Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi? "

Kai ta d'aga mai idanunta subyi tsuru tsuru, ta d'aga zata mike taji wani zugi a kafarta wanda sai da tayi 'yar kara saboda azaba, baya tai kamar zata koma kan kujera da sauri yasa hannu ya taro ta, idanunsu ne suka had'u da juna, Ashraf ya kalleta sannan yace " bakya gani ne? "

Kallansa tai batare da ta amsa ba, ya girgiza kai sannan yace " taya zaki bari har kiji irin wannan ciwon? "

Kasa tai da idanunta, saukar da ita yai ta koma ta zauna kan kujerar da ta mike.
Harararta yai yace " yanzu ya kike so muyi? "
Tai kasa da kai sannan tace " kaje kai ai jeranka ake ni zan karaso da kaina."

Ta d'auka bazai tafi ba ganin ba yanda za'ai ta iya tafiya, amma ga mamakin ta gani tai yayi gaba, kallansa tai idanunta suka ciciko, ta sukunyar da kanta cikin rashin jin dadi.

Batai auni ba taji kawai an sungumeta, a tsorace ta bud'e idanunta cikin rud'ewa tace " Yaya saukeni dan Allah. "
Ya murtuke fuska yace " kina tunanin bazan iya ba? "

Kai ta girgiza alamar a'a, sannan tace " tsoro nake kar wani ya ganmu a haka."

Wani murmushin rainin hankali ya mata yace " ke dai kina tsoro kar Aneesa ta miki duka."

Nafi tai kasa dakai sannan tace " Allah dagaske nake ka ajiyeni please."

Bai kulata ba ya cigaba da tafiya, sun kusa isa filin gun sai ga Little da Habib sun taho ta gun suna Neman Ashraf.

Daga d'an nesa kad'an Little taga alamun kamar sune hakan yasa ta karaso gun da sauri.

Kallan mamaki ta musu, Habib ne ya karaso gun shima cikin mamaki yace " Ashraf meye hakan? "

Batare da ya kalleshi ba yace " name fa? "

Habib ya kalli Nafi wacce tai tsuru tsuru da ita yace " event d'in auranka fa akeyi? "

Yace " ehen sai me? Abun haramun nai ko me? "

Habib ya kara kallansu, sai dai amsar Ashraf yasa ma ya kasa magana, Little ta daure tace" yaya yanzu in mutane suka ganku a haka me kake tunani? "

Zaiyi magana kenan sukaji ana zabga salati daga bayansu.

Ashraf ya kallesu Umma ce da 'yan uwanta ga Aneesa a tsaye cikin tsananin mamaki.

Ashraf wuce su Little yai ba tare da damuwa ba ya gifta su Umma sannan ya ajiye ta a kan kujera daga baya, sannan ya kalli Umma yace" Umma me kuke anan?? "

"Kan jakar uba, abinda za ka tambayemu kenan? "
Ashraf ya kalli Aneesa wacce ta fara hawayen bakin ciki sannan yace" naga kamar abun yara ne ban d'auka manya ma zasu zo ba. "

A zuciye Umma ta matso tace " me kake aikatawa anan kai da waccan munafukar yarinyar a ranar shagalin bikinka? "

Ya kalli Nafi cikin salon rainin hankali yace " wacce? Waccan yarinyar? "

Umma ta kumbura kam, yai murmushi sannan yace" karamin accident ne ya sameta shine na taimaka mata."

Umma ta kalli Nafi cikin kuluwa sannan ta kalli Ashraf tace " accident? Shi accident d'in bai tashi ba sai a ranar bikinka? Ko dai tsabar kinibibi da muafurci ne hakan? "
Ashraf bai tanka ba ya kalli Aneesa da take kuka, matsowa yai kad'an sannan yace " muje ko mutane na jira. "

Hawayenta ta share sannan cikin b'acin rai tace " Duk wayar danake ma baka d'auka ba dan kana tare da waccan ne ko me? "
Kallanta yai cikin rashin kulawa yace " zakije ko kuwa in tafi? Dan naga kamar lokaci na kawai ake b'atawa anan."

Wata 'yar uwar Umma ta kalli Nafi wacce tai kasa da kanta hawaye kawai takeyi, tace " waccan munafukar ai d'azu muna jere itace ta shiga d'akinsa ba kunya ta dade aciki kafin ta fito, kun tabbatar ba wani abu na masha'a tsakaninsu? "

Umma ta kalli Ashraf sai dai gani tai kamar ma baisan me suke cewa ba waya kawai yake danna wa, zatai magana taga kamar tafiya ma zaiyi.

Da sauri Habib ya rike hannunsa yace " Ashraf ka jiraya mana. "

Hannunsa ya fizge sannan yace " zamanta nake? Ita har takai in mata magana taki tahowa? "

Aneesa ta matso inda yake jiki a sanyaye tace " Yaya amma.... "

Cikin fada yace " amma me? Ba ki yadda dani ba ko me? "

Kai ta girgiza sannan tace " ba haka nake nufi ba. "

Ya kalli su Umma sannan yace " to me kike nufi?"

Tace " ba komai kawai dai dama. "

Tsaki yai sannan yace " inzaki wuce muje to, in kuma bazaki ba ni inada gun zuwa. "

Nan ya fara tafiya, Umma ta maka mata harara alamar kar taje, da sauri Aneesa ta d'auke idanta akan Umma tabi bayan Ashraf da sauri.

Ran Umma ya b'aci sosai lalai ta kosa Aneesa ta auri yarannan insun samu kan dukiyarsa su salwantar dashi dan kuwa bazata iya jurar bakin cikin yaron nan ba.

Kan Nafi suka dawo a zuciye, gashi Habib ya tafi, duk yanda Little ke ba umma hakuri amma inaa idanta ya rufe duka ta shiga yima Nafi ba ji ba gani, itakam Nafi hawaye kawai takeyi.

Gaba d'ayawannan ranar mutane dayawa da bakin ciki suka taso daga gun nan.

Su Nafi suna sauka a mota, Little ta sakala hannunta ta kafa'adarta suka nufi ciki,sai dai me?

Suna shiga sukaga cincirindon mutane a tsakiyar farfajiya banda masifa ba abinda akeyi, Little ta kalli Nafi tace"ko me aka sake yi oho. "


Ji sukai da karfi wata tace " dan kut...... Uban yarinyar ai karyata zakuyi ba barinta zakuyi ba. "

Nafi kam ta rasa me yasa takejin gabanta na fad'uwa haka, jisukai ance " wai yarinyar ma daga ina take? Akan ke zaku yadda ta zauna a nan gidan? "
Little ce ta kalli Nafi yanzu kam sun gane inda maganar a dosa, Little ta kalleta tace " mu wuce ciki. "

Suna shiga ciki Little ta ajiye Nafi sannan ta fito tai gun Mumy.

A zaune taga Mumy tayi tagumi ga 'yan uwanta suma sunata magana, Little ta karasa ta zauna kusa da ita tace "Mumy wlh ciwo taji a dalilin neman yaya, ganin bazata iya takawa ba yasa ya d'auketa. "

Mumy tai ajiyar zuciya tace" Little ki fadama Nafi gobe ta shirya da safe a maidata makaranta saboda tsoron abinda mutane zasu mata dan nasan 'yan uwan maman Aneesa sarai bazasu tab'a barin maganar nan ba. "

Little tai shiru jikinta yai sanyi sosai, sai dai tana ganin hakan ne yafi sauki.


¤¤¤¤¤¤¤¤


A kachako kuwa d'an litti ya zake sosai yana aikin kasuwancin sa na babur, yana kuma jin dadin yanda uban gidan sa yake sanshi, fatanshi d'aya yai sauri ya kammala kud'insa ya taho kano neman Ashaf........

*THE INNOCENT TEAM*


*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*Wattpad As_AyusherMohd*



*Gaisuwa gareku 'yan sauyi, 'yar gaya, sankach, nagudu, sharubutu, Aisha Idris, Sub, Zee Sa'id and many more, tunda yanzu kun daina neman Aisha sai Zuciya to ga sakon Zuciya nan tana muku fatan alkairi....lol*

{ *31*}


Little jiki a sanyaye ta fito daga d'akin Mumy tai b'agarensu.

A zaune taga Nafi kan sallaya, Little ta karasa gunta tare da sama a kusa da ita, Nafi ta kalleta sannan ta kakaro murmushi tace " Little nayi dana sanin zuwa bikin nan."

Dafata Little tai tace " Laifinane dana d'aukoki duk da banga alamun kinasan zuwa ba."

Kai Nafi ta girgiza alamar a'a kawai zatai magana taji kamar intai magana kuka ne zai kufce mata.
Little ta d'au waya ta kira Ashraf, sai da ta kusa katsewa sannan ya d'aga tace " Yaya."

Daga can Ashraf dake zaune kusa da Habib yace " uhm ya akai? "

Kasancewar a kusa suke yasa Nafi tana iya jiyo maganar Ashraf, Little tace " dama fadama zanyi gobe Nafi zata koma inji Mumy."

D'agowa Nafi tai ta kalli Little, jitai Ashraf yace " to Allah ya kiyaye."

Little taso ya hana Nafi tafiya jin ya fad'i haka yasa jikinta yai d'an sanyi tace " Yaya wa zai maidata?"

A zuciye yace " da wani karambanin ne ma yasa ku d'auko yarinya tana makaranta? Sai kuje ku sami wanda ya saku ku tambayeshi."

Little zatai magana taji ya katse, jiki a sanyaye ta kalli Nafi wacce ke wasa da hannunta a zahirin gaskiya kalaman Ashraf sun mata zafi sai dai tasan koma meye ai laifin ta ne.


Ta kalli Little tace taimakamin dan Allah in kwanta."


Little ta kalli kafarta tace " Nafi ko muje Chemist? "

Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a tace "bafa wani serious bane. " a zahiri kuwa tanajin zafin gun sai dai bataso a cire handkerchief d'in Ashraf daga kafarta.

Little ta mike sannan ta shiga taimaka mata ta kwanta, idanu ta rufe kamar mai bacci, hakan yasa Little ta fito daga d'akin.


Tana fita Nafi ta fara zubar da hawayen dake cinta, Ashraf ta tuno sanda ya d'auketa, idanu ta runtse kalaman Ferry ta tuna data cemata san Ashraf take, Nafi ta share hawayenta sannan a fili tace " Ina na isa? In kuwa har haka ne lalai ina cikin gararin rayuwa."

Kalamansa na mota ta tuna dayace mata zai saketa in ta samu wanda takeso.


Ta dad'e tana hawaye kafin bacci ya d'auketa.

Washegari da sassafe kuwa Drivern Mumy ya mai da ta makaranta, ko Ashraf bata sa a idanta ba.

Nafi ta dage sosai da ta koma makaranta, ba wai a kan karatu kad'ai ba sai dai kullum suna tare da Ferry tana kokarin canza halayenta.

A wannan zuwa gidan datai lalai ta fahimci abu biyu, na farko Ashraf wasa kawai yake da ita da jawo mata tsana agun mutane bayan ba santa yake ba, na biyu kuwa lalai in har tanasan Ashraf ya fara santa sai ta zama mace daidai shi.


A can kuwa an gama biki lafiya ankai Amarya d'akinta, sannan kowa ya watse.

Anyi hutu amma Nafi ta kira Habib akan zata zauna a gidan Principal ya tambayar mata ita, saboda a lokacin hutun ta samu isashen lokaci na karatu, wannan jarabawar ita tazo ta karshe a aji batajin kuma za ta iya nunama Ashraf wannan dakikantar datai.

Habib ya tambaya, ba tare da wani dogon Nazari ba ta amince, bayan kowa ya tafi gida itama ta koma quaters.

Little taji ba dadi sai dai bayan Nafi ta mata bayani ta waya yasa ta gamsu.
Nafi ta dage sosai......


Shekararta d'aya kenan a makaranta, duk hutu ba ta wani zuwa gida, sai dai duk cikin hutu Little na zuwa ganinta da sakon Provision daga Mumy da kud'in kashewa.


A iya wannan Shekara d'aya ba shakka Nafi ta canza sosai da sosai, ita da Ferry kam sun zama Aminai sosai, sai dai in a b'angaren karatu ne kuma da Jibiya sukeyi.

Yanzu suna S1 Nafi ta canza sosai, bata tunani ko sha'awar zuwa gida duk da kuwa yanda zuciyarta take tsananin rashin Ashraf kamar ranta.


Yanzu sun shiga Ss 2 a a wannan lokacin ne kuma Nafi ta shirya dan zuwa gida, Little tace "wannan karan kam gaskiya sai Nafi tazo gida, dan akwai bikin kawar Little ko ince Aminiyarta da za'ai.

A wannan lokacin shekarun Nafi 18, duk da ba kiba gareta ba sai dai kirjinta ya cika da dukiyar fulani, Nafi ta goge sosai, kamar ba makarantar kwana take ba, komai nata tsaf dan in Little zata kawo mata kaya har da mayuka masu kyau take cewa ta had'o mata.

Nafi tana tsaye kusa da Ferry ga Jibiya a gefensu, Nafi ta kalli Ferry tace " Na nawa kikai?"

Ferry tai d'an tsaki tace " Ai Yaya Yusuf ya rainan hankali wai ta 7 dan tsabar rashin mutunci."

Nafi tasa dariya ita da Jibiya, Ferry ta had'e rai tace " kubarni da abinda ke damuna."

Jibiya ta sake dariya tace " lalai zakisha Fada'a gun Abba dan ni na 2 nai."

Idanu Ferry da Nafi suka zaro, Nafi ta kalleta sannan ta had'a hannayenta ta tafa mata tace " wow! Jibiya kina kasheni."


Ferry ta harareta tace " Zama ta raya ki, ke Feena na nawa kika ci?"

Nafi ta juya kai tace " Secret."

Ferry tai dariya tace " badai irin na last term ba na 12 ba?"

Nafi ta d'an rangwad'a kai cikin tsokana tace " na 8 nai."

Ferry cikin d'aga murya tace " WHAT?"

Nafi tai murmushi tare da ware takardar, murna suka shiga yi sosai, can Ferry tace " Kai naji dadi kin daina cin double number, amma da alama sai na dage kar next term ki dawo gabana."

Suka sakeyin dariya.
Ferry ta kalleta tace " Feena zakizo d'in ko?"
Nafi ta d'an juya ido tace " zanzo insha Allah amma banasan zuwa yayanki nanan."

Ferry ta harareta tace " Gaskiya Feena bazan juri wulakantamin yaya da kike ba, tunda yazo visiting ya nuna yana sanki amma kike wani disgashi, in bakiyi wasa ba har gidanku zan kawoshi."

Nafi ta zare ido tace " wa? Rufan asiri."

Jibiya tace " kema kinsan bazata yarda wani saurayin ya bita gida ba saboda sanda takema yayan nan nata."

Tsaki Ferry tai tace " wlh Feena in har kika bari ya gane kin mutu akansa haka lalai sunanki sorry."

Nafi ta tsuke baki tace " Ke nima yanzu ba daina sanshi yaushe rabon ma da inganshi, kila ma ko a hanya naganshi bazan ganeshi ba."

Ferry ta d'aka mata duka tace " ni zaki maida gara? Kullum fa sai kinyi labarin yayan nan naki."

Nafi zatai magana ta hango kamar Little ta fito daga wata zukekiyar mota, tana sanye da sun glass tayi kyau sosai da sosai, Nafi tace " anzo d'aukana."

Nan suka mik'e suka taimaka mata da kayanta, Ferry tundaga nesa tace " Kai Feena gaskiya Little tana kasheni da gayu, ki bari nika inje gida dattin makarantar nan ya fita daga jikina lalai zan tsorata maza."

Nafi tace " Nima ki bari sai nazo gida kin ganni kiga yanda zan kasheki da nawa gayun."

Dariya sukai harda tafawa.

Sun karasa gun, Little ta karaso cikin murna, ta rungume Nafi.

Sunsa kaya a motar sannan Nafi ta leka dan ganin wanda ya kawo Little.


Habib ya sakar mata murmushi yace " Tantancewa akeyi ne?"

Murmushi tamai itama tace " Ai ba sai na tantanceba dama can jikina yaban kai ka kawota."

Nafi kenan ba shakka kim canza wato yanzu bakya kunyar maidamin kalamai na."

Ta d'aga kanta batare da ta amsa mai ba, sannan sukai sallama dasu Ferry ta amshi number Ferry da jibiya tasa a wayar Little.

Nan suka shiga mota, Habib jefi jefi yana kallanta ta glass d'in mota, ba shakka yarinyar nan ta girma, ganin haka yasa Nafi ta matsa daga setinshi ta koma ta can b'an garen.

Little ce tace " Nafi yau ji kad'ai nasan farin cikin danakeyi, nayi missing d'inki sosai."

Nafi tai murmushi sannan tace " nimafa kawai daurewa nakeyi jinake kamar na biyoki inkika zo ganina."

Little ta harareta tace " ba wani nan kedai kawai kinzama 'yar college tafi gida dadi."

Dariya suka d'anyi Nafi ta juya tan kallan window.

Little ta juyo ta kalleta tace " Nafi au Feena baki tambayi ina yaya ba, ko visiting nazo bakya tambayarsa."

Habib ne yai katsal yace " ita meya dameta dashi bayan yayi aure yamanta da ita."

Har cikin ranta Nafi taji haushin maganar Habib amma sai ta daure tace " Ya Habib kenan, dama can ba wani shiri muke dashi ba balle ya nemini."

Little ta kalleta tace " Nafi yanzu kin daina shigar ma yaya ne?"

Ta tab'e baki tace " ni a wa? Dama can bawai shigar mai nake ba kece baki fahimceni ba, ai Yaya Neesa itace zata shigar mai bawai ni ba."

Habib ya saki dariya yace " Gaskiya ne Feena gwara ki fara bayyana musu komai."

Nafi ta kwantar da kanta akan window tare da lumshe ido, tace " Little bacci."

Little ta d'an had'e rai tace " shikenan nayi shiru."

Habib ya kalli Little yace " Ai cewa tai bacci bawai kiyi shiru ba."
"Hmm ai tun da dadewa na gane Nafi au Feena in batasan magana sai tace wai bacci."

Habib ya juyo ya kalli Nafi sannan yace "yarinyar nan ta canza dayawa."

kai little ta jinjina tace " ai naji dadin makarantar nan."

Haka sukai ta maganganunsu itakam tana kwance tana jinsu a cikin zuciyarta take magana " Yaya ba sai ka basar da ni ba, nafi kowa sanin rashin matsayi danake dashi agunka, kila ma inya ganni bazai ganeni ba, ba komai Allah ya kawomin wani mai sona nima inyi kokarin ganin na yakece wannan soyayyar da take one_side."


Nace Uhmmmm zaki iya????.


*THE INNOCENT TEAM*


*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

©
*na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*Wattpad As_AyusherMohd*


{ *32*}

Sun isa gida Habib ya gangara yai parking, sannan suka fito, Nafi ta rataya jakar bayanta uta kuma Little ta ja wo trolly d'in ta.
Habib ne ya matso kusa da ita yace " Gimbiya Feena kawo in tayaki mana. "

Ta kalleshi sannan ta kalli kanta tace " da me fa? "
Nuna mata jakar bayanta yai, tai murmushi sannan tace " ni ai ba kaya na d'auka ba Little ce mai kaya, da alama baka kula ba. " tana fad'a tai gaba.

Habib ya bita da kallo, gaskiya yarinyar nan tayi, shi dama tun tana yar kauyenta burgeshi takeyi.

Little ce ta karaso tace " yaya mun gode."
Ya rufe ido tare da yin mika yace " Princess na gaji. "

Ta kalleshi cikin kulawa sannan tace " yaya kaje b'angaren su Asim ka kwanta. "
Kai ya girgiza mata yace " a'a gida zan wuce, ai tunda Ashraf yai aure na daina kwana a nan gidan. "

Kanta ta sunkuyar kasa alamar rashin jin dad'i ya matso tare da sa yatsar sa ya d'ago kanta yace " sai munyi waya."

Kai ta d'agamai, ya mika mata key yace " Ungo kiba Ashraf zan d'auki motata nai gaba nima."

Ta d'agamai kai, tana kallo ya koma ya shiga motarsa yai gaba.

Nafi kam tana shiga d'akinsu tai wani ajiyar zuciya tace " Kai nayi Missing d'akin nan. "

Kaya ta shiga cirewa ta d'aura karamin towel sannan ta fara ninke kayan makaranta.
Little ce ta shigo, ta kalleta cikin shagwab'a tace " kina gani Feena har Ya Habib ya tafi? "

Nafi ta karasa ninkewa sannan tasa agun kayan datti ta kalleta tace " Little wani irin so kikema Ya Habib? "

Little tace " so mai yawa wanda yanzu ya zama jinin jikina."

Nafi ta tab'e karamin bakinta tace " Shifa? "
Little ta fad'a kan gado, ta d'an mirgina tace " Shifa haryanzu a kanwa ya d'auken."

Nafi ta girgiza kai a ranta tace " Little nima matsalar dake damuna kenan, gwara kema banaji kinajin rad'ad'in da nakeji in na tuna Ashraf fa mijina ne sai dai yamin nisa. "

Toilet kawai ta shige batare databa Little amsa ba tai wanka.
Ta dad'e tana gurza jikinta a cewarta dattin makaranta ya fita.

Sannan ta fito, bataga Little a d'akin ba hakan yasa ta zauna a gaban madubi ta fara goge fuskarta da cleanser.

Hoda kawai tasa batai wani kwalliya ba, sai dai tayi kyau sosai, ta mike kenan sai ga Little ta shigo ta tiren Abinci, Nafi ta kalleta tace " Little ina kayana? "

Little ta bud'e mata inda ta jera mata nata kayan, Nafi tai murmushi ta sani sarai daba dan Little ba lalai da zaman gidan nan ya gagareta, nan ta zab'o wata atamfa riga da siket, mamaki tayi dataga tana sa kayan da kyar, Little tai dariya tace " ai dole kigafa dad'ewar da kikai bakizo ba, ga yanzu kin kara girma bawai kiba ba ina nufin kin girma ta sama da kasa. "

Nafi ta harareta tace " lokacin girman ne yazo, da alama Little sai kin ban aran kayanki inyaso sai mukai a bud'amin nawa anjima. "

Little tace " ki d'auka mana, sannan kinsan fa yau da yamma zamu kamun Yusra sai ki gwada kayan ko da yake cewa nai a kiki daidai ni kawai dai karya kai nawa fad'i ne saboda nad'an fiki kiba. "

Nafi ta saka wata doguwar rigar material sannan ta zauna suka zuba abinci suka faraci.

Nafi ta kalleta tace " Little ya gunsu Amarya?"

Little ta tab'e baki tace " hmm ke dai bari Nafi bayan kin tafi biki an gamashi lafiya sai dai a ranar da aka kaita sukai fad'a kaca kaca. "

Cikin mamaki Nafi tace " fad'a kuma? "

Little taja wani tsaki tace " Ita wai a dole a daren takesan ya bata wasiyyar mahaifinsa shikuma yace ba wanda ya isa ya sashi ya bada abinda baiyi niyya ba. "

Nafi ta tab'e baki tace " ya suka kare to? "
"Hmm kedai bari Dady ne yaje da kansa ya sasanta yace Yaya yai hakuri gobe ya bata tunda dai hakkinta ne, ita kuma karta kuskura ta sake tambayarsa. "

Nafi ta d'an juya kai tace " Na d'auka tanasan shi dayawa, meye nata na damuwa da abinda baiyi niyyar bata ba? Indai har tana gudun b'acin ransa? "

Little tace " Zigata akai ya Asim da Umma."
Nafi ta d'anyi karamin tsaki tace " san da takemai baiyi nisa dayawa ba kenan indai har za'a zigata akan dukiyarsa."

Little tai ajiyan zuciya, Nafi tace " yanzu fa? An bata ai nasan hankali ya kwanta. "

Little tace "Hmm Yaya wai cewa yai wasiyyar dama mahaifinsa ne yace aba matar sa ta farko million d'aya ko ince wai ya ajiye kud'in a banki, to Yaya yabata kud'in sai dai Umma tace itakam gaskiya bata yarda wai kud'i kawai akace ba."

Nafi ta had'e rai tace " shi kuma yayan me yace? "
"Uhm bai kulasu ba kinsan shi ai. "
Nafi ta kara tab'e baki tace " Allah ya sauwake. "

Little ta amsa da Amin sannan ta d'aura da cewa " kigama muje ki gaida Mumy sannan kije kiga b'angaren Amarya. "

"wa? Bada ni ba, inje in musu me? " sukasa dariya a tare.


¤¤¤¤¤¤¤¤

A b'anagren Ashraf kuwa ya nemi aiki yanda kowa yake nema ya kuma samu ba babban aiki bane

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment