!d� bukata, wannan shine tafiyarsa ta karshe."

Ashraf ya jinjina kai yace " ba wani abu na mamaki da ya faru game da ni?"

Malam yai shiru kafin yace0"`|abbas aKw�y na tuna, abinda ya dade yana bani mamaki."

Ashraf ya kalleshi cikin zakuwa da sanjmn0oenene.


Malam yace " mu shiga ciki."


Nan suoa0lufi mckisantar.


**********

* �Iau Datti yanq 4{qk)qar bqc#a ya tashi cikin fhr�ice tare da kwallama Nafi kira, sai kuma ya saki wani irhn�kuka mai Ba�0tausayi.

Yayansa ya shigg D#akin a tsorecu"ganin tsakar dare ne gashi ya tashi mutane da dama.


* �Tatti yana kuka yana cewa " a kiramin Naf) d@n Allah ku taimaken ku kiram)n oafi."

Yayansa ya shiga mA��rashi yanA �u7a Jai shiru Datti da alama ka samu lafiya tunda ka fara magana.

Sai dai ina Datti kam abin ya canza salo daga!k�ka sai a kira masa Nafi kaaI$yake cewa.

�anbru�a shiga tambayarsa a wani gari N�fi, take a kirata?"

Kai�ka5ai ya g)rgHxawa alamar bai sani ba.

Mamaki da �so0o ya kamaSu.

Mahaifiyarsa dake kwance ba lafiya tace "kila saidata yai saboda tsabar san kudinsa nikam na shiga uku na."


Datti kam cewa yake a kira masa Nafi......


Nace ta yaya kenan?🤔



*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*72*


Bayan sun zauna Malam ya kalli Ashraf wanda ya nutsu yana kallansa.

Ashraf ganin Malam na kallansa baice komai ba yace " Malam ya akai?"

Malam yai murmushi yace " tunowa nai lokacin da mukai wannan tafiyae bakafi dan haka ba " ya fada yana gwada tsayin Ashraf a lokacin.

Ashraf yai kasa dakai yana murmushi.

Malam yace " A wannan rana munje kauyuka da dama na kusa da na nesa, a karshe muka isa wani gungurmin kauye, wanda 'yan garin kana ganinsu kasan suna cikin tsananin wuya da talauci, nan muka isa gun mai garin aka tara 'yan garin aka fara basu sadaka, kaima kana mikawa.

Gun yayi cunkoso wanda ya janyo turereniya agun, wasu suka dinga faduwa saboda karfin da kowa yake gwadawa.

Ganinka mukai kabar gun rabon da dan gudunka.

Nan Abbas ya leka ya ganka gaban wani bawan Allah, tsoho ne tukuf gaba d'aya gashin kansa fari ne ya tsufa sosai, wanda aka tureshi garin rigima ya fadi kasa.
Da saurinka ka karasa kana neman d'aga mutumin, tsohon wanda kowa yake kyararsa sai cimai mutunci akeyi.

Nan Ashraf ya taimakamai ka maidashi gefe, wani mutum ne ya jawoka yace " kai yaro ka raba kanka da wannan tsohon maye ne."

Ashraf ya kalleshi shikam yarinta baisan ma me ake nufi da maye ba ya koma gunsa tare da d'auko abin sadaka guda biyu ya kaimai.

Duk inda Ashraf yai sai mutumin nan ya bishi da kallo wanda hakan yasa muma jikinmu yai sanyi.

Bayan kowa ya watse mutumin nan na nan a zaune ya taso dakyar yazo gun mu.

Abbas ya kalleshi yace "Baba lafiya?"

Tsoho ya kalli Ashraf wanda ke gefe yana alwala ya kalli Abbas yace " kaine babansa ko?"

Cikin mamaki Abbas yace " ya akai ka sani?"
Tsoho yai danyi dariya sannan ya kara kallan Ashraf ya kuma kalli Abbas yace " kwanakinka basu da tsayi, ko ince kwanakin ka sunzo karshe."

Malam cikin b'acin rai ya kalli tsoho yace " kai miye hakan? Ta yaya zakazo ka samu mutane ka dinga fadamusu zancen banza haka? Kai Allahn masaru ne?"


Tsohon ya girgiza kai sannan yace " ko d'aya ba kuma na fada bane dan ranka ya b'aci ba sai dai kanada makiya dayawa na jikinka kuma."

Abbas ya kalleshi cikin shakkun kalamansa tabbas yasan yanada makiya amma bayasan aminta da maganan wannan tsohon da ya kai kusan shekara 100.

Tsoho ya kalli Ashraf yana murmushi yace " kayi dacen d'a sai dai rayuwarsa zata zama a kewaye take da makiyansa."

Abbas da Malam kawai kallan tsoho sukeyi, tsoho yacigaba " sai dai akwai farinciki a rayuwarsa in har ya rike matarsa ta farko, in kuwa ya rabu da ita banaji akwai wani farinciki da zai samu a rayuwarsa."

Abbas ya mike cikin mamakin mutumi yace " malam wani irin zance kakeyi haka? Tayaya daga ganin yaro zaka fara cewa wai ba farinciki a rayuwarsa? Kasan me kake fada kuwa?"

Tsoho yace " kamar yanda makiyanka na jini basa sanka kana tunanin zasuso d'anka?"

Yana kainan ya juya zai tafi sai kuma ya kara juyowa yace " D'anka zai zama abin alfahari ga mutane, matar da zai aura ta farko itace zata zamar mai farincikinsa nan gaba."


Yana kainan yai gaba, Abbas ya bishi da kallo kafin cikin tsoro yabi bayan mutumin sai dai babu shi ba alamar sa.

Mai gari dake zaune yanajin komai ya kalli Abbas yace " Mutumin nan da kake gani ba wanda ya sanshi, shekararsa kusan d'ari ba aure ba zuri'a ba komai, ba wanda yake kusantar ko da magana dashi ne, sannan abun tsoro ga mutumin in dai ya fadi abu to fa sai dai wani iko Allah, shiyasa muke tsoron harka dashi, wasu sunce maye ne, wasu sunce baiwa gareshi wasu sunce kambun baka wasu sunce aljani ne, a zahirin gaskiya kowa da abinda yake fada sai dai Allah ne kadai masani."


Malam ya kalli Ashraf wanda gaba d'aya shi hankalinsa nakan Malam.

Malam yai murmushi yace "munyi mamaki kwarai da abin al'ajabi na wannan tsohon sai dai abinda ya tsoratamu shine mun gama sadaka muna kokarin tahowa aka sanar da mai gari mutuwar wannnan tsoho."


Idanu Ashraf ya zaro yace " muna garin ya rasu?"

Malam yai ajiyar zuciya yace " ban taba ganin abin al'ajabi irin wannan ba."

Ashraf yai shiru yana kallan malam.

Malam yace " shiyasa dakazomin dazancen rabuwarka da matarka ta farko naki aminta saboda inaji a jikina itace farin cikinka, bawai dan na yarda da abinda wani bawa na Allah ya fada ba sai dai shi dan Adam Allah ne kadai yasan baiwar dayama kowa."

Ashraf yai shiru kafin daga bisani yace " to inkuma da ace Anisa na fara aure fa?"

Malam yai murmushi yace " shiyasa nacemaka baiwar dan Adam Allah ne kadai yasan yawanta, dama can Allah ya tsara ba ita zaka fara aura ba."

Ashraf yai shiru, tunaninsa ya tsaya cak.

Malam yace " muje inada gun zuwa."

Ashraf ya fito jiki a sanyaye ya shiga motarsa, idanunsa ya lumshe a zuciyarsa yace " kaddarace ta kaini kauyen garinsu, shi dama d'an adam rayuwarsa a tsare take."

Sako ne ya shigo wayarsa ya d'aga wayar ya karanta kamar haka " _yaya inasan zuwa gidansu Ferry in ka bani izini, sannan zan kai mata kudin anko_"

Kallan sunan daya sa mata yai Baby Feenah, a hankali ya goge sunan ya maidashi Nafisa.


Yana kallan sunan daya canza mata ya furta a fili, I Am sorry Nafisa sai dai wannan ce hanya kadai dazaisa inyi fooling din kowa, inhar na sanar dake plan dina ba zakiji pain ba akan abinda zanyi sai dai hakan zai sa a gane ba gaskiya bane.

Yai ajiyar zuciya tare da cewa " I am sorry for using u."

Mota ya tada sannan yai gaba.

Gidansu Habib yai ya tsaya a wajen gidan ya kurama gate din gidan ido, bakincikinsa yanda yakesan Dady da Habib, yanda yakesan kannen Habib, ya kara kallan gidan yace " Dady kaci amanata."


Ya dade kafin daga bisani yaja motarsa yai gaba.

Gida ya wuce, direct bangaren Umma yai, Umma tanajin sallamarsa mamaki ya kamata cikin zumudi.


Bayan ta bud'e ya shiga kamar yanda ya saba fuskarshi a daure.

Zama yai sannan ya kalli Umma tare da gaisheta.

Umma ta baje baki tace " Ashraf yau da kanka?"

Kasa yai dakai yace " Umma hakkinane ai."

Ta kara washe baki yace " Anisa fa?"

Tace " tad'an fita dazu."

Murmushi yai yace " ok ba damuwa bari na wuce."

Tace " a'a ka zauna insa a kawoma abinci."
Ba musu ya amince da hakan."

Da sauri Umma ta fita kamar ya sani sai ta sanar da Mumy, yana zaune kuwa ya fara cin abinci kenan sai ga Afra.

Ta gaisheshi sannan yaga ta juya, ya sani mumy ce ta turota akan ta tabbatar ko yana can d'in.


Ashraf yai murmushi ya cigaba da cin abincinsa.

Ya kusa gamawa sai ga Asim.

Asim mamaki ya kamashi cikin tsananin mamaki ya karaso yace " Kai kuma me kakeyi anan?"

Ashraf ya kalli Umma.


Da sauri Umma tace " ni nace ya zauna yaji abinci."

Asim ya mata kallan mamaki, kallansa tai tamai alama da yaje d'akinta.

Nan yai gaba ta bishi a baya suka rufo kofa.

Ashraf ya mike ya bi bayansu.

Asim ne ya kalli Umma yace " Umma meye hakan?"

Tai dariya tace " Asim bansan meyasa kanka baya ja ba yaron nan yanzu ya san matsayin Anisa a zuciyarsa baka tunanin lokacine daya kamata muyi amfani dashi dan jansa a jikinmu?"

Cikin fada yace " mujashi a jikin mu kamar ya?"

Tai dariya tace " yanda zai saki jiki damu har ku gama gano komau kafin musan abinyi akansa."

Asim yai dan tsaki sannan yace " Ni Abba ne ke ban haushi sam yana nuna ni ba komai bane."

Umma ta kalleshi tace " kamar ya?"

Ya kara tsaki yace " share, amma Umma menene a cikin wannan akwatin na kasan d'akin Abba?"


"Shiiiiiiii" tamai alama da hannu tace " bakada hankali ne? Sai an jika? Ni kaina saboda wannan akwatin yasa inaji baya barin matansa sudinga shiga mai d'aki, inaji akwai wani sirri babba a ciki."


Ashraf ya kalli kofar kafin ya juya yai gaba, akwati??? Ya maimaita a ransa.

B'angarensa ya nufa, a bakin kofa ya hango kamar Nafisa, hakan yasa ya had'e rai tamau.

Ko kallanta baiyi ba ya bud'e kofa ya shiga.


Nafi wanda ganin yanda ya shareta kamar shara yasa jikinta ya kara sanyi, yau tun safe ruwan zafi kawai tasha sam ta kasa cin ko abinci.


Ganin ya shiga yasa tabi bayansa, ta ajiye masa tiren abincin data kawo mai akan dinning sannan ta tsaya daga nesa tana kallansa.

Gani tai ya d'auke kai daga kanta kamar baisan tana gun bama.

Har ta bud'e baki zatai magana taga ya mikr ya shiga d'aki tare da rufo kofa.


Hawayen da suka zubo mata ta share sannan ta fito a hankali tai b'angarensu.

A falo taga Little tana kallo, bata ce mata komai ba tai d'aki.

Little ta taso ta shigo tace " Yaya yace kije sannan in zakiyi amfani da kudi ki daina tambayarsa."

Nafita dago a hankali ta kallu Little.
Little tace " wai fada kukai? Akan me zai turob text bayan kinada waya?"

Mikewa Nafi tai ta shiga toilet.

Tsugunnawa tai sai kuka.



*#ASHRAFEEMAH TEAM*


💞

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*73*


Little ta kalli Habin tace " Yaya sai yau fa naganka!" cikin shagwaba tai maganar, ya kalli kofar da Nafi ta shiga yace " Princess nazo ai bamu hadu bane ba kawai."

Ta dan turo baki tace "na kiraka ma baka dauka ba."

Ya hada hannayensa biyu yace " sry mayb ban kula bane."

Ta kalleshi tace " naga sako na gode."

Kallan mamaki ya mata yace " sako?"

Kai ta daga alamar eh tace " eh mana wanda kaba Feenah ta bani."

Shiru yai a ransa yace " au kayan dana bata ma Little taba?"

Bai dawo daga tunaninsa ba Little tace " yaya, bari inje inga Feenah da alama yaya ne ya b'ata mata rai, nayi mamakin ganin ta haka."

Sannan ta karasa maganar a hankali " Naga they get along with eachother very well, da alama fadan masoya sukai."


Ya kalleta yace " Ai Asharaf sai a slow, amma...."

Little ta kalleshi jin yayi shiru, kallan mamaki ya mata yace " me kikace daga karshe?"

Cikin rashin damuwa ta maimaitamai tace " Allah naga tunda mukasan tsakaninsu kullum suke tare da juna."


Cikin tsananin mamaki yace " me kikace?"

Yanda yai maganar yasa jikinta yadanyi sanyi tace " oh bakasan fa ashe matar yaya bace fa ko?"

Gani tai yadan yi baya tare da rike kansa, cikin wani irin yanayi yake kallan Little wanda yasa tasha jinin jikinta, yace " matar wa?"

Kasa maimaitawa tai sai kallansa kawai datakeyi, ganin tayi shiru yasa ya juya jiki a sanyaye yai gaba batare da ya kara cewa komai ba.

Little tabi bayansa da kallo me kenan? Ko dai shock ne irin wanda sukaji da suma suka samu labarin?"

Ciki ta shiga ta samu Nafi ta sauko daga kan gado ta zauna a kasa tare da d'aura kansa a kan jikin gadon.

Little ta matsa kusa da ita tace "matar yaya da alama fada kukai ko?"

Nafi ta kalli Little sai dai batace komai ba, Little tai dariya tace " karma ki fadamin nima ba san ji nake ba, na kuma san goben nan zaku shirya."

Ta karasa maganar tare da mikewa.

Nafi da kyar ta tashi ta watsa ruwa kawai tai sallah ta kwanta, sam ta kasa bacci ita ba wai ganin yanayin da suke ciki da Anisa bane yafi daga mata hankali, kiss din da sukai a gabanta shine ya tsaya mata a kwakwalwarta, ai karama wani abun ce, ta tuna sanda yake ce mata su zauna a shagari su biyu.

Wani dogon tsaki taja tace " kamar irin da gaske ya manta da matarsa din nan."

Sam kasa barci tai sai juyi kawai take, da kyar baccin ya d'auketa.

A b'angaren Ashraf kuwa sun zuba love shida nisa sai dai sam yaki yadda ya kusanceta, ganin ta matso da hakan yasa ya d'an matsa kadan, haushi ya kamata tace " Hubby meye hakan?"

Kallanta yai tare da rike hannunta yace " sry Nisa."

Ta fizge hannunta cikin fushi tace " me? Kana tunanin matarka Nafisa ne ko me?ko kuwa so kake kace baka sha'awar yi dani bayan kayi da yarinya?"

Jawota ta yai jikinsa ya rasa me zaice, baisan sanda yace mata" ba haka bane, banajin dadi ne wanda likita ya hanani saduwa amma inani ina kin matata?"

Nisa ta kalleshi cikin zargi tace " me ya sameka? Sannan naji Umma tace ka kwana da Nafi fa!"

Kara jawota yai yace " zargin Umma ne kawai karki wani sashi a ranki."
Da wannan yasa ta saki ranta, shikuma ya kwanta yai bacci.

Tana gani yayi bacci ta mike a hankali ta bud'e drawer din nan a hankali ta zaro takardun nan tai falo.

Karantasu tai taga tabbas kuwa takardun filayene da wani babban gona.

Tai dariya tace " da alama zan gano komai wannan karan."

Nan ta dau hotunan a waya ta turama Asim, sadi ya kara kamashi tace " yaya in sato su?"

Yace " a'a ki maidasu sai mungama ganin ragowar tukunna karya gane."

Ta jinjina kai cikin gamsuwa sannan ta maidasu a hankali ta koma ta kwanta.

Hankalin Ashraf a kwance ya tashi yai asuba, duk yanda yaso ta tashi tai sallah taki, dama inda sabo ta saba dan bata sallah sai rana ta fito.

Sai daya gama shirinsa na gun aiki sannan ta farka ta kalleshi yana fesa turare.

Mikewa tai tazo ta bayansa ta rungume shi, yai murmushi yace " kun tashi My Neesa?"

Wani irin sanyi ne ya ratsata tace " eh hubby."

Ya juyo da ita gabansa yace " da fatan kinyi bacci mai dadi."

Kai ta daga tace " sosau ma, na dade rabon danai bacci mai dadin haka."

Yai murmushi yace " gud, ni zan fita."

Kiss ta mannamai a kuncinsa tace " sai kadawo."
Kai ya d'aga mata baice komai ba.

Yana fita waje yasa hannu ya goge inda tamai kiss din sannan yai waje.


A waje yaga Asim da kansa ya karasa ya mikamai hannu suka gaisa wanda hakan yai bala'in ba Asim mamaki, Ashraf yai murmushi yace " Asim dama inasan magana dakai."

Asim yace " inaji."

Ashraf yace " kamar ya kamata muwa Kawu magana ya karama matsayi inaganin kamar inda aka maidakai yanzu is too low for someone like u."

Cikin tsananin mamaki Asim ya kalli Ashraf yama kasa magana, Ashraf ya dan dafa kafadarsa da hannu daya yace " barshi in baka so."

Yana kai wa nan yai gaba, da sauri Asim yasha gabansa yace " da gaske kake?"

Fuskar Ashraf a maze kamar yanda yake kullum yace " wasa nakeyi to da?"

Asim ya sa dariya yace " mamaki nake yi ai bantaba tunanin za ka taimaken bane ba ai naga tun muna yara bama wani shiri."

Ashraf yace " ko ba ma shiri ai kai dan uwanane."

Yai gaba abinsa daga fadar haka, Asim yai dariya yace " wai yau me nakeji haka?"

Bangaren Kawu ya nufa cikin zumud'i ko sallama baiyi ba ya tura kofar d'akin, kawu na gaban wannan akwatin, jin Asim yasa yai saurin rufewa tare da turashi karkashin gado da sauri, ya kalli Asim cikin fada yace '" kai wai sai yaushe zakai hankali ne?"

Asim yabi akwatin da kallo sannan ya basar yace " Abba anya kan Ashraf d'aya kuwa?"

Kawu yamai kallan mamaki yace " ban gane ba."

Asim ya matso yace " yanzu wai yacemin ya kamata muma magana ka karamin matsayi wannan matsayin nawa na yanzu is too low for me."

Kawu yai wata dariyar rainin hankali yace " amma ba kada hankali ko?"

Asim cikin mamaki yace " bangane ba."

Kawu yai dan tsaki tare da mikewa yace " Kanaso kacemin Ashraf ne yace ma haka?"

Da sauri Asim ya daga kai, Kawu ya hade rai yace " ba ka cikin hayyacinka da alama mafarki kai."

Asim zai sake magana Kawu yace " mu fita ni."

Haushi ya turnuke Asim yai waje a zuciye, har yayi nisa ya dawo gun Kawu yace " Abba me kake nufi dani?"

Kawu ya kalleshi cikin mamaki ba tare da ya amsa ba, Asim ya cigaba " menene baka yarda dashi ba game da ni? Ni din ne baka yarda Ashraf yayi acknowledging din aiki na ba ko kuwa baka yarda da zan iya wani abun bane?"

Kawu ya kalleshi cikin kulluwa da wannan halin nashi, yace " duka, u always disappoint me."

Yana kai nan yai gaba yabar Asim a tsaye a gun.


Asim yabi Kawu da kallo cikin tsananin takaici da haushin yanda Kawu yake mai.

Kawu kam mota ya shiga cikin takaici.

***********


Nafi kam bayan tayi wanka tana zaune a d'aki ita kadai duk abin duniya ya isheta ta kira Ferry a waya nan sukai ta hira har Ferry ta sanar da ita jarabawarsu ta fito.

Nafi tace " haba?kin dubo?"

Ferry tace " a'a amma ya Nabil yau zai dubo min."

Naf tace " kice ya dubo da nawa "

Ferry tace " to, amma Nafi karfa ki yaudaren kije ki cike wata makarantar ba BUK ba."

Nafi tai dariya tace " karki damu duk inda kike nima ina nan, sai dai in samu ne banyi ba amma ina zani?"

Sun dade suna hira kafin suyi sallama bayab sun gama tsara bikin Jibiya da za'a fara nan

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment